MAH~NOOR🌹

By AfricanQueen300

85.4K 8.1K 1.3K

Free book I grew up with this, I had best friends became enemies and then best friends again. I love it now... More

Prologue
destinations
Welcome to Hamoud Boualem Company...
Meet Mr Hot Guy
She take my position
Hamoud Boualem Family
Promotion
Personal information
Sisterhood
Big Mistake
Dreams
MR Arrogant
hateatfirstsight
Courage
My Nikkab
The Name
hypocrisy
Kidnapped
Escape
Injured
Exclusively
Approched
Mine
My Favorite
Silent
You are my Destiny
i'm in luv
Contract Marriage
Confessing
Bonus page
Tracking
stupidly
Chased Game
The Game is Over..
My wife...
Hopefully
Am sorry
Other side
The Family
Faruq
Happy end.... Mr And Mrs Mahir Hamoud Boualem
Lover

Interview

1.6K 227 27
By AfricanQueen300

https://my.w.tt/oCPVBn764bb
MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 1️⃣1️⃣
MrsUsmaa400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM
#Interview
Idanun  shi lumshe yayi cikin nutsuwa, yana jin wani irin yanayi yana shigar shi, ba zai ce na Meye ba. Ganin bai da hujjar sawa kanshi damuwa yasa shi bude shanyayyun idanun shi masu kama da wanda ya kwankwadi kayan maye.

                A nutse ya dauki tap din shi ya shiga nazarin abinda zai kai shi Yola, tare da jin a ranshi koda ya isa yana bukatar yaji wani irin yanayi kamfanin su yake ciki. Kuma ya kome yake tafiya mishi.

      •••
"Wai Noor me ya sa kike haka ne? Don Allah ki tashi muje kinji. Yau baki daya baki da kuzari!"
   
       "Baby Queen! Jiki na ne babu dad'i, kawai kije ni ba zan sami zuwa ba kuma ki gayawa Badar."
  Kura mata ido tayi sannan itama ta koma bakin gadon ta zauna tare da cire yar karamar fashion hijab ɗinta, ta zauna tana kallon Noorh din.
"Ok nima na fasa zuwa."

"Don Allah tashi kin san yau mr Mahir zai zo kuma koda ban je ba, babu matsala. Ke kuma Mr Nazzir zai damu akanki."

    Cikin sauri ta d'ago kanta tana kallon Noorh, sannan tace mata.

     "Noorh! Kin hakura mr Nazzir din ne?" Ta tambaye ta cikin tsoro.
Tashi zaune Noorh tayi tana kallon ta, sannan tace mata.
"Yanzun banda b'atar basira dama me zanyi da shi? Ai sai ke. Ni bana son irin shi.
           Mijina Ready made ne, mijin da zan aura ya kere sa'a'o'in shi, first Class Handsome guy ne, irin me zafin nan, dai dai irina wanda bai damu da kyale kyale mutane ba."

   "Toh idan kin gan shi kece zaki fara Crushing din shi ko shi zai yi crush dinkin.?"

       Tashi zaune Noorh tayi tare da rungume kafaffuna, tana murmushi cikin wani irin ƙasaitacciyar murmushin da yaki barin fuskarta, lumshe idanun ta tayi tare da bude shi akan Tasleem. Sannan tace.
"Tasleem! A yayinda zamu hadu, zai zama na rana ce ta musamman. Ranar sai ya kasance mafi daraja a gare mu, domin zai zo mana a matsayin our first meeting, zai zama ranar da yafi Kowani rana Fantastic."
Ta faɗa cikin dariya.

       Jikin Tasleem ne yayi sanyi sannan tace mata.
"Ke baki da ra'ayin soyayyar shan minti ne, kafin aure."
Sauka tayi daga gadon, sannan tace mata.
"Ai idan Kinga namiji ya tab'a ni, toh ki yarda akan kaddarar ce ya gifta tsakanin mu, bayan haka bana fatan wani ya tab'a jikina. Ke bana fatan wani ya tab'a hijab dina.
      Ke nifa saurayi ganin asara nake nace mishi ina son shi, duk maneman da nake, bana cewa ina son su, haukar su suke kawai.

       Sabida banyi imani da soyayyar duniya a, dan haka manta kawai taso muje."

     Mikewa tayi cikin sauri, suka shirya. Koda suka iso falo babu kowa haka suka tab'a abinci sannan suka kuma fita daga gidan.

     A hankali Tasleem take jan motar. Har suka shiga kwantar da zata kai su kamfanin kawai, suka daki motar kamfanin,  cikin masifa Tasleem ta fito tana bawa driven motar hakuri, basu bude motar Ba, kuma bai sanya sun tafi ba. Abinda ya bani haushi, ina zuwa na make glass din motar, sauke glass din motar aka yi. Na zubawa driven motar  ido.
"Toh ishashe zaka bamu hanya mu shige ko dai na kara dukar motar ku, ka zauna da uban gashin baki kana hura hanci kai gaka nan ishashe.

     Tabbatacce. Toh bamu hanya ko kuma na fasa tayar motar. Wallahi ka godewa Allah ban iya mota ba, da ka shiga uku sai na budeka da kura. Dube shi kawai katon mutum da kai."

    Can bayan motar ta jiyo wani murya yana cewa.
"Wali ya katsaya?"
"Ok sir naji kace na tsaya ne."
Siririn tsaki ta ja, sannan ta bar gurin su,  ta nufi motar su tana cewa.
"Ke kiyi overtaking din yan banza, dan na lura akwai wani kazan gidan gona ne a cikin motar."

   Dariya Tasleem tayi tare da jan motar a fisge, tana zuwa kuwa tayi wani irin shan kansu, garin kauce wa, sai da drivan ya buge kanshi motar kamar zata kifa dasu. Shima Mahir da yake bayan motar sai da ya kusan fasa hancin shi.
Da sauri ya dakatar da Wali.
"Sauka mu shiga asibitin kamfani."

  "A'a sir zan iya tuka motar hancina ne kawai yake jini, amma zan iya fa." Duk da wali babban mutum ne bai hana Mahir rufe shi da fada ba, akan lallai ya sauka shi ya ja shi. Aikuwa haka ce ta faru, ya sauka Mahir ya ja motar, suka nufi cikin kamfanin ya wuce da Wali Clinic aka duba shi. Sanan shi kuma ya wuce cikin kamfanin a wani irin shiga na niman aiki taga jan magajan.

       Domin anyi sanarwan za a debi sabin ma'aikata, da yazo parking spaces ya hango motar da tayi musu tsaya, takawa yayi ya saka wani karfe da ya gani a gurin ya daki tayar motar, sai da ta fashe. Sannan ya shige ran shi na kunna.

        Yana son yaga yadda ake diban ma'aikata ne a kamfanin shi. Koda ya shiga, aka nuna mishi idan zai zauna, gashi ya b'adda kama sosai, har wani kasumba ya tara, dayawa basu san tsarin ba, dan haka sun dauka kawai za ayi masu tambayoyi ne, yana zaune wasu yan mata gudu biyu daya tacewa daya.
"Me yasa kika zo niman aikin?"
Dariya dayar tayi, sannan tace mata.
"Saboda bani da yadda zanyi, dole na amshi aikin kafin na samu wanda yafi wannan karki! Aikin gwamnati yana wuya a kasar nan, kuma ina da mahaifiya mara lafiya, ga kanena suna sun zasu lalace saboda rashin kulawa, Kinga nan kuma naji aikin su na da kyau, amma koda kabar aiki babu pension da garatuti, zanyi hakuri na rike wannan, idan yaso ko koyarwa sai na nima a makarantar gwamnati."

"Ayya! Kinga kuwa kusan nima haka ce, amma Ni mijina nane babu lafiya, sanan kuma matsalolin rayuwa, ya sani zuwa niman aikin..koda basu biyan pension zan rike shi haka, baka san inda rana zata fadi ba!"

Haka suka yi tattauna, tare da bawa juna shawara, can gefe  wasu samaruka ne, suke tattauwar su, dayan yace.
"Kasan Allah da zaran na fara aiki zan fantsama gari fa"
"Ni kuwa idan na fara aikina, kafin naci kudin su, sai na bawa kamfanin gudunmawa ta sosai, domin zan tsaya ka in da na in, nayi musu aiki tukuru,

        Nasan cewa gumina naci ba haram ba, nayi alfahari da abinda na tara, wannan shine abinda ya kawo ni, nayi aiki da kamfanin da zata yi alfahari dani."

       A gefen Mahir wata mata ce, ganin yadda yake a dame, tare da rubuce rubuce, yasanta kallon shi.
"Malam! Ka nutsu sai b'ata takardan kake, kuma shi wannan yanayin na lallai bane ni na samu aiki amma kai sai ka samu, ka na al'amarin Ubangiji ba ayi mishi dole, ka nutsu Insha Allah zaka dace, ka bar damun kanka. Yanzun zasu fara diban mu."

   Murmushi yayi sannan yace mata.
"Yanzun idan baki samu aikin ya zaki yi?"
Dariya tayi sannan tace mishi.
"Ya kuwa zanyi ban da Nagodewa Allah nasan yana sane dani."

          "Tab wallahi bazan iya daukar wannan renin hankali ba, muzo tun safe ace ba a ɗauke mu ba, ai akwai renin hankali."
Inda wasu matasa. Yana kallon su. Shidai yana ta wasa da biron hannun shi, can yace musu.
"Time Up"
Fitowa Wasu mutane suka yi daga Office din CEO,  tare rigar saman kayan suiter din shi, me zubin Overoll, ya ya mika musu takardun hannun shi, tare da cire katon madubin idanun shi.

       Sannan ya cire gashin afro da ya saka,  a hankali ya koma ya zauna ya cire takalmin kafarshi. Sannan ya amshi kayan hannun su ya saka a hankali yana gyara wuyar shi da zaman tie. Din shi,

         A hankali Mr Nazzir da ya iso gurin, ya tawo da sauri ya rungume Mahir yana faɗin.
"Barka da zuwa Lion Man"

       Tafawa suka yi tare da juyawa suka bar gurin, Babban sakataren Mr Nazzir yace musu.
"An gama interview. Kuma ya dauki wanda suka dace, sauran kuma yana baku hakuri."

A hankali aka fara kiran sunan su, mata na farkon nan an dauke su, haka matar da ta bashi shawara an dauke ta, daya matashin da yace zai yi aiki domin gina kamfanin ta samu cigaba an dauke shi, ya dauki mutanen da suka dace, sauran muka ya basu hakuri tare da cewa a basu wani abu da zai sanya  ba zasu yi danasanin zuwan su ba.

        A bakin wani kasaitaccen office, suka tsaya sannan Badar da Noorh suka iso, mika almakashi tayi bata damu da ta kalli me ake yi ba, hankalinta na kan wayar hannunta, ya  yanka
Zaren Sauran staff Officer suna tare a gurin, bude mishi office din akayi yace.
"Wowwww! Tiger. Haka ka gyara min Office din"
"Abinda yafi haka ma, zanyi Lion Man!" Dariya aka saka shi kuma ta sake murmushi, daga nesa take son ganin waye ya mallaki wannan muryan wanda daga jin  shi sai da ya karya mata zuciya. Kokarin duba shi take, amma bata ga fuskar shi ba.

   Karshe haka ta hakura, amma tana iya hango kwantaccen gashin kanshi har keyar shi, ya juya baya ana tattauwar dashi.

    ..karshe rufe kofar akayi inda suka shiga tattaunawa a officen sun shi,  su kuma suka dawo. Zama suka yi ita da Badar.
"Noorh! Lokacin yayi fa, sannan akwai wani abu da na gani yanzun lokacin da Mr Nazzir yake gabatar da wasu files ga Mr Mahir, kuma ban sani ba. Ko na meye ne domin domin jiya bayan fitar ki naga mr Jecob yazo gidan Mr Mahir.

      Abinda na sani duk inda mr Jecob yake babu alkhairi a gurin, mutum ne da yasan kan shedancin."

    "Toh ni meye nawa a cikin wannan al'amarin saura wata uku na gama abinda ya kawo ne don Allah karka sanya ni cikin damuwa."

A hankali ya maida kujeran shi yana fuskarta ta.
"Ban nemi ki tayani dan na salwantar da rayuwar ki ba, nayi haka ne domin kane na guda biyu, da suka rasa rayuwar su sabida gurbattacen lemon da aka fitar daga cikin kamfanin.

       Kiyi nazari sosai, ba iya giya ake sarrafawa ba, sabida tsadar kayan sansu, a wannan shashin akwai inda ake sarrafa, gurbattacen lemon kwalba, a kara musu wasu sinadirai. Nasan kina da kima, kuma kina da kwarjinin da zai sanya kafin ayi zargin ki zai dauki lokaci, please ki bani hadin kai. Dole muyi aikin nan tare don Allah."

   Shiru tayi tana kallon shi sannan tace mishi.
"Zanyi amma zan boye kaina, sabida ina tsoron matsala."
"Insha ALLAH babu matsala." Da haka suka yi ta tattaunawa har suka gama, sannan Tasleem ta shigo kanta na rawa. Ta nemi guri ta zauna, sannan ta fara yatsina fuska, tana cewa.
"Kinsan me?" Tayi magana cikin wani shegen yauki. Girgiza mata kai  Noorh tayi sannan ta cigaba da cewa.
"Kinsan Dad ɗin Baby Naz shine me kamfanin nan, toh wai bro din Baby naz yazo, shine Baby yake gaya min, wai yazo cin Arziki ne"

            Cikin sake gwiwa Badar yace mata.
"Toh Queen Tasleem! Hamoud Boualem Company na Mr Mahir  ne, da kanen shi kar wani Shashanci ya kuma kwasar ki, ki gayawa wani wannan shirmen, ba Nazzir ba uban Nazzir cin arzikin Mahir yaƙe, na lura baki san inda kike ba, kina cikin kamfanin da d'aga murya idan kayi kora ne, balle kuma wani abu ya hada da CEO ki je ki tambaya shi idan zai dauki ma'aikata, Interview na musamman yake kuma a shekara, sau daya yake ɗaukar mutane kamar yadda yayi yau kuma kowani shekara da yadda yake ɗaukar su."
🤣 Baby Queen baki ya mutu 🙄
Jikar Hauw karki kuma damu na gobe babu typing 😠😡 domin basu Vote wallahi na gaji

Continue Reading

You'll Also Like

277K 17.7K 48
The feeling of being abandoned by one's own family was not unknown to Aadhira. She hates her family for abandoning her when she was only a newborn, l...
38.8K 1K 20
Isabella Rose Ivy Valencia-Moretti, the only girl born in Italian Mafia family after so many generations. Not only she is the princess of Italian Maf...
161K 7.6K 28
Hooked onto drugs, no family, no guidance or sanity until she met HIM. Cover Creds: @Triceynexttdoor ❤️ -BLICKY.
504K 11K 51
Two girls are exchanged at birth and are given to the wrong mothers and after 13 years the truth comes out Rosabella Rossi is different from her sist...