MAH~NOOR🌹

By AfricanQueen300

87.2K 8.2K 1.3K

Free book I grew up with this, I had best friends became enemies and then best friends again. I love it now... More

Prologue
destinations
Welcome to Hamoud Boualem Company...
Meet Mr Hot Guy
Hamoud Boualem Family
Promotion
Personal information
Sisterhood
Big Mistake
Dreams
Interview
MR Arrogant
hateatfirstsight
Courage
My Nikkab
The Name
hypocrisy
Kidnapped
Escape
Injured
Exclusively
Approched
Mine
My Favorite
Silent
You are my Destiny
i'm in luv
Contract Marriage
Confessing
Bonus page
Tracking
stupidly
Chased Game
The Game is Over..
My wife...
Hopefully
Am sorry
Other side
The Family
Faruq
Happy end.... Mr And Mrs Mahir Hamoud Boualem
Lover

She take my position

2K 179 33
By AfricanQueen300

https://my.w.tt/aRlDAIh8Dbb

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 0️⃣4️⃣
MrsUsmaa400
Free book
For You Jikar kulu
I have many problems in my life...But my lips don't know that' they always smile..

BISMILLAH RAHAMANIH RAHEEM

~#shetakemyposition~

      "Kun fahimce ni?" Ya tambaya cikin dakakkiyar murya.
"Yes sir"
Duk muka amsa, har zai wuce ya juyo tare da kallona, yace min.
"Are you ok?" Jinjina mishi kai nayi, ina kallon yadda Tasleem take harara na, ya sa kai zai fita. Yace.
"Tasleem Elhussain Jimeta, ina jiran ki" sai nan naga fuskarta a sake, tabi bayan shi, har office din shi, tunda ya bar gurin matan suka shiga kananun magana, ina jin su ban kula su ba. Hayaniya ce bana so a rayuwata. Shi yasa nayi banza dasu.  Zuwan Badar ya sani mik'ewa muka fito, zuwa inda zamu zauna. Kallona yayi sannan yayi magana kasa kasa.

"Noorh! Ki tsare kimarki, karki yarda da MD, ki kame kanki. Please karki zama balagazza shaddar kasuwa, ki zame macen da ke namiji zai bi ba kece zaki bishi ba don Allah, wallahi kallon kanwata nake miki."
Gyad'a mishi kai nayi tare da cewa. "Insha Allah zanyi yadda kace" yadda nayi maganar ne ya bashi dariya a dan tsorace.
"Karki damu, babu abinda zai faru" daga haka ya shiga min bayanin yadda kome yake tafiya a Office din shi yace min. "CEO baya nan, yana kasar Qatar, akan kasuwancin shi na man fetur, sannan wannan kamfanin about mutane dubu goma suke aiki a cikin shi, sannan akwai leburori masu kananun aiki. Mr Mahir bai da matslar kome, sai dai bai da dadin zama, har gwara MD akan shi. Sabida matukar yana nan toh wallahi kullum sai yayi kora.
              Yana karban gyara amma banda na mace, matukar zaki mishi gyara koran ki."
       "Ya Badr gyara koran su zai yi, domin babu abinda ya dame ni dashi" na fadi haka a sanyayye, kallona yayi sannan yace. "Toh naji koran su zai yi!"

Nan muka Cigaba da hidimar aikin.
         ★
   "Da nace karki kuma mata magana shine kika mata."  Ya cire rigar shi, tare da zama a kujera yana balle cire suit din jikin shi yayi, sannan ya shiga zare neck tie din shi, ya kalle ta tare da kiran ta da hannu. "Ki min tausa"
Wani irin girma kanta yayi tare da wani bada sauti na musamman, yau ita ce zata yiwa daya daga cikin young billionaire boys na naija. Jin wani irin karsashi ya shigeta, a hankali ta isa bayan shi, tare da fara mishi tausa, a sannu a hankali. Take mishi, yana aiki tare da lumshe idanun shi. Karar wayar shi tayi wacce take saman table din Office din, ya kai hannun shi ya d'auka.
         Lion Man! Ya gani, murmushi ya sake sannan ya kunna tare da sakawa a amsa kuwa.
"Barka dai Lion!"
"Tiger!" Ya kira sunan cikin wata irin kasalalliyar murya, juyawa yayi ya kalli Tasleem, da sauri ta tashi ta koma daya daga cikin kujerun cikin office din, ta zauna wasu gray colour, ta daura daya akan daya.
"Lion! Kana bukatar wani abu ne?"
         Shiru yayi, yaki bashi amsa. Sai da ya kuma maimaita abinda yace sau uku kafin yace mishi.
"Please ka daina min ihu,"

       "Ok what do u need? Ko kana bukatar zafaffan Yan mata zasu jiyar da kai dad'i." Wani irin iska yaja tare da yaji, sannan yace.
"No need, yan bautar ƙasan sun iso ko? And ka zab'a min daya a cikin su.  Wanda zai taimaka min da aiki Insha Allah ina hanya kowani lokaci."

       "Ok boss!"
Karamin tsaki yaja, jin ya kira shi da boss. Yana kashe wayar ya kalli Tasleem, yaga itace ta dace da Office din Mr Mahir, murmushi yayi sannan yace." Hey" da sauri ta mike tare da isa gurin shi, ta Cigaba da aikin, yana wani juyar da wuyar shi

         Zuwa gabanta yayi tare da zuba hannun shi duk biyu a aljuhun wandon shi.
"Zaki iya aiki da kuwa, akwai brother na, da zai dawo dan haka ki nutsu karki janyo ya kore ki "

Gyada mishi kai tayi, sannan ta juya zata fita yace mata.
"Kice Aeesha tazo."

     .... Ciki ciki ta amsa mishi, tana me fita a ranshi yace.
"Hmm!"

Muna tsaka da aiki tare da Badar ta shigo, tsaki tayi sannan ta juya ta zauna tare da cewa, "kije Mr Nazzir yana kiranki."
          Mikewa nayi na fita, kallonta Badar yayi yace.
"Kina kishi da ita ne?"
Wani kallon banza tayi mishi tare da wani gatsine face, kafin ta Cigaba da abinda take.

.. ina shiga ya kalle ni, tare da nuna min gurin zama na zauna.
"Ko zaki zauna a Office dina kina tayani aiki?"

      Shiru nayi kafin nace mishi.
"Kayi hakuri! Ba zan iya zama da wani namiji a guri guda ba, domin duk yadda aka zauna mace da namiji sai ka samu na ukun su iblis ne! Am sorry service muka zo ba kebewa ba!"

Ina gama gaya mishi haka na mike tare da barin Office din. Murmushi ya sake tare da cewa.
"Dama nasan da haka."
Tunda na koma muka cigaba da aiki, tare da nuna min wasu abubuwan na kamfanin, har aka yi break, muka nufi gurin cin abinci. Ban iya cin kome ba, sabida da kunya nayi ta cusa abinci a gaban mutane. Abinda bai tab'a faruwa ba yau shi ya faru. Zuwan Mr Nazzir gurin cin abincin.
.     Ya amso shima ya zauna a kusa da ni,
"Ko baki murna da gani na ne?"
"A'a," na fada da sauri."toh kici mana" yace min,
"Ban iya cin abincin a gaban jama'a bane." "Ok, idan babu kowa zaki iya ci?"
    "A'a ba sai haka ba, zan ci a Office."
"Toh muje office dina!"
"No...no, nan ma yayi."
D'ago kai yayi sannan ya kira wani security yana tawowa ya sunkuyar da kanshi, suka yi magana.
Mutumin na d'aga kai, ya kalli yadda kowa yake juyawa yana kallon mu, sannan ya bude murya yace.
"Kowa ya bar nan, kuje Office din ku, ko gurin da kuke ku ci abincin ku, ku bar nan cikin minti biyar."
     Cike da mamaki, ake kallona, sannan suka shiga daukar abincin su. Suna fita, irin ransu a b'acen nan kallon zaki sani Tasleem tayi min.

        Nima mik'ewa nayi ya rike tiren abincin yana faɗin.
"Zauna muci."

"Amma!"
Hannun shi ya saka a baki tare da lumshe idanun shi, dole na zauna na fara cin abin ba wani abu bane, snacks ne sai namar kaza da kuma juice, ganin juice din shi nayi ba irin namu ba, dan haka ma ɗan saci kallon goran, na cigaba da cin abincin, guda daya naci. Sannan na goge bakina na mike ko inda yake ban kalla ba, na barshi zaune.
"Hotness! Ina zaki?"

     Cak na tsaya, kafin na juya tare da nuna mishi agogon hannuna, min cinye lokacin mu. Har mun shiga na aiki. Table baki yayi tare da mik'ewa, ya biyo ni.
"Baki ce min kome ba!"
"Da aka yi me?"
Na maida mishi tambayar shi,
"Baki tambaye ni, Number na ba"
"Bashi ya kawo ni ba! Abu nazo yi, kuma idan na gama zan kara gaba."
"Tare zamu kara gaba?"
Juyawa nayi na kalle shi, sannan na wuce inda zai kai ni office din Badar, muka shiga aiki, shigowa yayi yaga yadda nake mai da hankali ga bayanin da Badar yake min, a hankali ya iso tare da sunkuyawa yana kallon laptop din, sannan ya tab'a wani gurin, yadda ya kwanto ya bayyana yasani jan kujeran kamar zai fadi.
"Sorry! Kimar hijab dina nake karewa;" na fada mishi haka a hankali, lokacin da ya juya yana kallona, murmushi yayi sannan yace.
"Karki damu!"
Tab'a mouse na laptop din nayi, tare da kai arrow din side din da yace ai yarda a shiga ba, yana ganin haka ya yayi maza ya kai hannun shi kan nawa, da sauri na juya. Girgiza min kai yayi, janye hannun nayi tare da yarfe hannun. Kamar na tab'a wuta,
"Bana son ki tab'a gurin, tsohon gurin sarrafa abubuwan kamfani ne yanzun baa cika amfani dashi ba. Badar kayi mata bayani, har da Tasleem yadda zasu fahimta."

Yana gama fadar haka ya fice abin shi,.yana fita,.itama tana fita.
"Noorh, kin san Allah zaki b'allo min August, wannan side din ba'a shiga, sannan na gaya miki karki na barin yana tab'a ki, Kinga kamfanin nan, mugun guri ne! Mutane da yawa sun mutu sabida wannan kamfanin, yan bauta ƙasa irin ki sun mutu, sai samun gawar su ake a gidajen su.

       Noorh, jami'an sirri sun mutu, kuma su kan su kamfanin suna da goyan bayan gwamnatocin kasar nan domin idan aka zo campaign, suna bada gudummawar su na fitar hankali. Sabida asalin mai kamfanin yayi hidimar siyasa, kuma har yau ana siyasa a cikin gidan su. Dan haka ki kula koda anyi wani abu b'oyewa suke."

    "Amma kasan abin shan mu dana shi ba ne iri daya bane. " Buge min baƙi yayi, tare da magana kasa kasa.
       "Baki da hankali, kiyi kokarin dakatar da nazarinki idan ba haka ba, sunanki gawa."

    Ya faɗa min tare da Cigaba da aikin shi, shiru nayi tare da rike goshina ina kara tunanin rubutun jikin lemon kwalbar, ina kara juyar da lumshashen idanuna, a hankali na sauke akan  da sauri na bude idanuna, tare da kallon shi kasa kasa nayi da muryana kamar karyaciya nace.
"Abin."
"Hm" yace min tare da mik'ewa ya nufi wani daki, bai fito ba sai karfe sha biyu saura, yana fitowa ya kalle ni.
"Sannu!"
"Yawwa!". Can ya cigaba da abinda muke, ban ga Tasleem ba har kusan karfe ɗaya muka fita sallah, muna dawowa, na sameta tana wasu dube dube a wayarta.

"Tasly!" Ture hannuna tayi, cikin wani irin kallo, sannan ta mike tana faɗin.
"Karki min karuwanci,  karuwa kawai. Da kika tafi office din MD."
Ture ta nayi cikin bakin ciki, tare da nuna ta da yatsa, kawo hannu tayi zata murɗe min yatsar na kama hannunta, na juyar da ita, sai shegen baki babu karfi.
"Karku kuma kira na da kalmar karuwa, dan wallahi zan baki mamaki, ni ban iya niman maza su soni ba, halitta tace, duk wanda ya zauna dani sai ya bukaci haka a tare dani.

   Sannan da kike cewa, naje office din Mr Nazzir, kece zaki gayawa kanki haka, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, yace idan dayan ku ya jefe ku da kalmar da ya kasance muzanci ne da b'atanci, kuma bai nemi yafiyarku ba, idan har baku aikata ba, Allah ba zai tab'a kyale shi ba har sai ya aikata abinda ya gaya muku, dan haka ki nemi yafita, domin ba zan yafe ba." Na cigaba da murde mata hannunta tana kuka.. shigowar Badar yace.
"Subhanallahi! Noorh! Saketa bana son shirme!" Ture ta nayi ta fadi.
Ya d'ago Tasleem tana kuka kamar wacce aka saka mata wani abu.
"Me ya faru!" Zuciya ta hanani bashi masa tace mishi.
"Hm! Fisabillahi! Kome Noor, kowa Noor! Babu wanda ya dame da how am feel, she take my position! Ta dauke hankalin kowa, d'azun kaga yadda MD ya kore mu sabida ita, Why sai Noor ?" Tana gama fad'ar haka ta dauki jakarta ta bar Office din.

        ..... Bata kula Mr Nazzir da yake bakin kofar ba, ni kaina kuka nake, tare da ɗaukar jakata, zan bi bayanta, yace min.
"Ki dawo kiyi muku sign, sabida asan kun zo kun fara abinda ya kawo ku."

     Zuwa nayi, na cika mata tare da nawa, na fito ina zuwa naga ta tafi, wani irin kuka ne yazo, ya tsaya a gabana.
"Zo na kai ki"
Kallon shi nayi, sannan na shiga motar ina yi ina share kwalla na, har muka isa gidan, ya har cikin gidan ya kai ni,sannan ya tsaya tare da mika min tissue, na bude tare da cewa."thanks!"
Na ficce abuna, tunda daga bakin kofar shi gidan cikina ya murɗa, dan na hango ta tana kuka a jikin window..
Ina shiga ta juya gurin Mommy, cikin kuka tace..
"Mommy shine ya kawo ta, Mr Nazzir Abu Aswad, Mommy na shiga uku mutuwa zanyi don Allah Mommy ku kore A'isha daga gidan nan!"

#Vote
#Comments
#Share😍😘🌹

Continue Reading

You'll Also Like

18.7K 1.3K 39
"You were magnificent, Satoru Gojo. I will never forget you for as long as I live." Satoru Gojo laid there, bisected in half, as if the universe itse...
Ice Cold By m

General Fiction

2.8M 99.4K 54
COMPLETED [boyxboy] Wren Ridley is always two steps ahead of everyone, or so he thinks. His life seems out of his control when he starts having feeli...
27.9K 1.3K 20
What happens when a suicidal twenty-two year old meets someone who pushes her to be more than her grief. In return she teaches him how to be patient...
146K 15.3K 18
[Sequel of 'MY SUBCONSCIOUS DESIRE'] Once again, a tale of desire and respect Once again, a tale of Rathod and family bond A multi-couple story. F...