👨👩👧👦ZAMAN YA'YA👨👩👧👦
*Based on true life story*
Story&Written by Mmn Muhibbat Abdullah
Vote on wattpad@Mmnmuhibbat
Dedicated to Taskira members.
Page 14
#####Gidan hajia salma🤣
Salma ce zaune tana lissafa furan da zata saya wurin wata yarinya da take kawo mata tallan fura ,huran ta na da dadi da tsafta shiyasa take sonta sule zata saya mawa dan yana kaunar fura sosai yana gari ya zo jiya ya ce mata zai kwana biyu wannan karin shiyasa take ta rawar jiki da shi.
Sule ne ya fito daga daki zashi fita tahowa tayi dan tayi mashi Allah ya kiyaye hanya salma tayi mashi.
Amsawa yayi ciki ciki shi ala dole ga boss.
Kofar gida ya tsaya domin yana jiran yarinyar da ya ke jin muryanta suna cinikin fura da salma dan yana jin muryansa yaji tayi masa.
Yana tsaye sai ga yarinyar ta fito. Tare ta yayi yana mata sallama tsaywa tayi tana kallonsa tambayrta sunanta yayi
Ta ce "SADIYA sunanta yanzu shekarata 18 sbd ita ba'ayi mata auran wuri da ake yi ma sa'aninta ba sbd bata samu mai son ta da aure ba yanzu ma wannan tallar furan da ta fito sbd ta rage gorin da ake mata cikin gidansu matan baffaninta da kakaninta.
A wajen gidan su ma mutane na mata gorin taki aure abun yana mata zafi sosai sai kace ita zata kawo ma kanta mijin aure.Iyayen ta masu rufin asiri ne shiyasa baa abunda ta rasa(Sannu zaira daga tmbyr suna 🤣🤔Sai rattahi).
Murmushi yayi dan ta bashi dariya ya kuma ji dadin wannan dumi nata dan ya samu amsar tambayoyi da dama .
Maganr so ya fara mata ba wuya ta amsa yo taga dan birni 🤣bata san bogi ba ne.
Ce mata yayi zai aureta shin ta yarda idan ta yarda tayi mashi kwatancen gidansu.
Kwatancen tai mashi na garin su ita yar kauyen ajiwa ce babu nisa garin su da cikin gari ya ji dadi kwarai dan haka ya zura hannu cikin aljihu ya zaro 5k😳ya bata dadi taji sosai ashe zata caski dala.
Jiki na kyarma ta amsa tana godia shi kuma yana bude hanci shi ga mawadaci.
Haka ya taka mata har bakin hanya ta hau mota dan tafiya garin su.
Dakin uwarsa ya koma cikin gida bayan ya wuce sashin su salna tana zaune su hassu na bata labarin kayan mata da suka sha da irin bidirin da aka sha.Salma ji take inama inama dan kuwa sule bai cikin maza masu sha'awa sosai bai damu da mace ba in ba ita ta kawo kanta ba, irin mazan da kyan su azumi kawai bawai aure ba tunda shi ba iya kula da hakkin matarshi da yaranshi yake ba, da kudinsa sannan da jiknsa ma zero.tun da duk wannan dadewar da yake Abuja bai neman mata ba su gabanshi amma kun ganshi wata zai kinkimo ko tsoron hakki bai yi😏😏(Shi aure yana halatta ne ga mutumin da yake financial and physical nashi is stable)
Shiga dakin yayi ya iske innarsa kwance da kanwarsa da ta zo yini .wuri ya samu ya zauna anan ne yake gaya ma innarsa yayi budurwa aure zai kara .
Murna suka kama yi suna son barkaa sbd daman wasu matan idan dai dan uwansu zai kara aure murna suke suna cewa ai daman namiji mijin mace hudu ne. Amma idan mijin su zai kara sai su ce mijinsu zai kara mance namiji mijin mace hudu ne domin watan baya aka sha rigima da salame kanwarshi akan mijin zai kara aure kuma babu abunda ta rasa na hakkin da Allah ya dora ma mijin yana da halin karin amma kirmisisi ta hana mijin karin auransa .kuma ba wata cikakkar kulawa take bashi ba kullum yawo bata gidan ango bata gidan amarya.kuma haka uwarta ta goya mata baya har bokaye ta shiga aka rufe maganr .Amma yanzu murna suke dan za'a kawo ma salma ba su dubawa suyi mashi nasiha ai bai sauke nauyin salma ba ina zai kai yarinya.
Tambayarsa innarsa tayi wani daki zai saka amarya dan taga ai daki 2 ne sashin sa. ce mata yayi "dakin su samha zai sakata su kuma su koma dakin uwarsu ko su dawo dakin innar.
Innar ce wa tayi a'a bata son takura kar a takurata su kwana dakin uwar su (😏🤔wato ita dayake ba mutum ba ce).
Salame ce ta ce gaskia shawaran yayi yaya (Alhali ita gidanta babba ne sashinta sashin miji har da sashin yara har da dakin yaranta maza har da ce ma mijinta babu wuri gidanta😏).
Tsara yadda bikin zai kasance kawai suke har da fidda anko salame tayi dan uwanta zai karo aure zasu kara yawa suma.
Ita kuwa salma tana can bata ma san me ake ba tana can tana sana'arta wato kitso. Yanzu har cin cin take da dubulan na amare ita da hassu shiyasa yanzu bata da damuwar kudi sosai.
Dan ma bala bai barinta ta tara da tafi haka yanzu har kudi take bama uwarsa sbd ya ce idan bata bama uwarsa kudi ba sai dai ta fasa sana'ar haka take bata kudi ga dawainiyarsa ga ta uwarsa amma ita tata uwar kullum cikin ce mata bata da shi take sai dai taje gida ita ta dauko na mahaifiyarta amma ita bazata kaiba idan hafsat ta kawo ta hada ta dauke da hafsat ta gane tasha wulakanci dan tace wlh bata isa ba.
Ita batai ma iyayensu ba sai bautan gardi ta zo fa dauke wanda ita ta kawo ranar salma baram baram sukai da hafsat wai ta ce ma mijinta kato hafsat ta ce na ce ,haka zaki lalace gindinsa ba tsiya ba arziki.
Gidan ta bar masu wai tayi zuciya mamarsu na jin su bata ce komai ba dan ita kanta halin salma na damunta,Amma Allah ya shiryata.
Ranar da aka kai kudin neman auran sule ranar ya ke gaya ma salma zai kara aure zai auri sadiya salma bakin ciki ne ya kamata kmar tayi hauka ta ce aure kuma?
Ya ce eh ko haram ne?
Ta ce a'a amma tsakani da Allah baka iya sauke nauyin mu ka yayo ma kanka wani nauyin?
Ce wa yayi eh aure dai sai ya kara bai ga uban da ya isa ya hana shi ba ehee ita yanzu ko kunya bata ji take hana shi. sunna.
Salma tace ai ba ance sai wanda zai iya ba sannan kana da wurin aje ta ne.
Ce mata yayi dakin su samha zai aje ta ita kuma ta maido su dakinta idan ya zo kwana dakin ta sai su koma dakin amarya.
Ta ce haba sule yanzu yadda muke kuntace yara 5 ina tunanin inda yaran nan maza idan sun girma za su fara kwana shi ne zaka hade mu da su daki guda haba sule kaji tsoron Allah.
Ta so mata yayi da fada da bala'i wai ai gidansa ne ya na da ikon da zai saka ko wace mace ya ga dama ba tare da izininta ba dan haka ta tsaya matsayinta kar ta wuce iyaka.
Kuka ta kama yi na takaici da bakin ciki shi kuwa baccinsa yake ba abunda y dame sa (Na ce malam sule ba lallashi oh ni mairo🤔)
Haka ta kwana zaune tana lissafin yadda takee kaunar sule wai kishiya zai mata duk wahalr da take mashi duk kudinta da take bari masa sbd kar ya ce zai mata kishiya amma shi ne sai d ya dauko yarinya karama.
sannan ma abun haushin ko biya mata bukatunta bai iyawa bare yarinya, shi ne har da kari.
Washe gari haka ta tashi ranta ba dadi. Hassu ce ta shigo ganinta haka ne ya saka hankalinta ya tashi zama sukai kan tabarma tana shaka mata ai sule aure zai kara
Aure!!!😳kutt ke baki koshi ba shi ne zai dauko maku wata jangwam.
Amma kin san me salma kiyi hkr watan cin kaniyar sule ta zo ki bar shi yayi auran kina zaune amarya zata kwatar maku yancin ku.
Dadin taji sosai da wannan shawaran har ta ji sanyi wlh maganr hassu gaskia ce wlh zata jure takai zuciyarta nesa yayo amaryan tana zaune zata ci kaniyarsa.(mata da dama suna tunanin wai idan miji yayi aure kishiya na canza shi wani mijin ana canza shi amma wani mijin cigaba zai yi da wulakancinsa musamman idan ya fahimci ba ki da baki)
Kawun Sule ne suka je ajiwa saka rana.Haka aka saka nan da wata 5.Suma iyayen daman ba masu bij lamarin yaransu bane dan haka ba wanda yasan halin da salma take ciki ba na rashin mai kulawa.
Sadiya da sule a kofar gidanshi suke zancen kullum SADIYA idan ta saida furan ta zata zo kofar gidan sule ta jirashi ya fito asha zance ya rakata ta koma ita ke zuwa zance🤣sbd rawar kai.
Salma na cikin gida bata san tsiyar da ake tsulawa ba kanen sule ne ya tona su masu asiri ya gaya ma salma ai amarya suna kofar gida da sule.
Taji bakin ciki sosai gwanin takaici ace uban ya'yanta wai mutane na wucewa kofar gidansa yana zance .Hassu ta tambaya gaskiyar labari dariya hassu tayi ita da mariya domin sun dade da sani kawai gaya mata ne ba su yi ba matar da take ma kitso ce ta ce mata ai duk unguwa kowa ya shaida suna zance a kofar gida abun yai mata ciwo amma ta yanke shawaran ya rika shigowa ciki ana zancen dakinta😳🤔
Haka da ya dawo take cewa su rika shigowa ciki sbd mutane kar su rika ganin su.Dadi yaji bai ji komai ba ,ba kunya ba kara ya ce tou.
Washe gari da sadiya ta zo zance🤣cikin dakin salma suka shige ita ko kunya bata ji har da kan dawo da gero ta kawo ma innarsu sule jiki na rawa ta amsa tana kara jin kaunar sadiya ashe mai ungo ce zata rika bata wadatacce kenan idan ta shigo fiye da salma.
Wata rana hafsat ta shigo unguwar kawai ta iske sule zaune daki da sadiya da farko ta sakayar uwansu ce sai da salma take cewa ga aunty su samha.
Kallonta tayi galala ta ce wa ce aunty?
Amaryan sule mana inji salma
Kutt amaryan ce take zaune cikin dakin ki da yake baki da zuciya ke sakarar ina ce wai sule ubanki ne da yake son kashe ki da bakin ciki.Shiru tayi wannan karon dan kuwa abun yama mata zafi sosai amma ta hakura ne sbd ba ta da yadda za tayi da shi ne da a zubda ma yaranta mutunci gwara ta hadiye ko wane damuwa.
Kallonta hafsa tayi domin kuwa duk ta kare ta rame ta lalace sbd wahala ga kishi kuma.
Sule ne ya fito ya na ce ma hafsat baya da mutunci zata bata mashi gida ta na son kashe ma salma aure.
Hafsat ce wa tayi ita da zata samu ta kashe kaddararren auran salma da ke kanshi da tayi murna.
Bala'i ya kamayi yi ya ce ta fitar mashi gida zama tayi ta ce bata fita ya ciccibeta ya wurga waje dan Allah.
Sadiya da ke cikin daki duk tayi tsuru tsuru ta ji wadda ta fita bala'i.Fitowa tayi sumi sumi ta wuce sbd ta ji tsoro binta yayi daga baya .
Hafsat kuwa bala'in ta cigaba da yi tana.wanke salam kina zaune sai ya kashe ki da takaici ba mai jinuarki tunda yaranki kananan ne.
mama da baba ta kansu suke amma ke baki tausan kanki.
Haka ta yini bata shawarwari da bin hanyar da zata bi ta rika ma sule magana kila ya ji maganarta ya gyara wani abun duk da sunyi nisa daman farkon aure ake gyara miji.
Haka sule ga hada lefensa amma salma ko allura bai bata b sai da tayi mashi magana ina kayan lefenta itama wai sai ya ce ai itama yai mata da zai aureta (🤔ko ina kayan lefen salma suke yanzu wannan al'ada tana bata mani rai sai ace wai ai kema tunda ya auro ki ai yayi maki tou badan amarya tayi kwalliya ya saka yayi mata ba ita uwargd kenan bai son ganin kwaliyyarta kenan tunda ai mata lefen ya kare.Shiyasa wasu mazan ke rawan kai idan sunyi aure yo sabon amarya,sabon fuska,sabon kaya,sabon daki,ga sabon katifa ba dole ke uwargida da tsohon zanenki da yamusashiyar katifan ki, kila wata ma tun ta aure ta ina zai zumudinki kamar amarya.)
Da taima innarsa magana ma abu daya suka maimaita da sule ai yai mata itama sadda zai aureta kuma bata ga sule baida karfin yi mata ba.
Kudinta ta fidda tai ma kanta yan kayan fitan biki da yaranta.
sai saura sati daya biki ya bata atamfa caras ita da yaranta godiya tayi mashi ta aje ta.
Haka aka sha biki dangin sule har da kidan kwarya sbd murna dan uwan su yayi aure.
Haka aka kawo sadiya gidan angonta sule kanta na ta rawa.Haka aka sha amarcin kwana 7salma na masu girki.
Da dare sule na jiran salma ta kara masu kwana yadda yaga wasu matan na wannan shirmen a bama miji space wai dan yayi aure, ai hajjaju tunda dai zaki koma mashi ko wata nawa kika bashi , ranar da zaki koma kenan aji ya zube .
Ya zo ko kwanciyar kai da kafa ne kuyi ai dai ya kwana wurin ki randa kika sauko daga kishin sai ki amshe sa ba wanda zai gane maku.
Salma tai mashi mirsisi kamar bata san me yake so ba haka ya gaji ya kwanta ita kuma tayi shimfida tayi kwanciyarta kasa abunta.
Da safe da bala'in yara sun yi fitsari suka karya na sadiya sbd daman shimfida tai masu suka kwanta kasa aiko kananan suka jike shi jagab da fitsari.
Sule ne y fito zai mata masifa ai yaranshi ne kuma ai dan shi aka Kawo mata bargon.
Wanke sa tayi tas ta ce bai isa ba kuma wlh sai ya saka an wanke shi ko shi ya wanke a daketa a hanata kuka.
Dolensa ya bada shi wurin mawanka aka wanke.
Ta ce kuma wlh sai dai su koma dakin inna da kwana,dolensa ya maida su dakin inna ya bata hkr kan idan ranar kwanan sadiya ne za su kwana wurin uwarsu.
Haka sule ya gama shan amarci duk da ba wata tsiyar yake tsinanawa ba dan ma sadiyan amarya ce bata gani raggon maza take aure ba.
A dakin sadiya ya shirya ganin yana shirin fita ya saka ta ce ban gane ba ina kudin cefane?
Shiru yayi yana mamakin sadiya wai daman haka take(na ce baka ga komai ba)
Ya ce gani nayi ai akwai gara da aka kawo ki da ita ko?
Ta ce yo in akwai gara shikenan kuma cefane da lalura in ta tashi shikenan da shekaruna zan yi.
Shiru yayi ya ce mata zai bata tare kofa tayi ta mika hannu haka ya zaro 20k ya bata ya ce ta kaima salma su raba kallon kudin tayi a shkeke ta ce me wannan za su isa .
Ce mata yayi wannan ma cikin dukiyar angon da iyayenta suka bashi ne bai kashe ba .
Haka ta raba kudin biyu ta kaima salma rabi salma tayi mamakin wanna sabon canjin kudin cefane ai tun tana amarya lallai sule wato ita ya maida jaka kenan kuma dan wulakanci ita da ke da yara ne za'a bama kudi daya da sadiya.
Tunda ya tafi daman ta daina dora abinci da innar sule ta ce ba abincin da danta ya kawo bane ta bari sai ya kawo sannaan inna ta sha mamakin rashin kunyar sadiya amma ta hakura akan idan sule ya dawo zai mata maganin ta.
Plate daya take bama salma da yaranta shiyasa ma salma take girkinta dan ba isar su zaiyi ba.
Bayan wata biyu sule ya dawo wanna karan salma tayi mamaki amma ta share shi haka yayi sati 2 ya koma amma sadiya sai da tayi bala'i al'amarin sadiya yana ba ma salma mamaki yadda sadiya ke juya sule kuma yake shiru amma ita kam bata isa ba Hassu ce ta ce kila asiri tayi mashi kin san yaran kauye bare wannan da idonta tsaye yake wawiyar yadda tayi bata san sadiya hakkinta take amsa ba kuma mace tun farko wata ita ke bata miji bata gaya masa abunda take so wata bata ma san ya zata gaya mashi ya ji ba wani zafi yake bukata ayi masa kamar sule wani kuma cikin ruwan sanyi ake gaya masa ya dauka.
Dawowar sule 2 sannan kayan sadiya na abinci ya kare daman zuwan karshe sule ya gane ai abinci ya kusa karewa shiyasa yai alkawarin wannan karin sai ya dade bai dawo ba dan kar sadiya ta saka shi yin sayayyar kayan abinci na dole dan ba wai ya saba bane halinsa na nan na zalunci dan haka salma ta dauki nauyin sadiya ma idan yunwa ta ishe ta yasan dai ai baza ci ta hanata ba ko😏😳😏..
Sadiya kuwa ganin wankin hula na son kai ta dare ya saka ta maganta da yake tana ganin girman salma sule dai ne yake cin kaniyarsa ko da yke tace hakkinta take amsa ai .
Shiryawa tayi zata bi sule abuja dan taga abunsa bana hankali bane yau watan shi 4 rabonsa da gida ba zuwa ba aike dan haka tun cikin dare ta hada kayanta daman taje gidansu ta saido awakinta guda biyu ta kulla kudinta 20k dan kar yayi mata iskanci idan ta isa wurin sa dan kuwa tayi alkawarin kafarta kafar sule idan anga ta dawo katsina tou tare da sule ne.
Da Assuba ta yi ma salma bankwana zata wuce abuja salma mamakin sadiya take yi yo ita ai har 9mnth ya sha yi bai zo gida va amma bata taba binsa ba sadiya ce mata tayi kin ji zaki iya ne maman samhan ni kuwa bazan iya ba kin ga tafiyata salma tayi tayi ta zauna amma ta ce wlh sai taje dan haka tana ganinta ta bude kofa tayi gaba abunta ko inna batai ma bankwana ba.
Salma zama tayi tana mamakin aiko watan mutuwar auren sadiya yayi da bata bishi ba wlh ta kyalesa da halinsa shi da Allah.
ita kuwa sadiya tashar KSTA ta shiga sai Abuja.
ALLAH YA KIYAYE SADY🤣