GUDU A JEJI

By fateemah0

3.1K 120 4

GUDU A JEJI, LABARI NE MAI CIKE DA TAUSAYI, CIN AMANA, HASSADA, KYASHI DA SON ZUCIYA, KARKU BARI A BAKU LABAR... More

page 1-2
3-4
5-6
7-8
9-10
11-12
13-14
15-16
17-18
19-20
21-22-23
24-25
29-30
31-32
33-34
35-36-end

26-27-28

140 7 0
By fateemah0

🌳
🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳

*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Short story✍🏻

(Doter surayyah dan ango ALLAH yabawa mom dinmu lpy fans asa mom a adduah)

بسم ا لله لر حمن لر حيم

🅿-2⃣6⃣➡2⃣7⃣➡2⃣8⃣

Bayan ta kai masa ta dawo suka cigaba da aiki a kitchen suna taya mami girki har akayi sallarh magriba kafin suka gama gabaki daya safreena tagaji anya ita ta taba aikin girki kuwa ta tambayi kanta ?
To ma banda abina wazai bani amsa mtsww

Haka dai suka wuce bedroom itada madina suna shiga madina ta zube a bed gamida cewa wash Allah na nagaji wlh sis

Murmushi safreena tayi tace ahh ahakan kuma zamu kaiki gidan yaya nabeel din ɗan wannan aikin shine kike cewa kin gaji ?

Murmushin farin ciki madina tayi dan tanajin nishadi idan aka kira sunan abincin ruhinta wato nabeel

Sis najma kinsan wani abu kuwa ?

Aa saikin fadamin

Wlh ina mugun qaunar nabeel har jinake kamar bazan iya rayuwa batare dashi ba

Riqe baki safreena tayi tana kallon madina tace tab lallai kam kinyi nisa wannan so haka gashi nikam bansan shi ba ko pic dinsa baki taba nunamin ba

Hararan wasa madina tayiwa safreena tace kajiki fa sai kace kina zama muyi wata hiran arziƙi bayan wani lkcn ma nizan tamiki magana amma kimin banza ta fada tana murguda baki

Dry safreena tayi ta zauna kusa da ita
Ta rungumo kafadarta tace haba madinatuna wlh ba haka bane a condition din DA nake ciki na rashin sanin wacece ni na tabbata idan kece haka zaki zama kamarni

Karki manta bansan sunana ba bansan daga ina nake ba bansan wani nawa ba kullum inaso na tuno ko da abu daya ne tak agame  da rayuwata amma dana fara hakan sainaji kaina yanamin barazanar tarwatsewa dole nake hakura

Kuma a yanda kuka riqeni da kunya nace wa mami inaso atayani neman ahalina to barin ma kuma yaya sameer da kullum yake dawainiya dani hakan sainaga kamar nayi muku butulci ne

Amma insha Allah daga yau nayi miki alkawari zan sake  daku zan zauna daku amma zan cigaba da addua Allah ya bayyana min wacece ni
Ta karashe mgnr da kuka mai ban tausayi wanda baya fitar da sauti sosae

Sosae madina taji tausayin safreena tanason tayata kukan amma bataso taƙara karya mata zuciya dan haka ta daure ta hau bata baki har tasamu  tadanyi shuru kafin ta miqe tace bari na watsa ruwa kafin nayi sallah dan wlh jikina  kamshin abinci yakeyi

Madina tace nima haka kiyi ki fito sai nima na shiga na watsa ko kuma bari naje nayi a dayan dakin ta fada tana miqewa  ta fice
Safreena kuma tashiga bathroom din dakin domin tayi fresh up

Su dad basu iso ba sai bayan sallar isha kafin suka iso  sallama sukayi acikin babbar parlorn dad da sauri sameer dake tsaye yakaraso gabansu gamida durqusawa yana gaida iyayensa

Dagosa dady bashir yayi ya rungumesa cikin wasa da dry yace ah my son kafa qara girma kodai idona ne
Shima dryn yakeyi batare da yayi magana ba dady abdulsalam yace ai wlh aure zamuyi musu karsu tsufa batare da sun ajjiye mana jikoki ba wata kilama aciki jikokin ma samu wanda zamuyi  ƙari dasu

Dry dad yayi wato mahaifin sameer (ALHAJI MUKHTARH JAFAR)
yace ah to baku kuke sangartasu ba gashi dai ɗana nabeel kwanan nan zan auran dashi
kai Alh bashir nace kabani ihsan na hadasu kace ba haka ba ai saiku ta zuba masa ido

Gaban sameer ne ya fadi dan babu abinda yafado masa illa najma da yaji dad dinsa ya kira sunan wata da  sauri yace my dad's kuyi hakuri kun iso amma na tsayar daku dry sukayi kafin suka wuce cikin parlor din suka zazzauna dad kuma ya wuce part din mami domin kuwa ba ƙaramin missing dinta yayi ba so yake yaje yayi tozali da beautiful face dinta b4 yashiga wanka lolx

Su madina suna daki suna hira wayar madina yana hannun safreena tana kallon pics din da madina ke nuna mata na nabeel

Safreena tace amma fa sis madina nabeel dinki fa kun dace dashi
Wani fari da ido madina tayi na jin ddi tace da gske sisna?

Ehmana to amma wanene wannan nagansu atare yawancin pic din ?

Mugani cewar madina
Kalla tayi tace yaya saeed ne abokin yaya sameer da kuma nabeel din wanda tare dadynsu  zasu dawo daga tafiya yau tare da  dad kuma.....bata karasa ba wayarta yahau ringing tace lahh kinga ihsan ce ke kira kanwar yaya saeed ce takanzo tayi hutun ta anan but yanzu ta jima batazo ba shiyasa bakusan juna ba amma tanajin lbrnki awajena kuma yaya sameer ma yana bata lbrnki murmushi safreena tayi batare da tayi magana ba

Ɗaukar wayar tayi suka fara gaisawa sannan tace ya sis najma
Lpyrta kalau waike yaushe zakizo ne ?

Ihsan tace to ni nadinga zuwa kenn ke bazaki zo ba ?

Dry madina tayi kafin ta sassauta murya tace sis saurin me kikeyi ne nida zan dawo zama na dindindin gabaki daya

Dry itama ihsan din tayi tace lallai fa naga alama kin ƙosa ya kamata su dad suyi harzarin saka bikin nan ayisa mu huta
Yanzu dai bani sis najma mu gaisa
OK gata
Ta fada tana miqawa safreena wayar wanda tunda suka fara mgn da ihsan ta  zuba musu ido tana kallon madina tanajin muryan ihsan

Karba tayi ta mata sallama ihsan ta amsa cike da fara'a sannan suka gaisa
Ihsan tace sis yaushe zakizo mana zaria ?
Murmushi safreena tayi tace idankinaso ai gobe ma saina zo. Dry ihsan tayi tace inaso mana inason muga juna sannan mu saba sosae afili amma nasan ke bazaki zo zaria yanzu ba dan na kira yaya sameer nake tmbyarsa yaushe zakuzo yacemin ko da zakuzo ba yanzu ba amma ni insha Allah ina gama peper na a wannan satin zanzo

Ayya to Allah ya kawoki lpy sis

Ameen sis najma tnx
Ke baki da waya ne ?
Shuru safreena tayi kafin tace eh bani dashi tukunna amma zamu dinga gaisawa da wayar mrs nabeel

Dry ihsan tayi tace ok shikenn sis najma bye
OK bye

Ta miqawa madina wayar  ta karba tasa akunne
Ihsan tace su dady basu iso bane inata kiran wayarsa bata shiga harda wayar dady abdulsalam lpy dae ko ?
DA Sauri madina ta miqe zaune tace wlh sis namanta akan cewa su dad zasu dawo yau maybe ma sun ISO bari muje mu duba dan banji motsin motoci ba gsky dan wlh gabaki daya hankalina yana kan wata littafi da kuma wayata dake hannun sis najma ina nuna mata pics dinsu yaya nabeel da yaya saeed amma bari muje mu duba

OK Idan sun iso lpy saiki kirani ki fadamin
OK ba damuwa bye
Kashe wayar tayi ta kalli safreena tace sis najma tashi muje
Mu duba mugani ko sun iso kinsan Allah gabaki daya na shafa'a kuma zaman hiran da mukayi ne yasani namanta

Safreena tana dry ta dauki dogon hijab dinta har ƙasa tasa kafin tace yoo dama ana hiran nabeel kam ba dole ki manta dad zai dawo yauba

Itama madina dryn take ayayinda ta dauki nata hijab din tana sakawa domin kayan bacci ne ajikinsu tace wai nikam rufamin asiri kar dad yaji yaƙisa bikin nan kusa tana fadi tayi waje tana dry

Murmushi safreena tayi tabi bayanta tace Allah ya shiryaki madina

Atare suka taho hanyar da zata sadasu da babbar  parlorn dad sukayi safreena bata taba bin hanyar ba dan itakam daga dakinsu dakin mami  sai kitchen sai kuma part din sameer dan ita tafi zama acikin daki ma abunta dan haka duk zamanta agidan ba ko ina ta taba shigaba kuma dama bason shigan take ba

Har sunsa hannu zasu bude kofar parlor din sameer shima yadanno kai zai fita karo sukayi da safreena da sauri ta matsa baya tace yi hkr yaya bansan kataho ba murmushi yayi yace is ok najma ina zakuje haka da wasu manya manyan hijabai sai kace masu shirin tashi sama ko kuma wanda zasuje tafsiri ?

Dry suka sa kafin madina tace yaya su dad sun iso ne ya bude baki zaiyi magana sukaji muryan dad na cewa eh auta mun iso yanzu nake tmbyar maminku akan cewa ina yarana suke
DA gudu madina taje ta rungumi mahaifinta cikeda jin dadi da farinciki
Kafin ta sakesa ta duqa har ƙasa tana gaidasa wanda hakan ya zamo tarbiyyar gidan ALHAJI MUKHTARH JAFAR dole idan yara zasu gaishe da iyayensu tofa ya zama dole su duqa sbd girmamawa

(Akasin wasu gidajen da tarbiyya tayi ƙaranci yaro zaiga mahaifinsa amma bazai duqa  ya gaishesa ba saidai atsaye zangangan ko kuma yana gaishesu amma hankalinsa yana kan waya yana dannawa wani gidan ma kam yaro zaiga  iyayensa amma saidai ya wuce ya shige kansa asama dan  Allah ya kamata agyara kuma wannan gyaran bana kowa bane face ke UWA domin rabi da kwatan tarbiyya ahannunki yake domin shi UBA idan yafita yabarku watakilama ba lallai bane yaƙara dawowa gidan  ba sai dare dan haka mu daure gyara Allah yasa mudace)

Safreena gefe ta koma ta rakube banda kwalla babu abinda ke fita a idonta sai gogewa takeyi da sauri Ko itama tana da iyaye oho sannan suna mata irin wannan son oho azcyrta tace Ya Allah kafitar dani daga wannan halin ka turomin haske acikin rayuwata domin na tuna wacece ni

Duk halin da take ciki sameer yana kula da ita ya kafeta da ido har ƙasan zuciyarsa yaji babu dadi
Dago kanta tayi suka hada ido dashi ya girgiza mata kai

Mami ce tace doter najma ya naga kina murza ido kuka kikeyi tazo gabanta ya ɗago fuskarta

Aa mami ba kuka nakeyi ba abu ne ya faɗamin a idon yanamin zafi

Ayya sannu ko najma murmushin karfin hali tayi tace yama dai min zafin yanzu mami
To jeki ga dad dinku

Gabansa taje ta duqa har ƙasa itama cike da girmamawa ta gaishesa amsawa yayi gamida riqo kafadarta ya ɗagota  yace masha Allah ƴata kisaki jikinki kinji ko murmushi tayi tace to dad

Suka shiga parlorn atare
Gaishe dasu dady bashir su madina da safreena sukayi daga nan mami ta hau. .serving dinsu abinci

Bayan sun gama ne dady bashir ya tashi yace to masha Allah alh Mukhtarh mungode sosae bari mu wuce masaukin kafin gobe kuma mu qara ɗaura wata tafiyar

Dad yace to ba damuwa

Saida safe kenn ko
Zamuyi waya kawai mu katasa mgnr ba damuwa
To Allah yabamu Alkhairi

Suka fita gabaki dayansu dady Abdulsalam sai tsokanar madina yakeyi wai sirkata sai ankawo ki zaria
Sai rufe fuska takeyi ajikin safreena

*************

Khalifa zaune adakin nabeel suna hira wanda khalifa sama sama yake amsawa

Izuwa yanzu khalifa yaɗan saba dasu iyayen nabeel da saeed sannan sun yaba da hnklnsa da natsuwarsa

Nabeel yace gobe fa dadyna zai dawo kuma kullum ina basa lbrnka hajia ma tana basa lbrnka

Murmushi khalifa yayi yace Allah yakawo dady lpy nabeel ya amsa da ameen

Sallaman saeed sukaji da mamaki suka daga ido suna kallonsa dan a lkcn shaɗaya saura

nabeel yace dawowa kuma kayi
Yace eh wlh dadyna ne wai nazo nan na kwana idan sun iso gobe saina muce dashi gida
Ok kawai nabeel yace

Khalifa yace to miye wannan a hannunka saeed?

Guntun tsaki yaja yace ihsan ce ta hadani dashi wlh

Dazu ma wai sun sha waya da kanwar  barrister S.M.J wai sunyi wata sabuwar kawa mema sunanta am um wai NAJMA

Gaban khalifa ne yaji yafadi amma ya dake batare da yayi magana ba ya kata maimaita sunan aransa yace NAJMA
To miye hadina dake ana kiran sunanki naji zcyta ta amsa mtsaw to ma miye ruwana

Nabeel yace ai kullum sainaji lbrn najma awajan madina saidai ban kirata ba

Khalifa yace wai dan Allah menene Asalin sunan barrister S.M.J dinnan?

Saeed ne yayi dry yace inkiyarsa ce S.M.J awajan aiki
But full name dinsa
Shine

BARRISTER SAMEER MUKHTARH JAFAR

🥺🥺
Wayyo sai mun hadu a next page

Comments

And

Share

Continue Reading

You'll Also Like

132K 2.2K 27
រឿងមួយនេះជាប្រភេទ BL s*x ចង់អានក៏អានចុះតែបើប៉ះពាល់អារម្មណ៍កុំបន្ទោសអ្នកសរសេរឲ្យសោះហើយក្នុងនេះក៏មានពាក្យមិនសរម្យច្រើនដែល🤏🔞 Taekook all story 🤯 ___...
34.4K 4.8K 71
A cute story with little twist and turns! *A Baker with a Billionaire* "Sivaangi, a talented baker, has built a life around her past heartaches, but...
35.2K 3.4K 48
. .
30.8K 2.2K 28
This is a Muslim story She fell in love with her handsome cousin {Zaid Siddiqui}. People say that we cannot fell in love with our cousins ​​but, it...