GUDU A JEJI

By fateemah0

2.6K 111 3

GUDU A JEJI, LABARI NE MAI CIKE DA TAUSAYI, CIN AMANA, HASSADA, KYASHI DA SON ZUCIYA, KARKU BARI A BAKU LABAR... More

page 1-2
3-4
5-6
7-8
9-10
11-12
13-14
15-16
17-18
19-20
21-22-23
26-27-28
29-30
31-32
33-34
35-36-end

24-25

132 6 0
By fateemah0

🌳🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳

*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

A gsky GUDU A JEJI FANS BANI DA BAKIN DA ZAN NUNA FARIN CIKINA SBD GOBARAR🔥🔥 COMMENTS DIN DA KUKAMIN KUMA YA KARAMIN KARFIN GUIWA Yau ma ABU DAYA KAWAI ZAN IYA CEWA SHINE WANNAN PAGE DIN MA NA MALLAKA MUKU 💃🏻
Am busy that's why bazan iya lissafuku ba luv urs oll mah ppls🥰

Short story✍🏻

بسم ا لله لر حمن لر حيم

🅿-2⃣4⃣➡2⃣5⃣

Murmushi khalifa yayi yace inna ba haka kika so ba ko kinso ace na mutu tunda haka kika dinga fadi na mutu inna ban mutu ba da rai na yanzu ma kuma nazo na gaisheki ne sannan na duba lafiyar ki kuma Alhamdulillah nagani kina lpy ina miki addua Allah yaƙara miki lpy da nisan kwana kici gaba da aibata ni yana kaiwa nan ya juya  ya fice abunsa su saeed suka rufa masa baya suna son yimasa mgna but yanda sukaga fuskarsa babu walwala dan haka suka ƙyalesa

Kafin su koma an gyara gidan tass mai gadi da matarsa da yaransa

gdy khalifa ya musu

Ya kalli su Ahmad yace zamuyi sallar magriba ne ko kuma mu fara wanka shap shap?
Nabeel yace aa gsky mu fara watsa ruwa tukunna idan yaso sai muyi sallah mu wuce tunda lkc ya ƙarato
Ok mu  shiga
Suka rufa masa baya

Babbar parlour ne kam wanda yaji ɗima ɗiman kujeru na alfarma daidai wadaida sannan akwai toilet a parlor din daga hannun dama akwai wata qaraman parlor da toilet itama acikinta

Sai manya manyan bedroom ko wanne dauke da toilet  

kallon gidan su Ahmad keyi suna jinjina kai afili suka hada baki gamida cewa kai Masha Allah khalifa gidan ka kam tubarkallah yayi mugun kyau
Murmushi yayi yace ango ga bedroom dina can kashiga kayi wanka aciki
Saeed nabeel ga rooms ku shiga kuyi wanka
Ni zan shiga nayi a bathroom din ƙaramin parlour
OK sukace kafin
Ahmad yayi hanyar dakin da khalifa yamasa nuni dashi su kuma su nabeel suka shiga ɗaɗɗaya

Har zai shiga kenn Ahmad yafito yace kayanmu suna both din mota fa yace ok bari nasa ashigo mn dashi kasamu kashiga wanka gashi ana kiran sallah
Ok kawai Ahmad ya fada ya juya ya shiga daki
Khalifa kuma yayi waje yana kwala kiran haruna ɗan baba mai gadi yace ya shigo musu da kayansu dan Allah
Daga nan shima ya wuce ya shiga wanka

Shap shap suka shirya khalifa ya fito yashiga dakinsa yasame su dukkansu sun gama shiryawa ango yana ɗaura agogo yasha kyau sai ƙamshin angonci yakeyi khalifa yace ango kasha ƙamshi fa
Murmushi Ahmad yayi yace ngd aboki ai wani shagalin sai Allah ya kaimu gobe
Nabeel yace kuji dan iska to dawa kakeyi
Oho muku da wanda ya tsargu nakeyi
Saeed yace Allah yaso ban tsargu ba

Khalifa dry kawai yake musu batare da yayi magana ba ya bude  wata ƙaramar akwatynsa wanda yasan kayansa ne aciki ya ɗauka ya shirya shap2 shima saida suka yi sallarh magriba tukunna suka fito

Sai kamshi ke dashi
Baba mai gadi ya kira yace zasu dawo anjima amma baisan karfe nawa zasu dawo ba domin dinner ne

To yallabai khalifa adawo lpy suka shiga mota
Suka kama hanya

Tsaki khalifa yaja daya tuna ATM dinsa yana abuja kuma yanada kuɗi a  account dinsa akalla zaikai 10m to ko wannan dan iskan daudan zai bar mishi to ma dauda mai zaiyi da wa innan kudin nawa  ƙalilan bayan gashi ya ƙwamushe masu dinbin yawa wanda bazasu lissafu ba
Dauda ko kana inane yanzu oho
kai koma ina kake wlh ina nan zuwa gareka domin bazan maka ta dadi ba yanda ka wargaza rayuwar safreena kasamu GUDU A JEJI nayi maka alkawari saika ɗanɗana baƙar azaba a hannu na ni khalifa daka kira da sunan yaro duk wannan maganganun khalifa ya ɗauka acikin zuciyarsa yakeyi baisan afili yakeyi ba gabaki dayansu kallonsa sukeyi harda saeed da yake driving yana kallonsa ta  mirror

Lumshe ido khalifa yayi gamida cewa SAFREENA !SAFREENA!SAFREENA !
Allah ya nuna min ke nan kusa  domin dole saida ke zan iya ɗaukar miki fansan abinda dauda ya miki
Nasan bazaki mutu ba batare da kinga karshen dauda ba bazaki mutu ba my safreena inaji ajikina kina raye sannan jikina yana bani kema kinfita awannan wahalalliyar JEJIN

Allah yasa kina hannu nagari safreena jiyayi hawaye yana shirin wanke masa fuska yayi saurin mayarwa shi kam kwata kwata ya manta ma a ina yake balle yayi tunanin dasuwa yake tare bai ankara ba yaji karan ta fi rap rap da sauri ya bude ido yaga fa ashe ba shi kadai bane rufe baki yayi a zuciyarsa yace badai sunji abunda nace bane muryan nabeel yaji yana cewa gsky zan so nasan wannan luv story din dan wlh daga ji zai bata onga

Ahmad zaiyi magana wayarsa ta dauki ringing ya dauka yace mufa gamu a kofar hotel din mun iso
OK kawai yace kafin ya ajiye wayar

Khalifa yace au wai dama mun iso ne saeed yasa dry yace ah lallai kam kayi nisa tun yaushe muka iso amarya yanzu muke jira dan mun rigasu isowa kasan shirin mata ashafa wannan amulka wannan agoge wancan dry suka saka dukkansu
basu wani jima ba amarya ta iso da kawayenta tasha kyau

Fitowa su khalifa sukayi da ango suka rakasa har wajan kofar motan amarya kawayen amarya sai wani kallon abokan angon sukeyi barin ma khalifa kamar zasu haɗiyesa

Ango ya kama hannun amaryarsa
A yayinda akayi layi domin rakasu

Anshiga an zauna anyi shagali ansha rawa anyi addua tare da fatan alkhairi dan kuwa basu tashi awajan ba sai sha biyu saura ahakan ma dan ango yace agajiye yake sannan gashi gobe zasuyi asubanci
aje daura din ma akwai wata dinner din dan haka suka tattara badin sunso ba kawayen amarya sai hari suke kawowa khalifa amma ko kallon inda suke baiyi ba hakan nan kuma wasu suka dinga cewa yana da girman kai dan ya gansa yana da kyau

Ko da suka koma gida sun gaji dan sai sha biyu da rabi suka isa gidan
Wanka sukayi suka zauna a parlor suna dan taba hira sama sama saeed yace nifa wlh yunwa nakeji

Ido khalifa ya ware waje yace ai kuwa gidan nan babu kayan abinci ko ƙyalli dan tunda aka gama gininta baifi sati acikinta ba nafita sannan rabona da gidan nan wlh saeed bazai ce maka gashi ba

Yace to kenn yanzu ko tea bazan samu ba
Wlh babu saeed
Nabeel yace ai da kayi mana magana mun biya mun saya kafin mu dawo inba haka ba zamu zauna da yunwa ne
Gwanda shi wannan ango ne bazaiji yunwa ba tunda aurensa akeyi mu kuma fa ?

Khalifa yace to ko zamu fita nema ne !
Nabeel yace Mee Nee Afita neman Mee karfe 1 yanzu wlh babu inda zanje azamanin yanzun nan tab inaa badani ba wai gaɗa a maƙabarta samm dry gabaki dayansu suka saka khalifa yace haba jarumina wlh bai kamata kadinga bada maza ba
Nabeel ya galla musu harara yace au haba
To wlh kuma ina baku shawara karku fita mu hakura da safe ido naganin ido muje

To shikenn nabeel mun hakura

Shuru wajen ya ɗauka nadan lkc kafin saeed yace khalifa ya kamata muyiwa juna introducing sbd kaine kawai baka sanmu ba
Muna kuma haka

Nidae sunana shine
SA'EED BASHIR AWWAL kuma ni haifaffen garin zaria ne mahaifina dan kasuwa ne nima kuma  ina business ta hanyar arkallan motoci
Ata ƙaice kenn sannan biyu ne kacal nida kanwata ihsan

Murmushi khalifa yayi gamida jinjina
Kai

Ni kuma sunana NABEEL ABDULSALAM GAMBO
nima dai dan zarian ne domin kuwa da mahaifin saeed danawa abokaine kuma sana'arsu daya wato kasuwanci ni kadaine awajan iyayena ni kuma arkallan gidaje shine business dina

Nan ma khalifa murmushi yayi batare da yayi magana ba

Ni SUNANA AHMAD GARBA ATULE MAGAJI ni dan daura ne kuma nan iyayena suke mukam munada yawa dan matan babana biyu ne kuma abotanmu a university muka hadu
a) a.b.u zaria daga nan shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninmu

Amma ni aikina yasha banban danasu domin kuwa ni CBI ne wato jami'in bincike

Kai fa khalifa ?

Shuru khalifa yayi yana nazarin shi kam ta ina zai fara karanto musu wannan lbr nasa

Kamar sunsan me yake tunani nabeel ne ya dafa kafadarsa yace khalifa ka yarda damu karka damu karka boye mana komai agame dakai domin mun fuskaci kana cikin damuwa ka dauke mu amatsayin aminai na haqiqa

Ajiyar zuciya khalifa ya sauke kafin fara da cewa
Zakuji lbrn da baku taba jinsa ba kuwa

Nidai sunana KHALIFA ABDULLAHI TASI'U
Haifaffen garin katsinan nan kuma wnn local government din ta dutsenma
Ni kadaine awajan mahaifiyata matan babana biyu zan iya cewa ma bansan mamata
ba domin tana maifata Allah yamata rasuwa mahaifina kawai nasani shima inada shekara goma cif  Allah yamasa rasuwa na koma zaman awajan matar babana babu kalar wahalar daban fuskanta ba

Amma na kasance tun ina qarami niba rago bane ko malalaci kamar wasu yaran mazan
Ga shi inason karatu kuma ina sha'awar aikin engineering sbd abu idan karfe ne ina iya sarrafata ta ko wace siga sannan ina gyarawa dan haka nashiga kasuwa duk aikin dana samu indai bai sabawa addini ba inayi da haka nasa kaina a mkrnt
Makarantar
Muhammadiyya kuwa tun ina dan shekara tara nayi sauka kafin rasuwar mahaifina
DA haka har Allah ya taimake ni harna shiga university kai na kare muku zance harnayi digree dina

Amma sani agaban da inna tayi gashi na gama karatu Sai
Yawon neman aiki nakeyi bansamu ba yasani kwashe  kayana na koma abuja........daga nan yacigaba da basu lbrn aikin da yasamu agareji da sharrin da aka masa aka koresa da saida purewater din da yafara har Allah ya hadasu da abban safreena wato ALHAJI MUHAMMAD BELLO BADIMASI
DA dan uwansa dauda kalar cin amana da kisan wulakancin da dauda yayiwa mahaifin safreena agabansa shi da safreena din
Babu abinda yarage musu

Har akazo lbrn GUDU A JEJI da kalar baqar wahalan da suka sha shida safreena har izuwa rabuwarsu
da haduwarsu dasu saeed da taimakon su daya nema

Banda kuka babu abinda su saeed nabeel ahmad sukeyi

Cikin kuka saeed yace ko a film da gidan tv da mujallu ban tabajin wnn lbrn ba gsky dauda ya cika azzalumi butulu maciyi amana marar tausayi marar imani
Gsky ya kamata dauda yagane kurensa ace ka kashe dan uwanka akan dukiya wayyo duniya ina zaki damu ne

Cikin kuka nabeel yace haqiqa da ban bar saeed ya taimake ka ba
to da ban yafewa kaina ba kayi hkr khalifa insha Allah zaga sakayyar ubangiji na wannan jahadin da kayi domin kuwa jahadi ne tsakanin rayuwa ko mutuwa bakaci amana ba ka kula da safreena gsky kai mutum ne khalifa

Karka damu zamu taimaka maka idan har kana bukatar taimako daga garemu muma a shirye muke damu tayaka daukar fansa akan dauda ko ya kuka ce? ya fada yana kallon su ahmad da saeed

Ahmad wanda tun dazu yakasa magana sbd kuka muryansa harta soma dashewa yace nabeel aiba saika tmbye mu ba
Khalifa muna tare dakai duk rintsi duk wuya sannan akwai abokin mu lauya ne bai samu damar zuwa bikina bane da kun hadu sunansa barrister S,M,J
Yana da kirki nasan idan yaji lbrn nan shima zai shigo cikin wnn aikin ladan ayi dashi

Saeed yace shima abokinmu ne kuma iyayenmu ma abokaine mgnr da nake maka ma dadyna da dadyn nabeel dashi dadyn S,MJ din tare sukayi tafiya dan sunkai 6months basu gari

Sanadiyyar abotan kuwa ya nuna nabeel yace kanwar S,M,J din budurwarsa ce dasu dady ma sun dawo inaji za afara mgnr aurensu

Wani dadi ne yakama khalifa cikin hawaye yace nagode muku my guys
Kunsan wani abu kuwa ?
Atare suka ce aa saika fada yace wlh ban taba abokanai ba kwata kwata nikam bani da aboki amma dashike Allah yanaso na a lkc daya nayi abokai uku cikon na hudu sai mun hadu dashi tukunna kuma dukkansu nagari gsky Alhamdulillah

Ahmad yace yanzu dai ku dakata duk ba wannan ba babbar tashin hnkln shine safreena ina zamu ganta?
Domin kuwa wani abun dole sai tana nan barinma zaman kotu

Khalifa yace wlh nasan da haka
Kullum ina mafarkinta inaji ajikina safreena tana raye

Saeed yace kodai jejin zamu koma ne

Nabeel yace to tawani hanya zamu fara bi kaji ka fa da wata magana

Khalifa yace inaji ajikina safreena tabar jeji amma bansan ta inda zan fara nemanta ba fatana daya Allah yasa idan tafito ta fada ahannu nagari domin su kulamin da ita

Ahmad yace insha Allah zamu nemeta amma tayaya ?

Kana DA pic dinta ne khalifa ?

Eh inada shi

Yawwa gud khalifa ina pic din yake ?

Khalifa yace yana bangon zuciyata

Mtsww  ana serious matter amma ka kawo wasa

Saeed yace aa nabeel gskyrsa ne tana bangon zuciyarsa dry suka kwashe dashi

Ahmad yace to Allah yabamu sa'a
Suka amsa da ameen
Suna tashi sukaji ashe har antada sallar asuba
Ido suka ware dukkan su gamida asuba

Alwala sukayi da sauri suka fita izuwa masallaci

Suna dawowa suka kwanta karfe 11 suka tashi sukayi wanka

Suka fara biyawa restaurant sukaci abinci tukunna kafin su dauki hanyar daura karfe 4 suka isa

Haka aka cigaba da hidimar bikin ahmad da amaryarsa khairat
Anyi shagalin lpy angama lpy Sai fatan Allah yabada zaman lpy

KO da khalifa zai koma katsina su nabeel da saeed sukace samm saidai yabisu su koma zaria idan ya koma katsina aikin mezaiyi haka ya tattara suka koma zaria

******

Safreena zaune abun duniya ya taru yamata yawa wani lkcn ba takan rasa tunanin me takeyi amma ta warke tayi tass abunta

Da sauri madina ta shigo dakin ta ajiye mata kaya ajiki

Sis najma gashi nan naki ne yaya sameer yace in kawo miki murmushi tayi ganin kullum saiya siya mata abu ko gajiya ba yayi ne

ki tashi muje Kitchen cewan madina wajen mami mu tayata girki yau dad zai dawo daga tafiya

Shuru safreena tayi to ita tama iya girkin ne
Au to ashe babansu nada rai yo duk zamana agidan nan ban taba ganin saba 

Tace yww sis madina dama inaso in tmbye ki ina dad yake da zama murmushi madina tayi tace dad dan kasuwa ne Sai ya kai miki wata biyar wata shida wata bakwai ka wani lkcn ma har shekara baya gida yanzu ne ma mami ta daina binsa

Jinjina kai safreena tayi madina tace amma yaji lbrnki sosae awajan ya sameer da mami da kuma ni

Dan tabe baki safreena tayi ta miqe tsaye ta dauki gyelenta ta yafa tace muje

Mami suka samu a kitchen suka mata sannu tace yawwa sannunku yan matana maza maza madina zo ki dauki fruits din nan kiyi juice keda najma to mami

Domin su ukune wai zasu dawo
Mami su uku kuma eh madina

DA dadynku bashir da dady sirkin ki
Murmushi madina tayi tana rufe fuska
Mami tace yar'ne ma yau kuma ni kikejin kunya

Safreena dai ido kawai take binsu dashi suna burgeta
Hawaye ne taji ya cika mata ido tayi saurin mayarwa

Ta kalli madina sai murmushi takeyi

Sallaman sameer sukaji amsawa sukayi ya gaishe da mami ta amsa safreena ta gaishesa batare da taɗago ba ya amsa ya kalli madina yace kema fa naga alama kina shirin zaucewa kitafi zariya ko da yake ma ashe can zamu kaiki
Dry ne ya subucewa safreena sbd mgnr da sameer yayi karo na farko kenn
Da ta taba dry suka gani wanda haƙoranta farare tass suka bayyana

Wannan dry ma ƙaramin kashe sameer yayi ba dan saida yaji shock acan ƙasar zuciyarsa

Madina ce kawai ta lura da yanayinsa azuciyarta kuwa cewa tayi duk yanda akayi yaya sameer ka fada tarkon so

Amma idan kuwa haka akwai matsala sbd basusan najma ko wacece itaba tana da aure bata dashi
Tab yaya karka sa kanka awahala

Amma zanyi jarabawa domin na tabbatar wa kaina cewa ko kana SON NAJMA ne ko aa

Tashi ta ta dibo ruwa a cup tazo gabansa tace yaya ga ruwan firgigit yace no madina ba ruwa ba najma ki hadamin coffee din da kike hadamin ki
kawomin part dina
Kai aƙasa tace to yaya yafice mami tabisa da kallo ta girgiza kai tace sameer kenn

Idon madina ƙyam akan coffe din da safreena ke hadawa ta gama tafice

-------

Afuwa my fans am so busy wlh kuyi
Hkr
Yadda naga comments dinku naso ace nayi muku typing yafi haka
Amma ku cigaba da comments ni kuma zan cigaba da anbaliyar typing

Share it

by mmn Ahlan

Continue Reading

You'll Also Like

153K 2.6K 68
Just some short stories about my favorite Ninjago couple, Jay and Nya. This book contains canon oneshots. I have a second book called "The Jaya Chro...
11.8K 72 6
စိတ်ကူးယဥ် အပြာဇာတ်လမ်း.စိတ်ကူးယဥ်သက်သက်နော်. နမချင်းမစာနာတာတေဘာတေလာမပြောနဲ့ ကြိုက်ရင်ဖတ် မကြိုက်ရင်နေ လာမ blameနဲ့ ဆရာမ ဖာဇာတ်လမ်း ။ဖတ်ပြီးရင်တော့ကြ...
14.4K 3.4K 21
A Lawyer, Bold with a bit of anger issues, Smart, Not in good terms with his Father. A Girl, Sweet but Insecure about her weight, With Career tension...
104K 2.4K 51
Alissa Iris De León the daughter of both the Spanish and Italian Mafia. A week after she was born she was sent away from her 2 brothers to live with...