GUDU A JEJI

By fateemah0

2.6K 111 3

GUDU A JEJI, LABARI NE MAI CIKE DA TAUSAYI, CIN AMANA, HASSADA, KYASHI DA SON ZUCIYA, KARKU BARI A BAKU LABAR... More

page 1-2
3-4
5-6
7-8
9-10
11-12
13-14
17-18
19-20
21-22-23
24-25
26-27-28
29-30
31-32
33-34
35-36-end

15-16

134 6 0
By fateemah0

🌳🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳

*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Kuyi hakuri fans 🤦🏻‍♀har yanzu babu labarin waya
Wannan page din Ku ne 💘Allah bar kauna💘

Sannan ina barar adduar Ku mahaifiyata bata da lpy Ku tayamu da adduah Allah yabata lpy🤲🏻

Kuyi manager✍🏻da wannan

Short story✍🏻

بسم ا لله لر حمن لر حيم

🅿_1⃣5⃣➡1⃣6⃣

Har yashiga helicopter aka kunnata taki tashi
Akayi akayi amma taki
Tsaki dauda yashiga jerawa ba qaqqautawa cike da qunan zuciya ya kalli mutanansa yace to uban me kuma yasamu jirgin yanzu?

Daya daga cikin mutanan nasa ne  yace oga wlh lpyr jirgin nan qlu bansan mai kuma yasameta yanzu ba

Idon dauda ne ya canza kala zuwa jajur da karfi ya kwala kiran sunan khalifa
Yana huci saina kashe ka khalifa ni dauda nine ajalinka saina kashe ka saina nuna maka cewa ni  hatsabibi ne saina gwada maka dauda bayada imani ko kadan nayi da wa inda suka fika jida taurin kai kuma duk na shafesu

Kallonsu yayi yana huci yace agyara jirgin nan domin jejin nan dole naje dole na koyawa Dan iskan yaron nan hanabakayana kaiwa nan ya koma cikin gida rai bace

Yana shiga wayarsa ya hau ringing yana dubawa yaga sunan black snake tsaki yaja kafin yadauka cikin isa da gadara yace miye ne kam black snake kafa ta kuramin dame zanji ?

Cikin fushi black snake yace kai dauda kai karamin Dan iska ne ni zaka gayawa zancan banza to wlh nabaka nan da 1wk mutane na su dawo

Dry dauda ya sheke dashi yace dauda shima gagare ne ba kanwan lasa bane mu zuba mugani black snake shege ka fasa yana gama fadi ya kashe wayar

******

Yau safreena ta tashi da wata matsanacin ciwon ciki da ciwon Mara sai juyi take a bukka takasa fitowa khalifa yana waje duk a tunaninsa bacci takeyi domin tunda tafito tayi alwalan asuba ta koma bukkan ta kwanta bata kara fitowa ba har wajan karfe 1 jin shurun yayi yawa yasa khalifa ya lekata idan ma bacci take ta tashi tazo taci abinci ga mamakinsa yana lekawa ya ganta kwance fuskanta shabe shabe da hawaye da kyar numfashinta ke fita sama sama tana rike da cikinta da maranta

Cikin tashin hankali marar misaltuwa yakarasa wajanta ya dago da kanta ya daurata abisa cinyarsa jikinta duk ya jike da zufa alamu tanajin jiki

Murya na rawa ya hau jera mata tmbyoyi
Safreena! Safreena! Safreena
Meya sameki ? Meke damunki ? Me yake miki ciwo ? Sannu Dan Allah ki fadamin menene ke damunki

Cikin wahalalliyar murya tafara hada kalmomin mgn
Tace yaya khalifa cikina marana ciwo

Khalifa yama rasa yanda zaiyi da ita
ajiyeta   yayi yafita ya dibo ruwa yazo yayi tofi ya dagota yabata ta karba tasha
Shuru tayi ahankali taji ciwon namata sauki
Ga kasanta yafara jiqa

Wani hawaye ne mai zafin gsk ya zubo mata gashi bakon watanta yazo kuma baya mata da sauki yanzu yazatayi ga khalifa wani kunya ne taji yakamata ta fara tsinewa dauda acikin zuciyanta

Bacci ne mai nauyi yayi gaba da ita ajikin khalifa

Bata farka ba sai wajan karfe 4 tana farkawa da khalifa tafarayin tozali murmushi ta sakar masa
Ya maida mata shima tashi tayi taji batajin ciwon sosae ba kamar dazu ba

Tana tashi zaune taga jini ya gangara har bakin kofar bukkan da suke zaune wata kukan bakin ciki tasaki tasa tafin hannuwanta ta rufe fuskanta

Sai a lkcn khalifa ya kula Dan shi tunda tafara bacci yatafi duniyar tunani Dan haka bai San halin da take ciki ba sai yanzu

Da yagane me takeyiwa kuka yatashi yafita

Ba da jimawa ba yadawo amma bai shigo ba lekowa yayi yace safreena ki daina wannan kukan kinga bakida lpy karya kara miki ciwo kitashi kije rafi ki gyara jikinki

Cikin kukan bakin ciki tace to wani kaya canza ?

Shuru yayi zcyrsa na masa zafi ga tausayin safreena

Yace bari na cire nawa nabaki ido waje take kallonsa kafin tace kai kuma fa

Murmushi yayi yafita ya dibo kasa ya zuba sannan ya jire rigansa na saman yarage vest ajikinsa tace to barshi haka zanyi manager na daura Dan kwalina

Murmushi yayi

Ta hade rai tace to rufe idonka na wuce
Ba musu ya rufe gamida juya bayansa tafita

Taje rafi ta wanke jikinta da kayan bata koma inda khalifa yakeba har gefen magriba saida kayanta sukasha iska tukunna tasa ta yanka Dan kwalinta kadan tayi ciko dashi agabanta

Tadawo tasa mesa zaune ya kunna wuta murmushi tayi tamiqa masa rigansa

Yace kixo kici abinci yamutsa fuska tayi alamun batajin dadi bazata ciba

Girgiza mata kai yayi alamu bayason gardama
Haka kawai ta tsinci kanta da kasa yimasa musu akan bazata Ciba duk da batajin zata iya ci

Khalifa da kansa yadinga bata kifin daya gasa Wanda shine abincinsu
Awannan sabon jejin da suka shiga

Agurguje

Kwanan safreena biyar ta warke tayi wankan tsarki khalifa yace safreena tunda kinji sauki yakamata mubar wajan nan

Tace to amma yaya khalifa anya zamu fit...bata karasa ba yace mata shiii batason jin komai kawai muyita adduah dama Allah yace zai jarrabe bawansa ta inda baya tunani ki kaddara wannan  itace jarrabawan mu kuma allah yana gwadamu yaga ya karfin imaninmu yake Dan haka karki karaya mucigaba da gudu a jejin nan har Allah ya fitar damu

Murmushi tayi hawaye na zuba a idonta tace muje yaya khalifa na yarda da kai million%

Shima murmushi yayi suka tashi
Suka fara tafiya

Dauda

Angama shirya helicopter 
Dan haka sai jeji

Sunyi tafiya kusan kwana  biyu  kafin wata camera mai nuni Wanda su dauda suka taho dashi yafara nuna danger alamun akwai mutum mgn yayi Wanda yake kula da camera din yace oga akwai mutane anan wajen cikin qaguwa yace asauka anan

Su khalifa da safreena suna cikin tafiya sukaji karan helicopter gabaki dayansu saida hanjin cikinsu ya tsinke afili khalifa yace !daudaa!

Ido waje safreena ta dafe qirji tace baba dauda dai kuka tafara tana cewa mun shiga uku da wannan bakin mugun azzalumi butulu baciyi ama.....bata karasa ba taji bindiga

Hannunta khalifa yakama suka fara gudu amma inaa mutanan dauda sun kewayesu khalifa baiyi auni ba yaji saukan kotan bindiga akai yasaki hannun safreena ya fadi kasa rufesa da duka sukayi baji ba gani

Yayinda wasu ke riqe da safreena
Jina jina sukayiwa khalifa kafin dauda yafito khalifa yana ganinsa ya hau dryn karfin hali naushi dauda ya kaiwa khalifa Wanda hakan yasa takardun dake jikinsa ya fado kasa yasa hannu zai dauka dauda ya harbesa ahannu
Amma yaki yasaki ihu safreena CE tayi kara gamida cewa yaya khalifa

Daukan takardun dauda yayi yace dama na gaya maka yaro rijiya bawajen wasan makaho bane yanzu wayayi winning din game din ?

Murmushi khalifa yayi yace dauda wasa bai kare ba yanzu aka fara ai dama jarumi baya nasara lkc 1 kasa aranka zan dawo domin na nuna maka  banbancin jahili da mai ilma

Dryn mugunta dauda yayi yace idan ka rayu kenn yana fadin haka yakarawa khalifa harbi har biyu safreena CE ta kwace taxo gaban dauda ta wankesa da maruka har biyu

Da iya karfinsa ya mareta ta gangara wata tsiririyar rami mai kamar hanya

Takardun ya kalla yayi wata murmushi yace lkc yayi dauda

Yace Ku cillar da Dan iskan yaron nan kuzo mutafi

Cilla khalifa sukayi

Suka shiga helicopter dinsu 

Su tashi sai gida

Tofa anayinta kudai kubiyo ni muji su khalifa sun mutu ko suna raye

Comments

And

Share

By momyn ahlan✍🏻

Continue Reading

You'll Also Like

30.7K 4K 26
sᴏ ʜᴇʀᴇ ɪ ᴄᴏᴍᴇ ᴡɪᴛʜ sᴇᴀsᴏɴ 𝟸 ᴏғ ᴛʜᴇ ᴍᴏsᴛ ᴅᴇᴍᴀɴᴅᴇᴅ ɪᴛᴠ sᴇʀɪᴀʟ ᴍᴀᴅᴅᴀᴍ sɪʀ❤️..ʜᴇʀᴇ ʏᴏᴜ ɢᴜʏs ɢᴏᴛ ᴡɪᴛɴᴇss ᴏғ ᴛʜᴇ ɴᴇᴡ ᴊᴏᴜʀɴᴇʏ ᴏғ ᴍᴘᴛ ᴍᴇᴍʙᴇʀs ᴀғᴛᴇʀ ᴛʜᴇ ʙᴏ...
Fate By v xxxiri v

Short Story

18.5K 1.3K 11
A story of a young boy Vishnu who lives along with his cold brothers in India, wishing to be taken care and loved by them
14.6K 3.5K 21
A Lawyer, Bold with a bit of anger issues, Smart, Not in good terms with his Father. A Girl, Sweet but Insecure about her weight, With Career tension...
20.6K 256 50
A WOSO Oneshot book Oneshots of favourite Women's footballers Mainly the Lionesses, Arsenal Women's team,Chelsea Women's team, Man City Women's team...