GUDU A JEJI

By fateemah0

3.1K 120 4

GUDU A JEJI, LABARI NE MAI CIKE DA TAUSAYI, CIN AMANA, HASSADA, KYASHI DA SON ZUCIYA, KARKU BARI A BAKU LABAR... More

page 1-2
3-4
5-6
9-10
11-12
13-14
15-16
17-18
19-20
21-22-23
24-25
26-27-28
29-30
31-32
33-34
35-36-end

7-8

161 6 0
By fateemah0

🌳🌳🌳🌳🌳
       🌳🌳
     GUDU AJEJI
🌳🌳🌳🌳🌳
      🌳🌳

       Na

     Zahra Abdul

     (Momyn ahlan)

🌈kainuwa writers association✍🏻
Dashen Allah

Assalamu alaykum fans kuyi hakuri phone dina yasamu problem amma ga kadan kuyi manage

Bismillahi rahmanirrahim

🅿_7⃣➡8⃣

Dagota yayi ya hau jijjigata yana kiran sunanta safreena Dan Allah kitashi karki karaya a kwana 15 safreena kuka yasaka yana neman taimako amma babu mai taimako rungumeta yayi ya cigaba da mgn yana jijjigata amma ko motsi safreena batayi babu alamun sauran numfashi atare da ita

Gabaki daya ya rasa yadda zaiyi duk ya rude kallonta yasakeyi yana kuka safreena Dan Allah ki bude idonki karki mutu Dan Allah ki tashi kece karfin gwiwata na gudu ajejin nan Dan Allah kitashi

Ya kai kusan awa biyu awajan yana rungume da ita can kamar daga sama ya hango wasu halittun mutane maza su biyu jikinsu kayan fata ne daka gansu kaga qabilun jeji

Ihu ya hauyi yana kiransu bayin Allah taimako
Su kuma da sukaji ihu sun dauka wani naman jejin ne suka hau waige2
Can suka hango su khalifa wajansu suka karaso
Sai kallonsu suke SBD basu taba ganin halitta mai kyau kamarsu ba dayan cikinsu ne yasa hannu ya shafi fuskan khalifa yana murmushi khalifa kallon ikon Allah kawai yakeyi
Dayan ne shima ya miqa hannu zai shafi fuskan safreena da sauri khalifa ya buge hannunsa ya hade rai ya girgiza masa kai alamun aa ja da baya yayi

Mgn yake musu amma sun tsaya kallonsa SBD basu gane yaren da yakeyi shima kuma baya gane nasu da hannu ya musu alama da suna neman taimako

Mgn suka hauyi da Dan uwansa kamar fada fada
Bayan sun gama ne suka kalli khalifa suka masa alama da hannu sutafi

Tashi khalifa yayi ya dauki safreena kamar baby ahannu Wanda har yanzu bata motsi tafiya suka hauyi Wanda da kyar khalifa keyi SBD shima agajiye yake ga yunwa ga qishin ruwa
Sunyi tafiya kusan awa daya kafin su iso wani dan karamin kauye Wanda duka duka mutanen kauyen bazasu wuce 25 ba da yan bukkokinsu kanana
Sai kallonsu khalifa sukeyi da safreena wani Dan karamin bukka suka nuna masa ya kai safreena wajan
Bukkan yashiga yaga wata tsohuwa fuskanta duk ya yamutse murmushi ta masa
Sannan tayi masa nuni da gadon kara alamun ya kwantar da safreena akai ba musu ya kwantar da ita domin matar kamar mai magani ce

Fitowa yayi yana neman ruwa can ya hango wasu manya manyan tuluna da ruwa acike fal da wata gwangwani aciki dauka yayi ya hau shan ruwan nan kamar ba gobe  yan' kauyen sai kallonsa suke yana gamawa yafadi kasa asume da sauri suka daukesa suka kaisa wani bukka

Magani suka fara yi musu SBD gabaki daya kafarsu ta kumbura sannan wani waje ma harda yankan qaya

Dauda agaban wani mutum daka gansa gaka cikakken mugu marar imani da tausayi fuskarsa baqiqirim amurtuke ga tubi  babu alamun rahma shi karan kansa dauda rissinawa yayi agaban mutumin mai suna black snake

Dauda yafara mgn cikin rawar murya black snake taimako nazo kamin da mutanen ka wani dan iskan yarone ya gudu min da dukiyata shida wata yar'iskan yarinya na tura mutane sunfi aqirga amma sun kasa kamasu SBD gudu ajeji sukeyi wasu mutanen ma basu dawowa wai naman jeji ya cinyesu shine Nazo ka taimaka min wani abokina ne yabani lbrnka akan cewa idan kasa yaranka aiki mutum yasa aransa aikinsa yayi angana shiyasa nayi tattaki nazo tundaga abuja har lagos Dan Allah ka taimakeni black snake

Wanda aka kira da black snake ya kalli daya daga cikin yaransa yayi mgn yace idan harka yarda zaka raba dukiyar taka kashi uku mu dauki kashi biyu ka dauki daya zaro ido dauda yayi kafin yace haba dai ina ma laifi kuce arabata kashi biyu na dauki daya Ku dauki daya

Wannan karon black snake dinne yayi mgn yace idan ka amince to idan kuma baka amince ba tashi katafi

Tunani dauda ya hauyi idan fa bai amince ba to hakika babu Wanda zai iya kamo mishi su khalifa Dan ya fahimci yaro ne mai matukar wayo sannan ko a kashi dayan nan ne tofa dole sunansa ya fito aduniya wato alhaji dauda yahya wani murmushin mugunta yayi kafin yace ya amince

Black snake yace jeka kawai kasa aranka takardunka sunzo hannunka murmushin nasara dauda yayi yace akashesu duka yaro da yarinyar takardun kawai nake bukata

Black snake yace amma sainan da sati daya tukunna zan tura mutane na sbd a helicopter zan turasu
Jejin da kake mgn bazaiyu ace antura mota ko aje da kafa ba amma parat daya zamu musu
Dauda ya miqe tsaye yana cewa babu damuwa black snake ngd ayi musu kisan wukalanci kafin yasakai yafice

Khalifa bai farfado ba sai dare yana farkawa yaga hasken wuta awaje tashi yayi yafito yaga ashe wuta suka kunna sbd dare wato karare yana fitowa hanyar bukkan daya kwantar da safreena yayi wani tsoho ya riqesa amma ya kwace hannunsa bukkan yashiga yaganta kwance har zuwa yanzu bata motsi wasu zafafan hawaye ne suka wanke masa fuska na tausayin safreena lallai saiya koyawa dauda hankali saiyasa dauda duk second na rayuwarsa mutuwa ce tunda yasasu gudu ajeji

Wannan tsohuwar ce ta kamasa ta zaunar dashi kusa da safreena wasu kwanuka ne ta dauko  masa Wanda akayisu da kwallon kwakwa abinci ne aciki tana murmushi ta tura masa gabansa budewa khalifa yayi yaga wani bakin tuwo da bakin miya wanda ko kashesa za ayi ace yafadi tuwon miye ne bai sani ba

Tunani ya hauyi dole zaici wannan abincin domin ya rayu SBD mutanen kauyen shi sukeci suke rayuwa Dan haka shima  da safreena zasuci domin su rayu
Su tozarta dauda a idon duniya

Tuwon ya hau ci baji ba gani saida yaji karfi sosae ajikinsa  kafin yabari ruwa tsohuwar tabasa ya karba yasha sannan ya tashi ya fito waje ya hau alwala duk suka koma kallonsa har yagama ya gyara guri yatada sallah duk suna kallonsa harya idar tukunna ya koma inda safreena take ya zauna yasa kansa agefen gadon karan datake kwance nan  wata bacci mai nauyin gske tayi awun gaba da shi

Bai farka ba saida rana tayi zafi sosae tukunna yatashi agurguje yayi alwala yayi sallah nan ma saida suka tsaya kallonsa

Wasa wasa saida safreena ta kwashi kwana uku bata farfado yashiga tashin hankali marar misaltuwa Dan shi gani yake kawai ta mutu amma suna kwantar masa da hankali akan cewa tana raye duk da ba yaren juna sukeji  ba

A kwana ukun nan sosae khalifa yasaba dasu  wani lkc har rafi yake binsu kamun kifi
A daren kwana ukun ne 
Safreena ta farka kamar kullum  khalifa yana zaune kusa da ita yaga hannunta yafara motsi
Da sauri yatashi yafara kiran sunanta ahankali ruwa tsohuwan tabasa yabata dagota yayi yamata masauki akatafaren qirjinsa sannan ya hau bata ruwan tana sha tana gamawa ta hau tari yana bubbuga bayanta ahankali da kyar take iya hada harafin sunan  yaya  khalifa

Hannunta yakara kamawa yace safreena gani akusa dake zakici abinci? Daga masa kai tayi alamun eh da kansa yadinga bata abincin tana ci harsai da ya tabbatar taci dayawa kuma ta koshi tukunna yabarta

Da washe gari ta warware dama gajiyar gudu ajeji ce da yunwa da rashin bacci ga kuma tashin hankali

Sosae suka saba da yan kauyen duk da basu iya mgn da juna saidai mgnr kurame

Yau sati daya tacika dauda sai murna yakeyi yau za akashesu khalifa da safreena sannan akawo masa takardun dukiyarsa

Su khalifa da safreena da yan kauyen suna rafi gabaki dayansu sunata wasa da ruwa safreena sai tsokanar khalifa take da gangan zata dibo ruwa ta watsa masa

Yayi kamar bai San tanayi ba

Hade rai tayi tazo gabansa cikin shagwaba tace shine kayi banza dani zaro ido yayi yace na isa nayi banza dake ai sai Allah ya tmbyeni kawai zanso ki natsu ne SBD naga alama kamar kin manta kalubalan dake gabanmu sannan kum.....bai karasa ba yaji karan bindiga daga sama

Da sauri safreena ta rungumesa SBD tsoro

Jan hannunta  yayi cikin tashin hankali amma inaa an kewayesu ko ina harbin bindiga ne

Saiga mutane sunfara  zubewa kasa sakamakon bullet din dake huda cikinsu
Duk a mutanen kauyen nan babu wani kwaro da yayi saura araye

Idon safreena a kulle gam tana jira taji bullet ajikinta amma can anjima taji shuru tana bude ido tayi arba da gawanwaki ihu tasaka da karfi tafara kiran sunayen yan kauye amma ina babu mai sauran motsi khalifa mutuwar tsaye yayi domin a idonsa mutane sukadinga zubewa kuma da gangan su aka ki harbinsu aljihunsa ya shafa yaji takardun suna nan Dan baitaba rabuwa dasu ba 

Karasowa gabansu
Sukayi wani yasa hannu zai kama safreena da zafin nama khalifa ya fizgota bayansa

Amma ance sarkin yawa yafi sarkin karfi
Yanje safreena sukayi da karfin tsiya suka rufe khalifa da duka baji ba gani
Gabaki daya sunyi mai jina jina safreena ihu kawai take tana kuka





Wayyo kuyi manage da wannan sai mun hadu a next page
Wlh wnn ma da kyar nayi insha Allah gobe zan sake typing

Comments

An

Share

By mommyn Ahlan

Continue Reading

You'll Also Like

133K 2.2K 27
រឿងមួយនេះជាប្រភេទ BL s*x ចង់អានក៏អានចុះតែបើប៉ះពាល់អារម្មណ៍កុំបន្ទោសអ្នកសរសេរឲ្យសោះហើយក្នុងនេះក៏មានពាក្យមិនសរម្យច្រើនដែល🤏🔞 Taekook all story 🤯 ___...
13K 203 51
luke hughes instagram story
10.5K 1.7K 15
Another collection of Short Stories
690K 2K 50
🔞🔞🔞 warning sex!! you can cancel if you don't like it.This is only for the guys who have sensitive desire in sex.🔞🔞