NAUFAL (THE CHARMING) (COMPLE...

Da missxoxo00

39.6K 2K 27

Labarin sanyayyar tacacciyar soyayyar ruhi biyu.. Wanda akai wa auren dole da juna, Amman basu san da hakan b... Altro

EPI 1: THE BEGINING
EPI 2:
EPI: 3
4
EPI 5
EPI 6
Epi:7
Ep:8
Ep:9
Epi :10
Epi 11
Ep:13
Epi 14
Epi 15
Epi 16
Epi 17
Epi 18
Epi 19 (FINALE)

Epi:12

1.7K 97 0
Da missxoxo00

•⭐•⭐•⭐•⭐•⭐•

     

AYUSH najikin window inda taga motoci a convoy sunyi parking akofar gidansu ankashe titin unguwar ga gidan yacika ba wurin parking space.tsaki tai tareda komawa kan gado. Janyo locker dake side drawer dinta tai sannan tadakko wani eye drops dinta datasan Tana sawa yake sata hawaye tareda,sa hannunta ta tacire contact  lens din dake cikin idonta sannan tadigashi nan danan idon yai mici mici yai ja murmushi tai bayan takalli kanta a mudubi sannan ta janyo bargo takwanta tasa hannu tarike cikinta irin wadda ciwon cikin nan ya takurawa tatakure waje daya tareda kashe AC din dakin.

Meanwhile angwaye nashigowa gidan akadau guda..shide NAUFAAL se sunkuyar dakai yake musamman dayaga sunnufi inda mommy take mahaifiyar AYUSH ga kuma mamaa mahaifiyar neerah duk atare suke waje daya sunci super wax atamfar su Iri daya sak ta mommy purple and black ta maama kuma orange and black.gayshesu sukai sannan suka nemi wuri suka zauna.nanfa me gaskiya photography yafara kashe pics atare iyayen suka tashi aka dauka dasu tareda angwayen biyu NAUFAAL dakuma mahbub.kawayen amaren se raba Ido suke tabbas neerah da AYUSH sunyi Dace. Se asannan ashram tasaki baki da hanci Tana kallon NAUFAAL tabbas shine wanda aka kira yai biography din ango a bikin Hafsat matar sameer .amma AYUSH daxata yiwa kanta wannan santalelen THE CHARMING din ya amsa sunansa.bata Ida zancen zucin datake ba mommy tace taje sama takira amaren biyu su sakko si hotuna da angwayen sauri suke xasu tafi.

Ashram tanufi saman da sauri dakin neerah tafara shiga wadda se dauri take akanta sample din turban knot head Wanda ake cewa xahra buhari.ga face dinnan Tasha foundation dasu Contor da highlight hancinnan anyi blending dinshi yashige ciki.

Sanye take cikin wani tsadadden lace skirt da Riga,skirt din tanaja har kasa plain color ne na blue xalla se pearl dake sakale ajiki blue yasha dinki Wanda malaabis by maymz tadinga se material vein shima blue.tayi Kyau ba karya dama gata fara wai akace farar mace alkyabbar mata... Ashram takarasa ciki kinyi Kyau hajiata wannan matso Kyau haka? You looked so take away ..Neerah tai murmushi Kai ash karfakisa kaina tai kato gashi kinsa nafara wani blushing..ashram tai Daria Allah kinyi Kyau neens ita kuma AYUSH nata lace din pink ne ko??neerah tace ehh Komi Iri daya ne ai itakuma pink ne nata..ashram tace Allah  xafa ku matso Kyau mrs mahbub kar incikaki dasurutu kije injisu mommy da mamaa ,mahbub najiranki akasa kije xaku kashe pics. Neerah tamike Tana gyara mayafi toh ganinan kalla fuskana bawani gyara ko??? Wannan kwalliyan naki ko Hasidin iza hasada ai bare kusheba. Neerah tai murmushi to nagode sannan tanufi kasa se wani rausaya take.

Dakin AYUSH,ashram tashiga, bata lura da kan gadonba Dan taji motsin ruwa A bandaki. AYUSH Habibty amma de yar wulakanci ce ke Wlhy ,sisters din mijinki tundaxu ke kasa ana masu kunshi ko gaysawa bakwi ba se faman tambayanki suke dama Nadia suka sani ita kuma Tana afficent sunje Kai savouniers. To fito mommy nakira mijinki yaxo yana kasa xakwi pics ga neerah tundaxu tagama shiryawa tasauka kasa ke kullum kece karshe akomi kinfiso kibatawa mommy rai. kofar bandakin taje Tana bugawa amma shiru hakan yabata damar budewa amma wayam bakowa se asannan takalli kan gadon AYUSH ce kwance a lullube Tana bacci.. Kut ashram tace Allah de yasa lapia inkwa lapiar ki kalau kike bacci Wlhy sena sharara maki Mari! Yaye bargon tai ganin AYUSH jikinta daxafi se gumi take ga AC akashe sa hannu tai tabude idon AYUSH yakankace yai jaa se hawaye yake. Salati ashram tai sannan ta nufi kasa ,se pics akewa neerah da mijinta itade ashram gurinsu mommy tanufa dake hira agefe dawasu yan Uwa. Mommy naganin ashram tace Inatake tayi halin nata ko? Ashram ta girgixa Kai mommy AYUSH ba lapia fa,Dan da alama wanka xatai ta Tara ruwa a baho xatai wanka amma Batai ba, AYUSH batada lapia sosai mommy Dan AC dinma kashe take ga jikinta yai xafi idonta ya kankance yai ja,may be fever ne!

Mommy tamike itama Tana salati toh Allah yabata lapia sannan ta fadawa su mamaa da sauran Matan dake wajen. Hawa mommy tai saman tanufi dakin AYUSH din ,taba jikinta yai tabbas da zafi ga idon nata ya kankance .tashinta mommy tai ke meyasa meki? AYUSH tai wiki wiki da Ido mommy dama tunjiya nakejin ciwon ciki sannan neerah takwomin abu a cup tace Injiku inshanye, toh dama inada stomach upset shine naketa gudawa kuma inaga da zazzabi Ma! Mommy taji tausayin yar' tata sannan tamike Tana fadin Allah yasawwake bari namiki allura  xuwa anjima xakiji dansauki kyaje Elegants eve din kawai dama mijin kine yaxo ake pictures nace akiraki. Fita mommy tai danxuwa tahado allura , AYUSH taxaro Ido shikenan ko alluran meye mommy xatamin?? Allah de yasa bata zazzabi bace nashiga uku..Tana rufe baki mommy tashigo dauke da alluran a hannunta ,, AYUSH tai murmushi mommu dama kinbari xeyi sauki ae, mommy tace baride inmaki anti bacterial ce ai, inaga food poisoning kika samu.hamdalah AYUSH tai azuciarta sannan mommy tamata alluran ,kwanta Allah yasawwake barin gaya masu bakida lapia. Mommy naxuwa tafadawa NAUFAAL shide se sunkuyar dakai yake yaga sirikarsa,bayan anje andubata sannan sisters dinsa Nabeelah da na'eelah suma suka shiga Wanda Asmahan ta yarfa masu lalle. Nabeelah takalli NAUFAAL dake kan kujera Yaya kahau kadubata semuwuce inyaso Elegants eve din maje tagida Dan dinkinmuma banajin tailor dinann ya Dinka.

Nodding Kansa kawai yai sannan suka hau saman tare,dakin tafara shiga aunt Jiddah ga Yaya xedubaki sanann ta fice.Itade AYUSH murmushi kawai amma azuciarta bnda bacin rai babu kome Kai wannan ustax ko maye toh de kwalelanka ba xa'asamu damar daukar pics din daniba.shiga tai cikin bargo tareda rufe kanta.da sallamarsa yashigo dakin amsawa tai a hankali Tana cikin bargo .kallonta yai yanda tacukwiwiye da bargo se abin yabashi Daria yace yajikin Hawwa?? Dasauki tace ,,toh Allah yakara sauki yadanxauna shiru taki magana kawai seya mike yafice.. Daria AYUSH tai tareda mikewa tanufi bandaki tai wanka tareda maida contact lens dinta .

  Karfe 2:30 aka fara tafiya Elegants eve, amaren sunci ado cikin dogayen riguna na wani Abu Wanda nikaina bansan lace bane ko material yasha ado dogon rigar mehade da riga kaman  Riga da skirt amma dogon rigane se ja yake da kasa sosai sosai bagwaggaro bane no nada musu shi akai kaman abaya da mayafinta sunyi Kyau ,they looked so amaizing  and beautiful abin sewanda yagani.

Motoci aka tafi a convoy se afficent event center dake kano tent dinci yasha Kyau ,kawaide guessing Irin Haduwar da gurin yai xakwi can nahango DR SAMEER AMEER da matar shi NASREEN agefe da little sultan,suna shigowa  bridal train aka saki wakan korede Bello#DoLikeThat.high table din was beyond amaizing.komi de yayi Kyau sosai blah Blah blah...nahango su Nafee Anker,cute xarah,Hafsy rano ,miss Hafsy da Qurratul ayn hardasu Huddah dake gefe daya dasu miemie bee da anee su stylish da Yaya Hajja harda is su zee yabo da ayusher ga maman shakur  gasu Zaynab Ibrahim .harwani extra table waina yan excellent writers da online Hausa writters suma sunci ado abinse Wanda yagani. Suma su home of novels su Billy s fari,miss pina ,mom heena,Myriam ,mjay ,khadija,nidarh dasu safiyya from hugumas grp su lymerh,maimuna,Billy Billy,meenat and lots of loved ones na home of novels suma yan xoxo's palace ba abarsu a bayaba#BFF..

  In conclusion anci ansha anyi liki anyi rawa dukda ba maxa amma abinse yaburge mutum ga savouniers kamar mutum yagudu Dan tsabar yawa.karfe 6pm aka gama Komi sannan suka nufi gidah su Nabeelah da naeelah kwalliynsu yayi masifar Kyau.sannan aka fara shirye shiryen Kai amarya neerah dakin mijinta ita kuma AYUSH segobe tunda gidanta a Abuja yake.

Koda aka koma gidah bawani abin akeba Banda shirye shryn Kai neerah dakin miji,dukda baaba ne xekaita da kansa amma yan Uwa sunce xasu.yammata se gyare gyare ake xa'ai siyan baki koxasu samu nasu mr right din acan(ko mr left kukasamu kwayi dragging idiot din to the right)gashi mahbub ya Matsa kan lalle se NAUFAAL yaje gidansa ansai baki dashi.gidan neerah dake hotoro aka kaita flat(bungalow)Komi yaji tsaf dashi bayan anmata fadan yi nayi Bari nabari.su neens dadi kashewa xa'agidan miji though tayi kuka ba lefi musanmn xata rabu da yar'uwarta AYUSH wadda tace koxataje kaita sedaga baya anjima dantaji ance siyan bakin da wuri xa'ai and batasan haduwa da ustax dinnan NAUFAAL.haka aka fita da neerah xuwa gidan mijinta mahbub tareda dandaxon yammata dansu samo nasu rabon suma,amma AYUSH ko ajikinta sema adduar da tai na Allah yahadashi da Wata acan.

Hmmm AYUSH kenan miss xoxo is going to mind her business and eat her dumamen tuwon shinkafa miyar karkashi + manshanu and wash it down with kunin aya me sugar .miss xoxo cannot take Panadol for AYUSH undetected headche o.now this dumame is too delicious family!lemme enjoy it in peace. I don't know what TeamAYUSH will say about this. But for my teamNaufaal I will advice you too to find delicious JOLLOF rice and eat While minding your business..you can't help someone who doesn't want your help person like AYUSH.

                 😂🙈

    Fili gareku teamAYUSH I dunno what you guys gonna say sha...

                  •⭐•

•⭐•⭐•⭐•⭐•⭐•

BAYAN ankai neerah gidanta manya duk sukatafi bayan sundan Kara mata fada,tadanyi kukanta sanann aka barar raje ita da yammata masu jiran siyan baki.neerah tamike tanufi dressing mirror dinta Tana gyara face dinta kwalliyan looked so dull ,Nadia tace a'a dande kinyi kuka ne hajiata amma daxu Kinga yadda kikai Kyau kamar cindrella.neerah tace to Dan temaka Nadia gyara min kwalliyana please..Nadia tai Daria osheeey gwara damuka aurar dake Wlhy..Neerah tai murmushi okay dase nataxama agidah kenan inataya maama abinci impossible kinji kowacce diya mace dakin mijinta shine gatanta. Nadia tace toh Allah yakawo baby boy sannan tadakko cosmetics kit din ..neerah tace healthy babies masu albarka ba.

Haka de sukai ta hirar su sukuma sauran yammatan nawaje ana tsadancewa da abokai kudin siyan baki.banda NAUFAAL dake gefe kamar yatashi yashake Wata ikram kawar amarya sewani fari take Tana magana be ida tunaninsaba ikram tacigaba gaskia we can't let you in yes that's it..100k mu kusan 20 ai yayi kadan gaskia ko akara ko mutafi da amaryarmu.ango mahbub dake gefe yai Daria toh nawa xamu Kara?! Wani makokan bakin ciki ne ya'ishi mahbub aikwa zuruf yamike yanufi inda ikram take excuse me please..ikram sewani juyi take taga Dan THE CHARMING yanace mata excuse azatonta wani abin arxikinne*mba no o, laughs* NAUFAAL yace yes kince bara kibari a 100k ba nace wannan siyan bakin al'adane ko sunnah ce?? Hell no!to please 100k xa'abaku kidena wani bubbling words tunda amarya de dole kutafi kubarta anriga andaura aure ...saboda haka wani maida magana ya isa haka say no more pease ,kina wasting mana time inbaku San 100k din fine haka mukeda karfin shi kawai,bejira tayi magana ba yasa hannu a aljihu yaciro wrapper na 100k notes ya aje agabanta.sannan yajuya yakalli mahbub angon ,mahbub Ni inawaje inkunyi settling mahbub yamashi godia sosai abokai akadau THE CHARMING firgita yammata.

Itade ikram kasa Ma magana tai bawai abinda yafada mata ke hanata magana ba no CHARMING face dinsa da kuma voice dinsa datake dukan dodon kunnanta se tariyo wa take Tana lumshe ido*gross* Ashram da tunda yafara magana takasa sukuni yana fita ta sulale tabi bayansa..daga can gefen bakin gate din tahangoshi xaune kan irin kujerun Robar nan na xama farare.gyara fitted gown dinjikinta tai tareda dedeta daurin dankwalin kanta na ture kaga tsiya Wanda ya xauna cif danhar takarda taninka tasa ciki. Cat walking tafarayi Tana tafiyarta cikin daukar hankali dukkoda shi Kansa a akasa yake yana Danna wayarsa hasken wayar ya dalle masa face dinsa se alokacin ashram takara tabbatarwa NAUFAAL din bakaramin THE CHARMING bane... Allah de yasa burinda ta taka azuciarta yai galaba akansa..

Karasawatai wajensa batare da tayi magana ba taja kujera taxauna hello handsome tace mashi Tana wani fari da ido Tana wani faman chest out. NAUFAAL yai shiru kaman yataba ganin face dinta somewhere even though he can't recall but yataba ganin fuskan for sure ,murmushi yai yana magana azuciya Bari yadanyi game of chess dinann de tinda dama he's bored..yace hi gorgeous.nanfa ashram takara rikicewa ganin yadda NAUFAAL ya amsa mata seta nemi wani fargaba ta rasa tabadawa idonta kasa ta ajiye kawancen su da AYUSH a gefe duk azatonta har zuci NAUFAAL yafadi haka batasan yafita runs ba...takara wani kashe murya tareda shigar da ita ta sirantata kunsan yammata da different voices Wata voice dinma  alokacin ake manufacturing dinta. Dama nabiyokane nabaka hakuri kan little argument dindakuka samu kaida friend dinmu ikram kayi hakuri on her behalf. NAUFAAL yai murmushi ohh about that,,no it's okay ai,,bawani abu ninama manta hutawa kawai naxoyinan thanks for caring.

Ashram tai murmushi you deserve more than that..xankoma ciki suna jirana sannan tadakko wayarta pls can I have your digits(number)) can we be friends?! NAUFAAL yasaki baki yana kallonta toh haka era (zamani)dinkuma yakoma mace dakarban number din namiji?!wayanta yakarba sannan yasa mata number gashi ko..ashram tamike Tana gyara mayafinta mekamada abin tatar ko ko.its nice meeting you though bamusan sunan junaba.. NAUFAAL yace I'm popularly called THE CHARMING you?! Ashram tace wow nice name well Kaci sunanka ai my friend. Sanann tai shiru ganin karta fadi sunanta asirinta ya tonu sunana nana amma amfi kirana da cherry. NAUFAAL yai Daria I cherish you ..Wayyo kuxo kuga blushing da flattering gun ashram gaba daya haka daya fadi she feels on top of the world Kamn ammata albishir da babban Rabo.sannan sukai sallama tatafi ko number ta NAUFAAL be karbaba Tana tafiya yai Daria Kai wasu Matan akwai xubda aji wallahy sannan yakira mahbub yamasa sallama yatafi Dan akwai important abunda yakeson yi.

NAUFAAL yana tashin motarsa yana tafiya, AYUSH tai parking nata motan itada bilal kaninta sannan suka shiga cikin gidan,nan aka dauka da amarya..itade murmushi tai sannan tashiga dakin da neerah take mazan duksun watse wasu kawayen Ma babu se yan biyu da nadia dakuma ashram(cherry). AYUSH takarasa kusada neerah Tana Daria Hajia gakifa agidan mahbub..yau mahbub xemaida neerah tasa.itade neerah murmushi tai kema aigobe xaki tafi gidan naki mijin.. AYUSH tamike Tana who told you so?!daga komawa Abuja gobe se akaini gidana your not serious . Neerah tace shi yaxo yadauki kayansa ai.. AYUSH tace Wlhy niba Kaya bace kinji atoh. Neerah tace toh pardon Ina nufin toh matarsa. AYUSH kyaji dashi  Nina tafi gidah seminxo suna .baba yace kar indade shi yahadoni da bilal..neerah tace toh nidake aga Wanda xeriga wani haihuwa ai.. AYUSH itade murmushi tai sannan takira bilal suka wuce gidah.ashram se wiki wiki take da Ido abinka da guilty conscious ko cikin ruwa se anganeshi.

NAUFAAL nakomawa gidah ya wuce dakinsa yaciro files na case din faruk kamis na Nile university Wanda ake zargi yakashe sister dinshi  yakira wani awaya taredasawa a handsfree hello mutumin ya?! Wanda ake kira da mutumin yace THE CHARMING Komi is ready xaka iya xuwa ka karba gobe..NAUFAAL yace toh nagode kamil kamar karfenawa?!saboda gobe xantafi Abuja kasani ai.. Kamil yai Daria I know right NAUFAAL Ina newly bride din amika gaysuwana insha Allah xuwa 8 everything is ready. NAUFAAL yace toh nagode sosai xataji sannan katabbatar komi kasa yadda yaka mata da Muhammad Areef xa'aringa kirana age 27 level 200 Nile university ,department of law ko?! Saboda by Monday nakeson infara gudanar da aikina.kamil yace kakka damu mutumina ,sanann NAUFAAL yakatse kiran tareda lumshe idonsa AYUSH ta Ina xanfara nemankine niko SAMEER xankira ne?!hakade yaita maganar sahibar tasa harde bacci yadaukeshi...

Da sassafe yana breakfast yawuce wajen kamil karbar abunda yasashi yana Fita,yan gidansu AYUSH akakawo AYUSH tareda manya gaisuwar uwar miji/budar Kai.tabbas Ammi tayaba da hankalin hawwa_jiddah (AYUSH )din dukkoda a lillibe AYUSH din take cikin lafayarta ta alfarma pink and black Sannan low hill shoe dinta ma black tayi Kyau ba karya.ga abinci nan anyi kala kala se wajen 10nasafe Sannan sukai masu sallama xasu tafi bayan Ammi Tama AYUSH fada irin na uwar miji , ko Ina na gidan yakarade da aunty jiddan Yaya NAUFAAL ce taxo kunsan auren Dan fari namiji yadda akeji dashi ,Tasha Kaya kama daga perfumes ,atamfofi,laces,da kudi da yawa yan Uwa aka Tara mata ita kwa nata Ammi saukar akwati tabayar sukutum cike da Kaya Sannan sukai masu sallama kan suxasu farayin gaba dankai amarya gidanta dake Abuja sukuma sauran yan uwan ango NAUFAAL se bayan azahar jirgin rana xasubi sudasu Nabeelah da Na'eelah Ammi dakanta takarba number AYUSH tareda doriyar itama mahaifiyarta ce kartaji Komi takawo karar NAUFAAL inde hakan tafaru Sannan duk abinda takeso takira ta tambaya gakuma su Nabeelah nan suma agarin suke xasu ringa xuwa.itakanta AYUSH din tayaba da irin dattako,karamci dakuma sanin yakamata irin na uwar mijinta dakuma yan uwansa hakika sunkarbesu hannu dubu bama biyu ba.inama ace iyayen Wanda takeso ne haka?!sallama suka masu sanann drivers sukaja motoci suka tafi.

nanahafsat.wordpress.com

                      •⭐•

It's a love story that you wouldn't afford to miss out,check out my blog to read the interior fun part of the lovers team#NAUFAALOVERS👄

118

PART 2

    It's all about love story between a charming handsome and a beautiful lady..NAUFAAL&AYUSH.congratulations perfect couple Allah yakawo healthy babies😂💕

     •⭐•⭐•⭐•⭐•⭐•⭐•

Koda suka koma gidah bawani abun akaiba shiri kawai suka sakeyi Sannan aka debi yan Uwa guda 10 including mommy datace xata koma gidah saboda aikinta.se mamaa dakuma aunties na both mommy da baabaa.karfe 11 Dede jirginsu yasauka a Nmandi azikwe dake Abuja Capital territory. 11:20 Dede suka Isa kofar gidansu AYUSH Sannan suka firfito Dan kai amarya se after magrib akace tunda yan uwan angonma se da rana jirginsu  xe iso.shiga sukai ciki Kai tsaye AYUSH tawuce dakinta tareda sakin wani kuka matsinaci shikenan ustax yagama da rayuwarta yasata ahalin tsaka me wuya batagama tunanintaba Nadia tai knocking kofar tareda shigowa .

Mata agidan NAUFAAL. AYUSH taja tsaki wannan kuma kekika sani waye NAUFAAL?!nadia tai murmushi sunan sound like melody ko?! Well sunan mijinki ne..tsaki AYUSH taja to me ruwana wai Ma meya kawoki dakina?! Nadia tadinga Daria harda rike ciki matar NAUFAAL yi hakuri mana nan dakin na Nadia ne itakadai yanxu ai kintashi daga medakin bankibade inkinxo haihuwa ko inyayi tafiya kya iya xuwa ki kwana.bari Ma kiga Sannan Nadia tadauki akwati guda daya tareda Jan daya tabude kofar Tana kiran su bilal su kwashi sauran xa'akai gidan amarya AYUSH.wani sabon kukanne yaxoma AYUSH tabi pink dakin nata da kallo medauke da posters din mufti isma'il menk.sannan tasaki wani kukan .nadia taturo kofar Tana waka taxama taxama taxama,taxama dakko riga taxama dakko wando taxama.bata gamaba AYUSH tamike tana huci,kafin tace wani abu Nadia tagudu Tana fadin kije inji baba Yana parlor dinsa na dakinsa.seda taci kukanta Sannan tawanke face dinta tanufi parlor din babanta.

Da sallamarta tashiga ciki,baban ya amsa Yana shan ruwan lipton gefe guda kuma snacks ne Akan plate..Baaba yace Yawwa mamana xokixauna mana. AYUSH takarasa Tana hawaye.baba yace a'a banasan kukannanfa haba mamana aure fa akai miki bawai saida ke xa'aiba. AYUSH tai shiru se ajiyar zuciya datake. Baba yace Yawwa mamana takaina dama alkawarin danadade damaki yau nacika makishi. AYUSH tadago jajayen idonta dasuka kumbura saboda kuka Tana kallon babannata. Baba yace dafarkode nextweek xakufara lectures ko?! AYUSH tai nodding kanta,baba yace toh munyi magana dashi NAUFAAL din yace ba matsala insha Allah xaki je.sannan Abu nabiyu kuma da sabuwar motarki xaki fara xuwa school din taki halak malak irin wadda kikeso benz red color right?! Ai AYUSH data dire wani tsalle tai hugging babanta seta nemi bakin cikin datakeji tarasa,tadade tanasan motar kanta amma baba yace a'a in lokaci yayi xebata,togashi yanxu yabata kuma dream car dinta benz lover ce dama gashi favorite color dindatakeso red.

Baba yaci gaba da cewa yauwa nasiya maku harda Nadia da neerah sede su ba Benz bane, Camry ce kowannensu ke saboda biyayyar dakikamin amatsayina na mahaifinki Dana xaba maki miji kuma kika yarda kika amince shysa namiki wannan babbar kyauta. AYUSH tai hugging mahaifinta tana hawayen white stomach*laughs* nande baba yamata fada sosai kantabi mijinta AYUSH kibi mijinki NAUFAAL kada kitauye masa hakkinsa na aure domin mala'ikun Rahama suna tsinewa duk matar datai haka ,hakade baba yaita bama AYUSH fatherly advice Sannan yace tatashi tashiga ciki kar anemeta Allah yamaki Albarka idan anyi servicing motar xa'akawo maki har gidah. AYUSH tai godia Sannan tamike tashiga ciki tana mewa Allah godia dawannan babbar kyauta da mahaifinta yai mata.sannan tafice xuwa nata dakin.

Nanta tarar da kanwar mommy aunty lubna da cup a hannunta madara ne dayasha zuma se slices na water melon(kankana) Yawwa AYUSH rike Kinga lokaci Yana tafiya shanye tsaf akwai abinda xami.bayadda AYUSH ta iya adole tasa hannu ta karba cup din tashanye duka Sannan ta mika Ma aunty lubna..aunty lubna tace Yawwa yar gari ga ruwan wanka can a toilet karki wasa dashi pls hadin gaf gaf ne ,itade AYUSH nodding kanta kawai tayi Sannan tashiga bathroom din tai wanka da ruwan kamar turare dan kamshi take jikinta Yaxama so smooth and silky. Futowatai sannan taxauna abakin gadon duk aunty lubna na tsaye itade AYUSH tsayawatai Tana kallon ikon Allah! Nanfa aunty lubna tadakko wani roba na mangashi kamshi yatashi da aka bude nan tadinga shafa mata agashin line by line yadda mrs nawarma tayarfa mata kitson yan maiduguri Wanda akayishi da allura dama ga gashin AYUSH din tubarkAllah har gadon baya! Sannan aunty lubna tabi duk wani lungu da sako na jikin AYUSH tashafe mata shi da turare dakuma mai medaukar hankalin Wanda yashaka kamshin..atamfa kirar super Sheraton red and black ne design din aunty lubna tadakkosu akan kambasa sunturaru da kamshi Sannan taba AYUSH rike kisa Sannan tadakko wadataccen mayafi red tamika mata tareda mika mata sarkan gold da bangles dinta da takalmi flat red shima..light makeup aunty lubna tama AYUSH Sannan tamike kigyara abinda beyi ba yanxu xakiga lokaci yayi.

Bude drawer dinta tai tafiddo wani box karami da alama documents dintane ciki,wani pic din saurayi taciro Tana kalla daka karshe kuma tayayyaga shi Tana hawaye I entrust you sa'eed Ashe sakayyan daxakaman kenan that's so stupid of you..how can you?!bata karasaba wani kukan yasake fito mata ashe ba sona kakeba I just hide it amma bayan rabuwanmu no calls no messages no any sign that's shows you truly care for me.its all fake Allah yamana sakayya dakai sa'eed bakasan xafin soyayyaba I guess! Wani siririn tsakin takaici tasaki sannan tayaga pic din taxuba a dustbin...tadade Tana tunani har aka Kira sallar magrib sannan Nadia tashigo woww OMG wannan kamshi haka aswr ko company din alharamein albarka osheey kingyaramin daki fa. Itade AYUSH tai shiru kawai Tana kallonta se jan carbinta take bayan ta idar da sallah. Nadia de tagama neman tsokanrta sannan tace kixo inji mommy Tana dakin babaa yan uwan mijinki sunxo xa'akaiki batajira cewar AYUSH ba tafice.

Itade AYUSH karfin hali kawai tai Sannan tamike tanufi dakin mommy xaune take itada baaba ,Tana ganinsu tasa kuka dakyar suka mata fada Sannan baaba yasake mata tashi yai yafice Dan hawaye harya fara gangaromai..dakyar akataru aka bambare AYUSH daga jikin mommy,daga ita har mommy kuka suke..rabuwa da iyaye se ahankali(mothers are huge blessings from Allah,ya Allah make aljannatul firdaus thier final abode)...motoci har 8 sune suka tafi rakiyar AYUSH xuwa gidan mijinta NAUFAAL.dake a unguwar garki Abuja,halak malak abbansa yabashi kyauta yace base yaxauna agidan judicial representatives dake unguwar apo ba.dakuna har 4 parlor 3 se balconies da little garden.gidan yayi Kyau sosai...(inata baxa ido Nadia tace miss xoxo muje kiga gidanmna kyaji dadin fadawa readers dinki.murmushi nai Sannan nabi bayanta tafara xagayawa dani).

Kanashiga gidan da balcony xakafara cin karo tasha kujerun hutawa guda 4 sekashiga ciki kitchen Yana kallonka Komi purple ne.sanann se parlor by the left Komi yellow se Dayan parlor by the right komi black and white da daki aciki Komi coffee,se stairs kana hawa parlor ne komi maroon nd light cream se dakuna guda uku daya Komi white nace wannan na THE CHARMING ne se wani Royal bed purple and black nace wannan na AYUSH ne Sannan wani dakin Komi pink ne se dinning area shikenan.akwai kitchen da store both sama da kasa dukda na sama karamine da alama anyi shine for little purpose haka Dan hada coffee ko warming abinci haka.cike store din yake da foodstuffs to haka itama AYUSH din akaxo da gararta cikin akori kura mota.babu abinda babu aciki duk yadda al'ada tasaba ammata yadda yakamata. Sannan aka watse akabar AYUSH dasu Nadia,Nabeelah da Na'eelah suma basu dadeba naeelah takira NAUFAAL yace gashinan karasowa gidan..dakyar suka yage AYUSH dake faman masu kuka Sannan suka mata sallama suka tafi.

                  •⭐•

Thank you so much for the warm write ups I totally lost it when I checked my whatsapp conversations it was really beyond my wildest expectations..#teamAYUSH,#teamNAUFALOVERS❤

Continua a leggere

Ti piacerà anche

5.1K 234 48
Labarine akan soyayya,cin amana da tausayi,tunasar da iyaye da emmata da ilimintarwa.sakayya Read and find out d main lesson in it
25.6K 1.6K 42
....what action would you take.. if you found out dat someone whom you hold so dearly.is cheater, and he secretly tried to sleep with your loved wif...
14.9K 467 56
labari ne data kafu aka kadara🙇🙇 Kubiyoni ku ji yanda LabariDr. Essha Ahmad zata Kaya da Young Tycoon Namji Mai ji dankashi Aliyu Umar Tycooon 💃...
45.7K 6.2K 42
He turned abruptly to face her, she was already getting on his nerves. "What in the name of Allah is wrong with you?" he asked with a sigh."You don'...