ANYI GUDUN GARA

By AyshaGaladima666

11.8K 802 24

Kirkirarren labarin wata yarinya me matukar tsoron mutane masu saka kaki,mussaman masu rike bindiga,wadda tak... More

ANYI GUDUN GARA PAGE 1
ANYI GUDUN GARA PAGE2
ANYI GUDUN GARA PAGE 3
ANYI GUDUN GARA PAGE 4
ANYI GUDUN GARA PAGE 5
ANYI GUDUN GARA PAGE 6
ANYI GUDUN GARA7&8
ANYI GUDUN GARA 9-10
ANYI GUDUN GARA 11-12
ANYI GUDUN GARA 13-14
ANYI GUDUN GARA 15-16
ANYI GUDUN GARA17-18
ANYI GUDUN GARA 19-20
ANYI GUDUN GARA 21-22
ANYI GUDUN GARA 23-24
ANYI GUDUN GARA 25-26
ANYI GUDUN GARA 27-28
ANYI GUDUN GARA 29-30
ANYI GUDUN GARA 31-32
ANYI GUDUN GARA 33-34
ANYI GUDUN GARA 35-36
ANYI GUDUN GARA 37-38
ANYI GUDUN GARA 39-40
ANYI GUDUN GARA 41-42
ANYI GUDUN GARA 43-44
ANYI GUDUN GARA 45-46
ANYI GUDUN GARA 47-48
ANYI GUDUN GARA 49-50
ANYI GUDUN GARA 51-52
ANYI GUDUN GARA 53-54
ANYI GUDUN GARA 57-58
ANYI GUDUN GARA 59-60
ANYI GUDUN GARA 61-62
ANYI GUDUN GARA 63-64
ANYI GUDUN GARA 65-END

ANYI GUDUN GARA 55-56

317 24 2
By AyshaGaladima666

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)

*PG 55-56*

_______________________________

A hankali ya karasa saukowa, dube dube ya fara Yana neman khaleel,Dan shi daya yasan da dawowar tasa, se can ya hangesa karasawa yayi , khaleel na ganinsa ya fara murmushi,saboda shima yayi kewar Abokin nasa ba kadan ba

Yana karasowa ,rike hannun sa yayi Yana murmushi kafin yace" Angon Amal Naga ka canza sosai Cairo ta karbe ka da yawa "

Shima murmushin ya mayar masa be ce komai ba ,se can yace

"Ina my baby da mamanta"

"Duk suna Nan lafiya Lau "

Shiga motar suka yi domin tafiya gida Nan khaleel ke ce masa
"Yau ummee zaka ma surprise kenan"

Wani killer smile ya masa kafin yace "ai ba ummee daya Zan ma surprise ba"

Jin abunda yace yasa khaleel yayi saurin yin parking gefen hanya ya ce

"Me kake so kace,harda Amal"

Kallonsa yayi "yace kaga malam ban son gulma ka tada motar Nan mu tafi Dan sa'ido kawai"

Dariya kawai khaleel yake yi baji ba gani,se da yaga farouk na kokarin fita motar sannan ta dakata,ya kunna motar suka ci gaba da tafiya

Dariya da tausayin Abokin nasa yake ,saboda kwanakin baya ya hadu da Amal din yaga yadda ta canza sosai kamar ba ita ba,yaga yadda take komai nata cikin aji,da ya tambayi abokinsa ma cewa tayi ya bar Mata maganarsa ma,shiyasa ya fara tausaya masa Dan ya san akwai drama Nan gaba

Share sa farouk yayi be masa maganar dariyar da yake ba har suka isa gida ,Yana tsayawa da motar ya fice ya barsa ko jakarsa be dauka ba,da Ido khaleel ya bisa Yana girgiza Kai ,shi ya dauko jakar ya biyo bayansa

Yana shiga falon ba kowa Dan haka ya wuce sama dakin ummee da sallama yashiga,da sauri ta dago kanta Tana kallonsa da mamaki,kafin tace

"Babana baza ka bar dawowar bazata ba ko,duk kayi tafiya?"

Sosa Kai yayi kafin ya shigo dakin ya zauna kan sofa Nan suka gaisa sosai ,har ta ke cewa ya Kos din  da kaje yi ,da fatan an samu abunda ake so,yace "eh" Alhamdulillah

Tashi yayi yace "ummee Bari naje na watsa ruwa na fito na ci Abinci,duk na Yi kewar abincin kasata,fita yayi

Ta yi murmushi Tana Kara jin soyayyar danta a ranta,

Uwa kenan🥰🥰


_____________________________

A yau ne jajibirin suna ,Amal suka je ita da husnah karbo dinkinta da ta bayar ,sun karbo har sun fito suka tsaya jiran adaidaita ,wata  hadaddiyar mota tayi parking a gabansu, sauke glass din motar Akayi wani matashin saurayi ne a ciki ,kallo daya zaka masa ka gano irin yaran masu kudinnan ne da suke yadda ransu ke so.  "Hy beb" yace musu

dauke Kai sukayi suka matsa daga wurin motar

Adaidaita suka tare suka shige ,me motar Ashe Yana Nan biye dasu har suka iso gidan Anty Ramla ,se da yaga shigarsu sannan ya juya Yana cewa"ai na samu matar aure ,dole na dawo mu daidai ta gobe baby🤣

Tunda Farouk yayi wanka ya fito yake Raba Ido Yana son yaga ta inda Amal zata bullo be ganta ba har ya ci Abinci ,Kuma kunyar tambayar ummee yake ji daki ya shiga ya Kira Al'amin a waya

Da mamaki Al'amin yaga Kiran yayan nasa da number 9ja
Dagawa yayi cikin farin ciki yace"Yaya ka dawo ko mafarki nake?"

Dariya yayi yace "kazo na mareka se ka farka"
Dariya yayi suka gaisa nan yace "Ina yarinyar Nan take?"

Murmushi Al'amin yayi gano wadda yake nufi,Nan yake fada masa ai Bata Nan Tana kano taje sunan Aunty Ramla

Kashewa yayi tsabar bacin Rai be jira Al'amin din ya gama fadar abunda ze fada ba

Wani irin bacin Rai yake ji Yana taso masa,Yana mamakin me yarinyar Nan ke daukar kanta da har zata yi tafiya Bata Kira shi ta fada masa ba,ji yake badan yammah tayi ba da ba abunda ze hanashi zuwa kano ya dawo da ita

Tashi yayi ma ya fice daga gidan

A gidan biki Kam Koda suka dawo Amal tsaki kawai take ,saboda mutumin da ya musu magana ba karamin haushinsa taji ba,husna Kam dariya kawai take

Koda Aunty Ramla ta tambayi me ya faru husna ta fada Mata ,kallon Amal tayi tace "ai dole kowa ma ya tare ku ki kalli mayafin da kika yafa a wuya kamar ba matar aure ba fissabillilahi ,ai da Naga sanda Zaki fita da shi bazan barki ba ma wallahi"

Turo Baki Amal tayi gaba tace"habah aunty doguwar Riga ce fa idan bansa gyalenta ba me kike so nasa, ko hijabi Zan dauko na zuba kamar wata matar liman"

"Ai matar aure ce ke idan kin manta na tuna Miki Ni Allah yasa sojan Nan ya dawo ma ko ya saita ki"

Tashi tayi tsam ta bar wurin ta shige daki,ba ta San me yasa ba yanzu bata so ana Mata maganar Yaya farouk,Dan gani take har yanzu bata da wani muhimmanci a wajansa ,se wani cusa ta ake a wurinsa

Se dare farouk ya dawo gidan ko da ya shigo falo ya isko Al'amin da ummee ,neman wuri yayi shima ya zauna

Ummee ce ta katse shirun da cewa"babana baka tambayi 'yata ba "

Al'amin har ya bude Baki ze yi  magana ya masa wani mugun kallo dole tasa yayi shiru,tashi ma yayi ya bar falon

Juyowa yayi Yana kallon ummee da ta tsura masa Ido"munyi waya ummee tana kano ai, Nima gobe Insha'Allah zanje "

Murmushi tayi tace"ai kuwa da ka kyauta"

'yar fira suka taba kafin ya Mata se da safe ya nufi dakinsa

Tun da wuri suka tashi,suka gyara gidan da kyau ,dama Aunty Ramla abincin biki duk bayarwa tayi aka Mata kala biyu masu kyau,danbun shinka fa da white rice and stew se coslow da suka hada,bayan me jego tayi wanka ,me kwalliya tazo ta Mata kwalliyya , Masha'Allah ta fito Shar Abunta,Suma su Amal duk an masu ,kar kuso kuga yadda Amal Tai wani fitinannen kyau ,ita kanta me kwalliyar se da ta yaba  kyawun da tayi

Farouk misalin 10:00am Yana bayan motar sa ya hakimce wani soja na jansa ,yayi matukar kyau cikin wata shadda milk colour,ya saka hularsa zannah bukar ,ga agogon Rolex ya saka ,se tashin kamshi yake kamar Ranar daurin aurensa ,kano suka nufa dama ya Kira Yaya Sadiq ya fada masa Yana Nan tafe Nan ya fada masa unguwar da suke

Misalin karfe ukku na Rana Aka Aiko ana Kiran Amal a waje ,mamakin wake kiranta ta shiga yi can dai ta tashi tace Bari taje kila Yaya Sadiq ne wani figigin mayafi ta yafa ta fita Koda ta fita Bata ga kowa ba har zata juya taji an Mata sallama Tana juyowa taga mutumin jiya ne,se dai yau cikin manyan Kaya yake

Shiru tayi bayan sun gaisa nan yake fada Mata sonta yake
Dariya tayi tace"yi hakuri Ni matar aure ce"

Dai dai lokacin da motar su Farouk ta shigo unguwar ,a hankali driver ke tukin ya na shigowa
Wata ya hango wata kamar Amal
Se yace "oga waccan kamar madam Amal ko gidan ne can"

Aje magazine da yake dibawa yayi jin abunda driver yace Yana dago kansa ko idonsa suka fada kanta ,Tana tsaye tare da wani se washe Baki take ,ga wani mayafi da ta saka Wanda dashi da babu duk daya.

Wani tukuki yaji zuciyar sa nayi jikinsa har rawa yake ya balle murfin motar ........................✍️

*Ayaha galadima ce*

Vote
Comment
Share

Continue Reading

You'll Also Like

604K 20.3K 168
The young lady from the Xue family was talented and beautiful, and married the dream husband at the age of 16. They had a loving and harmonious relat...
Alina By ihidethisapp

General Fiction

1.5M 39.2K 80
The Lombardi family is the most notorious group in the crime world. They rule both the American and Italian mafias and have many others bowing at the...
282K 20.6K 25
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...
480K 17K 194
Won Yoo-ha, a trainee unfairly deprived of the opportunity to appear on a survival program scheduled to hit the jackpot, became a failure of an idol...