ANYI GUDUN GARA

By AyshaGaladima666

11.8K 802 24

Kirkirarren labarin wata yarinya me matukar tsoron mutane masu saka kaki,mussaman masu rike bindiga,wadda tak... More

ANYI GUDUN GARA PAGE 1
ANYI GUDUN GARA PAGE2
ANYI GUDUN GARA PAGE 3
ANYI GUDUN GARA PAGE 4
ANYI GUDUN GARA PAGE 5
ANYI GUDUN GARA PAGE 6
ANYI GUDUN GARA7&8
ANYI GUDUN GARA 9-10
ANYI GUDUN GARA 11-12
ANYI GUDUN GARA 13-14
ANYI GUDUN GARA 15-16
ANYI GUDUN GARA17-18
ANYI GUDUN GARA 19-20
ANYI GUDUN GARA 21-22
ANYI GUDUN GARA 23-24
ANYI GUDUN GARA 25-26
ANYI GUDUN GARA 27-28
ANYI GUDUN GARA 29-30
ANYI GUDUN GARA 31-32
ANYI GUDUN GARA 33-34
ANYI GUDUN GARA 35-36
ANYI GUDUN GARA 37-38
ANYI GUDUN GARA 41-42
ANYI GUDUN GARA 43-44
ANYI GUDUN GARA 45-46
ANYI GUDUN GARA 47-48
ANYI GUDUN GARA 49-50
ANYI GUDUN GARA 51-52
ANYI GUDUN GARA 53-54
ANYI GUDUN GARA 55-56
ANYI GUDUN GARA 57-58
ANYI GUDUN GARA 59-60
ANYI GUDUN GARA 61-62
ANYI GUDUN GARA 63-64
ANYI GUDUN GARA 65-END

ANYI GUDUN GARA 39-40

265 19 2
By AyshaGaladima666

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)

*PG39-40*

____________________________

Fita kawai yayi a gidan be bi ta kanta ba se dai ko da ya shiga mota fuskar ta ce ta dawo masa a Rai yana tunanin kamar ya taba ganinta tsaki dai yayi yaja motar ya fice a gidan

Tana farfadowa da kuka ta farfado se dai bata ga kowa a falon ba ,sannan gata jike da ruwa da sauri ta Mike ta kwasa da gudu zuwa dakinta har da su saka key

Nace kuwa bayan hari🤣

Ta dade zaune Tana kuka Tana tunanin wanna mutumin me kayan sojoji da ta gani kakkarfa da shi ba dai shine mijin nata ba?
ai ko in shine mutuwa zatayi kawai , Anya ma su Abbah sunsan soja suka  aura Mata ta, dade Tana kukanta se da ta gaji Dan kanta ta Dena , cikinta ne ya fara kukan yunwa ba arziki ta bude dakin ta fita da sanda ta nufi dinning din ,kulolin abincin ta fitar a kwando ta Dora akan table din ganin ba ko spoon yasa ta shiga neman kitchen, shiga tayi se kuma tayi tsaye Tana kallon tsaruwar kitchen din , takawa tayi ta shiga ciki cup da spoon da Kuma plate daya ta dauka ta fito dinning table ta nufa ta zuba kunun gyadar data gani ,se ta zuba dankali da dan farfesu   data zuba a gefe da sauri ta suri kayan ta shiga dakin ta ta rufo kofa

_____________________________

Amarya Ramla Ana kano ana ta cin Amarci tun Tana jin kunyar Abubuwan har ta fara sakin jikin nata,Dan yaya sadeeq be je Mata da Wasa ba,kun San Abu ga sabon shiga Dan har ciwo na kwana biyu se da tayi kafin ta fara gogewa a yanzu ,se dai Tana cikin kewar 'yar uwarta kamar me

Yau ma Tana zaune a falonta cikin wata Dubai gown red colour rigar ta matukar yi Mata kyau Masha'Allah se dai ta rafka uban tagumi Tana tunani ,hannunta taji an cire daga fuskarta , firgigit ta dawo daga tunanin da take ,yaya Sadiq ya daga girarsa sama yana cewa"Tunanin me kike haka my happiness ,tun dazu na ke ta sallama Baki Amsa ba"

A hankali tace "Ina kewar Amal ne "

Shiru yayi yace "Ni Baki yi kewata ba se ta Amal ?"

Rufe fuska tayi tace"A'a
Wayarshi ya Ciro yace bari na Kira Abokin mijinta Dan Na karbi number sa a lokacin
Ai ko se ta washe baki kamar gonar auduga, yana ko Kira wayar ta shiga daidai lokacin khaleel na office din farouk, sabuwar number ya gani kamar baze dauka ba Kuma ya dauka
Sallama Sadiq ya masa daga dayan bangaren su ka gaisa nan yama sa bayanin koshi waye nan suka sake gaisawa, nan yake ce masa ,
"in akwai number da za'a iya samun Amal da ita ya basa , sister din ta ce duk ta damu Tana son magana da ita ,
shiru khaleel yayi na 'yan sakanni sannan yace "ba damuwa Zan tura ma number yanzu, Ina gaida Amarya"
Sadiq ya Amsa masa da zata ji sukayi sallama

Tunda khaleel ya fara waya hankalin farouk na kansa ,se dai be tambayesa da wa yake wayar ba
Khaleel number farouk ya tura ma yaya sadiq ba bata lokaci wayar farouk ta fara ringing be dauka se da aka sake Kira ya dauka
Gaisawa sukayi a mutunce nan yake masa bayanin kansa da Kuma dalilin Kiran ,ce masa yayi baya gida yanzu se In ya koma sukayi sallama ,kallon tuhuma kawai yake bin khaleel da shi, shi Kuma yaki kallonsa ma se can kome ya tuna yace

"Malam wa ya baka damar rarraba number ta ga mutane?"

"Su waye mutane surukan naka?"
Inji khaleel yana kallon sa

Cewa yayi" Naga Alamar ka sansu saboda shishigi irin naka"

Dariya yayi yace na dai ji

"Yawwa dama Ina so na tambayeka wannan yarinyar ta na da wani ciwo ne ?"

Juyowa khaleel yayi yana fuskantarsa da kyau yace "wace yarinya?"

Shiru yayi be bashi Amsa ba
Se can khaleel din yace "ohh Amal"

"Me ya faru ne?"
Shiru yayi be bashi Amsa ba se can da yaga dama yace
"Ina fitowa dazu falo ta kwalla min Kara kamar zata fasan dodon kunne ,har da Suma Nike tunanin tayi"

Shiru khaleel yayi yana mamakin abunda farouk yace 
Tunani ya fara se ya tuno ranar da ya fara rage musu hanya irin Abubuwan da Amal din tayi a motar sa da Kuma bayanin da Ramla ta masa akan abunda take tsoro
Kallon farouk yayi da fuskar tausayi yace "Allah sarki Amal har ta ban tausayi "
Wani kallo farouk din ke binsa da shi ,be San me yasa ba Amma yaji haushin furucin da khaleel din yayi

Se yace "in ze yiyu kabar shiga da uniform gida ko kabar bari Tana ganinka in ka saka please saboda yarinyar Tana matukar tsoron masu uniform ko ba Kai ba duk taga wani da kaki Tana iya shiga halin da kaga ta shiga dazu"

"Tana tsoron kaki kace fa ,to ita wane tsautsayin ne yasa ta yarda da aure na?"
Cewar farouk

"Ai yadda kake tunanin an matsa ma ita ma kusan hakane a wurin ta , biyyaya kawai tama iyayenta ta aure ka ,Dan haka naso ka hakura ka rungumi aurenka"
Cewar khaleel

Wani haushi ne ma ya taso ma farouk jin Wai ta tsani me kaki sannan ma dole a ka Mata. Ta aure sa kamar wani Wanda yayi kwantai
Ganin yadda yanayin farouk din ya canza nan take yasa khaleel yace "yadai?"

Tashi yayi yana tattara kayan gabanshi yana zubawa a wata jaka se da ya gama ya kalli khaleel yace
"Zan tafi gida ne "

Sanin halinsa yasa khaleel da sauri ya Sha gabansa yace"friend dan Allah kabi yarinyar nan a hankali kar kayi abunda ze sa ka dawo kana Dana sani "

"Malam ya ishe ka haka fa ,ai ba'abun da ze sa Ni da na sani ita Kuma zata yaba ma aya zakinta ,zata San tayi auren soja, badai kaki ta tsana ba to dole ta dawo Tana son kaki "

Fuuuuu ya rabe shi ya fita.........................✍️

*Aysha galadima ce*

Comment
Share

Continue Reading

You'll Also Like

509K 32.6K 41
Let's see how different personalities mends with each other to form a beautifull bond together. Where the Eldest is calm and cold, Second is aggress...
Gentle touch By K

General Fiction

66.2K 1.4K 33
It had been mere months after her eighteen birthday, when she was pulled from the safe haven of her life and forced into the fantasy the women had cr...
60.6K 3K 52
The Rajputs well known as the most powerful and devil's for the people who tries to messed up with them people got goosebumps just by listening to th...
333K 10K 81
(Fixed/Fan-TL) Top idol group Stardust, whose members disappear like dust. The group that used to have seven members ends with four members... "Is...