ANYI GUDUN GARA

By AyshaGaladima666

11.8K 802 24

Kirkirarren labarin wata yarinya me matukar tsoron mutane masu saka kaki,mussaman masu rike bindiga,wadda tak... More

ANYI GUDUN GARA PAGE 1
ANYI GUDUN GARA PAGE2
ANYI GUDUN GARA PAGE 3
ANYI GUDUN GARA PAGE 4
ANYI GUDUN GARA PAGE 5
ANYI GUDUN GARA PAGE 6
ANYI GUDUN GARA7&8
ANYI GUDUN GARA 9-10
ANYI GUDUN GARA 11-12
ANYI GUDUN GARA 13-14
ANYI GUDUN GARA 15-16
ANYI GUDUN GARA17-18
ANYI GUDUN GARA 19-20
ANYI GUDUN GARA 21-22
ANYI GUDUN GARA 23-24
ANYI GUDUN GARA 25-26
ANYI GUDUN GARA 27-28
ANYI GUDUN GARA 29-30
ANYI GUDUN GARA 33-34
ANYI GUDUN GARA 35-36
ANYI GUDUN GARA 37-38
ANYI GUDUN GARA 39-40
ANYI GUDUN GARA 41-42
ANYI GUDUN GARA 43-44
ANYI GUDUN GARA 45-46
ANYI GUDUN GARA 47-48
ANYI GUDUN GARA 49-50
ANYI GUDUN GARA 51-52
ANYI GUDUN GARA 53-54
ANYI GUDUN GARA 55-56
ANYI GUDUN GARA 57-58
ANYI GUDUN GARA 59-60
ANYI GUDUN GARA 61-62
ANYI GUDUN GARA 63-64
ANYI GUDUN GARA 65-END

ANYI GUDUN GARA 31-32

259 16 0
By AyshaGaladima666

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️


         *NA*
    *AISHA GALADIMA*


*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*


_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(08064933819)

*PG 31-32*


_______________________________

Kamar ance Ramla ta dago kanta ,suka hada Ido da khaleel

Ci gaba tayi da kallonsa Tana mamakin ta in da ya fito
Shi dai mai da hankalinsa yayi wurin tuki yana tunanin to ya akai haka ta faru , sannan Wai ma wacece matar Abokin nasa a cikinsu

Sake dago Kai tayi suka sake hada Ido se tace mai"Ina wuni"
Yace "lafiya lau ,ya hidima"
Tace "Alhamdulillah"

Ummah me kudi ce ta kalli Ramla tace"kin San shi dama shine tun dazu Baki gaida sa ba, ko Abokin Sadiq ne?
Ramla tace "A'a ummah na sanshi a kd ne"
Ummah me kudi tace "oho"
Nan shima khaleel ya gaida ummah me kudi
Da yake ummah me kudi wayayyiyar mace ce tako saki jikinta suka gaisa
Nan khaleel ke cewa ai shi Abokin farouk ne dayan angon
Nan ummah me kudi tace "Allah sarki mijin Amal kenan " Tana juyowa Tana kallon Amal din data sunkuyar da kanta ,kamar ma bata a motar

Take khaleel ya fuskanci cewa Amal ai ita ce matar Abokin nasa ,aiko ba karamin dadi yaji ba da hakan ta kasance ,dariya yake so yayi Ammah ya danne saboda ummah me kudi , har dai in ya tuna cika bakin da farouk keyi na cewar yar 20years ta masa yarinya , ganin wannan ma da ko 20 din bata Kai ba

To  a haka dai suka isa kano cikin dare ,direct Ramla gidan mijinta a ka wuce da ita, ummah me kudi kuma gidansu Sadiq aka wuce da ita ,Amal dai gidan amarya zata kwana kasancewar akwai wasu bakin da zasu kwana a can
Shima khaleel se dai suka nemi hotel din da zasu kwana gobe su wuce Kd

Gidan Amarya Ramla Masha'Allah su Abbah sunyi kokari sosai an kawata gidan yadda yadda ya kamata kasancewar ita dai akama komai ba da Amal ba
Da ka shigo falon gidan babba ne madaidai ci an kawata shi da kujeri da labulayya har zuwa fentin falon lemongreen and orange ne se dinning area daga hannun dama se kuma dakin Amarya  Ramla,da kuma master room dake can kurya akwai kuma dakin Baki , kitchen na can kusa da dinning area

Dakunan gidan se sambarka komai yaji gishiri😀👌🏻

Ramla dakinta suka shiga ita da Amal sauran mutane biyar din da suke tare suka shiga dakin Baki
Suna shiga Amal se santin gidan na yayarta take , ita dai Ramla shiru tayi Tana tausayin kanwar ta ta har dai da taga khaleel ta fara tunanin tabbas farouk shine mijin Amal gashi soja abun da take tsoro
Lallai wannan shine *ANYI GUDUN GARA*

Tana tunanin yadda kanwar ta ta zata iya Rayuwa da farouk gashi yadda ta lura mutum ne me saurin fushi tunda baza ta manta Marin da ya taba ma Amal din ba

Amal ce ta katse Mata tunanin da cewa "aunty ana Kiran wayarki "

Karbar wayar tayi taga yaya Sadiq ne , daga tayi taji yace"fito gani nan falo" se da taji gabanta ya fadi

Juyowa tayi tace Amal ta rakata se taga har ta tayar da sallah ,dole bata da wani zabi ta dauki mayafinta ta fita
Ko da ta shigo falon yana zaune akan kujera ,tunda ta fito yake binta da kallo ,kujerar nesa da shi ta zauna da kyar tace"yaya Ina wuni "

Tashi yayi ya dawo kusa da ita , se ko jikinta ya fara rawa ,shi dariya ma ta bashi se dai ya kanne

Kallonta yayi yace"ya gajiyar hanya beauty"

Shiru tayi Tana Wasa da yatsun hannunta se kallon yatsun nata yake lallenta ya matukar burge sa ba zato taji yayi kissing hannun da sauri ta Mike tsaye Tana zaro ido. Kamar wadda tayi karya

Murmushi yayi kawai ya kula ba karamin tsoron sa take ji ba
Ledar hannunsa ya Mika Mata
Ta karba yace "ki tabbatar kin ci fa kafin ki kwanta"
Se da ya sunbaci goshinta sannan ya nufi dakinsa

Da sauri Ramla ta nufi dakinta Amal ta isko har ta kwanta ta tadata  tana tashi ledar ta karba dama abincin da khaleel ya siya musu bata wani ci ba

Budewa tayi ,kaza ce a ciki taji Hadi

Irin ta yahuza suya😀

Take ko ta fara cin Naman
Ramla tashi tayi ta shiga ban daki domin ta watsa ruwa

Amal ko ba sauki take cin kazar nan

Nace a ci sannu Amaryar farouk..............✍️

*Aysha galadima ce*

Comment
Share

Continue Reading

You'll Also Like

58.9K 1.4K 40
standalone ~ mafia siblings series "You can't make me stay here! I will get an emancipation." I yell. Flashbacks of the gun in my hand, the almost-de...
141K 6.8K 28
Hooked onto drugs, no family, no guidance or sanity until she met HIM. Cover Creds: @Triceynexttdoor โค๏ธ -BLICKY.
39.5K 3.6K 10
Wanna visit rajasthan than read this special book about my love Rajasthan ๐Ÿ’—
269K 17K 47
The feeling of being abandoned by one's own family was not unknown to Aadhira. She hates her family for abandoning her when she was only a newborn, l...