ANYI GUDUN GARA

By AyshaGaladima666

11.8K 802 24

Kirkirarren labarin wata yarinya me matukar tsoron mutane masu saka kaki,mussaman masu rike bindiga,wadda tak... More

ANYI GUDUN GARA PAGE 1
ANYI GUDUN GARA PAGE2
ANYI GUDUN GARA PAGE 3
ANYI GUDUN GARA PAGE 4
ANYI GUDUN GARA PAGE 5
ANYI GUDUN GARA PAGE 6
ANYI GUDUN GARA7&8
ANYI GUDUN GARA 9-10
ANYI GUDUN GARA 11-12
ANYI GUDUN GARA 13-14
ANYI GUDUN GARA17-18
ANYI GUDUN GARA 19-20
ANYI GUDUN GARA 21-22
ANYI GUDUN GARA 23-24
ANYI GUDUN GARA 25-26
ANYI GUDUN GARA 27-28
ANYI GUDUN GARA 29-30
ANYI GUDUN GARA 31-32
ANYI GUDUN GARA 33-34
ANYI GUDUN GARA 35-36
ANYI GUDUN GARA 37-38
ANYI GUDUN GARA 39-40
ANYI GUDUN GARA 41-42
ANYI GUDUN GARA 43-44
ANYI GUDUN GARA 45-46
ANYI GUDUN GARA 47-48
ANYI GUDUN GARA 49-50
ANYI GUDUN GARA 51-52
ANYI GUDUN GARA 53-54
ANYI GUDUN GARA 55-56
ANYI GUDUN GARA 57-58
ANYI GUDUN GARA 59-60
ANYI GUDUN GARA 61-62
ANYI GUDUN GARA 63-64
ANYI GUDUN GARA 65-END

ANYI GUDUN GARA 15-16

259 18 0
By AyshaGaladima666

🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️
*ANYI GUDUN GARA*
🌸🌸🌸💞💞💞🙆‍♀️

         *NA*
    *AISHA GALADIMA*

*DEDICATED TO*

*HASSAN ATK*

_Muna siyar da Arabian gowns na kasashe daban daban,na yara Dana manya,laces,Atamfa,shoes,bags and _kitchen utensils ga masu bukata_ zaku iya tuntubar wannan number_
(080649333819)

_Wannan shafin naki ne kaco kam, comment dinki yana sani Nishadi_
*Raleeyer*

*PG 15-16*

_____________________________

Ramla da sauri ta kalleta tace" Amal lafiya?"

Se nuna gaban motar take Tana boye kanta cikin jikin Ramala

Khaleel shima da sauri ya juyo yana kallon su yace
"Lafiya kuwa?"

Ramla har ta bude Baki zata bashi Amsa Idanunta suka sauka kan farouk da ke gaban mota sanye da kayan sojoji

Tuni ta mai da maganar da ta tashi yi , tace ma khaleel ba komai

Ta dukar da Kai ta tace"ki natsu ba abunda ze Miki kinga shi ko juyowa be yi ba , kiyi shiru mu samu su sauke mu gida"

Daga Mata Kai tayi daga cikin hijab din Ramla da ta shige

Duk abunda ke faruwa farouk ko juyowa be yi ba, yi yayi tamkar be San hidimar da suke ba

Kuma duk maganar da Ramla tama Amal yana ji, saboda ji ne da shi kamar me kunnen maciji se ma lumshe idanun sa yayi

Suna tafe khaleel na tambayar Ramla inda ze Kai su

A hankali take take nuna masa hanya har suka iso kofar gidan na su yayi parking, bude kofar Ramla tayi tace " malama daga ni mun iso ki fita"

Se da ta dago kanta a hankali ta kalli Ramla ,sannan ta kalli kofar data bude ,ai ko da gudu ta fita ta shiga gida

Khaleel mi ze yi inba dariya ba ,ya juyo yana kallon Ramla da ta fito a motar yace
"Wai waccan kanwar taki lafiyar ta kalau kuwa?"

Se da ta kulle kofar motar ta kalle sa ta danyi murmushi ta nuna ma sa motar da hannunta tace"mutumen ciki ta ke tsoro, mun gode fa "

Rufe bakin sa yayi yace "tasan shi ya mareta ne?"

Tace"A'a Tana tsoron masu saka uniform da masu rike bindiga "

Yace "ikon Allah daga ni har shi kuma duk sojoji ne fa, an dai yi sa'a na cire uniform ni"

Rufe Baki Ramla tayi Tana murmushi sannan tace "mun gode "
Suka yi sallama ta shige gida

Shima mota ya shiga , Koda  ya shiga ya tarar da mutumen ya cika yayi fam se huci yake

Tada motar yayi be ce masa komai ba

"Wai Kai wane irin Dan rainin wayau ne , ka tsaya kana ta wata dariya da kananan  yara Dan na San ma kila zaka haife su ko kunya baka ji, se na fada ma Asmah kana nan kana neman wasu Dan na tabbata wadannan baka hada komai da su ba karya kawai ka min"
Cewar farouk

Khaleel yace "miye abun jin kunya anan ,da kake cewa na haife su ,ke nan Kai kakansu ne kuma kaje ka fada Mata din nasan zata fahimce ni daga na taimaki yara zaka dinga min fada , kodai akwai wadda tama cikinsu"

Wani uban tsaki farouk yaja  be sake tanka ma khaleel da ke tsokanar sa ba

_____________________________

Koda Ramla ta shiga gida ta tarar har Amal ta cire kayan jikinta

Ummah ce ta shigo dakin tace "yanzu cikin ruwannan kuka fito me makon ku bari a gama

Da sauri Ramla tace "sanda muka fito umma ba'a fara ruwan ba"

Dan tasan tsab Amal zata iya fada Mata a mota aka kawo su

Ummah tace "to yayi  kuyi sauri ku canza kayan kar kuyi mura,

Ramla tace" to"

A kwana a tashi ba wuya  wurin Allah har su Ramla sun gama jarabawar waec da neco yayin da Amal ta yi  j s l c

Bayan kammala
Jarabawar su da sati biyu Abba ya siya ma Ramla waya kirar Tecno L5

Ranar ba karamar murna suka Sha ba ita da Amal

Kwana biyu tsakani da yamma Tana kwance a dakin su se ga Kira ya shigo wayar ta , kallon wayar ta yi ta ga number ce ba suna bata dauka ba har wayar ta tsinke , aka sake wani Kiran daga wa tayi , tayi shiru

Daga can bangaren Aka yi sallama ta Amsa

An dau sakanni ba'ayi magana ba se tace"wake magana?"

Har ta cire ran baza'ayi mayana ba

Se aka ce " aljanine "

Zaro ido tayi ta saki wayar..................✍️

*Aysha galadima ce*

Comment
Share

Continue Reading

You'll Also Like

Cecilia By Anastasia

General Fiction

27.2K 639 26
Cecilia's father, a well-known and successful lawyer, was tired of her problems. Tired of the issues she had been causing for the family and it's nam...
72.8K 4.1K 53
M/n, a victim of bullying who took his own life, got a chance to be reborn as Vasilyev Konstantin, a Russian political figure in the world of lookism...
896K 20.3K 43
Enisha , a 3 year old who never saw the light of the sun ; never felt loved and never understood the meaning of family just because of someone's hat...
327K 9.8K 79
(Fixed/Fan-TL) Top idol group Stardust, whose members disappear like dust. The group that used to have seven members ends with four members... "Is...