Baki ɗaya ƙafafuwansa kasa ɗaukar shi suka yi. zubewa nan ya yi yana wani irin nishi mai ƙarfi.
Shi kaɗai ya san abunda yake ji.
Ganin yake yi a duniya bai taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba.
Ya san ba ma yanda za ayi ya iya jewa Iyayensu da wannan maganar. kuma ya tabbatar da idan bai aure Afnan ba zai iya rasa rayuwarsa a yanda yake jin sonta cikin zuciyarsa.
Daƙyar ya samu ya lallaɓa ya tashi yana bin bango ya bi ta ƙofar baya. Allah ne kaɗai ya kai sa gida lafiya a wannan lokacin.
Yana shiga ɗakin mahaifiyarsa ya zube k'asa yana rusar kuka tamkar wata macce.
Ganin halin da yake ciki ne ya sanya Hajiya Zuwaira ta yo kansa da sauri tana tambayarsa.
"Me ya sameka haka Yaseer?" Ta tambaya cikin ruɗani.
"Mamie mutuwa zan yi."
"Me yake faruwa ne wai? Me kake faɗa ne? an bada yarinyar ga wani ne ko me? Ka yi min baya ni mana dan Allah"
"She left me Mamie. She choose some one over me. Mamie she choose him, mutumin da na tsana fiye da kowa Mamie shi ta zaɓa ta bar ni"
"Wace irin magana kake yi haka Yaseer wa ye ta zaɓa ni ban gane ba ka yi min yanda zan fahimta"
"Mamie Afnan choose Yazeed over me."
Wata irin uwar ashar Mamie ta saki. "Yazeed fah ka ce? Chab uban nan ai wallahi ba zai yiyu ba. Nabeelah fah? Ina it can't be ba zan taɓa bari Yazeed ya aure wata ba idan ba Nabeela ba. ta ya zai rushe min plan ɗina ne? Sam ba zai yiyu ba wallahi. Shin dama yana son yarinyar ne ko kuma aikin uwarsa ne?"
"Nima ban sani ba Mamie. Banga wata alama da ta nuna yana son yarinyar ba shiyasa ma ni ban damu da zamanta gidansu ba"
Kwashe yanda suka yi da Afnan ya yi ya faɗawa Mamie, saboda ba abinda bata sani ba har na fyaɗen da ya yi mata.
Sosai hankalinta ya tashi. Saboda tana ganin tonuwar asirinta ƙarara idan har Yasser ya faɗi shi ya yi mata fyaɗe. Cikin tashin hankali ta ce.
""Kan uban nan lallai wannan yarinyar ta zo da abunda ba zai taɓa yiyuwa ba. Ta yaya zaka je ka gayawa Alhaji kai ka yi mata fyaɗe kuma da sunan gudan jininsa? kai gaskiya wanna ba zai taɓa yiyuwa ba"
"Mamie ba zan iya bari ta aure wanina ba must especially ma Yazeed. Gaskiya zan yi duk abunda take so dan in aureta"
Da tsawa Mamie ta katse sa. "Ka kuwa san abunda kake faɗa?"
"Na San abunda nake faɗa mana. Sannan ko ma miye ke kika ja min da tun farkon da naso na faɗa gaskiya kin bari ni na faɗa da duk haka bata faru dani ba"
Ganin yana so ya ɗahe mata yasa ta ce."Ka yi haƙuri Yaseer. Duk wannan abun ba zai faru ba. Na yi maka alƙawarin idan dai har sunana Zuwaira to sai ka aure wannan yarinyar. Sha kuruminka bari kawai Alhaji ya dawo gidan nan."
Wani sanyi ya ji a zuciyarsa jin kalaman mahaifiyarsa. Tabbas ya san dole ta yi wani abu a kai ko dan yanda ta sha burin ganin Yazeed ya aure Nabeelah. Ya tabbatar da zata iya aikata komai don ta hana auren Yazeed da Afnan. A yanda ya san mahaifiyarsa ya san duk abunda ta gayawa Daddy bai isa ya tsallakesa ba. Da wannan ya ji ya samu nutsuwa mai yawa a zuciyarsa.
Kamar yanda Ammie ta yi alkawari Hafsa na dawowa suka je suka kai Afnan gida. Mommy ta yi murna sosai ta kuma yi ta yiwa Ammie godiya da karamcin da ta yi masu.
Ita kuwa Afnan ganinta cikin gidansu ba ƙaramin daɗi ta ji ba, nan take ma sai ta ji tana neman ta manta damuwarta.
Daƙyar Hajiya Zuwaira taga safiya ta waye mata saboda jiya kwana ta yi tana kiran wayar bokanta bata samesa ba. Yau tun da sassafe ta bar gidan ta yi ƙauyen da yake.
Misalin karfe goma na safe ta isa ƙauyen. Kwashe duk abinda ke tafe da ita ta yi ta gayama Nakan tudu.
Sai da ya ƙare yan surkullensa sannan ya dube Mamie ya yi dariya.
"Kika ce cikin satin nan ne ɗaurin auren ko?"
"Eh boka yau ma su Alhaji zasu je su tsaida magana da iyayen yarinyar kamar yanda na gayama.
Wani turare ya ɗauko cikin wata kwalba ya bata. "wannan turaren da kike gani muddun kika sanya shi, Alhaji ya shaƙi ƙamshinsa to da zaran kin ce a fasa ɗaura auren da Yazeed a ɗaura da yaseer ba za a ɗaura da Yazeed ɗin ba sai da Yaseer ko da kuwa ranar ɗaurin auren ne"
Murmushin jin daɗi Mamie ta yi. "Toh su iyayen yarinyar fa ya za ayi su amince?"
Wata dariya ya yi. "Ki bari in mutu mana kafin ki binneni. Ai turaren da na baki na karkatar da tunani ne. Har Alhaji za ki sanyawa.
Shi ma da zaran mutane suka shaƙe turaren daga jikinsa shikenan duk abunda kika ce masa shi zai faɗa kuma ta zaunu ba wanda zai yi gardama ko jayayya kan hakan"
Mamie ta ji daɗi sosai. "Toh ya maganar auren shi Yazeed ɗin da Nabeela? ka san ka ce kar mu sanya gaugawa a ciki."
"Kar ki damu. Matukar bai aure kowa ba toh ba shida wata mata sai Nabeelar".
Sosai Mamie ta ji daɗi ta yi masa ɓarin kuɗi sosai kafin ta wuce.
Sai bayan azahar ta isa gida tana ta addu'ar Allah yasa Alhaji bai riga ya tafi neman auren ba tayi masa bugu guda tun yanzu a wuce wurin. Sai dai addu'arta ba ta ci ba koda ta isa aka ce mata ya fita. Bata wani damuwa ba saboda ta san tanada sauran lokaci kafin ɗaurin auren.
Misalin ƙarfe tara na dare. Mamie na zaune parlour ta cika ta yi fam saboda ganin har zuwa lokacin Daddy bai dawo ba. Gashi kuma ta yi ta kiran wayarsa bai ɗauka ba.
Ga Yaseer sai faman kiranta yake yi, saboda ya ƙagu yaji an ce Afnan zata zama mallakinsa.
Sai guraren karfe goma Daddy ya shigo gidan. Tun da ya doso falon yake jin gabansa na faɗuwa.
Da sallama ya shiga falon. Kallo ɗaya ya yi ma Mamie bai sake marmarin sakewa ba.
Murmushi. yaƙe ya yi tare da cewa. "Uwargida ran gida. A yi haƙuri fa na san na yi laifi." Ya faɗa yana tunanin cewa labarin abunda ya faru ya zo kunnenta.
Wani kallon uku saura kwata ta yi masa. "Ai dama nasan haka zaka ce. yanzu Alhaji saboda Allah tun yaushe naketa daman jiranka. Gashi har kwalliyar da na yi maka tana nema ta goge." Ta fad'a cikin kissa da jan hankalin mai saurarenta.
Ajiyar zuciya Daddy ya yi dan ganin ba abinda yake zargi ne ba.
"Ayya a yi haƙuri. ke san ai ke ta daban ce ko ba ki da kwalliya kyau kike yi" ya fad'a yana sakar mata murmushi.
Dawowa ta yi kan hannun kujerar da yake zaune ta zauna tana shafa fuskar sa da hannayenta da ba a barsu a baya ba wurin banka masu turaren boka ba.
Marairaicewa ta yi ta ce.
"Yanzu Dan Allah Alhaji abunda aka yi min a gidan nan an kyauta?"
Sai kawai ta fashe da kukan kissa.
Shikenan abinda yake tsoro ya faru. Ya nasawa zuciyarsa. Amma a fili sai ya ce.
"Me aka miki Zuwaira?"
Ta ce cikin kuka. "Yanzu dan anga ba ni na haife Yazeed ba a ce za a ɗura masa cikin satin nan ban sani ba. Anya kuwa Alhaji ka ɗauke ni matsayin uwarsa kuwa?
"Wallahi Zuwairah sam ba haka abun yake ba. nima kaina ban san da maganar ba sai yau da Yazeed ɗin ke gaya min mahaifin yarinyar na nemana. Kuma lokacin da zan je na zo in gaya maki ban same ki ba"
Shashatar da maganar ta yi tare da cewa. "Ban san ko sai yaushe zaka daina nuna banbanci tsakanin Yazeed da Yaseer ba. Don ba kai ka haifi Yaseer ba ai bai dace ka riƙa tauye masa hakkinsa ba duk irin tsananin biyayyar da yake yi maka"
Duniya idan akwai abunda ya tsana toh bai wuce waɗannan kalman na Hajiya Zuwaira ba. Shi Bai taɓa nuna cewa Yazeed ne ɗansa ba ba Yaseer ba. hasalima ya fi yi ma Yaseer abunda yake so kan Yazeed don ɗai gudun irin haka. Amma koda yaushe Hajiya Zuwairah sai ta jefesa da wannan mugun kalamai na cewa yana nunawa yaronta banbanci.
Cikin ɓacin rai ya ce.
"Ban gane abinda kike nufi ba Zuwaira."
Sake tamke fuska ta yi.
"Yarinyar da Yazeed ya cema yana so ya aura ba yin kansa ba ne. Mahaifiyarsa ce ta tilasta mai ya aureta don kawai ta kuntatawa Yaseer tunda taga yana son yarinyar"
Kan Daddy ya ɗaure sosai dan shi ya ɗauka ma faɗan kan Nabeelah za ta yi."Ban gane inda zancenki ya dosa" ba fah." Ya tambaya cikin ruɗani.
"Na san ka gane sarai abunda nake nufi Alhaji. Ka sani ba komai yasa Ameenah ta yi haka ba sai don ta raba auren Yazeed da Nabeela ne, ta kuma kuntatawa Yaseer shi yasa take son haɗa auren Yazeed da Afanan"
"Haba Zuwairah wai me yasa kike son ki kawomin ruɗani cikin wannan lamar ne. Idan dai don Nabeela kike haka ki sani dole ne Yazeed ya aureta ko yana so ko baya so tunda dai har ita tana sonsa."
"Gaskiya Alhaji sam wannan ba zai yiyu ba. Nabeela ba za ta taɓa zama da kishiya ba. ka sani sarai tun tana yarinya take son Yazeed. Me kake tunanin zata ji idan ta dawo ta tarar Yazeed ya aure wata ba ita ba?"
Shiru Daddy ya yi yana nazarin kalamanta. Ganin yanda jikinsa ya mutu ne yasa taci gaba da magana.
"Bama wannan ba. Yanzu haka Yaseer yana ɗaki kwance baida lafiya saboda yarinyar da ka je nemawa ɗanka aure. Da shi suka daidaita bada Yazeed ba. Yana sonta itama tana sonsa amma lokaci ɗaya kuma Yazeed ɗin ya sanya masu katangar ƙarfe a tsakaninsu."
Kan Daddy ya sake ɗaurewa. "Me yasa Yaseer ɗin bai gaya min yana son yarinyar ba? Da tun farko ya zo ya gaya min ai da ban dauke zancen Yazeed ɗin ba tunda shi dama yana da wadda zai aura. Amma yanzu kam aikin gama ya gama bakin alƙalami ya riga ya bushe dan an Riga an DAURA AUREN YAZEED DA AFNAN YAU DIN NAN.