Diyam bata samu shiryawa ba har sai data ji horn din mota a waje, sannan ta bambare jikin ta daga Sadauki ta ruga daki da gudu tayi refreshing. Tana cikin saka kaya Fanna ta shigo dakin tana kallon ta tace "wai sai yanzu kike shiryawa?" Diyam tace "da wannan complain din da kike yi dama jakar da zan tafi da ita kika dauko min a closet. Na riga na hada kayan da zanyi amfani dasu a can tun a gida" Fanna ta shiga ta fito da karamar jaka a hannun ta, lokacin Diyam har ta yafa mayafin ta tana checking contents din handbag dinta sannan ta kara abinda zata kara tayi zipping dinta ta rataya.
Suna saukowa Fanna tace "baku da abinci a gidan nan? Ki zubo min dan Allah ko a mota ne sai inci yunwa nake ji" Diyam tace "nima yunwar nake ji, in kin samu nima ina so".
A waje Sadauki ne a tsaye tare da Al-mustapha wanda yake cousin din su Sadauki kuma daya daga cikin samarin Fanna suna magana, ya dora jallabiya akan shorts din dake jikinsa. Su Diyam suna fitowa Al-mustapha yazo ya karbi jakar hannun Fanna ya je ya saka a mota, Fanna tana kallon Sadauki tayi wa Diyam raɗa tace "baiwar Allah me kika yiwa yaya na? Na ga ya zama fari cikin dare daya. Ko dai man bleaching kika shafa masa?" Diyam tana dariya tace "kakan bleaching ba bleaching ba" amma ita ma sai ta lura fatar Sadaukin tayi haske sosai, wani annuri a kwance a fuskarsa and he seemed to have a smile glued to his face.
Al-mustapha ya dawo suka gaisa da Diyam yana kallon Sadauki, Sadauki ya lura tsokanar sa yake son yi sai yace "to ya isa haka, shiga mota" ya nuna Fanna yace "kema shiga, ko a gaban ku zanyi sallama da mata ta?" Almustapha yace "kaji masu mata, muma dai mun kusa zuwa gurin" Sadauki yace "kun kusa, amma baku zo ba. Ka bari sai kazo gurin sannan sai kazo mu jera, amma yanzu kana baya na" duk suka yi dariya, sannan su biyun suka shiga mota.
Ya karaso gaban Diyam yana kallon ta, kanta a kasa tana wasa da fingers dinta da murmushi a fuskarta, sai ya mika hannu ya kama nata, tace "zamu tafi" yace "Allah ya kiyaye hanya. I will be on the next flight insha Allah. Take care of yourself for me kinji? Sai nazo anjima" tayi murmushi tana gyada kai, sai kuma tayi ɗage on her toes tayi kissing beard dinsa. Ya bude mata kofa, ta shiga sannan ya gyara mata mayafin ta ya manna mata kiss a tsakiyar palm dinta sannan ya rufe mata kofa.
Suna jan mota Fanna tace "I will pretend kamar banga komai ba" Diyam ta harare ta tace "to ai dama babu abinda kika gani yarinya. Ni yunwa nake ji wallahi". Suna zuwa airport suka wuce VIP lounge. A can suka tarar dasu Mama already har sun isa, sai a nan Diyam ta samu tayi breakfast kafin su tafi. A lokacin ne kuma ta yi studying maman su Fanna sosai, sai ta ga cewa akwai tsantsar ilimi da wayewa a tare da ita wanda Diyam ta fahimci cewa shine dalilin da yasa bata daukan Sadauki a matsayin abin ki sai dai abin so, dan jahilci da rashin aikin yi suna playing role sosai akan wadannan abubuwa.
Kafin 11 na safe sun sauka a Maiduguri. Tun daga yadda akayi musu a airport, da irin motocin da Diyam taga sun zo daukan su harda motar security, anan Diyam ta kara tabbatar wa lallai ɗan Umar Mustapha Abatcha ta aura. Gidan da suka je kuwa ba gida bane ba, Diyam ta fahimci kamar wani estate ne amma family estate mai dauke da gidajen kakanni, iyaye da ya'ya. Gidan baban Sadauki a ciki yake, uncles dinsa kusan duk suna ciki, da kuma wadansu daga cikin cousins dinsa da sukayi aure.
Ko wanne gida ka gani a cikin estate din abin kallo ne, amma babban abin kallon shine gidan Umar Abatcha, tsarin gidan, motocin da suke gidan, kayan alatun da aka kawata gidan dasu, su suka saka Diyam ta fahimci dalilin da yasa Sadauki baya jin fitar kuɗi daga aljihunsa dan akwai su din.
Yadda ake tayi mata ya saka take ta jin kunya, abincin da aka sauke su dashi ma takasa ci sai da Fanna ta ja ta suka tafi part dinsu na yammatan gidan wanda shi a kansa ma gida guda ne. Fanna tana ta tsokanar ta "wallahi in kika ce kunya zaki ringa ji ko? To a gidan nan sai an kusa mayar dake tababbiya" Diyam tayi murmushi, amma ita tasan ba zata iya cire kunya daga ranta ba kamar yadda ba zata iya cire jini daga jijiyoyin ta ba.
Anan ta samu taci abinci sosai tare da sauran yammatan, sai kuma duk suka yi wanka har ita suka fara shiryawa, ta jawo jakar kayanta zata saka sai Sa'adatu tace "Mama fa ta bayar anyi miki dinkin da zaki saka yau, sai dai ki gwada abinda baiyi ba aje yanzu ayi miki adjusting" Diyam tayi godiya, amma kuma ta so saka nata kayan data tanada musamman saboda yau din sai dai kuma hausawa sunce yaba kyauta tukuici, in bata saka kayan ba Mama ba zata ji dadi ba. Dan haka sai ta yanke shawarar zata saka yanzu in yaso in an jima sai ta saka nata.
Aka kawo mata kayan ta saka, komai yayi mata sai hips ne da za'a dan buda mata saboda ya kamata sosai. Nan take Sa'adatu tayi waya aka zo aka karba kuma suna cikin yin kwalliya sai gashi an dawo dashi. Farar shadda ce da akayi mata wani irin stone work da golden brown stones a gaban rigar da kuma hannayenta, in ka gani zaka dauka aikin sirfani ne amma stones ne kawai aka jera su, Falmata tayi mata dauri mai kyau da dankwalin shaddar sannan ta saka set din sarka da bungles na danyen gold wanda ta dauko daga kayan lefenta, ta saka takalmi ta rike clutch golden brown ta yafa farin mayafi marar kauri nan take ta fito a matsayin Mrs Aliyu Abatcha.
Bayan suma su Fanna sun gama shiryawa sai suka fita babban palon gidan, aka zaunar da Diyam a kan kujera kusa da Mama wadda taci kwalliyar ta irin ta wayayyun manyan mata, Diyam tana zama ta rike hannunta tana yaba kyawun da Diyam din tayi.
Already mutane sun fara zuwa gidan, yanuwan Sadauki, kannen babansa mata da matan kawun nan sa, matan abokan babansa, abokan arziki da sauran matan manyan gari. Duk wadda tazo zata zo su gaisa da Mama sannan Diyam ta gaishe ta, Mama kuma tayi introducing dinsu, kuma duk sai sun yaba kyawun Diyam sannan suyi mata wasa saboda kasancewar su barebari ita kuma sai dai tayi murmushi kawai dan ba zata iya mayarwa ba. Camera man kuwa yana ta aikin sa.
Wasa wasa gida ya fara cika, duk girman palon sai Diyam taga mutane suna neman cika shi. Kowa kuma tazo zata kawo mata gift ta karba tayi godiya sannan sai Mama ta saka a shiga dashi ciki. Sai a lokacin ta fahimci ma ashe ba wai anan ne za'ayi taron ba, akwai hall da suke dashi a gidan wanda suke amfani dashi dan gudanar da tarurruka ko kuma family meetings.
Sai da akayi la'asar sannan aka fara kai mutane can gurin taron, Diyam kuma ta koma daki dan shiryawa. Tana shiga sallah ta fara yi sannan ta dauko kayan da ta taho dasu ta ajiye akan gado a lokacin da Sa'adatu ta shigo dakin tana kallon kayan tace "wow" Diyam tayi murmushi. Kayan Fulani ne na saki complete set din da abin wuya da hannu da kafa da komai. A gaggauce tayi wanka, sannan ta danci abinci kadan kafin ta shirya tsaf ta fito a cikakkiyar bafulatanar ta.
Nan take ta dauki kanta a hoto ta turawa Sadauki wanda tun lokacin da suke tare da su Mama yake ta kiranta a waya amma ta kasa daukan wayarsa a gabansu. Yana gani yayo reply
"Diyam, na taba gaya miki kuwa cewa ke din kyakykyawa ce?"
"Really? Ba zan iya tunawa ba. Maybe ka taba fada but not directly"
"To yanzu zan fada directly din. You are very beautiful Halima. Kina da beauty na fuska, na jiki dana zuciya. Ki godewa Allah Diyam dan yayi miki komai"
"Anya kuwa na kaika kyau Aliyu? Ni in ina kallonka har mamakin kyawunka nake yi. Komai naka tamkar kai ka zabar wa kanka. Komai ya dace da komai a fuskarka wadda ita kuma ta dace da jikin ka. Jikinka kuma ya dace da sunanka, Aliyu Sadauki. Strong in the heart and the body".
Imojin heart mai beating
"I love you so much my husband"
"I love you more, my wife".
Dakin taron ya cika sosai da manyan mata, ga makada nan suna ta aikin su mata ana ta cashewa ana barin kudi. Diyam tana zuwa aka saka ta a tsakiyar fage aka fara yi mata ruwan kudin da har sai da ta fara tunanin anya wannan ba almubazzaranci bane ba? Ba'a tashi daga event din ba sai da aka fara kiran magrib.
Karshen gajiya Diyam ta gaji, jikinta gabaki daya ciwo yake yi mata dan haka tana komawa daki ta chanja kayanta zuwa simple doguwar riga ta material budaddiya kuma mai laushi sannan tayi sallah, akan sallayar anan ta zame ta kwanta sai bacci. Cikin baccin aka zo aka tasheta wai taje su gaisa da matar governor wadda bata samu zuwa dazu ba sai yanzu. Can palon Mama aka kaita ta tarar dasu suna ta hirar su suna dariya, ta gaishe su suka amsa mata da fara'a suka yi ta tsokanar ta tana rufe fuska sannan matar ta dauko wani set din scent burner mai dan karen kyau tare da manyan containers na turaren wuta iri iri ta bata a matsayin gift sannan tayi musu sallama, Mama tayi mata godiya sannan ta tafi ta raka ta.
Bayan Mama ta dawo ne sai kuma ta zauna tana ta yiwa Diyam nasiha da kuma dabaru irin na zaman aure da hanyoyin da zata bi ta juya mijinta kamar waina a tanda ba tare da boka ko mallam ba, wadansu maganar sai Diyam taji sunyi mata nauyi da yawa amma kuma duk tana ganewa kuma tana dauka. In dai Sadauki ne, she can and will do anything for him.
Suna tare su Fanna suka shigo, sannan aka gabatar musu da abinci suka hadu a dining din Mama suka ci tare sannan suka dawo palo suka cigaba da hira, Diyam tana ta mamakin yadda Mama take yi da yayanta kamar kawayenta. Suna nan tare Sadauki ya shigo, Diyam ta kalleshi sau daya suka hada ido ta sunkuyar da kanta, ya je ya gaida Mama sannan ya samu guri ya zauna yana amsa gaisuwar kannensa cikin kulawa, Diyam ma ta gaishe shi ya amsa ba tare da ya kalle ta ba yana danna phone dinsa, Fanna tayi dariya Diyam ta harare ta.
Mama tace "kaje gurin babanka kuwa?" Yace "eh, muna tare dashi ai tunda nazo, sai daya shiga ciki sannan na shigo". Ya turo wa Diyam text
"ki taso mu tafi"
Tayi reply "ina?"
"Dakina"
"Lallai ma, kar ma ka saka rai"
"Dan Allah"
Ta karanta sai ta dago kai ta harare shi. Ya hade hannunsa alamar roko sai ta gyara zamanta yadda bama zata ke kallon sa ba ta kuma ajiye wayar ta a gefe bayan ta saka ta a silent. Sai kawai suka cigaba da hirar su shida Mama, tana bashi labarin taron da irin matan da suka zo da kuma gifts din da Diyam ta samu. Sai yayi mata godiya sosai sannan ya mike tsaye yana cewa "Fanna kawo min abinci daki na, Please" Mama tayi sauri tace "wacce Fanna kuma? Mu ai mun yaye ka yanzu. Halima tashi maza ki hada abinci ki bishi ki kai masa" bai ce komai ba yayi hanyar waje sannan ya juyo a wayence yana kallon Diyam, yayi mata gwalo.
Ta tashi ta hada masa duk abinda tasan zai so ta zuba a basket sannan tace da Fanna "tashi ki rakani" Fanna ta harare ta "kinga in kika fita daga gidan nan ki kalli gabas, gini na farko da kika gani a gurin shine part dinsa" Adama tayi dariya tace "me dakin gabas kenan, shi yasa mu a gidan nan bamu fiye kallon gabas ba sai in zamuyi sallah" Falmata tace "to ai dan kar mu kalla ace harara mukayi" Mama ta jefi Fanna da remote tayi mata magana da barbarci sai ta mike suka fita tare da Diyam.
Suna fita Diyam tace "kun takurawa bawan Allah nan. Mutum mai hakuri da kawaici irinsa, mutumin da ko hannu aka saka masa a baki ba lallai ya ciza ba" Fanna tace "waye hakan? Lallai so hana ganin laifi. To in gaya miki saboda muguntar sa kwanan baya sai da ya saka ni Fanna na share gidan nan gabaki daya, tun daga sama har kasa" Diyam tayi dariya tace "daga ji wani babban laifi kika yi masa, shi bawan Allah ne mai sanyin zuciya mai kuma hakuri da yafiya idan aka bata masa" Fanna ta tsaya ta rike kugu tana kallon Diyam tace "anya kuwa ya taɓa yi miki tsawa? Idan yana yi wa daya daga cikin mu fada gabaki daya gidan nan amsa kuwwa yake yi. In yayi miki tsawa kuwa sai kin kusa sakin fitsari a tsaye" Diyam ta rufe bakin ta tana dariya, a lokacin suka zo kofar part din Sadauki.
Fanna ta bude kofa ta tsaya a gefe tace "maganar yafiya kuwa, wacce take fadar maganar tafi wacce ake fadawa sanin cewa ba gaskiya take fada ba. Good night my friend" Diyam tana murmushi tace "yanzu zan dawo ai. Abinci kawai zan kai masa" Fanna tace "we will see about that".
Tana shiga dan karamin palour ta tarar wanda yasha kujeru madaidaita da suka dace da komai na wajen, ta ajiye abincin tana studying kyawun gurin, kofofi ta gani guda biyu suna kallon juna sai ta tafi kofar da jikinta ya bata yana ciki tayi knocking ta tura kofa, yana kwance a kan gado da waya a hannunsa, dakin cike da sanyin ac da kuma kamshin sa, ya ajiye wayar yayi mata murmushi yana folding hannayensa akan kirjinsa yace "welcome wife" ta tsaya daga inda take tace "ga abincin" ya dan bata rai "waye yace miki yunwa nake ji?" Ya langwabe kai "Ni matata nake so" ta fara bubbuga kafa a kasa cikin shagwaɓa "ni wallahi bacci nake ji, ni wallahi na gaji jikina ciwo yake yi min" ya mike zaune yace "good. Kinga sai inyi miki massage" ya fada yana tattare hannun rigarsa.
Ya nuna gefensa akan gadon yace "come and lay down here inyi miki tausa. You will thank me tomorrow". Ta yi kamar zata yi kuka, ya miko mata hannunsa yana kara marairaice wa, ta sake protesting "in nazo hana ni tafiya zaka yi, kuma kaga gidan surukai ne nan" ganin ba zata zo ba sai ya karaso inda take ya zagaye ta da hannayensa ya dora goshinsa akan nata yana murmushi yace "ina ne gidan surukan? Gida na ne nan. Gidan ki ne nan. Kin taba ganin inda amarya ta bar gidan angonta washegarin da aka kaita ta je ta kwana a wani gidan?"
Ta zagaye shi da nata hannayen tana jin daɗin dumin jikinsa da ya fara ratsa nata jikin, already zuciyarta tana gaya mata cewa anan zata kwana, anan tayi belonging, in his room, on his chest. Amma sai ta kara jan ajinta "ai ba nan gidan aka kawo ni ba, kuma yanzu ni bakuwa ce, ni bakuwar Mama ce"
Yace "okay, naji, ba zaki kwana anan ba, amma dai wannan massage din ba za'a hana ni ba. I will make sure na cire miki gajiyar da kike ji sai in raka ki da kaina har kofar dakin Fanna" ta jawo hannayenta daga bayan sa ta rike fuskarsa da su tace "kayi alkawari?" yayi murmushin da ta kasa fahimtar ma'anar sa yace "nayi alkawari".
Yana gama fadar haka taji ya raba ta da kasa, ta ɗan yi dariya tana jin dadin strong arms dinsa sannan taji ya sauke ta a tsakiyar gadonsa yace "welcome to me once empty, cold bed, which is neither a yanzu" tayi murmushi tana tuno lokacin da Saghir yayi masa wannan gorin. Ya sunkuyo yana kokarin kai fuskarsa kusa da tata sai ta saka ɗan yatsanta a saman lips dinsa tace "kar ka manta, tausa kawai muka yi alkawarin zaka yi min" ya sake murmushi irin na dazu sannan yace "with pleasure".
Ya juya ta ta koma ruf da ciki sannan ya fara matsa mata bayan wuyanta a hankali da finger tips dinsa, ta lumshe ido tana jin daɗi, a hankali ya sauko saman kafadunta yana matsa mata su cikin nutsuwa, a lokacin wani bacci mai daɗi ya dauke Diyam, wannan ya sa bata san sanda ya zuge zip din rigarta ba, ba kuma ta san sanda ya matsa duk inda yake so ya matsa ba har inda babu gajiya a gurin, sai sanyin ac taji yana ratsa tsokar jikin ta sakamakon barin jikinta da kayan ta suka yi, amma kafin tayi complain taji dumin naked jikinsa ya maye gurbin sanyin, sai ta rike complain dinta dan itama a lokacin ko ance mata ta tafin ba zata iya tafiya ba, itama mijinta take so kamar yadda yake son matarsa, dan haka babu bata lokaci ta fara karbar sakonnin sa tana kuma aika masa da nata.
Da safe sai da kowa ya tashi a gidan aka kuma gama komai har breakfast an gama shiryawa amma babu Diyam babu Sadauki babu kuma labarin su. Anyi ta kiran wayoyinsu kuma da suna shiga amma daga baya switched off. Sai da aka zo yin breakfast sannan Papa yace aje a kirawo su, yana son suci abinci tare gabaki dayansu saboda a ranar yake son komawa Canada.
Cikin bacci Diyam taji kamar ana knocking kofa, ta bude ido da kyar saboda nauyin bacci ta sauke su akan kirjin Sadauki da take kwance a kai, ta daga fuskarta tana kallon tasa fuskar so deep in his sleep sai kawai ta dulmiya wajen kare masa kallo tana murmushi tare da dawo da memory din daren jiya, ta kasa bambance jiya da shekaran jiya wanne ne yafi tafiya da hankalin su baki daya. Ta kasa banbance wanne ne Sadauki yafi mace wa a kanta. Sai ta tuna da sanda yace yana so duk sauran dararen su su kasance kamar daren farkon su.
Wani bugun kofar da aka sake yi shi ya dawo da ita daga duniyar kallon Sadauki. Ta mike zaune tana gyara rigar jikinta sannan ta mike tsaye tana kallon Sadauki ko motsi bai yi ba, ta yafa mayafin ta itama still cikin baccin ta fita palour ta bude kofa tana murza ido. Fanna ta gani a tsaye, ta harare ta tace "kika ce min ba kwana za ki yi ba" Diyam tace "wannan ne dalilin da yasa kika dame mu muna bacci? To bara inje in kira wo shi sai ki maimaita a gaban sa" ta daga hannu tace "Allah ya baku hakuri, ni yar aike ce. Papa ne yake kira, in kuma inje in gaya masa kunce kar a dame ku ne to?" Diyam ta buɗe ido, tunanin ta ya fara dawowa, sai ta juya da sauri ta koma ciki tana salati tare da yayyarfa hannu, ta tashi Sadauki ta gaya masa sakon kira sannan ta fita da sauri a ranta tana cewa "wannan wanne irin abin kunya ne nayi ni Halima".
Da sauri tayi brush ta wanke fuskarta ta chanza kaya sannan suka tafi part din Papa inda anan ake neman nasu. Tana shiga Sadauki shima yana shigowa, fatar idonsa a dan kumbure alamar bacci bai ishe shi ba. Shi ya fara zuwa ya durkusa ya gaida mahaifinsa sai bayan da ya zauna sannan Diyam itama ta karasa for the first time ta gaishe da surukinta. Ya amsa da madaukakiyar fara'a "Halima, ance min jiya kinyi kyalliya da kayan fulani, ni kuma sai nace to lallai zamu zana miki tribal marks din barebari a fuskar ki dan mu tabbatar miki kin zama tamu yanzu" duk suka yi dariya har Diyam data rufe fuskarta da mayafinta.
Sai data zauna sannan ta samu damar ganin fuskarsa. Sai a lokacin tayi mamakin yadda akayi duk ganin da take yi masa a hotuna bata fahimci suna kama sosai da Sadauki ba sai data gan shi ido da ido tukuna. Bayan shekaru, banbancin fuskarsa data Sadauki shine hancin Sadauki yafi nasa tsaho, sumar Fulani da Sadaukin yake da ita, da kuma tribal marks da shi Papa yake dasu wadanda shi Sadauki bashi da su.
Suna zama masu aiki suka matso suna tambayar kowa abinda za'a zuba masa daga cikin menu, kowa ya fada aka fara serving, Fanna kuma ta fadi nata dana Diyam dan tasan ba zata yi magana a gaban su Papa ba.
Sai da suka gama cin abincin sannan Mama ta sake yiwa Diyam barka da zuwa family. Papa kuma ya dora da cewa "ina so Halima ki saka a ranki cewa nan gidan ku ne ba wai gidan surukan ki ba, ki dauke ni a matsayin baban ki ba wai baban Aliyu ba. Saboda baffanki, malam Usman yayi min halaccin da babu wanda ya taba yi min irinsa a duniya. Ya rike min Aliyu tamkar shi ya haife shi dan haka nima zan rike ki tamkar ni na haife ki insha Allah. Wannan shine abinda zanyi in kwatanta abinda Usman yayi min".
"Nasan Aliyu ya baki labarin dana bashi akan rabuwata da mahaifiyar sa amma ban gaya masa dalilin da yasa bayan nayi bincike na gano wanda yake neman halaka su kuma na dauki mataki akan sa ban koma na dawo dashi gida gurina ba. Na barshi ya cigaba da zama a hannun Usman ba tare da yasan nine mahaifinsa ba saboda a lokaci nayi tunanin hakan shine dai dai a gurinsa, maybe I was selfish, but I wanted what was best for my son. Ni mutum ne mai harkoki da yawa wanda ban fiya samun lokacin kaina ba ballantana na iyali na, tarbiyya, nuna soyayya, nuna kulawa ga dan karamin yaro bayan kuma bana tare da mahaifiyar sa ba abu ne da zai samu a gurina ba. Wannan ne yasa na bar shi a hannun Usman da Zainab. Na kuma boye kaina daga gare shi ne saboda ina son ya zama strong, bana son yasan nine mahaifinsa ballantana ya dora wani abu a ransa ko kuma ya raina marikansa. Sai na nemi alfarmar Usman nace ya koya masa neman na kansa tun yana karami. I used to go to the garage duk sanda na samu dama, I used to watch him work, drenched in oil and sweat, na kan ce a raina "good, yanzu zaka san darajar kowacce kwandala da ka samu".
"Usman kuma bai taba neman ko kwandala daga wajena ba saboda kula da Aliyu, sai lokacin daya kasa samun admission ne ya nemi in taimaka masa ni kuma nace ya barshi ya sha wahala ya samu da kansa, har yayi fushi dani a lokacin yana ganin kamar nayi tsauri da yawa. Amma yanzu gashi naga result din abinda nayi din, Aliyu yayi turning into more than yadda na saka rai. Yes, na bashi kuɗi nace ya juya, shekaru biyu bayan nan dana bincika sai naga already yayi doubling kudin da na bashi. A yanzu haka bansan adadin me yake dashi ba. Allah ne kadai yasan me ya tsara wa rayuwar sa amma ni ina saka ran cewa this is just the beginning for him. Allah yayi muku albarka gabaki dayan ku, Allah kuma ya baku zaman lafiya da zuriya mai albarka".
Duk suka amsa da ameen. Diyam ta saci kallon Sadauki sai taga kansa a kasa amma fuskarsa tana nuna tsantsar farin ciki. Mama tace "a matsayin wedding gift, Papa and I decided to give you two, Aliyu da Halima, gidan mu na Oxford, mun bar muku shi duniya da lahira. Allah ya baku zaman lafiya" nan take gurin ya kaure da murna, siblings din Sadauki duk suka taho suka rungume Diyam suna taya su murna. Ta gefen idonta taga Sadauki ya durkusa gaban mahaifinsa yayi godiya, sai taga ya dago shi ya rungume shi a jikinsa yana bubbuga bayan sa.