KISHIN MATA

Por Hafnancy01

2.3K 27 6

"Don girman Allah Suleiman karka sakeni,ka tuna fa igiya ɗaya ce ta saura atsakanina dakai,ka tausayamun kark... Más

1
2
BABI NA UKU
BABI NA HUDU
BABI NA BIYAR
BABI NA BAKWAI
BABI NA TAKWAS
BABI NA TARA

BABI NA SHIDDA

158 3 0
Por Hafnancy01

*🍃KISHIN MATA🍃*
               🍃🍃🍃
         _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_
           _*[Hafseesee]*_

   _*💫Dedicated to:-Anty Bahijjata & Grandma Zm Chubado*_

   
*#An_Intense_Jealousy_Story*

          _*💫BABI NA SHIDDA...✋☝*_

     "Amin waʼalaykis salam yʼata da fatar duk kun tashi lafiya?ya kuma kwanan bakʼuwar taku?ʼʼ sai da ta hadʼiye wani miyau mai dʼaci kan tace"Lafiya qalau momy fatar kuma kun wayi gari lafiya?ʼʼ

"Muma nan dʼin alhamdulillah! kiyi hakʼuri na kʼiraki ah irin wannan lokacin ban bari gari ya kʼarashe wayewa ba dama so nake nace miki karku dafa komi su kasim zasu kawo muku breakfast zuwa bakwai shiyasa na kʼiraki sabida kar kiyi saurin shiga kitchen don nasanki sarai..ʼʼ

  Wani sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tana kallón Gidado wanda shima dʼin yaji kómi dón ah handsfree ta saka,Allah sarki ita dai momy akwai kulawa don alokacin Jameelah ah kwanakin amarcinta ta jera sati guda tana aikó musu da abinci ne,na safe,rana dana dare,Jameelah bata aza tukunya ah wuta da sunan girki ba har sai data cika kwana bakwai agidan Gidadó;cike da tausayinta tace cikin kwantar da murya''Haba momy ke bakʼya gajiya ne da hidima?don Allah wannan karon ki huta plss ba gani ba?tou miye amfanina agidan?ʼʼ

  Momy tace''Nasan dake ai ammh raʼayina ne don haka karki damu yʼata...ʼʼ har zata sake musa mata kuma taga Gidado yayi mata ido alamun karta mata gaddama,tace''Tou shikenan momy Allah ya saka da alheri..ʼʼ daga haka sukai sallama,ya fuzge wayar ya jefar saman gado tare da jawota ya matseta ajikinsa,yace'' wai fushin menene akeyi dani ne haka?ʼʼ

    Kamar baza tayi magana ba can kuma tace''Meya kawoka dakina bayan acan yakamata kayi sallah da kayi wanka?on a serious note Sahibuna abunda kakeyi be dace ba,haba karka kasance cikin mazan da basa kwatanta adalci atsakanin matayensu mana...ʼʼ
    

     Da mamaki yake kallonta kan yace''Ai kowa ma yasan idan na auri wata tou fa zatasha bakʼar wuya don dole zata ga banbanci kʼiri kʼiri sabida Jameelah alone ownʼs my heart,,Allah dai ya yafeni tunda ma baʼa son raina na aurotan ba ammh zan dʼanyi kokari naga na kwatanta adalci buh my dear it wonʼt be easy at all...ʼʼ

dʼan Matsa kafadunta yayi yace''Yauwaa tukunnah ma dai hearthrob wani wanka kike nufin nayi?ʼʼ  kwace kanta tayi ta zauna agefen gado tare da kʼawar da ganta daga gareshi,sai ta koma kallon labulen window,ajiyar zuciya ya sauke kan ya matsa kusa da ita ya tsugunna agabanta gami da dafe gwiwowinta,ya shiga lekʼa fuskarta abun ma har yaso ya bashi dariya ganin yadda ta hadʼe fuska tamkʼar bata tabʼa sanin dariya ba,yace''Hearthrob kar kice mun wankan sarki kike nufi..?come on swthrt i think itʼs too early for dat,,infact saurin meh zanyi bayan itʼs not my first tym?so kibar tunanin nan pls ni banyi kowani wanka baʼʼ ya ida maganarsa yana cijen lips,

Duk da cewa kishi na cinta ammh hakan be hana kunya kamata ba,da sauri ta mikʼe da gudu tayi bandakʼi kuma kafin ya cafkota ta murzawa kʼofar key,sai kuma ta fashe da kukan kishi,shi kuwa tausayinta ne yakamashi sosai,ya sani sarai cewa Jameelah tana kʼaunarsa don she can even sacrifice her life for him,ya zama dole tayi kishi sabida duk wani mai maka soyayyar gaskia dolene yayi kishi akanka,daʼace yana da iko ne da kansa da wallahi babu yadda zaʼayi yayi abunda su iyayensa keso beyond his wish,ammh ina ya zama dole yayi musu biyayya don ya faranta musu sannan kuma azauna lfy,kada kai yayi yabar dakin ganin shidda har ta kusa kuma yasan Hafsa nanan kwance har yanzu bata tashin ba,

Wani abun mamaki kuma yana kutsa kai cikin dakin ya hangota saman sallaya ta idar da sallah tana rera karatun qurʼani cikin amon sauti mai dadin sauraro,jikinsa ne yayi sanyi kʼalau da wannan alʼamarin,ahankali ya zauna akan sofa yana mai lumshe idanu da karatun da take don har wani sanyi da imani ne yaji yana ratsa zuciyarsa,idanunsa akanta harta kʼare,be gama shanye mamakinsa ba sai gani yayi tazo inda yake ta russuna cike da ladabi tamkʼar ba ita ba tace''Mijin mata biyu ina kwana?fatar ka tashi lafiya?ʼʼ

Tsura mata ido yayi cike da mamaki da al'ajabi,wai shin matayen nan nashi meyasa suke da ababen mamaki ne haka? ya ayyana aransa,saida yayi gyaran murya kan yace''lafiya kalau matar dʼan sanda ya bakunta?ʼʼ

Murmushi ta saki mai hadʼe da kunya wanda hakan ba karamin bashi mamaki yayi ba wai Hafsah ne da kunya yau,cikin sanyin murya tace''Alhamdulillah....ʼʼ

   ''Hafsah wai in tambayeki man?ʼʼ

Tace''Ina jinka ranka shi dadʼeʼʼ

    ''Dama ashe kina da wannan hankalin da nutsuwar ammh jiya kiketa abubuwan marasa kunya da rashin hankali?kiyi hakuri fa ammah seriously speaking azatona mahaukaciya na auro,pls ki dena idan kinason ni dake mu zauna ah inuwa guda,inason acigaba da tafiya da wannan dabiʼar kina jina ko?ʼʼ

  Sosai taji zafin kalmar daya dangantata dashi wató _*'mahaukaciya'*_ ammh kuma sai tayi kókarin danne abunda ke neman taso mata ah zuciya tace tana murmushi''Kayi hakʼuri wallahi duk cikin _*'KISHINMU'*_ na  _*'MATA'*_ ne ammh zanyi kókari naga na kiyaye,da yardan Allah bazaka sake kuka dani ba..ʼʼ

Ajiyar zuciya ya saki mai kʼarfin gaske dón sosai yaji dadin kalamanta kuma insha Allahu zaiyi kokari yaga ya kwatanta adalci atsakaninsu,ware hannaye yayi yace''Come on baby give me a hug...ʼʼ

Ah kunyace ta mikʼe ta isa gareshi don dama ta kʼosa ta jita ajikin mijinta itama tasan tayi aure,wani irin shock ne dukkaninsu suka ji ah saʼilin da suka rungume juna......

  

     __________*********

Kafin bakwai momy da 'ya'yanta mata sun kammallah breakfast wanda zaʼa kai gidan Gidado,kwantar da hankali sukai sosai suka hadʼa musu lafiyayyen girki,toasted sandwich,smashed chicken and ground beef cabbage sauce sai kuma kunun gyadʼa mai shinkafa,bayan an kimtsa komi ta samu Kasim acan dakinsa na bʼangaren matasan gidan,yana baccinsa mai dʼan karen dadi ta tayar dashi tare da fadʼa mishi bukatarta nason ya mikʼa sakʼo gidan Gidado,dʼan siririn tsoki yajah cike da takaicin yadda aka katse masa baccinsa,kuma Allah ya gani bason zuwa gidan nan yake sabida yadda Gidadon ke saka masa zafi,sam sam basa shan inuwa dʼaya don Kasim ya kasance manemin mata ne,momy ta lura da yadda yaketa cuno baki gaba tace''Yi hakʼuri don Allah kaji Tankona...ʼʼ kasancewarsa dʼa namijinta kwara dʼaya tak kuma farko sauran biyun duk mata ne,Hanifa saʼar Baddo da kuma kʼanwarta Mardiya.

  Yace''Tou wacece zata mun rakiya acikinsu don gaskia ni bazan shiga ciki ba idan munje...ʼʼ Momy tace''Eh tou su Hanifa dai duk sun koma bacci sabida gajiya ammh dai bari na nemo Baddo Allah yasa itama dʼin ta tashi dai...ʼʼ wani ddi ne yaji ya lullubʼe mashi zuciya don dama yana son ya sake kʼebancewa da ita.Beci mata musu ba ta tashi ta tafi,ai kuwa ta samu Baddon bata komi,ta sata ta sako hijabi bayan ta gaya mata inda zasu ita da kasim,ita ba tsoron zuwa gidan ne taji ba illah da wanda aka ce zasu je taren wato kasim,tana tsoron kar Gidado ya fille musu kai wannan karon idan har ya gansu tare,

   Ah motar yabban Kasim suka fita,saida sukayi dʼan nisa sannan Kasim ya gangara gefen hanya ya paka motar,da sauri Baddo ta dubeshi tace''Ya kuma naga ka tsaida motar lfy kuwa?ʼʼ ta fadʼa da mamaki

Kallonsa yayi da jajayen ido yace''Mubeenah plss karki bari ayimun iyaka dake don ina mugun sonki,ki sani idan har ya kasance babu ke zuciyata tamkʼar wata fure ce da Allah ya halicceta domin ki dunga bata ruwa,toh inason ki gayamun idan ya kasance babu ke wazai dunga bata ruwa?ki sani dole ta bushe ta yamutse,so pls Mubeenah am begging you letʼs fight for our right mubar jin tsoron Hamma Gidado,kalli wlh duk barazana ce yake mana ammh babu abinda zai iyayi...ʼʼ

Haka dai ya cigaba da gaya mata kalamai don canza mata raʼayi har dai ta samu kwarin gwiwar soyayya dashi,yace yana murmushi''Naji ma ance zaki tsaya kiyi hutunki gaba dʼaya anan garin ko?ʼʼ

amsa masa dakai kawai tayi tana murmushi,yace''Yesss kinga kafin ki koma mun gama gina soyayyar juna azuciyoyinmu...ʼʼ da sauri ta rufe fuskarta da tafin hannayenta don kunya,can yaja mota yayi gaba,ahanya ma ya cikata da surutu ne har suka isa,dama sabon gida ne ana saura sati daya bikinshi da Hafsa shine suka tare aciki,yace da ita ta shiga ta mikʼa sakʼon zai jirata awaje..waro masa idanu tayi cike da tsoro tace''Gaskia kai kaje ni zan jiraka awaje wlh banson haduwa ne da wannan mugun...ʼʼ ta fadi tamkʼar zata saki wani dʼan marayan kuka,shi kanshi agaskia yana tsoron hadʼe idanu naji kawai waske mata yakeyi kamar be tsoron nashi,dakyar dai da sudin goshi ya samu ta dauki kafcecen basket dʼin ta nufi gidan shi kuwa yabi bayanta da kallo cike da tsantsar shaʼawarta zallah,knocking ta shiga babu gaggautawa kuma baʼa dauki tsawon lokaci ba security yazo ya budʼe mata kofa,tayi mishi bayanin kanta ya matsa mata ta shige...............

 

Comment &
Share pls

Seguir leyendo

También te gustarán

615K 17.9K 23
Beau HATES Oliver Fowler. But Oliver doesn't hate Beau.. quite the opposite actually. Oliver is the univeristies 'Golden Boy', adored and admired by...
1.6M 96.8K 39
"You all must have heard that a ray of light is definitely visible in the darkness which takes us towards light. But what if instead of light the dev...
672K 26.1K 74
Lilly found an egg on a hiking trip. Nothing abnormal on that, right? Except the egg was four times bigger than supposedly the biggest egg in the wor...
599K 63.3K 25
في وسط دهليز معتم يولد شخصًا قاتم قوي جبارً بارد يوجد بداخل قلبهُ شرارةًُ مُنيرة هل ستصبح الشرارة نارًا تحرق الجميع أم ستبرد وتنطفئ ماذا لو تلون الأ...