KISHIN MATA

Autorstwa Hafnancy01

2.3K 27 6

"Don girman Allah Suleiman karka sakeni,ka tuna fa igiya ɗaya ce ta saura atsakanina dakai,ka tausayamun kark... Więcej

1
2
BABI NA UKU
BABI NA HUDU
BABI NA SHIDDA
BABI NA BAKWAI
BABI NA TAKWAS
BABI NA TARA

BABI NA BIYAR

180 3 0
Autorstwa Hafnancy01

*🍃KISHIN MATA🍃*
               🍃🍃🍃
         _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*♟ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_
           _*[Hafseesee]*_

   _*💫Dedicated to:-Anty Bahijjata & Grandma Zm Chubado*_

   
*#An_Intense_Jealousy_Story*

          _*💫BABI NA BIYAR...✋*_

…! Zama yayi akusa da ita tare da jawota ta fad'o jikinsa,kuka take sosai mai tsuma zuciya wanda ya had'e da kukan kishi,hura mata iska yayi acikin kunne don yasan abinda tafi so kenan idan har zai lallasheta kana yayi mata rad'a ah kunne''Hearthrob wannan kukan na menene haka ko duk na kishin ne?I beg you karki daga hankalin Gidadonki plsss,,trust me nadai auri Hafsah ne akan tursasawar iyaye ammh zuciyata tana tare dake ne....!ʼʼ

  ''..Naji na kuma amince ammh ai gashi shi gangar jikin kuma ka raba mana ai,,Suleiman hakikʼa ina tsananin kishinka ammh kokari nake na danne zuciyata don banison na kasance acikin matayen dake tafiyar da rayuwarsu akan kishin jahilci,,bani son ganinka cikin tashin hankali mijina balle ace niche sanadin shigarka cikinta,,tun baʼa kwan ba Hafsah ta riga da ta nunan da kalar data shigo ammh karka damu sahibul kalbi zanci maganin hakurin zama da ita saidai kuma ta kiyaye kar hakurin nawa ya kare wataran,,Sahibuna plsss na rokeka karka dunga biyewa fitinarta gaji.....ʼʼ

      Wani kallon shaukʼin so yake binta dashi yana jin wani irin zazzafar soyayyarta na shigarsa dakyau,,ahankali ya zame hular kanta ya cusa kansa aciki yana shakʼar kamshinsa,da sauri takai hannu ta rikʼe kan nasa tace"No no no plsss stop it sahibul kalbina its wrong,pls karmu shiga hakkʼin amarya ka tashi kaje gareta tana jiranka,,yau din darenta ne don haka dnt spoil it for her plsss.....ʼʼ ta ida maganarta tare da rushewa da wani sabon kuka,,da sauri ya dago fuskarta ya hadʼa da nashi,,goshinsu ya manne dana juna,yace in a very romantic voice"Hearthrob ahakan kikeson in tafi ga wata sannan ke in barki cikin damuwa bayan you are d woman dat trully ownʼs me?no wlh bazan iya ba,,gashi tun baʼa kwan ba ta soma gwada mun halayenta wanda na tabbtar da nan gaba bazan iya cigaba da zama da ita ba idan har bata sauyaba,,kai My Jamila i really love youuuu,,believe me ke din ta dabanceʼʼ ya rungumeta sosai ajikinsa yana mai jin tausayin kansu na ratsa bargon zuciyarsa,ita kuwa kuka take rerawa ahankali.....!

     __________★
Hafsah dai daga baya an canza raʼayi an shiga bandaki aka tsalo wanka sannan ta sanya doguwar night gown dinta wanda ko gwiwa bekai ba,mai vest hand gashi kuma shara shara dashi don tsab ake hango pant dinta da kuma shape dʼin nipples dʼinta,,wai ita nan don taja raʼayinsa ne fa😂,ta feffeshe jikinta da turare har kala hudu tare da jefa mint abaki sannan ta zauna abakin gado gami da hardʼe kafafu tana jiran shigowar oga,lokaci zuwa lokaci take tsotsar alawar,can dai taga zaman bazai amfaneta da komi ba don shirun tayi yawa,taja tsoki tare da mikʼewa tayi kofa tana fadin"wai kazar an koma yinta ne ah london dayake neman taking foreva awaje?ji kusan sha biyu ake nema fa?ʼʼ

Ta furta tana duban agogon bango kafin ta murdʼa handle na kofa ta fice take fadin"Ai zai dawo ya sameni ne...!ʼʼ

    Idan ba idanuwanta kʼarya suke mata ba tou kuwa tabbas Gidadonta ne dai take gani yana romancing Jameelah kishiyarta don har nema yake ya fita cikin hayyacinsa,,ita kuma Jameelar nema take ta kwace kanta ammh yaki bata wannan damar sai dadʼa kankameta yayi yana tsotsar lips dʼinta dkyau hadda wasu lumshe idanu,harta matso kusa basu sani ba sai kallon tsantsar mamaki da alʼajabi take binsu dashi baki sake,,bbu abunda kake ji sai kʼarar french kisses da Gidadon ke aikawa Jameelah wacce daga baya ta shiga karbʼa cuz she canʼt reject it anymore...!

      " _Innalillahi waʼinna ilaihi rajiʼun....!_ Suleiman ina can daki ina jiranka ka kawomun kaza ashe wayau kamun kazo nan kana cin taka kazar hankali kwance,,tou na rantse da Allah bazan tabʼa yafe muku cin amanata da kukai ba...ʼʼ ta rushe da kukan haushi,,su kuwa ah firgice suka saki juna tare da dagowa suna dubanta don bbu wanda yayi tunanin zata fito falon,gara ita hearthrob tayi tunanin hakan shiyasa take ta turjewa ammh shi sahibul kalbin he never saw it coming at all😆

  cike da kunya ya shafa kansa yace''Hafsah! am so sorry nayi kuskure...ʼʼ

  kallon rainin wayau ta wulla masa tace''Kamar naji ka ambaci kuskure??tou ka sani wannan ba kuskure bane illah son zuciya,,ayau daya kamata ace ina cikin tsantsar farin ciki ammh gashi u guys hav spoilt my wedding night wanda ya kamata ace nabar dadadʼar tarihi akansa,,ammh ga dukkan alamu sun nuna cewa tarihin nawa daren farkon zai rufe ne da kayan takaici wanda aduk sanda na tunashi zai jefani cikin kunci ne,Allah ya isa tsakanina daku kuma sai Allah ya bi mun hakkʼina,,wayyo kishiya bata yi ba wallahi.....ʼʼ ta sake rushewa da kuka tare da kʼarya gwiwowinta zuwa kʼasa,,jikin Jameelah ne ya dauki rawa sosai sai hawaye sharrrr cuz she felt so guilty,,da rawan murya tace"Haf...sah...don girr..man Allah kiii yaaa...femun wallhiii bazan kuumaaa ciin amanarkii ba...ʼʼ

Adaidai lokacin wayar Gidado ta dauki kidʼa,yana dubawa yaga Sagir ne,bayan ya dauka yace masa"Kai mallam yi sauri ka sameni awaje dare yaja....ʼʼ da tou kawai ya amsa masa sannan ya mikʼe yace da Jameelah"Ke wuce part dinki kuma karki sake na dawo na sameki anan...ʼʼ

Ta amsa masa daa tou,ya dubi Hafsa ransa ah matukʼar bʼace yace"Kema haka...ʼʼ

Tsoki taja tace cike da tsiwa"Anki atafin maci amana kawai...ʼʼ murmushi kawai yyi sannan yasa kai ya fice don yasan bbu yadda zaʼayi Hafsah ta taka matsayin Jameelah ah zuciyarsa,,rashin kunyarta kadai ma ya riga yasa tayi fail,bayan fitarshi Jameelah ta koma Jameelarta fuska ayamutse tace"Ke! bari kiji idan kina cin kʼasa tou tabbas ki kiyayi ta shuri don naga kamar da rawar kai kika shigo gidan,ni idan kika takani bazan wani damu ba ammh karki bari kice zaki dauki wannan banzar dabiʼar ta cin mutuncin mijina agaban idona ko agaban wani don asannan ne zaki san ainihin kalata sbd ni hawainiya ce mai canzawa aduk sanda taso,, _*DCP  SULEIMAN ALASSANA GIDADO*_ ba abun rainawarki bane harki tsaya kina tanka masa magana muryarki asaman nashi,,don haka hattara amarya in ba haka ba uwargida zata gyara miki zama....!ʼʼ

   Cike da tsantsar mamaki Hafsah ta mikʼe tsaye tana fadin"Lallai na yadda kishiya da ababen mamaki take,,wato kukan da kike ta sharbʼawa da kuma tsantsar tsoron da kika bayyana mana duk ta munafurci ce ashe,zuwa dakkoni da kikai ma nasan tabbas akwai wani abunda kika kulla ammh sai Allah besa kinci nasara ba,,kai kishiya akwai munafurci wallahi ammh ki......ʼʼ

Jameelah tayi sauri taran numfashinta"Malama abunda kika gani ba munafurci bane illah kishin ilmi irinta wayayyun mata ba irin naki na en kʼauye masu nuna kishin jahilci ba,,ada kin so ne na dunga biye miki don mu hana masa kwanciyar hankali agida?sannan ya koma ya tsaneni?tou wallahi kinyi kʼarya kuma kinyi kadan,,ki sani ke baki isa kija da mace kamata ba matar dʼan sanda....ʼʼ

Wani miyau mai dʼaci Hafsah ta hadʼiya kan tace"Dake ni dʼin kuma ba matar dʼan sandar bʼace sai matar direban gidanku ko?idan kuna ma da direban kenan,waya sani ko daga cikin tsiya aka tsamoki zuwa cikin daula...ʼʼ

Akʼaikaice Jameelah ke kallonta don sosai kalamanta na kʼarshe suka soya ranta,murmushi ta sakar mai ciwo kan tace"wannan kuma ina ganin ba damuwarki bace ammh abunda kawai nakeso ki sani shine ke dʼin ba dʼaya kike dani ba,zaman kishi da matar dʼan sanda is very annoying sbd sheʼs already trained,sumbar da kika kamamu ma muna yi na tabbata you were very shocked and suprised sabida baki tabʼa ganin irinsa ba,kadan kenan kiga gani kuma idan kikai sakaci zan dauke hankalin mijin ya dawo kaina ke kuma ki rasa gane kanshi gabaki dʼaya,don haka kibi asannu....!ʼʼ

   
     ★★_____________

  Acan waje kuma Gidado ya amshi ledojin kazar da Sagir ya kawo masa hadda kwalayen lemummuka ahadʼe,yayi masa godiya sosai,Sagir sai tsokanarsa yake yace"Malam kai dai kabi yarinyar mutane asannu banda rawar kafa kasan dai watakila sabuwar shiga ce..ʼʼ tsoki Gidado yaja kan yace"Dadʼina dakai kai dʼin dʼan iska ne,rawar kafar meh zanyi bayan dakai dani duk munsan cewa ba yau ne zan soma ziyartar wannan duniyar ba...ʼʼ

   "Amma dai ba iri dʼaya bane ai...ʼʼ ya furta yana kʼyakʼyatar dariya,Gidado ya bʼatsar da zancen yace"Gara dani ma ina da har guda biyu kai kuwa dʼayan ma ta gagareka ajjewa,,gwauro kawai...ʼʼ murmushi mai ciwo Sagir ya saki kan yace"Ai ni tunda kuka hanamun auran Surayya toni da aure kuma sai wani ikon Allah...ʼʼ yana gama fadʼar hakan yaja mota yayi gaba ayayin da Gidado yabi bayan motar da kallo cike da tausayinshi,hakʼikʼa Sagir sunso juna da Surayya ammh Allah beyi cewa ita matarsa bace sbd Tsoho ne ya hana,tunda dʼan aminin mahaifinsu wato Awwal ya nuna yanason Surayya kuma dake mahaifinshi nada kʼyakkʼyawar alakʼa da Tsoho shiyasa kai tsaye Tsohon ya rufe ido ya bawa Awwal dʼin ita ya hana Sagir....

  Jan jiki yayi ya koma ciki tare da umartan security daya rufe gidan goma..

   "Inaso ki sani kafin na rufe tarihin daren farkona ya zama dole nabar miki abun mamaki wanda bazai tabʼa gogewa ba acikin zuciyarki....ʼʼ Hafsah ta fadʼa tana watsa mata kallon tsana

"Allah ko?hmmm then Iʼll anxiously be waiting! zanta jiranki daga ciki don bazan so mijina yazo ya ganni anan ransa ya bʼace yace nayi disrecpecting nashi banbi umarninsa ba,kinsan ni matar aljannah ce..ʼʼ ta ida maganarta tare da kashe mata ido dʼaya,Hafsah na shirin magana suka ji Gidado na kʼokarin budʼe kʼofa,taku dʼaya biyu Jameelah tayi ta sadata kanta da part dʼinta dake tana kusa da kʼofar sabʼanin na Hafsa dake can nesa da inda take,saida Jameelah ta aika mata da gwalo kan ta rufe kʼofar wanda adaidai lokacin ne shi kuma ya sako kai ya shigo,

Kallonsa ya sauka akan Hafsah rai amatukʼar bʼace yace"Hafsah da gani zamu samu matsala ni dake,wato ke bazan baki umarni kibi bako sai abunda ranki yaso shine zakiyi right?ga yarʼuwarki nan ita tabi maganata ta wuce bʼangarenta ammh dake ke dʼin fitinanniya ce mara kunya mai neman rigima shiyasa kika nunan cewa ke kin isa...ʼʼ

Azuciye tace"Ita da kake yabonta ai yanzu itama ta shige aguje data jiyo motsinka....ʼʼ

    "Tunda har ban sameta anan dʼin badai ai shikenan,kuma ni tsoron data ji ta gudun ya burgeni sbd ta gujewa bʼacin raina ne ammh dake ke baki damu ba shiyasa kikayi tsayuwarki bbu alamun tsoron,,kinga ni karbi kazar da kike tawa mutane hauka da balli akanta...ʼʼ ya fadʼi yana mikʼa mata,fusgewa tayi sannan ta juya zuwa part dʼinta tana rusar kuka,yabita da kallon ina da aiki sosai agabana,ya latso Jameelah yace ta fito ta kʼarbi tata kazar,koda ta fito bata bari sun hadʼa idanu dashi ba ta kʼarba tare da godia sannan ta koma ciki,

  Kai tsaye part dʼin Hafsan ya nufa ya tarar da ita kwance saman gado tana rusar kuka,ledar kazar kuma tayi jifa dashi har yakai can kʼarshen gadon,sai yaji duk ta bashi tausayi ammah be nuna mata hakan ba yayi tubʼewarsa ya shige bandakʼi don watso ruwa,bayan ya gama ya dauro alwalarsa ya fito,,abun mamaki sai ganinta yayi tana yagar kazar tana korawa da lemur,da gani ta canza shawara daga baya kenan,kala bece mata ba har ta gama tayi gyatsa,anan ta mikʼe akʼasa ta bingire da bacci,yaso ya tada ita ta dauro alwala su gabatar da sallah ammh kuma sai ya kʼyale kawai,,can ya dakkota ya kwantar asaman gado tare da lullubʼa mata bargo sannan ya koma saman doguwar kujera ya kwanta bayan ya kashe musu wuta,wayarsa ya jawo ya shiga neman Jameelah awaya ammh be sameta ba,haka ya haqura ya rungume hannayensa saman kʼirji,,bbu jimawa wani nannauyar bacci yayi awon gaba dashi shima,itama Jameelar anata bʼangaren sai data ci kukanta kafin bacci ya kwasheta,,tata kazar kuwa ah fridge dʼin dakinta ta jefashi don bata cikin mood dʼin cinsa...

    Asuba nayi shine ya soma tashiwa ita kuwa gimbiyar tana nan kwance tana sharar baccinta hankali kwance,ga wani irin munsharin da take jaa wanda ko kadan bayaso,matsawa kusa da gadon yayi yasa hannu ya tabʼota,yaci saʼa ta budʼe ido yace"ki tashi kiyi sallah asuba tayi...ʼʼ tsaki taja ta juya masa baya ta cigaba da baccinta,kwafa yayi yace"Karki sake in dawo in tarar baki daga ba...ʼʼ yana gama jawabinsa ya kadʼa kai ya fice daga dakin zuwa part dʼin Jameelah don itama ya tayar da ita duk da cewa ya tabbata ta daga don bata wasa da ibadah,

  Ah bathroom ya tarar da ita tana daura alwala sai shima ya shige don suyi tare,ko kallonsa batayi ba har ta gama sabʼanin shi da yake ta jifanta da murmushi,shine ya jasu sallar kuma yaso ne su hadʼu duka ah babban falo har Hafsan sannan ya jasu sallar ammh yasan in har Hafsan daya sani ne tou kuwa bata daga ba kuma bayason ta bʼata musu lokaci shiyasa kawai ya jasu sallar,bayan sun idar ya jawota jikinsa ganin bata da niyyar gaidashi yace"Haba hearthrobe yau ko dʼan annurin fuskarki bazan samu bane balle akai ga batun gaisuwa?ʼʼ bata kai ga bashi amsa ba sai ji sukai wayarta ta dauki kidʼa,shine ya tashi da kansa ya dakko mata,cike da mamaki yake fadʼin"Meya faru kuma da maman su Kasim ke kʼiranki da wannan asubancin?ʼʼ  [yana nufin matar Baba Munniru]

   Wuf! ta mikʼe itama dauke da mamaki da tsoro akan fuskarta tace cikin rawar murya"Anya lafiyaa kuwa?ʼʼ

    "Dauka dai muji...ʼʼ ya furta yana mikʼa mata wayar,tasa hannu ta kʼarba jiki na rawa tare da danna receive tace"Assalamu alaykum Momy barka da asubanci.........!ʼʼ

  _*Kash!kuyi haquri na yanke muku jindadi ammh duk salon ne yazo da hakan,tofa meyasa momy take kʼiran Jameelah ah irin wannan lokacin?*_

_*Ga Gidado nan dai da matayensa,da mai 'KISHIN JAHILCI' da kuma mai KISHIN ILMI' ...koya zata kʼaya? muje dai zuwa*_

_Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

07065481260..Ko kuma 09069067488

_*#HAFNANCY_LURF💓*_
_*#KISHIN_MATA*_
_*#2020_NOVEL*_
_*#SALO_NA_DABAN*_
_*IWA🖊*_

  

Czytaj Dalej

To Też Polubisz

242K 1.1K 36
Warning - Extremely erotic and sexual. People below 18 might find it disturbing. Suggestion to my readers - Visualize everything! Description - I am...
3M 192K 89
What will happen when an innocent girl gets trapped in the clutches of a devil mafia? This is the story of Rishabh and Anokhi. Anokhi's life is as...
311K 25.3K 15
MY Creditor Side Story ပါ။ Parallel Universe သဘောမျိုးပြန်ပြီး Creation လုပ်ထားတာမို့ main story နဲ့ မသက်ဆိုင်ပဲ အရင် character ကို ရသအသစ် တစ်မျိုးနဲ...
424K 23.7K 17
𝐒𝐡𝐢𝐯𝐚𝐧𝐲𝐚 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 𝐱 𝐑𝐮𝐝𝐫𝐚𝐤𝐬𝐡 𝐑𝐚𝐣𝐩𝐮𝐭 ~By 𝐊𝐚𝐣𝐮ꨄ︎...