KISHIN MATA

By Hafnancy01

2.3K 27 6

"Don girman Allah Suleiman karka sakeni,ka tuna fa igiya ɗaya ce ta saura atsakanina dakai,ka tausayamun kark... More

1
BABI NA UKU
BABI NA HUDU
BABI NA BIYAR
BABI NA SHIDDA
BABI NA BAKWAI
BABI NA TAKWAS
BABI NA TARA

2

246 1 0
By Hafnancy01

*KISHIN MATA🍃🍃*
               🍃🍃🍃
         _mai dauke da salo na daban🤙..!_

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى  ASSɷ*✍

   *NA*

         _*HAFNANCY LURF💕*_
           _*[Hafseesee]*_

_*💫Dedicated to:-Anti Bahijjata & Grandma Zm Chubado*_
   
*#An_Intense_Jealousy_Story*
*#Love#fiction*
_•Copy cats ar advised not to transform diz publication by any means_

_#In this article, we will investigate what is going on in the minds of men who seek to marry more than one wife. What are their views on the matter? We also want to know what their wives think about their husbands’ looking to marry again_

         _*💫BABI NA BIYU…✌*_

___________★Akan idon Gidado motoci suka tashi kuma duk yana kallon irin gudun gangancin da Jameelah takeyi da mota asaman kwalta,ahankali ya furta''ke kuwa Jameelah salon naki kishin kenan?tou Allah ya kyauta...!'' komawa yayi inda yabar wasu abokan aikinsa wa'enda basu samu zuwa daurin aure ba shine sukazo tayashi murna da yammacin nan,wasu acikinsu sai cewa suke matarsa ta burgesu ayayin da wasu ke cewa suna tsoro kar tayi fuckup cuz mayb she's upto something freakish,murmushin yake kawai Gidado yayi tare da cije kakkauran lips dinsa yace''I trust my wife bazata ta6a bani kunya ba...!'' daga kafadu sukai suna fadin''Tou Allah yasa,fatanmu dai Allah ya baku zaman lfy dukah..''

Ameen shine abunda ya amsa da kana suka sallameshi shi kuma yayi musu rakiya wajen motocinsu,bayan wucewarsu ne ya koma ciki sai part din mahaifiyarsa *'Yumma'*

Ya cimma jama'a sun dan ragu ah part dinta,tsirarun mutane ne kawai ke zaune ah katafaran falon mai alfarma,bayan ya gaishesu ya wuce dakin Yumma direct,da sallama abakinsa ya shiga cikin dakin,Yumma ce kawai ta iya amsawa don ita da Ramlah kanwarsa ne kadai adakin,fad'a take mata sosai akan cin zarafin Jameelah da tayi acikin jama'a,ita kuwa Ramlar sai kuka take kaman zata hadiye zuciya ta mutu,Yummah na ganinsa ta yanke fadarta bayan ta amsa mishi sallamar,itama Ramlar shiru tayi da kukanta kamar anyi ruwa an dauke,tsit kakeji don mugun tsoronsa take kamar wani mala'ikan mutuwa,

Idonsa k'yam akan Ramlah wacce sai faman ajiyar zuciya take ta saukewa ajere,tun kafin ya karasa wajensu ya doka mata wani irin gigitacciyar tsawa''K…! maza knees down tun kafin na karaso wajen na tattakaki awajen stupid gal kawai...!'' ya fadi da jajayen ido,ai tuni ta zamo daga kan gado jiki na rawa takai gwiwowinta kasa kamar yadda ya umarta,yana isa gareta beyi wata wata ba ya daga hannu zai sharara mata mari,da sauri Yumma ta daga hannu ta tareshi,cike da dacin rai tace''Haba Gidado meye haka ne wai kke kokarin yi?wai kai meyasa idan ranka ya 6aci sai ka nemi ka fita cikin hayyacinka ka koma tamk'ar mahaukaci ne?ni nasan abunda kake wa zafin ran ammh ai yakamata ka dakata tunda ka cimma ina mata fad'a ne,,mutumin banza kawai mtssss...!''

Cike da mmki yake nuna Ramlah yace''Ya rabbi…! Yumma yanzu agaban mara kunyar yarinyar nan ne kike zagina salon ta kara rainani...?'' saurin taran numfashinsa tayi''Kai kana da kunyar ne?ba agabana kke kokarin jibgarta ba?dake kai baka da ta ido dukan d'a agaban idon iyayensa,tou wlh kar inji kuma kar in gani ka sake dukan Ramlah agidan nan,karshe ma daga daketa sai data kwanta jinya dake kai baka da imani ko kadan.....!''

Maganarta ta karshe ya kara fusatashi yace''Ai wlhy bata ma kwanta jinya dakyau ba har sai naga na fasa jikinta da belt tukun idan har bata fita aharkar matata ba,ga matar dan'uwanta nan Azeema da kuma yar'uwarta Surayyah cikinsu duk bbu wanda ya haihu ammh dake tawa matar ta raina shiyasa take takata son ranta kuma ana gani ayi shiru,tou wlh Yumma ki gargadeta bazan sake daukan wannan rainin da wulaqanci ba,ni kowa ya fita daga harkan matata,tunda dai kunsa na qaro wani auran zamu gani ai ko ita din zata haihun ammh adai cin zarafin Jameelah banaso.....!''

Ji kke tatatasssss Yumma ta kwasheshi da wani irin mahaukacin mari,,muryarta na rawa tace''wallahi suleiman ka fita daga cikin idona in rufe,lallai ashe rashin kunyar taka ba'a kan Tsoho kawai ya tsaya ba har yana neman shafarmu mu iyayenka?ai kuwa da sakel ya zama dole na dau kwakkwaran mataki akai,,maza fitar mun ah daki kafin raina ya karasa jagulewa...!''

Cike da tsantsar mmki yake kallonta hannunsa rike da kumatunsa inda yasha wawan marin,,

   ''Ko bakaji abunda na fada bane?I said getttt outttt...'' ta sake fadi cikin hargowa tare da nuna masa hanyar kofa,da sauri yayi waje gudun kar ta tara musu jama'a....

Shidai yau yaga rayuwa,ayau ya karbi zafafan marin mutane biyu na Baba Munniru da kuma na mahaifiyarsa abunda wani acikin zuri'ar bai ta6a gigin masa ba kenan kuma duk akan yana fad'ar gaskiyarsa?shi bama wai don tursasashi da sukayi kan ya qaro aure bane ke soya ransa ba kamar yadda aka matsawa matarsa Jameelah,anbi an tsangwameta da rashin haihuwa bayan ga matar dan'uwansa mustapha yana nufin Azeema ko 6atan wata itama bata ta6a yi ba,haka ma k'anwarsa Surayya dake aure ah kaduna duk ba'a saka musu ido ba sai shi??tou meyasa?amanta da batun Surayya tunda gidan wani take,shi mustaphan meyasa baa takurashi da tasa matar ba sai shi?Tsoho bai ta6a bada shawarar wai mustapha ya karo aure ba sai shi harma yana ikrarin har ta uku sai yyi idan wannan da zata shigo itama tazo bata haihu ba,wai kuma Tsoho ya kira hakan da So?wani irin so kenan ana takura rayuwar mutum shiba karamin yaro ba?at 37 yakamata ace an fita daga harkarsa ai ya tsara rayuwarsa yadda yakeso,,shi abinda yafi daure masa kai ma be wuce yadda su ukun nan wa'enda ke ciki daya suka kasa haihuwa ba,shi,Mustapha da Surayya,ita Ramlar ce auta kuma batayi auran ba,ansan iko sai Allah ammh gsky abun da mmki ace duk matayensu ko 6atan wata bata ta6a yi ba haka ma kanwarsu Surayya,ita kanta tana fuskantar tsangwama da kyara acan dangin mijinta,duk wani jikan Tsoho  ah zuri'ar nan wanda yayi aure,matan ne da mazan duk kowa ya haihu ammh tsatson mahaifinsa Alassana bbu wanda yaga gudan jininsa,sai yake zargin kamar akwai wani lauje cikin nadi ammh bayason ya daura zargin akan kowa,don zato zunubi koda ya kasance gaskia,,zai dai cigaba da kaiwa rabbi kukansu don yasan abun na damun iyayensa ba kadan ba shiyasa Yumma wasu lokutan takan huce haushin akan ko wanene idan an 6ata mata rai,tai ta fad'a akan abun da bai taka kara ya karya ba,kuma duk yasan abu na cinta ne arai ammh ta kasa bayyanawa,ajiyar zuciya ya saukar sannan ya nufi part din Hajju don ita kadaice kurum zata iya saukar masa hankali ahalin yanzu,,shaquwa na musamman ne ke tsakaninsu,ko kadan bata mashi kallon d'an kishiya,ji take tamk'ar ita ta haifeshi da cikinta,gashi kuma Allah bai ta6a bata haihuwan ba itama...!

   Bayan fitarshi Yumma ta zauna agefen gado tare da dafe kanta dake barazanar fashewa tsabar ciwon kai,dkyar ta iya duban Ramlah dake shesshek'a ta doka mata tsawa tace''Kema tashi ki fitar mun adaki kafin na huce haushin akanki..!'' da sauri ta mik'e jiki na rawa ammh taki motsawa sai kokarin 6ata hakuri take,

''Ramlatu...! nace ki bace mun daga gani ko?wlh idan baku dena 6atamun rai keda wanki ba tou na rantse da Allah bazaku sake ganin sakin fuska awajena ba tunda ku din ba 'ya'yan mutunci bane...! ta furta cikin tsananin fushi...

''Yumma don Allah kiyi hakuri bazan sake ba...!'' ta fad'a with a breaking voice,wani wawan kallo Yummar ta watsa mata,da sauri ta fice tabar mata dakin,,,fitarta keda wuya Yumma ta rushe da kuka tare da zu6ewa saman gado,hakika tana jin zafin rashin haihuwan 'ya'yanta uku,Gidado,Mustapha da kuma Surayyah,tasan tabbas ba hakanan kawai aka barsu ba,akwai lauje cikin nadi,ammh kuma yadda zuri'ar nan take da yawa tou waye zata dora ayar tambaya akansa?zata dai cigaba da kaiwa Allah kukanta don shine kadai yasan gaskia kuma da karfin mulkinsa zai magance matsalar insha Allah....!

Cikin karyayyen murya wanda ya cakud'e da kuka tace''Zuri'ar Tsoho why??ni Ummerherny meh na muku ne wanda har yasa kuka huce haushin akan 'ya'yana?how can three of my children unable to conceive?such isnt possible....!'' ta furta tana share hawaye gami da jan majina kan ta cigaba''Akwai sa hannun wani acikin wannan al'amarin ammh ni Ummerherny na barwa Allah komi don shine zai mana maganinsa,,Allah ya saka muku Suleiman...!'' ta sake rushewa da kuka,ji tayi Goggo Boddiya na tunkaro dakin tana kwala mata kira,da sauri ta mike ta shige bandaki ta wanke fuska gudun karta gano taci kuka........

     ★__________★

      _*★THREE ARMS ZONE,ABUJA*_

Sagir best frnd na Gidado shine yayi kokarin shan gaban motar Jameelah yana mata magana''Haba..! Haj.Jami kibi ahankali mana,menene amfanin tseren motar?''

     Tsoki tajah ba tare data tankashi ba ta kara gudun motar,na gefensa Suraj yace''Ammh lallai na yadda da maganar mutane da suke cewa wai rikicin duniya da mai rai ake,nifa ban ta6a ganin mace irin wannan bafa?wai da ita zaaje dakko kishiyarta shi kuma Gidadon ya daure mata gindi bbu jan ido,anya Sagir baka ganin cewa diz woman is upto something stupid?

    ''Ni kaina abun ya dad'e yana bani mmki abokina ammh ai zamu gani,,ni bbu abunda ma yake bani haushi kamar gudun da take da mota sai kace ma tasan gdnsu amaryar ne,,aff! nafa manta cewa Allah ya kawomu zamani,karka sha mmki ma tafi shi gogan sanin kan gidan,,kasan wasu matan da zarar sunji za'a musu kishiya sai kaga sun soma shige da fice suna binciken gidan dayake neman auran,,gashi dai mun shigo 3 arms zone and she's the one leading us sai mu cigaba da bibiyarta....'' Sagir ya ida maganarsa yana shafa gashin bakinsa,hannunsa daya kan sitiyari,Suraj dai ya kurawa bayan motarta ido ne yana kallon abun al'ajabi...!

     

     __________★

   ''Jameelah don girman Allah ki rage gudun motar nan pls kar ki jawo mana accident,shin wannan wani irin zafin kishi ne haka?donna tabbata duk haukan nan acikin salon naki *'KISHIN'* ne....'' Azeema ta ida maganarta cike da zafin rai,,Jameelah bata saurareta ba har sai data isa ga gate din wani madaidaicin gida,,ji kke kiiiiiiiiii taja wani wawan burkin daya tada kura wanda hakan ya janyo hankulan yara dake wasa ah kofar gidan,ihun murna suka fasa ah sa'ilin da suka tabbatarwa kansu da cewa yan daukan amarya ne suka iso sbd jerin kwanon motocin da suka hango can nesa suna tahowa well organized abayan na Jameelar,da gudu sukayi cikin gida don bada sanarwa,cike da mmki Azeema tace''Jameelah dama kinsan gidan ne?wlh duk azatona sunan unguwar kawai kika sani ashe hatta kofar gidan kin sani,haba shiyasa naga ko jiransu Sagir bakiyi ba kiketa sharara uban gudu....''

Da jajayen idanu Jameelah ta dubi Azeema har saida Azeemar ta tsorata da yanayinta,''Menene ma ban sani ba akan Hafsa?inajin kawai yadda tayi rayuwa acikin mahaifiyarta kafin ta fad'o duniya ne kawai ban sani ba,Azeema kar kiyi mmki idan nace miki nasan abubuwa da dama akanta wanda shi Gidado be sani ba.....'' dan dakatawa tayi tare da sanya yatsa tana dauke guntun hawayenta,ita ko Azeema sake baki tayi tana binta da kallon mmki,ta cigaba''Azeema an gaya miki kishiya abar wasa ce?ki gode Allah ke ba'a wani takura miki kamar yadda ni aka tasani gaba acikin wannan fitinanniyar zuri'ar,Azeema ko kadan ban ta6a nadamar auren Gidado ba ammh ina meh cike da takaicin shigowa Zuri'a irin wannan,,Azeema rashin haihuwar ma ni bata wani dameni ba kamar yadda nake jin zafin yadda zan hada miji da wata gidahuma can,ayau Gidadona na shirin raba zuciyarsa da kuma gangar jikinsa gida biyu yamallakawa wata bayan ya tabbatawar dunia cewa shi din mallakin Jameelah ce ita daya,,,sister Azeema am sorry to say banajin zan iya cigaba da danne zuciyata salon na yiwa kaina illa,it's time to show dem the real me.....!'' ta ida maganarta tare da bugan sitiyari tana meh fashewa da kuka mai tsuma zuciya,sosai Azeema ta tausaya mata hadda er kwallarta,tace''Sister Jameelah pls dnt fall my hands,don Allah take it easy,,bani son ki kasance cikin sahun mata masu tafiyar da rayuwarsu akan *'KISHIN JAHILCI'* wlhy yadda kke da ajin nan kamata yayi ki tafiyar da rayuwarki akan *'KISHIN ILIMI'* ....

Sagir ne ya katse musu hirarsu ta hanyar kwankwasa motar,da sauri suka fito idanunsa ya sauka kan wasu tsirarun mutanen da suka fito lek'en en daukan amaryar,Sagir yace''Haj.jami aganina da kin koma cikin motar kinyi zamanki idan yaso su Goggo Karime tunda sune manya sai su shiga su fito mana da amaryar ammh motar taki din dai zata shiga...'' kallon uku saura kwata ta wulla masa kan tace''Amaryarka ko tamu?'' kallon ban fahimceki ba yay mata,,gane nufinsa yasa tajah dogon tsoki tana fadin''Dallah malam bani wuri in wuce sai shegen shisshigin da bbu kwarjini...!'' tajah hannun Azeema suka nufi gate din gdn,,Suraj yayi hissing cike da haushinta yace''Diz woman is an animal wlh,wai meye haka take yi ne wai don Allah?wani irin kishi ne haka?sai ka kira salandon mijin nata kace masa taki jin maganarmu...'' [dake dama shine ya basu umarnin su dakatar da ita karsu bari ta shiga gidan idan ankai],

Aiko tun kafin Sagir yakai ga latsoshi sai ganin call dinsa yay yana shigowa,da sauri ya danna receive ya kora masa bayani,hannu yasa akai yana shafawa tare da cije lips yace''Allow her,,idan har akwai sauran yadda da aminci tsakanina da matata Jameelah tou nasan she wont try doing anyting stupid kawai kokarin daga hankulanmu take....!'' ya fad'a not fully sure of himself,,ta6e baki sagir yay kawai yace''Toh Allah yasa...''

     Sai safa da marwa yake yi adakin Hajju,duk abun duniya sun taru sun masa yawa,ina ne zai soma dafawa?yana cikin wannan halin kuncin ne sai ga Hajju ta fito wanka,she was shocked to see me in tears,yana ganinta yayi saurin isa gareta ya rungumeta tare da fashewa da kuka yace''Hajju zuciyata namun zafi sosaii,,ina zan saka raina inji sanyi ne?" Cike da tausayinsa ta shiga bubbuga bayansa take fadin''Haba d'ana dena wannan kukan share hawayenka ba'a san dan sanda da kuka bafa,da jarumtaka akasanshi,,nasan da damuwarka ammah ka sani bbu abunda zan iya yi akai illa tayaka da du'a'i,ka gayawa Allah damuwarka don shine zaiyi maka maganin komi...!'' jan hannunsa tayi ta zaunar agefen gado sannan taje ta dauki kofi tadan dibi ruwa kadan aciki ta zauna ta shiga zuba addu'o'i tana tofawa aciki har dai ta kammallah sannan ta bashi yasha,nan da nan yaji wani irin dadadar sanyi ya mamaye masa zuciya,haka take masa akodayaushe idan yana cikin kunci,sai tayi masa tofi ta bashi yasha sannan ransa ke sanyi,,sallama yay mata sannan ya fita,ita kuma ta hau shiri don tarbar amarya,,akwai wani al'ada acikin wannan Zuri'ar,,wato duk matar da aka kawo aure gidan,Tsoho ne ke fara sanya mata albarka kana akaita wajen Hajju ta sanya mata tata albarkar kafin sauran,Hajju takan jika magani aruwa irin tamu dai ta gargajiya sannan ta bawa amarya tasha,yin hakan wai kariya ne agareta da kuma tsareta daga mugun nufin wani,,haka ma idan ya'ya mata zasu fita agidan wato zasu je aure,suma din takan basu *'RUWAN KWARYA'* kamar yadda ake kiransa susha don kariya agaresu,bbu wata wacce ta shigo ko ta fita da zaace ta tsallake wannan al'adar..............

     _*Tofa! muje zuwa muga ko akwai wacce zata iya tsallakewa nan gaba?muddin kuma wannan din ta tsallake aganina tana iya 6ata komi,,juz guessing oowh😄*_

_Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

07065481260..Ko kuma 09069067488

_*#HAFNANCY_LURF💓*_
_*#KISHIN_MATA*_
_*#2020_NOVEL*_
_*#SALO_NA_DABAN*_
_*IWA🖊*_

Continue Reading

You'll Also Like

1M 24.2K 42
Limited Time Only: Binge this series for a chance to win FREE coins until June 2! Read 10+ chapters of this story and win 30 Coins (2000 Winners) Whi...
1.8M 137K 62
"ရှင်သန်ခြင်းနဲ့သေဆုံးခြင်းကြား အလွှာပါးပါးလေးကိုဖြတ်ကျော်ခါနီးမှာမှ ငါမောင့်ကိုစွန့်လွှတ်တတ်ဖို့ သင်ယူနိုင်ခဲ့တယ်၊ လူတွေက သံသရာမှာ ရေစက်ရယ်၊ဝဋ်ကြွေး...
2.8M 186K 89
What will happen when an innocent girl gets trapped in the clutches of a devil mafia? This is the story of Rishabh and Anokhi. Anokhi's life is as...
285K 850 10
Fun wlw sex. Different kinks and stuff, all about trying things. May even include potential plot lines and will definitely include some form after ca...