Assalamu alaikum. This is a late update because my little one wouldn't just let me look at the computer 😀Allah bless him.
But he is finally asleep and here we are, better late than never they say, right?
We have been on number 10 on the romance category and I have you to thank. Please keep voting, and sharing. 😘😘don't forget to also place your comments. I love hearing from you.
Asiya ta kura wa makeken akwatin da ke kan gadon ta idanu, ta gagara cewa uffan. Muhibbat ta kwashe duk wata suturar da ta fada idanun ta.
“Muhi, tafiyar ta kwana bakwai ce, ba ta barin garin ba.” Ta furta, a kokarin ta na hana ta kara zuba wasu. Zallan kayan matsu ne da tsuku irin na turawa. Atamfa da leshi bas u wuce kwaya hudu ba. Kuma su ta fi saba sakawa.
“Mece ce matsalar a nan? A kan ki za ki dauka har can, ko kuwa?” Muhibbat ta tambaya a lokacin da ta ke kara lafta kayan barci kala kala a kan wadan da ke akwati.
“Matsalar a nan, su Ummah za su dauka kin zo ne ki sace ni. Ji fa yadda ki ke kara lodin kaya. Sai ka ce wacce za ta rika canjin kaya kowane bayan awa?”
“Ya na da kyau ki san muhimmancin honeymoon a rayuwar aure, tun da Allah Ya sa kin samu damar samun hakan.”
Duk da sanin cewa Muhibbat ce kadai a wajen, sai da kunya ta dan kamata. Ta shiga kame-kame, “Ba fa wani abu ba ne. Rakiya kawai zan yi.”
“Mijin ki zai dauke ki zuwa wani waje, ba kuma tare da Amatullah ba. Ki kira shi yadda kika ga dama, amma mu nan, honeymoon za mu kira.”
Ta ci gaba da lafta kaya har da na barci kala kala. Kunya duk ta ishi Asiya. Me Yusuf zai ce idan ya ga kayan nan? Yaya za ta yi ne da Muhibbat? Don kuwa ta san ba za ta saurare ta ba duk yin ta. Haka Allah Ya yi ta, idan ta saka su a gaban ta, to fa sai ta aiwatar. Sai ko wani ikon Allah. Idan kuwa ta ki abu, to fa ta ki shi ke nan.
Ta nisa. Muhibbat ta ki fada ma ta yadda suka yi da Dokta Hadi. Amma ta san dai har a lokacin ba ta gam aba da kai ba bori ya hau. Saboda ita Muhibbat ce, ko za ta amince da shi, sai ya dan wahala. A halin yanzu dai bau wanda ya san gobe. Ta da ice wa Asiya, a taya ta addu’a, idan alheri ne to Allah Ya tabbatar; idan kuma babu alheri, to Allah Ya canja da abin da ya fi shi alheri.
Muhibbat ta zuba kayan kwalliya ma su yawan gaske, wanda Asiya ba ta san amfanin fiye da rabin su ba. Ta zuba turarruka ma su kamshi irin na Larabawa da na Turawa.
“Turare abu ne mai taimakawa wajen dauke hankalin namiji, ya kuma zuba masa sha’awa. Wajibi ne a kan ki, ki ja hankalin sa zuwa gare ki. Kin san ba za a rasa turawa a can Yankari ba. Kar ki sake ya karkata zuwa gare su.”
Asiya ta dan so ta yi dariya, “To Anty Muhi.” Amma a can kwaryar zuciyar ta, taraddadi da zumudi sun mamaye zuciyar ta. Da gaske ne, wannan ne karo na farko da za ta taba yin irin wannan kebantar da namiji, wanda kuma ya kasance mijin ta ne.
Ya kamata a ce ta tabbatar da ba zai manta da wannan rakiyar da za ta ma sa ba. Sai dai ba ta san yadda za ta yi ba. Za ta bari ne kawai komai ya bi yadda ya dace ya bi ba tare da tsananta wa kan ta ba.
Bayan azahar Yusuf ya dawo daga asibiti, kafin nan ya sa Bature ya mayar da Muhibbat.
Ta ji dadin hakan, amma ta shiga kadaici da kewa. Ta dan koma wajen Umma ta yi mata ‘yar kwalema zuwa lokacin da Sara ta iso. Ta yi ma ta bayanin cewar Yusuf ne ya nemi ta je don tallafa ma ta wajen kimtsa gidan kafin su bar garin.
Ta san ba wai don gazawar ta bane ya sa shi hakan, don ko ita da Larai bai fi karfin su ba. Sai don ita ma ta rage mu su kadaici kafin su tafi. Tare suka kimtsa kicin, sannan suka koma dakin Asiyar, wurin da take tambayar ta yadda a ke shafa kayayyakin adon fuskar nan da Muhibbat ta zuba ma ta su cikin akwati.
Sara mai son caba ado ce. Ko da dama ta samu gare ta, sai kawai ta shiga yin bayani ta na nuna mata a zahiri ta hanyar yi ma ta a fuska. Ta nuna mata su eye shadow prima, foundation, da sauran su. Har ma da koya mata zana gira mai adda. Lokacin da ta gama ta nuna ma ta madubi a gabanta.
“Ki ga yadda ki ka sha kyau, masha Allah Tabarakallah.”
Asiya dai murmushi kawai ta yi, ta na neman wurin da fuskar ta ta shiga. Ta san dai ta na karkashin wannan hodar da sauran jagbe-jagben da a ka shafa ma ta.
A lokacin Yusuf ya leko, “An gama?”
Asiya kusan ta gagara numfashi ganin irin shigar sa ta wando jeans da shat mai launin sararin samaniya. Kayan sun karbe shi, sun mayar da shi saurayi dan shekara sha biyar.
Ta zuki numfashi, lokacin da ya jefa ma ta wani irin kallo. Ita ma ta gagara kawar da nata idanun daga nasa. Gaba daya duniya ta tsaya cik. Yusuf ya mamaye zuciyar ta. Dan gusawar da ya yi ma tayi kewar sa fiye da zaton ta. Mata nawa ne ke yin sa’a irin nata a duniya?
“An gama Yaya. Saura tafiya.”
A lokacin ne Asiya ta sunkuyar da kai kasa, ta na mai jin kunya sosai. Sarah ta fita daga dakin da kayan ta, ta bar Yusuf tsaye a bakin kofa. Sai da ba sa jin motsin ta, ya mika mata hannun sa, idanun sa na rokon ta same shi wurin da ya ke.
A hankali ta tashi zuwa gare shi, Ta dora hannun ta cikin nasa, shi kuma ya rike gam-gam. Ya ja ta zuwa jikin sa a hankali. A lokacin rudani da zogin zuci sun hana ma ta wani tunani. Kamshin sa kawai ke kara birkita kwakwalwar ta.
Ya sauke muryar sa sosai, ya koma ga rada-rada, ya ce, “Kin kawo min farin ciki sosai cikin rayuwa ta Asiya. Kamar ne a ce mutum ne daga duhu ya koma haske. In Allah Ya yarda, daga yau zan dandana mi ki kwatancin farin cikin da ki ka saka ni ciki. Zan shayar da ke daga tabkin kaunar ki.”
Ya ja hannun ta ya dora bisa kirjinsa, ta na iya jin motsin bugun zuciyar sa, a yayin da idaniyar sa ke nuna buguwar so da kauna cikin su, “Yau zan gwada mi ki cewa kowane bugun wannan zuciya tawa da sunan ki ta ke yi.
Babu wa ta cikin zuciyar, sai ke.”
Asiya ta rude, rudanin ya wuce kwatance. Ga kunyar da ta matsa ma ta tuntuni. Ashe haka so ya ke? Ashe haka kauna ta ke? Ba ta taba sanin dadin sa ba, sai yanzu.
Ta na da bukatar yi ma sa magana, don haka ta daure zuciyar ta, ta ce, “In Allah Ya yarda, daga yau zan zama abar alfaharin ka. Zan yi ma ka biyayya bisa zallar so da kauna. Don hakika, yau na tabbatar Allah ya min baiwa, da Ya mallaka min kai, da son ka, da Ummah, da Amatullah. Alhamdullilahi, burina yau ya cika. Na fi son ka kwantar da hankalin ka, domin a yau, ka yi dace da matar da ta ke son ka, ta ke kaunar ka, wadda duk duniyar nan ba za a samu wacce ke ma ka irin son da na ke ma ka ba. Har abada...”
Irin sautin dariyar sa ta kara jefa ta cikin shaukin kaunar sa, wanda ya kara tabbatar ma ta da kalaman ta. Lallai ba za a samu mai son sa ba kamar ta.
Ba yanzu ba, har abada. Ta fara ne da yin aure domin Amatullah. Yanzu tana son zaman aure ne domin Allah, da kuma bin umarnin manzonmu(SAW), tare da yin biyayya ga yusuf, da kuma nuna masa dimbin kauna.
“Mu je mu salami Ummah.”
Kanta a manne ya ke da kirjin sa, ta na jin sautin bugun zuciyar sa, wanda yayi daidai da na ta. Tunanin cewa karo na farko tun shigar ta gidan da zata fita, ta bar Amatullah da Ummah ya fado ma ta. Ta yay a za ta kalli Ummah ta sallame ta? Ta yay a za ta fara rabuwa da diyar ta har na tsawon kwanaki bakwai?
Har a lokacin bai mots aba, amma ya ci gaba da cewa, “Mu je wajen Amatullah mu lallabe ta don kar ta yi kewar mu sosai. After all, mu na burin kawo ma ta babban tsaraba ne bayan mun dawo.”
Ta dan kalle shi, “Tsarabar me?”
Ya yi murmushi, “Tsarabar ‘yan biyu mana, kannen ta. Har kin manta?”
Ta sake manne kanta da kirjin sa, kunya da farin ciki su ka cike zuciyar ta. Hakika, za ta so a ce ta samu hakan, ta samu wannan farin cikin a rayuwar ta.
“Yaya ku mu ke ta jira a waje, tun dazu. Ko kun fasa tafiyar ne?”
Muryar Sara kawai su ka ji, ba su ganta ba. Ga alama ta gan su ne, ta makale a lungu ta na daga muryar ta. Hakan ya kara saka ta jin kunya sosai.
Ta yi sauri ta janye daga jikin sa, ta nufi sashen Ummah, ta wuce Sara, wacce ke ta yin ‘yar dariya. Ita kuma ta kusa yin tuntube don tsananin kunya.
Sun bar gidan misalin biyar da rabi na yamma, bayan sun yi sallama wa kowa. Su na tafe su na daga hannaye wa junan su. Asiya na kallon Amatullah ta mudubi, wacce Sara ke daga ‘yan dugwuin hannun ta a matsayin bankwana. Za ta yi kewar ta sosai.
Yusuf ya dafe tafin hannun ta ya rike. Hannun sa ya cinye na ta wajen girma, ta dan kale shi, ya yi ma ta murmushi. Nan ta ji haske ya cike zuciyar ta.
Tabbas! Ta kara tabbatar da cewa ba kowace mace ba ce a duniyar nan ta yi sa’a kamar yadda ta yi. Ita ma ta mayar ma sa da murmushin a kunyace, sannan ta gyara zaman ta a motar, ta na kara yiwa Allah godiya!
* * *
Gidan a cike yake da mutane, maza da mata. Babban falon cike da mazaje, mata kuma suna bangaren da Dokta ya wae wa Asiya don taba bakin ta a duk lokacin da suka je. Hatta sashen Umma a cike yake da yawan ma su shiga da fita wadan da yawancin su kawayen ta ne da ‘ya’ya ko jikokin su.
Har da ma’aikatan Asibitin Sauki sun halarci gidan Dokta Yusuf Haruna a wannan rana, don ta ya Asiya da Yusuf murnar samun ci gaba, na matsayin Chief Medical Director wato CMD na Asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke garin Bauchi.
Duk da dai ba babban alo ko shagali su ka shirya ba, an yi tanadin ciye-ciye da lashe-lashe don tarbar ma su zuwa taya murna. Matan abokan Dokta da ma Sara duk sun hallara a kicin, suna ta dorawa su sauke kawai.
Filin ta baya a ka yi tanadi wa yara don su yi wasa, su kuma ci abinci. A can suka baje kolin su, suna ta wasa da tsalle-tsalle a kayan wasan da Yusuf ya tanadar wa Amatullah idan ta girma ta yi wasa da su.
Leshi Asiya ta saka mai launin sararin samaniya, Amatullah kuma ta tsuke cikin kayanta na riga da siket mai kyau designer (Mark and Spencer) cikin wadan da Yusuf ya kawo mata su akwati guda daga Ingila, wata guda da ya wuce.
’Yan kafafuwan ta dugwi-dugwi, ta na dan taka su cikin takalman ta ma su ban sha’awa, da kuma tsada. Sai ihu ta ke yi na murna, ta na sheka dariyar jin dadi. Ita dai kawai ta ga an cika gidan su ana aha, abin ya burge ta.
Kowa maganar ta yake yi irin yadda ta girma cikin koshin lafiya. Asiya ta kara gode wa Allah fiye da kirgen ta. Diyar ta ta kawo misali, domin ta cika shekara daya ke nan da sati biyu da haihuwa.
Amma a duk lokacin da ta gan ta, kammanin Mariya ke kara bayyana a fuskar ta. Wani irin bakin ciki sai ya rungumi zuciyar ta. Da a ce Maree ta na nan, ya ya za ta ji cikin zuciyar ta? Wane irin kumburin dai zuciyar ta zata yi? Sai dai ta riga ta yi watsi da wannan dama tun ranar da ta bace mu su. Har yau ma fa babu duriyar ta.
Amatullah ta je da gudu ta fadi jikin Yusuf, wanda ya daga ta sama ya na jijjiga ta, ita kuma ta na kyalkyatar dariya, ta na ihun. Zuciyar Asiya ta kara sosuwa.
Ya ya ma za a ce wannan yarinyar ta rasa mahafiyar ta bayan kwanaki kadan da haihuwar ta? Anya, Mariya ta na hayyacin ta kuwa a lokacin? Me ta yi tunani ne da har ya sa ta yar da Ama ta gudu ba tare da waiwaye ba?
“Mama.”Ta jiwo muryar Amatullah na ambato. Zuciyar ta ta kara cikewa da farin cikin ganin ita su ke gani a lokacin. Yusuf ya riko ta sun shiga kicin din, ya na mata wasa. Amatullah kuwa sai kara dariya ta ke.
“Mama.”Ta kara ambata tare da mika wa Asiya hannu kan ta dauke ta. Ta sa hannu ta karbe ta, ta na jin zuciyar ta kumbura kamar za ta fashe. Ama kuwa ta rungume ta tare da makalkalewa.
Tun ranar da ta fara jin wannan kalmar daga bakin Ama, zuciyar ta ta yi makil da farin ciki. Tabbas, ba ta yi sadaukarwa a banza ba. Domin duk wani farin ciki na duniya ya na gefe guda, farin cikin zama uwa ya koma gefe guda shi ma sun a takara.
Asiya, babu shakka ta samu kan ta cikin farin ciki marar misaltuwa. Yusuf ya cike zuciyar ta da kaunar sa, ya gwada mata ma’anar soyayya ta yadda ba ta da sauran shakka game da rikon amanar sa. Ta yarda da shi, dari bisa dari. Ta san zai kasance kusa da ita a lokacin da za ta fadi don ya kama ta. Muddin sun a tare, babu abin da zai same ta cikin ikon Allah.
Ba ta shayin nu na ma sa hakan. Shi ma kuma bay a ma ta koron kaunar sa. A halin da a ke ciki ma ta yi nisa a karatun ta na share fagen shiga jami’a. daga wajen sa har Umma, ta samu goyon baya matuka.
A lokacin da mutane su ka tsagaita suka rage abokan sa kawai da matan su, Sadi ya mike ya bayar da sanarwar, “Ya kamata yanzu mai hoton nan ya shigo ya dauke mu, ko ya ya?” Da kan say a kira mai shagon hoto na B Shaggy don ya dauke su hotuna a samu na tarihi.
“Kai ka fiye son daukar hoto.”Hadi ya furta ma sa, “Sai ka ce wani karamin yaro.” Dukkan su sun san halin Sadi ta wannan fannin. Ko dan zama a ka dan yi sai ya dauki hoto. Don haka wayar sa cike ta ke faal da hotuna iri iri. Balle a ce kyamarar sa ta hannu, wanda har biyu ya mallaka.
Sadi ya mayar ma sa martani, “Well, ba zai yi kyau ba a ce kullum mu rika abubuwa kamar manya. Wani lokaci zai yi kyau idan mun dan taba yarintar.” A lokacin mai kyamarar ya shiga falon, ya ci gaba da cewa, “Yauwa, shigo nan ka watsa ma na filasha don Allah. Mu nan yara ne.”
Mai hoto ya yi murmushi, sannan ya shiga shirya yadda kowa zai dauki hoton. Su ka kira matan na su, a ka shiga dauka ta waya da kyamarar hannun ma duk.
Farko kowa dai dai a ka dauke shi. Sai kuma a ka dauki kowane miji da matar sa. Sannan kuma a ka saka Amatullah cikin kowane miji da matan. Daga nan kuma sai su dauka dukan su. An kuma yi zallan maza, da kuma zallan mata.
“Saura Umma.” Asiya ta furta, ta na kallon sa tare da neman y aba da izini wa mai hoton don shiga cikin gidan har sashen Umman. “Zai yi kyau ta yi hoto da kawar ta.”
Yusuf ya gyada kan sa, alamar ya amince, y ace, “Ki je ki sanar ma ta cewa mai hoton na tafe nan da mintuna goma.”
Da sauri ta fita, don kuwa alla-alla take yi ta bar wurin ko ta samu shan iska mai ni’ima. Ta na sane da yawan tsare ta da idanu da Suhaima ke yi tun zuwan su dazu. Suhaima ba ta nuna alamar ta san wani abu game da neman da ke tsakanin mijin ta Hadi da Muhibbat ba.
Ba mamaki, kila Hadin bai fada ma ta ba, kamar yadda y ace, har sais hi da Muhi sun tsayar da Magana mai karfi tukunna. Amma alamu sun nu na, ta san wani abu a kai. Haka kawai Asiya ke jin hakan a jikin ta. Balle ma magana irin wannan ba ta buya.
Hadi mutum ne mai nacin tsiya. Duk kin Muhibbat, sai da ya kutsa sannan ya sha kan ta. A kusan duk karshen mako biyu, sai ya kai ma ta ziyara can Dagauda. A kullum kuma, sai su dade suna soyewa a waya.
Musamman ya sayi waya, ya kai wa Asiya har ma da layin sa, ya roke ta kan ta aika wa Muhibbat din a matsayin ita ce ta saya mata, don gudun gurguwar fahimta daga bangaren Muhi din. An dai yi sa’a ta karba ba tare dacewa komai ba.
Hadi ya fahimci Muhibbat mace ce da mutum zai yi nasarar shiga zuciyar ta ba don burgewar arziki ko nu na isa ba. Sai dai ta tafiyar da rayuwa yadda ya dace, a tsare. Ba mace ba ce mai son kasancewa cikin mafarki ba. Ita mai rike ne da zahiri a bayyane, babu ruwan ta da munafurci, abin da ya ke cikin ta, shi ya ke waje.
Wadan nan dabi’u na ta su ka kara sa Hadi zube wa, wanda ya sa shi yi ma ta kuka da hawaye a wani lokacin da ta nemi su dakata da zancen neman kawai, ya hakura. Abin har tsoro ya ke ba wa Asiya. Wace irin so ne haka, kamar yaron da bai taba soyayya ba?
Lokacin da Asiya ta ke barin falon tare da Amatullah a hannun ta ta na murmushi, ba ta san dalilin da ya sa idanun ta ya hade da na Suhaima ba a karshe.
Suhaimar murmushi ta ke ko kuma yake, amma idanun ta su na bayyana tsananin bacin ran ta. Abin ne da Asiya ke gudu tun farko. Kawai dai komai ya fi karfin ta ne. Sai kuma gyaran Allah.
Ba ta karasa wajen Umman ba, ta jiwo muryar Yusuf, wanda ya nemi ta tsaya. Ya kwala kira wa Sara, kan ta karbi Amatullah ta kai wa Umma, sannan sai da ta bace gaba daya, sai ya ja hannun Asiya zuwa wani dakin da ke gefe, wanda ba sa komai da shi.
Akwai dai tarukucen ababen da ba a amfani da su, kamar kwalayen talabijin din gidan, na home theatre, cooker da na kwan lantarki da sauran su.
Bai bata lokaci ba, ta ji ya rungume ta. A dan dakika biyun da suka bi bayan hakan ita ma ta biye ma sa, ta shagala ta na jin dumin jikin sa mai garwaye da kamshi, sannan ta nutse cikin bugun zuciyar sa. Nan kuma ta yi kokarin zare jikin ta, amma ya kara rike ta gam.
Tsoro da fargaba su ka kama ta, “Me ka ke yi?” ta tambaya idanun ta a zare, ta na kalle-kalle. Su kadai ne, amma duk da haka ba za ta yi sakaci ba. “Nan fa waje ne. idan a ka gan mu fa?”
“Kin san ba na so ku nisanta da ni, ko da na minti daya ne.” murya sa a shagale ta ke, ta na nuna dimbin sha’awar ta.
Ta dan yi dariya tare da nasarar ture shi, alhali zuciyar ta akasin hakan ta roke ta da ta yi. Ta kalli idanun sa, wadan da ke buge da mayen kaunar ta, ta ce, “Kai da ke barin mu kullum fa?”
Shi ma ya yi murmushi, “Wannan dole ne ya sa. Amma in kin ce na bar aikin, sai na bari.”
Ta sake yin dariya, “Wace ni? Aikin taimakon al’umma, idan ban goya maka bay aba kuwa ai b azan sanyaya maka gwiwa ba.”
Ya saki dariya, “Shi yasa na ke kara kaunar ki, tare da gwada mi ki a ko yaushe. Na fi son idan ban a nan, ki yi ta kewa ta kamar yadda na kan yin a ki a wajen aiki.”
“Amma ai yau a gida mu ka yini, tare kuma.”
Ya dan shafa gefen fuskar ta, ya na lallausan murmushi, “Eh, na yi mi ki wannan ne don nu na mi ki jin dadina ga me da yadda ki ka tsaya a kan kafafuwan ki, ki ka tarbi bakina tare da fidda ni kunya. Thank you.”
Ya na gama furta hakan ya sumbaci gefen kumatun ta. Nan take ta ji yaar din wutar lantarkin kaunar sa. Kunya ta lullube ta, ta sunkuyar da kai kasa ta na shafa wajen sumbar. Ta daure tare da cewa, “Aikina ne, ba sai ka gode min ba.”
Ya kalle ta sosai, daga sama har zuwa kasa. Ya rika kurbar adon ta da kuma tsarin yadda rigar ta ta karbe ta. Ya ce, “Wannan kwalliya Masha Allah.”
Sannan ya dan duka dab kunnen ta na hagu, ya sauke muryar sa sosai, “An jima za ki min bayanin kalar ta ko?”
Ya Allah! Gaba daya ta saka tafukan hannun ta ta rufe fuskar ta, sannan ta fice daga dakin kusan a guje. Ta na iya jin sautin dariyar sa mai dauke da sakon da ke sa zuciyar ta daduum!
Watanni shida ke nan da dawowar su daga Yankari, amma soyayyar tsakanin sub a alamar tsagaita wa. Kullum Likita sai ya fitar da sabon salo.
Ba su cika haduwa da safe ba kam. Amma duk bayan azahar, misalin karfe biyu, Asiya za ta kira lambar wayar sa, don ta ji lafiyar sa a wannan yinin.
Har ya saba, ko da ba ya kusa ta yi, sai ya zo ya ga rashin kiran ta wato missed call. Wasu lokutan kuma sako ta ke ma sa, wanda yawanci na kara karfafa ma sa gwaiwa ne da addu’ar sa’a, musamman idan ya na da tiyata a ranar.
Shi kuma a ta bangaren sa, yak an fita da su yawon shan iska duk karshen mako, sai ko idan bay a garin, ko ayyuka sun ma sa yawa a asibiti. Ya san hakan bai wadatar yadda yake so ba. Shi yasa yak an yi ma ta abubuwa a duk lokacin da ya samu dama kasancewa da ita.
* * *
Ba ta fi mintoci sha biyar ba a wajen Umma, amma ta gaji tamkar wacce ta yi yini ta na aikin noma. Amatullah ta tabbatar mu su ta na da karfin jiki, da ma na lafiya. Rike ta waje guda ma don a yi hoton aiki ne jajur. Amma dai sun samu sun dauka da dama. An kuma yi mata ita kadai da dama.
Yusuf ya isa gare su, a daidai lokacin da mai daukar hoton zai kara yi ma ta hoto ita kadai. Ya dafa kafadar sa, ya ma sa magana kadan. Ta lura ya dan razana, amma dai ya yi murmushin dole, sannan ya dauke ta.
Yusuf ya ma ta alamar ta je gare shi da hannu, a lokacin da Ummah ba ta lura ba. Ita ma din sai da ta tabbatar da ba mai kallo tukunna ta je. Ba ta san dalili ba, amma ta hango wani abu a idanun sa musamman a lokacin da ya tsaya gefen mai hoton kafin ya dauke ta. Ko kuma a cikin muryar sa ce a lokacin da ya ke magana ne?
Bayan sun dan fita suna tafiya ne ta tambaye shi, “Me k ace wa mai hoton nan ne lokcin da ka tsaya?”
Ya tsaya ya na fuskantar ta. Ba su yi nisa ba da dakin Umma. Hasali ma su Umman sun a iya kallon su. Ya amsa, “Ce ma san a yi ya tabbata ya dauki wannan a matsayin na karshe ne. don idan ya ci gaba da kallon min ma ta to zan kwakule idanun na sa, ba bus hi ba sake daukar hoto.”
Ta dan yi dariya, “Allah Sarki bawan Allah. Shi yasa man naga duk ya tsure. Dauriya na yi, ai da na fashe da dariya.
Yusuf murmushi kawai ya yi, idanun sa suna kyalli, amma dai hakan ya kaa tabbata ma ta cewa akwai abin da yak e son fada ma ta.
“Akwai wata ‘yar matsala.” Ya shaida mata, bai jira ta tambaye shi ba. Fuskar sa ta nuna alamar fargaba.
Nan take hankalin ta ya natsu, ya koma a gare shi. Ba ta taba ganin sa cikin wannan yanayi ba. Yanayin da ya kusan wannan, shine ranar zuwan Yafendo ne na farko gidan. Amma duk da haka, bai birkice haka ba.
“Me ya faru?” Ta tambaya, muryar ta na rawa.
Yusuf ya nisa. Ya kalli wurin da Umma ta ke da Amatullah, sannan ita Asiyar.
“Mene ne?” Ta sake tambaya, zuciyar ta na gudu da sauri. Wani abu ya faru, tabbas. Fatan ta, ba mai tsanani ba ne. Ko dai Hadi ne da Suhaima suka kaure da tashin hankali? Asibiti ne a ka kira shi? Hatsarin mota a ka yi, a ka kai mutanen asibitin su? Ko me ye ne?
“An samu Mariya.” Ya furta, bayan ya nisa.