AMARYAR ZAYYAD

By rahmakabir

6.1K 184 15

Sanin abinda ke cikin labarin sai an bini daki daki amma akwai sarkakiya. More

1
2
3
4
5
15
16
6
7
8
9
10
11
12
14
17
18

13

221 8 0
By rahmakabir

*AMARYAR ZAYYAD*

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir

Page 13.

Safna tana kwance a cushing a falo ita kaɗai, Zayyad a sashin Rashida ya kwana shiyasa bata damu da haɗa abin karin safe ba sakamakon ta wayi gari da ciwon kunne duka biyun, ita kaɗai tasan irin azabar da take ji dan gane da kuɗar da yake yi mata, dama tana da history akan ciwon kunne shara uku da suka wuce tayi fama da shi sai da suka dage da magani sosai daga na asibiti har na islamic kafin ta samu lafiya, abinda ya fi damunta a yanzu shine yadda kunnenta na hagu ya toshe bata ji sosai da shi har ya sakar mata da ciwon kai. Sallamar da Zayyad yayi daga ƙofarta shine yasa ta miƙe jiki ba kwari ta isa ta buɗe masa sai ta juya ta dawo ta zauna a cushing, da ido Zayyad ya bita ganin ba ta da walwala da kuzari, ya tura ƙofar ba tare da ya rufe ba ya zo ya zauna yana cewa.

Madam Zainab barka da safiya, amma lafiya na ganki wani iri.?

Safna ta miƙe ta isa gareshi fuska kwaɓa kwaɓa kamar zata fashe da kuka ta zauna a cinyarsa tana dubansa.

Sirrina kunnena ke mini ciwo duka biyun, na hagun nan ma ya toshe bana ji sosai da shi.

Ta ƙare maganar hawaye yana sauka a kuncinta, Zayyad y tallafo fuskarta da duka hannunsa cike sa tsantsar kulawa.

Subhanallahi ciwon kunne kuma, sannu ƙaunata Allah ya ƙara sauki. Ina ganin ki shirya yanzu mu fita tare inna sauke yara a makaranta sai mu wuce asibiti likita ya duba ki dan abinda ya shafi kai ba a wasa da shi.

Ya ƙare maganar yana manna mata kiss a leɓenta tare da share mata hawayen da hannu. A lokacin ne Ilham ta turo ƙofar ta shigo kamar an korota ba ko sallama, cikin tsawa Zayyad ya dakatar da hanzarinta.

Wannan wani irin shashanci ne zaki faɗo ba sallama.

Mamanmu ce tace in kiraka mun shirya.

Ai nasan kun shirya wuce ki bani guri, kuma ki ƙara shigowa ba tare da sallama an baki izinin shigowa ba, sai na gauraya ni da ke.

Ilham ta fice da sauri tana turo baki dan bata son ayi mata faɗa, Safna tace cikin sanyi.

Da ka yi mata haƙuri, kasan yara in sun shirya zuwa makaranta nan hankalinsu yake tafiya.

Hmmm Ƙaunata kenan, nafa tuna malamar makaranta ce ke, ya kamata ki ware lokaci kina yiwa yaran nan lesson a gida.

Sai ka sanar dasu tare da mahaifiyarsu su sani, dan ni ko wani lokaci suka zo banda damuwa.

Godiya muke Amaryar Zayyad, yanzu jeki shirya da sauri Allah yasa ma kin karya.

Bana jin yunwa sai mun dawo na samawa kaina abinda zanci.

Shiyasa naganki ba kuzari ai, da yanzu zance mu shiga daga ciki ba zaki taɓuka komai ba.

Waye ya gaya maka? ai kasan bana taɓa yarda ka ƙure mini gudu sai dai mu jera, kuma ko a yanzu zaka sha mamakin karatun da zan biya maka.

Safna ta faɗa tana 'yar dariya ta nufi ɗaki zata shiga, Zayyad ya yi dariya shima.

Iye lallai na auri daidai ni, Ko dai zamu gwada ne mu ga waye gwarzo a yanzu.

Ban yarda ba.

Ta faɗa tana shigewa ɗaki, Zayyad ya saki murmushi yana girgiza kai wato Safna ce daidai shi in dai a wajen sakin layi ne tana bashi haɗin kai yadda ya kamata, hakan kuma yana sawa tana ƙara samun gurbi a zuciyarsa, duk wani hanya da salo na kula da miji tana ƙoƙarin yi, wanda da ace ita ya aura tun farko baya jin zai iya ƙara aure sai dai in yana cikin ƙaddararsa, duk da bata gama gwanancewa a harkar gado ba amma tana iya ƙoƙarinta ganin ta faranta masa, abin burgewa duk yadda yazo mata da salon kwanciya tana jure masa ba tare da ƙorafi ko raki ba, saɓanin Rashida da komai nata bata mayar da shi mai muhimmanci, ya rasa wani iri tunani Allah ya ɗaura mata, ita baga girki ba baga shimfiɗa ba komai nata ci baya ne, ga rashin iya magana da rashin kunya dan sosai ta raina shi, ya tabbatar tarbiyyar Safna da bambanci da Rashida, hakan yasa Safna ta soma samun babban gurbi a zuciyarsa sama da Rashida. duk da yana sonta amma Safna ta fara cin galaba a zuciyarsa da babban matsayi.

Safna bata tsaya ɓata lokaci ba ta saka doguwar riga baƙa da aikin farin duwatsu, ta saka hijab har ƙasa kana ta ɗauki glass ɗinta ta saka wanda ya ɗan cika mata fuska, ba kwalliya a fuskarta amma tayi kyau Masha Allah, ta saka turare mai sauƙin ƙamshi a jikin kayanta ta fito riƙe da waya, Zayyad ya kura mata ido har ta ƙaraso tana cewa.

Na shirya mu tafi.

Zuwa asibiti har da tabarau matar Zayyad, anya kuwa zan yarda da wannan mugun wasan, salon wani ya gama kalle mini ke gaki dai ba kwalliya amma kinyi kyau sosai, gaskiya kin san sirrin ado yarinyar nan.

Matar nan dai zaka ce, kuma ina cikin mota waye zai ganni? kasan tun ina gida ina ƙaunar tabarau dan Allah karka hanani sawa.

Ta ƙare maganar cike da shagwaɓa, banko ƙofar da aka yi yasa duk suka juya, ita dai Safna sai da gabanta ya faɗi, Rashida suka gani a tsaye fuska a ɗaure tana dubansu.

Zayyad amma abinda kake yi kana kyautawa, yara sun shirya zasu tafi makaranta kazo nan ka shagala, idan ban shiryasu da wuri ba kayi ta faɗa da mita, amma gashi kusan minti nawa ka ɓata anan, ke kuma saboda baki san zafin haihuwa ba balle kisan darajar karatun yaran shiyasa kika tare shi saboda mugunta da son kai, ki cigaba da abinda kike yi.

Tana gama faɗar haka ta juya ta wuce kamar guguwa, Zayyad da Safna suka kalli juna.

Mu tafi kuma bana so ranki ya ɓaci akan maganganunta.

Haba Ruhi bakomai, nasan rashin fahimta ne kuma ita muka yiwa laifi sai ka bata haƙuri.

Ta ƙare tana ɗan murmushi, sosai maganarta ya burge shi wanda ya nuna tsantsar tarbiyya a ciki, tayi shi cikin tauna harshe da kuma kawaici da haƙuri, hakan yasa shi kasa magana ya wuce gaba ita ta bishi a baya har suka isa wajen mota. Sun samu yaran suna tsaye yace su shiga baya su zauna, sai Safna ta shiga ta zauna a gefen driver, Zayyad ya zagaya zai shiga gurin driver ya hango Rashida ta rungume hannunta a ƙirji tana kallonsu, saboda ya wanke kansa daga zargi sai ya wuce sashinta ya tsaya a gabanta yana cewa.

Safna ba tada lafiya tana fama da ciwon kunne shiyasa zamu fita tare, inna sauke yara na ƙarasa da ita asibiti.

Hmmm sai ku jira ni mu tafi tare nima nayi muku rakiya.

Yadda tayi maganar cikin haɗe fuska yasa shi yin shuru bai tanka ba sai ya juya ya koma ya shiga mota, ita kuma ta shiga ɗaki tana ciwon yarda da jin wani raɗaɗin zafi a ƙirjinta wanda tun sadda Ilham ta koma ta sanar da ita Zayyad ya korota kuma taga Safna zaune a cinyarsa, ba ƙaramin dukan zuciyarta maganar tayi ba, tsabar kwazzaba jiya ya gama naniƙarta har da sambatunsa amma kuma yaje yana mannewa Safna, bayan tasan magungunan da ta sha ba ƙaramin aiki suka yi mata ba dan sosai taga sauyawarsa saboda tuni duk wani fushi da yake yi da ita ya daina, dama rabonsu da juna tun kafin bikinsa da Safna sai jiya ta sauke kai taje ɗakinsa ta bashi dama, ta ɗauka zaita rawar ƙafa akanta duba da lokacin da suka ɗauka ba mu'amalar aure, duk da yana samu a gurin amaryarsa amma ta zaci irin da ne da yake yawan nane mata, shiyasa ta dage da yin gyara musamman magungunar da ƙawarta Kubura ta kawo mata daga niger, amma wai ya je sashin Safna ya shantake kamar an aiki bawa garinsu, tayi kwafa tare da ɗauko hijab ta ɗaura akan riga da siket ɗin atamfar dake jikinta, ta fito ta rufe ƙofa ta isa motar ta tsaya a ƙofar da Safna take zaune.

Malama sai ki fito ki bani guri na zauna.

Rashida miye kike yi haka ne? ki shiga baya mu wuce tunda ta riga ta zauna.

Amma kasan dai uwargida ce ke da gaban mota.

A naki ƙaulin ba, amma ko wacce tana da damar zama a gaba in dai mace tana da girki, kije ki ƙara tambaya.

To ai nice da girkin.

Ta faɗa tana tsuke fuska, Safna ba musu ta buɗe ta fito ta zaga ta zauna a baya ta gefen Zayyad, Rashida ta shiga ta zauna Zayyad ya tada mota suka wuce cike da takaicinta.

Bayan ya sauke su Ilham sai ya juya alakar motar zuwa asibiti, sun hau kan titi sosai Rashida ke cewa cikin sakin fuska.

Abban Ilham yaushe rabonmu daka fita damu unguwa a mota har na manta, ya kamata ace nima yanzu ka saya mini mota, kaga kaima ka huta da jigilar kai yaran nan makaranta.

To kai ki unguwa Rashida ai kamawa take yi, mota kuma a yanzu banda halinta sai dai kiyi mini addu'a Allah ya hore mini nan gaba na siya muku keda Safna.

Amma ai zaka iya siyan mini daga baya ka siya mata, ba dole sai lokaci ɗaya ba.

Hakane sai ki taya ni da addu'a.

Ya faɗa a takaice tare da gundura da maganarta dan ya kula Rashida tana da son kanta, Zayyad ganin Safna tayi shuru ya kalle ta yana cewa.

Safna kin yi shuru kamar ruwa ya cinyeki ko ciwon kunnen ne?

Uhum da sauƙi Alhamdulillahi.

To ko kina tunanin Allura ne.

Ni bana tsoronta saboda ni jaruma ce.

Allah ko? kar dai sai kin ganta ki saka mana kuka.

Ni ɗin? haba dai Sirrin Ruhi gaka a kusa dani mai zai saka ni kuka, na tabbatar har ayi a gama ba zanji zafinta ba, kuma kamata yayi a raba ruwan allurar biyu a yi mini rabi a maka rabi nasan zanfi samun sauƙi akan lokaci.

Taya za ayi mini rabi bayan ni ƙalau nake.

Ka manta da cewa wanda aka yi maka zai dawo yayi aiki a jikina.

Zayyad sai da ya kalle ta ta madubin saman kansa, ya ga shi take kallo tana sakar masa murmushi.

Na yarda amma da sharaɗi.

Ya bata amsa yana nuna mata yatsun hannun damansa guda huɗu.

Naƙi wayon.

Ta bashi amsa tana maƙe kafaɗa, Zayyad ya saki dariya har yana dukan sitiyarin mota, gabaɗaya sun shagala kamar su kaɗai ne a motar, Safna murmushi ta dinga saki ta mayar da dubanta gefen hanya, dan tuni ta gano jirginsa akan nuna mata yatsunsa guda huɗu da yayi, hakan yana nufin kusancin aure zai yi sau huɗu a dare ɗaya, karatu ne daga shi sai ita suka san kansa, Rashida kamar ruwa ya cinyeta dan ba ƙaramin ƙular da ita suka yi ba, hakan yasa ta kunna data ta hau online zuciyarta kamar zata fashe, sai ta koma tana dana sanin biyo su da tayi, dama gulma yasa tace zata je dan bata yarda asibiti zasu ba duba da bata ga Safna a wahalce ba balle tayi kama da mara lafiya.

*Kuyi haƙuri da wannan. Da kyar na jure typing ɗin a cikin daren nan*

METAFORCE
Tsari ne mai matukar kyau daya zo mana a saukake, dan samun kudin shiga ta hanyar amfani da wayar hannunka. Kana kwance a gadonka zaka tare 'yan daloli bisa jajircewarka.

MENENE METAFORCE ⁉️
Kasuwanci ne na network marketing da ake gudanar dashi da wayar hannu, kasuwanci ne wanda kowani reshe ka ta6a kudi ne, kasuwanci ne wanda yake biya 💯percent, kasuwanci ne wanda kowa ma zai iya yinsa, kasuwanci ne da yake da tsaro da kuma tsari wanda yake akan blockchain technology. Project ne me zaman kansa saboda decentralized ne, babu Wanda ze iya HACKING, DELETING KO EDITING. Wani abu daga kasuwancin koda kuwa founder na METAFORCE ne wato Mr.lado saboda an riga an tsara shi Kuma a haka zai ci gaba  da tafiya💯 Alhamdulillahi
Alhamdulillah metarforce ana samun arziki da shi sosai. Duk wanda ya shirya dm 09034940106

Continue Reading

You'll Also Like

1.3K 2 56
Membaca cerita ini, kamu akan memahami manusia lebih mendalam, agar dalam bertingkah laku dan berbudaya, dalam hidup di tengah-tengah masyarakat dan...
92.6K 3.6K 27
Labarin wata budurwa ne wacce aure yayi mata wahala. Amira kenan 'yar kimanin shekara 24 da hud'u, tayi samari fiye da biyar amma dukkan su sai maga...
13.3K 609 53
MAKAUNIYAR RAYUWA- KASHI NA UKU- BABI ASHIRIN### Fatan alkhairi gareku masoyana a duk inda kuke,alherin Allah ya kai gareku, ubangijin Allah ya biyaw...
SAI DAKE.! By Billy s fari

Historical Fiction

14.7K 647 72
SAI DAKE.! Qagaggen labarine Mai cike da tarin darussa da kuma qayatacciyar soyayya da zata zamuku da wani salo na zazzafar qauna, SAI DAKE..! labari...
Wattpad App - Unlock exclusive features