A SIMPLE DARE (WASA DA SO)

By marteybee

431 7 16

More

new book
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page ten
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20/21
Page 24/25

Page22/23

10 0 0
By marteybee

✨✨

                     SIMPLE

                                         DARE

                              ✨✨

                       (WASA DA SO)

                WRITTEN AND STORY
                                  BY
                  NERNAH MARYAM
                           (MEEMARH)

       ✨ _*GORGEOUS WRITERS FORUM*_ ✨

         ✨ _*G.W.F*_ ✨

_*HOME OF GORGEOUS, INTERLLIGENT,AND EXPERT WRITERS,WE THE BEST AMONG THE REST*_

             Kofa a bude take ga duk me son yin joining group dina😌,Amman Hajiya don Allah in kin san ba yin comment ko karanta littafi na zai kawo ki ba I beg you in the name of Allah kiyi zaman ki ba sai kin shigo ba!!haka zalika wanann group din na mata ne zalla don Allah Maza should stay away from my group👏

       My What's app group link👇🏻

           https://chat.whatsapp.com/EUrVVaKJnIBDTlQsxurZv0

           Bismillahi Rahmanin Raheem............

      (    In the name of Allah the most beneficient,the most merciful)

 
  Kofa a bude ta ke ga duk wani me good quality product da ya ke son Advertising ɗin shi,as Kaya masu kyau,da inganci (TALLAH) should contact me via :
                              08100046388

                 Page 2️⃣2️⃣/2️⃣3️⃣

           TALLA!!TALLA!!TALLA!!!

       https://chat.whatsapp.com/ImtxMSS1tuSKqvBpPqc03P

Assalamu'alaikum sisters🤗
KAMSHI* mace Mai kima, mace Mai daraja, mace Mai izza, mace Mai aji itace tasan darajan kamshi, if your perfume is not unique hajiyata you're just using ordinary air freshener🤣, hajiyata ko nawa Zaki kashe indai a turare ne baki Fadi ba😘 matan da suka gane suka San yanda zasu kankaro da martabar su, suke amfani da turare, a *BAKHOOR BY FAIXY* Zaki Sami Main chic, Bachelor, Husband snatcher, Her royal sexiness, Mysterious girl, Pleasure, Boovilous, White khumra, Maroon khumra, Black khumra, Hair perfume, Turaren wanka, Turaren  wuta, Turaren tsuguno, Turaren mopping,Turaren carpet Shu'umat khumra,and more, yar uwa kar kibari abaki lbr, (wholesale and retail) WhatsApp 09067621681, siyan na gari Maida kudi gida🥳

Instagram @Bakhoor_by_faixy

******************************

     Dakin Mama Zuhra ta shiga tare da dauko daya daga cikin aboyoyin da Sabeeha ta bata,sabon ciki wanda bata taba sanya wa ba,Onion color ta kawo Sabeeha tace maza ta shiga tayi wanka ta fito ta kai mata ruwan zafi sai ta sanya kayan tunda bata dauko kaya daga gida ba,tashi Sabeeha tayi ta shige bandaki tana yaba irin raya gurmi na Zuhra,dake da soap kawai tayi wanka so ba ta jima ba ta fito,nan fa Zuhra ta taya ta shirya wa within no time sai gashi ta fito fesss da ita banda kamshi babu abinda take yi,sabon dankunnan ta Zuhra ta dauko tare da sanya wa Sabeeha,inda ta mata light kwalliya ba karamin kyau kuwa tayi ba,barin da tayi rolling din mayafin kayan dan gashin gaban kan ta sun fito inda suka kwanta luf da su gwanin ban sha'awa sai ya kara mata kyau Masha Allah,turaruka masu sanyin kamshi ta fesa mata sanann ta kalli kan ta a madubi ita kan ta sai ta ga tayi wa kan ta kyau,hakan ne ya sanya ta sakin murmushi me kyau cikin sanyin murya tace "goofy angel Wlhy yau nayi kyau sosai, ban taba kyau irin na yau ba"

Dan dariya Zuhra tayi tare da yi mata kiss a kumatu inda Sabeeha tayi saurin tureta "matsa dallah don't smash my make up"dariya Zuhra ta kuma sake wa sannan tace "bakauyiya sabida anyi light make up yau shine har ake ture kiss din Zuhra,yayi miki kyau"

Riko ta Sabeeha tayi sanann tace "dallah to in kika bata kwalliyan wanda aka yi domin shi be gani ba fa?"baki bude Zuhra ke kallon Sabeeha kafin tace "enyee yam matan Umma is finally in love 😻 dole ki ce mun haka,Soyayya dadi kawata Allah ya baki FIK mu sha biki"

Cike da jin kunya Sabeeha ta amsa da "Ameen"tana dariya itama Zuhran dariya ta sanya tana matukar ji wa Sabeeha dadi kallon ta Sabeeha tayi a hankali tace "Goofy angel daman haka ake ji in ana son mutum?"

"Bani labarin yanda kike ji?"Zuhra ta tambaya tana zama kusa da ita,dan fari Sabeeha tayi da idanu sanann tace "ni ban ma san me zan ce ko ya zan miki bayani ki fahimta ba,Zuhra Wlhy ko motsi nayi Shi nake tunawa,komai zan yi yana cikin zuciya ta,fuskan shi kuma na idanu na,Zuhra sai ina ji kamar ban da lafiya ko wani abu zai same shi in ba muyi magana ba,I just don't know how?Where?or when?Nayi developing feelings me yawa akan shi,Wlhy ni kai na at times har mamakin kaina nake yi ashe haka daman soyayyan yake?Sai na ji kamar na fada masa sai na kasa,Zuhra zuciya ta sai tayi ta azzalata in kira shi nayi masa magana ashe wai duk son shi nake yi"ta kare tana dariya kamar wata karamar yarinya.

Kallon ta kawai Zuhra ke yi ta ma kasa cewa komai banda gode wa Allah da take ta yi a ranta yau Sabeeha ce da bakin ta yake cewa wai ta kamu da soyayyan wani ashe za ta ga wanann ranar a rayuwar ta,ashe dai mahakurci mawadaci,ta kuma ji dadi da Allah ya sanya wahalar FIK be tashi a banza ba,gashi yanzu da yayi hakuri ta fada son shi,ta sani babu wanda zai kai Sabeeha sa'a da dace in ta samu FIK a matsayin miji,domin she is very sure zai kula da ita fiye da zaton me tunani.

Ganin Zuhran tayi shiru tana ta kallon ta ne ya sanya ta cuno baki tare da snapping fingers din ta a kan face din ta "Hellooo Goofy angel,ina ta magana kin yi shiru,ko dai na fada son da ta yawa ne?Maybe I overreacted ko?"ta kare tana cuno baki.

Kai Zuhra ta girgiza a hankali tace "ko daya my love babu wani overreacting din da kika yi,I'm very sure soyayyan da yake miki ya fi wanda kike masa sau dubu dari biyar,am just so happy for you,I can't wait to see how this your love story will end,after long years of waiting Goofy angel dina is in love dole nayi sadaka,Wlhy ba karamin perfect couples za ku zamo ba,and your babies za suyi masifar kyau,Allah ya tabbatar da Alkhairi a tsakanin ku,and Allah ya sa maganar da zai miki cewa zai yi turowa gida yake son yi a masa tambayar Auran ki,da mun gama exams mu sha biki"Zuhra ta kare da tsantsan farin ciki,inda dariya kawai Sabeeha ke mata ita kan ta ta rasa wani irin farin ciki take ciki,sai take ta cewa Allah ya sa maganar Auran zai mata domin da gaske har cikin zuciyar ta ta kamu da so da kaunar shi wanda ita da kan ta bata san a yaushe ta fara son shi ba,but how she feels at the moment is like she couldn't live without him even if she wanted to, wato ashe ba fault din yanmata bane idan sunce ba za su iya rayuwa ba tare da abinda suke so  ba ashe this is exactly how they feel lallai turawa sunyi gaskia dasukace love is a very strong weapon.

Ringing din wayarta ne ya katse musu hirar da suke yi  number ne tagani kan wayar hakan ya tabbatar mata driver'n FIK ne dauka tayi inda driver cikin ladabi kamar tana ganinsa ya gaisheta sannan ya shaida mata yana waje, jin haka Zuhra cikin sheqiyanci ta sake  feshe ta da turare tana cewa "Kawata kin san  amarya saida turare"kai Sabeeha ta girgiza tace "ke nikam rabu dani sai na dawo" cike da zolaya Zuhra tace "ko dai  nayi rakiya ne? Na kalli yanda sabin shiga a soyayya suke yi"Sabeeha ta galla mata harara tare da cewa "toh in kina wurin taya zan fada masa ina son shi ke dai yi zaman ki Hajiya ta zan baki labari in details"

Baki Zuhra ta turo sanann tace "Allah ya isa ko A in kika cire baki fada mun ba,bari na dauko hijab na raka ki kofar gida to tunda kin ce ba zan biki ba"Sabeeha ba ta tsaya kula ta ba takalmi ta sanya don in tace za ta biye wa Zuhran sai su kwana su tashi don ta ga alamun yau tsiyar Zuhran kan ta ya tashi,saida suka biya dakin Mama inda Sabeeha ta sanar da ita za taje ta dawo,inda Mama tayi mata Allah ya tsare hanya har tana tsokanan ta tayi kyau,yau ranar farko da ta gan ta da kwalliya,dariya Sabeeha tayi tace "kai Mama"inda Maman tace "yoo ai Gaskiya ce kila surikin nawa ne ya zo,to a gaishe shi a kuma dawo da wuri don Allah"da haka suka rabu tana dariya wa Zuhra wai taya Mama tayi saurin gano ta haka,har kofar gida Zuhra ta raka ta inda cike da farin ciki tace

"A gaishe da Pastelito Goofy angel make sure ki aje kunya ki sanar mishi yanda kike son shi kin ji?"murmushi Sabeehar tayi sanann tace "Ai yanzu kam kin maida ni mara kunya tunda na bari kika gane am in love,sai na dawo Goofy angel thank you so much for everything and I love you 300 times"ta kare tana rungume ta,murmushi Zuhran tayi sanann tace "silly yayi yawa,take care have fun okay,ina jiran jin good nice"da haka suka rabu zuciyoyin su kal,Sabeeha ta shige motar da driver ya bude mata,Zuhra kuma ta shige gida tana fadin "yoo irin wanann kauna haka,nima bari na kira Habeebey ya zo mu sha love kan wanann sabon shigan ta dawo"

Tafiya driver'n ke yi cike da nutsuwa babu gudu babu komai,ga wata sassanyar kamshi da sanyin da ke fita daga motar,inda karan kidan wakar 'Zuciya' (By Auta Waziri)ke playing a cikin motar, lumshe idanu tayi a hankali,yau ne rana ta farko da ta ji wakar amman sai ta ji tayi bala'in yi mata dadi, inda ita kadai sai tana sakar wa kan ta murmushi ta rasa yanda za ta misalta irin farin cikin da take ji,wai shin daman haka so yake ne?Ko kuma nata ne ya zo mata da haka?Don za ta ce in ta taba to ta manta amman a duk rayuwar ta babu moment din da ya kai wanda suka yi spending da FIK dadi,wato he was a best friend and more to her,bata taba tsammanin she can be so happy and free around ko wani na miji ba a duniya sai akan FIK,the guy was full of vibe and more,ai bata ma da wani hujja da ya wuce ta bi umarnin zuciyar ta ta sallama amanar kan ta da zuciyar ta a gare shi,domin abun da take gudu for long daman mallaka wa wanda be dace ba amanar zuciyar ta ya je at the end yayi wasa da ita ya karya mata zuciya,to Alhamdulilah Allah ya hada ta da wanda ya san darajar zuciya ya kuma san mutuncin ta,tana kawai hasko irin dadin da zai ji in har ta fada mishi tana son shi a yau,domin ta kudurta wa ran ta yau za ta sanar da shi sirrin ran ta,ta lula duniyar tunani sosai har bata san lokacin da suka iso destination din su ba,sai jin karar tsayuwar motar tayi tare da fitowan driver ya bude mata kofa,cike da ladabi yace "Madam mun iso"sai a lokacin tayi firgit tare da dawowa tunanin ta

Murmushi tayi wa driver din tare da dauko jakar ta sanann ta ziro kafafuwan ta a hankali,kallo take kare wa gurin domin tun da uwar ta ta haife ta bata taba zuwa nan gurin ba,kallo daya za ka yi wa gurin ka san guri ne na Alfarma wanda me gurin ba karamin kudade ya narka ba gurin gina gurin,domin komai da ke gurin Masha Allah ya hadu sanann sai masu kudi irin su FIK ke zuwa gurin,don yanzu ta taba abincin gurin sai a kira maka kudade,ta fadi hakan a ran ta tare da daga idon ta don ganin sunan gurin 'Gusto Restaurant' ta gani a rubuce inda ta karanta a hankali tana tambayar kan ta "oh daman nan ne Gusto din da Zuhra ta dame ni akai?Ai ko yau akwai labari zan sanar da ita na zo Gusto"ta kare tana yar dariya,sanann ta kalli driver din cikin siririyar murya ta tace "uhmmm yana ina ne?"cike da ladabi ya amsa ta da fadin "ya ce kina shiga ta right din ki za ki gan shi madam"ya kare yana shige wa motar,tare da ja ya bar gurin.

Cike da takun nutsuwa kamar me tsoron taka kasa take takawa cikin gurin,tana me yaba kyau da tsaruwar gurin,ko don bata taba zuwa bane take ganin kyan oho?Amman babu karya kam gurin ya hadu,saidai abun ya daure mata kai,ya kuma bata mamaki ganin bata ci karo da mutum ko guda ba a duk girman fadin gurin,shiru kamar wani wanda aka yi mutuwa,saida ta shiga ciki ta dan ji zuciyar ta na bugawa inda tayi saurin kawar da duk wani negative thinkings kamar yanda Zuhra ta fada mata tare da sakin murmushi adaidai lokacin da ta hango FIK yayi mata waving hannu alamun ta karaso,ba musu kuwa cike da takun nutuswa inda in ba sanin ta kayi ba sai kace jan aji ne ko kuma tsoron kasa ko iyayi take yi,inda duk wani gaba a jikin ta ke motsa wa a lokacin da take tafiya,bata kawar da murmushin kan fuskan ta ba har ta iso inda yake zaune,inda da sauri ya mike tare da ja mata kujera,saida ya sakar mata tsadaddiyar murmushin sa me kara tafiyar da zuciya tare da imanin ko wace mace sanann cikin calm loin voice din shi yace

"Welcome My love have a seat Princess"ya kare yana me mata nuni da hannu,murmushi ta saki tare da girgiza kai yau na farko ta ji wani irin nauyi tare da kunyar shi sun lullube ta,har ta tsinci kan ta da kasa hada idanu da shi,kasa kasa tace "yo miye na ja mun kujeran to"

Saida ya saki dariya sanann yace "I have to you are Mi lady kin ga kuwa ba komai bane in na miki Princess treatment,seat down pls"ya kare yana zama shima,nan ta zauna sanann kan ta kasa tace da shi

"Ina wuni?Ya gajiya?Ya gida?Ya su Mommah?"a tare duk da jero masa tambayoyin nan,saida ya sauke ajiyar zuciya sanann yace "Bebe duk ni kadai tambayoyin nan basu mun yawa ba?"

Baki ta dan turo shi be san a matukar rude take ba inda ya kafe ta da idanu sai take ji kamar an daddaure ta da jijiyoyin jikin ta, "babu wani yawa Pastelito ni dai kawai ka amsa mun"ta kare a dan shagwaben da ba ta ma san ta masa ba,dan kallon ta yayi sanann ya dan talle baki yace

"Ni Mommah na ta hana ni amsa tambayoyi da yawa",cike da tsokana tace "Ni kuma Umma ta tace in nayi wa Pastelito tambayoyi da yawa,kuma ma in Mommah ta hana,am sure bata hana amsa nawa ba"ta kare tana hararan shi,shima hararan nata yayi sanann yace

"Komai lafiya Alhamdulilah Babe ya Umma?",sai lokacin ta tuno Umma bata ma sanar da ita za ta zo nan ba,ta dai fada mata za ta gidan su Zuhra tun da safe,dan numfashi ta sauke sannan tace "Umma na nan lafiya Alhamdulilah jinin nata ne ma ya dan hau shekaran jiya tayi ta complain din ciwon kai amman da sauki"

"Cike da tausayawa yace "Ayya Allah ya kara sauki,make sure ki tsaya a kan ta tana shan maganin ta on time,don maganin me kyau ne sosai shi Daddy yake sha,in tayi dace ma a hankali za ta rabu da shi har abada,kin san jikin girma in ka girma abubuwan
sai ya zamo sai a hankali,I can't wait na ga Bebe ta an girma an fara tsufa"ya kare yana dan dariya.

Itama dariyar ta sanya sanann tace "waya ce maka zan tsufa?A young zan zauna ehee!!Saidai kai ka tsufa"nan ya dan Harare ta sannan yace "naki wayon in har ke ba za ki tsufa ba to nima ba labarin tsufa,kin ga sai a sanya mu a BBC da CNN couples din da ba sa tsufa"dariya ta fashe da shi sannan tace "lokaci daya za mu yi popular mutane da yawa za su ce mu basu abinda muka sha muka zauna a young forever su ma su sha"shima saida ya dara sanann yace "kin ga cikin sauki mun samu way of making money,sai mu ce sai sun biya in dollars kafin mu basu sirrin"kai kawai ta girgiza tana jinjina wa shakiyaci irin na FIK dan shiru duk suka yi sanann yace

"Pardon me ba a kawo miki ko ruwa ba,me kike son kiyi order?Ban yi placing order ba ban san ko akwai specific abinda ran ki ke son ci yau ba"ya kare ya a kokarin kiran daya daga cikin ma'aikatan gurin tare da mika mata Menu kan ta zabi abunda yake son ci da sha

Da sauri tace da shi "aa wlh a koshe nake"kallon baki ma isa ba ya bata tare da kiran ma'aikacin ganin ta ki bada order ne ya sanya shi placing wa both of them,daidai lokacin message din Zuhra ya shigo,wanda ya sanya ta sakin murmushin da bata yi niya ba,inda take fadin a ran ta "lalle Zuhra saidai a bar ta,akwai ta da son jin gurmi"domin text tayo mata ma hope ta fada mishi tana son shi har sun fara soyayya,ta fara kokarin ciro Ashobe da shirya events din da za a yi a biki,kasa ma yi mata reply tayi banda kai kawai da ta gyada tare da aje wayar,daidai lokacin an kawo order din da yayi musu,inda lafiyayun abinci da abun sha aka shiryo musu wanda kallo daya za ka musu ka san zai yi mugun dadi.

Kallon ta yan dan yi sanann yace "Bismillahi abincin su akwai dadi try it,you won't regret it"murmushi tayi a hankali tace "I'm okay saida na ci abinci na fito"baki ya turo sanann yace "kin ma isa ai ko dole ki ci,see you sai kace yau muka fara cin abinci tare,bayan har plate daya mun ci abinci,in kuma kunya kike saboda public to kwantar da hankalin ki nayi reserving gurin gaba days a na yau babu wanda zai zo daga ni sai ke ne,so pls ki ci abinci"dan kallon abincin tayi yanda yake turiri ita sam ba shine gaban ta ba zuciyar ta na ta azazzalar ta kan ta sanar da shi tana son shi itama sanann ta saurari abunda ya sa kira ta.

Tsintar kan ta tayi da fadin "in na ci abincin zaka fada mun important maganar da kace za muyi?"ta kare kan ta kasa,kai ya gyada mata yana kurban lemu sanann yace "yeah Barbie doll in kika ci dole na fada miki,don ya wuce yau ban kuma san randa za mu kara haduwa da ke ba"da sauri ta dago tare da kallon shi don bata fahimci inda maganar ta shi ya dosa ba,inda shi kuwa murmushi ya sakar mata sanann yace "don't panic okay eat first sai muyi maganar"kwata kwata sai ta ji ta jikin ta ma ya mutu ta ji ma sam babu sha'awar abincin a ranta duk da dadin da yayi kuwa inda shi ya ke cin abincin shi cikin kwanciyar hankali yana pressing phone din shi,ganin ta kasa taba komai ne ya sanya yace

"Wlhy zan miki d'ure yanda ake wa yaran talakawa in sun kin cin abinci"idanu ta watsa mishi sai tayi saurin rufe baki tare da cewa "I don't mean that eat something pls,don ke fa na sa aka kawo abincin nan"ba dai don ran ta ya so ba ta dauki spoon tare da fara tsakuran abincin don har ga Allah ko gane taste din shi ma bata yi,bata wani ci sosai ba inda shi kuwa ya ci kusan rabin plate ya sha lemu sanann yace a zo ayi clearing gurin.

Idanun ta na kasa tana wasa da ring din hannun ta,sai lokacin take jin zuciyar ta na bugawa,a hankali ta shiga furta "Inalilhi wa ina ilaihi raju'un"inda ta ji ya kira sunan ta a hankali "Beeha!!"dagawa tayi a hankali ya kalle shi don it's been long da ya kira ta da hakan.

Tashi yayi tare da dawowa kujeran kusa da ita inda za ta fi fahimtar shi da kyau sanann ya cigaba "it's been 3 months now da haduwa ta da ke,and I can't lie wanann 3 months din sune best months din rayuwa ta,I got to know you,love you,and be around you for the past 3 months,ban taba sanin haka soyayya take ba sai a kan ki,Barbie doll ban taba sanin FAIZAAN na da zuciya yana kuma da kirki ba saidai na hadu da ke,babu wanda ya isa ya sanya FIK yayi ko ya bari a rayuwar nan hatta Mommah abinda nake so shi nake a duk lokacin da na so saida na hadu da ke,babu wnada ya taba raising voice din shi akai na balle har ya sanya hannun shi a jiki na sai a kan ki,kin yi mun abubuwa da yawa haka zalika na koyi abubuwa da yawa a gurin ki more especially ma na Addini na,you are just one of a kind you are rare gem my love ban jin akwai kamar ki duk duniyar nan,you have given me nothing but peace laughter and happiness for the past 3 months din nan,and I really appreciate and adore you and will do that for the rest of my life,thank you letting me love you,be with you,and be around you at most thank you for coming into my life,you have changed me into the person I am today,thank you for correcting and forgiving each one of my mistakes,Wlhy bani ma da bakin gode miki saidai nace Allah ya saka miki don kin yi kokarin maida ni human being me zuciya a kirji,Allah ya sani Sabeeha ina son ki yeah,da gaske ina son ki kuma I want to be with you in aure ki mu gina family tare,but I have to let you go , domin abu ne da ba zai taba faruwa ba,da sauri ta dago ta kalle shi,inda ya gyada mata kai tare da sauke ajiyar zuciya sanann ya cigaba,nayi iya kokari na gurin ganin na cire ki a zuciya ta but hakan be faru ba,I respect your decision tun day 1 da kika ce mun baki soyayya,Wlhy na so na rabu da ke tun wanann lokacin but na kasa,nayi duk wani abunda nake ganin ya dace in yi don na janyo attention din ki,Babe har gurin Soul sis nake zuwa tayi mun classes na yanda ake sace zuciyar mace duk saboda ke,ban son magana bana kuma yawan magana amman akan ki saida na koma parrot ma nan ya gan ni ya bar ni,to yanzu kam na fahimci duk yanda zan yi ba shi zai sanya ki so ni ba,so I have no other option da ya wuce na bar ki,nan ma da sauri ta kalle shi,inda a raunane yace yeah gwamma na Kyalle ki,takuran tayi yawa ke ma sai ki huta in babu ni,za ki huta da gani na kullum da kike yi,za ki huta da yawan surutun da nake miki,in fact na yanke shawarar barin kasan zan tafi can kasar waje kasa me nisa da mu don na samu na manta da ke,don muddum na cigaba da zama a nan to na sani ba zan taba daina son ki ba,which na sani ina takura ki so daga yau you are free my love go live your life yanda kike so no more FIK da damuwowin shi,FIK zai rabu da ke amman kar ki taba manta da ya so ki kamar ran shi,sanann be san rannan da zai daina son ki ba,I'm wishing you nothing but the best,take care of yourself pls"ya kare yana kokarin mike wa,da sauri tace

"Wai gaske kaima tafiya za ka yi ka bar ni kamar yanda Abba na ya tafi ya bar ni tun ina jinjira?"ta kare idanun ta na ciko wa da kwalla,kallon ta yayi sanann yace "ya kike son nayi Beeha?Uhmm ya zan yi miki? Sabeeha love is also reciprocal you give and also receive which in my situation I'm the giver and I don't receive any and it brings us to a moment where I have to let you go so I won't be a pest in your life no more,so I have to go"ya kare yana kallon ta,idanu kawai ta zuba mishi tana jin zuciyar ta kamar zai fado kasa,ganin tayi shiru ne ya sanya shi gyada kai "alright I think baki da abun cewa kuma ko?It's okay take care of yourself sai anjima"ya kare a raunane tare da juyawa,ganin gaske fa tafiya zai yi ya bar ta, bata san ya aka ayi ba kawai sai bin umarnin zuciyar ta tayi tare da saurin mike wa har tana cin tuntube domin bata san ya za ta yi ba in ya bar gurin nan gaske kasar zai bari shike nan ta rasa shi na har abada,tayi Yaya da tulin soyayyar da take masa cikin ran ta?Cikin sauri ta riko kasan bayan rigan shi,inda cak ya tsaya ba tare da juyowa ba cikin sarkewar murya tace

"Pastelito stop!!!Wait pls you don't have to go,you don't have to leave me here all alone"juyo wa yayi tare da tsare ta da idanu sanann yace "I won't I?Me ya sa ba zan tafi ba? Don't worry yourself I will be fine and zan kira driver ya zo ya maida ki gida in tunanin ki ba za ki samu abun hawa bane"

Harara ta maka masa sannan tace "waya ce ma maganar abun hawa nake ma?Na san hanya I can go home on my own,kaine bana son ka tafi"tayi karfin halin fadan hakan,da sauri ya nuna kan shi "ni!!!kar na tafi and why ba zan tafi ba?Sabeeha babu amfani na a rayuwar ki kuma"

Da sauri ta katse shi da fadin "waya ce ma baka da amfani a rayuwar Sabeeha?Waya ce maka kai ba kowa bane a rayuwar Sabeeha?Sabeeha ce ta gayya to ka rayuwar ta?Kai ka shigo a sanda bata neme ka ba sanann sai a lokacin da ta ke da bukatar ka za ka ce za ka tafi?How dare you??I refuse to let you go"ta kare tana girgiza kai.

"Why won't you let me go??Huh Sabeeha just why tell me one reason da zan cigaba da zama a rayuwar ki ina takura miki,why zan zauna ina son ki ke baki so na?"da sauri tace da shi "Who said bana son ka?Pastelito Waye yace da kai Sabeeha bata son ka?I love you so much"ta fada daga can karkashin zuciyar ta,da sauri ya kalle ta

"Excuse me???I don't think na ji abinda kika ce,can you repeat yourself pls"ya fadi yana kafe ta da idanu dan murmushi tayi wanda ya kara fito da ainihin kyan ta sanann tace

"When we first met,I was not looking for love,I was running away from it ;but you were so kind and gentle that I felt my heart slowly opening up to you,and before I knew it,I was head over heels in love with you,FAIZAAN ISMAIL KWAIRANGA ina son ka"ta kare tana rufe idanun ta,wata irin farin ciki ne ya lullube FIK inda yace

"Noooo Sabeeha wasa kike,ko kuma ni ke mafarki,don Allah gaske kike kina so na?Say it again pls"ya kare yana kallon ta ya ma kasa sanin yanda zai sanya kan shi don murna,dariya ta fashe da shi sanann tace

"Silly you ba mafarki kake ba I never thought zan ga wanann ranar a rayuwa ta,FAIZAAN bani da any reason da zan ki son ka,kayi mun proving ba duka maza suka zama daya ba,dan dariya tayi sanann tace Lucky you ko a mafarki ban taba tunanin zan fada soyayya ba sai gashi out of nowhere na kamu da son ka, and I could shout to the whole world that I love you and I'm yours,I love you so much Pastelito"ta kare da dan karfi tana dariya tana jin zuciyar ta kamar an daga mata katan stone,farin cikin da take ciki baki ma ba zai musalta shi ba

A hankali ya tako har ya matso dan da ita,fuskan shi dauke da murmushin da na kasa gane na miye ne,cikin taushin murya ya ce "say it again Barbie doll"cike da tsantsan shaukin farin shiga a soyaya tace "I love you Faizaan and I cannot live without you"ta kare tana turo baki,wani irin wawan dariya FIK ya saki tare da tafa hannu sanann yace "Guys I have won"inda kamar daga sama ta fara jiyo tafi

'Raf!!!Raf!!Raf!!!Raf!!!Raf!!!!haka take juyo karan clapping daga bayan ta inda a hankali suka bayyana tare da zagaye ta,suna tafi tare da sheke wa da dariya,a hankali ta dago idanun ta daga kasa tare da zuba musu shi tana bin su da kallo daya bayan daya kan ta ba karamin kulle wa yayi ba,Nabeel,Jawad, Akram,Farouq,ta gani tsaye gaban ta suna watsa mata kallon da ba ma isa ta iya fasarasu ba,kan ta be kulle ba saida ta ga Faizaan ya kalli Nabeel yace

"Finally Beel yau fushi ya kare ko?"da sauri Beel ya rungume shi tare da sakar masa kiss a kumatu yana jin kamar ya maida shi cikin cikin shi don murna "yeah bro yau kam an gama mun komai Wlhy,ji nake kamar na mutu na shiga aljannah Wlhy I never thought you will go through with this I thought we have lost you"ya kare a raunane

Dariya Faizan ya kwashe da shi sanann yace "c'mon lost me?For who,wai to this little Twat???Haba Beel FIK ne fa,never"kallon shi tayi bakin ta har na bari gurin furta "Pastelito what all this ban fahinta ba"Haba nan duk suka kwashe da dariya tare da kwaikwayon muryan ta gurin fadin

"C'mon pastelito what all this ba mu fahinta ba,explain more to her"suka kare suna kara kwashe wa da dariya,dan kallon ta Faizaan yayi from head to toe sanann ya dan juya ya fara magana cikin kakkausar muryan shi sai ya koma sak FIK din da team leader din Rocket gang cikin isa da izza yace

"What a fucking performance,from the mighty FAIZAAN ISMAIL KWAIRANGA,that's my name Bitch not Pastelito and what a great actor I am,excuse me who the hell do you think you are???Do you think I could ever loved a low level class bitch like you??What the fuck girl think again,hmmm okay pls remain me of what you said early,that I am lucky to have found you,huh you are the luckiest one bitch,kin san darajan FAIZAAN ismail kwairanga kuwa??Da har na taka kafa na je wanann dattin unguwar naku,na shiga ciki dattin gidan ku,da dattin yan uwan ki masu creating scene for no reason,more especially that fat woman remain me of her name again,ohhh yeah Ladi right,da wanann thug dan nata wai Fatah yake ko Waye sunan na shi ma I don't give a damn akan sunan na shi,Beel wai nan din dauka tayi son ta nake yi,haba Baby girl yanzu ke ko mafarki kika yi wanda be kai ni ba ma yace yana son ki sai ki yarda balle Faizaan Ismail kwairanga??Haba ke ma kin san karya ne Ai"Ya kare cikin halin ko in kula.

Dan dariya ta sanya in disbelief din abunda ya gama fada mata sannan tace "Stop it stop this joke it's to expensive for me to buy,haba dai Faizaan tell me all this is a joke pls"ta kare tana putting smile din dole

Kallon su Beel yayi sanann yace "Wai tambaya ta take wasa nake yi mata ko gaske?"A zafafe Nabeel yace "Ke dan uban ki mun yi kama da sa'a in wasan ki ne?"a zafafe ita ma tace

"Can you shut up with this your dirty mouth tunda ba da kai nake magana ta ba"ta kare tana hararan shi,da sauri yayo kan ta inda Akram ya rike shi "kai Beel akwai ka da hanzari yarinyar da za tayi kuka har ta gode Allah dukan na miye za ka kara mata?"tsaki ya ja tare da ba wa kan shi hakuri ya tsaya don ganin yanda za su kare da Faizaan.

Takowa tayi zuwa gaban shi ta tsaya sanann tace "Faizaan you are joking right?Maybe you are still tasting me ka ga ko da gaske ina son ka ko karya ne,Wlhy Faizaan da gaske nake maka ina son ka kamar yanda kake so na,so ka aje maganar wasa a gefe pls ka ji"ta kare a raunane.

Dariya duk suka kwashe da shi har da shi kan shi Faizaan din sanann yace "kina bani dariya in kika ce na aje wasa a gefe,Sabeeha ta Yaya zan aje wasa bayan akan wasa muka gina komai ni da ke kuma abinda ya kawo ni ke nan,Sabeeha Wlhy kina da abun mamaki wai gaske kin dauka son ki nake?"jin haka ya sanya ta saurin daga kai alamun eh sanann tace "In ba so na kake ba to miye?So na kake mana kuma Wlhy nima ina son ka"

Kai ya girgiza sanann yace "Akram get me some tissue pls don ya kamata na yi wa wannan Twat din kuka,yanzu ke don Allah in aka ce miki ina son ki sai ki yarda?Wannan same Faizaan din ne dai mata tarbiya wanda kika ce ya je gida a koya masa tarbiya shine kike fada wa ba za ki iya rayuwa babu shi ba,don baki da kunya Faizaan din da kika daga hannu kika kwada wa mari a tsakiyar school kika fasa wa glass din mota shine dai same Faizaan din da kike cewa kina so ba za ki iya rayuwa babu shi ba,Same Faizaan din da ya kashe muku dukiya lokaci da lafiyar shi kika ta wulakanta shi shine yanzu kike cewa ba za ki iya rayuwa babu shi ba,Faizaan din da ya kwana ruwa na dukan shi duk saboda yayi proving shi din Faizaan ne sanann kike cewa a bar wasan haka yaushe ma aka fara wasan da za a bari?Dauka kike wai kin kai ne ya sanya Faizaan yayi ta bibiyar ki kina masa duk wulakancin da kika ga dama?Dauka kike Faizaan ya mace a kan ki ne ya sanya kika yi masa duk abun da kike so?Dariya ya fashe da shi sanann yace sakarya shashasha,little Twat wai har kin manta Rocket gang ne?Cikin sch kika dauke ni da mari sabida rashin mutunci irin naki dauka kike wai banza kika mara?Kin dauka shike nan sabida ni na fi kowa son mata kin mare ni kuma sai na zo na mutu a soyayayr ki ko?You must be joking sweetheart"da sauri ta katse shi idanun ta sun kada sun yi ja domin sam bata gane abubuwan da yake cewa Wlhy,dauka take duk wannan an yi su in the past sun wuce miye na dago abun da ya wuce bayan yace ya yafe tun ba yau ba,cikin barin murya tace

"But that was just a silly mistake how could you have judge me with that?Besides kace ka yafe and kana so na nima kuma ina son ka so why bringing back abubuwan da sun Riga da sun wuce?"kallon ta ya dan yi sanann ya ce "I think you are not getting this in the right way but...hannun ta ya kama tare da jan ta inda ta saki jiki kawai tana bin shi don ita kan ta bata ma san halin da take ciki ba gaban tampatsetsen mirron da ke manne a jikin gurin ya kai ta tare da tsayar da ita a gaban mirror din a zafafe yace

"Take a look at you do you think you deserve me?Sabeeha haba mana Sabeeha,kalle ki ki kuma kalle ni ke a tunanin ki don Allah kin yi deserving FIK ya so ki?Wlhh you deserve someone like Farouq" da sauri Farouq yace "holy shit Allah ya mun tsari wanann Ai sai dai Akram ba dai Farouq ba,na dauki wanann na kai ta ina?"

Inda Akram shiga yayi saurin cewa " Allah ya sauwaka me zan yi da low life kamar wanann tab saidai Jawad"inda da sauri Jawad ma yace "over my death body wanann Ai Wlhy da na aure ta gwamma na mutu babu aure saidai ko Nabeel"

Harara Nabeel ya watsa masa sanann yace "Da In zauna da wanann matsiyaciyar gwamam na kare rayuwa ta babu mace"cikin dariyar mugunta FIK yace "to kin gani ko Sabeeha gaba daya babu wanda zai iya zama da ke balle har kiyi tunanin ni,kin san tsada na kuwa?kin san mata nawa nayi turning down a rayuwar ta kuwa,Sabeeha don't ever think me and you could ever be in the same boat,because I will always follow a plan ke kuma a kasa kuke yawo,hanyar jirgi daman na kafafuwa daban don ba zan ce mota ba don babu shi a wannan dattin gidan naku,don haka me and you it's over!!!Over an gama Sabeeha kamar yanda kike jin dadin fada kullum to ki manta da kin taba sanin FIK a rayuwar ki domin babu abinda zai yi dake"ya kare yana kokarin barin gurin

Bata san ya aka yi ba sai jin hawaye masu dumi tayi suna bin kumatun ta,cikin dauriya tace "FAIZAAN mun e nayi maka a rayuwa da na cancan ci haka?I want to know me na maka ka zabi kayi mun haka?Why will you do this to me bayan ka sa na kamu da son ka,Don Allah in ma wani abun ne let sort it out between us amamn don Allah kar ka rabu da ni,zuciya ta ba za ta iya daukan hakan ba,ban taba so ba sai a kan ka,ka ji tausayi na don Allah FAIZAAN"ta kare tana kuka.

Dariya ya fashe da shi tare da tafa hannu sanann yace "Nabeel I told you guys daman sai nayi breaking din ta into million pieces sai na sanya tayi kuka a gaba na ta kuma fada mun ba za ta iya rayuwa da ni ba,back to you stupid tunda na ga karamin brain gare ki har yanzu baki gane abinda nake nufi ba okay then lemme break it down to you,Sabeeha tun randa kika sanya wanann filthy dirty hand din naki kika mare ni,nayi ta tunanin hanyar da zan bi na dauki revenge zagi da cin mutuncin da kika mun ya sa na rasa nutsuwa da bacci na na kusan kwanaki nawa?Daga nan muka shirya ni da su Jawad don ganin mun dauki fansan abunda kika mana,domin ko na miji be isa yayi mana abinda kike yi ba,kin mare ni sanann kika yi mana zagin fitan arziki,a lokacin ne muka shiga binciken ke yar gidan Uban Waye da har za ki mare ni,Waye Uban ki a Kano wa kika sani wa ya san ki?A nan ne muka gano ashe ke ba yar gidan uban kowa bace,hasalima ke ba kowa bace face matsiyaciya talaka me siyar da Alawar madara to make a living,a lokacin da na so da na sanya zaman garin Kano ma ya gagare ku,amman I wanted to break you down ina son yi miki tabon da ba za ki taba mantawa da shi ba a rayuwar ki,a nan ne na shiga tunanin me zan miki don ko nayi rantsuwa wa Allah sai na saki kin yi kukan jini,ana haka sai ga labari ya zo mun kan baki taba soyayya ba saboda kina tsoron heart break,a daidai nan ne nace ga weapon nan na samu wanda zan yi destroying din ki da shi, inda nan take muka yi bet da abokai na suka yi Daring dina kan na sa ki fada so na nan da wata uku,in na fadi zan basu motana in kuma na yi winning za a bani Rolex domin babban Nabeel,na san baki san miye Rolex ba illiterate expensive watch ne wanda ko duk family din ki aka siyar ba zai siya agogon ba,jin haka ya sa cikin sauki na je gurin baby Elephant ban sha wahala gurin shawo kan yar banza ba I have to put some act ta yarda cewa ina matukar son ki,a take ta bani number din ki,and from their kin san karashin labarin,ban taba ganin mace me taurin kai da tsaurin ido irin naki ba,at first wlhh ban dauka zan iya shawo kan ki cikin sauki ba,amman wai me ake cewa ma?"

Da sauri Akram yace "kudi maganin zaman duniya,Alh in da kudin ka Ai kome kake so za ka samu"a take suka kwashe da mugun dariya, kafafuwan ta ne ta ji suna mata nauyi,inda ta ji wani irin jiri na neman yar da ita kasa hakan ya sanya cikin sauri ta dafe bango,tare da saurin rintse idanun ta sai yanzu take jin kalaman shi na dawo mata a kunne,one by one

"Wlhy yanda na ji tana ta ruruta ni bana soyayya,I hate love and men,bana soyayay ka dauka shegiyar da gaske take,amman kalli cikin sauki an karya wanann record din makaryaciya munafuka har wani wai baki taba soyayya ba to gashi cikin 3 months kin kamu da soyayyar FIK har kin fada da yawa shame on you Twat"Akram ya kare yana mata dariya.

"Shame on her daya ko biyu,Akram in banda hauka da dabbanci irin taki Sabeeha ni FAIZAAN na miki kala da wanda zai so ki?Har ke kin yi kalar matar da zan so?Haba Sabeeha!!Haba why kika yaudari kan ki haka?Yanzu don Allah ba abun kunya bane ace na nuna ki wa duniya a matsayin matar da zan aura,ai wlhh ke ma sai kin ji mun kunya,me kuke da shi?Nawa kuka tara?Wa kuka sani wa ya san ku?Wlhy da na aure ki gwamma na Auri Nabeel na san Dan uwa na na miji na aura kina nan ke ba kyau ba ba kuma jiki me kyau ba,Sabeeha ki sani Wlhy tallahi ban taba son ki ko da na rana daya ba,it was just A SIMPLE DARE da muka yi having ni da friends dina and I have finally won,so read my lips baby girl 'I hate you so beyond words,ban taba son ki ba,kuma har a bada ba zan so low life mutum irin ki ba,all what happened it's just a play WASA DA SOYAYYAR ki kawai nayi Sabeeha amman baki da abunda zan so a jikin 'ya mace"ya kare yana mata kallon tsana

Da sauri Beel yace "Kyalle ta Gee gani take ta gama making a rayuwa a lokacin da kake ta bin ta,a dabbanci irin nata dauka yake za ka yi sauko this so low to her level har ka fada soyayya da Jaka irin ta,kila har an bazama neman malamai da bokaye don a mallake ka a ci dukiya kasan abun ku da yar gidan tsotsan tsamiya"a zafafe Sabeeha tace

Dariya duk suka kwashe da shi sanann Jawad yace "Ni fa Bro Mom kawai nake tuno wa in ka kai mata wanann Gorilla din a matsayin matar da za ka aura"da sauri FAIZAAN ya tofar da yawu,inda yayi saurin cewa "I reject it,over my death body na auri yar mace a rayuwa ta,ai Wlhy in na kai wa Mommah wanann sai tayi hanging din kan ta,banda hauka ma ita Sabeeha da Umman ta har sun kai suyi surkantaka da Mom?Banda talaka da dogon buri,Umman da bana ji ta taba daura super a rayuwar ta itace za ta zama Mother in law din Mommah,my love are you okay kuwa?Yanzu Umman ki tayi kama da wace za ta zamo Sirikar Hajiya Samha Kwiranga?Umman da I'm very sure ko secondary bata yi ba,balle ace Diploma,matar da bata iya standing on her own ta karba wa kan ta yanci ita ce za ta zamo Sirikar Mommah matar da Allah na tuba da ke da ita Maids din gidan mu ma sun fi ku aji da komai da sanin rayuwa da Waye wa shine zan hada dangi da ke da ita,Yar mace ce ke fa yarinyar da ta tashi babu Uban ta"a zafafe Sabeeha tace

"Ya ishe ka FAIZAAN ya isa!!!!Yin shirun da nayi ba shi ya baka daman fadan komai da ka ga dama ba,idan har da sauran kunya a idanun ka ko me nayi maka Umma bata cancanci maganar banza daga gare ka ba balle har ka zage ta in har kana da hankali"

Ido cikin ido yace da ita "and so fucking what in an zage ta??Karya nayi ba diyar mace bace ke?Waye be san Uba na ba,amman ke Waye Uban naki?waya ce miki da Uwa ake ado Twat da uba ake ado wanda ke kuma bana tunanin kina da shi saidai wannan Umman taki"a zafafe tace

"FAIZAAN!!!!!!How dare you!!!!"ta kare tana daga hannun ta don kokarin dauke shi da mari don ba karamin sosa mata zuciya wanann maganar ta shi tayi ba,da sauri ya riko hannun ta tare da murda wa da karfi,har saida ta dan yi kara kwalla na zubo mata yace

"Back off and don't you ever try that again in your fucking life ki tuna abinda ya sanya ki a wanann halin da kike ciki marin da kika mun ne,to just imagine yanzu in kika mare ni me zan miki kuma gaba?Sabeeha last time ma da kika mare ni ban bar ki ba balle yanzu so kul kar ki kuma tunanin mari na,marin da kike mun shi ya sanya na yi soyayar karya da ke don na karya miki zuciya,to Wlhy yanzu rayuwar ki gaba daya zan karya in hannun ki ya kara taba fuska na"ya kare yana watsa mata harara.

"Ta ma mare ka Ai Wlhy sai na sumar da shegiya,dan uban ki akwai karya a abunda ya fada ne?Ke ga ki me hannun mari ko?Ga ki nan me ido a tsakar ka da kin iya marin maza ko?a tunanin ki wato kun samu dami a akala ko an ga dan masu kudi an makale masa sabida a tandi zagi da maiko ko?An dauka an ci bagas an samu wawa za a tande masa arziki,da kike maganar kar a zagi Mahaifiyar ki,ita Uwar taki Uwar zinare ce?Uwar taki nace Uwar wa tafi?To Sabeeha nace Uwar ki taci Uwar ta"ya kare babu alamun kunya a tattare da shi

Tassssssssss ta wanke fuskan Nabeel da wani irin gigitatce mari,inda kafin ya Ankara ta kara dauke shi da wani marin me masifar zafi,a zafafe suka yo kan ta banda FAIZAAN da ya ja gefe yana kallon karfin hali irin nata.

Cikin daga murya da ihu tace "na rantse da girman Allah duk uban da ya kara taku daya sai na masa abunda har ya mutu ba zai manta ba,ta kare tana daukan knife tare da yin pointing a gare su,domin yanda take jin zafi cikin zuciayar ta babu shakka za ta iya aikata musu komai ma Wlhy,Kai Nabeel ni kake zagin Uwata?sabida baka da hankali kuma baka da kunya,to Wlhy ba dai Uwa ta ba Uwar ka ka zaga Jaki Wawa mara tarbiya,Wlhy kun yi asara kuma kun ji kunya da kuka kasa gane talauci da arziki duk na Allah ne,kai FAIZAAN ka sani kuma suma sun sani ban taba rokon ka naira daya ba,sanann ban zauna da kai don abun hannun ka ba,saboda ba abunda ke gaba na ke nan ba,yeah na sani ni yar talakawa ce a ghetto area na taso cikin family house me datti,sanann da family masu datti,amman Alhamdulilah abu guda da aka koya mun a wannan gida me dattin akwai tarbiyya,hawayen ta tayi saurin goge wa sannan ta cigaba a cikin wanann gida me dattin ciki na taso,a nan kai ma ka shiga ciki ka kuma yaba da irin tarbiyan gidan,yeah na yarda Umma ta ba yar boko bace amman kuma Alhamdulilah tayi makarantar addini tunda har ta iya bani tarbiyyan da ya dace,a je muna da dattin da kace ba wannan dattin ya hana ka zama cikin mu har ka ci abinci tare da mu ba,FAIZAAN na ji ina saida Alawar madara don na rufa mana asiri amman ya fi mun don na san halal dina nake nema,ban kuma zauna jiran Uwa ko Uba na ya bani kudi nayi facaka da shi ba,yeah Alhamdulilah ba mu da komai kuma ni ba kowa bace amman ina da self respect,kuma Alhamdulilah bana yawo da tarin shara da hauka a matsayin abokai,wanda duk mental asylum ya ka mace su,dan shiru tayi tana kokarin maida hawayen da ke kokarin zubo mata

"Daman haka ne kuma Bahaushe yayi Gaskiya da yace me hali baya taba fasa halin shi,FAIZAAN riban me ka samu na wasa da soyayya ta da kayi?Dan murmushi tayi sanann tace be ma kama ta na tambaye ka haka ba,domin ka san arziki da yara ance masifa ne kamar yanda arzikin Uban ka ya zamo masifa a gare ka kai kuma ka zamo masifa a gare su,yau ka kara tabbatar mun da cewa eh da gaske ne duk maza halin su daya and Wlhy Alhamdulilah da ka fito mun da real intentions din ka tun yanzu,kasan ko kadan ban ji haushin ka ba,haka zalika ba zan zage ka ba domin ni Sabeeha yar gidan talakawa me alawar madara na san darajan kai na da kuma na iyaye na,da kake maganar ni yar mace ne,yeah ko a ina zan bugi kirji nace eh ni yar mace ce amman Alhamdulilah duk wanda ya san Sabeeha ya san tana da Uba ba a layi aka yi cikin ta ba,sanann kowa ya san Mahaifina Mal Usman Allah karban abun sa yayi tun ina yarinya,sannan Alhamdulilah wanann macen da bata taba daura super wax ba,itace macen da ta fara koyar da ni na kuma haddace Al-Qur'ani,sanann ta ce dai same matar da ka ci darajar ta har na karbe ka na fara son ka,Dan dariyar bakin ciki tayi sanann tace FAIZAAN ka san the funniest part here is that kai ka kasan ce butulu!!Domin duk mutanan da suka taimake ka su ka ci wa mutunci,sanann ba karamin abun kunya bane a gare ni in na aure ka Wlhy sabida ana aure ne don samar wa yaran ka uba na gari wanda kai da wannan taran fools din abokan naka duk uban da ya baku aure be san abunda yake yi ba,maganar ka Gaskiya ne hanayar jirgi daban na kafafuwa daban,amman wait and see inda Allah zai daukaka wanann kafafuwan ya kai su inda baka zato ba,kace ban yi deserving Auran mutun irin ka ba right?Ai zai zamo mun babban disgrace ace na auri mutun irin ka,domin wallahi da na yi asara don kai ba mutun bane dabba ne ,sanann kuma Ai ba kai ne Allah ba da yardar Allah sai na samu wanda ya fika da komai sannan ka rubhta ka aje ba za ka taba samun rabin Sabeeha ba ma balle Sabeeha,and Wlhy ko yanzu Sabeehar da kuke rainawa wanann yar talakawan ta kai inda baku yi tunani ba,tunda dai ita ce ta hana ku sukuni for good 3 months baku zaune baku tsaye har kwanan waje dan attajiri yayi akan ta,ai ko Alhamdulilah ko banza na daukaka na kuma hana ku kwnaciyar hankali da mutuwar ku,ko iya haka na gode wa Allah da ni yar talakawa aka bi ba ni na bi dan masu kudi ba

FAIZAAN ni kayi WASA DA SOYAYYA TA right?Ni ka sanya kuka?Kayi breaking heart dina into pieces bayan duk kokarin kare kai na da nayi,to shike nan in sha Allah yanda ka sani kuka da hawaye na akan ka,FAIZAAN sai kayi kukan jini gaba,yanda ka yi breaking heart dina,in sha Allah kai Allah destroying life and peace din ka zai yi,Allah ya sani ban taba cutar da kai ba na zauna da kai zuciya daya amman kayi mun haka,ko sanda na mare ka akan daidai na na mare ka tunda kokarin taba mun mutunci kayi amman kaima ai you are a future father yourself sanann kana da sister kana kuma da Niece don't think kayi min abun da kayi kaci bulus ke nan,my Allah will punish you for me,Wlhy my biggest regret and sin da ba zan iya yafe wa ba shine son ka da nayi,inda ina roka maka Allah ya jarabe ka da son abinda ba za ka taba samu ba a nan ne za ka san Allah na baya bacci"ta kare tana kuka.

Shiru duk suka yi domin ba karamin haushi maganar ta basu ba,inda a zuciye Jawad yace "Ka ga matsalan ka ko?Faizaan da muka gama fada mata abinda za mu fara da mun yi tafiyar mu domin ka san yaran talakawa ba fa tarbiya gare su ba"dan murmushi FAIZAAN yayi sanann yace

"Kai Kyalle yar mahaukaciya duk wanann ihu take bayan hari rasa abun fadi tayi,kallon ta yayi sanann ya kwashe mata da dariya tare da yi mata gwallo "ko banza I just took away your ego,I could've taking away your pride but ohh pls you are to local for me,so sweetheart nan gaba a daina dreaming big okay,wannan thug din cousin din ki Wlhy shine ya dace da ke ba yaran masu kudi ba,talaka Ai sai yar talakawa so a daina tunanin FAIZAAN domin be taba son ki ba,Wasa da soyayyan ki nayi yeah kamar yanda kika fada and wasa ta kare,so kowa zai tafi separate ways din sa ki dauka baki taba sanin FAIZAAN ba,sanann duk wani abun da na taba baki ki dauke shi matsayin CHARITY harda wanann rigar jikin naki don Helping the Poor is my passion,in Banda rashi taya za ki saka kayan da saurayi ya baki ki zo gurin shi da shi?Kin ga ko banza na kara miki yawan wanann gwangwanin da kike tara kayan ki a ciki,and da kike cewa Allah ya mun kaza bla bla bla...Allah Ai ba Mahaifin ki bane da zai dauki maganar ki,shashasha duk wani curse da za ki yi gare ni kan wanann dattin family din ki zai kare,sai a je a cigaba da saida alawar madara don nan ne kaddarar ki and for your information da kike cewa wai na jira na ga inda za ki da wanann left 2 legs don naki,ina kuwa za ki je Ai destiny din ki da komai a iya wanann ghetto area din naku zai kare,hannu ya sanya a aljihu tare da ibo kudi sabin yan dubu daya daya har guda 20
inda ya watsa mata a fuska yace pick this up, book for a cab and go back to your ghetto area,Guys let's go"ya kare yana juyawa inda a zafafe ta kwala masa kira

"FAIZAAN Ismail Kwairanga!!!!!Ka rubuta ka aje ko ba yau ba Allah sai ya wulakanta mun kai ya kuma kaskanta ka kamar yanda ka wulakanta ni kai da wanann Mahaukatan,Wlhy tallahi Allah sai ya saka mun ba zan taba yafe maka ba,Allah ya isa ban yafe ba,in sha Allah in takamar ka dukiya ce sai ka zo neman Alfarma a inda dukiyar ba za tayi amfani ba,I hate you with all of me I cursed the day da na fara ganin ka,and I hate myself da na yarda da kai har kayi playing dina"ta kare tana kuka,dariya ya kwashe da shi sanann yace "Go to hell Bitch and burn to ashes duk wanann maganganun naki kan ki za su kare banza a banza yar talakawa"ya kare yana fita daga Restaurant din inda suka bi bayan shi kamar jela zuciyar su kal banda Nabeel da yake ji kamar a bar shi ya kashe Sabeeha don marin da ta dauke shi da shi,mota suka fada inda tunda suka shiga FIK ya kasa cewa komai shiru kawai yayi tare da lumshe idanun shi,maganganun ta nayi masa yawa a kunne,sai yanzu yake jin haushin kan shi da ne wanke shegiya da mari ba,inda su Jawad kuwa ana ta kyalkyale dariya tare da maida labari ana fadan yanda idanun Sabeeha suka yi da yace be taba son ta ba,Beel ne ya kusa haukace musu kan akan me ya sanya suka hana shi rama marin da ta masa?Har yar talakawan can ta isa ta mare shi kuma ta mari banza?Wlhh to tunda suka hana shi rama wa su jira su ga abunda zai yi,da kyar suka yi calming din shi down tare da cewa yau ranar celebration ne sun rama abun da aka musu finally sanann sun sanya Sabeeha bakin cikin da har ta mutu ba za ta manta ba,so dole aje party,shi dai FAIZAAN kala be ce da su ba,ganin haka ya sanya suka dawo kan shi wai ko gaske ya fada son ta ne be ji dadin abunda aka mata ba?Inda da sauri yace Allah ya sauwaka kawai yana jin haushi da be wanke shegiya da mari bane,nan Beel yace da shi ya kwantar da hankalin shi ya san yanda zai yi da yar iska tunda bakin ta be mutu ba don ba haka suka so ba,sun so su yi mata tas tayi shiru su tafi aci Tuwo a kan ta a sha miya sai kuma
aka yi rashin dace ta tanka,hakan ne ya sanya Beel cewa zai yi abinda zai rufe mata baki na har abada in junin ta rashin kunya ne za ta ga karshen rashin kunya kuwa,a nan dai aka cigaba da hira har suka iso club din da za su shiga don cin uwar sabadan karaya zuciyar baiwar Allah da aka yi🤧🥺FIK why na💔💔.


Nan kasa tun bayan fitan su ta zauna tayi shiru ta rasa me daya ma ke mata dadi,ji take kamar za ta mutu,inda komai ma na jikin ta ba zallar heart din ta ba ciwo suke mata,bata ma san me daya za ta yi ba,inda take ji kamar ta sanya hannu a kai ta kurma ihu ko za ta ji sanyi da dadin abunda take ji,ta dade nan zaune har aka fara kiraye kirayen magrib har aka shiga aka fito bata san me daya za ta yi ba banda shiru da tayi tare da tsura wa guri guda ido,don neman hawayen ma tayi ta rasa.

Daya daga cikin ma'aikatan ne ta lura da ita hakan ya sanya ta nufan ta cike da ladabi ta dan taba shoulder din ta tace "Madam hope komai lafiya ko?"sai a lokacin Sabeeha tayi firgit ta dawo daga tunanin da bata ma san na miye take yi ba,hakan ne ya sanya ta daga wa matar kai kawai alamun babu komai,ganin haka yan sanya matar cewa za su rufe gurin don yau da wuri za su tashi tun daman FIK reserving whole place din yayi na ranar yau,jin haka ya sanya ta yunkura don mike wa domin ita kan ta bata ga amfanin zaman da take yi a nan ba,ai ko da sauri tayi baya inda matar tayi saurin taro ta tana fadin "be careful Madam take it easy"don kallo daya tayi mata ta gano tana cikin damuwa.

Ganin haka ya sanya Matar kama Sabeeha ta mike a hankali ko takalman ta bata sanya ba,jakan ta kawai ta dauka inda matar ta biye to da takalmi da kudaden da ta gani a kasa,da taimakon matar Sabeeha suka fito inda matar ce ta tsare mata abun hawa tare da sanya Sabeeha a ciki,ta mike mata takalmin tare da kudin a hankali Sabeeha ta girgiza kai tare da fadin

"Na gode and bana bukatar kudaden nan ki rike na bar miki,Malam kai ni Kundila"ta fadi da kyar,matar nan kasa ta duka tana godiya tare da sanya wa Sabeeha Albaraka inda ko kula ta Sabeeha bata yi ba me adaidaita ya ja suka yi gaba,cike da murna matar ta soke kudaden ta tare da komawa ciki

Tayi iya yin ta gurin ganin ta yi kuka amamn ina abun ya gagara,banda nauyi da take ji a cikin kirjin ta a haka har suka iso,inda ta hango Zuhra tsaye a bakin kofa ita da Habeebeey suna hira,fitowa tayi kamar wanda aka jika da ruwan zafi,ko takalman ma ba ta iya dauka ba,ganin halin da take ciki ta sanya me adaidaitan dake dan mutunci ne yace ta bar kudin ta je Allah ya bata lafiya,inda ta taho kamar wata mutum mutumi,daga nesa Zuhra ta hango ta inda ta washe baki tace "Habeebeey ka ga bakin shiga soyayya an samu dawowa sai yanzu,ka ga yar halak yanzu fa na ga maka maganar ta ina cewa ko sai na je nemo ta ashe tana hanya"ta kare cike da farin ciki

Kai Mansoor ya girgiza sanann yace "Habeebtey akwai ki da son gulma wlhy,na san dai tunda kika ga ta dawo to lokaci na ya kare"ta bude baki za tayi magana ke nan ta ga Sabeeha ta iso inda suke a halin da take ciki mamaki ne ya mugun kama ta tare da tunanin lafiya ko dai accident suka yi a hanya to? Ko kula su Sabeeha bata yi ba kai tsaye gidan ta shiga inda direct dakin Zuhra ta shiga ko zama ta kasa yi.

Ganin haka ya sanya hankali a tashe Zuhra tace "Habeebeey ina jin ka tafi kawai za muyi waya,kamar Goofy angel da abunda ke damun ta bari na shiga"murmushi yayi mata sanann yace

"Shike nan Habeebteey ki shiga gida gurin ta don ga duk kan alamu da kwai abinda ke damun ta kama don nima na ga yanayin ta ya canza ba kamar yanda na saba ganin ta ba,ki gaida Mama,ki kuma kula mun da kan ki sai mun yi waya,ina kaunar ki"sam ita ba gane me ma yake cewa take ba burin ta kawai ya tafi ta shige cikin gida gurin Sabeeha,hakan ne ya sanya ta saurin fadin "ka kula kai ma nima ina son ka bye bye"bata jira ya kuma cewa komai ba tayi saurin shige wa gida har tana hada wa da gudu,ganin bata gan ta tsakar gida bane ta kuma san Mama ta shiga makota ya sanya ta saurin fada wa dakin ta inda ta tarar da ita tsaye gaban madubi ta zuba wa kan ta idanu,wata wawiyar ajiyar zuciya Zuhra ta sauke tare da saurin karasawa inda take tsaye hannun ta ta riko a hankali tace

"Goofy angel!"Shiru Sabeeha bata amsa ba haka zalika bata juyo ta kalle ta ba,hakan ya sanya Zuhra cewa "Sabeeha me ke damun ki?Wani abun ya faru a fitan da kika yi ne?Ko hatsari kuka samu ne na ga kin dawo a wani iri ba kamar yanda kika fita kina dariya ba sanann ko takalma babu a kafafun ki,ina takalman naki suke?"ta kare tana kare mata kallo

"Zuhra don Allah ki fada mun Gaskiya akwai abunda nayi lacking na cikkakiyar 'ya mace bata a talaucin da muke fama da shi?Yeah na sani ni yar gidan talakawa ce amman bayan nan don Allah ina da muni ko wani aibin da zai hana wani na miji so na?"ta kare a matukar raunane

Da sauri Zuhra tace "Subhhanalli Goofy angel lafiyar ki kike irin wanann maganar kuwa?Kin taba ganin Halittan Allah me muni?Komai Allah ya hallita me kyau ne saidai mu yan Adam kan kushe halittar sa wanda in an bar ka baka isa yin ko rabin sa ba,sannan babu wanda yake da muni a halittan Allah saidai ki ce wani ya fi wani hasken fata,kyau ko diri,Sabeeha ki kalle ki fa Masha Allah son kowa kin wanda ya rasa Wlhy ni dai ban ga me kyan ki duk fadin garin nan ba domin Allah ya baki duk wani halittan kyau da na kyan jiki da ake nema a gurin mace,Wlhy hatta gwamman garin nan ya aure ki saidai ace shi yayi dace tare da sa'a a masa barka ba dai ke a miki ba"ta kare da iya kan gaskiyar ta.

Cikin sanyin murya tace "Zuhra in har gaskiya ne abunda kika fada to shi me ya sa yace be taba ganin me muni na ba?Zuhra me ya sanya yace da ya zauna da ni a matsayin mata gwamman ya auri dan uwan sa na miji,domin bani da kyau balle tsarin matan da zai yi sha'awa har ya aura yayi rayuwar aure da ita,Zuhra me na rasa don Allah?"ta kare tana kallon kan ta da kyau tare da juyowa ta kalli Zuhran don ta kare mata kallo da kyau ta fada mata gaskiya, kai Zuhra ta girgiza tare da riko ta gam

"Sabeeha kin fara bani tsoro Waye ya sanar mike da duk wannan maganganun?Ko kuma fitan ki kin yi gamo ne da Aljanu shine duk suka firgita ki haka?Ni kam ba mun rabu kan za ki ganin FIK bane?Ko ba ni na raka ki kika shiga mota saida na ga tafiyar ku na dawo gida ba?Ina shi FIK din yake ko dai hatsari kuka samu hanyar dawowar ku ko kuma wani abu ne ya same shi?Ina shike don Allah kila shi ya fada mun abunda ke damun ki tunda ke kin kasa fada mun"

Ai kawai sai ji tayi Sabeeha ta fad jikin ta tare da fashe wa da wani irin kuka me tsuma ran me sauraro duk wanda ya ji kukan ya san daga can kasan zuciya kukan ke fitowa,me yin san kuma yana cikin tsantsan damuwa a razane Zuhra tace

"Inalilhi wa ina ilaihi raju'un Sabeeha don Allah ki daina tsinkar mun da gaba,ni kam ko mutuwa FIK din yayi ne?"cikin kuka Sabeeha tace "Ba mutuwa yayi ba Zuhra amman a guri na FAIZAAN ya mutu na har abada"ta kare tana kuma fashe wa da kuka inda ta rungume Zuhra kam tana rera kukan a jikin ta,in hankalin Zuhra yayi dubu to ba shakka yau duk sun tashi,Jan Sabeehar tayi tare da nufan kan katifa da ita,inda ta zauna tare da zaunar da ita don lura da tayi Sabeehar na iya faduwa any moment from now don ganin yanda kafafuwan ta ke rawa a raunane tace

" "Don Allah ki nutsu ki daina kukan nan, kiyi mun bayani yanda zan fahimta me ke damun ki",dagowa tayi idanun ta na zubda kwalla tana jin zuciyar ta nayi mata zafi tare da tsanan ta bugawa,ko kadan bata taba hasaso irin wanann ranar ba a rayuwar ta,wai yau ita ce ke zubda hawaye tana kuka akan 'da na miji,ita ce ke kuka akan Soyayya!!ita ce ke kuka kan Da na miji ya karya zuciyar ta,wai shin daman haka zafi da dacin so yake??? Ashe haka mata ke ji a duk sanda saurayi ko mijin su ya yaudare su?Ashe haka ne soyayar?Daman haka radadin da ake ji ke nan a duk sanda aka yaudari zuciya?Shine abubuwan da ke ta kai kawo a cikin ran ta.

Inda da kyar ta iya budan baki tace "Zuhra!!Zuhra are you happy now🥹in ce yanzu kin yi farin ciki?kullum baki da zance da ya wuce in fada soyayya,ki ba wane chance,at the end kin sanya na fada Soyayya gashi tun ba a je ko ina ba ya yaudare ni ya karyan zuciya!! Zuhra I have finally fallen in love and got my innocent little heart broken and shattered into million pieces duk zama na da shi ashe wai be taba So na ba,Zuhra ashe wai be taba kauna ta ba,for all this while ashe ba so na yake ba WASA DA SOYAYYA ta kawai yayi Zuhra just to get back at me,Zuhra wai ashe duk wannan soyayar da ya mun so yake yayi winning Dare din da suka sanya shi da abokan shi,can you believe this akan Rolex ya zabi ya karya mun zuciya Zuhra 🥹🥹,Me yasa me yasa wasu Mazan ke WASA DA SO NE??🥹Me yasa suke daukan Zuciyar mace matsayin Riga su sanya sanda suke so su cire sanda suke so??Zuhra fada mun miye laifi na don na so shi,me nayi masa da na cancanci irin wanann hukuncin daga gare shi,Meye laifi na??Wlhy Zuhra da gaske nake son shi,da gaske na kamu da soyayyar sa,laifi na daya don ina son shi da gaske ashe shi da wasa yake yi Zuhra me nayi masa?Wlhy zuciya ta zafi take mun,ji nake kamar zan mutu,ki taba kirji na Zuhra taba ki ji yanda take bugawa ina jin kamar zuciya ta za ta fado,Wayyo Allah na,ashe daman haka ake ji in aka yaudare ka?"ta kare tana sakin wani irin marayan kuka me mugun tsuma zuciya.

Gaba daya kan Zuhra ya kulle domin kwata kwata bata san inda zantukan Aminyar nata suka dosa ba,sun rabu lafiya tana farin ciki da dauki  akan yau zata baiyana wa FIK SIRRIN ZUCIYAR TA,yau tayi niyar sanar da shi dumbin soyayyan da ta ke masa,ganin yanda ya dade yana bibiyan ta tare da kasakantar da kan shi a gare ta duk da kasancewar shi dan gidan masu kudi,ita kanta sheda ce yanda Kawar nata tayi ta basar wa tare da kin amsan tayin soyayyan shi don ganin ko kadan ba su dace ba,sanann duk makarantar babu wanda be san Waye shi ba,amman da dadin baki da kasakantar da kai saida ya san yanda yayi ya jawo hankalin ta,abinda bata taba yi ba a rayuwa ta wato fadawa soyayya sai gashi wai yau kuka take wiwi wanda ko sanda Adda Nawwara ta rasu bata ga tayi irin wannan kukan ba,tabbas da ta san abinda zai faru ke nan da bata shige masa gaba ba gurin ganin ya samu zuciyar kawar nata,at times har fada suke yi ganin yanda take nuna halin ko in kula a gare shi,gaba daya kan ta  ya kulle in ta fahimta daidai kamar FIK yayi wa kawar nata halin su na maza,to ina tulin soyayayn da yake mata?ina kuka da wuni a kofar gidan su da ya ke yi?saida ta yarda ta bude zuciyar ta ta sanya shi ya zabi ya wulakan ta ta,rungumo ta tayi a kirjin ta suka cigaba da rera kukan tare domin tun suna yara damuwar daya na daya ne,and duk sai take gani kamar laifin ta ne don ita tayi ta pushing din ta kan sai ta so shi,sai ta ke jin duk ta ma bi tsani kan ta,saida suka sha kuka sosai idanun su yayi ja har muryan Sabeeha na toshe wa kafin Zuhra ta koma tana lallashin ta,inda cikin kuka Sabeeha ta kwashe labari from A to Z ta sanar wa Zuhran ba tare da ta boye mata komai ba,inda in ran Zuhra yayi dubu duk sun baci,ta tsine wa Rocket gang ya fi kwando dubu dari biyar,tare da yin Allah wa dai da su,inda tayi danasani tare da daura wa kan ta laifin komai don garin yaya ta bari suka yi fooling din ta har ta basu number din Sabeeha,sai yanzu take nadama da danasanin rashin daukan maganar Sabeeha da basu yi ba serious,baiwar Allah tun day one taki taki amman saida ta san yanda tayi ta shawo kan ta har ta yarda ta fara son shi,miye sa FAIZAAN zai yi haka?Ribar me zai samu gurin karya zuciyar kawar ta,banda hauka irin nashi wa ya ce da shi ana wasa da soyayya?Waya ce masa ana wasa da zuciyar mutum?Wlhh da za ta gan shi sai ta wanke fuskan shege da mari ne dan karan zafi,tare da fada mishi maganar da ke ran ta,tana nan rungume da Sabeeha inda har yanzu bata daina kuka tare da fade fade ba,addua Zuhra ta shiga tofa mata tare da shafa kan ta da bayan ta,tun tana jiyo sumbatu da sheshekan ta har ta fara jiyo saukan numfashi da ajiyar zuciyar ta alamun bacci ya dauke ta.

A jikin ta Zuhra ta gyara mata kwanciya tare da tsura mata idanu yanda fuskan ta yayi fayau lokaci guda,idanun ta ba karamin kumbura suka yi ba,haka zalika fuskan ta,kallo da ya za ka mata ta baka tausayi,inda take sauke ajiyar zuciya da numfashi alamun ta ci kuka har ta gode wa Allah,a hankali Zuhra ta cigaba da nata kukan domin ko mutuwar Nawwara bata ga Sabeeha ta shiga wanann halin ba,kai ta yarda soyayya masifa ce,Wlhy da ta san abunda zai faru ke nan da bata shige wa shegen yaron nan gaba ba,abun haushin ma da Sabeehar ta fara son shi,yau da ace bata kamu da son shi ba da komai zai zo musu da sauki,sama ta kalla a hankali tana hawaye tace "Ya Allah an zalunci baiwar ka,kai kace babu hijabi tsakanin ka da adduar wanda aka zalunta,ya Allah ka saka mata Allah ina rokon ka duk wani nutuswa da sanyin zuciya Allah ka saukar wa Sabeeha ta,Allah ya bata juriya da hakurin daukan wanann kaddarar da ya zo mata,shi kuma Allah kai ka san yanda za kayi da shi Allah ka bi mana hakkin mu"ta kare tana kuka.

Sai around 9:30 Sabeeha ta samu ta farka da wata naunauyan ajiyar zuciya,kallon ta Zuhra tayi tare da sake mata murmushin karfin hali tace "kin tashi goofy angel,sannu ya kike jin jikin naki yanzu?In kawo miki abinci za ki ci?"

Cikin zubda hawaye tace "Zuhra har yanzu zuciya ta zafi yake mun,Wlhy sai ina ji kamar ana danne mun numfashi na kirji na kamar zai fado,bana sha'awar cin komai"hannu Zuhra ta sanya tare da goge mata hawayen ta

"You are stronger than this my love you can fight this okay,don FAIZAAN yayi miki haka ba shine yake nuna karshen rayuwa ba,kowa na gari yayi don kan shi ne,don Allah stop crying kin ji,kukan ki na daga mun hankali wlhh in hada miki ko tea ne ki sha sai na baki PCM na san kan ki zai yi ciwo sai ki sha ki samu ki kwanta"

Girgiza mata kai tayi sannan tace "za ki iya kai ni gida yanzu?Ko ki kira Umma ta zo ta dauke ni,daman yar mace ne ni kin ga dole ita za ta mun komai,ina son ganin Umma ta,Zuhra ina son na rungume ta na ji dumin jiki ta,ina son na bata hakuri kan zagin da na ja aka mata"saurin rufe mata baki Zuhra tayi da tafin hannun ta

"Shhhhh Sabeeha ya isa haka ki daina kuka da irin maganganun nan pls,wai ko kin manta ke kike adawa da mata masu kuka akan saurayi ya rabu da su?Nan kike fama da ni kullum in ina kuka akan Mansoor yanzu FAIZAAN har ya kai ki zubda hawayen ki a kan sa"

Cikin kuka tace "Zuhra a lokacin da na fadi haka ban san so bane,ban san haka zafi da radadin shi yake ba,wlhh da na sani da duk wanda take kuka ni zan taya ta da kai na,ba kan shi nake kuka na Zuhra kuka nake garin Yaya na tsaya har yayi playing dina"a raunane Zuhra tace "Ke Musluma ce na san sarai kin san kaddara,and kin yarda da ita akwai kaddara me kyau da kuma mara kyau,Allah kuma na jarrabaar bawan da ya ke so ne,so ki dauki wannan matsayin jarabawa,and tunda kika riga kika hada shi da Allah to ki jira randa Allah zai dauka miki fansa don am sure adduar ki ta karbo,don Allah ki daina kukan nan kin ji,yana can tana jin dadi ke kina nan kina kokarin kashe kan ki,in kika mutu nayi Yaya da rayuwar ta?"itama ta kare tana kuka,saida suka sha kuka nan ma sosai sanann Sabeeha ta dage kan lalle gida za ta tafi,babu yanda Zuhra bata yi ba kan su kwana a nan ta bari sai gobe amman ina taki yarda sam,saida ta cire abayan domin daga shi har komai na shi ta tsana tare da maida kayan da ta zo da su sanann Zuhran ta riko ta suka fito,cewa Mama tayi Sabeeha ba lafiya za ta maida ta gida sanann za ta kwana can don taya Umma kula da jikin nata,inda Mama tayi mata Allah kara sauki sanann suka fita.

Cikin rahma na ubangiji kuwa suka samu abun hawa inda ta sanya ta ciki sannan ta shiga ta janyo ta tare da kwantar da kan ta a kirjin ta,a haka har suka iso tana jikin ta,Zuhra ta biya kudin sanann suka shige,dadin abun ma babu wuta ko wace shegiya na daki,don tun randa wancan abun ya faru aka daina zaman gulma da munafurci.

A kofar suka tarar da Umma tsaye hankalin ta a matukar tashe don yanzu take da shirin zuwa gidan su Zuhra neman Sabeehar don bata taba yin dare har haka ba,da ganin su kuwa tace

"Ya Rahma Zuhra sai yanzu,Auta bana hana a fita a yi dare ba?Shine kika dauko Zuhra don a rufe mun baki wai"ta kare tana hararan su,jikin ta Sabeeha ta fada tare da fashe wa da wani irin kuka me cin rai,a rude hankali a tashe Umma tace

"Na shiga uku ni Bilki Inalilhi wa ina ilaihi raju'un,Sabeeha wani abun aka miki?Me ya same ta Zuhra?"ai kawai Zuhra itama sai ta sa kuka,inda Suka kadar wa da Umman nutsuwa da hankali,inda a rude ta shiga tambayar su lafiya kukan na miye?Wani abun ne ya same su,don a halin da Umma ta gan ta dauka take ko dai an samu wani mara imani da tsoron Allah ne ya taba mata yarinya,don Wlhy tunani take ko dai Fyade aka yi wa Sabeehar,ganin kukan nasu ba na kare bane kuma suna cigaba da saka taba damuwa da zulumi,ya sanya Umma daka musu tsawa "za ku daina kukan nan ku sanar da ni abunda ke faruwa ko sai na ci Uban ku,kuna hauka ne ina tambayar ku kuna kuka so kuke sai nawa zuciyar ta buga ko me"ta kar a tsawace

Hakan ya sa cikin shesheka Zuhra ta karanto wa Umma duk abunda ya faru daga A har Z bata boye mata komai ba wani jiri ne ya zo wa Umma amman tayi saurin rike  kan ta,kallon su tayi duk su biyun sanann ta zaro Sabeeha a jikin ta tana kallon ta cike da tausaya wa don tunda ta ke da ita bata taba kuka irin haka ba,duk sai ta bata tausayi tabbas ta san soyayya ta kuma san zafi da radadin da ake ji in an rasa abunda ake so,amman kuma tayi mamaki sosai da jin abinda FAIZAAN yayi lalle dan Adam kayan Allah,yanzu daman yaron nan mugun nufi ya zo da shi har ta kusa yi wa yar ta magana mara dadi akan shi,ta matsa wa Auta duk don ta karbe shi taki ta ki amman saida ta san yanda aka yi ita da Zuhra su ka shawo kan ta,daman ba yaron kirki bane ashe fuska biyu gare shi,saurin maida hawayen ta tayi sanann ta shafa kan Sabeeha tace

"To shine me in ya rabu da ke ko yace WASA DA SOYAYYAR KI yayi?Shine me in ya zage ni?Shine me in ya rabu da ke?Umman ki na nan tare da ke daga yau har ranar da za a nade duniya ba za ta bar ki ba,miye na kuka?Akan me za ku na zubar da hawaye akan abunda be kamata a masa tunani ba ma balle kuka?Kowaccan ku ta goge idanun ta Zuhra kai mun ruwa bandaki ke kuma Auta mu je ki cire kaya maza kiyi wanka"ta kare tana jan hannun Sabeeha daki,kaya ta cire ta mika mata zani ta daura sanann ta kai ta bandaki tana tsaye a waje ta gama
Wanka ta fito,inda Umma da kan ta ta shafa mata mai tare da taya ta saka kayan bacci sanann ta hada musu shayi me kauri ta mika musu "bana son musu kowa ta shanye kofin shayin ta"ta kare babu alamaun wasa a muryan ta.

Ba don  Sabeeha na jin dadin shayin ba don Umma dai ta kafa kai tare da fara sha,saida Umma ta tabbatar sun shanye tana kokarin yin amai ma Umma tayi saurin rike ta tare da shafa bayan ta,saida ta ga ya wuce sanann ta balla musu PCM ta basu suka hadiya sanann tace  "bana son na ji kun ce komai sanann ko hawaye ban yarda ku zubar ba don babu amfanin shi,tunda a nan za ki kwana Zuhra ku kwanta kuyi bacci maza,Allah ubangiji yayi muku Albaraka ya kuma hada ku da abinda ya fi Alkhairi a rayuwar ku,duk abunda ka samu daman rabon ka ne in kuma ka rasa to daman can Allah ya rubuta ba naka bane,Sabeeha ke musulmace kuma me addini,kin kuma yarda da kaddara don haka kar ki budulce wa Ubangijin ki,kuka ba shi da amfani banda ya kara maka ciwo,and na bar ki kin yi don ki samu ki damuwar ta ragu miki,Uwata Muhammadu ba shine karshen duniya ba,don Allah ki cire damuwa kiyi bacci in kina son hankali na a kwanta,Allah ya muku Albaraka kuyi bacci zan tashe ku da asuba"ta kare tana gyara musu bargo tare da daukan wayan Sabeeha ta sanya musu karatun Alqurani sannnan ta fice daga dakin.

Alola tayi sanann ta shige daki ta shimfida abun sallah,nan fa ta fara nafila sai a lokacin ta sake kukan da take ta kokarin rike wa,ba karamin karya mata zuciya ganin Sabeeha a haka yayi ba,ta bata tausayi ba na kadan ba ace farkon fadawar ka soyayya kuma ya kare haka,tayi blaming kan ta tayi kuka sosai wanann daran sai take a kamar duk lafin ta ne haka ya samu Sabeehar,inda daga karshe ta yi ta kuka wa Allah tare da rokon shi kan ya sassauta musu wanann irin jarabawar domin ita nata jarabawan kan yaran ta ne,hakan ma akan maza a farko na miji ne yayi sanadin mutuwar ta sanann yanzu na miji na neman kai mata diya rami,har yanzu ta kasa yarda har yanzu wai Muhammad yaron da ke zuwa ya wuni yana mata magiya kan ta bashi Sabeeha shine yayi musu irin wanann diban albarakan lalle na miji munafuki ne,gani yanda ya mai da kan shi Wawa har Umma na jin haushin Sabeeha kan tana wulakanta shi ashe ya shirya mugun nufin shi a ran shi ne,wanann daran duk su uku basu iya bacci ba,Umma kwana tayi tana kai kukan ta gurin Allah,while Zuhra da Sabeeha kowa da zancen zucin da yake yi tunda Umma tace kar suyi magana a haka bacci barawo yayi awun gaba dasu sai sauke ajiyar zuciya suke ta faman yi.

            A month later

Ba karamin kokari da jarumta Sabeeha tayi ba bayan faruwar haka,domin Umma da Zuhra a tsaye sauke a kan ta kullum cikin lallashi  addua tare da kwantar mata da hankali suke,saidai ta kara koma wa shiru shiru duk da can din ma daman ba wai maganar ta dame ta bane,inda ba wai ta manta bane ko abun baya mata ciwo amman tayi kokarin danne wa ko don lafiyar Mahaifiyar ta,tunda yanzu har tana murmushi,zama tayi ta duba ta ga miye amfanin ta sanya kan ta a damuwa shi da yayi soyayyar karya ka ya cigaba da rayuwar shi sai itace za ta boye kan ta miye laifin ta to?Hakan ya sanya ta daukan duk wani abunda ya shafe shi ta hade su guri guda za ta kona Umma ta hana ta,Alhamdulilah yanzu har abinci tana iya ci don su kan su Umman ma sun yi mamakin jarumtar da tayi hakan kuwa ba karamin dadi yayi musu ba.

Tunda abunda  ya faru bata kuma shiga School ba sai yau domin a yau ne za su fara jarabawa,hakan ya sanya tun safe take shirin shiga makaranta,domin akan su kam ba za ta ki zuwa makaranta ta ki zana jarabawar ta ba,cikin shigar mutunci ta shirya inda tana sanye da hijab din ta har kasa ta hado kayan bukatar ta sanann ta je yi wa Umma sallama,Nasiha sosai Umma tayi mata tare da bata shawaran kar ma ta nuna ta san shi ko sun ce za su tsokane ta kar ta tanka su in sun gaji za su bari ai shi tsokana baya fitowa a jiki,cike da jin dadi tace da Umman in sha Allah hanyar da suka bi ma ba za ta bi ba,inda Umman ta mata adduoi sosai tare da mata fatan nasara sanann ta dauko dubu daya ta mika mata kan tayi kudin abun hawa da shi,godiya tayi wa Umman sanann ta fito a hankali take kallon wajen tana tuno memories din da suka yi having da FIK hawayen ta tayi saurin maidawa sannan ta tari me adaidai tace ya kai ta BUK.

   Hankali a matukar tashe,jikin  ta har na karkarwa gurin kiran wayar kawar nata,ganin kiran Zuhra na yawo akan screen din ta ne,daidai lokacin sun iso bakin gate ya sanya ta sakin murmushin da ta mance rabon da tayi shi,dauka tayi cikin siririyar murya tace "Goofy angel"wata wawiyar ajiyar zuciya Zuhra ta sauke sanann a matukar rude tace

""Goofy angel kin shiga wani kafar social media yau?"idanu ta dan lumshe sanann tace "Zuhra wayar ma don ta zamo dole nake rike wa amman rabo na da wani media tun last month I think,me ya faru?"wata wawiyar ajiyar zuciya Zuhran ta sauke daman abinda take tsoro kar ta shiga Media ta ga abinda ke Treading....

Jin tayi shiru ne ya sanya ta fadin "Kin yi shiru,kina ma ina ne gani a kofar gate din school,yanzu isowa ta"da wani irin firgita Zuhra tace "Goofy angel kiyi wa girman Allah kar ki shigo cikin makarantar nan,go back home gani nan fitowa nima zan same ki a gida don Allah ki ce wa me adaidaitan da ya kawo ki ya maida ki gida gani nan zuwa"ta kare tana yarfa hannu.

Dan tsaki Sabeehar ta ja sanann a sanyaye tace "dadi na da ke Zuhra hauka,zan yi ta zama indoor ne har depression ya kashe ni??Exams dina kuma wa zai rubuta mun??Kee in tunanin ki kan wancan Coward din ne am over him since,ko na gan shi Wlhy ba zan ma nuna na san shi ba,in kuma tsokana ta yan gang din su za suyi Zuhra suyi su gaji,magana baya tabo a jiki,akan Soyayyar karyar da ya mun ba zan kashe kaina na fasa karatu na ba,don haka ki fada mun a ina zan same ki gani nan shigowa"

A matukar rude Zuhra tace "Ba za ki fahimta ba Goofy angel ba za ki gane ba,don Allah kar ki shigo ki taimake ni ki koma gida,nace miki yanzu.....hello!!hello!!"shiru ta ji alamun an kashe wayar

Da idanu Zuhra ta bi wayar da kallo tare da dafe kai tana furta "Inalilahi wa ina ilahi raju'un Goofy angel why baki jin magana ta,yanzu ta ina za ki iya facing duk makarantar nan bayan abinda ke trending a ko wace page din sadarwa,Wlhy duk wanda yayi wannan abun Allah ya isa ba za  mu taba yafewa ba"ta kare a raunane tana hawaye hankalin ta a matukar tashe ta mike daga cikin class tare da saurin fitowa don tare kawar nata daga shigowa makarantar.

Tafiya kawai take cikin sauri tana hadawa da gudu gudu gudu har ta nufo bakin gate inda suka ci karo da Sabeeha tana shigowa cikin makaranta,cikin sauri Zuhra ta nufe ta tare da kamo hannun ta

"Ke lafiya na gan ki a rude haka?Ko wani abun ne ya faru?"Sabeeha ta fadi tana kare mata kallo,cikin sauri Zuhra tace "Goofy angel babu abinda ya faru amman ki koma gida don Allah kin ji,bari na tsare mana abun hawa mu koma gida"

Hannun ta Sabeeha ta fauce sanann tace "Ke Wlhy zan ga sanda za kiyi hankali wai na koma gida akan miye ne wai?Tunda na tambaye ki kin ce mun ba komai to Wlhy babu inda zan koma na dauka za ki fi kowa farin ciki da dawowa ta sch amman wai ke kike ce mun na koma gida,to exams din wa zai zana mun?Ko dai kin ga banzayen nan ne duk hankalin ki ya tashi kike tsorata?To Wlhy ni basu isa su mun komai ba na Riga su nace Allah kuma babu abinda zan ce da su so ki wuce mu shige cikin sch kar muyi late"

Babu yanda Zuhra bata yi da Sabeeha ba kan ta duba girman Allah ta koma gida amman Sabeeha sam tace bata san zance ba,a haka suka shigo cikin school din inda a take idanu ya koma kan ta,inda masu nuna ta nayi masu zind'en ta suna yi,masu zagi duk gasu nan,kan ta ya kulle gaba daya don ta rasa gane miye a tattare da ita na zagi da dariya har haka da kuma
nuni,fiye da wata bata shigo school ba kuma ma harkan kowa take shiga ba to lafiya me ke faruwa da ita??.

Wani matashi ne da ba zai haura 24 ba shi da friends din shi suka nufe su inda Zuhra tayi saurin kamo hannun ta za ta ja ta su bar gurin da sauri yaron ya riko hijabin Sabeehar cike da iskanci yace "Ke munafuka ina kuma za ki kai ta?"a fusace Sabeeha ta fauce Hijab din ta tare da galla masa harara

"Ba zan zage ka ba tunda ga dukkan alamu tarbiyan yayi maka karanci amman ka sani in hannun ka ya kuma kuskusran taba ni to Wlhy sai na zamo night mare din ka"ta  kare tana watsa mishi kallon banza dariya yaron ya sheke da shi sanann yace

"Ke dai Wlhy anyi cikkakiyar mara kunya har wai ke kike maganar wani be san tarbiyya ba?Ke gidan uban wa kika san tarbiyya?Ai Wlhy an yi walkiya an ga kowa da ma cire wanann Hijabin kika yi don babu amfanin shi domin kowa na cikin makarantar nan kallon fanko yake miki,amman Wlhy babu karya kin hadu ashe abunda ya sanya kike rufe surar ki ke nan,Gaskiya kallon farko da nayi wa wanann irin body naki saida nayi wankan tsarki,Bura uba amman Gaskiya ke gwana ce a harkan sarrafa na miji,Gaskiya duk sanda kike son kara sakin wata video din naki don Allah ki kira ni muyi tare don ba karya na san za kiyi dadi,wancan shegen ba karamin kaya ya kwasa ba Wlhy"ya kare yana tande baki,tsaban mamaki ma Sabeeha ta kasa cewa komai ganin haka ya sanya Zuhra saurin Jan hannun ta suka yi gaba,inda duk wanda suka hadu maganganu mara sa dadi suke fada wa Sabeeha wasu suyi Allah wadai da ita wasu kuma su fada mata maganar batsa tare da mata tayin kan su,can bayan classes Zuhra ta ja ta tana kuka inda Sabeeha a rude ta kalle ta tace

"Zuhra kai na ya kulle don Allah sanar da ni meke faruwa?Wai me ya faru don Allah mutane ke mun maganar banza haka?"ta kare hawaye na taruwa a idanun,zuciyar ta na bugawa da sauri inda tsoro yayi mugun lulube ta.

"Ki kwantar da hankalin ki goofy angel ki rabu da su ba fa komai bane,kila su Faizaan ne suka fada musu wani abun"ta kare tana hawaye,kai Sabeeha ta girgiza sanann tace "Aa Zuhra karya kike mun Wlhy akwai babban abu ne ma ba karami ba,in har babu komai kukan me kike yi?baki ji me suke fada bane yar iska fa suke kira na,dole Wlhy da wani abu a kasa ki fada mun don Allah kar zuciya ta ta buga"ta kare a raunane

"Babu komai Goofy angel kin ga ba lafiya ta ishe ki bane,don Allah kar ki sa komai a ran ki,da akwai da ni da ni da kaina zan sanar miki"cikin tsawa Sabeeha tace

"Karya kike Zuhra Wlhy idanun ki ma sun gwada mun karya kike,in kina kaunar Allah da Manzon shi ki fada mun me ke faruwa?In kina son iyayen ki to kar ki boye mun komai ki sanar da ni duk abunda ke faruwa don Allah"ta kare a raunane.

Ai sai Zuhra ta fashe da kuka cikin kuka tace "Sabeeha tun cikin dare aka saki video din ki inda yanzu haka shi ke ta trending daga jiya zuwa yau mutanan da suka gani ban san adadin su ba,Wlhy kuma ban san Waye ya saki video din ba don ni kam
ma turo mun aka yi personally"ta kare tana kuka.

Da kyar Sabeeha ta iya budan baki zuciyar ta na bugawa tace "Video???Video na kuma wani irin video ke nan har zai sanya ana ce mun yar iska?Kina da Video din ina ce nuna mun na gani"ta yi karfin halin fadan haka,da sauri Zuhra tace "aa Sabeeha ba zan iya nuna miki ba na san Wlhy karya ne kawai hadawa aka yi ki bar shi ba sai kin gani ba"

Hannu Sabeeha ta mika mata "bani wayar taki ki sa mun video din na gani,tunda aka kai na ne kowa ma ya gani balle ni,samun Zuhra ina son na gani don Allah"ba yanda Zuhra bata yi ba kan Sabeeha ta bar batun video din nan amman sam Sabeeha ta nace kan sai an nuna mata,hakan ya sanya  Zuhra bude wayar tare da shiga mata video din ta mika mata wayar.

Idanu Sabeeha ta zaro a daidai lokacin da Video din ya fara playing tare da saurin rintse idanun ta tana fadin "Inalilhi wa ina ilaihi raju'un,Zuhra na shiga uku na Allahuma ajirni fi musibatin Wlhy tallahi ba ni bace,Zuhra ba ni ce ba"ta kare tana yin baya luuuuuu tare da faduwa da sauri Zuhra ta riko ta tare da rungumo ta tana fadin cikin kuka

"Na sani Goofy angel ba ke ce ba Wlhy ba halin ki da tarbiyan ki bane haka,Sabeeha talk to me kin ji ki kwanatr da hankalin ki Allah zai wanke ki"shirun da ta ji ne ya sanya ta saurin kallon ta ganin babu alamun numfashi a tattare da ita ne ya sanya a rude tace "na shiga uku Goofy angel don Allah kar ki mun Haka ki tashi don Allah,tashi don Allah kar ki mutu"ta kare tana kuka hankali a tashe tana girgiza Sabeehan da ko motsi bata yi,ganin fa halin da suke ciki in ta tsaya kuka ba inda zai kai su ya sanya ta dauki wayar ta tana kuka ta kira Mansoor tare da sheda masa Sabeeha fa ta fadi tana tsoron kar dai ta mutu,da kyar Mansoor ya kwantar mata da hankali tare da ce mata bari yanzu ya karbo motar makocin su yanzo su kai ya asibiti in sha Allah babu abinda zai same ta..............

    
     Ayi mun afuwa da typing errors,ban yi editing ba wlhh kuma Keyboard dina na bani matsala.

  In sha Allah Saura 1 page book one ya kare inda sai bayan Azumi kuma in me kowa me komai ya so ina godiya da kauna da adduoin ku a gare ni Allah ya saka ya kuma bar zumunci.

😂🤧💔Yan team Sabeeha ina me muku jajan abunda ya faru,yarinta ke damun FAIZAAN don Allah a masa uziri kar a zage shi da yawa ya kara daidaicewa🫣🫣Ina kuma fatan Allah ya ba wa Sabeeha lafiya.

A karshe kuma ina yi wa kowa fatan Alkhairi ❤️.

Continue Reading

You'll Also Like

54.9K 7.2K 78
"Se refiere a la belleza de corta duración de la flor de cerezo" ╰──➢ Advertencias ✧ ⁞ ❏. Omegaverse < SLOW BURN ⁞ ❏. Todoroki Bottom! ⁞ ❏. Smu...
179K 8.8K 42
After going through a number of disasters I realized that actually I am reborn as the villainess character, more of a brat, Chloe Bourgeois, in a chi...
615K 8K 32
Lost, Lose (Loose Trilogy #1) She's a girl of hope, Lisianthus Yvonne Vezina. A teen-year-old girl who focused on her goal... to strive. But everyth...