A SIMPLE DARE (WASA DA SO)

By marteybee

431 7 16

More

new book
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page ten
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 20/21
Page22/23
Page 24/25

Page 19

16 0 0
By marteybee

✨✨

SIMPLE

DARE

✨✨

(WASA DA SO)

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MEEMARH)

✨ _*GORGEOUS WRITERS FORUM*_ ✨

✨ _*G.W.F*_ ✨

_*HOME OF GORGEOUS, INTERLLIGENT,AND EXPERT WRITERS,WE THE BEST AMONG THE REST*_

Kofa a bude take ga duk me son yin joining group dina😌,Amman Hajiya don Allah in kin san ba yin comment ko karanta littafi na zai kawo ki ba I beg you in the name of Allah kiyi zaman ki ba sai kin shigo ba!!haka zalika wanann group din na mata ne zalla don Allah Maza should stay away from my group👏

My What's app group link👇🏻

https://chat.whatsapp.com/EUrVVaKJnIBDTlQsxurZv0

Bismillahi Rahmanin Raheem............

( In the name of Allah the most beneficient,the most merciful)


Kofa a bude ta ke ga duk wani me good quality product da ya ke son Advertising ɗin shi,as Kaya masu kyau,da inganci (TALLAH) should contact me via :
08100046388

Page 1️⃣9️⃣

TALLA!!TALLA!!TALLA!!!

https://chat.whatsapp.com/ImtxMSS1tuSKqvBpPqc03P

Assalamu'alaikum sisters🤗
KAMSHI* mace Mai kima, mace Mai daraja, mace Mai izza, mace Mai aji itace tasan darajan kamshi, if your perfume is not unique hajiyata you're just using ordinary air freshener🤣, hajiyata ko nawa Zaki kashe indai a turare ne baki Fadi ba😘 matan da suka gane suka San yanda zasu kankaro da martabar su, suke amfani da turare, a *BAKHOOR BY FAIXY* Zaki Sami Main chic, Bachelor, Husband snatcher, Her royal sexiness, Mysterious girl, Pleasure, Boovilous, White khumra, Maroon khumra, Black khumra, Hair perfume, Turaren wanka, Turaren wuta, Turaren tsuguno, Turaren mopping,Turaren carpet Shu'umat khumra,and more, yar uwa kar kibari abaki lbr, (wholesale and retail) WhatsApp 09067621681, siyan na gari Maida kudi gida🥳

Instagram @Bakhoor_by_faixy

******************************

Ko bayan tafiyar FIK Umma ta so magana da Sabeeha don ba karamin tausayi yaron ya bata ba,and ta matukar yaba da Kamala da hankali irin nashi,domin har kasa kamar zai shige cikin ta gurin gaida ta,ta kuma ji dadi inda lokaci guda ya dauke ta matsayin uwa har ya iya sanar da ita duk abinda ya faru sanann ya kare da neman yafiya tare da nuna mata tsantsar nadamar shi,nan Umma cikin dabara da siyasa ta masa nasiha me kama jiki,sanann tace tambaye shi dan gidan Waye shi?Waye Mahaifin sa?Be boye mata komai ba inda ya sanar da ita shi dan gidan Isma'il Kwairanga ne,saida gaban Umma ya fadi jin dan hamshakin Attajirin me kudi ke wanann naci akan Sabeeha ita ba diyar kowa ba,inda ganin kamar hankalin Umman ya tashi ne ya sanar da ita shi Wlhy son Sabeeha yake sanann arziki da talauci Ai duk na Allah ne,sosai jikin Umma yayi sanyi inda bata mance ba saida tayi mishi fada kan barin kudin da ya ringa yi musu,ya gwada shi babu komai Wlhy akwai ne ya sanya yayi sanann akan Sabeeha ko ran shi ne zai iya bada wa shi dai burin shi kawai ya same ta a matsayin mata sanann ta yafe masa abunda yayi mata da har yau take kallon shi da shi,sun yi hira sosai inda Umman ta gasgata maganar Zuhra ba shakka mutumin kirki ne (Kuskuran wasu iyayen ke nan saurin yarda duk a ance wai gane halin mutum ko sanin mutum sai Allahn da yayi su,blindly Umma ta amince da FIK tare da kaunatar shi ba tare da sanin mugun nufin da yake neman diyar ta da shi ba,one thing da Uwa shine in kana son ka shiga ran ta to ka gwada kana son nata a nan take za ta yarda da kai ta kuma so ka kamar nata,Allah ya tsare mu sanann ya hada yaran mu da abokan zama na gari),Tabbas bata ji dadin abunda Sabeeha tayi masa ba,ko ba komai sai ya ci darajan tana zaune a gurin,banda abun Sabeeha da ba a yafiya da waya ce mata za a kawo iyanzu?Ta rasa gane wanann mugun fushi da riko da Sabeeha ta k'oyo don ba za ta ce gadon shi tayi gurin ta ko Mahaifin ta ba,don daga ita har Abban su tare da Margayiya Nawwara ba su da irin wanann fushi da riko irin na Sabeeha,ta so samun ta suyi magana ta sanar mata abun da tayi bata ji dadin shi ba,amman sai ta hana kan ta,tare da daukan shawaran bari ta zuba wa Sabeehar ido,don ta ga alamun har yanzu girman ne amman hankalin kam da sauki,da wanann shawaran ta shige daki,inda Sabeeha bayan tayi wanka ta zo dakin suka sha hira tare ma suka ci abinci ko a fuska Umma bata nuna mata tana son magana da ita ba,balle ta nuna mata abinda tayi bata ji dadin sa ba,inda Sabeehar ce ma da kan ta tace da Umma kan kar ta kuma sauraran FIK mayaudari ne kuma makaryaci,inda Umma ta girgiza kai kawai tace "A yaushe kike zauna da shi har za ki fahimci halin shi?Balle har ki ce mayaudari ne kuma macuci ance sanin mutum sai Allah amman wanann yaro Auta ban ga alamun abunda kika lissafo tattare da shi ba"

"Umma Wlhy baki san halin shi bane wlhh kaf makarantar mu ba wanda be san su ba,don suna da kudi sai suke ga komai suka yi daidai ne,Umma shine wanda ya watsa mun ruwa kuma don nayi magana ya nemi dake mun duwawu na,shine ni kuwa na wanka mishi mari,Zuhra da kan ta tace ba mutanan kirki bane,sanann babu wnada ya isa ya taba su ba su rama ba"ta kare tana bata rai.

"Har yanzu kin ga ya rama?"ta ji Umma ta jefo mata tambayar,kai ta girgiza a hankali alamun a'a,kafin Umma ta daura da fadin "kin ga hakan ya nuna mutum na iya canzawa a ko wani lokaci in Allah ya so,zaki ga me aikata aikin yan wuta ma Allah ya shirya shi gab zai mutu ya koma aikata na Alkhairi ya mutu ya kuma shiga Aljanna to miye Allah baya yi?Sannan kar ki manta yaron nan Dan masu kudi ne tare da connection kika dalla masa mari a tsakiyar makaranta amman ya dawo yana bin ki tare da neman yafiyar ki,inda yana da nufin cutar da ke zai miki irin hidimar da yayi da ke da ni ne?"ganin tayi shiru ne ya sanya Umma cewa "ki tashi ki je kiyi alola ki kwanta kina da makaranta gobe kin kuma ce da ni kuna shirye shirye ko kun ma fara text yake ko test"dan dariya tayi tare da mikewa tace "test ake cewa Umma saida safe"har ta kai kofa ta ji Umman ta kira sunan ta,hakan ya sanya ta ja ta tsaya

"Sabeeha a kullum ina so ki sani rayuwar duniya karamin guri ne,sanann Allah yayi mantuwa don Samar wa yan adam sauki a duk sanda suke cikin damuwa kamar yanda yayi hawaye da dariya,shi rike mutum a rai ba halin musulmin kwarai bane,sanann duk Musulmi an san shi da tausayi yafiya tare da maida damuwar wanin shi nashi,sanann yawan fushi da fada ba shine karfi ba iyakan me karfi shine wanda ya iya mallakan zuciyar shi a yayin da yayi fushi Hadisi ne guda,ina me rokon ki da ki sassauta wa zuciyar ki tare da koya wa kan ki hakuri da yafiya tare da manta abu in ya same ki,Ubangiji ya tashe mu lafiya Allah kuma yayi miki Albaraka"ta kare tana mike wa tare da karkade gadon ta don kwanciya bacci,jiki a sanyaye Sabeeha ta je tare da yin alola sanann ta shige daki inda tayi kuri ita kadai tare da zuba wa guri guda ido tunanuka da yawa na kai kawo a cikin ran ta,jikin ta yayi sanyi sosai da maganganun da Umma ta fada mata,saidai ta rasa me ya sanya take jin tsantsan haushin FIK,sam babu karya ko cutar wa a cikin maganganun Mahaifiyar nata amman bata jin abunda Faizaan yake nema zai samu a tattare da ita,ba shi ba a rayuwa bata jin akwai na mijin da za ta fada soyayyar shi,ta tsani maza!!Haka zalika ta tsani soyayya balle kuma aure,kan ta ya kulle don Haka kawai ta kasa yarda da FIK ko da na second guda,ta rasa me ya sanya Umma aminta da shi tare da yarda da shi lokaci guda haka?haka tayi ta juye juye ita kadai tana tunani inda za ta bullo wa matsalan FAIZAAN tun kan ya hada ta da Mahaifiyar ta kamar yanda ya hada ta da kawar ta don ganin take taken shi ke nan,sam babu Alkhairi a tattare da shi haka jikin ta ke bata,tunda suke basu taba fada da Zuhra ba saida ya shigo rayuwar ta,sanann yanzu yana son hada ta da Mahaifiyar ta abinda kuma ba zai taba yuwa ke nan ba,haka wannan Daren tayi ta tunani ka har bacci ya dauke ta tana ganin irin kiran da yake tayi mata inda taki dauka don ba karamin haushi ya kara bata ba yau.

******************************

Sallama tayi wa Umma cikin sauri ta fice daga gidan domin yau za su fara C.A so tana son isa da wuri,inda ko ba karamin kyau tayi ba don sanye take cikin wata gown din Atampa yellow da sky blue a jikin atampan inda aka mata dinkin gown me dogon hannu,duk da ba wani style aka sanya wa rigar ba amman ba karamin kyau yayi mata ba,don ya mugun zama mata a jiki,face din ta fayau kamar kullum banda kwalli da man lebe da ta sanya wanda sai sheki yake yi kuwa babu komai a face din nata,sai ta murza daurin ture inda ya kafu kuwa a kan ta gashin da ta parka ta daure da ribbon sai daurin ya zauna mata daram a kai,madaidaiciyar sky blue veil ta yafa a kan ta sai ta fito kamar wata sabuwar amarya Masha Allah da takalmin ta ma sky blue flat shoe,cikin sa'a kuwa ta samu abun hawa inda suka yi ciniki sai makaranta.


A bakin ajin su ta hadu da Zuhra inda ko ba a fada mata ba jiran ta take yi,rungume ta Sabeeha tayi sanann tace "good morning goofy angel,saura kadan in ce a aje ni a hostel na dauka baki fito ba ai"dan dariya Zuhran tayi sanann tace

"Morning Iron Lady Sabeehatun Umma kuma goofy angel din Zuhra masifaffiyar kawata,na fito tun dazu ya na ga idanun ki a kumbure kamar wace tayi kuka,ko bata samu ishashen bacci ba,hope dai lafiya?"ta kare tana riko hannun ta.

"Hmm ke dai Goofy angel bari Wlhy wanann FIK din yana neman zamo mun ciwon wuya,kin ko san jiya ina isa gida sai na tarar da shi gidan mu shi da Umma kamar sun shekara da sanin juna"

"Goofy angel to shine me don ya zo gidan ku?", "Haba Zuhra ya za ki ce shine me?What if Umma ta yarda da soyayar karyan da yake cewa yana mun tace na aure shi fa?"

Katse ta da fadin "to Goofy angel miye a cikin in kin aure shi din?Na ga yana kaunar ki,sanann Wlhy babu macen da za ta same shi ta so rasa shi,ba karamin sa'a za kiyi ba in kika zamo matar shi,don ya hada duk wani abunda ake nema a gurin na miji,sanann uwa uba kuma yana bala'in so da kaunar ki,Wlhy da za kuyi aure da sai na fi kowa farin ciki domin ba karamin kyau yaran ku za suyi ba"ta kare tana murmushi.

Numfashi Sabeeha ta fitar sanann ta kalli Zuhra "na rasa gane me ya sanya kuka kasa ganin yaron nan ba da pure intentions ya zo guri na ba,bani da wani prove da zai gaskata haka,amman jiki na yana bani kamar akwai abinda yake nufi na da shi,kiyi tunani mana Zuhra bayan na mare shi be rama ba be mun komai ba sai ya ce yana sona harda aure kuma wai na yarda?"

"Sabeeha!!Goofy angel why kike da taurin kai ne?Yanzu dai muka tsaya dragging kan issue din nan sai mu kwana mu tashi ba mu gama ba,ki zo mu shiga C.A muka fito sai mu yi magana don na ga kina bukatar full class na lecture"ta kare tana jan hannun ta,hararan ta Sabeeha tayi tace "sannu Malamar soyayya"duk suka sanya dariya sanann suka shige aji tare da zama suna dan duba handout din su don ba a wani taru a ajin ba.

Ko da suka fito fir Sabeeha taki bin Zuhra hostel inda ta nace ita gida za ta tafi tana da abun yi,in ta biye wa Zuhra sai ta kai Magrib wanda a zahirin Gaskiya kuwa tana gujewa maganar da Zuhra tace za ta mata ne akan FIK.

Suna tafe kuwa suna hira game da test din da suka yi don Alhamdulilah sun fahimta sosai kuma suna da hope za su cinye gaba daya,kamar daga sama suka ga motar FIK a gaban su,inda ya sha gaban su a take Sabeeha ta tsuke fuska tare da riko hannun Zuhra kam,tana kokarin Jan ta ya bude kofar motar,wanda karan tsayuwar motar ce ta janyo attention din sauran students masu wuce wa da masu zaman gindin bishiya.

Ba tare da ta Ankara ba sai ganin shi tayi tsaye gaban ta da bouquet na flower a hannun shi,yayi matukar kyau yana sanye in all white daga sama har kasa komai na jikin shi fari ne in ka cire shade din idanun shi da kuma gashin kan shi da ke ta kyalli,ba karamin kyau yayi ba hakan be sanya Sabeeha ta daga ido ta kalle shi ko da na minti daya banda Jan hannun Zuhra da tayi tare da jan tsaki a bayyane a ran ta kuma ta furta "Mayyen banza mayyen wofi Wlhy saidai kayi ka gaji ka bari"

"Sabeehaaaaaa!!"inda ya ja sunan nata ya sanya ta daga ita har Zuhra suka ja suka tsaya cak,ba tare da sun juyo ba inda be damu ba ya cigaba da magana "na sani ban kyauta ba amman I beg you da kyawawan suna yen Allah 99 to forgive and forget duk wani abu da na miki,Wlhy I can't stand losing you in my life"ya kare kamar zai yi kuka,a fusace ta juyo inda ta gan shi zube akan knees din shi,mamaki ne ya kamata tare da zaro idanun ta waje inda mutane suka hau dariya masu dauka a waya nayi masu gulma nayi masu Madallah nayi masu tausaya masa nayi inda shi ko a jikin shi idanun shi sun rufe ya manta da Waye shi ya manta da Rocket gang damuwar shi kawai ya shawo kan Sabeeha.

Takowa tayi har inda yake tsungune ba yanda Zuhra bata yi ba ta hana ta amman taki,saida ta iso gaban shi ta watsa mishi kallo sanann tace "What is the meaning of all this?Get up and stop all this drama can't you see kana creating scene ne?Wai miye damuwar ka da ni ne FIK?"ta kare kamar ta kwada mishi mari.

Baki ya turo gaba kamar karamin yaro sanann yace "Babe all I want is you and I don't care kowa ma yace komai in dai a kan ki ne,Guys have fallen head over heels for this damsel and I don't care ko wanann ku mai zai ce coz babu me bina bashin bayani,all I know is that I love her and can fight ko ma Waye yace zai shiga harkan ta,so from now on stay far away from my love ko kuma ku fuskanci fushin FIK"ya kare ko a jikin shi inda mutane masu dauka suka yi saurin sauke wayar,masu mamaki suna yi daman FIK yana da heart a kirjin shi har zai iya soyayya,wasu suna cewa eh Ai Sabeehar ta kai ko ma Waye ya so ta,while wasu na cewa sun yi mamaki ya rasa wa zai so sai ita,yam mata masu crushing akan shi take suka shaka tare da fara auna wa Sabeeha zaguna.

A fusace tace "can you cut this drama of yours pls,wai which part of leave me alone ne baka fahimta ba?Shebi I stated it very clear to you ka bar ni ka bar rayuwa ta amman baka fahimta ko?I told you babu abinda zan yi da kai,bana son wata alaqa da kai ko ana dole ne?"ta kare tana hararan shi,riko ta Zuhra tayi da sauri

"Goofy angel let's get going lokaci na kure wa,FIK don Allah ka tashi ka tafi kar ka yi embarrassing kan ka,will talk to her and zan kira ka komai zai tafi daidai"Zuhra ta kare a sanyaye, mike wa yayi tare da sakin murmushi "it's okay our Goofy angel babu komai and komai Sabeeha za ta mun ba zai bata mun rai ba,ni dai don Allah try ki sanar da ita don Allah nake son ta kuma Auran ta nake son yi,za ta iya mun komai one thing da ba zan dauka ba shine tace na bar rayuwar ta ko ita ta bar nawa I can't stand that"ya kare tana juyawa inda suka ci karo da Beel ba tare da ya tanka shi ba ya bude motar shi har zai shiga sai kuma ya tsaya

"The party it's over munafukai sai kuma na gobe sai kowa ya watse ko?Duk wani wnada yake jin shi dan iska ne yayi posting wanann abun a social media don Allah ya ga abunda zai same shi"ya fada babu alamun dariya a fuskan shi a take aka fara watse wa da kadan da kadan har kowa ya waste ana dan gutsiri tsomi.

"Gee what the hell is all this?Why on earth kake son sai ka zubar mana da mutunci ne saboda Allah,yanzu har an yi yarinyar da za ka durkusa kan gwiwar ka kana rokon ta a tsakiyar school?Faizaan baka ganin yawan mutanan da suka kalli wanann abun?So kake sunan mu ya baci ko me?For crying out loud ka kyauta mana?Mu da ake tsoro yanzu ka zubar mana da mutunci fa,duk saboda shegen kafiya da tsinanniyar taurin kai irin naka,enough is enough FAIZAAN you have to put a stop to all this bullshits,ya isa haka a bar dare din nan haka ,na ji na kuma yarda kaine winner zan kuma baka Rolex watch din Dad in kana so ma zan baka harda mota na,amman don Allah a bar shi haka nan wulakancin yar talakawan nan ya fara yawa"

Dan dariya Faizaan yayi sanann ya bude motar shi saida ya shiga ba tare da ya kulle kofar ba yace "Beel ke nan,ka Riga ka san ni sarai bana taba fara abu ban gama shi ba,ni nace a yi Dare din nan don haka sai lokacin da ya mun zan ce a tsayar da shi so don't you ever a rayuwan nan ka fada mun abinda zan yi"daga haka ya kulle motar shi tare da ja ya bar school din a tsiyace da kallon ban haushi Nabeel ya raka bayan kuran motan Faizaan da shi,yana me jin bakin ciki akan me za su tsaya kan wani bet din banza Faizaan na neman zubar musu da mutunci yarinyar da ba yar uban kowa ba,ya tsane yarinyar nan with passion and abunda Faizaan yayi masa yau ya kuma sanya wa ya kara tsanar Sabeeha.

*****************************

Kwana uku da faruwar haka Sabeeha sam ta rasa nutsuwa da kwanciyar hankalin ta,domin ba karamin takura ta FIK ya ke yi ba,wuni yake a gidan su yana magiya don ganin ya shawo kan ta amman ina,haka zai wuni gurin Umma yana me rokon ta ta taimaka ta bashin Sabeeha,don ba karamin sabo suka yi ba,nan yake cin abincin rana don Umman Sabeeha ba karya ta iya girki.

Hakan ma be masa ba a school kowa yanzu ya san yana kaunar ta,har zuwa ake ana bata shawarar wai ta karbi proposal din shi don ba karamin dadi za ta ji ba in ya aure ta,sanann Zuhra ma ta kunna mata wuta kamar yanda shima FIK ya kunna wa Zuhran wuta kan ta shawo masa kan Sabeeha,don is like he is losing his sense,ba karamin haushin shi su Beel suke ji ba domin ganin yanda yake wani rawar jiki akan ta ita kuwa kamar bata san yana yi ba,don kallo wannan na arziki ba ya hada ta da shi,maganar ta guda kullum shine ya fita a hanyar ta bata bukatar komai daga gare shi don saida ta nuna fushin ta akan yanda yake ta banzartar da kudin shi kan ta,tace sam bata so don har yau bata bude paper bag din da Zuhra ta kawo saboda da ita ba.

Tun safe yau garin da ni'ima aka tashi don alamun ma kamar da hadiri a sama saboda yanda garin yayi damshi kamar wanda za ayi ruwa,suna daki suna hira da Shatu da Umma don sai zuwa 4 suke da CA din yau inda gobe kuma early in the morning suke da practical karfe 7:30 so gudun kar tayi late ya sanya ta yanke shawarar kwana a Hostel gurin Zuhra don bata da tabbas za ta samu abun hawa da wuri haka.

Dan nisawa tayi sanann ta kalli Umma tace "Yauwa Umma gobe ajin sassafe gare mu kuma Wlhy practical muke da shine daman nace ko zan kwana gurin Zuhra in ba damu in mun gama da yamma sai na dawo gida"ta kare da muryan shagwaba,dan dariya Umma tayi sanann tace

"Auta ke kam dai zan ga sanda za ki daina wanann shagwabar taki",da sauri Shatu tace "Umma na tabbatar duk randa aka kai ta dakin Uncle FAIZAAN daga rannan shagwaba ta kare"da sauri Sabeeha ta daka mata duka me zafi a cinya "gidan ku Shatu Wlhy in baki raba kan ki kin raba ni da maganar FIK yake ko Waye Wlhy zan ci muku mutunci daga ke har shi"ta kare tana hararan ta.

"Amman Sabeeha in ban mance ba na hana cin zalin nan da kike wa bayin Allah na ba gaira ba sabab,yanzu don girman Allah laifin me tayi miki kika make mata cinya?"baki Sabeeha ta turo kamar me shirin saka kuka sannan tace "Umma wai baki ji me tace ba don Allah wancan me kan kwallon goruban take hada ni da shi fa"caraf akan kunnan FIK da shigowar shi gidan ke nan.

Daga bakin kofan dakin yace "Umma kin ga ina zaman zama na ana cin nama na,ya sanya ashe nake ta rame wa,don Allah Umma wai kaina kamar na kwallon I can't even pronounce it ban ma san abun ba but I'm sure kaina ba kamar haka bane"ya kare yana turo baki.

"Lah Uncle FAIZAAN kaine tafe"Shatu ta fada ciki da farin ciki don yana kawo mata kayan dadi duk gidan da ita kadai yake magana don tsakanin shi da su Hajiya daman kallon banza ne,tare da yaba habaici wanda at times baya ma sanin meaning din wasu Hausar da suke yaba masa,shi ba su ne gaban su ba don ko ta kan su ma baya bi.

Labulan dakin Shatu ta daga sanann tace "Wlhy na dauka yau ba za ka zo ba,har nace wa Umma yau kar ayi maka dan wake,na ga da hadiri a gari"hararan wasa ya mata sanann yace "Ai ko yau babu ke babu chocolates tunda kika hana Umma yi mun fav food din Bebe dita"

"Umma good afternoon"ya fada yana me tsunguna wa, "ya kake Muhammadu ya gida ya su Umman taka?", "suna lafiya Umma sun ce a gaida ki,mutuniyas yau ma ba za ki kula ni ba?"ya kare yana kallon Sabeeha,harara ta watsa mishi a fakaice sanann ta mike "Sannu"shine iya abunda tace da shi a wulakance sanann tayi ficewar ta, "Umma bari nayi wanka to 3 ake nema kar lokaci ya kure"jin haka ya sanya shi saurin mike wa shima tare da fitowa da dariya Umma ta raka bayan sa tana cewa "kai dai an ji kunya ka koma bita zai zai sai kace ba na miji ba kayi zuciya kawai mana"dariya yayi daga wajen yace "Umma yo Ai zuciyar ce Beeha ta gudu da ita tun tuni abunda nake kokarin karba ke nan amman ta ki ta bani",daga Umma har Shatu dariya suka sanya masa don wanann rawar kafan da yake akan Sabeeha har ta so ta fara yawa ko nace ta ma fara, daki ta shige inda ta cire kayan jikin ta tare da dauro zani,ta sako karuwar hijab har kasa sanann ta dauko kayan wanka.

Saida ta kai toilet sanann ta dauko bucket ruwan zafi ta juye don yau an tashi da sanyi sannan ta nufi bakin rijiya don jan ruwan sirki,karasawa inda take yayi da sauri yana dan tari.

"Bebe lemme help you out"ya kare yana mika mata hannu kan ta bashi gugan,harara ta watsa mishi sanann tace "ka bar shi na gode ba sai ka taya ni ba besides ka ma iya jan ruwa ne da za ka ce za ka taya ni?"

"Uhmm maganar Gaskiya ban iya ba ban ma taba ganin well ba sai yau but in zaki koya mun Wlhy sai na ibo miki ruwa,don zai miki nauyi,ko to in sa hannu sai mu ibo ruwan tare?"

Kallon shi ta dan yi na mintuna sanann ta girgiza kai "ka bar shi na gode,zan iya da kai na bana bukatar any help daga gurin ka"daga haka bata sake kula shi ba banda ruwan da ta shiga ja,yana tsaye yana ganin yanda take jan ruwan a hankali,dan kallon ta ya dan yi kafin yace "an taba fada miki kina da masifar kyau?"

Kallon shi tayi sanann ta ce "Duk fa wannan tricks din naka ba zai yi working kai na ba,better for you ka rabu da ni"daga haka bata kuma kula shi ba ta dau ruwan ta tare da shige wa toilet inda shi kuma ya koma gurin su Umma aka shiga hiran da shi,don Umma kam kamar 'dan da ta haifa take jin shi,coz yana mugun respecting din ta.

Saida Sabeeha ta gama guna gunin ta akan nacin zuwan da FAIZAAN ke yi gidan su sanann ta shiga wanke jikin ta,ba wani bata lokaci tayi ba ta fito inda saida ta daura alola sanann ta shige daki,cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ta gama shafa tare da gyara gashin ta ta parka guri guda sanann ta shirya kan ta cikin wata Pakistani dress kallon yellow da fari,inda riga ne da wando,inda ko ya zauna mata daram a jiki,abun ku da me shape me kyau ko wani kaya mutum ya sanya sai ya cika shi ya karbe shi sanann ya masa kyau.

As usual kwalli da man baki kadai ta sanya a lips din ta sannan ta sanya farin hula akan ta,kafin ta feshe jikin ta da turaruka masu dadin kamshi,farin hijab ta saka wanda ya kai mata har gwiwa daidai lokacin an fara kiraye kirayen La'asar,so turarukan ta kuma
Shafawa inda take dakin ya hau kamshi,saida ta gabatar da sallah tayi adduoi sanann ta mike ta shirya jakan ta,duk wani abunda ta san za ta bukata daga yau zuwa gobe ta shirya a jakan sanann ta dauki wayar ta ta fito.

"Umma na gama shiri zan wuce"murmushi Umma tayi sanann tace "kin yi kyau sosai Autar Umma Allah ya kara wa rayuwar ku Albaraka ya kuma bada saan karatu,don Allah a kula na yarda da ke kar ki bani kunya kin ji"

"In sha Allah Umma ba zan baki kunya ba,kafin na kwanta ma zan kira ki don ki tabbatar ina cikin koshin lafiya,Shatu za ta kwana a nan ne?In shiga na tambayi Maman ta?"

"Aa yi tafiyar ki don dai na rana guda sai na ji tsoron
kwana ni kadai sai kace wata ke,ki dai tabbatar da kin ci abinci,Allah ya tsare sai zuwa goben ko?"

"Ameen thuma Ameen Umma da wuri ma goben zan dawo,Umma kar ki manta ke ma ki ci abinci ki sha magani,Shatu in bata sha ba ki fada mun"dan dariya Umman tayi sanann tace "ba sai ya kai ga haka ba ma zan sha"da haka suka yi sallama ta so sanin ina FIK ganin baya dakin amman sai ta basar kar a dau ta damu da whereabout din shi ne.

A kofar gida suka ci karo yana kokarin shiga ita tana son fita saura kiris su gwari juna,tayi saurin ja baya "Ai ko da yau Bebe kin gware ni sai na rama don ba a yin gware so guda bad luck yake jawo wa"harara ta watsa masa inda shi kuwa yayi mata blowing kiss tare da sakar mata murmushi

"Kin yi kyau sosai Babe komai kika sanya kyau yake miki,don Allah marry me and be mine forever"ya kare yana hada hannaye guri guda,inda ta sakar masa kallon baka ma da hankali Wlhy "I'm serious Babe you are the best thing ever happened to me,and I'm going to keep telling you that each and every day and I have always dreamt of being with you my love,your love is all I need,pls Babe forgive and take me in you won't regret it this is a promise don Allah kar ki ce aa"ya kare kamar zai yi kuka.

"Sai kayi kuma,wai FIK don Zuhra da Umma sun yarda da kai shine kake tunanin nima zan yarda da kai ne?Never!!ba zan taba yarda da kai ba,and ba zan taba yarda kana so na ba"

"Ni kuma Bebe yau ba sai gobe ba sai na miki proving eh da gaske nake son ki,I will stay here just for you zan jira ki je ki dawo ko karfe nawa ne ba zan je ko ina ba har sai kin yarda da ni,I don't care a kira ni mahaukaci ko mara hankali all I want is you,and won't stop har sai na same ki,na san ko na ce zan kai ki ba zan ki yarda ba so stay safe my love will be here waiting for you,ya kare yana sake mata laulasar murmushi,ko kallo be ishe ta ba don ba ta dauki maganar na shi serious ba kan idon shi ta tare abun hawa tare da yin ciniki sai BUK.


Kamar wasa FIK na nan tsaye kofar gida na jiran dawowar Sabeeha inda har aka kira Magrib bata dawo ba shi kuma be shiga ya tambayi Umma ba,don so yake ya nuna wa Sabeehar yau fa ko shi ko ita ne,masallaci ya shiga yayi sallah tare da fitowa yayi daidai da iska me karfi da aka fara,goshi ya dafe don be fito da rigar sanyi ba,don ba da mota ya zo ba kawo shi aka yi aka maida motar,iska sosai ke kadawa inda kowa sai rige rigen komawa gidan sa yake yi domin yanda sama tayi baki kirin din nan ba karamin ruwa bane zai zubo,wayar shi da ke ringing ya zaro daga aljihun shi ganin Mommah ke kira saida ya dan sha jinin jikin shi

"Hello Charm charm ina ka tsaya?Why har yanzu baka dawo gida ba?Baka ganin iska da hadirin da ake yi ne?Ko ka mance na tuna maka you are Asthmatic this weather is not suitable for you"ta kare kamar za ta yi kuka,don hankalin ta ba karamin tashi yayi ba ganin baya gida har yanzu.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "Mommah Wlhy wani important abu ne ya rike ni but don't worry yourself promise you I'm safe and ba abunda zai same ni,muna tare da su Beel fa"sai sanann hankalin ta ya dan kwanta.

"Baby boy don Allah stay safe for Mommah sake ka ji?Kar ka bar wani abu ya same ka,and make sure ka sanya sweater Allah ya sa inhalers din ka na tare da kai"saida ya dan yi murmushi sanann yace "Worry no more my love I'm safe babu abunda zai same ni,take care of yourself"

"I will charm charm love you okay ka ce ina gaida Mommyn Nabeel din", "to Mommah za ta ji love you too"da haka ya kashe wayar sallar Isha'i aka shiga inda kamar jira ake a idar ruwa ya barke kamar da bakin kwara,FIK na nan tsaye be sanya lahadin tafiya ba ruwa na jibgan shi amman sabida mugun nufin da ya sanya wa zuciyar shi kan Sabeeha ya sanya ko tuna yana da Asthma baya yi,babu wani tsoro ko fargaba a tattare da shi,in banda dakalin da ya samu dake dan lugun gidan tare da zama,yana me ji a ran shi tabbas Sabeeha ta dawo ta tarar da shi dole zuciyar ta yayi sanyi.

Karfe 12 na dare************************

Sama sama cikin bacci Umma ta ji ana buga mata kofar daki,wanda a mugun furgice ta farka bakin ta dauke da salati,zuciyar ta har ma tsinke wa don a iya tunanin ta ta rufe kofar gida,to Waye zai buga mata kofa cikin daran nan haka?Don sai lokacin ta kallo agogo ganin har 12 ta dan gota,jin bugun ya ki tsayawa ne ya sanya ta sauko wa daga kan gadon tare da tunanin to ko Sabeeha ce ta dawo?Sai kuma zuciyar ta ya bata me zai dawo da Sabeeha cikin daran nan,hakan ma ana ruwan sama,bugun kadan kadan kamar dai ba a son bugun haka take ji,hakan ne ya sanya ta daura dankwali tare da kunna hasken tocila kasancewar babu wutan nepa ta nufi bakin kofar

"Waye nan cikin daran nan haka?"Umma ta fada,shirun da ta ji ne ya sanya ta son koma wa don ganin kamar ba kofar ta ake bugu ba,dan kara karfin bugun aka yi hakan ne ya sanya ta dan daga murya kadan tunanin da tayi maybe saboda saukan ruwa ya hana jin tamabyar farko da tayi

"Nace wai Waye a gurin ne?"kasa kasa kamar munafuki yace "Bilkisu bude ni ne"jin muryan na miji ya sanya tace "ban gane kai ne ba in bude?Wai Waye ne?"kasa kasa yace "Bilki taimako don Allah bude kofar nan Shafa'atu ce babu lafiya na buga kofar kowa shiru na san ke ce baki da nauyin bacci,don Allah bude kar ta mutu wlhy idanun ta har sun fara kokarin burgewa"

Da jin haka Umma ta koma tare da sanyo hijabi har kasa sanann ta bude kofar don sai yanzu ta gane Ahmadu ne Mahaifin Latifa,da budewa kuwa ya fado dakin tare da saurin maida kofa ya rufe

"Haba Bilki bude kofa saida na kusan hour guda a waje"kallon ban fahimci wannan kulle kofar ba ta watsa mishi sanann tace "dake dare ne yanzu an kuma ce dare mahutan bawa bacci nake ya sanya ban ji ba,me ya samu ita me dakin naka tana kuma ina?"ta kare babu alamun fara'a a fuskan ta.

Hannu ya sanya tare da dan sosa keyar shi sanann ya washe hakwara "kai Bilki Masha Allah Wlhy Allah ya gama miki komai nan duniya ga kyau ga diri ga murya me dadi,Wlhy Bilki babu wanda zai kalle ki ya ce kin haifi yara yan mata har biyu,saboda irin kyau da kyan jiki da Allah ya baki"

Da sauri ta daga mishi hannu "dallah dakata Ahmadu ban fahimce ka ba,cewa kayi ina matar ka babu lafiya na zo na kama maka ita a kai ta asibiti,menene abun wanann zancen kuma"ta kare a fusace

"Haba Bilki haba Bilki wai fushin duk na miye ne?Bilki wai ke dutse ce yau kimanin shekaru 21 da mutuwar Usmanu amman baki kara aure ba kuma baki...sai ya dan fashe da dariya,kafin ya cigaba baki jin sha'awa ne?Ko ke ba mutun bane?Bilki Wlhy da kin san irin so da kaunar da nake miki da kin tausaya mun"

"So??Kauna?Ahmadu So ko kuma Sha'awa ta"dan dariya yayi sanann yace "eh to harda sha'awar ma kin san inda babu so sha'awa bata zuwa ki rufa mun asiri Bilki ki bani hadin kai Wlhy ba za kiyi danasani ba za ki ji dadi sosai tunda yaushe rabon duniya da ayayyaraye"ya kare yana kokarin cire riga.

"Amman Ahmadu Wlhy kayi asara,saboda rashin tunani ni matar kanin naka za ka shigo har dakin bacci na babu tsoron Allah a ran ka babu tsoron wani ya gan ka,kana nema na da alfasha?Lafiyar ka kuwa?"

"Haba Bilki don Allah wai me ya sanya kike mun haka ne?Bilki tun ba yau ba nake nuna maita na akan ki sarai kuma kin sani amman sabida Allah abun nan fa daga ni har ke za mu ji dadin shi,kuma wa zai sani sabida Allah Ai ina da sirri ke ba yarinya bace nima ba yaro bane so ba me jin maganar nan,ki kwantar da hankalin ki muyi abun nan don da alama yau Allah ke so na da Alkhairi ya sanya ya saukar da ruwan sama,yi sauri don Allah hakuri na ya fara kare wa"ya kare yana nufo ta.

"Wlhy ka kara takowa gare ni sai na tabbatar da na illata ka,Ahmadu na rantse in baka fice mun a daki ba zan maka abunda ba ka so,ban damu ka mutu ko na mutu ba amman Wlhy mayafi na ba za ka taba ba,saboda babu Allah a ran ka ban yi Zina da kuruciya ta ba saida girma na?Hauka ne na kwana da Wan miji na haba kazantar ai tayi yawa,wuce ka fice mun daga daki tun ban tara maka mutane ba su zo su ga abunda kake shirin yi da matar kanin ka,ka kuma ji kunya mutuncin ka ya kuma zube wa a karo na biyu ina kuma maka fatan Allah ya shirye ka,fice mun daga daki tun muna mu biyu" ta kare a zafafe.

"Ban taba ganin me taurin kai irin ki ba Bilki,tsakani da girman Allah miye a ciki in mun yi wannan abun ko da sau daya ne?Wai miye zai rage ki in mun jiyar da juna dadi,ke wai baki gaji da cin kashin da ake miki a gidan nan ba?Kowa ya na juya ki yanda yake so kamar kwallan tamola,baki gaji da zaman rashin yanci da kike a gidan nan ba,Wlhy ki bani hadin kai muddum kika bani ba za ki taba nadasani ba zan jiyar da ke dadi,zan zamo gatan ki sanann zan tsare miki duk wani cin mutunci da zai fito daga gurin yan gidan nan,alkwari nayi miki Bilki zan nuna miki so da kauna zan tattala ki kamar yar baby,sanann zan zamo uba ga diyar ki duk wani damuwar ku yanzu ta zamo nawa,ni dai hadin kai daga gare ki kawai nake nema"ya kare yana adduar Allah ya sa ta yarda domin ba a karamin hannu yake ba.

Pim Umma bata ce da shi ba,illa raba shi da tayi tare da nufan kofa bude wa tayi sannan a zafafe tace "Wallahi tallah ban taba haduwa da rikeken dan iska ba irin ka,Ahmadu ka haifa mata kai uban mata ne na dauka ko ganin wani kayi yana kokarin ci mun mutunci sai yanda karfin ka ya kare gurin kare mun martaba ta amman wai kai da kan ka ke neman yaga mun rigan mutunci na,saboda baka da kunya babu kuma Allah a ranka wai ni kake tsayawa a gaba na kake nema na da Zina inalilhi wa ina ilaihi raju'un"ta kare tana hawaye

Cikin ko in kula yace "Bilki miye na wani kuka yarinya ce karama ke da za ki ce baki saba ba?Iya tunani na ba wanann bane karan ki na farko kasancewar ki da na miji,sanann don rashin kunya ni kike kira da dan iska?"ya kare a zafafe

"Eh na kira ka dan iska in da sunan da yafi haka ma zan kira ka da shi Wlhy,zo ka fice mun daga daki Wlhy tun ban tara maka mutane ba,na rantse da girman Allah in baka fita ba sai nayi ihu kowa ya ji ya zo ya kama ka ka zo kwartanci dakin matar kanin ka da ya mutu ya bari wanda kuka kasa rike wa,in har sai ka kwanta da ni zan samu yanci a gidan nan to na zabi na mutu a kaskancin"ta kare tana goge hawayen ta.


Nan fa kamar tsohon maye Abban Latifa ya shiga rokon Umma Allah Annabi kan ta taimaka ta bashi hadin kai ko da sau daya ne,amman fir Umma ta ki,makiya yayi ta yi mata harda durgusawa a kasa kan ta taimake shi amman sam tace bata san zance ba kamar zai mata kuka don makiya,ganin abun nashi ba na kare bane ya sanya Umma dan daga murya tana fadin "Wayyo Allah taimako jama'a a kawo mun dauki Kwarto"Ai tuni ya tsorota yace

"Ya isa haka baki da hankali ne Balki ni kike son tona wa asiri?Ni za ki tozarta don ina son taimakon ki?"a fusace tace "fice mun daga daki Ahmadu da kai da taimakon naka duk Allah ya fi ku,gurin Allah kadai nake neman taimako ba gurin ka ba,Allah ya isa shigo mun daki da kayi da maganganun banza da ka fada mun Wlhy ka kuma minti guda dakin nan sai na tona maka asiri"

"Ya isa haka zan fita ba sai kin ci mun mutunci ba amman ki rubuta ki aje kin yi da Ahmadu Wlhy tallahi sai na shayar da ke mamaki za ki gani,ba dai ni kika hana kan ki ba"ya kare a fusace tare da nufan kofa "da yardar Allah Alkhairi zan gani ba sharrin ka ba,baka isa yi mun abinda Allah be so ba"ta kare tana raka shi da harara,be ce da ita komai ba ila kofa da ya bude ya fita zuciyar shi na tafasa domin babu karya yau ya so kwana da Bilki ko ya rage abinda ya dade yana ji a game da ita.

Tsaye yayi inda ita ko ta rufe kofar ta tare da dauro alola nan cikin dakin ta tayar da sallah,ko za ta ji sanyi a cikin zuciyar ta,a tsakar gida ya tsaya don lokacin kusan 3 ake nema ya ma kasa sanin abun yi,ba karamin bata masa rai Bilki tayi ba kuma Wlhy sai ya rama wanann abun da tayi masa sai ya ci mata mutunci ya tozarta ta kamar yanda ta so tozarta shi murmushi na ga ya sake irin na muguntan nan daidai lokacin da ya gama yanke wa kan shi abun da za yi mata.

Asuban fari Umma ta fito don yin alola,kicibis suka yi da Ahmadu tsaye a kofar gidan hakan ya tabbatar mata da cewa na gurin ya kwana ke nan,kai ta dake kamar bata san da tsayuwar shi ba,tayo alola tare da juyawa don komawa daki

"Har yanzu kina da sauran dama ta karshe Bilki ki bani hadin kai in janye abinda nayi niyan aikatawa a gare ki,kar ki zo kina yar danasani daga baya"

Kai Umma ta girgiza sanann tace "ka dade baka yi ba Wlhy Ahmadu ko mutuwa nayi ka taba gawata ban yafe maka ba duniya da lahira sharrin ka kuma kan ka zai koma da yardar Allah na riga ka nace Allah"

Kafada ya dage sanann yace "Allah ya gani na baki zabi kika yi wasa da damar ki,to Ai shike nan yanzu kuwa za ki san Waye Ahmadu"daga kare fadan haka ya nufo ta gadan gadan tana me ya ja da baya har suka isa bangon dakin ta,Hijab din ta ya sanya hannu tare da kamawa idanu ta zaro tana kokarin faucewa,kawai ta ji ya kurma ihu da iya kan karfin muryan shi.

"Wayyo Allah na shiga uku jama'a kuma ina ne ku kawo mun dauki,Bilki me na miki a rayuwar nan da za ki nemi bata mun aure,ki rasa wanda za ki nema duk mazan duniya da alfasha sai ni Ahmadu wan mijin ki Inalilhi wa ina ilaihi raju'un"Ya kare yana kurma ihu,mamaki ne ma ya hana Umma iya cewa komai,ganin yanda yake ihu kamar ana yankan naman jikin shi.

Ihun shi ne ya sanya mata da mazan gidan shigowa sashin da sauri har ana ture ture,turus suka yi ganin abun da ke faruwa,da ganin su kuwa yayi saurin sakin hijab din tare da saurin matsawa

"Allah na gode maka Allah kuma ya tona miki asiri,saida kika ga idanun mutane kika sake ni amman Bilki kin ji kunya Wlhy tallahi na hada ki da girman Allah kan ki Kyalle ni amman kika ki,ko ba ki ji tsoron Allah ba Ai kya ji kunyar Hajiya Ladi da Shafa'atu me daki na"

"Kunya Abban Latifa kunya fa na ji ka ce,wai har daman kana tunanin wanann matar ta san kunya ne?Bilki me na miki a rayuwa kike son sai kin ga baya na ne?Miji na ne kadai na miji a gidan nan da kika bi kika sanya mishi ido saboda girman Allah,ko kunya baki ji ba ace da girman ki sabida hauka da dabbanci kina bin mijin aure mijin ma mijin Shafa'atu in kin manta in tuna miki Wan mijin ki ne jaka da kike ta maita a kan shi"ta kare a zafafe kamar za ta wanka wa Umma mari.

"Amman Wlhy Bilki kin ban kunya in aure kike so ki fada mana ba sai ayi miki ba,kya tsaya kina bin mijin wata,haba Bilki Wlhy kin ban kunya kin kuma ban mamaki,saboda Allah me kuke son maida mana gida ne?Yar ki na neman maza kan idanun mu mun yi shiru har ace wai budurwa kamar Sabeeha na miji ke daukan nauyin ku ke da ita,ace war ki ba mu sani bane idanu kawai muka zuba muku,amman yaron nan da ke sintiri kullum gidan ku in ba nema suke ba uban me suke yi?Nace Uban me suke yi?Bilki ita yar taki na neman maza ke kuma kina neman mijin wata inalilhi wanann wani irin bala'i ne?Uban wa kuka fi lafiya ko sha'awa da ba ku da aiki sai neman maza"Hajiya ta kare tana watsa mata harara.

Cikin matsananciyar kuka Umma tace "inalilhi wa ina ilaihi raju'un,Ahmadu ni za ka wa sharri,na rantse da girman Allah Hajiya sharri yake mun,Wlhy tallahi ban taba ba kuma ba zan taba neman wani ba ma balle kai Ahmadu"

"Ke dallah rufe mun baki har kin san Allah a ina,Wlhy tallahi Bilki yau me raba ni da ke sai Allah,sai na yaga miki rigar mutunci Wlhy tallahi tunda kika san ki nemi miji na sai na yaga miki rigar mutuncin ki,sai na tube ki na jika ki na zane miki jiki,gaba ko wa kika gani ba za ki kuma bi ba,shegiya jakar mata,me kike da shi da har mijina zai biki?Akan a tunanin ki ban sani ba irin biyiyan da kike tayi masa yana ki shine har za ki daura masa sharri Wlhy yau ko ni ko ke ne"ta kare tana cukumo kwalar rigar Umma.

Riko ta Hajiya tayi "Shafa'atu sakar ta kar ki ibi nazasa domin taba me bin maza karya irin ta ma akwai zububi,sum sum sum ka taba ta kamar na Allah amman kwarguman munafuka ce"

"Hajiya sakar ni Wlhy tallahi yau ko ni ko ita ne a cikin gidan nan,sai na canza mata kamanni,sai na mata abunda gobe ko kyauta na miji ya neme ta ba za ta bude masa kafa ba balle ita da kan ta ta nemi shi,ba dau Ahmadu mijin. Shafa za ki nema ba Wlhy kin tabo abunda ya fi karfin ki yau sai kin san shayi ruwa ne shegiya mataiyaciya a maza me shegen son mazan tsiya"

Kuka sosai Umma ke yi tana rantsuwa harda girman Allah da Qur'ani kan ba ita ta nemi Ahmadu ba,ba kuma ta taba neman shi ba,shi ne ya neme ta kuma ta ki amince wa amman sam ba wanda ya yarda da ita in ka cire daidaiku a cikin matan gidan irin su Shatu da Mahaifiyar ta,kuka sosai Umma take tana rantse wa kamar ran ta zai fita,don tunda ta zo duniya bata taba ganin masifa irin wanann ba,inda fir Abban Latifa ya rintse idanu tare da rantsuwa kan Wlhy tallahi ita ta neme shi.

A fusace Maman Latifa tace "in ba za ku iya ba ku matsa in lakada wa shegiya na Jaki,don Wlhy ba zan taba hakura ba ba zan bari ba rainin wayon yayi yawa"

"Aa Shafa kar ma ki bata lokaci gurin dukar ta,ki bari a hada shegiya da hukuma mu kai ta Sharia court a yanke wa yar banza hukuncin kisa ta hanyar jifewa a haka rami a jefe shegiya kowa ma ya huta tunda ta taba aure Qur'ani hukuncin jifa ne ya hau kan ta,ta mutu kowa ma ya huta in ta je lahira ta cigaba da neman mazan a can"Hajiya Ladi ta kare tana hararan ta.

"Aa Hajiya mu fara bugun ta Wlhy mu fanshe bakin cikin mu kan mu hada ta da hukuma inda za ta san ba ko wani miji ake taba wa a zauna lafiya ba,banda rashin azanci irin naki Bilki mijin Shafa za ki nema?" Atika ta kare tana hararan Umma.

"Yanzu na ji zance Atika duk wani me kauna ta ya zo ya taya ni mu tube wanann fasikan mu zane yar iska"Shafa ta kare tana kokarin Jan hijab din Umma,nan ko suka nufi Umma gadan gadan tana kuka tana rokon su Allah Annabi su Kyalle ta ta samu tayi sallan Asuba,inda Hajiya ta make bakin ta saida ya fashe yayi jini "shegiya har kin san wani sallah?Ko waya ce miki sallan me Zina Allah na karba,ke da za ki mutu ai ibada ba taki bane ki dai bar mu mu cigaba da neman Aljanna domin yasin ke kam wuta za ki shiga"Hajiya ta kare tana fincike Hijab din nata da karfi ta cire daga kan nata.

Cikin kuka Ameena Mahaifiyar Shatu tace "Hajiya ki duba girman Allah kar ku yi mata tsirara ku yi hakuri Wlhy ba halin Bilki bane"

"In baki mun shiru ba Meenou ke ma sai na ci gatan Uwar ki har kina da bakin magana manya na magana,Uwata kuyi mata duk abinda ya dace ita ta jawo wa kan ta"Fatah ya kare yana wani cize baki.

"Allah ya kara wa rayuwa Albarka Sadaukin Hajiya"Hajiya Ladi ta fada tana me watsa wa Meenou kallon banza,inda ya amsa da "Ameen Momcy ki dade kiyi lasting in ta muku gardama bari na taya ku yaga rigar yar wuta"ya kare yana tahowa tare da mika hannun don kama zanin jikin Umma da ta damke gam,tana kuka kamar ran ta zai fita,Allah sarki mutuwa me tonan asiri,yau da Abban su Nawwaara na raye waya isa yi mata haka?kuka sosai take tana adduan duk da ya zo ranta,inda Ahmadu ya ja gefe tare da tsayawa yana dariya kasa kasa ganin hakar shi ta cimma ruwa.

Kamar daga sama Fatah ya ji an damke tsintsiyan hannun shi,wanda hakan ya dakatar da shi daga kokarin yage wa Umma zani da yake shirin yi,a fusace ya juyo "Kan Bura uba wani shege ko shegiyar ke rike mun hannun ina kokarin zartar da hukuncin Allah,akan wace jinin ta ya hallarta a kashe"ya kare a fusace

Tsaye ya ga FIK fuskan shi a matukar daure be damu da sanyin da yake ji ba sakamakon dukan da ruwa yayi masa a daran jiya,don da kyar ma ya iya jan kafafuwan shi ya shigo sakamakon shige da ficen mutane da yake ta gani,tare da juyo hayaniyar da ake tayi a part din Umman hakan ya tabbatar mishi da babu lafiya,inda yana shigowa kuwa Shatu ta nufe shi tana kuka ta fada mishi abinda ke faruwa inda rai a matukar bace ya shiga gidan daidai ya tarar da Fatah na kokarin yaga wa Umma zani.

"Sake ta ka kuma ja da baya"shine abunda FIK ya fada cikin kakkaurar murya,shekeke Hajiya da su Shafa ke kallon shi,irin kallon rainin hankalin nan

"Idan naki sakin ta fa?Ubana za ka ci ko Uwata?"Fatah ya fada babu alamun tsoro a tattare da shi,murmushin gefen baki FIK ya sake sanann ya ce "babu ko guda amman jikin da za ka ci za ka so da Uwar da Uban naka aka hada aka cinye"

A zafafe ya daga hannu zai wanke FAIZAAN da mari inda yayi saurin rike hannun tare da murdawa sannan ya zuba masa mari me shegen zafi akan fuskan shi,dan ihu Fatah ya sake don marin ya shige shi,ganin haka ya sanya Hajiya saurin zuwa inda suke

"Yau na ga ikon Allah ka lafiyar ka kuwa?Ka shigo gidan matan aure ka kwada wa Dana mari akan wani dalili?"ba tare da ya kula ta ba ya nufi inda Umma ke tsaye tana kuka kamar ran ta zai fita,Hijab din ta ya dauka tare da mika mata sanya wa tayi da sauri ta riko hannun shi

Cikin kuka tace "Muhammadu Wlhy tallahi ban aikata abinda suke zargi na da shi,na rantse da girman Allah shi ya neme ni na kuma ki bashi hadin kai shine ya hada mun sharri"ta kare kamar za ta shide,ba karamin tausayi Umma ta bashi ba har yana jin kamar ya taya ta kuka

Cikin lallashi yace "na san halin ki Umma ba za ki taba yin haka,goge hawayen ki ki shige war ki daki,babu abinda zai same ki tunda na zo yanzu kam"

Dariyar rainin hankali Hajiya ta sanya sanann tace "yau nake ganin bariki,to dan iya me guzurin kinibibi uban Waye kai da za ka ce tayi shigewar ta daki?Hukuma ne kai?A kama mata tana neman wan mijin ta za a ayi mata hukunci kace kar ayi,sanann saboda isa ka zo har gidan uban yaro ka dake shi a gaban uwar shi Ai ko mutuwa aka ce na kunyar idon Mahaifiya"

A zafafe ya ce "Wai nan din har kin san abunda ya dace da wanda be dace ba?Da kike maganar Hukuma ku kan ku akwai Hukuma cikin ku da za ku yanke mata hukunci?Akwai wanda ya kama su tirmi da tabarya suna alfasha da har za ku yanke hukunci?A ma sanya sun yi din nan sashin Waye?A iya sani nan nan sashi Umma ne,kuma shi aka kama a sashin ba ita aka kama a sashin su ba,don haka wanda ya ke nema shi ya kamata ya kai kan shi ba wanda ake nema bane zai kawo kan shi,amman dake dukkan ku dakikai ne Jahilai marasa ilimin both addini da na boko kuka hau kuka zauna don ya ce da ku ita ke neman shi,ba za kuyi amfani da common sense din ku ba,har kuke kokarin yi wa Mace Uwa tsiraici a bainan jama'a shame on you all Wlhy"

Chak suka yi tsit domin sai yanzu kuma hankalin kowa ya dawo jikin shi,tabbas inda ita ta neme shi da ita ya kama ta a tsinta a dakin shi ba wai shi a tsince shi a sashin ta ba,amman dake yan duniya ne wai in mutum ya tsane ka ko ruwa ka shiga sai ya ce ka tayar da kura

"Yanzu Hajiya saboda girman Allah wanann karamin yaron da ba a san daga ina ya fito ba za ku dauki maganar shi ku bar nawa?"Abban Latifa ya fada kamar shirin kuka.

Juyo wa FIK yayi tare da watsa masa kallo "amman Wlhy ka ji kunya sanann baka da mutunci ko kadan amman babu komai daga yau ba za ka sake yi wa kowa sharri ba har ka koma ga Allah I will make sure nayi putting naka in your place ko kyauta aka ce kayi wa mace sharri gaba ba za kayi ba,Umma uwa ta ce ba zan dauki kowa ya ci mata mutunci ba,Wlhy tallahi gaba dayan ku sai na sanya an yi jailing din ku duk sai kun kare rayuwar ku a jail mutanan banza kawai"

Da sauri Hajiya tace "Sadauki mecece kuma wai Jan yake ko jail??"ta kare cikin ta na duran ruwa ganin yanda yaron ya hade rai ba karamin kwarjini ya bata ba.

"Momcy wlhy kasusuwan nan zai hada mu da su wai jail Ai bayan kanta ne"da sauri hajiya ta dafe kirji "Wai Folis sitesion kake nufi zai kai mu Sadauki"ta fada tana zazzare idanu

Kallo ya watsa mata sanann yace "can nake nufi Illiterate in kika je kika sha bugu you will get back to your fucking sense and za ki daina sa ido a abunda ne shafe ki ba ba ke ba Wlhy duk sai yan sanda sun kama ku duk sai na tabbatar da kun wulakanta kamar yanda kuka yi kokarin wulakanta Umma"ya kare kamar zai rufe su da duka.

"Bura uba kai dan gidan uban Waye da za ka shiga gidan mu kana fada wa Momcy na magana?"Fatah ya kare yana kokarin kai wa FIK bugu,kaucewa FAIZAAN yayi ba shiri ya kara dauke shi da mari "better maintain yourself you low life na fika hauka in baka sani ba,da kake maganar gida har wanann dauka kake gida ne?Shame on you and your fucking Dad da ya gina wanann wawan gidan da kake tunkaho da shi a matsayin gidan uba,dan Uban ka ni ba sa'an ka bane domin mune da Kano one phone call Wlhy sai na sanya a batar mun da kai da family din ka gaba daya,domin muna da halin haka don Baba na shine Isma'il Kwairanga ka ga kuwa mu ke
da garin Kano da kewaye baki guda and I promise you sai na sanya ka ka gane kuskuren ka da kai da wancan tsohon dan iskan don't think kuma zan Kyalle ku ne,daga ke ya nuna Ladi har ke ya nuna Shafa da Atika duk Wlhy sai an tafi mun da ku,sai na tabbatar an ci mun uban nin ku sannan za ku rubuta Undertaking babu ku babu ita ba za ku kara shiga rayuwar ta ba sanann a sako ku,in dai kudi da connection na aiki a kasar nan yau sai kun ga abun mamaki"ya kare yana daukan wayar shi.

Hankali a matukar tashe Hajiya Ladi tace "na shiga uku ni Ladi wanann shine daga zo ka ji sai ka ji duka,miye abun kiran yan sanda haba Wlhy kai dai Ahmadu ba mutumin kirki bane yanzu don wulakanci kamar Bilki za kayi wa kazafi?Wlhy ka ban kunya ke kuma saboda sakarya ce Shafa har kika dauki maganar wanann lusarin mijin naki har kuna kokarin tube baiwar Allah akan laifin da ba nata ba kuna neman kashe ta a banza,Wlhy da badun wanann yaro dan Albaraka ba Ai da an yi abun kunya,Ayya Bilki kiyi hakuri ko Wlhy ashe ba laifin ki bane wanann shegen me mugun nufin ke neman ki da sharri,Wlhy ka tattare su ka kulle shegu gaba ba za su kara ba,ni a nan na zan rubutua Unpataking yake ko Waye,daga yau ma babu ruwa na Wlhy daman ni tsakani na da Bilki Ai sai san barka"ta kare tana yaken dole.

Idanu kwai duk suke bin ta da shi,don ta basu mugun mamaki inda take kokarin zame kan ta,inda FIK ko a bin ta kan ta be yi ba a kira CP tare da requesting mota guda na yan sanda yanzu yanzu ya kashe tare da fada musu inda za su zo yanzu su same shi

Da jin haka kuwa suka fara kokarin zame wa ciki ko harda Hajiya Ladi inda ta fada toilet sai zawayi yau in aka kai ta station Ai kashin ta ya bushe,nan fa FAIZAAN ya sanya aka rufe masa kofa ba tare da bata lokaci ba kuwa yan sanda suka iso inda da hannu ya nuna musu Ahmadu Fatah,Atika da Maman Latifa yace a tafi da su sai ya zo,hankalin Shafa be tashi ba sai da ta ga an tisa keyar su an sanya su a mota snanan ta fara nadamar me ma ya kai ta biye wa Mijin ta bayan ga Gaskiya nan tana gani akan idon ta,Atika kuwa saida aka buga mata tsawa don zagi da cin mutunci ta shiga watso wa Shafa da mijin ta,sam be lura da Hajiya Ladi bata cikin su ba sakamakon yankan jikin da Umma tayi nan kasa babu numfashi a tattare da ita,hankali a matukar tashe ya kira driver tare da sanar da shi maza maza ya zo da mota yanzu yanzu,inda yace da Meeno da Shatu su shirya Umma kafin Mota ya iso sai su wuce asibiti,ba tare da bata lokaci ba kuwa driver ya iso saboda warning din da FAIZAAN ya buga masa a waya,inda kuwa da taimakon su Shatu da Mahaifiyar ta tare da sauran matan gidan aka sanyan Umma a bayan mota babu alamun numfashi a jikin ta FAIZAAN ya shiga tare da cewa Shatu ta shigo su tafi tare in sun isa a kira Sabeeha a sheda mata halin da ake ciki,inda ba musu kuwa ta sako Hijab din ta ta shiga a mugun tsiyace suka dau hanyar asibiti........

Ayi hakuri da typing errors ban riga nayi editing ba.

A cigaba da commenting da shearing saboda Allah🙏

Ina godiya tare da jin dadin adduoin ku da fatan Alkhairin da kuke mun Allah ya so ku fiye da haka na gode sosai

Ina yi wa kowa fatan Alkhairi ❤️

Continue Reading

You'll Also Like

5.4K 19 5
القصة تحچي قصة هيثم طالب بالصف السادس الادبي لاحد المدارس الاهلية المختلطة
27K 4.3K 13
In the elite ranks of DRDO, Ardik Rajwasnhi, a young prodigy, is fueled by ambition to secure a coveted position among the legendary Team Phoenix. Ho...
179K 8.8K 42
After going through a number of disasters I realized that actually I am reborn as the villainess character, more of a brat, Chloe Bourgeois, in a chi...