A SIMPLE DARE (WASA DA SO)

By marteybee

496 8 16

More

new book
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page ten
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20/21
Page22/23
Page 24/25

Page 15

27 0 0
By marteybee

✨✨

                     SIMPLE

                                         DARE

✨✨

                       (WASA DA SO)

                WRITTEN AND STORY
                              BY
                  NERNAH MARYAM
                           (MEEMARH)


Kofa a bude take ga duk me son yin joining group dina😌,Amman Hajiya don Allah in kin san ba yin comment ko karanta littafi na zai kawo ki ba I beg you in the name of Allah kiyi zaman ki ba sai kin shigo ba!!haka zalika wanann group din na mata ne zalla don Allah Maza should stay away from my group👏

My What's app group link👇🏻

https://chat.whatsapp.com/EUrVVaKJnIBDTlQsxurZv0

           Bismillahi Rahmanin Raheem............

      ( In the name of Allah the most beneficient,the most merciful)


Kofa a bude ta ke ga duk wani me good quality product da ya ke son Advertising ɗin shi,as Kaya masu kyau,da inganci (TALLAH) should contact me via :
08100046388

                 Page 1️⃣5️⃣

           TALLA!!TALLA!!TALLA!!!

https://chat.whatsapp.com/ImtxMSS1tuSKqvBpPqc03P

Assalamu'alaikum sisters🤗
KAMSHI* mace Mai kima, mace Mai daraja, mace Mai izza, mace Mai aji itace tasan darajan kamshi, if your perfume is not unique hajiyata you're just using ordinary air freshener🤣, hajiyata ko nawa Zaki kashe indai a turare ne baki Fadi ba😘 matan da suka gane suka San yanda zasu kankaro da martabar su, suke amfani da turare, a *BAKHOOR BY FAIXY* Zaki Sami Main chic, Bachelor, Husband snatcher, Her royal sexiness, Mysterious girl, Pleasure, Boovilous, White khumra, Maroon khumra, Black khumra, Hair perfume, Turaren wanka, Turaren wuta, Turaren tsuguno, Turaren mopping,Turaren carpet Shu'umat khumra,and more, yar uwa kar kibari abaki lbr, (wholesale and retail) WhatsApp 09067621681, siyan na gari Maida kudi gida🥳

Instagram @Bakhoor_by_faixy

******************************

     "Geeeeee!!wai anya baka ganin you are taking this SIMPLE DARE!!!way to far?FIk what the hell is wrong with you ne don Allah this is just  A SIMPLE DARE for crying out loud why kake yi kamar wanda ya ke bala'in son ta?"Nabeel ya kare a zafafe

"Hold it Pls Beel just hold it and let me be,ni ba karamin yaro bane for your own information na san abunda nake yi,and left for me ko ina son ta ko bani son ta wannan ba damuwar ka bace,all that really matters is sai nayi proving abunda na fada within 3 months,bana magana biyu and ba zan fara a kan ka ba so left for me in san yanda zan yi putting plans dina in action wanda babu ruwan ka da koma miye zan yi,Beel ba kudaden ka nake kashe mata ba na farko ke nan,and ba kai nake sanya wa ka kira ta ba balle kace ka soma gajiya,hasali ban ce ka taimake ni da komai gurin winning heart din ta ba so don Allah ka shafa mun lafiya haka nan ka fita harka ta,just ka koma ka zauna kayi kallo in har wata uku suka cika Sabeeha bata ce tana so na ba then my fav Car is yours,da wanann kananun mitan da kake mun kullum da zuwa kayi ka fara planning yanda za ka dauko mun Rolex din Old Man din ka da ya fi maka don I'm very sure ba zan fadi ba"ya kare yana mike wa tsaye.

Hararan shi Nabeel yayi sanann yace "But FAIZAAN!!!",hannu ya yi saurin daga mishi don har ga Allah ya gaji da wanann korafi da Beel ke masa a kullum bayi da magana sai zance guda a zafafe yace

"Nabeel!!!can you stay out of this pls,haba yanzu fa na gama maka bayani sai kace baka fahimta ko baka gane wa,what else kake son ji daga guri na kuma??Sarai ka sani bana son dogon magana musamman ma wanda zai bata mun rai,haba wani irin abu ne haka magana daya mun yi ta yi ke nan"da sauri Farouq ya ce

"Haba Geee be calming down mana miye haka akan wata banza can za ku tsaya fada a tsakanin ku??Kuna ganin hakan yayi haba"

"Kyalle shi Farouq Ai ba gane wa yake yi ba,sarai ya san abun nan duk saboda mu nake yin sa,I don't think duk duniya akwai wanda ya kaini tsanar yarinyar nan,in kun san yanda nake daure wa in danni heart dina kafin in kira ta sai kun tausaya mun,I'm doing all this for your guys ba wai don kai na kawai ba amman Beel ya kasa fahimta,in har ban yi haka ba a taya za ta saki jiki da ni har ta yarda eh da gasken son ta nake har ita ma ta so ni??Kar fa ku manta wace ce ita manta da ta fito daga middle class family yarinyar akwai Jan class da self respect sannan  uwa uba bata taba soyayya ba in har ban yi haka ba a taya zan janyo attention din ta har ta fada soyyaya da ni?Duk tunanin Beel son yarinyar nake yi wanda mentality ne kawai irin na shi,kai ka sani ko in ce duk kun sani sam bata da qualities din da nake nema tattare da mace,na yi zama cikin turawa da Larabawa duk ban so su ba sai Sabeeha??Wai kake thinking zan fada soyayyar ta??Bata da wayewar da nake nema a gurin mace sanann bata da aji da nake so tattare da mace,In fact Sabeeha bata da ko daya daga cikin abubuwan da nake nema a gurin mace  amman sam ka kasa kwantar da hankalin ka ka fahimci I'm just playing her ne,haba I'm fade up with all this bullshit of yours wallah"ya kare a zafafe yana son barin dakin.

Riko hannun shi Beel yayi tare da dawo da shi ya zauna sanann yace "C'mon dude I'm sorry okay ba wai in fadan haka don na bata maka rai bane,kawai ina jin tsoro ne kar along the line ka fara developing feeling wa ita ya sanya nake fadan haka"

"Beel mark my words ni Faizan babu feelings din Sabeeha da zan yi catching don't you trust me??Ko ka mance Waye ni ne FIK ne fa,haba Ai ya ci ace a wani za ka bada labari na ba wai a baka ba,so worry no more okay I got nothing to do with her,daga 3 months sun cika ka bani watch dina Sabeeha will be out of the picture,kana tunanin wai yarinyar tana burge ni ne??Ko gani kake ni ban tsane ta ba?Beel
She slapped me right on my chic fa and kana tunanin in fara son ta haba wake up guy,ko za ku iya mance wa ku yafe mata ka san na rantse maka I must avenge marin da tayi mun,and tunda nake ko da wasa ba wanda ya taba kai hannu jiki na sai ita and kana tunanin ta daki banza ne,shirya mata nake wlhh sai tayi kuka kukan da bata taba yin irin sa a rayuwar ta ba and bana jin har ta koma ga Allah za ta kuma irin sa,sai na yi breaking din ta down into smaller pieces inda ba za ta iya kallon kan ta a mirror ba ma balle tayi tunanin hado pieces din back ta tayar da kan ta,just watch and see how I will destroy her life,banda abun ka Ai 3 months ya kusa so time will speak ba sai na ce komai ba,ku tashi mu tafi kar a fara party babu mu,in samu mu dawo in kira that Middle class Twat of mine,na samu na kashe shegiya da kalamai masu zafi🥱"ya kare yana saka Expensive Shade din shi a idanu tare da feshe jikin shi da turaruka masu shegen kamshi.

Wata wawiyar dariya duk suka sanya sanann Akram yace "ku ji tsoron Allah guys ku tsoraci FIK,Kai FAIZAAN!!Baby girl din ta ka kake kira Twat??Tunda nake na jima ban ga shege irin ka ba gata Twat ga ta Middle class,abun yayi yawa ai"

Dan dariya yayi sanann yace "Akram to in ba Twat ba me zan kira ta da shi?Ai sunan shine ya dace da ita"dan dariya Jawad yayi sannan yace "Wlhy in badun mun san Waye kai ba babu wanda zai ga yanda kake kashe yarinyar nan da kalamai ya dau ba son ta kake ba,Breakfast har gida fa aka kai mata yau,Wlhy ko Zuma rock ne ya danne heart din ta sai ka shiga mutumi na,na san tana can tana tunanin ka don babu abunda yam mata ke so irin haka Wlhy duk wace ta samu Romantic and caring babe like you to ita kan ta ba za ta san time din da za ta fada son ka ba,shege fada mun a ina ka iya duk wanann abubuwan?"

Kafadan shi ya dan daka sanann yace "tsaya wasa Mommah da Soul sis ke bani course na musamman Ai nima jiki na na bani na kusa shawo kan yar banza wannan cika bakin bana soyayya bana soyayya duk zai kare Ai tunda ta shiga harkan Rocket gang sai mun koya mata hankali,ku zo mu tafi, tayi ta tunani na tun safe sai zuwa anjima zan kira ta in kara birkita mata lissafi,don ma tana da taurin kai Ai da tun day one na samu soyayyar ta,amman ba komai with time da ni take wasan"ya kare yana juya car key din hannun shi,duk dariya suka sanya tare da yi masa shegiyar kirari dake kara wa kan shi girma sanann suka fito daga side din dake mallakin su a gidan su Beel,tare da fadawa mota suka fita a tsiyace,wanann daman a rubuce yake duk gidaje biyar din nan suna da part guda wanda yake mallakin su ne,in sun zo duk nan suke zama.

   *********************Sabeehatu

     "Auta Gaskiya wanann Abokin nan ki ba dai zakin hannu ba,ko a gidan abinci sai haka,ki ji girki kamar ba girkin maza ba",dariya Sabeeha ta fashe da shi tana daunan cinyar kaza a hankali sannan tace "Umma Ai akwai maza da yawa da suka iya girki wanda a wani lokacin ma ana samun sun fi wasu matan iya girki,ko a class din mu akwai maza da yawa wanda suke karantar course din,amman bana jin shi yayi abincin nan Umma"

Kallon ta Umma tayi sanann ta ce "ikon Allah yau ni Bilki ni na ga yaran zamani da idanu na,to wai ke har yaushe kika san shi da za ki banbance girkin shi da ba na shi ba?Auta anya baki dade da sanin yaron nan ba kuwa?Kike boye mun"Umma ta kare tana tsare ta da idanu.

Da sauri ta aje cinyar kazar sanann tace "na shige su ni Sabeeha Umma wai da me zan rantse miki ne ki yarda da ni don Allah,Umma wlhh ni ban san shi ba,kuma da na san shi sai na boye miki haba Umma"ta kare tana cuno baki.

"Yo Ai abun ne da daura kai,na ji kin ce ba shi yayi girkin ba,to in ba sanin shi kika yi har haka ba a taya za ki fahimci shi yayi ko ba shi ba,Auta ki ji tsoron Allah ki daina mun boye boye"

"Yau na ga ta kai na da Hajiya Bilkisu"dakuwa Umma tayi mata sannan tace "kin ci gidan ku,nace gidan ku Sabeeha,wato daga fadin Gaskiya shine kin ga ta kan ki da ni"

Dan dariya Sabeeha tayi sanann tace "kwantar da hankalin ki Umma,Wlhy ni dai ban san shi ba ba karya kuma nake miki ba,and abunda ya sanya kika ji na ce ba shi yayi abincin ba Umma Wlhy yaron spoiled brat ne"

Kallon ta Umma tayi sanann tace "shi kuma meye?Meye wani Spoiled brat?",dan murmushi tayi sanann tace "Kai Umma to ina nufin shagwababen yaro ne wlhy ba ki ji ba inda kika san wani dan goye abu daya Mommahn sa an sanganta shi sosai,da sosai Umma,bana tunanin wanann ko ruwan zafi ya iya dafa wa balle ace wanann whole abincin"

Kai Umma ta girgiza sanann tace "kai ni raba ni can ku kuka sani,yaro dai yayi kokari ubangiji yayi mishi Albaraka ya kuma ba shi sa'an shawo kan Autan Umma cikin sauri a sha biki"ta kare tana yar dariya.

"Ummaaaaaaaaaa!!!!Allah Umma ki bari ban so"Sabeeha ta kare tana matso kwalla,dariya Umma ta sanya "ikon Allah yau na ji abunda ya girmi kaka na,to don Allah a yaushe kika ji na kira sunan ki?In ce Autan Umma na ce?Ke kuma na ga ai sunan ki Sabeeha,ko sunan ki Autar Umma??"Umma ta kare tana danne dariyar ta.

"Ni Wlhy Wlhy Umma ban yarda ba,babu wata Autar Umma sai ni Ai ni ce Autar ke kuma Umma yasin da ni kike yi"ta kare tana yar kananun kuka daga ji kun san na zunzurutun sangarta ce da samun guri.

Ture ta Umma tayi sanann tace "kin mun shiru ko ko?Ai ba dai kin ci kin koshi ba dole kiyi mun sakalci,Allah Auta ki fita idanu na tam"baki Sabeeha ta cuno sanann tace "yau ga ikon Allah Umma ga mari ga tsinka jaka ke da za ki lallashe ni,yasin Umma kin daina so na yanzu kam"ta kare tana matso kwallan gulma.

"Kin maida kwallan gulman nan da kike shirin zubo su kin mike kin tattare gurin nan tare da wanke kwanukan nan ko sai na zane ki"Umma ta kare tana mike wa.

Dariya Sabeeha ta sanya tare da tashi ita ma "Haba Umma yanzu tsakani da Allah babba da ni sai ki zane ni?"ta kare tana sunkuyawa don tattara gurin,saukan dundu ta ji a gadon bayan nata wanda saida ya sanya ta bankare wa tare da rintse idanu tace cikin muryan sangarta "Wayyo Allah Abba na"

Harara Umma ta maka mata "ko gidan miji kike Auta kika yi ba daidai ba zan zane ki balle yanzu har nawa girman taki take?Maza wanke kwanukan ki aje su kitchen sai ki zo ki tafi kasuwa"

Kallon Umman tayi sai ga hawaye na zubo mata wanda ban ma san lokacin taruwan su ba,ai take hankalin Umma ya tashi in a duniya akwai abunda ta tsana to be wuce kukan Sabeeha ba

"Auta wani abun aka miki kike hawaye?"Umma ta tambaya a rude,cikin jan hanci da salon gulma irin na Sabeeha sai kai ta girgiza alamun babu komai.

"Kin taba ganin an yi kuka ba tare da dalili ba?Hwaye kan zuba wa mutum ne a yayin da yake tsantsan farin ciki ko kuma akasin haka,taki kukan ta mecece?"ta kare tana ruko hannun ta.

"Umma baya na ne ke mun zafi,sai kuma kika dunde ni shine na ji kamar an raba bayan biyu,ban ma san lokacin da hawaye suka zubo ba"ta kare tana share hawayen nata,kai Umma ta girgiza don sarai ta san iskanci ne kawai da sangarta irin na Sabeeha ko in ce rikicin Autan ne yau suka matso in banda haka nawa hannun nata ma yake and dukan ma ba me zafi tayi mata ba shine harda su hawaye,wai daman ance me neman kuka to da kashin Awaki aka jefe shi sai ku ga ya wangale baki.

"To afuwan Autar Umma hannu na ne ya subuce goge hawayen kin ji,faran mace bata kuka"dan dariya Sabeehar tayi daman abunda take son ji daga gurin Umman ke nan,a take kuwa ta tattare gurin ta nufi waje don wanke su ta shiryo ta tafi kasuwa.

Bata dau lokaci ba kasancewar kwanukan ba yawa gare su ba,inda ya shiryo cikin basket haka ita ma ta maida komai ciki bayan ta bari ruwan ya tsane,kitchen ta shiga tare da aje wa a gefe guda sanann ta koma dakin ta don karasa shirya wa ta wuce kasuwa.

Dake ba canza kaya za ta yi ba so dan kwalli ta kuma shafawa tare da man baki,sanann ta gyara rolling din ta tare da feshe jikin ta da turaruka,sannan ta sanya takalmi,har ta fita sai kuma ta dawo dakin tunowa da tayi ta baro wayar ta akan katifar ta,daukan wayar tayi tare da kunna home button din inda ta ga kiran Zuhra da messages sun fi goma,dariya ta sake tare da yin kwafa sanann ta bude wayar,saidai abun da ya dan bata mamaki babu kiran Mr I love you kamar yanda take kiran shi.

Daga sanda ya fara kiran ta a waya bata samun hutu yayi ta damun ta ke nan,ta dauka tun safe za ta tarar da kiran shi sai ta samu ta mishi godiyar break fast amman shiru,dan baki ta tabe sanann tace "may be yana busy"daga haka ta jefa wayar jaka,har ta fito sai kuma ta kuma tsayawa tare da bude jakar ta dauko wayar.

"Ko ba komai ai ya kyautata mun,godiya kuma hali ne me kyau,duk wanda baya gode wa Alkhairin mutane to alamun ba ya gode wa Allahn shi"ta fada a hankali tana me turo baki ita kadai kamar an mata dole,tsintar kan ta tayi da bude wayar tare da nemo number din shi sanann ta shiga inbox din ta

   "Hey thanks for the breakfast,it's was delicious,I really enjoyed it!!"

    Shine sakon da ta rubuta take ta karantawa ya fi sau goma amman ta kasa turo sakon da ta rubutan saida ta ji Umma ta kwala mata kira ne,wanda ya so firgita ta,inda tayi saurin danna send tare da jefa wayar cikin jaka,ta rufe jakar kirif kamar mara gaskiya.

Da sauri ta fada dakin Umman sanann ta ce "na tsaya kara shirya wa ne Umma"dan hararan ta Umma tayi sannan tace "Ke kam sai Allah ni ban ga amfanin shirin ba Ai,tunda ko an tare ki ba tsayawa kike ba,au na mance ashe yanzu kam Alhamdulilah an samu cigaba tunda har ana wayar dare"

"Ummaaaaa,yasin yamma za ta yi fa ban je kasuwar ba balle a san abun dafawa"dan numfashi Umma ta sauke a hankali sanann tace "Auta rayuwar ce yanzu Wlhy sai a hankali kullum kaya kara hawa yake yi,tunani nake yan kudadan hannun na mu ba wani siyayyan kayan arziki zai yi mana ba,a yanda Dalla da Man fitri ke ta hauhawa kullum na ranar Allah babu wani sauki da talaka zai samu sai gurin Allah,yanzu ko dubu dari kika shiga da shi kasuwa za ki kashe su tsaf a abunda ba zai kai hour guda ba ma,and abun haushi be wuce ki ga dan siyayyan dan kadan a cikin Leda ba amman ki ji ana kira miki kudade"

Ajiyar zuciya Sabeeha ta sauke ita ma sanann tace "Wlhy Umma abun kam akwai abun dubawa rayuwa kullum dada tsanan ta yake,babu wani sassauci ko dadi in ba kana da kudin ba yau za ki sai abu a farashi kaza zuwa gobe ki ji ta canza,ubangiji ya kyauta ya kuma kawo mana karshen wanann hali da muke ciki ba don halin mu ba"

"Ameen thuma Ameen Auta Ameen Allah ubangiji ya amsa,tunani nake kar mu kwashe duk kudaden hannun namu a siyo kayan abinci mu tashi kuma ba
mu da sisi,ga Hajiya da zan cire mata kudin ruwa da wuta,sanann ke ma ga na tafiya makatanta tunda gobe Monday"Umma ta kare tana ciro iya kudaden hannun nata da basu taka kara sun karya ba.

"Umma ki kawo nayo cefanan yau da gobe zuwa jibi in ya so sai mu jira mu ga abunda Allah zai yi,maybe kafin nan na kuma samo wata order din, sannan Umma a kullum ke kike fada bakin da Allah ya tsaka baya taba hana shi abinci,I believe in sha Allah watarana komai zai wuce zai zamo labari"

"Allah ya wutar mana da shi Auta Allah ya sa,ubangiji ya kuma miki albarka,yanda kike so na kike tausayi na ubangiji ya so ki ya tausaya miki kamar haka,tashi maza to karbi nan 15k ne kina ga zai isa Ai ko?"

Karba Sabeeha tayi tare da sanya shi a jaka sannan tace "zai yi Umma,Allah ya kara rufa miki asiri,ya baki ladan ciyar da marainiya,sai na dawo Umma zan biya ta gidan su Zuhra sai ta raka ni kasuwar"ta kare tana fita daga dakin.

Da kallo Umma ta raka ta tana me jin hawaye na ta ruwa mata a cikin idanun ta,duk duniya babu abinda take so take kuma alfahari da shi a yanzu sama da Sabeeha,tana kara wa Allah godiya a kullum da ya bata yarinya me hakuri nutsuwa  kwazo da sanin ya kamata irin Sabeeha,in kuma adduar Uwa karbabbiya ce akan yaran ta yi ba shakka kullum cikin roka wa Sabeeha daukaka da samun nasara take a rayuwar ta.

"Ki kula Auta,ki kuma gaida Maman Zuhran Allah ya kiyaye hanya kar ki manta da yin adduar fita daga gida da kuma na hawa abun hawa"da to Sabeeha ta amsa snanan ta fito daga cikin sashin na su tana yar wakar ta na 'Shape of you'hankali kwance ta fito waje don bata tarar da kowa tsakar gidan ba,ita kan ta ta ji dadin hakan ko banza ta samu bakin ta ya huta haka zalika ears din ta ma sa huta,su ma su huta wa nasu ran.

Saida ta dan taka kasancewar rashin abun hawa hakan ya bawa kananun samaruka masu yawo da wando a sabule daman bin ta da sunan wai suna son ta ta kuma basu number din ta,kallo ba su ishe ta ba balle har su sanya ran za ta amsa su,sarai duk wanda ke unguwar ya san wace ce Sabeeha sanann babu wanda zai ce ya taba kama ta da wani tsaye ko kuma
Mota ya zo da sunan zance ya zo gurin ta,amamn duk da hakan ba a rasa yan naci wanda kallo daya za su wa kawukan su,sanann su kuma kalle ta su san eh tabbas ta fi karfin su,amamn saboda zalama da kai kai inda Allah be kai ka ba,wai sai sun tsare ta.

Duk yanda suka so pim ba su ji daga bakin ta ba,hakan ya sanya suka hakura suka Kyalle ta,gaba kadan tayi kuwa cikin saa ta samu abun hawa so hawa tayi tare da fada masa  inda zai aje ta,har ta matsu ta kalli idanun Zuhra don sarai ta san ba karamin Shaka mata tayi ba.

Ba wani dogon tafiya suka yi ba kasancewar basu da wani nisa,za ma ka iya takawa da kafa ma ka je,biyan shi tayi kudin sa tare da karban change ta jefa a jaka sanann ta shiga gidan,a zaure ta tarar da Abban Zuhra zai fita,cike da fara'ar ta ta durgusa har kasa tare da fadin

"Sannu Abba ina wuni"kallo ya watsa mata irin mugun matsiyacin kallon nan kafin yayi kwafa ya ja tsaki tare da barin cikin gidan ko duba be kara mata ba,jiki a sanyaye ta mike tare da bin bayan shi da kallo har ta bace wa ganin ta,mamaki take me ya faru ko gaisuwar ta ya kasa amsa wa?Duk da can daman ba wani sake mata fuska yake ba amman duk ta zo ta gaishe shi yana amsa wa har ma ya tambaya ya Mahaifiyar ta take,to ko tayi masa wani laifi ne?Shine abunda take ta tambayan kan ta.

Jiki ba kwari ta mike tare da shige wa cikin gidan bakin ta dauke da sallama,a tsakar gida ta tarar da Mama zaune tana gyaran Alaiyaho, cike da fara'a tace "ah Sabeehatuwa ke ce tafe cikin ranar nan"

Dan dariya Sabeehar ta sanya sanann ta karasa kusa da Maman tare da durgukasa "eh wlhy Mama ni ce ina wuni?"ta kare tana kokarin karban gyaran ganyen da Mama ke yi,don taya ta.

"Lafiya klau Autan Umma,ya gida ya Umman taki,fatan duk kuna lafiya ko?Bar shi Sabeeha Ai na zo karshen gyaran ma nima ina shirin tashi in daura girki ne"ta kare tana hana ta karban gayen hannun nata.

"Mama duk muna lafiya Wlhy Umma ma tace na gaida ki,tana ta son shigowa bata samu lokaci bane", "Ai abubuwan ne yanzu sai a hankali,tunda da rai da lafiya Ai Alhamdulilah komai ma me sauki ne,tashi ki shiga tana ciki tun safe tana kwance wai bata jin dadi,ciwon ciki take"

Tashi wa Sabeeha tayi sanann ta nufi dakin Zuhran tana fadin "Subhhanalli ashe ma bata jin dadi,no wonder mana na gaza samun kwanciyar hankali ashe Habeebteey darling babu lafiya"ta kare tana yaye labulan dakin,dan dariya Umma ta sanya domin ganin wanann kaunar da ke tsakanin Zuhra da Sabeeha ko ciki daya suka fito sai haka.

Cinyar ta ta samu  inda ta  dunkule guri guda tana bacci tare da maka mata wata wawiyar duka,tare da cewa "tashi uwar son jiki ke dai Zuhra da bacci kamar wata me yaron ciki"ta kare tana zauna wa akan kafafuwan ta.

Dan kara Zuhra ta sanya tare da kokarin mikewa saidai nauyin Sabeeha ya hana ta tashi, "Wayyo Allah na Mama wanann katuwar za ta karya miki ni"ta kare tana dan daga murya,da sauri Sabeeha ta rufe mata baki tare da mike wa daga kan kafan nata

"Ke fa dadi na dake rashin hankali,so kike Mama ta ji ko me"mikewa Zuhra tayi tare da zama sanann ta galla mata uwar harara, "kin san Allah Sabeeha in baki bar dakin nan ba sai na ci miki mutunci"ta kare tana kan hararan ta.

Gyalen da tayi rolling ta kunce tare da aje jakar ta sanann ta fado jikin Zuhran "babu inda za ni yasin ko kina so ko baki so Zuhra haka za ki zauna da ni har randa za mu koma ga Ubangijin mu"

Tunkude ta Zuhra ta hau yi "Ke Kyalle ni ana dole ne?To ni bana son ki bana son zama da ke kowa ya kama gaban shi a rabu kawai ina dalilin zama da muguwa irin ki,bayan abunda kika mun ina kwance bana jin dadi amman saboda mugunta shine kike son karasa ni"ta kare kamar me shirin kuka.

"Goofy angel kin fiye raki Wlhy akwai haihuwa fa a gaban ki"dake ta Zuhra tayi da dan karfi sanann tace "ina ruwan ki😒,in ce ni zan haihun ba ke bako banda mugunta stomach cramps fa nake fama da shi,sarai kuma kin san yana bani wahala,ni tashi ki tafi ba zan miki magana ba don babu ruwa na da ke"

"Na shiga uku ni Sabeeha an fasa Auran Goofy angel da Habeebeey"da sauri Zuhra ta rufe mata baki "Ke raba ni ki raba kan ki rufa mun asiri kar yan ameen su amsa aka fasa aure na da Habeebeey Ai ba lafiya"ta kare tana hararan ta.

Dariya Sabeeha ta saka sanann tace "Baru uwar soyayya ke kam in baki auri Mansoor ba yarinyar nan ina ji duniya za ki shiga,tashi ki zauna to kin sha magani ya kuma jikin naki?"

"Ban sanin ba ya dame ki ne,Sabeeha Wlhy yau kashe ki ne kawai nan yi ba saboda ma san kisa haramun ne,Messages nawa na miki dropping amman don iskanci baki iya bude wa ba,sarai kin san in ina period ina jin kwadayi shine don mugunta kika turo mun irin wanann kayan dadin?A gidan uban wa ma kika samu har kika ci kika cinye baki tuna ni ba?Ko ke ma gani kika yi shine kika ce bari ki dagan hankali"ta kare tana hararan ta.

Dan dariya Sabeeha ta saka kadan sanann tace "yarinya man kaza,kina ina ni na ci dadin ga yasin ba ki ga Customized Mug  me suna na a jiki ba,Breakfast in bed aka kawo mun"

Idanu Zuhra ta dan zaro sanann tace "Tell me more Kawata kina son ki ce mun ke aka kawo wa duk kayan dadin nan?Abincin yan gayu ne fa,irin wanda sai ka je Restaurants kake gani,tunda nake ban taba ci ba kuma don bakin ciki kin san za ki zo baki iya kawo mun ba ko zero Ai na goge in na ci ko?"

Wata dariyar ta kuma yi sanann tace "Kawataaaaa ta kaina sorry about that nima Wlhy kamar wasa ban zaci za a kawo mun ba,I thought da farko wasa yake yi,kawai sai kiran driver na gani,kuma Wlhy in kika ji dadi kamar ka hada da fingers din ka ka cinye in kana ci"

"Au daman fa in kika ce dadi ma Ai kin ce daya,Wlhy daga gani a ido na san dole dole ya zamo dole ne ma yayi dadi,irin wanann abinci Goofy angel mun yi saurayi ke nan?Wlhy Sabeeha zan miki sending thunders in har baki daina boye mun abubuwan ki ba,shegiya sai kace kina da wace ta fini,ko kin yi sabuwar kawa ce bani da labari?Sarai kin san kullum abunda nake jira ke nan ki ce mun Goofy angel I'm finally in love,shine ashe kika munafurce ni har na fara kawo breakfast bani da labari,inda ni ce jiki na na bari zan sanar miki,yayi kyau Wlhy duk wanda ya ci amana ta Allah ba zai bar shi ba"ta kare tana hararan ta kamar idanun ta za su fado kasa.

"Calm down my love let me explain kafin ki fada conclusion,ba fa abinda kike expecting bane ni babu saurayin da nayi", "Ai Ex Goofy angel dita ko duk jiki na kunne ne babu abinda zai sanya na yarda da wanann maganar naki,ko kunya ta ma baki ji ba ni za ki kalla ki ce wai ba saurayin ki bane,uban Waye zai kawo miki wannan delicious meal din har gida,ke Goofy angel ki ji tsoron Allah Wlhy"

Dariya Sabeeha ta sanya har tana rike ciki sanann tace "Haba Babe Amarya a gidan Habeebeey hear me out mana,and for your own information ba zan taba zamo wa Ex a gurin ki ba har yanzu har gobe and will forever be your Goofy angel so kar na kuma jin kin kira ni da Ex,about this new guy issue kuma ba saurayi na bane,Zuhra kin fi kowa sanin wacece ni bana soyayya ban taba ba kuma ba zan yi ba,and ko nan ki tambaya ba ma ina da shirin sanar da ke Waye shi,ko na ce kin ma san shi,mutumin da ya bamu order ne fa"

Da sauri Zuhra ta tafa hannu tare da fadin "na sani daman Wlhy sai shi,ai kallon ki kawai nake Goofy angel,a marran rayuwar nan inda ake fama da rashi da babu,Waye zai dauki 100k ya kashe su akan Snacks?daman can na sani yasin son ki kawai yake yi"ta kare tana murmushin jin dadi don daman tayi tunanin FIK ne yayi and tunanin nata ya zamo Gaskiya,ita kan ta abun ya burge ta and ta san dole ya burge Sabeeha don abu ne da za ta ce bata taba gani a rayuwar ta anyi wa budurwan da ake nema ba,akan yi dai in anyi aure miji kan yi wa mata breakfast in bed amman banda in ana nema kan, "Gaskiya this guy is so super romantic ban taba sanin haka yake ba"ta fada out of excitement ita kanta bata ma san ta fada ba.

"Who is so super romantic har baki san haka yake ba Goofy angel?"Sabeeha ta kare tana tsare ta da idanu,dan rintse ido Zuhran tayi, sanann ta bata rai tace "ban sanin ba,ba maganar new guy din nan kike mun ba in ba shi ba da wa nake to?"

Kan ta Sabeeha ta kwade sannan tace "Ke Dalla ni nutsu in baki sauran labari"nan ko Zuhra ta gyara zama snanan tace "ina saurara"nan ko Sabeeha ta kwashe tas yanda suka yi da FIK tare da sanar wa Zuhra inda ta kare da fadin "Allah Goofy angel kai na duk kulle yake,ni ban ma san abu gudu da zan dauka ko zan tunana ba,ke kan ki kin sani I'm not used to all this,i can say this my first time da irin haka ke faruwa da ni,sam na kasa sanin inda ma ya dosa ni dai yace da ni yana son mu zama friends inda ni kuma nace aa coz duk duniya daga ke sai Umma kune friends dina kun ishe ni bana bukatar kari"ta kare tana cuno baki.

Dan kallon ta Zuhra tayi na yan mintuna sannan tace "do you like talking to him?I mean ina kina jin dadin waya da shi?"dan shiru ta dan yi sanann tace "actually I can say yes or no,but it doesn't matter,all I know is that yana bani dariya sosai duk sanda muke magana coz the guy is damn funny,yana da abun dariya sosai,ko ba komai yana keeping dina company"

"Goofy angel I never thought akwai ranar da za ki ce mun kuna waya da wani a rayuwa ta Wlhy,don tun ina da rai har na hakura,ashe dai za kiyi aure wataran"da sauri Sabeeha ta katse ta da fadin

"Zuhra!!!!can you stop all this pls,don mun yi waya da shi ba shi ke nuna muna soyayya ba fa,Zuhra ban san shi ba be san ni ba,and ko mun san juna friendship kadai yake nema daga guri na ba soyayya ba,shi din ma I don't think zan yarda,kawai na ga yana da hankali ne ya ma da nake magana da shi"

"What if son ki yake yi?kallon ta Sabeeha tayi irin What??,yeah kin ji ni da kyau what if son ki yake yi?I don't think haka kawai don friendship zai na miki irin wanann hidimar kila son ki yake gashi unfortunately ya zo gurin da soyayay ta Riga ta mutu babu halin karban shi"

"Goofy angel pls mana,ki daina irin wanann magana in sha Allah ma ba so na yake yi ba,I'm sure yana da budurwan shi can da suke soyayyar su,friendship din ma zan ce masa bani so,ko na huta da ke da Umma"ta kare tana mike wa tsaye.

Riko hannun ta Zuhra tayi sanann tace "aa Goofy angel kar kiyi haka,ba zai ji dadi ba in kika ce da shi kar ya kuma kira kuma ba ki karbi tayin abotan da yayi miki ba,just keep on talking to him,a hankali na san za ku rabu,kila ma tunani na ne ba son naki yake ba na tabbatar ma yana da budurwan shi so don't cut him off pls"ba tare da ta amsa ba tace "ni tashi ki shirya ki raka ni kasuwa"

"Amman Wlhy Goofy angel ban taba ganin muguwa irin ki ba,for Allah sake bani da lafiya baki kawo kayan dubiya ba sanann ki zo ki dauke ni wai na raka
ki kasuwa don mugunta da wulakanci"

"Ko ma miye ki ce Wlhy sai kin raka ni,ki tashi ki shirya ko na tube ki na shirya ki eheeeeee"ta kare tana murguda mata baki,dan dariya Zuhran tayi duk ta san haushin wai don tace kila son ta yake kuma ta roka ta cigaba da magana da shi shine take ta hade haden rai,ko hauka take  Ai ba za ta so ta daina magana da shi ba tunda ta Riga da ta san waye,and in ya cigaba a haka without her knowing zai sace zuciyar ta ta fada son shi bata ma sani ba tunda Alhamdulilah gashi da bakin ta tace tana jin dadin waya da shi.

Haka dai tana mita tana komai ta shirya suka tafi kasuwa bayan sun yi wa Mama sallama,ko da suka gama saida ta maida Zuhra gida sanann ta dawo gida inda Umma tayi ta fadan why ta dade ta je ta zauna
gidan su Zuhra sun samu tadi,bata ce da Umma komai ba ta shige kitchen sim sim sim tare da kokarin fara daura girki.

   *************************3 Days later

      Fitowan su ke nan daga Lecture inda Zuhra tace da ita su tafi Hostel ta dafa musu indomie su ci sai ta rako ta bakin gate ta koma gida,ba musu kuwa ta biyo bayan ta inda suna tafe hannun su rike da na juna har suka iso hostel din,kan gadon Zuhra ta fada bayan ta yaye net sanann ta lumshe idanu a hankali don ta dan gaji,wayar ta ta janyo tare da kunna wa saida babu missed calls ko guda,abun ya bata mamaki don tun randa ya kawo mata break fast ya kira da dare tare da fada mata he was so busy ne ya sanya ta ji shi shiru wanann ranan gaisawa sama sama suka yi ya kashe wayar kamar ba shi ba,saidai washe gari sai kiran driver ta gani kan ya kawo sako haka ya kara hado mata wata basket din full with kayan dadi,kwana ukun nan a jere ba a taba missing kawo mata break fast ba saidai shi din ne be kira tun abun be damun ta har ta dan damu,saboda Hausawa sun ce wai gaida me gaida ka ko ba zai amsa ba,tana son kira ta ji lafiya wani zuciyar kuma na hana ta,hakan ne ya sanya kullum take rike da Wayar ta har Zuhra da Umma suka lura don ita ba gwanan yawo da waya bane,sun tambaya lafiya?Tace da su ba komai,nan su ma suka watsar.

 
   Ko da Zuhra ta gama indomie din tare suka ci suka dan taba hira sannan tace za ta koma gida ganin bayan La'asar tayi to 5 ake nema,tashi Zuhra tayi tare da sanyo Hijabi sanann suka fito,Dan kallon Sabeeha Zuhra tayi sannan tace

"Ni ko ya kira kuwa?"da sauri Sabeeha ta kalle ta tare da fadin "wa fa?"dan dariya Zuhra tayi saman tace "Goofy angel ke nan,ji yanda kike pretending kamar baki san akan wa nake magana ba,to wanda ake expecting kiran shi kullum"

Hararan ta Sabeeha tayi snanan tace "kin ga bani son gulma da munafurci fa,ni babu kiran ko wa da nake expecting for your own information"dan dariya Zuhra tayi sannan tace "Allah ya shirya mun ke Goofy angel mu je ga adaidaita na tsare Allah ya kuma sa ya kira mu ko ma daina damuwa"

Dake ta tayi da duka "zan ci uban ki Zuhra ki fita a Harka ta bani son gulma da munafurci,ki koma hostel saura ki tsaya soyayya ki ki yin karatun Test din gobe Wlhy ba zan baki answer ko daya ba"

"Na ji kar Allah ya sa ki bayar din,a gaida Umma da Mr I love you,yarinya sai shegen zurfin cikin tsiya"ta kare tana juya wa zuciyar ta kal ko banza da alamun za suyi nasara soon banda ma Sabeehar akwai shegen taurin kan tsiya.

Ba tare da Sabeeha ta ce komai ba ta shige adaidai ta tare da sanar da shi inda zai kai ta,ko da ta isa saida ta biya dakin Umma tare da sanar da ita ta dawo ta gaida ta sanann ta shige wanka,bayan tayi salla ne ta shige dakin Umma tare suka ci abincin dare,suka sha hira har guraran 9:30 sannan ta fara hamma,Umma tace ta je tayi alola ta kwanta,mikewa tayi tare da yi wa Umma sallama sanann ta fito saida tayi alola sanann ta shige daki tare da rufe kofa,adduar bacci tayi sanann ta shige cikin bargo,kafin kace me bacci ya fara daukan ta.

Kamar a mafarki ta fara jiyo vibrating din wayan ta don tun randa Umma tace ta ji ta tana wayan dare ta daina barin wayan yana kara gudun kar ta kuma kamata in za ta kwanta sai ta sanya shi a vibrate.

Saida aka kira sau biyu a na ukun ne ta tashi tana musmussuka idanu sanann ta janyo wayar,ba tare da duba wake kira ba tayi picking tare da manna wa a kunne,cikin calm sweet voice din shi yace da ita "Assalamu Alaiki"

Ai firgit ta mike zaune tare da zaro idanu,da sauri ta cire wayar a kunne tare da kallon screen din ganin tabbas shi din ne ya kira ya sanya ta lumshe ido a hankali tare da maida wayar kunnan ta

"Hello kina ji na?"shine abunda ya ji ya fada cikin sanyin murya, "yeah ina jin ka wa alaika asslam,how are you doing?",cikin turo baki yace "yasin naki ba zan amsa ba,yanzu don Allah baki ji kunya ba?Kin kyauta ke nan?"ya tamabaya kamar yana ganin ta.

Dan baki ta turo sannan tace "ni kuma me nayi?"numfashi ya sauke sanann yace "Me ma kika yi kike tambaya ta,for god sake Babe for good 3 days ban kira ki ba and baki damu ki kira ki ji halin da nake ciki ba,you couldn't call to check up on me,was that fair?"ya kare kamar zai yi kuka.

Dan rintse idanu tayi sai yanzu take ganin rashin kyautawar ta da ta dau shawarar Zuhra ta kira ta ji ya yake tunda har kwana uku kam Gaskiya bata kyauta ba,haka kawai ta tsinci bakin ta da fadin "banda credit ne"

"Hmm Babe ban yarda ba ke dai kawai damuwa da so na ne baki yi na fahimta daman kina neman hanyar da za ki rabu da ni ki huta,in har credit ne baki da Ai ko flashing dina sai ki yi tunda kin san I will call back in na gani,Thank god ina da nisan kwana da yanzu kila ina grave dina"ya kare kamar me shirin kuka.

Dan shiru tayi sanann tace "ban yi tunanin hakan ba,but I'm sorry ba wai na tsane ka bane fa"da sauri yace "to kina so na?"dan dariya tayi sannan tace "kai dai Wlhy sai Allah,so how have you been?and you sounded some how today hope komai lafiya?"

Dan numfashi ya sauke sannan yace "I'm not fine Babe in fact ji nake kamar na mutu wlhy"da sauri tace "Subhhanalli don't say that,you are a Muslim remember duk abunda ya faru me kyau ko mara kyau jarabawa ne daga Ubangijin mu so ka daina fadin haka"

"Na sani Babe komai daga Allah ne but some people are just so wicked Wallah,kin san me ya faru?"Gyara zama tayi sanann tace "ban sani ba me ya faru?"

Saidai ya sauke ajiyar zuciya sanann yace " My Ex girlfriend just served me some hot breakfast is getting married in few days time"da sauri tace "Akan haka shine kake damuwa?Sai na ji kamar ka ce your Ex girlfriend Ai in kan wannan ne ban ga abun daga hankali ba tunda kun rabu da ita Ai dole tayi aure watarn kaima za ka yi"

"No Babe you are not getting this right,she is my girlfriend I mean I love that girl so fucking much,I love her with everything in me,ina mata son da bani yi wa kai na,we guys have been together for over 3 years tun tana secondary school,and ni dai God knows that I wanted to marry her,don har na fada a gidan su ma sai tace da ni ta fi son sai ta shiga University tukuna,saboda kar sai mun yi aure na hana ta karatu,na ce to ni na nema mata ma admission ta fara University,tunda ta fara sai ta canza gaba daya ta fara bani attitude,kullum saidai nayi ta kuka kin san ni mutum ne me sanyi sam ban iya fada ba,da Mommah ta ga na shiga damuwa da yawa sai ta je gidan su,shine fa yarinya da Maman ta suka ce wai su ba za su aurar da ita yanzu ba tayi karama sai ta gama Degree tayi Masters sai ayi auran,in za mu iya hakuri har lokacin to in ba za mu iya ba Allah hada kowa da rabon shi.

That day rai na ya baci sosai,Mommah tace na rabu da ita,amman ina jin ba zan iya ba coz deep down duk da abunda ta mun ina son ta like mad,and ina jin a jiki na ita ma tana so na maybe tana rawar ido ne ko wani abun ban sani ba,nan na ce da Mommah ba damu I can wait Ai kamar gobe ne a gurin Allah,haka na cigaba da bin yarinyar nan sai ta ga dama take  daukan waya na in nayi magana tace School stuffs sai kace akan ta aka fara school,kawai me zan gani,friend dina ya zo yake nuna mun Wedding invitation card din ta wai aure za ta yi next week ma za a fara program din Auran nata"ya kare murya a raunane

Ajiyar zuciya Sabeeha ta sauke sannan tace "Ya salam Gaskiya bata kyauta ba,yanzun ta gama Masters din nata ne?"

"Hmm wani Masters maganar da nake miki yanzu haka fa tana 300 level ne"Ai Sabeeha bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba har wayar tana kusan faduwa, "dariya kike mun?You think is funny right sai ya sanya kuka.

Da sauri ta rufe baki "Inalilhi are you really crying?Yi shiru don Allah,I'm sorry don mind me ba wa kai nake dariya ba Wlhy yarinyar ce ta ban dariya all this while she has been playing with your feelings amman daman can ba wani karatu kaine ta daina so ko nace ta samu wanda ya fika,shine ta fito ta fada ma Gaskiya ta kasa suka ma karya,Gaskiya this is very bad dole ran ka ya baci amman kayi hakuri ka daina kukan nan ka ji"

Cikin can hanci yace "why me ya sanya za ta mun haka,I tried all my best na ga na zamo best caring Boyfriend to her ina son ta sosai amman tayi deciding cin amana ta,daman haka mata suke?"

"stay calm pls ba duk mata haka suke ba,wasu matan dai haka suke,amman maganar Gaskiya abunda tayi be yi dadi ba kuma bata kyauta ba,tayi playing din ka,ni fa dalilin haka ya sanya a rayuwa sam ban taba soyayay ba kuma bana jin zan yi coz ina da tsoron heart break kana zaman zaman ka a sanya ka cikin damuwa,kayi hakuri haka Allah ya so ita kuma za ta gani in baka yafe ba sai Allah ya rama maka tunda har ta saka kuka"ta kare cikin muryan lallashi.............

  A cigaba da hakuri da ni don Allah Wlhy abubuwan
ne sai a Hankali kana naka ne Allah na nashi.

Ayi hakuri da typing errors ban yi editing ba.

Kar a manta da comment da sharing saboda Allah

Ina wa kowa fatan Alkhairi.

Continue Reading

You'll Also Like

12.1K 1.2K 31
«ឯងជាអូមេហ្កា ដូច្នេះឯងត្រូវធ្វើជាទាសកររបស់យើងពេញមួយជីវិត» មីន យ៉ុនហ្គី «បាទ!» «ពីពេលនេះទៅឯងត្រូវហៅយើងថា "លោកម្ចាស់" ព្រោះយើងជាអ្នកសង្គ្រោះជីវិតដ៏ថោក...
6.3K 1K 70
ရန်သူတစ်ယောက် အမှုဆင်ချောက်ချခဲ့လို့ မျက်နှာပုံပြောင်းပြီး အငှားယာဉ်ဒရိုင်ဘာဖြစ်လာရသူ ချန်ရှီ။ သို့မဟုတ် တစ်ချိန်က ပါရမီရှင်စုံထောက်ကျော် စုန့်လန်။...
248K 48K 128
Title - Dangerous Personality Author - Mu Gua Huang MC- Xie Lin x Chi Qing Chapter 161 + 2 extras ထူးဆန်းသည့် ပြန်ပေးဆွဲမှုတစ်ခုအပြီးတွင် ချီချင်းတစ်...
16.3K 439 21
ဒီကောင်မလေးကို ပြန်ပေးဆွဲထားတာဘာအတွက်လဲ ချစ်လို့လား ကြိုက်လို့လား လိင်ကိစ္စကြောင့်လား မဖြစ်နိုင်ဘူးလေ မင်းက Asexualတစ်ယောက်လေ.... possessive type, Re...