A SIMPLE DARE (WASA DA SO)

By marteybee

431 7 16

More

new book
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page ten
Page 11
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20/21
Page22/23
Page 24/25

Page 12

17 0 0
By marteybee

✨✨
        A
SIMPLE

DARE

                              ✨✨

(WASA DA SO)

WRITTEN AND STORY
         BY
NERNAH MARYAM
   (MEEMARH)

 
             Kofa a bude take ga duk me son yin joining group dina😌,Amman Hajiya don Allah in kin san ba yin comment ko karanta littafi na zai kawo ki ba I beg you in the name of Allah kiyi zaman ki ba sai kin shigo ba!!haka zalika wanann group din na mata ne zalla don Allah Maza should stay away from my group👏

       My What's app group link👇🏻

           https://chat.whatsapp.com/EUrVVaKJnIBDTlQsxurZv0

Bismillahi Rahmanin Raheem............

(    In the name of Allah the most beneficient,the most merciful)

 
  Kofa a bude ta ke ga duk wani me good quality product da ya ke son Advertising ɗin shi,as Kaya masu kyau,da inganci (TALLAH) should contact me via :
                              08100046388

Page 1️⃣2️⃣

TALLA!!TALLA!!TALLA!!!

       https://chat.whatsapp.com/ImtxMSS1tuSKqvBpPqc03P

Assalamu'alaikum sisters🤗
KAMSHI* mace Mai kima, mace Mai daraja, mace Mai izza, mace Mai aji itace tasan darajan kamshi, if your perfume is not unique hajiyata you're just using ordinary air freshener🤣, hajiyata ko nawa Zaki kashe indai a turare ne baki Fadi ba😘 matan da suka gane suka San yanda zasu kankaro da martabar su, suke amfani da turare, a *BAKHOOR BY FAIXY* Zaki Sami Main chic, Bachelor, Husband snatcher, Her royal sexiness, Mysterious girl, Pleasure, Boovilous, White khumra, Maroon khumra, Black khumra, Hair perfume, Turaren wanka, Turaren  wuta, Turaren tsuguno, Turaren mopping,Turaren carpet Shu'umat khumra,and more, yar uwa kar kibari abaki lbr, (wholesale and retail) WhatsApp 09067621681, siyan na gari Maida kudi gida🥳

Instagram @Bakhoor_by_faixy

******************************

  Kwankwasa kofar da ta ji ana yi ne ya farkar da ita a furgice,mikewa tayi bayan tayi adduan tashi daga bacci,sanann ta gyara zaman dankwalin kanta da ya soma zame wa saboda bacci,sam ta rasa garin ya tayi irin wanann baccin,sam jiya bata ma san bacci ya dauke ta ba tsaban farin ciki da dadin da ya ziyarce ta,Allah Allah take gari ya waye ta samu ta labarta wa Umma yanda suka yi da wanann Mr I love you din,don sai take jin abun kamar mafarki,ta kasa yarda wai yau after a long time ta samu big Order haka,a hakan ma wai rokon ta yake ta yi sanann double payment zai biya,additional 50k a free,bata san sanda ta saki murmushi ba tare da mike wa don so take daman kan ta ya tsaya guri guda,kasancewar daga tashi bacci ka mike lokaci guda tsaye kan yi causing ciwon kai,yana da kyau ka dan zauna for some mints kafin ka tashi,sama ta kalla a hankali sanann ta furta "Thank you Lord!!I love you so much Allah na Alhamdulilah"hakan yayi daidai da kwala kiran sunan ta da Umma tayi

Da sauri ta amsa "Umma naam,na tashi fa", "in kin tashi tsayuwar me kike har yanzu?Fito maza an fara shiga sallah,yau na rasa wani irin bacci ne ma kike yi,ko da yake ba laifin ki bane Ai jiya da kin kwanta da wuri,da kin tashi da wuri,kar ki bari na jiyo in samu kin koma bacci baki fito ba"ta kare tana dan daga muryan ta yanda Sabeehar za ta ji sanann ta wuce dakin ta,don gabatar da nata sallahn.

Cikin nutsuwa ta fito saida ta biya bandaki tayi tsarki sanann ta nemi dan kan dakalin tare da zama,sanann tayi alola,daki ta shiga tare da shimfida abun sallah,inda saida ta gabatar da Raka'atanil fajir kafin ta yi sallan asuba,bayan ta gama Azkars din bayan sallah ne tayi Azkars din safiya da maraice sanann ta janyo Qur'ani din ta,cikin muryan ta me sanyi da dadin sauraro ta shiga karanta suratul Ya~sin,inda ta kai karshe tare da rufewa daga Izu biyar zuwa Fatiha,nan tayi adduoin ta sanann ta mike lokacin gari ya fara haske,abun sallan ta nade ta aje sanann ta fito zuwa dakin Umma.

A zauna ta tarar da Umma da alamu ta gama nata karatun ne tana adduoi kamar kullum so zama tayi kusa da ita tare da bude hannuwan ta ita ma saida Umma ta gama sanann suka shafa a tare,juyowa Umma tayi tare da kallon ta inda take ta sake wa Umman murmushi sanann ta mika mata hannu,suka yi musabaha kamar yanda suka saba kafin tace

"Hajiya Umma an tashi lafiya?Ina kwana ya jiki jiki kuma"dan kwade kan ta Umma tayi sanann tace "duk lokaci guda kuma wa ni kadai,lafiya klau Alhamdulilah Sabeehatun Umma ya kika tashi?Da fatan dai yunwa bata hana ki bacci ba jiya?"

Saida ta dan zame tare da kwantawa jikin Umman sanann tace "lafiya kalau na kwana na tashi Umma ta,da adduoin ki jiki na babu abinda zai same ni sai abun da Allah ya so"

Kan ta Umma ta shafa sanann tace "Masha Allah Auta na ubangiji ya cigaba da iya mana,tare da rufa mana asiri duniya da lahira,Allah ubangiji yayi miki albarka sannan ya kare ki daga dukkan sharri,yanda kike kula tare da tattali na ubangiji ko bayan raina ya kula mun da ke da zuriar ki baki guda,Allah kuma ya baki miji na gari in wanke ki in kai ki dakin ki"ta kare tana murmushi.

"Ameen thuma Ameen Umma ta,in sha Allah ba za ki mutu yanzu ba sai nayi kudi na zamo babban mutum a kasar nan,sai na kai ki Makka da Madina,Umma in sha Allah sai na siya miki gida da Motoci,sanann na dinka miki Super da laces masu mugun tsada,harda gold duk zan siya miki in nayi kudi,Allah ya kara miki lafiya da tsahon kwana in jiya da ke dadi kamar yanda kike wahala gurin ganin kin inganta rayuwa ta Umma ta🥺"ta kare tana jin hawaye na kokarin zubo mata ba karamin tausayi da kaunar Mahaifiyar ta ba,bata da burin da ya wuce a rayuwa ta zamo wata don kawai ta jiyar da Mahaifiyar ta dadi,tana son ganin ta jiyar da Mahaifiyar ta dadi da mata da yawa suke sha,tana son ta sanya tufafi masu tsada kamar yanda manyan mata ke sanya wa,tana son ta ga ta je Makka ta kaita kasashen waje,bata da fata da buri da ya wuce Allah ya amsa mata tayi arziki ko don ta jiyar da Mahaifiyar ta dadi.

"Ameen Ameen Uwata ubangiji ya amsa Allah ya amsa ya baki budi me Albaraka ya tsare ki da cin haramun,Allah ya sa duk abinda kika taba ya zamo akwai budi a ciki da Albarka,ya kuma kara tsare mun ke mutuncin ki da kuma imanin ki"

"Ameen thuma Ameen Umma ta, ta kare tana lafewa a jikin ta, "daga ni ni kam mutum kamar kuliya sai shegen son jikin tsiya,tashi ki je kiyi wanka,sai a zo a nemi abun da za a karya da shi kuma"

Baki ta dan turo "kai Umma ki dan bari na dan ji dumin ki mana"ture ta Umma tayi "Ke matsa mun dumin me wanda tun kina ciki kike sha,maza tashi ki juye ruwan zafin cikin flask kiyi wanka,bari na shiga na karbo miki dan wake shi kam ai kina so ko?"Umma ta kare tana mike wa,itama tashi Sabeehan tayi har ta kai kofa kuma sai ta dawo

"Yauwa Umma na mance akwai abunda nake son fada miki" a bakin gado Umma ta zauna sannnan tace "ba dai wani abu aka ce ku siya ba ko ku kawo a makarantar na ku"ta kare a raunane,a kasa gurin kafafuwan ta ta zauna sannan ta daura kan ta akan cinyar ta kafin tace

"Umma jiya da dare wani ya kira ni", da sauri Umman tace "wanann wani me saa ne da ya sace zuciyar ki har kike bani labarin shi"ta kare tana dariya don yau ne rana ta farko da Sabeeha tace da ita wani na miji ya kira ta.

"Kai Umma daga na ce miki an kira ni shike nan kuma sai ya zamo soyayya,Umma ke da Zuhra kullum dai maganar ku daya yasin"kan ta Umma ta kwade "gidan ku to don Allah in ba Auran nan kuka yi ba za mu kwada ku mu cinye ne,Wlhy Sabeeha kika cika mun ciki sadakar ki zan bada"dariya duk suka sanya kafin tace "Haba Umman Sabeehatu ke ma Allan na san wasa kike sadaka sai kace wata dankalin Hausa"

"Za ki ga wasa ni tashi maza ki fada mun yanda kuka yi da yaron Allah sa ba yar hali kike yi masa ba don na san hali", "Umma!!Umma to kwantar da hankalin ki ba ma saurayi ko soyayya bane,yau dai da alamun kaji za mu ci da lemun kwalba a gidan nan"ta kare tana tafa hannu kamar wata yar yarinya.

"Ke ni da bani don shashanci da yarinta irin naki,wani irin kaji da lemuka ko a ina za ki gan su oho"ta kare tana girgiza kai don bata ga lefin Sabeehar ba it's been long da suka ci kaza dole tayi shaawar sa,ya zamo dole ta mike tsaye da neman kudi ko don ta samu ta jiyar da yarinyar ta dadi,don sarai ta san halin yaran yanzu Alhamdulilah Allah ya kare mata Sabeehar ta bata da DOGON BURI (By Mom Sayyid)balle kwadayi amman duk da haka zuciya bata da kashi,rayuwar mace abun a tausaya mata ne domin abu kadan ke jan raayin su,tare da sanya su salwantar da rayuwar su tare da barin mutuncin su cikin sauki,dole yau ta san yanda za tayi ta samu wa Sabeeha kaza ko da rabi ne ta ci,tunda har ta furta tana da bukatar shi.

"Umma baki fahimta ba fa,nan ta kora wa Umma bayanin yanda suka yi da FIK a daran jiya akan yana bukatar a yi masa Snacks pieces 50 50,inda ta kare da fada mata kan yace zai yi doubling payment din in har suka yi kokari gobe suka da yamma aka gama zai basu 100k"

Idanu Umma ta bude "Auta kina ganin kuma da gaske yake??And kin san sa ne?", "uhmm actually Umma nima Wlhy ban san shi ba saidai ya ce mun wai gurun wani ya karbi number na,inda na bar shi a kila gurin wani wanda ya taba siya ne,and yanda muka yi da shi Umma babu alamun wasa ko yaudara don tun jiyan ma ya nemi in tura account details dina ya sa kudin nace aa sai nayi shawara da ke tukun na,shin kina ganin in ce masa za muyi ko aa,tunda kin ga ba mu taba yin bulk order ba shine ma ya sanya ban ce da shi komai ba nace sai zuwa yau"ta kare tana adduar Allah ya sa Umma ta yarda don wanann one time opportunity ne da ba za ta so su rasa shi ba.

"Auta!!!sai kuma ta dan yi shiru,kafin ta nisa tace Auta na dade ban ji abunda yayi mun dadi na kuma samu kwnaciyar hankali ba irin wanann,saidai bana tunanin za mu iya yin Snacks har kusan 200 a tsakanin yau da gobe"da sauri ta katse ta da fadin

"Haba Umma ga ki ga ni ga Zuhra me zai hana,sanann Shatu ma na san za ta iya taya mu,Umma ta haka ne fa za muyi promoting business din mu,in har muka rasa wannan offer din to Umma ban san yaushe za mu kara samu ba,ina so na bude shago na na kaina tare da daukan mutanan da za su na taya mu aiki,amman for now kam dole Umma muyi hakuri muyi tunda har na amsa mishi kan za muyi kar ya zamo nayi magana biyu,and nace aa ran shi zai yi ba dadi don baki ga yanda yayi ta roko na ba,don Allah Umma ta ki yarda kin ji ina zuwa school zan fada wa Zuhra ta zo mu fara ragewa Birthday cake din kam ni zan yi shi da kai"ta kare tana kama hannun Umman nata.

Dan murmushi Umman tayi sanann tace "na yarda Uwata Allah ya kara wa neman ki albarka shi kuma Allah ya fidda mu kunyar shi sanann ya kara wa dukiyar shi albarka,daman ni gudun kar ba mu cika alkwari nake gudu amman in kina ga zamu iya ni wa ya isa ce wa Sabeehatu No ki tura masa account number din sai in kun tashi ku biya kasuwa ku siyo abubuwan bukata,don bana jin akwai sauran abubuwa a gida don mu kwana biyu ba a yi ba"tsalle tayi tare da rungume Umman nata sanann ta manna mata kiss a kumatu "I love you so much Hajiya me gadon zinari ta Allah ya kara lafiya da nisan kwana me amfani"dan murmushi Umma tayi sanann tace

"Sakar ni ni kan kar ki yarda ni maza ki je kiyi wanka,ki gode ma yau babu kwanukan wanke wanke iya kofunan shayi ne na kuma wanke su,kafin ki fito dan waken ki ya zama ready,saura kuma ki zauna a bandaki kamar me shirin canja fata"

Saida ta kai kofar daki sanann tace "Ai yanzu sharp sharp zan yi na fito Umma na"daga haka ta fada dakin ta inda Umma ita ma saida ta fadi tayi wa Allah Sujuddus shukur don gaba daya tunanin ta ya tsaya bata ma san a ina za ta samu kudi ba,a halin yanzu yan bashin da take bi da be kai ya kawo ba ko ta je karba raine kawai zai baci,domin kowa fama yake yi ga Hajiya ta sako ta gaba maganar kudin ruwa da wuta,duk da su wutan ma ba samun shi suke ba,ko sun samu ma ba damuwa da shi suka yi ba tunda basu da kayan kallo balle wani electronics na tashin hankali wanda za a ce za su ja wuta,ya ka dai fridge ne shima saboda sanaar da Sabeeha take yi ne,guri ta nema ta zauna tana me jin farin ciki from nowhere ita kadai sai tayi murmushi ta ce "Alhamdulilah,Allah ma ji rokon bayin sa"farin ciki kamar an ce da ita yau ne Auran Sabeeha ko ba komai za su dan huta na kwana biyu.

Daki ta fada cikin sauri inda tana shiga kuwa wayan ta na gama ringing har za tayi ignoring sai kuma tayi saurin fadawa kan yar katifar ta tare da janyo wayar inda yana matsa home button kuwa ta ga missed calls kaca kaca,goshi ta dan dafe don duk da bata yi saving number din ba ta gane Mr I love you ne,kafin ta kai ga maida call din wani ya kuma shigowa inda ta dauka kuwa da sauri tare da sanyi shi a speaker don tana son cire kayan jikin ta.

Cikin calm cool voice din shi yace "Assalamu Alaiki"inda ta daura wayan kan kirjin ta tare da fadin "Wa alaika asslam"saida ya sauke ajiyar zuciya wanda har tana iya jiyo shi kafin yace "wani abun na kara pls kika ki picking calls dina??I was so damn worried wlhh Saura kiris zuciya ta ta buga fa"

Dariya ta da kwashe da shi sannan tace "kai kam anya wanann zuciyar bata buga ba kuwa magana kadan heart din ka ta kusa bugawa"inda ya katse ta da fadin

"Ba ke ne ba🥹kuma yasin mommy na na so na sosai in na mutu ba za ta bar ki ba ke ma saidai ki biyo ni"ya kare yana turo baki gaba,baki ta tabe sannan tace "ohhhhoo wato Mommyn ka na son ka?"ta kare tana rolling big sexy eyes din ta

"Eh mana🥹sona take sosai sosai don haka kina lallaba ni kin ji"she can't help it but to laugh her ass out,saida ta dara sosai sannan tace "to kai kuma wa yace ma ba a son shi a gidan su?Umma na na kauna ya nima sosai and duk wanda ya taba mata ni sai inda karfi na ya kare"ta kare tana murguda baki.

"Yasin ni dai ki daina murguda mun baki I'm just a little baby fa🥹🥹child abuse kike yi yasin human right ya ci ace su kama ki"kai ta girgiza sannan tace "akwai aiki to kai a ina ka ga na murguda ma baki?"

"Yo Ai ni kam ina da idanu a ko ina" , "ohhh really?"ta tambaya kamar yana ganin ta,inda ya masa da "yeah Baby by the way tell me the good news Umma na ta amince ko?"

" ba Umman ka bace Umma ta ce and Congratulations tace bata amince ba so deal off"ta kare tana daura zanin wanka, dan karancin ihu ya sanya sanann yace "Yasin karya kike yi indai Umma ce na san ta amince just send your account details pls kar zuciya ta ta buga"

"Kai dai da maganar zuciyar nan sai Allah,funny you you are lucky Wlhy Umma ta amince so in sha Allah da yamma gobe kayan ka will be ready"dan ihun murna ya sanya sanann yace "that's my baby I love you and Allah ya kaimu"

Idanu ta zaro sanann tace "can't you stop all this unnecessary I love you din nan"baki ya dan turo sanann yace "to ina ruwan mutum da ni ba suna na bane in na ga dama in fada ko so nawa ne Ai ba sunan wata bane"ya kare yana murguda baki.

Kai ta girgiza sanann tace "to na ji kayi ta kira amman ba wani ba tunda na Riga da na san sunan ka Ai ko?",dan smile yayi sannan yace "in kin sani fada mu ji"

Hararar wayan ta dan yi sannan tace "Allah ya shirya ka,I will hang off now,na gode da contacting din mu da kayi", "yeah unfortunately dole in hakura ki kashe wayar ba don Raina ya so ba,can't lie kina da best sweetest and calm voice da ban taba jin irin shi ba a rayuwa ta,don't mind hearing this voice for my entire life,but na san kina da classes yau and it's gonna be a busy day for you guys,so pls make sure to take care of yourself okay,and in kika kula wani ban yafe ba"ya kare da muryan shagwaba,ba ta kai ga bashi amsa ba yayi saurin kashe wayar sakamakon bude kofar dakin shi da aka yi.

Hajiya Samha ce ta shigo cikin dakin sanye cikin wata ash Abaya irin yar Saurin nan,inda ba karamin kyau da amsan ta yayi ba,fuskan ta dauke da murmushi ya nufi kan gadon tare da zama inda tana zama yayi rolling tare da fada wa jikin ta.

"Mommah good morning"ya kare yana manna mata kiss a hannu,kiss ta manna masa a goshi sanann tace "Charm charm dina ka tashi lafiya,hope kayi bacci me dadi jiya?"Saida ya dan mata murmushi sanann yace "yesss Mommah lafiya ta klau,hope ke ma kina lafiya?"

"I'm good my love and Alhamdulilah tunda lafiyan ka lau,tashi mu je Daddyn ku na down stairs yana son magana da kai"agogon dakin ya kalla da mamaki sannan yace

"Mom Daddy kuma yana son magana da ni da sanyin safiyar nan,I hope I'm safe dai ko?"ya tamabayan yana tsare Mom din da idonu don ganin reaction din fuskan ta,murmushi ya sake mishi tare da mikar da shi zaune sanann tace

"Shike nan your Daddy can't talk to u in peace sai in kayi wani abu,I think kawai magana ce tsakanin yaro da Baban shi don ni kaina ma be fada mun maganar ba,but na san ba laifi kayi ba,ko laifin ma kayi dole a maka afuwa Charm charm dina baya laifi a idanu na"ta kare tana Jan kumatun shi kadan tare da mike wa ta mika mishi hannun ta inda ya kama suka fito hannun su sakale da na juna har suka iso parlorn inda Alhaji Ismail' ke zaune da news paper a hannun shi yana sanye da black trouser da shirt me hula a jiki saidai be sanya hulan ba ya daura kafa daya kan daya,yana  gurban coffee a hankali,don aladar shi ne in yana gida baya komawa bacci bayan asuba ana idar wa zai je ya dan motsa jiki a Gym din gidan sanann ya shigo ya sha coffee sanann ya karanta news paper kafin yayi wanka ya fita kuma wanann shine aladar da yake kullum don ba kullum ya cika cin break fast ba,don ma Hajiya Samha na magana amamn daga shi har yaran shi ba damuwa suka yi da cin abinci ba.

Har suka zaune be dago ba balle yace da su kala,ganin haka ne ya sanya FIK budan baki yace "Morning sir"

Sai a sannan ya dan cire farin glass din idanun shi tare da zuba wa FIK idanu kafin ya amsa a hankali "Morning how was your night"

"All good Dad"dan shiru ya dan yi don Daddyn na shi sam ba yanda Mom take masa yake masa ba No nonsense man ne,yana kuma da zuciya da fushi don zan iya cewa gado FIK yayi,ya sanya at times ko yayi abu yana kokarin ganin ya kau da kan shi don gudun maganar Hajiya Samha,ya rasa gane me yasa ta zabi FIK duk cikin yaran su tayi  watsi da tarbiyan shi,ya rasa me ya sa sam komai yayi daidai ne a idanun ta sam bata ganin laifin shi ko da kuwa me zai yi,a so da dama yana kokarin nuna mata wanann abun da take masa ba gata bane in ba mutuwa akwai girma wataran shima zai yi aure da wannan mugun dabiar tashi wace mace ne za ta zauna da shi?Amman sai ta nuna ran ta ya fi na kowa baci ta kan ce a bar shi in be yi yanzu ba sai yaushe ne zai yi,kuruciya ce da ya girma ko ba ce bari ba zai bari komai ai yar lokaci ne,tun yana yaro maganar ke nan gashi har Allah yayi ya mallaki hankalin kan shi,abun nayi masa ciwo ganin inda ya taso sakaka ba kamar sauran yan uwan shi ba,in ba rashin hankali da mutunci irin na FIK ba ace uban ka na cikin gida da Mahaifiyar ka amamn ka je ka musu gaisuwar safe shine aiki,saida ya aika aka kira wo masa shi,kai ya girgiza tare da furta "Allah ya kyauta"a hankali.

Jin shiru shiru ne ya sanya shi mike wa don be ga amfanin zama ba tare da Daddyn ya fada masa dalilin kiran na sa ba,ganin haka ya sanya Hajiya Samha saurin riko hannun shi tare da maido shi zaune a zafafe Daddyn yace

"Sakar masa hannu yayi tafiyar shi tunda shi ba yaron kirki bane,in aika a kira ka sanann ka zo ka tashi za ka tafi na ce da kai na sallame ka ne?"ya kare ran shi bace

"Aa Alhaji banda abun ka Ai Charm charm be da lafiya sabida Allah ka sanya an yi kiran yaro yana baccin safe ya tashi ya zo ka kuma aje shi ba tare da ka ce da shi komai ba,kar ka manta fa yana da zuwa school yau in be tashi ya tafi ya shirya ba yayi late kuma ya zamo wani abun maganar haba don Allah"ta kare tana girgiza kafar ta

Kallon ta ya dan yi sanann yace "wani makarantar??Tunani kike yaron nan wai karatun ne a gaban shi?Yaron da ban san adadin sau nawa ana fada mun baya attending classes ba,shine kike maganar wai a bar shi yayi shiri kar yayi late?"ya kare a kufule.

"Lalle Alh wlhh ka bani mamaki wai har yaushe har yaushe za ka na daukan jita jitan mutane akan yaron ka,dan nan dai fa yaron ka ne na cikin ka ba dan riko ba tsakani da Allah duk abunda aka zo aka fada maka sai ka hau ka zauna a kai,yaron da kullum bayi zaune bayi tsaye yana hanyar makaranta shine don munafurci da hana zaman lafiya wani munafukin zai dube ka yace da kai wai bayi zuwa makaranta,to gidan uban wa yake zuwa??Wlhy ashe Gaskiya ne da aka ce Munafukai suna kasan wutan Fir'auna"ta kare tana Jan tsaki ita ala dole ran ta ya baci.

Shiru Alh Ismai'l yayi yana mamakin hali irin na Samha,wato shi me hali be taba fasa daina halin shi,kai ya girgiza domin in yace zai biye ta to rayukan su ne duka zai baci hakan ne ya sanya shi kallon FIK kafin yace

"Kai Muhammadu me kake da kudade kwana biyun nan an ce da ni kana yawan cire kudade ba kuma
kananu ba?"shiru yayi don be ma san abun fada ba,ila susa kan shi da ya fara yi,ganin haka ne ya sanya Daddy rai a bace yace "you better speak up kafin raina ya baci"

"Haba haba Alh haba don Allah yanzu tsakani da Allah sai ka ce baka san condition din yaron nan ba ba isashen lafiya gare shi ba,sabida Allah miye abun tsawar to?Na ga yaron nan ba fa kurma bane yana ji kuma yana magana kayi masa magana a tattausan murya mana saboda Allah,da kake magana akan cire kudaden da yake yi yayi yawa miye amfanin rai daman?Aka ce amfanin rai ga me shi Ai ko,sanann da kai da kaya na ga Ai duk malakar wuya ce miye a ciki don yaro ya ci a cikin arzikin da Allah ya hore wa Mahaifin shi,ko baka san dukiyar nan da ka tara harda arzikin shi a ciki ba,sanann Alh ko nawa Charm charm zai cire ba zai taba yi wa dukiyar ka gibi ba tunda na ga ubangiji ya hore mana Alhamdulilah ba mi ba wanin mu ma be kama ta ace yayi talauci ba,so ni dai ban ga wani abun bacin rai ko bakin ciki don 'Da ya ci abun Mahaifin shi ba"

Ai da jin haka sai bakin shi ya mutu murus ya ma kasa cewa komai in banda idanu da ya kafe Samha da su ga halin ta da ya tsana tayi magana ta hade rai kamar ba ita tayi ba,ganin be da niyar sake cewa komai ne ya sanya FIK mikewa

"Dad I'm running late I want to go"ba tare da ya kalle shi ba ya daga mishi yatsa a matsayin ya je kawai,don ya cigaba da tsayuwa ma ran shi ne zai kuma baci,saida ya ga shigan shi part din shi sanann ya juyo tare da rufe Hajiya Samha da masifa kamar ya buge ta,ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba don ran shi ya baci babu karya,ganin haka ne ya sanya ta saka masa kuka,wai don ya ga bata da iyaye babu inda za ta ya sanya yake mata duk abunda ya so,miye laifin ta don ta kiyaye lafiyan yaron ta tunda in ciwon na shi ya tashi duk wahala ai za su sha,ala dole ya aje fadan tare da shiga lallashin ta yana bata baki,kafin a hankali ya shiga mata nasiha akan ta gyara irin yanda take wa FIK sanann ya na da kyau ya koyi tattali duk da Allah ya hore musu din amamn kashe kudade anyhow babu amfani,don dai a samu zaman lafiya tace da shi ba damuwa za a kiyaye,sanann yace da ita ta je ta hada mishi ruwan da zai yi wanka da shi.

      Sabeeha kuwa tunda ta kashe wayar ta masa Text din account details din ta sannan ta shiga wanka,ba ta daden ba kuwa ta fito inda ta tarar Umma ta aje mata cooler din Dan wake,plate fork da roban yaji a gefe,saida ta goge ruwan jikin ta tare da shafa mai sannan ta zauna ta shiga cin dan waken hannu baka hannu kwarya domin jiya ba karya da yunwa ta kwana kawai ta yi kokarin boye wa ne don ta samu ta kwantar wa da Umman ta da hankali,saida ta ci tayi nak ta sha ruwa sannan ta tashi ta shirya kan ta cikin  wata peach Material dinkin dogon Riga da ratsin sky blue a jiki,ba karamin zama mata kayan yayi ba kuwa inda ta kama gashin kan ta a tsakiya tare da daura dan kwali a kai,sanann ta shafa man baki da kwalli,hijab din ta da ya sha goga irin yadi me laushin nan kalan sky blue ta saka inda ya sauka mata har gwiwa sanann ta hado kan kayan karatun ta,wayar ta jefa a jaka inda saida ta duba ta ga kudin be shigo ba tukun na,don dauka tayi ya tura tun sanda ta tura masa account details din ta.

Cikin takun nutsuwa ta fito bayan tayi wa Umma sallama inda ta raka ta da adduoi tare da sanya mata albarka,dake yau garin a dan cike yake ya sanya bata yi wahalar samun abun hawa ba,inda take ji kamar ta karba ta tuka da kan ta don Allah Allah take suyi ido biyu da Zuhra ta bata labari.

Duk daukin ta kuwa suna haduwa aka fara lectures saida ta hakura aka gama guraran 1 sun ida Azahar Zuhra ta gama karanta mata cards din yau da Abayas inda ta nace saida Sabeeha ta bata guda sanann suka tafi Hostel,sai lokacin ma ta tuno da wayar ta hakan ne ya sanya ta bude jaka tare da fito da wayan inda ta ga text message ko in ce Credit Alert, na 100k Ai bata san sanda ta bude idanu ba,da sauri Zuhra tace

"Goofy angel kalan ki kuwa?wani abun ne"tsaban ta kasa magana ma mika wa Zuhra wayan tayi inda ita ma baki ta bude tare da dumbin mamaki tace "Kaiii Sabeeha Waye haka?kamar dubu dari fa nake gani??ko dai mistake ne?"ta kare tana kuma kallon alert din,kai Sabeeha ta girgiza mata sannan tace "dubu dari ne Zuhra Wlhy tun da nake ban taba ganin 100k alert ba ko na gan su da ido na,Zuhra ba mistake bane kudi aka turo mana"

"Kudi??ko kun shiga wata talafi ne ba mu da labari wanda ake raba kudi haka?"dan murmushi tayi sanann tace "Zuhra ban isa shiga tallafi baki sani ba,ke ma kin sani duk abunda na samu naki ne ba kudin tallafi bane wani ne ya turo yana son ayi masa snacks"ta kare tana murmushi

"Snacks?Sabeeha shine har na dubu dari?Ba fa dubu goma ko naira dari ba fa dubu dubu har sau dari,haba Sabeeha", ta kare cikin jin tsoro, "Ke dallah matsa kuliya kawai ina wanda ya kira jiya muna class to shine fa"da sauri Zuhra tace "kina son ki ce mun FIK??"ta kare tana zaro idanu saida ta fada kuma tayi saurin rufe bakin ta da tafukan hannun ta deep down tana fadin "Oh shit wanann baki nawa wataran sai ya kai ni Prison"..........

A cigaba da Comment da sharing saboda Allah ina Godiya da dumbin adduoin ku da fatan Alkhairi tare da kaunar da kuke nuna mun,Ubangiji ya so ku tare da kaunatar ku irin haka.

Ayi hakuri da typing errors ban Riga nayi Editing ba.

In sha Allah sai zuwa Thursday ko Friday ina yi wa kowa fatan Alkhairi.

Continue Reading

You'll Also Like

609K 7.9K 32
Lost, Lose (Loose Trilogy #1) She's a girl of hope, Lisianthus Yvonne Vezina. A teen-year-old girl who focused on her goal... to strive. But everyth...
7K 337 10
All that terrified 23-year-old Ayra were pink notes. Whenever she found one, she ran like hell. This time, her frantic escape led her to the bustling...
Burn Marks By Icecold101

Mystery / Thriller

4K 207 6
My TikTok - E.writer🖤 (whteverwhnever) I've just started the Hierarchy Kdrama And I love it !! ( I will definitely be editing this story a lot se...