A SIMPLE DARE (WASA DA SO)

By marteybee

431 7 16

More

new book
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page ten
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20/21
Page22/23
Page 24/25

Page 9

12 0 0
By marteybee

✨✨
        A
SIMPLE

DARE

                              ✨✨

(WASA DA SO)

WRITTEN AND STORY
           BY
NERNAH MARYAM
     (MEEMARH)

 
             Kofa a bude take ga duk me son yin joining group dina😌,Amman Hajiya don Allah in kin san ba yin comment ko karanta littafi na zai kawo ki ba I beg you in the name of Allah kiyi zaman ki ba sai kin shigo ba!!haka zalika wanann group din na mata ne zalla don Allah Maza should stay away from my group👏

       My What's app group link👇🏻

           https://chat.whatsapp.com/EUrVVaKJnIBDTlQsxurZv0

Bismillahi Rahmanin Raheem............

(    In the name of Allah the most beneficient,the most merciful)

 
  Kofa a bude ta ke ga duk wani me good quality product da ya ke son Advertising ɗin shi,as Kaya masu kyau,da inganci (TALLAH) should contact me via :
                              08100046388

  Page 9️⃣

TALLA!!TALLA!!TALLA!!!

       https://chat.whatsapp.com/ImtxMSS1tuSKqvBpPqc03P

Assalamu'alaikum sisters🤗
KAMSHI* mace Mai kima, mace Mai daraja, mace Mai izza, mace Mai aji itace tasan darajan kamshi, if your perfume is not unique hajiyata you're just using ordinary air freshener🤣, hajiyata ko nawa Zaki kashe indai a turare ne baki Fadi ba😘 matan da suka gane suka San yanda zasu kankaro da martabar su, suke amfani da turare, a *BAKHOOR BY FAIXY* Zaki Sami Main chic, Bachelor, Husband snatcher, Her royal sexiness, Mysterious girl, Pleasure, Boovilous, White khumra, Maroon khumra, Black khumra, Hair perfume, Turaren wanka, Turaren  wuta, Turaren tsuguno, Turaren mopping,Turaren carpet Shu'umat khumra,and more, yar uwa kar kibari abaki lbr, (wholesale and retail) WhatsApp 09067621681, siyan na gari Maida kudi gida🥳

Instagram @Bakhoor_by_faixy

******************************

"Soul sis kina ganin abinda kika ce in nayi shike nan zan shawo kanta?"zama Leemah IK ta gyara sanann tace "Charm charm din Mommah in har ka bi yanda na koya ma to babu macen da ba za ka shawo kan ta cikin sauki ba,ni mace ce ka sani and Wlhy babu macen da bata son kulawa,kace babe din ta mu bata taba soyayya ba ko,perfect opportunity ka ga babu burbudin soyayyar kowa a ran ta balle ace sai kayi wahalar share ta,in har ka dau tips din da na koya maka to ina me tabbatar maka za ta so ka,just take a look at yourself my love Allah ya baka kyau ga arziki babu macen da ba za ta so ka ba,duk da kace mun ita wanann ta musamman ne tana da kyau sanann abun duniya be dame ta ba,ya sanya na baka shawarar sace zuciyar ta ta hanyar kalamai masu dadi kai na miji ne sarai ka san me nake nufi duk da ba wai budurwa ka cika yi ba amman ka san hanyar da za ka janyo attention din ta kan ka,tunda lucky you baka da rival,saidai wlhh ka ga wanann fushi da zuciyar banzan ta ka babu macen da za ta dauke shi,ya zame maka dole in har kana son yarinyar nan ta so ka to wlhh sai ka aje wani isa izza takama,ji da kai da kuma zuciya domin shi me nema kullum shine a kasa,and mata da kake gani yan lallabi ne sam ba a nuna wa mace power domin a sanda ka ce za ka nuna mata ka isa sai ta bi abinda ka ke so dolen dole to a lokacin ne ita kuma za ta ce baka isa ba sai ka ga an yi ta samun matsala,so dole sai kayi hakuri tare da kau da kan ka daga kan kananun abubuwan da za ta na maka,sanann sai kyauta duk da ma na san wanann a jinin mu yake ko don Daddy,babu macen da bata son princess treatment ka fada mun kana yi to kara domin shi kyauta duk kankancin sa kara dankon kauna da soyayaya yake,haka zalika duk yanda mace ta kai ga son ka in har baka mata Ihsani to yasin fice mata a kai kake yi,domin zuciya na son me kyautata mata,ina tabbatar maka Lil bro in har ka dau wanann shawarar da na baka za ka shawo kan babe din ta mu duk taurin kan ta kuwa,but ni baka fada mun sunan ta da family name din su ba?"

Tsaki Beel ya ja sannan yace "Adda Leemah kina ta baiwa banzan nan shawara abun da zai fi komai baki haushi FIK kamar tsoron yarinyar yake,ita ba kowa ba ba kuma yar kowa ba fa,and abun takaicin ko phone number din ta baya da"da sauri FIK ya katse shi don har da farko ya tsorata don Wlhy ya dau Beel fada wa Leemah zai yi kan fake relationship yake son yi da Sabeeha.


"Soul sis rabu da Beel na rasa why ya tsani Baiwar Allahn nan"dan kallon shi tayi sannan tace "da gaske ne tsoron ta kake ji?And wai ko phone number din ta baka da shi?"

A hankali yace "ni fa ba tsoron ta nake ji ba kawai yarinyar ce akwai cika ido,duk sanda na tashi don tunkaran ta sai na ji na kasa,and be rasa hadi da rashin kula maza da bata yi,Soul sis ko sau daya ba a taba ji ko an gan ta da na miji suna zance ba kullum tana tare da kawar ta ko mata ma ba shiga harkan su take ba balle maza,zan iya ce miki babu me contact din ta duk makarantar to taya zan samu?"

Dariya ta fashe da shi harda tafa hannu sanann tace "wonder shall never end!!My lord you are so great Wlhy wai yau FIK ne is in love ikon Allah,kai charm charm daman zan ga irin ranar nan,Awnnn my little cute brother is in love"ta kare tana Jan kumatun shi cike da farin ciki don daga ganin yanda ya damu yake bata labari ta tabbatar ba karamin so da kauna yake yi wa wanann budurwar tashi da ko sunan ta be fada mata ba.

Hannun ta ya zame daga face din shi "can you stop this pls am nor more a kid yanzu in su Rayyan suka fito ai sa mun dariya"ya kare yana hade rai,Dan dariya ta kuma sanann tace "finally yaron Mommah ya girma hankali ya zo gwama kayi ka shawo kan ta mu aurar da kai ko ka bar mana gari yayi sakat,but seriously ban dau akwai wanda zai tsorata shugaban Rocket gang ba"ta kare tana kunshe dariyar ta,hakan ne ya hasala shi tare da mike wa ya kalli su Beel "guys let's get going"

Da sauri ta riko hannun shi sanin da tayi sarai fushi yayi "zo abun ka Autan Mommah,ai ba mu gama magana ba za ka tafi", "yo Ai gani nayi kina neman bata mun rai don na zo gidan ki"ya kare yana hade rai,kai ta girgiza sannan tace "to sorry koma ka zauna ka ga irin zuciya da fushin da na gama maka magana kan dole ka rabu da su in ba haka ba matsala za kuyi ta samu da ita yarinyar,maganar number kuma ya ci ace by now ka samo number din ta coz sending cards and flowers kadai ba shine zai sanya ta so ka kamar yanda kake son ta ba,yana da kyau ta san wa ke tura mata sanann ta wayar ce za ka yi kokarin gina fadan ka tare da koyar mata yanda za ta so ka ta kaunace ka,and a iya tunani na tunda ka ce ba kowa take kula wa ba banda kawar ta,to dole through kawar ce za ka sami contact din ta,ka gane ai?"kai FAIZAAN ya gyada mata inda abun ku da yar uwa ta zauna wanann ranar har kusan yamma koya wa FIK dabarun da zai bi ya samu kan Sabeeha, tare da koya masa yanda Sabeeha za ta so shi take ,inda su Beel bakin ciki kamar ya kashe su,don suna da zuwa joint amman ya kashe musu,Wlhy da sun san abunda zai kawo su ke nan da ba su biyo shi ba,don to sun san sarai wanann bata lokaci ne tunda ba wai soyayyar gaske bane,inda shi kuwa ya nutsu sai aukin gyada kai za ka rantse da Allah a class yake yana daukan karatu,cikin zuciyar shi ko dadi kashe ni don kan shi da farko kusan kullewa yayi,and ya rasa ta yanda zai samu number din ta daman,don sam be kawo tunanin zuwa gurin Zuhra ba,saida ta tabbatar ta sanar da shi duk wasu abubuwan da ya dace sanann ya rungume ta tare da mata kiss a goshi,dariya tayi tare da ture shi

"Kai dai charm charm zan ga sanda za ka girma,make sure dai na ji feedback me dadi,and ya ci a kawo mun wanann in law din nawa na gan ta in bata kyauta na wahalar mun da kai da tayi,tare da breaking record don ita ce mace na farko da na fara jin kace kana so,duk da ma baka fada mun sunan ta ba"

Dan dariya yayi sanann yace "kar ki ji komai Soul sis zan kawo miki Barbie doll har gida ki gan ta"baki ta bude tana dariya "ah lalle dole na fada wa Mom ta fara shiri yaron ta ya samu mata"ta kare tana shiga daki, "aa Soul sis ba haka muka yi da ke ba,dadin abun kin san makomar me karya promise"daga dakin ta sa dariya sannan tayi shouting "ba dai ni kake hada wa da Ayatu Munafikun ba"be kai ga bata amsa ba ta fito,side hugging din shi tayi sanann ta shafa kan shi "kar ka ji komai yaron Mommah ba wanda zai ji maganar nan,it's our little secret so ba damuwa and in sha Allah zan taya ka da addua Allah ya sa ka shawo kan ta da wuri,make sure kayi duk abinda na fada maka and let's stay in touch in case akwai abunda ya shige maka duhu,my regard to Mom and Dad in ka koma gida"hugging din ta back yayi sanann ya ce "kar ki ji komai Soul sis ki ce da Little Monkeys din ki na tafi"kan shi ta kwade a lokacin da ya bude kofar mota sanann tace "thank god Monkeys din nan kamannin Fav uncle din su suka yi"ta kare tana dariya sanann ta mika wa Jawad rapper yan dubu dubu guda 3

"Take this dear kwa sha mai na gode da ziyara"nan ko suka mata goodbye tare da godiya sannan suka baro gidan,inda ran FIK kal don ganin ya kusa samun nasara,kai tsaye Taheer guest palace suka nufa,inda direct dakin da suka saba zama suka karbi key sanann suka wuce,kai tsaye toilet FIK ya fada saida ya wanke jikin shi tas sanann ya fito tare da shirya kan shi cikin wata Maroon Jalabiyya wace ba karamin kyau tayi masa a jiki ba kasancewar shi farin mutum,turaruka ya fesa sanann ya fada kan gado da janyo wayan shi.

"Geeee!!"ya ji Nabeel ya fada,goshin shi ya dan dafe sanann a hankali yace "not again pls Beel allow me to reason something good,na san me kake son fada and answer din dai yes ne sai mun je gidan su so called Zuhran nan,left for you in kana son mu je tare in baka so kuma I won't force you amman ni kam zan je"

A hasale Nabeel yace "ni dai Wlhy wannan maganar yarinyar is getting on my nerves Gee bana son yarinyar nan and saisa tun day one nace ma wanann silly little idea din naka be yi ba sam Wlhy,ina jin tsoron along the line ka je ka fara developing real feelings wa yarinyar nan in haka ta faru muna wanne?FIK yarinyar da ta ci mana mutunci tayi mana abinda babu wanda ya isa yayi mana duk fadin duniyar nan,ka duba ka ga yanda kake wani rawar kafa akan ta sai wani siyayya kake yi mata,kullum baka zaune baka tsaye gurin tunano irin Romantic abunda za ka yi mata wanda zai burge ta,Wlhy ni sam bana son wanann dare din da muka yi da kai,kawai don ba yanda na iya da kai ne don na san a cikin biyu dole ayi daya,ko dai ka fada tarkon soyayyar yar matsiyata,tayi breaking heart din ka,reshe ya juya da mujiya,ko kuma kayi wasting time din ka a banza domin wallahi yarinyar nan idanun ta tar suke a bude,and Wlhy kan ta daga gani akwai masifan tauri babu alamun ya taba hawa wuta,ko Dog din Mahaukata ne ya cije ta na san babu yanda za a yi tayi accepting din ka har ku fara soyayay balle ka samu kayi breaking heart din ta,just think this twice Wlhy you are just wasting your time,yarinyar da tun da take a rayuwar ta bata taba sauraran wani da na miji ba,saisa da tun farko shawara ta ko na su Akram ka dauka da kayi saving time energy da money din ka daga wannan shashashar yarinyar me zubin mutanan ruwa"ya kare a hasale.

Dariya dan kadan FIK yayi sanann ya mike tare da dakan shoulder din Nabeel sanann yace "Zan shiga gari,akwai me son zuwa ko nayi tafiya ta?"mike wa Jawad yayi sanann yace "mu je Gee akwai abunda zan biya na karba daman"daga haka ya dau car key din shi,har ya kai kofa sai kuma ya tsaya tare da juyowa

"Beel FIK be taba sanya abu a gaban shi be samu cikar burin shi ba,in har na rasa abu to Wlhy ba zan taba barin wani ya mallaki kalan abun ba ma balle abun,ni na shiga Bet din nan don kai na,and na san dalili na na shigan ta,sannan nace da kai in nayi losing zan baka car din na,ka ga 3 months sun yi ban yi abunda nake so ba?Don haka pls ban son takura da damuwa abun nan ni nace zan yi a tunanin ka ni wai son ta nake??Wancan jakar har kana tunanin ni FAIZAAN zan so ta??Haba just take a look at me mana Ai da ko na shiga 3,don haka in ma tunanin ka wai daga WASA DA SO zai koma Soyayyar Gaskiya to ka farka coz you are day dreaming,don har yau ba a haifo macen da ta cika mace da za ta sace zuciyar FIK ba,don haka wannan ya zamo last time da za ka mun irin wanann maganar pls"ya kare yana me ficewa daga dakin,harara Nabeel ya watsa mishi sannan yayi kwafa

"Wlhy Akram ku rubuta ku aje watan rabuwar Rocket gang ya kusa domin am very sure FAIZAAN fadi Bet din nan zai yi,don na ga daga abun wasa shi to personal yake dauka,ina jiye mishi tsoron ya fada Soyayyar shegiyar yarinyar nan,wlhh shi talaka bayi da wata rana a duniyar nan,sai shegen isa fadin rai da jin haushin me kudi,wanann yar marasa tarbiyyan in har FIK ya bari ya fada son ta da gaske,Wlhy ba karamin Azaba zata gana mishi ba,sai ta ci uban shi ta kwashe duk wani tattalin arzikin sa,shegiyar gold digger I hate her with so much passion Wlhy" ya kare yana Jan tsaki kamar tongue din shi zai fita.

"Take it easy bro,duk fa mun san halin FIK babu me wanda ya isa sanya shi,haka zalika babu wanda ya isa hana shi,tunda har shi ya zaba yi mata haka kai naka a wanne za ka daga hankalin ka?Kar ka manta duk mu taya shi fada muke amman the real abun akan shi fa ya faru Marin shi tayi fa in baka manta ba,an taba mu ma ya tsaya sai inda karfin shi ya kare kana tunanin akan na shi ne ba zai yi abinda ya dace ba?Tunda ka ga ya nace akan hakan to dole yana da solid reason behind it,just watch and see ni na san FIK ba zai ba mu kunya ba,besides wace ce ma Sabeeha cikin mata ko daya bata da qualities din da FIK ke kauna da so a gurin mace so pls stop worrying and disturbing yourself over this small thing okay"Farouq ya kare yana dan murmushi,kai Nabeel ya gyada alamun gamsuwa sannan suka fara hira a tsakanin su.

Kai FAIZAAN ya gyada bayan ya gama jin abunda Beel ya fada,da maganar Farouq sanann ya girgixa kai, "Jawad har yanzu Beel be gama sani na ba ko in ce yana mancewa da ni,ni ko har anyi macen da za ta gana mun azaba a duniyar nan har ta ci Alh Ismail Kwairanga??Dan dariya yayi sanann ya daura da NEVER!!!!Ba a yi ta ba kuma bana tunanin za a yi ta har a nade duniya,wanann maganar da Beel yayi ya janyo Wlhy sai na yi doubling azabar da nake shirin gana wa shegiyar yarinyar can,wuce mu tafi zan ba wa Beel amsa amman ba yanzu ba,sai randa na nuna masa Nafeesa take ko Sabeeha a kasa tana rokon kar na rabu da ita,a lokacin ne zai san eh tabbas ban taba fadi a Bet ba,a lokacin ne sai san ba wanda ya isa ya taba FIK ya zauna lafiya,a lokacin da na karya ta kasa nayi breaking heart din ta into smaller pieces na sanya ta kuka tare da bakin ciki,bakin tsiya ya mutu a lokacin ne zai san eh da gaske na fi shi jin ciwon abunda tayi mana,Wlhy tallahi na rantse maka with my living God Jawad sai na kaskantar da yarinyar nan,sai na sanya mata damuwa kunci da bakin ciki,yanda ta dagan hankali har ta hani bacci randa ta mare ni nima sai na rama,shatin hannun ta da ya fito a fuska na,ta sanya nayi wa Mom karya sai na bar mata tabon da manta shi zai yi wahala,babu jakar abu a duniyar nan kamar Addiction when you are Addicted to something or someone duk sanda babu wannan abun haka za ka koma tamkar matacce,da ni take sai tayi danasin haihuwar ta a Kano ma da aka yi,sai ta ji dama bata shiga BUK ba a rayuwar ta,ba dai ita tsiya ba za ta ga ko za ta samu bakin tsiya gaba"ya kare yana huci domin a kullum da tsanar Sabeeha yake kwana yake tashi,jin Nabeel kawai yake in yana wakar ya tsane ta,shi da ya san irin tsanar da ya ma yarinyar nan da ko labarin ta da sunan ta ba zai na kira a gaban shi ba,dole ne kawai ya sanya zai yi plan din nan domin yana son yayi taking din ta by surprise ne yana so sai ta yarda da shi yayi stabbing din ta from behind a nan ne za ta gane bata da wayo,kuma tabbas ita din mata kunyar karya ce,sanann karyan rashin mutunci da iskanci take yi(Uwaye😩da Kawaye na Sabeeha,don't come after me ooo🤭🤭no be my handwriting be this🤧and kar wace ta sake ta zagi FIK ehee☹️☹️fansa yaran Mommah yake shirun dauka💃🏻💃🏻)

Hannun shi Jawad ya riko sanann yace "Kyalle Nabeel Gee dalla,wani time din sai yana magana ba tare da sanin abunda yake fada ba,tunda har kace ga abinda kake son yi mata mu Ai ba mu isa hana ka ba,so go on with your plan tunda har shi kake ganin yayi maka,na ga duk cikin mu ka fi mu jin haushin ta tunda kai ta mara ba mu ba,and ko dayan mu aka taba sai yanda karfin ka ya kare balle kuma kai da kan ka aka taba,ko sama da kasa za su hade na san babu abinda zai sanya ka yafe wa yarinyar nan"kai kawai FIK ya gyada sanann yace "mu je bro na san an kusa gama Polon ma,daga nan sai mu biya gidan su wancan baby Elephant din,hope ka san gidan"dan dariya Jawad yayi a daidai time din da suka shiga motar sannan yace "Haba Geee taya ma zan san gidan su Baby Elephant ni ba kewan Animals nake ba,sai dai mu tambayi wani Animal din ko ya san gidan yar uwar shi"duk sai suka fashe da dariya kuma,daga haka FIk ya tada mota tare da sake kida sai gari.

Ba su suka kammla da filin Polon ba sai guraran Magrib,so a gurguje suka fito,domin sam ba su ma so yin dare ba,saida suka tsaya suka yi salla a masallacin kusa da su sanann suka wuce School,don tunanin duniya FIK yayi amman be san inda zai samu address din su Zuhra ba,to Kano ba karamin gari bane balle ace ita kadai ce me sunan,tunanin da yayi kila akwai wanda ya san inda take zama a cikin yan Course din su,ya sanya shi yanke shawarar zuwa makarantar domin a yau yake son zuwa ayi ta ta kare,don in ya tsaya sanya 3 months sai ya zo ya wuce a banza ya ji kunya,don Wlhy ko kaffara ba zai yi ba in har ya fadi Dare din nan ba karamin dariya su Beel za suyi masa ba,don haka zama ba ta gan shi ba.

A kofar hostel din mata yayi parking motar shi,inda Jawad yace da shi ba zai fita ba ya kuma yi sauri,so fitowa yayi tare da jingunawa jikin motar yana sake sake a ran shi,ganin yanda yan tsirarun mata ke kai kawo ya sanya shi ma kasa gane wa zai fara tambaya,domin sam shi fa ya tsani shiga harkan matan BUK don yanda suke wani cika da jin kawukan su,ganin lokaci na wuce wa dare na kuma yi ne,ya sanya shi bata rai tare da tare wasu yammata sun zo wuce wa,da ganin shi kuwa duk suka zaro idanu domin kaf sun san shi sarai,kasa kasa Zulfa'u tace "inalilhi Hameedah FIK ne yau ya tsare mu"

Yan matan da ta kira da Hameedah ma kasa kasa ta maida mata da "Zulfa Allah ya sa cewa zai yi yana so na domin Wlhy na daidai ina kaunar shi"harara Zulfa'u ta kwada mata sanann tace "dadi na da ke Wlhy son kan masifa ni ce miki aka yi baya burge ni??Allah dai ya ba wa me rabon cikin mu sa'a domin samun FIK tamkar samun dami ne a akala ne kin ga ko ba abun wasa bane,don haka zo mu tafi a fafata"nan fa suka canza tafiya aka hau karkada dan jikin da be kai ya kawo ba duk don a burge FIK,yana tsaye jikin motar shi yana kallon ikon Allah don Wlhy dariya ma suka so bashi don yanda suke malkwada da dan karamin jikin su sam babu abubuwan juyawa shine abunda ya bashi dariya har ya kasa danne wa don yanda suke yi yanda kuka san kazar da ta shiga mai be ishe ta ba,cikin karyar da murya da juya idanu kuwa suka gaida shi.

 
  Saida ya tsuke fuska tare da hade rai kamar wanda be taba dariya ba sanann yace "can you behave well and stop acting kamar chicken din da ya sha hot oil da ran sa,ni tambayar ku zan yi"da sauri suka kame kan su don sanin hali aka ce wai ya fi sanin kama,ganin haka ne ya sanya shi dalewa kan motar shi,saida ya gama watsa musu kallon wulakanci sanann ya tabe baki yace

"A cikin ku akwai wanda ya san Baby elephant??"kallon juna suka a tare suka furta "Baby Elephant kuma?"goshi ya dafe sanann ya hade rai yace "nace a cikin ku akwai wace ta san wata yarinya Zuhra???"

Nan ma saida suka kalli juna kafin Zulfa tace "Aa ni ban gane ta ba,ko kin gane ta Hameedah?",saida ta dan yi murmushi sannan tace "Zuhra Abdul-Mudalleef  in ce kake nema?"

"Oho ni ba fa sanin sunan Baban ta nayi ba,na dai san sunan ta Zuhra tana course din Food and Nutrition"Ai da jin haka tace "eh wlhy ita ce kawar Sabeeha ina?"Da jin haka yayi saurin gyada kan sa alamun ita yake nema.

"Ayya Ai room daya muke da ita,saidai yau ba a Hostel za ta kwana ba,ta koma gida", "kin san gidan su?"shine abunda ya tambaye ta.

"Na dai ji tace a Unguwar Kundila take bayan wani Masallacin Jumma'a,wani abun za ta maka?Ai tunda bata nan I think mu ma za mu iya maka ko ba haka ba Zulfa'u"a take kuwa Zulfa ta wani kashe ido daya tare da murmushi,wani dogon tsaki ya ja tare da watsa musu kallon banza sanann ya sauko ya shige motar shi ba tare da ya ko kalle su ba,da sauri ya dau Perfume tare da feshe motar da jikin shi,don Wlhy wani wari ya ji suna yi,dariya Jawad ya shege da shi sanann yace "FIK baka da mutunci ko kankani Wlhy"

"Kai Jawad na raba ka Wlhy yaran nan yanda ka san ba su san me aikin Soso da soap ba ka ji warin da suke yi"shiru yayi tare da bude dashboard din sa rapper na yan 200 sabi ya dauko tare da zuge glass din motar suna nan tsaye mamaki ya kama su,watsa musu kudin yayi tare da dan daga murya "ga shi a samu a sai perfume don Allah a na shafawa kar ana sumar da yaran mutane"daga haka be kuma bi ta kan su ba ya ja motar shi a tsiyace suka bar school din,Jawad kamar cikin shi zai yi ciwo don dariya

"Wlhy gee daga dan iska sai kai ,Bura uba ka ga idanun su kuwa sanda ka ce su sai turare",a harzuke yace "kai ma dai Jawad da kin Gaskiya kake Wlhy,yara kamar wanda babu ruwa a Hostel to ko dai rashin ruwa ake?Saisa ko hauka nake ban hango zan iya zaman Hostel ba"ya kare yana dariya,Allah ya shirya ka Jawad yace yana dakan shoulder din shi,inda ya amsa da Ameen sanann suka dauki hanyar Kundila.

   
  "Kan uban nan Hameedah ashe rashin mutuncin wanann yaron har ya wuce tunani na,yanzu tsakani da Allah mu zai duba kamar ni Zulfa ya ce wai mu sai turare ke nan nufi yake muna wari ko me??Mu zai ce wa ba ma wanka?Na ga duk Department din mu har kwatance ake da mu gurin daukan wanka da kwalliya amman wai mu zai ce wa muna wari"ta kare kamar me shirin yin kuka,don ba karya ta ji zafin abunda FIK yayi musu, "hmmm ke Zulfa kina ma da bakin magana,Wlhy ni ji nayi tongue dina ma yayi mun nauyi,sam ban dauka yaron mugun dan iska bane,ko da  ake bada labarin shi ashe ya wuce nan,na ga uban da Zuhra za ta nuna mana,ke take da shi ba mu da,da har ya zabe ta kan mu,ko uwar me ma zai yi da gidan nasu oho,yarinya kullum kamar munafuka cikin rufe jiki,ita da Aljannar kawar tan nan"

"Ke Dalla Hameeda wai damuwar ki Zuhra ina miki maganar cikin mutuncin da yayi mana,masu wari fa ya kira mu harda ba mu kudin turare"harara Hameedah ta maka mata sanann tace "dole nayi miki ki tsaya ki saurare shi da za ki dame ni,ai sarai na ji abunda yace and tunda ya ba mu kudi Ai sai mu shiga kasuwa mu sai turaran mu fara fesa wa,ni fa Wlhy yaron burge ni yake"ta kare tana kwashe kudin tare da rungume su a kirjin ta,tsaki Zulfa ta ja don ganin irin cin kan da Hameedah ke neman yi,tare da wuce wat ta hostel tabbas da ba dun ta san Waye FIK ba da sai tace sai ta rama cin fuskan nan da yayi musu,amman ta san tabbas saidai ta rame ba dai ta rama ba don ya ci uwar ta ya yaga Leda a rashin mutunci,duk wankan sun nan ya kira su da masu body odor.

  (Matso ki ji yar uwa in baki wata sirri kyauta,shi warin jiki akwai abubuwan da kan kawo su,and mostly masu shi ba su sani,to ga hanya da in sha Allah in kika bi kika kiyayye ba ke babu warin jiki,

1.Chubby mata mata masu jiki ke nan,daga zubin halittan da Allah ya baki in har baki iya kula da kan ki da jikin ki ba to matsala ta samu domin akwai guraran da ke rike wari da yawa a jikin mutum,barin ma masu kiba,ya sanya ya zamo dole in har kina da jiki to ki yi takatsantsan da jikin ki,gudun zubar wa kan ki da mutunci a gurin mutane.

2.a duk sanda mace ta fita kura ya hau jikin ta ya na da kyau tana dawo wa tayi maza ta nemi ruwa ko ba sabulu ta watsa wanann kuran ya sauka domin in har bata wanke shi ba,shi ke haurawa ya taru a hammata ko kuma private part din mace sai ka ga yayi causing mata Body or Virginia order Allah ya kiyaye.

3. Yana da kyau a duk sanda mace za ta hada Murhu wanann tokan da zai hau jikin ki due to fifita wuta ko iska ki tabbatar kin wanke shi tsaf,ko da ace ba za ki samu chance din wanka baki daya ba yana da kyau ki nemi ruwan ki me kyau ki wanke tsaf inda ashes din ya zuba miki,ko da kuwa ba za ki sanya sabulu da soso ba,domin barin shi ya bushe a jiki shike shiga ta kofofin gashi a sanda suka bude yayi causing miki body order Allah ya kiyaye.

4.Gumi/Zufa akwai wanda naturally haka Allah yayi su masu halittan gumi ne ba lalle sai me jiki ba akan samu sirarra ma da yawan zufa,wani kuma bayan aiki ko an shiga rana,to yana da kyau tare da matukar amfani da zaran kin yi gumi nemi ruwa ki watsa ko babu sabulu ki tabbatar dai kin wanke
Wanann zufan domin barin shi ya bushe miki a jiki
Kan iya Haifar da matsalan warin gaba da warin jiki,wanda rashin magance shi da wuri kan yi wa wahalar rabuwa da shi saidai ayi ta kyamatar ki ana zindar ki a cikin mutane,abun haushin ma in kana yi baka cika sani ba🥺Allah ya bada ikon kiyaye wa sanann a guji zama a kasa akan tiles yana ila ga mace ba kadan ba,haka zalika yawo ba takalmi,sanann kar ayi wasa da turaruka don Allah,in sha Allah nan gaba zan sanar da ku abubuwan da ke brush da su don gyaran baki da kuma tsaftace baki🥰.

      Direct Kundila suka wuce inda da taimakon kwatancen su Zulfa suka iso har masallacin,saida suka yi sallan isha domin ba laifin FIK akwai kokarin tsaida Sallah duk iskancin sa,wani matashi suka tambaya ko ya san gidan su Zuhran?Inda kuwa yayi musu bayani ko in ce kwatance,baki FIK yayi ta tabe wa yana me gingina wa masu rayuwa a local area irin wanann,don ma Allah ya taimaka gidan su Zuhran ba cikin lungu yake ba da wanann ne zai kuma bata masa rai,barin motar shi bakin hanya a irin wannan unguwar da security ba isar su tayi ba,da ke sun gane kwatancen matashin sai ga su har kofar gidan su Zuhra,parking yayi a filin da ke gaban gidan tare da zuba wa gidan idanu,a ran shi yana fadin "shegu ji gidan yan iska ko gurin aje motoci na ya fi gidan nan girma,amamn sai uban fadin rai da girman kan masifa ku ba yan uban kowa ba"ya kare yana Jan tsaki,don sam unguwar da fasalin gidan ne masa ba tunda yake baya jin ya taba zuwa irin wanann unguwar ko irin wanann gidan,mamaki yake yanda suke rayuwa a cikin gidan nan,ko zai mutu baya jin zai iya shan ruwa a wanann gidan,duk da ma fa wai be shiga cikin gidan ba balle ya san yanayin gidan har ya yanke hukunci🤧.

  Ganin shiru har yanzu kuma be kashe motar ba ta sanya Jawad kashe wakar DND dake tashi a motar sannan ya kalli FIk "Gee lafiya?"

Dan guntun tsaki FIK ya ja kafin yace "Jawad kune masu yin harkan love din nan ni fa ba sanin komai yana yi akai ba,kawai dai am so desperate ne in nuna wa Nabeel ba a ja da ni,amman Wlhy ban ma san ta ina zan fara ba"ya kare tana dafe goshin shi,dan dariya Jawad yayi sanann yace "FIK!!Charm charm din Mommah"

"Ban son wulakanci Jawad"dariya Jawad ya kwashe da shi sannan yace "am sorry don't tell your Mommah pls"shima dariyan yayi sanann yace "ina waya ta lemme call my Mommy and tell her"nan duk suka sanya dariya kafin Jawad din yace "Ai yanzu dole sauka za ka yi a nemi yaro sai a aika shi ace Zuhra ta zo,tunda ba sanin mu suka yi ba balle mu shiga"

"Yanzu don ba su san mu ba ba za mu shiga ba saida a aika ta zo sai kace wa me saida abu akan street"dariya Jawad ya kwashe da shi,wani  haukar sai FIK yanzu aka bar shi sai ya shiga gidan su Zuhra ya mata maganar ma gaban maman ta ya fita abun shi.

"Can you stop laughing and talk to me"ya fada sounding a little bit angry, "okay fine am sorry,No vex Gee,kamar yanda na fada maka saidai a aika a kira mana ita,don haka na ga ana yi a irin local arean nan,amman ka shiga gidan ai sai a maka dukan barawo da daran nan"harara FAIZAAN ya kwada masa sanann ya bude murfin motar "Ai ko da Wlhy suka sake suka taba ni sai sun kare rayuwar su a prison,ni yanzu a ina ne ma zan ga yaron?this whole thing is stressing me aswear"ya kare yana Jan tsaki tare da saukowa daga cikin motan,dan dube dube ya fara wai ko zai ga dan aikan da Jawad ya fada masa,ana haka kuwa sai ga Baban su Zuhra ya dawo daga masallaci zai shiga gida.

Tun daga nesa ya hango hasken mota a kofar gidan shi,dake FIK ne Riga ya kashe motar ba,Talaka da dogon buri,nan take ya washe baki don tabbas ya san motar nan mutumin ciki me arziki ne,don daga ganin yanayin motar,and tunda ya ga motar a kofar gidan shi ya san yau ranar sa'ar sa ce,yasin ko da batan hanya suka yi basu isa tafiya ba sai sun yaga mishi wani abu,cikin gudu gudu sauri sauri yana leken bayan shi Allah sa Faisal dan shi baya biye da shi,a haka ya iso kofar gidan na shi,da sauri ya isa inda FIK ke tsaye jikin motar shi yayi folding arms as usual yana jiran wucewar yaro,da sauri kamar wanda zai fadi kasa yace

"Ahhh ran ka ya dade an wuni lafiya?Ya gajiya ya dawainiya da jama'a kuma?Kai sannu da kokari fa"ya kare yana dan dariya gaba daya ma ya rude ganin babbar mota ya ma rasa wani irin tuanni zai fara yi,jin maganar na shi ne ya sanya FIK juyowa duk da babu wuta a unguwar amman gari be gama duhu can ba so yana iya ganin Malam Abdul mudallif sosai,da kyar ya iya bude baki yace "Yauwa sannu"daga haka be kuma ce masa komai ba banda kan shi da ya maida gefe.

Ganin haka be sanya ran shi ya baci ba ila ma dada gyara murya da yayi sanann yace "ran ka ya dade in ce batan hanya kuka yi ne?Ko kuma wani kuke nema"be so amsa shi ba amamn jin ya matsa masa da yawan magana ya sanya yace

  "Gurin wata yarinya Zuhra ko Zahra Abdul mudallif muka zo,an kwatanta mana wai nan ne gidan to friend dina ne ya ce ba zan iya shiga gidan da kaina kiran ta ba saidai mu aika yaro,so yaron nake nema wani abun ne Malam?"ya kare yana daga mishi gira daya.

Ai da gama jin haka sai ga Baban Zuhra kamar bakin shi zai yage don murmushi in har ba yaudaran shi kunnuwar shi suke ba wanann me zukekiyar motar me jajjayen kunne me kama da bature ne ko balarabe diyar shi Zuhra yake nema,Wayyo dadi kashe shi.

Da sauri yace  "ka ce gurin Zuhra ka zo?Ikon sai Allah yau Zuhra ashe tana da jini me karfi har haka"ya kare yana washe baki ji yake kamar yayi tsalle babu abinda zai hana shi daura wa Zuhra aure da farin Balaraben nan cikin sati uku kadai kafin makiya da mahassada su shiga lamuran su lalata.

Saida FIK ya gama kallon shi yana ma tunanin anya wanann da lafiya shi kuwa "eh ita dai nake nema ka san ta ne?"ya tambaya yana tabe baki.

Da sauri Baban Zuhra yace "sani kai,wai ai na san ta farin sani ma,Diya ta ce Zuhra nan kuma gida na ne,ni ne Mahaifin ta Malam Abdul mudallif Ai duk unguwar nan kwatance ake da gida na tare da yara na,saboda irin tarbiyan da na basu,daman na san kyau da tarbiyyya irin ta Zuhra dole gidan manya za ta shiga ba gidan matsiyaci ba,tsaya a nan bari yanzu na shiga in kirawo maka ita,ko kuma za mu shiga tare ne?"shi kadai duk ya bi ya rude kan shi saboda mugun son abun duniyar sa.

Kai FIK ya girgiza sanann yace "ina jira a kira mun ita din" da jin haka ko Malam Abdul mudallif yace "ah to to,ba damuwa bari yanzu na shiga in fito ma da ita"da gama fadin haka kuwa ya kwasa da mugun sauri sai cikin gida,Mota FIK ya fada inda ya tarar da Jawad na ta shan dariyan Baban Zuhra,shima saida ya dara sanann yace "gee duk rintsi duk wuya make sure to stay far away from talauci,ka ga kudade shine komai a rayuwar nan,yanzu ga mutumin nan kamar ya shige stomach dina don ya gan mu da big car,wai shi da kan shi ma zai shiga ya fito mana da ita,ya sani ko sace ta ko wani abun cutar wan za mu mata tunda Ai be taba ganin mu ba,wasu mutanan sai Allah Wlhy"ya kare yana Jan tsaki.

"Hmm FIK ke nan kai ke wanann tunanin irin wanann mutanan ba su damu ko me yar su za ta yi ba in har za ta kawo musu kudi,ai kallo da ya na yi mishi na fahimci mugun don son abun duniya ne,shege yana son kudi tun yana young be tsaya ya neme su ba for God sake ga gidan su,da ya nutsu ya nema in ce da yanzu lokacin jin dadi da facaka ne?Amman ina basu da wanann tunanin kai dai Allah kyauta"da Ameen FIK ya amsa shi.

      Baban Zuhra kam tun daga zauren gidan ya fara kwala mata kira kamar zai yaga makogaran shi don kira,kasancewar tana toilet hakan ne ya sanya bata amsa kiran nashi ba,jin haka ya sanya Mama saurin fito wa dankwali a hannu,tace "Malam sannu da shigowa"

"Au ke daman kuna ji na saboda iskanci da wulakanci kuka yi wa mutane shiru,na fa gaji da iskan ci da hauka irin ta ki Wlhy,ina Zuhran take dan uban ta da nake ta kiran ta tana share mutane"ya kare kamar zai rufe ta da duka.

"Bandaki take Malam ya sanya bata amsa ba,bari na ce da ita tayi saurin fitowa tunda kana neman ta"daga haka Mama ta nufi kofar bandakin tare da dan kwankwasawa "Zuhra yi maza ki fito Abban ku na neman ki"daga haka ta juya don ta tabbatar ta ji ta tunda ta mata alama don babu kyau magana kana bandaki.

Jin haka kuwa ya sanya Zuhra saurin watsa ruwa tare da dauro zani ta fito da sauri bayan ta sanya Hijabin ta,tare da tunanin ne Abban ke nema a gurin ta kuma.

A tsakar gida ta same shi ya kasa tsaye bare zaune,durkusawa tayi tace "Abba sannu da shigowa,ka kira ina wanka,wani abun za a maka ne?"

"Yi maza tashi Uwa ta maza je ki shirya ki fesa turaruka masu kamshi na san kina da su,don na ga wata me shegen kyau cikin jakar ki jiya,tare da Doguwar Riga ko shi za ma ki sanya ne?So nake ki fito fesss"baki ta bude domin tun tasowar ta za ta iya cewa ta manta yaushe rabon Abba ya yi mata magana cikin sanyi da dadin murya don za ta iya cewa ma duk yaran babu wanda baya shiri da irin ta don bata daga mishi kafa ko kadan don ma Sabeeha na taka mata burki to sai abun ya daure mata kai har ta gaza hakuri tace "Abba kaya me kyau kuma?Ko unguwa za mu?"

  "Ke bani son yawan magana don Allah tashi maza ki je ki shirya kar ki bata musu lokaci,bako kika yi a waje"jin kalman bako da yayi ne ya sanya ta bude idanu a iya sanin ta Abba baya son Habeebi wanda ya sanya bata ma cika barin shi zuwa zance gida in ba in tana school ba,don a fili yake ci masa mutunci kasancewar shi ba wani budi gare shi ba shima fama yake da yau.

  Da kyar ta bude baki tace Abba "Habeebi ne ya zo?"da ke sunan da take kiran shi ke nan duk sai ya bi shi,dan dariya Abba ya kwashe da shi sanann yace "kin ji Sakarya ko Habeebin uban ki wannan matsiyacin har ya kai na zo nayi mishi kiran ki,ke wuce ki je ki shirya kar na ci uban ki cikin daran nan wani hamshakin me kudi kyakkyawa kalan Larabawa ke kiran ki a waje,gashi can tsaye jikin babbar mota kin ga yanda ake harkan girma ba irin ta wancan kyamusheshen shegen saurayin ki me riga guda ba,Wlhy Saura in kika fita ki bata masa rai ko ki masa rashin hankali yau sai na lahira ya fi ki jin dadi,ki sake jiki ku fahimci juna cikin sati uku a daura Aure ki kaini Makka da Madina maza je ki shirya"ya kare yana washe hakwara,mamaki ne ma ya hana Zuhra magana ila mikewar da tayi tare da nufan dakin ta duk ta ma rasa inda zancen Uban nata ya dosa jinin Larabawa ne babban mota a kofar gidan su kuma wai gurin ta?Me ya zo nema?A ina ya Santa ma?And yaushe yace wa Abba son ta yake da har yake maganar aure cikin sati uku,ganin in ta tsaya tunani za ta bata wa kan ta lokaci ne Abba na kuma iya shigowa ya ci uban ta ya sanya jiki ba kwari ta shiga shirya wa tana tuannin Waye wanann ya zo gun ta cikin daran nan.......

    Assalamu Alaikum 🥵🥵

Da farko dai ina fara wa da bada hakuri Wlhy kwana biyun nan hidima ne suka mun yawa ya sanya kuka ji ni shiru,lafiya ta lau🤭🤭masu kira da messages don jin ko lafiya Wlhy kalau sai Alkhairi na kuma
Gode da kulawa Allah saka da Alkhairi.

   Kuna raina Wlhy zama ne ban samu ba na kuma so ya fi haka amman Allah be so ba,so ayi manajin wannan yanzu kam Alhamdulilah am done with ko wani hidima za mu dawo update kamar yanda muka saba na gode sosai da kaunar ku gare ni😩❤️

  Ayi mun afuwa da typing errors saboda zumudin in tura muku ko editing ban tsaya yi ba.

   Ina yi wa kowa fatan Alkhairi.

Continue Reading

You'll Also Like

46.3K 1.3K 7
فَتاه قوية و لكِن القدر أقوى مِنها غدرت مِن اقرب الناس ، تعذبت و ضلمت مِن اشباه الرِجال كانت تحب لكن طعنت فدخل رجال آخر رغما عِنها هل ستقع في الحُب...
5.2K 69 7
Now you gotta ask yourself. What would it be like to find out that the people you love and would die for, turn out to be self centered assholes who w...
105K 3.5K 57
𝐒𝐂𝐇𝐎𝐎𝐋 𝐁𝐔𝐒 𝐆𝐑𝐀𝐕𝐄𝐘𝐀𝐑𝐃 "𝚝𝚑𝚎 𝚋𝚎𝚜𝚝 𝚠𝚊𝚢 𝚝𝚘 𝚐𝚘, 𝚒𝚜 𝚒𝚗 𝚜𝚝𝚢𝚕𝚎. 𝚆𝚑𝚊𝚝𝚜 𝚖𝚘𝚛𝚎 𝚜𝚝𝚢𝚕𝚒𝚜𝚑 𝚝𝚑𝚊𝚗 𝚊 𝚖𝚘𝚝...