A SIMPLE DARE (WASA DA SO)

By marteybee

434 7 16

More

new book
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 9
Page ten
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20/21
Page22/23
Page 24/25

Page 8

14 0 0
By marteybee

✨✨
        A
SIMPLE

DARE

                              ✨✨

(WASA DA SO)

WRITTEN AND STORY
            BY
NERNAH MARYAM
      (MEEMARH)

 
             Kofa a bude take ga duk me son yin joining group dina😌,Amman Hajiya don Allah in kin san ba yin comment ko karanta littafi na zai kawo ki ba I beg you in the name of Allah kiyi zaman ki ba sai kin shigo ba!!haka zalika wanann group din na mata ne zalla don Allah Maza should stay away from my group👏

       My What's app group link👇🏻

           https://chat.whatsapp.com/EUrVVaKJnIBDTlQsxurZv0

Bismillahi Rahmanin Raheem............

(    In the name of Allah the most beneficient,the most merciful)

 
  Kofa a bude ta ke ga duk wani me good quality product da ya ke son Advertising ɗin shi,as Kaya masu kyau,da inganci (TALLAH) should contact me via :
                              08100046388

   Page 8️⃣

TALLA!!TALLA!!TALLA!!!

       https://chat.whatsapp.com/ImtxMSS1tuSKqvBpPqc03P

Assalamu'alaikum sisters🤗
KAMSHI* mace Mai kima, mace Mai daraja, mace Mai izza, mace Mai aji itace tasan darajan kamshi, if your perfume is not unique hajiyata you're just using ordinary air freshener🤣, hajiyata ko nawa Zaki kashe indai a turare ne baki Fadi ba😘 matan da suka gane suka San yanda zasu kankaro da martabar su, suke amfani da turare, a *BAKHOOR BY FAIXY* Zaki Sami Main chic, Bachelor, Husband snatcher, Her royal sexiness, Mysterious girl, Pleasure, Boovilous, White khumra, Maroon khumra, Black khumra, Hair perfume, Turaren wanka, Turaren  wuta, Turaren tsuguno, Turaren mopping,Turaren carpet Shu'umat khumra,and more, yar uwa kar kibari abaki lbr, (wholesale and retail) WhatsApp 09067621681, siyan na gari Maida kudi gida🥳

Instagram @Bakhoor_by_faixy

******************************

Shigowar Hajiya Samha na uku ke nan dakin FIK amman har yanzu yana toilet,goshi ta dafe don ganin lokaci na kurewa ita ya sanya ta tayar da shi da wuri wuri akan yana da lecture din safe amman gashi yana bata time a toilet,a bakin gadon ta zauna tare da shiga folding masa kayan da ta gani sun yi daya daya a kan gadon cike da kauna,don sam bata ga abinda FIK zai yi a idanun ta ya zamo laifi ba,ba karamin kauna da so take mishi ba wani ya gani ya dau bata taba haihuwa bane shine kadai tilon yaron ta,kun san ko cikin yara kawai wanda ka fi kauna ya sanya Manzon Allah yace ku ji tsoron Allah kuyi adalci a tsakanin yaran ku,zuciya dole da wanda ta fi so amman ana kokarin dannewa.

Lallausan murmushi ta sake idanun ta zube a kan kofa jin alamun bude kofar da yake kokarin yi,fitowa yayi hannun shi rike da karamin farin towel yana tsane gashin kan shi, "Mommah yaushe kika shigo?"ya kare yana maida mata murmushin,tare da zama da aje karamin towel din kan stool din da ke gaban mirror din shi yana me nufan hanyar closet din shi.

"Charm charm tun dazu ina nan zaman jiran ka,da alamun yau dai za kayi late,wanann wanka sai kace za a gurin diyar Gwamna ko ta shugaban kasa,ko dai Charm charm ka gano mana wata kyakkyawa yar gidan manya ne ya sa ka fara dade wa a wanka haka"dariya me dan sauti ya sanya sanann yace "Haba Mom ai saidai a bini ba ni dai na bi yarinya ba,kuma sarai ke ma dai kin san na kan dauki time in na shiga wanka"bata ce da shi komai ba ila zama da ta gyara inda shi kuma ya shige cikin closet din wanda in Sabeeha ta ga kayan da ke shake ciki ta dauka wata babban kanti ne😂🤭,domin kaya ne masu aji tsadd da kuma mugun kyau inda suka sha shiri cikin kyayatattciyar closet din don tana da dan girma,cikin nutsuwa ya zauna saida ya gama shafa mai sanann ya mike ya shirya kan shi cikin black trouser with sky blue long sleeve shirt inda ko ba karamin karban shi kayan yayi ba,turaruka masu shegen karfi tare da fitinnaniyar kamshi ya feshe ko wani lungu da sako na jikin shi da shi,sanann ya fito.

Kallon shi Hajiya Samha ta yi tare da sakar masa murmushi sanann a hankali ya furta "Masha Allah dan Albarka kayi kyau!!maza zo zauna na gyara maka kan nan,kayi break ka samu ka tafi"baki ya dan turo sanann yace "Haba Mom yanzu fa na girma,I can do that myself"

Dan hararan shi tayi sanann tace "za dai ka girma,Charm charm ko yara dubu ka Haifa you will forever be my little prince,so maza zo ka zauna time na kurewa"kiss ya manna mata a goshi da kumatun ta sanann a hankali ya furta "I love you so much Mommah"goshin na shi tayi kissing back ita ma sanann tace "love you more baby maza zauna"ba musu kuwa ya zauna inda ta gyara mishi gashin na shi kuwa gwanin ban shaawa kafin kace me har ta kammala sai ga kai ya fito fess sai sheki yake,shi kan shi FIK saida ya rungume ta don ganin kyan da ya kara.

Plate din abincin da ta shigo da shi ta bude inda da sauri yayi shouting "OMG!!!Mom it's been so long I had this kind of breakfast,I missed French toast and your Creamy Coffee"ya kare yana kai hannu,da sauri ta buge hannun na shi tana yar dariya "da kace you are not gonna take your break haka za ka tafi school"

Kan shi ya kwantar a kafadan ta sanann kamar karamin yaro yace "but Mom this are my Fav and na dade ban ci ba,can I take a bite pls,baki na kamar tongue dina zai fado kasa"dariya ta dan sanya tare da kwade kan shi,sannan tace da shi ya zauna da kyau,a hankali ta shiga bashi abincin a baki,inda shi kuwa kamar wani dan yaro sai shagwaba yake zuba mata,da ke abinda ya jima be ci bane kuma yana so ya you saida ya cinye tasss,dadi sosai Mom ta ji don ganin kwana biyu na wasa da cin abinci ne ya sanya ta masa wanann da kan ta don ta san yana so.

Toilet ya fada ya kuma brushing teeth din shi sanann ya fito,sock Mom ta sanya masa tare da taya shi saka takalmin sa,sanann ta kuma feshe shi da turaruka,kafin ta janyo shi,kiss ta manna mishi a goshi sanann tace "take a good care of yourself Charm charm duk uban da ya taba ka let me know,Allah maka albarka and make sure ka dawo da wuri"murmushi yayi sanann ya dan bata side hug tare da fada mata kar ta ji komai da wuri zai dawo,har ya kai bakin kofa sai kuma ya juyo tare da tsaya wa,gira daya ta daga mishi alamun lafiya?dan baki ya turo kamar dan karamin yaro sanann yace

"Mommah what of kayan da kika ce za ki ban na kai wa Akram?"goshi Hajiya Samha ta dafe tare da sakin dan karamar dariya "kai ya Allah ni bana ma manta ba banda ka tuna mun yanzu Charm charm mu je suna daki na,daga haka kuwa ta kamo hannun shi tare da fitowa daga dakin suka nufi part din ta a jere suna yan hira da dariya gwanin ban sha'awa,direct dakin ta suka shiga tare,inda komai yake nan a kintse daki ne me amsa sunan shi daki irin na matan manya wanda suka san ta kan gayu,babu abinda babu na yayi banda sanyi da kamshi irin na su na yan Shuwa babu abinda ya ke yi,domin Hajiya Samha ba karya akwai tsafta da kuma son gaye.

Pointing tayi mishi da hannun ta inda paper bags masu shegen kyau suke guda biyar inda ko wani guda dauke suke da Arabian plus Egyptian Abayas different designs and colors masu masifan kyau da tsada domin duk ciki babu wanda kudin shi zai yi kasa da 50k,ko wani jaka daya Abayas biyu ne a ciki da turaruka masu masifan kamshi da tsada guda biyu biyu a ko wani jaka.

Murmushi ya sake sanann yace "Ai ko Akram zai ji dadi Mommah a wa Salima magana ta kai mun mota"ita ma murmushi tayi sanann tace "right away my love,wanne daga cikin motocin naka za ka fita da shi?"

"Da black Venza din ki zan fita yau Mommah,and kudin a account dina za a tura"kallon shi ta dan yi hakan ya sanya shi sakin dariya sanann yace "My love ba FIK bane zai ci miki kudi dai account din Akram akwai matsala ne and be Riga ya je bank yayi complain ba"

Dan hararan shi tayi sanann tace "Charm charm ka maida ni Jadda ko?zo maza ka tafi kar kayi late do take care of yourself pls,yanzu zan sanya a tura kudin,hope baka bukatan komai ko?"kiss ya mata a goshi sanann yace "babu komai Mommah and I will take care don't worry tataaa"daga haka ya fice bayan ya dau car key din ta,da kallon kauna ta raka shi kafin ta danna bell din dake sanar wa yan aikin gidan ana neman daya daga cikin su,ba bata lokaci kuwa Saleemar ta iso nan ta kwashi bags din tare da jera masa a booth din motar.

A tsiyace kuwa ya figi motar tare da barin gidan securities nayi mishi fata da adduar Allah ya tsare hanya,tafiya yake kamar titin na uban shi ne,ga glasses din motan duk a zuge duk gulman ka ba za ka san Waye cikin motar ba in ba ka ga plate number ba don duk motocin gidan ya fita daban saboda plate number Kwairanga and sons suke using,banda na FIK da nashi FIK ne a jikin motocin shi.

Kai tsaye hanyar gidan su Nabeel ya nufa da ke ba wani nisa bane tsakanin su babu abinda ke tashi a motar banda sanyi kamshi tare da wata shegiyar kida me tsinkar da zuciyar me ciwon zuciya😂😂yanda kuka san wani mini club ya tafe yana gyada kai har ya isa gidan su Beel,a kofar gida ya same shi so daukan shi yayi kawai suka wuce sauran gidajen friends din nasu,saida duk suka hade sannnan ya nufi inda ya ke siyan cards da flower ya karba sannan ya biya ya karbi chocolates,tsaki Nabeel ya ja tare da tabe baki "aikin banza yarinya ba yar gidan uban kowa ba,ba ko wan kowa ba amman ace wai ko wani rana sai ta ci kusan 100k ko nace over ma tunda 1 Abayar da Mom ta bayar ya ci rabin 100k shi kadai"

Dafa shi FIK yayi sanann yace "c'mon dude kai dai ba mu samu bukatar mu ta biya bane,kudi kuma ai akwai su ba wai babu ba so ta ci iya cin ta ba zai kare ba,so nake na jika ta da Naira duk da ance ba me kwadayi bane amamn Wlhy babu zuciyar da ta ki dadi akan wanann dan kyautar sai ka ga na shawo kan shegiya,yau Mom ma ta tura mun 2mil kasan nace mata Babe din Akram ce so kudin wa shi ta baiwa,ni kuma sisi ba zan ba shi ba"Ya kare yana wa Akram gwalo

Ai ko nan suka yi mishi chaaa a kai kan ya ma isa dole ya basu rabon su,shi kuma yana kan cewa kwandala ba yi bayar wa,saida aka kai ruwa rana sosai sanann ya yarda yace zai basu 10k 10k each,haba nan suka ce basu son zance ba da kyar dai aka samu yace zai ba su 100k each don ma Akram yace zai fada wa Mom in be ba su ba,yana harara da komai yayi musu transfer,su kuwa suka ce sun ji in ya so idanun shi su fadi kasa.

Direct school suka shiga inda kan su wuce department din su,FIK ya kira Sageer yaron da yake aika kai flowers ya bashi bag daya tare da flower card da box din chocolates tare da fada mishi yayi sauri ya kai kar ta zo,da haka Sageer ya wuce Department din su Sabeeha tare da aje wa a saman seat din ta,guri ya nema ya zauna a fakaice yana gadin kayan gudun kar wani me son ran ya dauke.

Be dade da zama ba kuwa sai ga Zuhra sanye da Hijabin ta sallama tayi wa matan ajin da suka dan taru sannan ta nufi seat din su,tana Allah Allah ta iso ta kira Sabeeha don ganin bata zo ba har yanzu,ai ko da isan ta Sageer ya mike tare da kama gaban shi,ta je zama ke nan idanun ta suka yi tozali da jaka da flower,ai bata san time din da ta zaro idanu tare da shouting "oh my  fucking whattt!!"tsaban mamaki ma ta kasa zama sai kallon kayan take,tare da saurin rufe bakin ta daga ihun da ya subuce mata ganin hankalin mutane ya fara dawo wa kan ta,da sauri ta zauna tare da janyo jakar baki har kunne ta ga box din chocolates irin na rannan da wanda suka ma fishi,ta kai hannu za ta bude jakar don ganin abunda ke ciki,sai kuma tayi saurin aje wa tare da kwade kan ta "what the hell is wrong with you Zuhra?This bag is not yours na Goofy angel ne,and is a very bad habit bincike a abunda ba naka ba"ta fada wa kan ta tare da maida jakar yanda yake,ita kadai sai ta kalla sai tayi murmushi domin duk da ba wai ta san abunda ke ciki bane amman ta san babban abu ne don daga gani wanann secret admirer din Goofy angel din ta ba na wasa bane,har yanzu tana iya tuna taste din chocolates din da ya kawo last time,and har Allah Allah take su zo class ko zai kuma kawo wa don har Habeebee ma ya sha ya ce ya masa dadi,and ba karamin kyau da burge ta jakar tayi ba,duk da bata ga abun cikin jakar ba,ita kadai sai ta kalla tayi murmushi tana son sanin wannan bawan Allahn don is high time da ya kamata Sabeeha ta fara soyayya ita ma,tana son ganin Goofy angel din ta da An Babyn ta,balle in wannan bawan Allahn son ta yake ba karamin dadi Sabeehar za ta ji ba don daga gani kan shi a Waye yake zai iya soyayya tunda gashi har Roses yake aiko mata,da chocolates kamar a wani Indian film 🤧😂.

Tana cikin wanann tunanin ne Sabeehar ta shigo ajin direct gurin Zuhra ta nufa da tun shigowar ta ta lura yau cikin nishadi da farin ciki kawar nata ta tashi,saida ta isa sanann tayi clapping hands din ta gaban face din Zuhran sanann tace

"Hello!!!!Madam how far you wanann fara'ar ta mecece don Allah?Ko dai Habeebi yace zai turo ne in fara goge dancing shoes dina,Auran Besty na guda kin san ba za a gane kaina ba"ta kare  tana sakin kayatattciyar murmushi,janyo hannun ta Zuhra tayi tare da watsa ta kan seat din ta

"Taho Goofy angel Wlhy ke dai yarinya ce me sa'a ni da man na san Allah ba zai ba mu kunya ba"kallon rashin fahimta take bin Zuhran da shi don sam bata gane inda zancen tan nan ya dosa ba,ganin haka ne ya sanya Zuhra dafe goshi sanann ta nuna wa Sabeeha jaka flower da kuma chocolates din da aka turo sabida ita,a take kuwa face din ta ya canza annurin da ta shigo da shi ya gushe a take ta hada rai da mugun mamaki ta kalli Zuhra tace

"Goofy angel not again pls,yanzu sabida Allah wake playing games da innocent soul iri na?Who on earth is sending me this cards and flowers?"hannun ta Zuhra ta riko a hankali sanann tace

"Take it easy my love am very sure duk me turo abun nan bayi da wani mugun nufi game da ke,baki cutar da kowa ba Allah ba zai ba da damar a cutar da ke ba,so chill okay,daga gani son ki yake ya na kuma tsoron tunkaran ki face to face"tsaki Sabeehar ta ja sannan tace "Maganar banza tsoro na??!and a tunanin shi wanann abun da yake yi shine zai sanya na so shi?Zuhra kika ma san ko dan Adam ne"

"Ke dai Goofy angel Wlhy kin fiye tsoro da taurin kai,Wlhy mutum ne kuma son ki yake yi tun ram farko da muka karanta abun cikin card din nan na gano hakan,Wlhy daga gani tsoron rejection yake ya sanya ya kasa bayyana miki abun da ke ran shi,ni duk ba ma wanann ba na matsu Wlhy in san abubuwan da ke cikin jakar nan"ta kare tana washe baki

Hannun ta Sabeeha ta kwada sanann tace "Mahaukaciya ana ga yaki kina ga kura,ke baki da wata zance da magana sai ta soyayya ne?Zuhra anya Romeo ba great grandpa din ki bane kuwa"dariya Zuhra ta sheke da shi sanann tace "kya ji da shi Wlhy soyayya tayi a rayuwa don dai baki yi ne,ni dai ba wanann ba bude  mu ga abunda ke ciki,Wlhy duk jiki na sai rawa nake in san miye a ciki"

Tsaki Sabeeha ta ja saannn ta harari Zuhra "in kin matsu ba sai ki bude da hannun ki ke ki gani ba"Zuhra ta budi baki za ta yi magana ke nan Malamin da zai dauke su ya shigo dole tayi shiru duk suka nutsu suna sauraran karatu,haka dai ba su samu kan su ba,har sai guraran karfe 3,so suna fito wa direct Hotel suka nufa Sabeeha nata hararar Zuhra ita ko ko a jikin ta tattaro kayayayyakin tayi har suka isa kan gadon ta nan ko Zuhra ta baje tare da bude card din ta fara karato rubutun ciki kamar haka

   "
My mornings just aren't the same when I'm not waking up next to you. Hope your day is as lovely as you. Missing you this morning🥺🤧I'm always the happiest and feel the safest when I wake up right next to you,hope you will have a good day ahead
               From your secret Admirer"

Ta kare karantawa sanann ta kalli Sabeeha tace "Awnnn kawata yasin wannan Secret Admirer din naki Wlhy is extra super Romantic,Goofy angel wlhh ba karamin kashe ni red roses din nan ke yi ba smell them pls they are still fresh and smells nice"ta kare tana mika mata flower bouquet din,wani harara Sabeeha ta watsa mata sanann tace

"Zuhra daga ke har Secret Admirer din zan zage duk generation din ku,to hell with the Roses and cards wa ya damu,ni fa Wlhy bana son shi tun ban ma san shi ba,kawai asarar kudi ne be ishe shi ba"

"Ke dai Sabeeha Wlhy baki da hali tsakani da Allah tun baki san mutum ba ki ce baki so,Sabeeha wai haka za ki yi ta zama saboda Allah ko Umma baki tausaya wa ita ma Wlhy ko bata fada ba deep down bata da burin da ya wuce ta ga kin yi settling a gidan na ki mijin"baki Sabeeha ta tabe sanann tace "kan ki ake ji,haka kuka yi da Umman da zaki ce haka?"

"Koma tace mun ko kar tace mun Wlhy Sabeeha hankali na ba zai kwana ta ba sai na tabbatar kin yi aure"baki Sabeeha ta bude da mamaki sanann tace "iko sai Allah,to Mama Zuhratu sai kiyi maza ki nemo mun mijin ko"ta kare tana dage mata gira daya

"Miji kam na samo miki ooo,bayanar shi kawai muke jira a sha biki wlhy,don daga gani dan gayu ne biki na keece raini za muyi,don haka kwantar da hankalin ki kawai,for now lemme see me ke cikin jakar nan"ta kare tare da janyo jakar tana me bude wa,ita dai Sabeeha da idanu kawai take bin Zuhran domin sam bata ga ma amfanin yi mata magana ba,don sam ba fahimta take ba,idanun ta sun rufe so kawai take ta ga ta sanya ta fada soyayya.

  "Goofy Angellllllllllll!!!"Zuhra tayi shouting tana kallon Sabeehar,harara Sabeeha ta watsa mata "Wlhy Zuhra zan ci uban ki da irin kiran mahauka da kike yi mun,uwar me kike gani a jakar da kike ihun suna na?"zaro Abaya guda tayi wanda yake Onion color anyi manyan pattern ga uban stones a jiki,sanann tace "kin ga Goofy angel Wlhy tunda nake ban taba ganin Abaya me shegen kyau irin wanann ba,inalilhi Wlhy ba karamin aji yayi ba and Wlhy ba karamin kyau zai miki ba,ke Sabeeha kin san kudin kayan nan kuwa?A taya ma ya san ke mayyar Abayas ne?"ta kare tana jujuya rigar cike da farin ciki don ba karya ya burge ta.

Kallon kayan Sabeeha ta dan yi sanann ta kalli Zuhran "Goofy angel wai kina nufin shi secret admirer din ne ya turo harda Abaya?"

"Tsaya wasa ba Abaya ba fa Abayas don Wlhy guda biyu ne,Whatttt ke wlhy red din nan ya fi kyau!!na shige su Sabeeha kin ga wasu Perfume masu shegen kyau🥹"Ai da jin haka Sabeeha sai durkowa tayi daga kan gado tare da fauce jakar

"Ke mu ga ban gane me kike fada ba"ta kare tana bude jakar idanu ta zaro lokacin da idanun ta suka yi arba da dayar Abayar da turarukar bakin ta har na rawa gurin fadin

"Zuhra anya mutum ne kuwa a taya ya san ina son Abaya da kuma kalan da nake so?Zuhra ki ga turarukan nan Wlhy tunda nake ban taba ganin irin su ba har kayan fa,Wlhy daga gani masu tsada ne ko?"

"Ke matsa dallah in aka ce tsada ai daya ma ke nan Wlhy Sabeeha Abayar nan kwanaki da na gani a wani group 50k ake saida ta,na dau me arha ce ma ke nayi wa sha'awar ta na ji ya fi karfin arzikin Uba na ma ba nawa ba"

"Zuhra kika ce 50k?", "Wlhy kudin ta ke nan don yan Dubai da Egypt ne Ai kayan masu kyau ne wlhy kuma sun ci kudin su,kin san kuma me ya fi mun dadi?"kai Sabeeha ta girgiza alaman sai kin fada ,zama  Zuhran ta gyara sanann tace "Wlhy dadi na da Allah ke nan kin ga ina daga zaune abun yayi ba zai wuce ni ba,Wlhy duk uban da ya ganni da Abayan nan ya ji kamshin turarukan nan ya san babu raini a dau yar gidan uban wani ne"ta kare tana dariya,idanu Sabeeha ta watsa mata sanann tace "Ke ban fa fahimce ki ba"

Ai dariya Zuhra ta kwashe da shi sanann tace "yanzu za ki fahimce ni Goofy angel,kafin nan bari na yi wa wanann secret Admirer na mu adduan ubangiji ya karo masa budi gobe ma mu ga wasu da suka fi wanann kyau,akwati na ya kusa cika da Abayas"ta kare tana washe baki.

"Kin san Allah Zuhra ki fita ido na ki mun bayani yanda zan fahimta", "yo Sabeeha akwai wani bayani da zan miki ne,mutumin nan ba sanin shi kika yi ba hasalima zargin Aljani kike masa ba kuma karban abun hannun shi kike ba,ke kika ce da shi da abun hannun nasa duk su je baki da bukata,to kin ga Ai wanann da duk abunda zai kawo mallakin Zuhra ne tunda ba za mu iya maida masa ba,ni kam sai dai in ce God bless your beauty my darling"ta kare tana kokarin maida kayan jaka.

"In kin isa Zuhra Allah tsine mun,kuttt ji mun karfin hali barawo da sallama ", "ban gane karfin hali ba?Na ga abun nan ke fa kika fada da bakin ki,me za ki yi da kayan mutanan boye?Mu da ba mu tsoron su kya bari muyi amfani da su"ta kare tana danne dariyar ta,fauce jakar Sabeeha tayi,da sauri Zuhran ma ta fauta

"Allah Zuhra ki sakar mun jaka ta tunda na ga Ai ba taki bane"dariyar mamaki Zuhra ta kwashe da shi sanann tace "shegiya karamar mara kunya har ni za ki kalla ki ce wai ba nawa ba"baki Sabeehar ya murguda mata sannan tace "eh din na ga ni Ai Secret Admirer na ne ba Habeebi bane ya kawo"

"Eh ba shakka Sabeehatun Umma kin cika yar iska,to yasin bani bayar wa tunda Ai ba ni na matse bakin ki ba kika ce ba ki son kayan hannun shi"baki ta kuma murguda mata "Eh na ji amman Zuhraty banda Abaya ke ma kin san kauna ta da Abaya daban ne,yasin ko Aljani mutum ne ma ba Aljani ba kayan nan sanya su zan yi"ta kare tana dada fauce jakar.

Hannu Zuhra ta tafa da mamaki "Ah lalle Sabeeha baki da kunya,to Wlhy baki isa ba Ai maganar farko shi ake dauka aui magana da shi"haka dai suka yi ta jayaya a tsakanin su,don Zuhra da biyu take  dada ce wa lalle sai Sabeeha ta bar mata,saida aka kai ruwa rana sosai kafin Sabeeha ta yarda kan to su raba,a take kuwa ta dau Red tare da baiwa Zuhra Onion color din,ta bata turare wanann karan kam chocolates din raba wa suka yi into equal Zuhra sai hararan ta take don ta so ta sha na sha ta rakar wa Habeebi Saura in ya zo zance ta bashi.

        **********************

Da sauri Gate man din gidan Leemah IK ya wangale wa FIK gate,a parking load ya aje motar sanann duk su biyar suka bude a tare sanann suka fito,ba tare da  sun tsaya amsa gaisuwar Baba me gadi ba suka nufi main house din,a harabar kofar shiga suka hadu da dan babyn ta Rayyan  wanda ba zai wuci 2 years ba a duniya yana kan keken shi yana wasa,yaro ne me shegen wayo da kyau domin tun randa ta haife shi aka ce Faizan ya dauko,ba karamin shakuwa bane tsakanin FIK da Leemah ya sanya ya ke Jan yaran jiki tare da kaunar su,da isar su kuwa yaron ya hau tsalle yana mika wa FIK hannun don yaron ma sarai ya san shi,ai ganin haka ya sanya FIK daukan shi tare da rungume shi a kirjin shi "hello little me"shine abunda ya ce yana me shafa kwantattacen sumar gashin yaron,nan ko ya hau dariya yana tsalle a jikin shi,big parlor din ta suka shiga in da suka tarar tana zaune ta ci ado akan kujera tana parking gashin Baby Aafreedah,jin hayaniyar su ya sanya ta dago kai a take ta saki murmushi "ah wa nake gani kamar  yan Rocket gang"dan dariya duk suka saki sanann suka karaso cikin parlorn da sauri Aafreedah ta fada jikin shi tana "uncle!!"dariya yayi tare da bata hannun "high five baby angel"hannu ta mika mishi suka tafa sanann ta dalle cinyar sa.

"Charm charm din Mommy tunda ka zo sai ka taya ni karasa parking din gashin,ka gan mu nan tun dazu muke abu guda yarinya ayi kitso bata so,ga shi  gashin sai faman kadewa shi kadai yake yi"

"Hajiya Leemah ke fa ba zuwa gidan ki ba sa aikin ki ne yayi yawa"baki ta bude sanann tace "Beel ka ji mun abokin ka ko,shi kuma dan aikin samun ladan ne bayi so,saboda Allah yaushe ne ma kake zuwa gidan nan balle har na sanya ka aiki,yaran nan dai ka san yanda suke son ka ko ni bani ji suna so haka"dan dariya yayi sanann ya karbi ribbon din "ba dole yara su so ni ba duk sun je sun dauko fuska na"duk dariya suka yi sanann ta kira yar aikin ta tace su shiga da su ciki,saida suka shige sanann ta juyo suka dada gaisawa da su Beel da Akram sanann FIK ya taso ya dawo kusa da ita kan shi ya kwantar da kafadan ta,kan shi ta shafa sannnan tace

"Faiza zan Mommah me ya faru?"kai ya langwabar nan ta saki murmushi wato yau shagwabar ce ta motsa da kyar yace "Yunwa nake ji Soul sis and Allah akwai maganar da za muyi"kan shi ta zamar sanann tace "Ai daman daga ganin ka na san magana ce ta kawo ka hope ba matsala kuka dada samu da Daddy ba"

  "Ke dai a bamu abinci mu ci zan koro miki bayani"pointing dining table din ta tayi musu sannan tace "ga can abinci yanzu aka gama maza ki je ki ci in ka koshi sai muyi magana"duk tashi suka yi tare da nufan dining din,nan fa duk suka zage suka ci suka koshi aka sha juice sanann suka dawo parlor

"To tunda an ci an koshi a fara koro mun bayani don ni duk na matsu in ji me ya kawo yan Rocket gang baki daya gida na"ta kare tana yar dariya wanda har ya baiyana hakorin makkan da ke makale a bakin ta.

"Wlhy Adda Leemah kin ga dalilin zuwan mu nan,mutumin ne duk ya taso mu daga school ana tashi yace mu biyo nan"Beel yace yana hararar FIK.

Duk dan shiru suka yi sanann Leemah tace "Charm charm am all ears ooo"dan shiru yayi don rasa ta inda zai fara mata bayani kafin can yace "Soul sis I want this to be between me and you okay,bani son Mommah ta ji labarin nan"Hannun ta sanya a throat din ta sanann ta ciro ta mika mishi palm din ta tace "pinky promise ba zan fada mata ba"shima hannun ya daura a kan nata sannan ya rike a hankali yace "Soul sis so nake ki koya mun yanda ake sace zuciyar mace,you are a lady also so na san kin san duk wani tactics da ake bi ganin an shawo kan mace,so ina so ki bani su in details"

Baki ta bude da mamaki don sam bata yi tsammanin jin hakan daga bakin shi ba,ita duk tunanin ta wani abun can ya hado shi da Daddy yake neman shawara a gurin ta domin duk duniya bayan su Beel babu wanda yake sanar wa damuwar sa ko neman shawara da ta wuce ta,zama ta gyara sannan ta kalli su Beel

"Beel yaushe FIK ya fada soyayay bani da labari?And wanann wace yarinya ce haka yar gidan President ko yar governor ce ko yar minister?Ko kuma yar wace kasa ce shine ma ya kama ta in fara tambaya"dariya duk suka kwashe da shi

"Ku fita ido na Wlhy zan kore ku in kuka ce dariyar banzan nan za kuyi mun a nan gurin" , "aa soul sis duk be kai haka ba,yanzu dai ki ba mu shawara babe Akram ya yi yake son shawo kan ta,yarinyar tana da shegen taurin kai ne"

Da sauri Akram yace "Adda Leemah karya yake mun babu wata babe da nayi shine dai yayi babe da yake tsoron tunkaran ta"harara ya watsa wa Akram din

"Shege da dogon bakin ka in ce ka ji dadi yanzu?" "Aa FIK ai ba shi za ka zaga ba ni saka zaga tunda ba laifin shi bane,tunda har ka iya samun budurwa tana wahala ka ka kuma kasa sanar mun"ta kare tana hararan shi,dan baki ya turo sanann yace "ni dai ba haka bane Soul sis Wlhy ko na miki bayani ba gane wa  Zaki yi ba ni dai kawai ki bani shawara"da kyar suka shawo kan ta don fushi tayi wa tunda be fada mata da wuri ba,kafin suka samu ta huce,sanann ta gyara zama don fara koya wa dan uwan nata dabarun sace zuciyar budurwa........

  Kar a manta da Comment da Sharing sabida Allah🤧🥹Meemarh na godiya da kaunar da kuke mun Allah ya saka wa kowa da mafificin Alkhairi,ayi hakuri da typing errors tsaban saurin in turo muku ban ma tsaya yin Editing ba.

Continue Reading

You'll Also Like

18.4K 725 31
MAFIA STEP - SISTER OF BANGPINK
5.5K 83 8
Now you gotta ask yourself. What would it be like to find out that the people you love and would die for, turn out to be self centered assholes who w...
110K 2.6K 12
حسابي الوحيد واتباد 🩶 - حسابي انستا : renad2315
5.8K 341 5
"𝘿𝙤𝙣'𝙩 𝙩𝙤 𝙩𝙝𝙞𝙨 𝙥𝙡𝙯 , 𝙄 𝙖𝙢 𝙨𝙤𝙧𝙧𝙮" She cried but her 𝙨𝙩𝙚𝙥 𝙢𝙤𝙩𝙝𝙚𝙧 didn't show any mercy and beat her from 𝙄𝙧𝙤𝙣 𝙧𝙤𝙙...