💖💫RUDANI💖💫

By herjjorh

13.7K 3K 4.7K

ANWAAR, AAMEER, AAMEEN, AHMAD, TEEMERH, XEENERH, ASHPHERT ... More

💖💫RUDANI💖💫 1
💖💫RUDANI💖💫 2
💖💫RUDANI💖💫 3
💖💫RUDANI💖💫 4
💖💫RUDANI💖💫 5
💖💫RUDANI💖💫 6
💖💫RUDANI💖💫 7
💖💫RUDANI💖💫 8
💖💫RUDANI💖💫 9
💖💫RUDANI💖💫 10
💖💫RUDANI💖💫 11
💖💫RUDANI💖💫 12
💖💫RUDANI💖💫 13
💖💫RUDANI💖💫 14
💖💫RUDANI💖💫 15
💖💫RUDANI💖💫 16
💖💫RUDANI💖💫 17
💖💫RUDANI💖💫 18
💖💫RUDANI💖💫 19
💖💫RUDANI💖💫 20
💖💫RUDANI💖💫 21
💖💫RUDANI💖💫 22
💖💫RUDANI💖💫 23
💖💫RUDANI💖💫 24
💖💫RUDANI💖💫 25
💖💫RUDANI💖💫 26
💖💫RUDANI💖💫 27
💖💫RUDANI💖💫 28
💫💖RUDANI💖💫 29
💖💫RUDANI💖💫 30
💖💫RUDANI💖💫 31
💖💫RUDANI💖💫 32
💖💫RUDANI💖💫 33
💖💫RUDANI💖💫 34
💖💫RUDANI💖💫 35
💖💫RUDANI💖💫 36
💖💫RUDANI💖💫 37
💖💫RUDANI💖💫 38
💖💫RUDANI💖💫 39
💖💫RUDANI💖💫 40
💖💫RUDANI💖💫 41
💖💫RUDANI💖💫 42
💖💫RUDANI💖💫 43
💖💫RUDANI💖💫 44
💖💫RUDANI💖💫 45
💖💫RUDANI💖💫 46
💖💫RUDANI💖💫 47
💖💫RUDANI💖💫 48
💖💫RUDANI💖💫 49
💖💫RUDANI💖💫 50
💖💫RUDANI💖💫 51
💖💫RUDANI💖💫 52
💖💫RUDANI💖💫 53
💖💫RUDANI💖💫 54
💖💫RUDANI💖💫 55
💖💫RUDANI💖💫 56
💖💫RUDANI💖💫 57
💖💫RUDANI💖💫 58
💖💫RUDANI💖💫 59
💖💫RUDANI💖💫 60
💖💫RUDANI💖💫 61
💖💫RUDANI💖💫 62
💖💫RUDANI💖💫 63
💖💫RUDANI💖💫 64
💖💫RUDANI💖💫 65
💖💫RUDANI💖💫 66
💖💫RUDANI💖💫 67
💖💫RUDANI💖💫 68
💖💫RUDANI💖💫 69
💖💫RUDANI💖💫 70
💖💫RUDANI💖💫 71
💖💫RUDANI💖💫 72
💖💫RUDANI💖💫 74
💖💫RUDANI💖💫 75
💖💫RUDANI💖💫 76
💖💫RUDANI💖💫 77
💖💫RUDANI💖💫 78
💖💫RUDANI💖💫 79
💖💫RUDANI💖💫 80
💖💫RUDANI💖💫 81
💖💫RUDANI💖💫 82
💖💫RUDANI💖💫 83
💖💫RUDANI💖💫 84
💖💫RUDANI💖💫 85
💖💫RUDANI💖💫 86
💖💫RUDANI💖💫 87
💖💫RUDANI💖💫 88
💖💫RUDANI💖💫 89
💖💫RUDANI💖💫 90
💖💫RUDANI💖💫 91
💖💫RUDANI💖💫 92
💖💫RUDANI💖💫 93
💖💫RUDANI💖💫 94
💖💫RUDANI💖💫 95
💖💫RUDANI💖💫 96
💖💫RUDANI💖💫 97
💖💫RUDANI💖💫 98
💖💫RUDANI💖💫 99
💖💫RUDANI💖💫 100

💖💫RUDANI💖💫73

65 24 55
By herjjorh


"And for what reason zakace ba zanje duba Aameer ba? Anwaar am sorry to say but I can't abide by your rules anymore" Ilhaam ta fada dan kullum tace zata sai yace Aa kuma ba reason, ita ta zata duk wannan ya wuce "Toh shikenan tunda ke kikeda iko da kanki sai kije ae" yana fadin haka ya dau key zai fita saidai kafin ya kaiga kofa Ilhaam ta taresa, kallonta yayi ganin er abun da ta tsaya daga masa hankali tun dazu "Kafin muyi aure bamu yi akan zaka na samun rules anyhow ba, ba haka ake mun ah gida ba" ta fada saidai koh da wasa bata bari sun hada ido ba "Move out of my way, don't cross me" ya fada in a serious tone ignoring what she said, matsawan kuma tayi fa, tana gani ya wuce bakin ciki kaman ya kasheta, da sauri tayi wajen wayanta, dauka tayi dailing number'n Yaa Ateekah, Yaa Ateekah na dauka Ilhaam ta fashe da kuka "Ilhaam lafiya dai ina?" Yaa Atee ta fara tambaya jin Ilhaam na kuka "Yaa Atee ya hanani zuwa duba jikin Aameer, kuma nasan shi dole zaije. Tunda Aameer ya koma gida Anwaar ya hana, Yaa Ateekah Anwaar is overprotective and am not a child please, Aameer is married so I am" tace "Ilhaam toh kiyi haquri mana zuwa gobe in Allah ya nuna mana ki gani in bai barki ba sai ki fada mun, I will try my best" Ilhaam harda girgiza kai "Yaa Atee nasan bazai bari bafa dan bakiga yanda yake wani bata rai bane tun jiya fa" tace "Toh dole sai akwae abunda kika masa" sake kad'an kan tayi "Ae kema dai kinsan ba abunda zan masa, Yaa Atee kawae dai jin kai ya motsa masa ne" dan murmushi Yaa Atee tayi "Toh kema tunda kinsan halinsa ae da sauki, yanzu dai kiyi haquri zuwa goben", "Allah ya kaimu, I'm hanging" da haka ta kashe wayan. Ta bangaren Anwaar kuwa bayan yabar gidan Ilhaam na Teemerh ya wuce dan tabbatar da bata sake kai Fadel wani wajen ba, he can't keep welcoming that stupid act of hers, taya za'ayi ta haifi yaron tace ita ta gaji, wai saidai ya nemo mai kulawa da Fadel tunda Munnirah ba zama take ba tana schl, ita ae koh a gidan su bata kulawa da yaro "Ina Fadel?" Tace "Bacci yake" ta amsa da sauri "Allah bacci yake, naji abunda kace ae" ta fada ganin kaman bawae ya yarda da maganan ta bane, jin yayi shiru tace "Wae Ashphert zata zo anjima ta dauke sa amma" kallonta yayi baice komai ba, shi fa baisan yawo but he can't say no to Ash, sure this will be the last time In Shaa Allah" dan shiru ne ya biyo baya kafin yace "Ban coffee" Teemerh was shocked and surprised at the same time, niyyan tambaya tayi amma ganin kallon da yake mata yasa tayi kitchen "Fatima am getting late" tace  "Sorry Babe gashi" ta fada tana basa, yana karba ta jawo wayanta tana cire musu pictures, kallonta yayi baice komai ba, yasan koh yayi ba bari zatayi ba dan bajin magana take ba, sai daga karshe yace ta bari haka, ita kuwa arai cewa tayi koba komai ta samu abunda takeso.
•••••

"Aameer you're hurting me" Ashphert ta fada hawaye daya na bin daya saidai ko da wasa Aameer bey dago ya kalleta ba kuma bai bar abunda yakeyi ba "Aameer you are bleeding dan Allah ka bari some other days sai kayi, ciwon ah jikinka yake amma nike jin zafin abun" shi wai akan meyasa zai bar exercise saboda wasu injuries da suke kan warke wa, bey kula ta ba saida yaga kukan nata na kara tsananta kafin ya sauka akan Vibro gym machine in ya dau towel yasa akan sa da sauri tayi hugging nasa. "I love you Aameer", "And I love you more" ya amsa mata tare da zagaye hanunsa ah bayanta "Shine nace ka bari kuma kaki ka bari?" Ta fada ah shagwabe "Toh saboda wannan minor injuries in sai nabar shiga gym, that is impossible Ash" Ya fada tare da kama hanunta suka fita daga gym in "Wannan kake kira minor injury?" Tasa hanunta kan hanunsa da yake bleeding "Ka gani fa" nan ta jashi ya zauna, dauko first aid kit tayi sannan ta cire wancan ta fara masa sabon dressing da bandage "Kice I'm living with a Doctor da kanta, kiga yanda yayi kyau" Dan murmushi tayi tare da sa kanta akan kirjinsa tace "Anything for my Sweetheart" sai jin doorbell yayi kara sukayi. Ashphert ce ta tashi ta bude sannan ta koma ta kara kanenaye mijinta, sallama yayi ya shiga, yana daga ido yaga Ashphert ah jikin Aameer kaman za'a kwace mata shi, dan karamin tsaki yayi "Ke kinada hankali kuwa? At least ki bari ya gama jin sauki mana" ya fada tare da zama akan daya daga cikin kujerun dake dakin, kallonsa tayi ganin yanda yake hade rai shi kadai, ita bata iyawa da halin Anwaar "Toh dan Allah Anwaar yanda kake magana kaman wani ba mijina ba?" Ta fada kasa-kasa wanda Aameer kadai yaji "Doctor ka iso?" Aameer yayi interrupting maganansu "Yeah, how're you feeling?" Yace "Da sauki Alhamdulillah".... "Ina Ilhaam?" Ashphert tayi saurin tambaya "Daga clinic nake" Anwaar ya bata amsa ah takaice sannan ya tashi zuwa wajen Aameer "Ashphert zaki dan iya bamu waje? Inason magana da Aameer" ba musu Ashphert ta tashi sannan Anwaar ya fara "Barrister I'm very sure Ahmad is behind all this tunda Ilhaam ta dage akai, I trust that girl so much amman bamuda evidence" murmushi Aameer yayi kawae jin yanda Anwaar yayi maganan "Doctor, yanzu bamu da daman filling case akansa saboda bamuda wani evidence as you said" yace "Hakane but Ilhaam, she is in pain" shiru Aameer yayi kaman mey tunani "I can understand how you are feeling, but law is beyond our thinking, Ilhaam tana tsoro ne kawae saboda Ahmad ya saba sending threats, take a good care of her saboda attacks nata, she has some panicks right?" Gyad'a kai Anwaar yayi "Tanaso tazo but I said No" kallon sa kawae Aameer yayi dan yasan Ilhaam tazo sai ta fara daga masa hankali kan Ahmad tukunna, and that's the main reason da Anwaar ya hanata zuwa, ah hankali suke bin komai "Yaushe zan koma aiki?" Ya tambayi important something nasa "Yanzu dai zan kara ma zuwa next week kafin jikin ya kara karfi sai ka fara fita, kaga yanzu injuries in basu gama warkewa ba" daukan waya yayi dailing numbern Ashphert sai gata ta sauko "Nasan kina kula dashi, amma ki kara kinji?" Anwaar ya umarce ta "Hakane Anwaar ina iya kokari na amma dazu Gym Aameer ya shiga and I told him not to" ta fada masa gaskiya "Gym?" Anwaar ya maimata "Barrister meyasa kake haka kaman baka damu da health naka ba?" Kanasan maida mana komai baya" ya fada fuska ba yabo ba fallasa "Naji zan kiyaye" kadai Aameer yace tare da tashi yana dingisa kafa yabar musu wajen, nan Anwaar yayi sallama wa Ashphert shima ya wuce.

9:53 pm

Ilhaam ce zaune da waya kawae taga post in Teemerh sai comments akeyi ana admiring nasu, hawaye ne ya cika idonta tamm dan ita harga Allah bata so taga kowa kusa da Anwaar in ba ita ba, jefar da wayan tayi ta tashi tana buga kafa kaman ance ta dawo kuma ta dau wayan tayi dailing number'n Auntie Aisha, ringing biyu ta daga "Ilhaam kina Lfy?", "Ae ba lafiya ba Auntie, kina ganin wannan yarinyan ta dage saita kwace mun miji saboda taga ta haifa masa yaro, imagine Auntie yau ah gida na yake amma koh breakfast yaki yi saida yaje gidanta fa kafin yayi, wannan wani irin cin mutunci" ta fara masifan da baida asali "Ilhaam ke waye yace miki ah gidanta yayi breakfast?" Tace "Gani nayi tayi posting" Aunty Aisha tace "Ilhaam I'm very sure tasa ne dan ki gani kuma gashi kin gani har ranki ya baci" tace "Whatever Auntie, I knw am at fault amma Anwaar baiyi komai daidai ba" tace "Ilhaam are you sure kinyi breakfast baici ba?" Shiru Ilhaam tayi dan ita ba abunda tayi bacci tayi abunta, ae bata tashi da wuri bane shiyasa "Ban tashi da wuri ba ae" tayi saurin defending kanta "Kinyi laifi accept and apologize "I will apologize amma-" saurin katse ta tayi "Ilhaam calm down, ki tambayesa gobe kizo ki sameni akwae maganan da zamuyi kinji?" Dan shiru tayi tuna yau ma an hanata fita "Allah yasa ya bari toh" tace "Amin" da haka sukayi sallama. Zama tayi tana jiran Anwaar yazo kawae ta basa haquri yabar fushi da ita, tasan yau batada gaskiya and she's ready to apologize, zaman ta cigaba dayi har bacci ya dauketa Anwaar bai dawo ba, shiko bai dawo ba sai 1:08 am, Anwaar and being late. Kamshin da akullum yakeso shi ya fara masa sallama, ay kuwa yanda yayi zato tana wajen saida ya karasa yaga bacci take, duba wristwatch in hanunsa yayi nan yaga dare fa yayi "Holy crap" ya furta dan yasan jiransa ta tsaya yi, daukanta yayi be ajiyeta koh ina ba sai dakinta, yana ajiyeta ta farka, zai juya tayi saurin rike hanunsa tana kokarin tashi "Shhhh go back to sleep, ba sai kin tashi ba" ya fada in a low pitch "Kaci abinci?" Ta fada da muryan bacci sannan ta tashi ta zauna tare da sake masa hanu tana squeezing eyes nata, ware ido yayi, shi cin abinci cikin daren nan? "I'm sated" yana fada ya juya, zai tafi ta sake rike hanunsa "I am sorry I erred, bazan sake ba" ta fada kaman mey shiri kuka "I know you are very sorry but I need to sleep right now" tace "Are you still mad at me?" Girgiza kai yayi "I am not, you know I love you" murmushi tayi ta sake masa hanun "Sleep sound" ya fada kafin ya fita. Shi fa ya zata Ilhaam tayi bacci, amma yana komawa dakin yaji ana shekan kuka, lights ya kunna yaga tana zaune kan abun sallah tana kuka, da sauri ta fara share hawayen ganin haske, ah hankali ya karasa ya zauna kusa da ita, it's her daily thing kuka da dare, yana bata haquri kullum in tayi amma taki bari yasa kawae da ta fara yake zama kusa da ita comforting her with all that he has "I want to give birth to Twins, Triplets, Quadruplets, Quintuplets, Sextuplets, Septuplets, Octuplets, Nonuple-" kafin ta karasa yayi saurin hugging nata "I love you so much, with or without the kids" ya fada dan yaga wannan batasan haihuwa da wuya bama, duk lissafin ta ba yaro daya, mey saukin kenan twins "I knw you do, but I want and love the kids also Anwaar" sai kuma ta sake sabon kuka, rarrashin ta ya cigaba da yi "I know it's hard Ilhaam, amma sai mu cigaba da addu'a and am very sure Allah bai manta damu ba" ya fada yana share mata hawayen ganin ta nutsu "Have you taken your medications?" Girgiza kai tayi a hankali "Make sure to always take them on time Ilhaam" he warned "And for the fertility issue, meet me at the hospital tomorrow please" shiru ta masa kawae dan ba musu zata masa ba amma wlh bazata ba "Okay now sleep and have some rest, it's already late" ya fada tare da dagata "I am not sleepy Anwaar, I can't sleep but you can if you want to" ta fada bayan ya ajiye ta kan gadon "My girl can't sleep then how can I?" Tace "Anwaar you have to, you have work tomorrow" ta fahimtar dashi "But I love you more, we can talk about some of our problems since we all can't sleep" tace "I failed you Anwaar, I know how you love babies but I can't even give birth to one" ta fada tana daurewa karta sake kuka amma ta kasa, tasan Anwaar nasan yara amma ita koh daya batada, Teemerh nada daya amma haryanzu itama shiru bana biyu "I don't love the babies Ilhaam, I love you. I can't see you always crying and forcing yourself to sleep. I can and promise to live with you in every situation, you are through enough but not anymore. I know you agreed to marry me not fully sure of what will come your ways, I am trying to always make you happy, I know that am sometimes harsh but that's in me and I can't change it. But believe me, I love you beyond words" share hawayen ya cigaba dayi mata "I know you do Anwaar, amma yanzu ba shine damuwa na ba" kallonta yayi yanaso yayi guessing damuwan nata "Say it out" ya fada ganin ya kasa gane miye "I am having an untying relationship with Ummi, it hurts Anwaar she is my Mum. It was her dream to get us married but she is against it now, she wants me out of your life which I know" shiru yayi dan ya rasa mey zai ce, shi kansa Ummi bata wani kulasa, amma zaiyi wa Malam Abdallah magana yasan in ya mata zataji tunda tana jin nasa, shikenan Ummi zata dena and Ilhaam will be happy again "Don't worry Ilhaam, our family is happy seeing us together. We are us to forever In Shaa Allah" tace "No one is happy in my family Anwaar, no one among them know my past, what will happen when they get to know that I got married after losing my pride? After carrying someone's illegitimate child? What will happen if they know that someone is Aameer?" Shiru ya mata kawae danshi kansa baida amsan abunda zai faru, sun ci amanan kowa wajen boye gaskiya "Can you please stop calling our child illegitimate? I dislike this humor of yours Ilhaam" pouting mouth ta fara "It is coming back to haunt me those days" tana fada ya kalleta, this can't be, murmushi tayi ta tashi kafin ta fara jin batasan zuwa wajen Aameer, ture lamp in dake kan night stand tayi bata sani ba ya fadi kan kafan ta "Ouch" tayi saurin matsawa Anwaar ya rike ta "Does it hurt? Ya tambaya yana duba kafan duk ya damu, dariya ma ta fara ganin yanda ya damu, eh ya mata zafin lokacin daya fadi amma bai ji mata ciwo bafa "Anwaar it fell on me, amma kai kakejin zafin?" Ta sunkunyar dakai tana kallon fuskan sa "Kede tunda baki ji ciwo ba shknn, don't try teasing me-" shiru duk sukayi jin wayan Ilhaam yana ringing, da sauri ta duba sai ganin Xeenerh "Nooooo, Xee is mad, she forgot the time differences" tana fada tayi declining Anwaar na kallon ikon Allah, kwana biyu banda masifa ba abunda ta iya, tunda ba bacci take ba ae sai tayi picking taji mey Xeenerh zatace "Am not answering and you know that, so what's the look for? Ni bacci ma zanyi" tana fada ta juya zata kwanta Anwaar ya rike ta "Asubah ya kusa, kikayi bacci yanzu ba iya tashi zakiyi ba" calculating baccin da zata samu ta fara da fingers nata "Tabb, ana zaman lafiya, kuma 7 kace mun zaka clinic? Ae bazai yiyu ba" ta sake juyawa Anwaar ya sake riketa "Don't worry I will make the breakfast and the the necessary things Angelic" yayi assuring nata "You sure?" Yace "Yes, very sure" tabe baki tayi "Someone is trying to be romantic" ware ido yayi ya girgiza kai "Daga taimako?" Ya tambaya "Anwaar all this aside, make sure to do everything the way am doing, I know you can cook but you can't take good care of the house" yace "Okay I promise" murmushi tayi ganin yanda yau yake behaving simply "I love you so much Anwaar, my forever is with you In Shaa Allah" he smiled back saying "I love you more" batayi bacci ba kaman yanda yace saida ta jira asuba, tayi sallah and everything harda adkhar dan yanzu tana kokari kafin ta kwanta, ita Allah ne yasan kalan baccin da zatayi ae.

*~*~*

Aunty Sham na zaune tana kuka, ita haka rayuwa zaiyi da ita? Ae kuwa bazai yiyu ba "Shamsiyya bafa kuka zakiyi ba, ya sake ki kuma har nan yazo yana kuka yace ya maida ki basai ki koma komai ya wuce ba?" Dama fa ita bakin cikin saki dayan da aka mata take "Yaya, shekara da shekaru muna tare da mutumin nan yanzu akan wata yamun har saki daya, toh ae kuwa nayi maganin ta sauran shi" tana fada Habeey ta kalleta, Teemerh na gefe jin yanda auren su ya kare dama ta fara tunanin nata, Aunty Sham mijinta ya maidata amma Yaa Xee anki ah maidata tukunna, ita yanzu so takeyi a zauna lafiya ma koh zatayi farin ciki dan Allah ta kasa ganewa Anwaar, he is nice today tomorrow harsh, ita dai yanzu zatayi risking suyi taking plan in karshe da Ahmad kafin nan tasan Anwaar will hate Ilhaam so much, in ya rabu da Ilhaam ita kuma saita basa haqurin duk laifin data masa su zauna lafiya, ita a duniya Ilhaam ne batasan gani tareda Anwaar, barin ma inta tuna yanda yakesan Ilhaam kawae sai taji wani bakin cikin da she can't say ga daga yanda ya fito "Zamu Lagos, sai ku fara shiri dan bazan lamunci rashin nasara ba" Mummy ta fada, kallon juna Teemerh da Habeey sukayi kafin Teemerh ta girgiza kai tana kallon Aunty Sham sanin wannan shawaran tane, ita ta gaji, kawae abarta ta zauna da Anwaar da Ilhaam tunda gidan su ba daya ba, ae in ba ta fada bama ba wanda zai ce tanada kishiya tunda Anwaar is not like Aameer komai private yakeyi, kawae dai ita zata haqura "Mummy a haqura" kallon mamaki suka bita dashi "Mummy wlh Anwaar bazai saketa ba, kuma mun rabata da komai da kowa kuma, har asiri muka mata kar ta haihu, an karya asirin jikinta dai amma gashi haryanzu batada ciki" Aunty Sham dake cikin kunci tayi saurin gama share hawayen tace "Kin gama? Kin gama dan ubanki?" Bata rai tayi "Aunty, inda aikin bokan nan yana aiki wlh da ba'a sake ki ba" sa hanu Mummy tayi akai "Shknn ta zageki, Fatima uwar naki kika zaga?" Ta tambaya tana bin Shamsiyya da kallo "Toh da aka sakeni kinga ban koma bane? Koh ita Xee wlh saita koma" ta fada tana huci "Ke Habeebah miye damuwan ki?" Mummy ta tambaya ganin itama tayi shiru "I want to marry Ammar, kuma in Mama ta cigaba da wannan halin Allah bazasu bari ya aureni ba, ae na fada masa dagaske muna zuwan wajen boka yace toh mu bari-" dauketa da mari Xee tayi "Shashashan banza da wofi, har namiji zaki budewa sirri, toh wlh bazai tab'a aurenki ba tunda shi ba jaki bane" nan fa su Mum suka farawa Xee godiya "Yanzu zakije ne koh Aa? Nayi muku alqawarin duk wanda yake cikin kunci cikin ku wannan karan sai ya fita cikin sa, ke Zainab zaki koma gidan mijin ki, ke kuma Fatima wlh mijin ki sai ya saki dayar matan sa, Habeebah ke kuma nasa auren ki a sati biyu" saurin kallonta duk sukayi "Yo toh kinada uwa kaman ni auren ki zai wani gagara ne, koh ce ma shi Ammar in kikayi bokan ne ma uwarki sai ya aure ki. Dama wasu en kudi ne sukayi mun kadan kwana biyu amma yanzu banida matsala" Habeey tace "Mama, kin tabbata in munje Ammar zai aureni?" Sake baki Teemerh tayi tana kallonta, ranan fa ta kirata tace ta koma islamiya tabar bin boka, lalle duk wanda yake tare da Aunty Sham toh saita gane shima zai gane, tsaki Aunty Sham tayi "Ke ae baki yarda da uwar ki ba sai da wani banza wai shi Ammar. Da ubanki ya sakeni baki ga har nan yazo yana kuka ba? Waye zai sa uban ki kuka in ba niba?" Shiru tayi dan yanzu kam ta yarda "Amma Mama kar a cutar da Ammar fa" murmushi Mummy tayi gane wannan yarinyan soyyayyah zai kaita ya barota "Aunty nima na yarda zan biki" Xee ta amsa dan so take ta gyara tsakanin ta da Daddy, yanzu koh ta kira bayi dauka abun sa, danshi yace bai haifi yarinyan da zata kunya tasa ba tukun, ae yaji labari Zainab ita ta nemi saki da kanta ta zata mijin nata bazai saketa ba sai gashi ya mata ganganci "Ke kuma fa? A wani ayar muka baroki?" Ta tambayi Teemerh da tayi shiru dan ita tsoro take "Aunty kun san dai nafi kowa san Anwaar ya saki Ilhaam koh? Toh yanzu na fara tsoro ne kaman bazan yi nasara ba. Amma indai kin tabbatar shikenan I've no excuse but to trust you" ta fada biting her finger "Ae ke ganau ce, ke barin fada miki gaskiya wannan mutumi ba Allah a ransa, shida matan sa suke aikin fa, kinga mugaye biyu sun hadu ae ba zaman lafiya, ita wannan matan nasa tanada aljanu kasan dubu biyar" Teemerh tace "Toh shknn, amma Mummy sai ki kira Anwaar a fada masa karya da gaskiya yanda zai bari naje" Aunty Sham ce ta amsa tun kafin Mummy ta amsa "Wawiya duk ke kika gwada masa yanda zai juya ki ta koh wani hanya ae, ji yanda kike magana da rawan jiki?" Teemerh hummed "Toh ae yanzu ba'a samu kan Anwaar ba tukunna Shamsiyya, kar tayi masa wani shirmen ya saketa dan mutuncin ubanta yake gani ba nawa ba" Shamsiyya tace "Toh ae yazo karshe, banyi alqawarin sa boka ya shiryar miki da Anwaar ba, Ilhaam kadai zan sa ya saka. In kinga dama kisa ya soki sosai, kin ga dama kuma in ta fita tabar miki gidan kema kiyi ta shirme har ya dawo da ita" girgiza kai Teemerh tayi "Nagode da wannan ma Aunty, indai ya saki Ilhaam bazata dawo ba dan zanyi kokari ya manta da ya taba san wata wae Ilhaam" murmushi Aunty Sham tayi ganin duk tayi convincing nasu "Toh yanzu nawa zan tura miki Aunty?" Teemerh ta tambaya dan ta gama yarda da Aunty Sham "Yanzu dai Fatima bari tukunna dan wannan bokan aikinsa da akwae hatsari" saurin kallonta duk sukayi "Eh akwae hatsari better na fada miki tun wuri kafin muje wajensa yace ga abunda zakiyi kice Aa, bayida imani dawo da abun kanki zaiyi" shiru Teemerh tayi dan yanzu ba abunda bazatayi ba "Aunty, wlh yanzu ba wani abunda bazanyi ba indai Anwaar zai saki Ilhaam. Ayi komai kawae dai ah samu ya saketa, sai nasa ya manta da ya taba san wata wae Ilhaam ah duniya" Aunty Sham tace "Yawwa, ku nutsu dukkan ku kuyi abunda ya bayar, karku sab'awa umarnin sa danshi aikin sa in asiri ya tashi tonuwa bayi fadi a kasa haka nan, kan mu zai dawo" Habeey tace "Mama, ki kwantar da hankalin ki indai Ammar ya aureni zanyi kokarin masa biyayya yanda koh laifi bazan masa ba balle wani abun ya faru" ita fa ran Aunty Sham ya baci, erta ne zata zauna namiji ya juya ta "Kiyi iya abunda zaki iya masa sauran ki barmun komai, ni bance kiyi masa biyayya over ba. Wawiya kawae" shiru tayi dan ita kanta yanzu tasan ta dawo wawiya "Kiyi haquri Shamsiyya, nasan baza'a samu matsala ba" Mummy ta bata haquri ganin ranta ya baci "Shknn da fatan Zainab naji na" ta tambaya ganin kaman Xee na tunani "Eh ina jinki Aunty, kawae tunani nake in abun bai tafi dai-dai ba" wani shu'umin murmushi tayi "Nasan duk kin fisu hankali ba abun da zaiyi matsala da yardan Allah" gyada kai tayi dan ita tasan dole ma ta koma gidan Mahmoud dan wannan karon Aunty Sham batazo da sauki ba, Mummy najin wayan ta ya fara ringing ta daga ta fita da sauri duk suka bita da kallo, sun san very important call ne tunda ta tashi cikin su "Mama zamu koma yau ba?" Sadeeq daya shigo ya fada, bata rai duk sukayi dan sun lura Sadeeq bai wani san zuwa wajen su "Kai in zaka ae sai ka dawo, ni yanzu haka sai na sake sati biyu na gwada wa uban ka na isa" ta fada tare da juya kai, kafada ya daga kafin ya wuce, shiyasa baisan zuwa Abuja dan bayisan ganin su Teemerh nan, shi kap duniya da Mallah yake shiri dan koh Habeey sai ya mugun kamawa suke magana, wai ita da take blood sister nashi kenan ma balle su Teemerh da they are just cousins "Aunty yaushe ne tafiyan?" Teemerh ta tambaya ganin Sadeeq ya wuce "Ae bari Yaya tazo yau mu dau hanya ma, kar ki damu da mota za'ayi tafiyan saboda ayi saving kudi dan kuwa ba kudin wasa mutumin yake karba ba" shiru tayi dan haka kawae take jin hankalin ta bai kwanta wa tafiyan ba "Allah ya kaimu" Xee ta amsa kafin Habeey da Teemerh suka tashi zuwa daki "Ke ba kince mun Islamiyya kika koma ba?" Ta tambaya sounding confused "Kinki ki fahimci abunda nakeso ki fahimta ae" sake kallonta Teemerh tayi "I love Ammar, ke kuma bakison Anwaar, you just envy his love" kallon mamaki yanzu Teemerh ta fara mata, har itane za'a ce batasan Anwaar? "What do you mean bani san Anwaar? You know I do" tayi saurin amsawa "Baki sanshi Fatima" Habeey ta daka mata tsawa and for the first time tace Fatima "In kana san mutum ae baka cutar dashi, so kakeyi yayi farinciki. Na yarda na taimaka miki ada saboda nima bansan abunda nakeyi ba, but after meeting Ammar na gane duk kuskure mukayi" bata rai Teemerh tayi "Yaushe na tab'a cutar da Anwaar? Abun naki harda sharri? Ae wlh Ammar bai barki haka nan ba" ta fada still da mamaki fa "Baki cutar dashi ba amma kin cutar da Ilhaam and he loves her so much kuma kinsan in bata farin ciki shima bayi yi toh akan mey zaki samu farin ciki bayan da kanki kika b'ata komai? I am not backing Ilhaam saboda na tsane ta, you know how very much I despise that girl amma hakan bashi zai sa mijinta ya tsaneta saboda munayi ba" tabe baki Teemerh tayi "Yanzu dai so kike na farawa Ilhaam biyayya?" Hararanta Habeey tayi "Ae bata kai ba" Habeey ta fada sai kuma taja tsaki "Ke duk mazan duniya ma ki rasa wa zaki so sai wancan mey shegen jiji dakai, ke nifa Allah shi Anwaar in ma na tsane sa" bata rai Teemerh tayi "Toh karya nayi? Bayida girman kan ne? Ganshi ranan on behalf interview da yayi attending mana, duk attitudes in da Aameer chan yake basu wannan shedanin mijin naki yayi x2 ga wancan shedaniyan Yesmin mey sake zuga sa, an tambayin dalilin da yasa yayi choosing private life ta chapke kaman ita aka tambaya haka ba'a bada answer ba. Wae who's she to him?" Teemerh tace "Ilhaam told me that Yesmin was his ex" ware ido Habeey tayi "Wae daman kuna magana?" Tsaki Teemerh tayi tana yatsina fuska "Ce miki akayi gaba muke ne? We are not opponents for the geez sake Habeey har tadi ina yi da Ilhaam in ya kama" dariya Habeey ta fara "You are not opponents keda Ilhaam? Ta sake maimaita mata dai "Tee, you and Ilhaam are opponents kuma dole a fada" Teemerh tace "Tasan Anwaar bazai sakeni ba yasa tun wuri ta kwantar da hankali, she just have different moods, yanzu za'a fara abun kirki da ita toh gobe baza'a yi ba. Har kirana takeyi wae zata ga Fadel" tabe baki Habeey tayi "Eh ae ta fiki san Anwaar yasa take haka" sosai fa yanzu ran Teemerh ya baci, gane hakan Habeey tace "Eh mana Tee, san da take ma Anwaar yasa ta kesan Fadeel kaman ita ta haifa, Fadel happens to be Anwaar's son for a reason. Inda ace Fadel yaron Ilhaam ne wlh Teemerh baza ki nuna kina so ba, na sanki kuma nasan halayen ki" hawayen da Teemerh ke boyewa ne ya sauko, tun dazu Habeey ke fada mata maganganu amma ae duk gaskiya ne "Shhhh, don't cry Teee" girgiza kai tayi Habeey ta jawota zata share mata hawayen ta kwace kanta "Yanzu ae bani nace wa Aunty inaso Anwaar ya saki Ilhaam ba" ta fada hawayen na cigaba da sauka "Kin tabbata bakiso ya sake ta?" Girgiza kai tayi "Inaso ya saketa Beey, amma nasan bazai saketa ba shiyasa na fara tunanin haqura, but after Aunty's assurance na yarda da duk abunda zai biyo baya yanzu" daga kafada Habeebah tayi irin koh a jikinta "Koh da hukuncin daga wajen Anwaar zaizo?" Saurin kallonta Teemerh tayi tabar sharen hawayen data fara "I love Anwaar, I gave him happiness and that is Fadel. Anwaar loves his son so much and he loves me too, I am the one messing up things. Kina tunanin Anwaar zai iya mun hukunci? Nayi imani da cewan koh mey nayi Anwaar bazai mun komai ba" kallonta Habeebah ta cigaba dayi "I like your confidence and I trust you. I am with you through this Teemerh, dole ma Ilhaam tabar miki gidan naki. Islamiya kuma na ajiye sa gefe yanzu sai bayan auren mu da Ammar zan koma" ta fada cikin farinciki dan tunda taga Abba ya saki Aunty Sham kuma yazo har nan yana kuka zai maidata gabadaya Aunty Sham ta jawota ta maida chan, dama chan addinin ba shiganta sosai yayi ba "Keee Ammar ke kirana" ta fada da murna da tau wayan, irin san da Ammar ke mata ne Yaa Xee zata ce wae ba auren ta zaiyi ba tunda tace suna bin malamai, wlh tsaf aurenta zaiyi dama chan dangin sane masu bakin hali. Zama tayi tana tunani kala-kala tana jin yanda Beey ke wani kanenaye murya, jin anyi knocking ta maida hankali kofa, Sadeeq ne ya shigo fuska ba yabo ba fallasa "Yaa Anwaar yazo, Mummy tace kije" ware ido tayi kar dai da gaske sun dage sai anyi tafiyan nan yau, hararan ta Sadeeq yayi ya fita "Maras kunyan banza" Habeey dake waya ta amsa wa Teemerh saidai Sadeeq bai jita ba. Jiki a sanyaye Teemerh ta tashi zata fita tana jin yanda Habeey ta soma narrating dalilin kiran Sadeeq maras kunya da tayi wa Ammar, ita fa ba abunda take boye masa, humming Teemerh tayi ta fice.



This Aunty Sham🙄

*~*
It's a long page...😇

RDN!

Continue Reading

You'll Also Like

347 53 12
An arrogant rich guy kidnapped a crazy innocent girl for a certain benefit. Read to find out what happens with Arfan and Fareeda
16.1K 3K 48
~Last BOOK IN THE DESIRE SERIES ~ #1 in Arewa on 4-august-2022
447 134 90
In the name of Allah, The Most Beneficient, The Most Merciful. Here, we will discuss the number of times Allah has directly referred to the Believers...
30.4K 4.4K 39
Nowadays,marriages fail to work due to circumstances that led to it or what the marriage was based on. In most cases,it is said to be that girls are...