A SIMPLE DARE (WASA DA SO)

By marteybee

496 8 16

More

new book
Page 2
Page 3
Page 4
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page ten
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20/21
Page22/23
Page 24/25

Page 5

13 0 0
By marteybee

✨✨
A
                     SIMPLE

                                         DARE

✨✨

                       (WASA DA SO)

                WRITTEN AND STORY
                 BY
                  NERNAH MARYAM
                (MEEMARH)


Kofa a bude take ga duk me son yin joining group dina😌,Amman Hajiya don Allah in kin san ba yin comment ko karanta littafi na zai kawo ki ba I beg you in the name of Allah kiyi zaman ki ba sai kin shigo ba!!haka zalika wanann group din na mata ne zalla don Allah Maza should stay away from my group👏

My What's app group link👇🏻

https://chat.whatsapp.com/EUrVVaKJnIBDTlQsxurZv0

           Bismillahi Rahmanin Raheem............

      ( In the name of Allah the most beneficient,the most merciful)


Kofa a bude ta ke ga duk wani me good quality product da ya ke son Advertising ɗin shi,as Kaya masu kyau,da inganci (TALLAH) should contact me via :
08100046388

         Page 5️⃣

      TALLA!!TALLA!!TALLA!!!

https://chat.whatsapp.com/ImtxMSS1tuSKqvBpPqc03P

Assalamu'alaikum sisters🤗
KAMSHI* mace Mai kima, mace Mai daraja, mace Mai izza, mace Mai aji itace tasan darajan kamshi, if your perfume is not unique hajiyata you're just using ordinary air freshener🤣, hajiyata ko nawa Zaki kashe indai a turare ne baki Fadi ba😘 matan da suka gane suka San yanda zasu kankaro da martabar su, suke amfani da turare, a *BAKHOOR BY FAIXY* Zaki Sami Main chic, Bachelor, Husband snatcher, Her royal sexiness, Mysterious girl, Pleasure, Boovilous, White khumra, Maroon khumra, Black khumra, Hair perfume, Turaren wanka, Turaren wuta, Turaren tsuguno, Turaren mopping,Turaren carpet Shu'umat khumra,and more, yar uwa kar kibari abaki lbr, (wholesale and retail) WhatsApp 09067621681, siyan na gari Maida kudi gida🥳

Instagram @Bakhoor_by_faixy

******************************

   Idanu wa ta zaro cike da mamaki bakin ta har na rawa gurin fadin "Zuhra kin ji kan ki kuwa?Kin ma san me kike fadi kuwa?taya za ki ce mun FIK da ya taimaken yanzun nan shine wanann rude arrogant person din da na wanke da mari"ta kare tana girgiza kai alamun sam bata yarda ba.

"Sabeeha ke nan Wlhy ke ma saboda baki magana da kowa ne da kin san Waye FIK tun randa kika mare shi,indai har shine Mal Jibril yace miki to ba shakka shine wanda kika mara,domin duk school din nan shi kadai ke amsa wanann sunan babu me irin sunan shi balle in ce miki wai ko shi ne,sannan kamar yanda kika fada ne dan hamshakin me kudi ne,so ba abun mamaki bane don ya sa ya karbi assignment din ki,don wanann babu abinda in ya so ba zai iya ba,kila yan kudade ya hada shi da shi ya sanya cikin sauki yace miki kin yi passing course din ki,ke goofy angel Allah ya azurta mu Wlhy kudi sun yi ne,in kana da kudaden to  kai kam ka huta  wa raini da wulakancin mutane" ta kare tana murmushi,har yanzu idanun Sabeeha na kan ta,domin sam ta kasa gaskata abun da Zuhran ke fada mata,akan me ma ya sa zai taimake ta bayan abun da tayi masa,domin Zuhra kwana tayi tana fada mata Wlhy ba zai taba yafe wa ba sai ya rama,da kyar ta iya budan baki tace

"Goofy angel don Allah are you serious same person da na kwada wa mari shine same FIK da yanzu ya taimake ni?", "Sabeeha in dai har FIK yace da ke to Wlhy shine wanda kika mara gang leader na Rocket gang ba,shine dai wanda kika fasa wa mota,amman tambaya ta anan shine why zai taimake ki?A iya yanda nake jin labarin su wlhy kika sake wani abu ya hada ku ko da sune basu da gaskiya zaman makarantar nan sai ya gagari mutum,balle in your own case ke ce ma mara gaskiyan akan wani dalili ya ji ya taimake ki?"

  "Zuhra nima wlhy abunda ke ta yi mun yawo a cikin raina ke nan,sam tunani na ya kasa tsayawa balle ya bani amsan da nake bukata,a iya sani na inda har shine same FIK to farin ciki ya kamata yayi amman why on earth will he help me out?Akan me ya sa"dan numfashi Zuhra ta sauke sanann tace "gaskiya ni kaina ban san reason din shi na yin hakan ba,kai na ma duk ya kulle gashi dai taimakon ki yayi balle nace ya shirya wata munafurcin ta karkashin kasa"goshi Sabeeha ta dafe sanann tace "ko ma miye shike nan ni kam na gode ya taimaken,at least shima yayi abu me kyau na farko a rayuwar shi,Allah ya bashi lada,mu je ki raka ni in hau abun hawa in koma gida,tunda kin ce ba za ki bini ba yau hostel za ki kwana"ta kare tana hararan ta.

"Sabeeha ke dai da son kai kike,tsakani da Allah kwana uku nayi gidan ku fa,ke yaushe rabon da ki zo na mu gidan ki kwana ko biyu ne?"

"Ke ma kin san saboda Umma ce bana son dade wa a waje don bana son barin ta ita kadai a gida,kafin su Hajiya su sako ta gaba da tijaran su kin san kuma sarai Umma ba iya tanka su za ta yi ba"

"Eh haka ne kuma Ubangiji ya shirya su ya kuma kara muku hakurin zama da su,amman dangin Uba kam sai Allah wlhy", "Wlhy Zuhra abu daya ne in na tuno ya ke sanya ni raga musu,saboda duk wani Kani ko wan Mahaifi na matsayin uba yake mun,kuma hakki ne a kai na in musu biyayya kamar yanda zan yi wa nawa uban aka ce kuma in na saba musu kamar nawa Mahaifin na saba wa Allah kuma sai ya tambaye ni ya sanya kawai nake daurewa nake kau da kai akan wasu abubuwan,tunda ance uban ka ko me zai maka Ai baka isa ramawa ba,to su ma Allah ya basu wanann matsayin ya sanya gwamma na bi su sau da kafa har me rabawa ya raba,in sun cigaba da cutar da mu,tare da zaluntar mu Allah na kallon su,shi zai bi mana hakkin mu,amman matsayi na na diyar dan uwan su bani da ikon hukunta su,don Wlhy bani da burin da ya wuce duk kan mu ya hadu mun zamo yan uwa masu kauna da tausayin junan su,duk da ance wai Zumunta ba na mutum daya bane,amman ni dai zan yi musu zumunci in sun so suyi mana in kuma ba su so ba,su ne Zumunci zai ci ranar kiyama na yanke su da suka yi"

"Haka ne wlhy ko nima na ji wa'azin nan don a yanda na ji ma ko kishiyar mahaifiyar ka baka da right din mata rashin kunya don matsayin ta daya da ta mahaifiyar ka a gurin ubangiji,don aka ce ko mata Mahaifin ka ya Auro suka kwana daki daya ma'ana mu'amalar aure ta shiga tsakanin su,sai washe gari ya sake ta tabar gidan to tana nan matsayin Uwa a gare ka kuma dole ne akan ka kayi mata biyayya,don aka ce ko tana wani gari ta kira ka in baka je ba Allah sai ya kama ka da laifin bijire wa unarnin Mahaifiyar ka,zumuntar yanzun ne dai sai a hankali Wlhy sam ba a valuing din zumunci muna manta akan shiga Aljannah saboda shi,haka zalika ana shiga wuta ma saboda da shi,amman sai ki ga an fake da ni kullum ke musu zumunta su basa son sadarwa gare ni,na hakura nima na watsar,a neman Aljanna waya ce ana jiran wani,abunda rige rige ake gurin ganin na shige ta"

   "Zuhra manta kawai Allah dai ya dada shirya mu ya kuma ba mu ikon yin Zumunta don shi,domin wasun wallahi ba wai zumuntar ba ce ba sa son sadarwa kila wanda za suyi zumuncin da su masu kudi ne,to kin ga duniyar mu yanda ta koma sai yi tunanin saboda abun hannun mutu kake zuwa gidan shi ko kake kiran sa,to kin ga ba za ka so ka cigaba ba,wasun kuma har ga Allah ka fiye zuwa musu sai su gaji da kai,a fara canza maka fuska,ke dai Allah ya kyauta ya kuma kara gyara mana zuciya domin in ba Addinin ka sani ba ana yi maka haka za ka ce ka hakura har abada ba ka kara magana da wanne"da Ameen Zuhra ta amsa sanann suka cigaba da takowa suna dan taba hira kadan kadan.

"Me Alawar Madara"shine abunda suka ji an yi shouting daga bayan su,tsayawa suka yi duk su biyun ba tare da sun juyo ba,da gudu kuwa dan saurayin ya nufo inda suke har yana dan haki.

"Am so sorry to shout out to you like that,Wlhy na mance sunan ki ne,alawar madara nake so,Allah ya sa da akwai ma"ya kare yana sa hannu a aljihu.

Dan murmushi Sabeeha tayi sanann tace "babu komai ai,akwai alawar madara harda iloka ma,na nawa ne daman kake so?"ta kare tana karban yar paper bag din da robobin ke ciki a hannun Zuhra,ran ta kal don ba wani cinikin arziki yau tayi ba.

"Na duka nake so"da mamaki duk suka kalle shi,domin na cikin roban zai kai na 5k,Zuhra ne ta kasa hakuri har saida ta kuma tambayan shi "kace wai na nawa ma kake so?"

  "Duk na gurin ku nake son siye wa"ya fada yana murmushi,ai ko da sauri Zuhra ta karbi robar tare da mika mishi,ganin ciniki har inda suke,Allah me jin tausayin bayin sa, "ga shi to duk ka nan na 5k ne,ka je harda roban an bar maka kyauta "ta fada masa,karban roban yayi tare da damka mata damin kudi a hannun ta,idanu ta zaro tare da kallon Sabeeha tana me nuna mata kudaden hannun nata

"Goofy angel kin ga"ta fada tana bata kudin,karba Sabeeha tayi inda ta ga kudin sun fi karfin 5k sosai ma,hakan ya sanya ta juyowa gurin me siyan don maida masa kudin shi,kila mistake yayi ya basu kudin da ya fi haka,saidai kamar iska sun neme shi bat sun rasa,babu shi babu alamun shi,sun duduba gefen su amamn sam sun kasa samun shi,abun haushi ma ba rike kammanin shi suka yi ba.

"Zuhra na shige su,kin ko san nawa ne a nan?"ta kare tana karasa irga kudin,da sauri Zuhra tace "Sabeeha I don't know actually saidai daga gani kudin suna da dan yawa ko?"

"Au Zuhra da ma kika ce,30k ne fa nan dubu talatin cif,a taya hankali na ma zai kwanta abun 5k ya bada 30k kila Wlhy be sani bane ya bada shi,and abun haushi ba mu same shi ba,taya zan ta tafi da hakkin wani gida?In ma fara ce wa Umma me?"ta tambaye ta tana kallon ta.

Numfashi Zuhran ta sauke sannan tace "Sabeeha to Wlhy ban san me za ki ce mata ba,amman dai kin ga mun neme shi sama da kasa mun rasa,dole dai kiyi hakuri zuwa gobe sai mu kara neman shi da kyau don  yanzu kam mutane sai tafiya gida ake ba kuma lalle mu gane shi ba"

Kai ta gyada alamun gamsuwa sanann tace "goofy angel ko zan bar miki kudin gurin ki zuwa gobe sai ki taho da shi mu bashi?"

Da sauri tace "aa Goofy angel ki tafi da shi gida kin ga hostel din mun nan yanda semester tayi nisa wlhy ba karamin sata ake ba domin ana fama da babu yanzu,kar kudin dan mutane ya tafi a banza,na san no matter what za ki fini kula da shi"ba dai a son ran Sabeehan ba ta sanya kudin a jakar ta,sanann suka fito bakin gate,sun dan tsayu a gefen titi suna hira kafin suka samu adaidai ta,sallama Sabeeha tayi wa Zuhran bayan ta bata 1k akan ta rike a hannun ta ko akwai abinda za ta bukata,don ta ji Zuhran na kukan bata da kudi a hannun,ita ma ba wai kudin bane gare ta don cikin dan ribar nata ma ta cire wa Zuhran 1k din,rungume ta Zuhran tayi tare da mata godiya cike da jin dadi ta koma cikin makarantar bayan sun yi sallama domin ko biyar bata magani,ita Sabeeha Napen ta shiga tare da fada masa inda zai kai ta.

  Cikan da ta gani a babban sashi tare da hayaniyar mutane ne ya tsinkar mata da zuciyar tare da jin duk wata gajiyar da ta ibo ma duk ya wassake,don a iya sanin ta duk sanda aka yi irin wanann cikar kwai da kwarkwatan yan gida harda magulmatan makota to wani munafurcin ko gulman ake isar wa ko kuma ana cin zarafin wani ko wata.

  Duk surutu tare da hayaniyar mutane be hana ta jiyo muryan Umman ta da ke magana cikin kuka me tsuma zuciya ba,fadi take "Na rantse da girman Allah Hajiya ban daukar miki kudi ba,sharar da kika ce na yi shi nayi tare da fita Wlhy tallahi ban dau komai ba,hasalima ban san da kudin ki a dakin ba Wlhy da ban shigo ba"

Wata uwar tsawa Hajiya Ladi ta daka wa Umma kamar wata uwar da ta haife ta "Kee dallah munafuka rufe wa mutane baki,shegiya Farar mayya Wlhy sai kin fito mun da kudi na,hauka ma ke nan,ko dauka na kike mahaukaciya da zan aje kudi ki shiga ki fita a nema a rasa,kuma ki ce kar na zarge ki,uban wa zan zarga to?Maganar ma banza na rantse harda girman Allah ko ki fito mun da kudi na ko na yi miki tsirara gaban uban kowa na caje ki ciki da waje"ta kare tana huci wata wawaiyar shewa Shafa'atu(Maman Latifa)ta sake sanann tace "Ke ko Hajiya har sai kin tsaya wani rantse rantse,wanann mata ko dan mutum aka ce ta sata a halin matsin nan da ake ciki sai ki ce karya?Ai Wlhy ita ce ma ta dauka domin duk cikin mu babu wanda be fi karfin kudaden ki ba kowa Allah ya hore masa banda Mayya dangin mayyu,don haka ki matse ta ta fito miki da kudaden ki,don Wlhy Itace ma ta dauka sai uban fadin Allah a baki tare da nuna tauhidin karya da yaudara,neman mazan mutane ke ce sata tare da dauke dauken kayan mutane ma wannan ma ba a barki a baya ba,Wlhy kin ji jiki kin kuma ji kunya turr da ke Bilki"ta kare tana galla mata harara

Kafafuwan ta ne suka fara rawa,tare da jin kirjin ta nayi mata nauyi tsaban bakin ciki,babu abinda ke kara daga mata hankali da ya wuce irin kukan da take jin Umman ta nayi tana rantse rantse kan bata dauka mata ko sisi ba,inda kuwa Su Latifa da Maman ta sai kara tunzura Hajiya suke kan kar ta kuskure ta yadda ta tsile ta ita ce barauniyar,cikin mutanen ta samu ta kutso kan ta tare da isa kofar dakin Hajiya Ladi,inda ta tarar da Umman ta durkushe tana kuka,ta rike zani da rigar ta kam don ji da tayi Hajiya tace in har ta irga 10 bata bata kudin ta ba wallahi sai ta tube ta tas ta zuba mata ruwan sanyi a jiki tare da Zane mata jiki,da sauri ta nufo Umman tare da rungumo ta,tare da fashe wa da kuka,wannan wani irin cin mutunci ne sabida Allah,jin Sabeehan a jikin ta ya sanya Umman kankame ta tare da fashe wa da marayan kuka, "Sabeeha Wlhy tallahi ban daukar mata kudi ba,ki taya ni fada musu ni ba Barauniya bace Wlhy ban taba sata ba tunda nake,na sani muna cikin matsin rayuwa amman hakan ba shi ya bani daman daukan kayan wani ba,Wlhy ni ba Barauniya bace ta kare cikin kuka sosai"numfashi Sabeeha ta sauke sanann ta shara hawayen ta tare da mike wa tsaye tana dago Umman nata,saida ta ga ta tsaya kan kafafuwan ta sannan ta shiga goge mata hawaye

  "Ya isa haka Umma don girman Allah ki bar zubar da hawayen ki akan wannan mutanan da basu san ciwo da darajar kan su ba balle su san na wasu,and daga yau Umma kar ki kuma durgusawa gaban ko wace shegiya Ai talauci ba hauka bane"

Da sauri "Shafa'atu tace "to rikakkiya mara mutunci wanda bata gaji arziki ba"A zafafe Sabeeha ta katse ta da fadin "har akwai mara mutuncin da ta wuci wace kike da a cikin dakin ki?Arziki har ya wuce kwakwalwar da ta haddace Qur'ani?Ko akwai arzikin da ta wuce samun wadatattaciyar tarbiya?Akwai arzikin da ta wuce ayi maka Aure ka zauna gidan mijin ka tare da neman Aljannar ka kayi biyyaya har ka mutu a binne gawan ka a dakin mijin ka?Ko akwai arzikin da ta wuce Allah ya raba ka da neman Maza?Neman mata?da kuma kare ka daga shaye shaye?To Alhamdulilah ni wannan Arzikin sun wadace ni bana bukatar kari" ta kare tana galla mata harara

  Da sauri Latifa tayo kanta "kan Bura uba!!ke Sabeeha dan Bura uban ki Ni da Uwa ta sa'annin ki ne da zaki fada wa  magana son ran ki kiyi tunanin kuma na Kyalle ki?" Wata uwar harara ta maka wa Latifan sanann tace

  "Na rantse da Allah Latifa in har kika sake kika iso inda nake Wlhy tallahi sai na sumar da ke,in kuma kika kuskura kika kuma zagar mun Uba sai na zubar miki da hakori,gwamma Uba na talaka ne,wata kuwa uban ta babu wanda be sani ba kwarto ne mane min mata,Akwai karya ne a abunda na fada?Baki kaso Auran kin bane saboda rashin sanin ciwon kai akan wanda ko a dan aikin gidan ki be dace ya zama ba,saboda lalacewa da mutuwar zuciya tare da asara wai shi kike so"

  A zafafe Hajiya Ladi tace "SABEEHAAA!!!Itama a zafafen ta amsa da "Naam Hajiya Ladi"baki sake duk suka bita da kallo kafin Hajiya ta ce "Ke ni kike kallon cikin idona kike kiran suna na haka?"

"Na kira din Ai in babba be ji kunya hawa Jaki ba to Jaki ma ba zai ji kunyar kwada shi a kasa ba,ki ma gode wa Allah na sakaya na sanya miki Hajiya ban kira ki da Ladi gatsau ba,and na rantse da girman Allah akan Uwa ta a shirye nake in tube mu bugu da mata ko yar mata,don na ga alamun rainin hankalin naku yawa take yi,ba komai ya sanya can nake Kyalle ku ba daman sai saboda Jini ya hada na kuma san darajan Zumunta!!a sanya ma ta yi satar laifin na Waye??a cikin ku babu wanda ya damu da mun ci ko ba mu ci ba,mun sha ko ba mu sha ba?Duk wani nauyin mu be dame ku ba,hasali ma mun tashi mun nema ma neman hanyar dakile ta kuke yi,ko da ace makota ne mu akwai hakkin makota ka a kan ku wanda dole ne ku sauke shi,domin ranshin sauke shi zai kai mutum wuta,balle Umma ta duk waya duk tsanani bata sata,barayi kuma mun san su muna kuma yi musu fatan shiryuwa"

Da sauri Umma tace "Auta!!ya isa haka,meye amfanin abubuwan nan da kike fada?Ban hana ki rashin kunya ba?"a zafafe Hajiya Ladi tace "Ke dallah rufe mun baki munafukan banza munafukan wofi,Waye za ki yi wa karyan iskanci?Ki ziga yarinya tare da koya mata rashin kunya sanann yanzu tayi ki zo kina wani burgan karya"

"Umma kin ji Ai duk abunda za mu yi ba taba burge mutanan nan muke ba,Umma sam zuciya ta ba za ta iya juran ganin ana wulakanta ki ba,Wlhy in da na dauka yanzu ba zan iya ba,zan iya hakura na ki yin magana in akai na ne amamn in dai kan ki ne sai inda karfi na ya kare,akan wani dalili za su daura miki sharrin sata?Sun kyauta ke nan"da sauri Hajiya Ladi ta cabe da fadin

  "Kun ji mun shegiya akwai karya a abinda na fada ne,ba barauniyar bace uwar taki?A taya daga shigan ta daki ta fito zan nemi kudi na na rasa,sanann saboda ina tsoron uban ki sai ace kar nayi magana?"

  "Hajiya!!!duk abinda za kiyi kar ki kuma kiran uwa ta da barauniya,sanann kar ki kuma zagar mun Uba domin yana kasa,a har nawa ne kudin naki da kike neman ci mana mutunci?Nawa ne kudin na ki"

  "Ah yarinya an girma in na zagar akwai uban da kika isa kiyi mun ne?Da kike wani bubude mun ido kina daga jijiyoyin wuya gurin tambayar nawa ne kudi na,na gani nan na ci da sha ma gaggarar ku take yi,dubu 20 ne cif kudi na da ta dauke,kuma na rantse da Allah sisi ba zan yafe ba sai ta biya ni,a da na so muyi ta cikin gida amman tunda na ga baki da mutunci har kin san ki karkada mun kirji tare da bude mun idanu Wlhy in har baku biya ba cikin mint 5 sai na kai ku police station sun fito mun da hakki na,domin ba zan dauki asara da rashin kunya ba"

Dariya Umman Latifa ta sheke da shi tare da tafa hannu "Ahyyyehh ana yi mun jin dadi,daman ance Ai ramin karya kurarre ne"hakan yayi daidai da durkusawar Umma hannu bibbiyu ta hade don bai wa Hajiya hakuri,a ina ta ga dubu 20 da za ta bata sabida Allah,da sauri Sabeeha ta dago ta tare da rungume ta

"Umma kiyi wa Allah da Manzon shi ki bar durkusa wa wanda babu tausayi ko burbudin imani a ran su", "to shegiya ke da akwai imanin Ai sai ki ce wa wahallaliyar uwar ki ta biya kudin ko Wlhy sai na daure ku don ba zan yafe ba"

Dan dariyan takaici Sabeehar tayi sanann tace "Wlhy Hajiya in kika yafe ma zan ce ba ke bace,and this should be your first and last time da za ki zagi uwa ta,don kika maimata za ki samu mugun matsala da ni"ta kare tana watsa mata kallo,da sauri Hajiya ta sha jinin jikin ta,kafin tace "to kuwa in kina nema wa Mahaifiyar ki mutunci a biya kudi na"

"Kudi kam za mu biya Allah duk da be yi mu masu kudi ba amman ya rufa mana asiri"ta kare tana bude jakar ta,saida ta irga 20k cash sanann ta fito da shi tare da danka su hannun Hajiya wanda ta bude ido da baki cike da dumbin mamaki don sam bata zata za su samu wanann kudin ba ganin yanda suke fama,to so ta ci zarafin su tare da yaga musu rigar mutunci a karshe ta kai su police station domin ba don Sabeeha ba ta so har tsirara tayi wa Umma

"Irga su da kyau 20k ne cash a nan,kudin da kika ce Umma na ta sata,Hajiya ga su na biya duk da kuwa na san sharri kike yi mata,ina so in tunasantar da ke kan ki ji tsoron Allah ki tuna za ki biya kina ranar Alkiyama,domin Wlhy ba mu yafe ba sharrin da kika yi mana tare da karban kudin mu ba tare da hakkin ki ba,and Wlhy tallahi da kin sake kin cire wa Umma kaya a gaban wannan shegu munafukan mutanann sai na tabbatar da na tube ki a gaban duk yan unguwan nan na zane miki jiki"da sauri Umma ta kwade bakin ta har saida ya fashe

"Sabeeha wai shin kina Hauka ne??Hajiyar kike fadi wa haka"Umma ta kare hawaye na zubo mata,cikin kuka Sabeehar ma tace "Haba Umma saboda Allah don Allah yayi ki me hakuri sai ko wani kare da doki yayi ta cin Tuwo a kan ki,Wlhy ba zai yu ba uwa ce ke kuma kin haifa akan wani dalili kan 20k har ana shirin tube ki"baki Umma ta rufe mata domin tana gudun abunda zai je ya zo daga baya,tare da kamo hannun ta don komawa sashin su,hannun Umma ta saukar sannan tace

  "Wlhy kar ku ga Umma ta ja ni,daidai nake da ko wace mata cikin gidan nan,akan Umma ta a shirye nake a jini da ko ma wace,kudin mu kuma Allah ya isa mun bar wa Allah hakkin mu da ake son a ci,ku kuma munafukai masu son yada jita jita sai a koma gida haka nan the show is finally over "da sauri Umma ta fizge ta tare da wuce wa sashin su.

Da kallon mamaki Hajiya ke raka bayan su,kan ta gaba daya ya kulle a ina Sabeeha ta samu kudi,and maganganun yarinyar sun tsaya mata a rai,quiet alright ta san yarinyar bata da tsoro kuma bata kunyar karban yancin ta amman bata san yaushe ta daina jin tsoron ta har ta kai ta ga fada mata magana son ran ta ba,ta dade sosai tsaye a gun tana mamaki tare da juya kudin hannun ta,domin sam hakan ta bata cimma ruwa ba,da kyar su Shafa'atu suka shawo kan ta tare da maida ta daki,domin cewa tayi sai ta zane wa Sabeeha jiki,inda suka ga Sabeeha na saman nan muddum suka bar Hajiya ta je to saidai a ibe yan kallo,hakuri suka yi ta bata tare da kwantar mata da hankali kan ta bari a cikin ruwan sanyi za su dafa Sabeeha tare da cin uban ta.

  Sosai Umma ta rufe ta da fada kamar za ta buge ta lokacin da suka shige dakin Umman,fada take mata sosai kan akan me ya sa za ta biye wa zuciya har su yi fadi in fada da su Hajiya,what if suka yi mata wani abu fa?Daman can ya suka kare balle ace kuma ta kara tunzuro su,kuka sosai Sabeehar take domin ba karamin zafi fadan Umman yayi mata ba,za ta iya cewa ma yau ne rana na farko da Umma tayi mata irin wanann fadan ga bakin ta har na fidda jini,aka ce tsakanin 'Da da Uwa sai Allah a take kuma sai jikin Umman yayi sanyi,tare da janyo Sabeehar jikin ta ta rungume tare da shiga lallshin ta,tare da nuna mata ba wai fada take mata haka kawai ba,tsoro take ji na abunda zai je ya zo,don ta san halin gidan sarai,and ko ma Yaya ne a matsayin iyayen ta suke be kamata tayi musu haka ba,inda Sabeehar ta nuna wa Umman ran ta ne ya baci akan me ya sa za su na musu haka,da kyar dai Umma ta samu ta shawo kan nata har tayi shiru sanann ta goge mata bakin,tare da shafa mata man zafi,sanann ta shiga ba ta labarin yanda abun ya faru,kan Hajiya ce ta aiko wai ace mata ta zo don Allah ta taya ta gyara dakin ta,daga gama shara ta fito sai ga Hajiyar na kwalo mata kira wai bata ga dubu 20 din ta ba,kafin kace me mutane sun taru ta shiga wulakan ta ta.

  "Umma Wlhy yau da badun ke ba a yanda nake ji na ko Hajiya sai na daku da ita", "kul Auta kar na kuma jin kin yi irin wanann maganar mu dai cigaba da hakuri komai me wuce wa ne in sha Allah,so don Allah kina hakuri kin ji?"

  Mikewa tayi ta zauna sanann tace "Haba Umma Wlhy rashin hakuri na kawai kike gani,amamn abubuwan da mutanan nan suke yi ya fara fita out of hand,yanzu don Allah ko da da gaske ne kin dau kudin Allah ya kiyaye ya kyautu tayi miki irin wannan cin mutuncin?Umma uwa ta ce ke fa,a taya kike tsammanin zuciya ta za ta samu nutuswa a lokacin da kike cikin damuwa,Umma da ban dawo akan lokaci ba fa,da ba a samu kudin ta ba,da gaske da tube kin za ta yi ke nan?Ko kuma police station din za ta kai mu,Umma wai me muka yi wa bayin Allah nan ne kwata kwata ba sa kaunar mu?Miye laifin mu don Allah?Kawai don Allah yayi mu talakawa shine?Daman Zumunta sai da masu kudi a tsakanin su suke yi?Haka rayuwar mu za ta cigaba da tafi babu wani canji Umma kullum cikin bakin ciki da kunci"ta kare tana hawaye.

Hannu Umma ta sanya tare da share mata hawayen sanann ta kuma janyo ta jikin ta

"Autar Umma!!ta kira sunan ta a sanyaye,dagowa tayi tare da kallon Umman alamun tana jin ta,sanann ta cigaba da fadin,kar ki taba dauka haka rayuwar mu za ta kasance,mun dai san farkon mu,tsakiya da karshen mu duk Allah madaukakin sarki shi ya fi mu sani,amman na tabbatar ance duk wani bayan wuya akwai dadi na nan zuwa,and Wlhy jiki na yana bani ba haka rayuwar mu za ta kare ba,Sabeeha kar ki taba sanya a ran ki kan wai shi talaka bayi da daraja ko kuma makasskanci ne,duk wani wanda kika gani duniyar nan da darajar shi,domin Allah da kan shi ya ce ya karrama halittan dan Adam,sannan ina so kina tausa tare da hadiyar fushin ki,domin Annabi da kan shi yace ba me karfi bane me saurin fushi,me karfi shine wanda ya mallaki zuciyar shi lokacin fushin farko,duk fa lallacewar su dangin Mahaifin ki ne,and babu inda muke da su da ya wuce nan,Sabeeha yau da ina da hali ko arzikin siyan gida ke ko da kama haya ne wlhy da na nema a wani gari mun tashi mun bar nan ko zan ga kin yi rayuwar farin ciki,amman ke ma kin san halin da muke ciki yau akwai ne gobe babu,don haka ina me kara tausar zuciyar ki da ki kara hakuri komai zai wuce ya zamo labari Wlhy,sannan ina so gobe in Allah ya kaimu ki je ki bai wa su Hajiya hakuri,ko sun ki mu'amala me kyau da dadi da ke,mu muyi kokarin kyautata musu namu zaman,sai ki ga ran Alhira Allah ya ba mu lada,Auta ta babu wanda na taba jin an ce yayi hakuri be ga riba ba don Allah wanann saurin fushin ana kokarin danne ta jin ji ko"ta kare tana riko hannun ta.

Kai Sabeeha ta daga alamun eh sanann tace "Umma Allah ya kara miki hakuri,da ace matan gidan nan duk kalan halin ki gare su da sun ji dadi wlhy,amman ni dai Umma Wlhy ba zan ba su hakuri ba domin ban musu komai ba iya Gaskiya na fada,kuma in sha Allah zan na hakuri kamar yanda kika fada,amman Wlhy iya hakuri na akai na ne,duk wanda ya taba ki ni da shi ne"

Kan ta Umma ta shafa tana murmushi sannan tace "Su Sabeehatun Umma an girma har an san zafin a taba maka Uwa hakan ma ba zai kuma faruwa ba in sha Allah,shike nan ni zan ba su in ke ba za ki ba su ba"

"Umma!!!!ta ja sunan nata,ba fa bayar wa ne ba zan iya ba sam ba su yi deserving mu basu hakuri ba domin mu aka yi wa laifi,kuma in ke ma kika ce sai kin ba su ba zan kuma cin abinci na wata daya ba,yasin kuma sai na aske gashin kai na duka na zamo me malu tandal"Umma can't hold it saida ta fashe da dariya don at times Sabeeha in tayi wani abun kamar yarinya karama

  "Yo Ai ke yunwa za ta tsinka wa hanji,malu kuma in mika yi mijin aure za ki rasa,don ba wanda zai so ya auri me tandal din kai,ko da kuwa shi din ma be da gashin kai,ya kamata ma ayi kitso Auta sanyi ya fara shigowa barin kan a haka zai kadar miki da gashi,ba ma wanann ba Sabeeha ina kika samu kudade masu yawa har 20 kika bai wa Haiya Ladi dazu?a iya sani na kin fita baki da ko sisi,sannan duk cinikin ki ko da za a siye tas ba zai yu ace kin hada 20k ba"ta kare tana tsare ta da ido.

Dan kai Sabeehan ta sosa sanann ta karanta wa Umman tas yanda aka yi ta samu kudin,dan shiru Umman tayi ganin haka ya sanya Sabeeha cewa

"Umma Wlhy na yi niyar gobe na maida masa kudin sa domin duk mun neme shi mun rasa,to ganin ana kokarin zubar miki da mutunci ne ya sanya na ari kudin in na samu sai na biya"

Goshi Umma ta dafe sanann ta ce "Auta ai da baki taba masa kudi ba,irin wanann in kuka hadu gobe fa?Ya kuma tambayi ina kudin shi me za ki ce masa?"

"Umma!!!na sani nima Wlhy ba da gangan na bada kudin shi ba,I just can't stand seeing you like that ina da hali kuma na kasa taimaka miki,Umma ba ni ba ko ma wacece a shoes dina the same thing za ta yi,in muka hadu gobe zan bashi sauran 5k din sai na ce ya bini bashin 25k zan bashi daga baya na san in sha Allah zai yarda"

Drawer Umma ta bude tare da dauko kudin ciki ta mika mata "karbi nan dubu 5 ce in ya so kya hada ya zamo goma kudin Wuta da Ruwa na aje don na san any moment za su iya zuwa tambaya,amman tunda haka ya faru na san Allah zai kawo mana wata hanyar"tana kokarin magana Umma tace "kar ki ce komai Auta karbi kawai Allah ba zai taba kunya ta mu ba,na yi imani da hakan ance duk wanda ya dogara da Allah to ba shakka Allah ya isar masa Allah yana gani kuma shi zai kawo mana wani hanyan"rungume Umman tayi kam a hankali ta furta "i love you so much Umman Sabeeha Allah ya bar mun ke a raye nayi kudi in jiyar da ke dadi"

Murmushi Umma tayi sanann tace "Ameen thuma
Ameen Auta na,jiki na yana bani in sha Allah sai kin zamo wata sai kin zamo babbar mace a rayuwar ki,yanzu dai je ki ibi abinci ki ci,kin dawo ba ki ci komai ba sai kiyi wanka ki canza kaya ki zo na miki kitso,don yau kam na gaji da ganin kan ki haka kamar akushin mahaukata"baki ta turo domin ita fa a rayuwa babu abinda take adawa da shi irin kitso, "duk kiyi ki gama in kin so bakin ki ya tabo Misra amman fa yau ba fashi sai an kitsa kan nan,in ma na wa ne baki so akwai dari biyu guri na ki karba maza ki je gidan kitso ayi miki zannan yawo"

Dariya ta kwashe da shi "haba dai Hajiya Umma Ai yanzu kam yasin na girmi zanan yawo"ta kare tana barin dakin saida ta biya dakin ta ta cire kaya tare da dauro zani sanann ta ibo abincin,nan ta shiga ci suna hira da Umman gwanin ban sha'awa (At times ba tarin dukiya ko abun duniya bane mutum ke samun farin ciki,just kiyi trying zama cikin yaran ki,ko yan uwa tare da iyayen ki,talk your mind out,kuyi hira aji matsaloli da cigaban juna wanann kadai ma farin ciki ne on his on,more especially in kin samu alone time with your mom🥹Allah ka kara wa iyayen mu nisan kwana da lafiya me amfani,wanda na su suka Riga mu gidan gaskiya Allah ya musu rahma,ya sanya suna Aljanna,in na mu ya zo ya zo ya sa mu cika da imani).

     ********************2 Days Later

      Zaune suke akan wani  bench  da ke gindin wata bishiya,iska ce me dadi ke kadawa sakamakon hadirin da ya fara haduwa a sararin samaniya,Zuhra ce ta kalle ta sanann tace "Goofy angel anya yau zai zo kuwa,kin ga hadiri ya fara haduwa,ko dai za ki zo mu tafi don in aka fara ruwa bana jin za mu samu abun hawa cikin sauki"

"Zuhra ki dan kara hakuri kwana uku ke nan kullum by this time yake zuwa,yau so nake ayi ta ta kare ban ga dalilin da zai na zuwa siyan kayana yana bani extra kudi haka ba,ki duba fa ki gani daga randa ya fara siya zuwa yau ya bani kusan 70k fa,tun ran farko
nace da Umma zan maida masa kudin shi,amman be bani chance din yin hakan ba ma,don the other day ba shi ya zo ba,ina dalili ni na ma fara tsorota,haka babu yanda na iya da ya wuce in boye kudin gudun kar Umma ta gani,don ko na fada mata ba ma lalle ne ta yarda ba tunda abun kwata kwata be yi making sense ba"tana kare zancen kuwa sai gashi ya iso ind suke

  Cikin sauri ya mika wa Zuhra damin kudin sanann yace "a bani alawar madara"da sauri Sabeeha tace "ba na siyar wa bane ko in ce da kai ba zan siyar maka ba"still be daina mika kudin ba yace "to shike nan ga dai wannan"ya aje kudin ganin haka ya sanya Sabeeha saurin mikewa tare da cewa "Mal in kana wa Allah Manzon shi da iyayen ka don Allah kar ka gudu,ka tsaya I want to talk to you"jin haka ya sanya shi tsaya wa cak

Saida ta isa gaban shi sanann tace "don Allah wane ne kai?A iya sani na ban taba sanin me kama da kai ba ma,a ina ka sanni?Why on earth kake bani extra money kullum?At first nayi tunanin bisa rashin sani kayi hakan,amman daga shekaran jiya zuwa yau na fahimci da gangan kake hakan,don Allah ka sanar da ni why kake bani irin wannan kudaden a irin tsadar rayuwar nan da ake ciki"

Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya nisa yace "yeah actually ban san ki ba nima,kuma duk abinda kika fada haka ne,da gangan nake yin hakan,saidai kuma sam ba wai kashin kaina nake yin haka ba,nima sanya ni aka yi tare da sanar da ni kullum in na ga kin zo na je na siye robar alawar madaran ki,na kuma tabbatar na baki kudi masu yawa don dubu hamshin hamshin aka ce ina baki,so kiyi hakuri kin san country hard ya sanya na kan dan cire wani abu a kai"

Daga ita har Zuhra da kallon mamaki suke bin shi kafin can ta nisa itama tace "ni fa duk ba wannan bane ya dame ni,don girman Allah ko za ka iya sanar da ni wanda ya sanya ka kana siye kayan madara na?"ta tambaye shi hoping ya fada mata gaskiya

"Yo me zai hana Alkhairin da na samu saboda ke Ai ko gurin shi kika ce na kai ki zan kai ki"da sauri tace "aa ba ma sai ka kaini ba for now ina son sanin ko shi wanene don Allah"

  "FIK shugaban Rocket gang,shine wanda ya sanya ni aikin nan,sannan duk sanda na siya roban wa shi nake kai wa,I hope kin gane ko"

  With full of shocked ita da Zuhra suka zaro idanu waje tare da furta "FIK kuma"a tare,kai matashin saurayin ya gyada musu sanann yace "yanzu dai kin samu answer din ki kuma saboda hada ni da Allah da kika yi ya sanya na fada miki,so ni kam kun ga tafiya ta",cak suka ja suka tsaya tare da bin bayan shi da kallo,don har yanzu sun kasa yarda da wai FIK ne ya ke turo shi siyan alawar madaran ta kullum....

   Ayi mun afuwa na rashin yin posting da wuri,hakan ya faru ne saboda yan wasu uzuririkan da na shiga,na so ya fi haka amman Allah be yi ba.

  Bare with the typing errors don ba Riga nayi editing

    Share🥰
    And
Comment

    Ina yi wa ko fatan Alkhairi.

Continue Reading

You'll Also Like

8.7K 122 29
the short summary , easy to understand the book "The 48 Laws Of Power " by ROBERT GREENE
248K 48K 128
Title - Dangerous Personality Author - Mu Gua Huang MC- Xie Lin x Chi Qing Chapter 161 + 2 extras ထူးဆန်းသည့် ပြန်ပေးဆွဲမှုတစ်ခုအပြီးတွင် ချီချင်းတစ်...
34.2K 5.6K 16
The Phoenix, embraced the shadows to protect his country. His true identity remained hidden for years, serving as a covert weapon against unseen thre...
9.4K 1.3K 80
Book 1 in my thriller quadrilogy. .......... Vaidehi is a young woman with her own set of dreams and disappointments. She faces a heartbreak w...