KOWA YA GA ZABUWA...

Od Gureenjo6763

13.9K 1K 46

Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko... Více

Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page 10
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20
Page 21
Part 22
Part 23
Page 24
Page 25
Page 26
Page 27
Page 28
Page 29
Page 30
Page 31
Page 33
Page 34
Page 35
Page 36
Page 37
Page 38
Page 39
Page 40
Page 41
Page 42
Page 43
Page 44
Page 45
Page 46
Page 47

Page 32

272 25 0
Od Gureenjo6763

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 32*

*FREE BOOK*

"Assalamu Alaikum warahmatullah..!"
Dakakkiyar muryarsa ta shiga kunnenta ta aika mata da wani sako me karfi har tsakiyar zuciyarta, bata san sadda ta zauna ba.. Muryarta na breaking tace

"Wa'alaikumussalam warahmatullah....ina kwana?"

Seda ya ɗau seconds kan yace
"kuna lafiya?"

Tana jan kasan dankwalin kanta dake bisa kirjinta tace
"Alhamdulillah..! Yaran...su suna school"

Lumshe idanunshi yayi yana kishingiɗa da kyau yace cikin kasalalliyar murya dake nuna gajiyawa.
"I know! didn't call the kids, I called you die hard."

Shiru duk suka yi na seconds kan yace a sanyaye
"na kasa cigaba da jurewa, I cannot believe soyayyarki tayi min Illar da take son hana min daily activities ɗina, die hard for this 8days ni kaɗai na san irin halin da na shiga da na hora kaina da jin murya da kuma ganin ki, I gave you space ko zaki fahimci kema kina jin a little bit abunda nake ji but to no avail babu abunda ya chanza ko? You hate me ko?"
Daga muryarshi take jin ɗacin zuciyarshi duk sbd ita, hawaye ne ya gangaro mata tana ta son yin magana muryarta na rawa..

"It's OK! Don't cry u don't have to, I understand. Take care"

Har ze sauke wayan tayi saurin cewa
"wait!"

Lumshe idanunshi yayi yana sake rike wayan da kyau a kunnenshi kaman wani ne ze kwace..

"Am...am so sorry for hurting ur feelings, it was never intentionally, it's just hard to believe cewa ni hidayat nice Muhammad Raed ya zaɓa a matsayin Abokiyar rayuwa duk tarin mata masu aji, kyau, nasaba, dukiya da kyaun asali..."

Hawayenta ta share da tafin hannunta kan ta cigaba a sanyaye..
"U pleaded with me to share my heart ko da ba zan baka duka ba, Raed zuciyar hidayat gabaɗayanta mallakinka ce, ni da kai kaman ruhi ɗaya ne dake rayuwa a mabanbantan jiki...! Ka rokeni na baka dama.. Na baka a yanzu Raed, na mallaka maka ragamar rayuwata please Raed be my only husband, sirrina, farin cikina, make me ur only woman bcs u are my true and last love, I love you every second of every day....we missed you beyond words pls come back home paapi"

Tana kai nan ta sauke wayan kunya na rufe ta, da gudu ta tashi ta shige ɗaki kaman wata yarinya ta zube bisa gado tana rufe fuskanta ji take wasai ta sauke abunda ya tokare mata zuciya, ita kanta bata san tana son shi haka ba seda taji bakinta na amayar da zancen zuciyarta wadda ita kam bazata ce ga sadda ta tsara su ba.

Sako ne ya shiga wayanta, da sauri ta janyo ta buɗe.

"Thank you! Thank you so very much, you don't know how badly I wanted to hear you say that! U made me the most happiest person in the world, I love you for exactly who you are today and I will love you tomorrow and the day after very same day🥺😘"

Murmushi ta saki tare da ɗaura wayan a saitin zuciyarta tana lumshe idanu, ƙaurin abincin ta yasa ta tashi da sauri ooh soyayya ya sa ta mance abu ta ɗaura da sauri tayi kitchen tana murmushin kanta.

****

"Daadida she accepted me, ta bani dama a rayuwarta.."
Yayi maganan muryarshi na bayyana irin farin cikin da zuciyarshi take ciki.

Murmushi me sauti Daadida tayi tace
"Alhamdulillah! Se ka ji tsoron Allah ka kula da ita saboda Allah, hidayat wata haske ce a rayuwarku wadda idan ka bari ta dusashe rayuwarku ma zata dusashe"

Kai ya gyaɗa yace
"Daadida I want you to cook for 200 people ayi sadaka wa almajirai Allah ya tabbatar mana da alkhairi"

Murmushi me kyau ta saki lallai rayuwar Raed akwai chanji me matukar girma, kalaman da da baya yin su wadda a musulunce suke kaman dole sbd sunna ne yanzu duk yana yi, da da ne sede ayi celebrating a kashewa abokai ayi kida amma yanzu almajirai yake so ya baiwa, da da ne ba ze ɗauki Kalmar tabbatuwar alkhairi da muhimmanci da har ze furta ba don be san menene Adu'ar ya kunsa ba se gashi yanzu ya sani.

Har ze kashe tace
"wani hanzari ba gudu ba! Raed hankalina baze taɓa kwanciya kasancewar ku yanzu a inuwa guda da soyayya babu aure ba, a duk lokacin da Zaku keɓe sheɗan ne ze zama na ukun ku, kaman yadda Allah ya faɗa a cikin Alqur'ani me girma, shi kuma bashi da wani buri illa na ya haddasa fitina a ban ƙasa, don haka zan shawarceka da ka natsu ka yanke hukuncin da zata ficceku tun kafin sheɗan yayi nasarar ratsa tunaninku don daga sannan kuma wannan soyayya zata samu cikas, rayuwar aurenku baze taɓa yin albarka ba don an kashe albarkar daga waje"

"zan yi tunanin hanya mafi bullewa kan in koma Daadida bana son abunda ze kawo mana rashin albarkar aure kaman yadda kika faɗa, in shaa Allah I will call back in faɗa miki hukuncin da na zartar"

Murmushi ta saki tace
"Allah ya maka albarka"

Ya amsa da Ameen kan ya kashe wayan, kuɗi masu yawa ya tura mata na sadakar da yake so ayi, kan yayi call akan a tura mishi numbern Farik Naik ze mishi tambaya..

Cikin mintuna talatin ya samu personal line ɗinshi sbd connections ya kira shi, bayan sun gaisa ya sanar dashi waye shi suka sake Gaisawa kan yayi mishi tambayar da yake so yayi mishi, gamsashiyar Amsa ya bashi wadda Alqur'ani da hadisi suka zo dashi, yayi mishi godiya suka yi sallama..

Hidayat ya sake kira, Aisha ce ta ɗaga suka fara mishi hayaniya, Seda duk ya gama jinsu wai next week zasu yi hutu, they want a holiday outside Paris.

"Where is ur mom?"
Ya tambayi Farrah, se ta fara kwala kiran hidayat

"mom! Mom dad want to talk to you"

Fitowa hidayat tayi tana sakin murmushi ta karɓi wayan tare da sallama... Seda ya lumshe idanu kan ya amsa yace
"Die hard when are you finishing ur exams?"

Tace
"Amm ina Tunanin in 8dys time"

Yace
"ok, I will be bit busy to then don zamu yi final muma in 10dys....!"

Tace
"kaiii...! U mean zaka fi week kan ka dawo?"
Ita kanta bata san sadda tayi maganan murya a karye ba.

Murmushi yayi me sauti yace
"someone is already missing me ko?"

Murmushi kawai tayi, yace
"I want us to go for a trip after ur examination"

Cikin zumuɗi tace
"where?"

Yace
"it will be surprise, ke de kiyi mana Adu'ar sa'a a wasanninmu masu zuwa don sun ɗauko zafi"

Tace cikin murmushi
"I trust you in shaa Allah ku Zaku yi nasara! Allah ya bada sa'a ku ɗauko mana UcL cup"

Sossai yaji daaɗin Adu'ar ya amsa suka yi sallama.

Daadida ya sake kira ya gaya mata hukuncin da ya tsayar taji daaɗi sossai tayi mishi Adu'ar nasara itama, ta so ta kawo mishi zancen Mahaifinshi sede bata so ta ɓata mishi mood na farin ciki da yake ciki, kudin da ya turo rabi ta kira Badi'ah ta tura musu akan a koma asibiti sbd ita yanzu bazata iya tafiya daga Kano zuwa gembu da mota ba, ko daga cikin jalingo zuwa gembu tafiya ne me nisa sossai dole se da jirgi kuma babu jirgin da ze iya kaita gembu in ba helicopter ko private jet ba.

A chan ɓangaren su Badi'ah kuwa kuɗi na shiga Seda suka kusa dambe a rabo, yana kwance a ɗaki cikin kashi da fitsari yana jinsu hawaye wani na bin wani a idanunshi... Kwarai Son zuciya da taake faɗar Mahalicci be da sakamako se na bakin ciki da dana sani, idan da ya girmama mahaifiyarshi ya mutunta ta da Raed be mishi abunda ya mishi ba ko da kuwa naman shi yayi ta yanka yana ƙarami, Dama an ce abunda kayi shi za'a yi maka, ya watsar da mahaifiyarshi a lokacin da ta fi bukatar shi gashi shima nashi ɗan ya watsar dashi a irin wannan lokacin.

Ya zalunci matarshi me kaunarshi sbd Allah da tausayinshi wacce tayi ta fafutukar ɗaura shi bisa hanyar bin mahaifiyarshi ba tare da ya san kanshi ya zalunta ba ya zaɓi ɓara gurbi irin su Badi'ah ya watsar da Mairamu, Daadida dae bata mishi baki ba, bata yi fushi ba sede Allah me cika alkawari ne a duk sadda ya ɗauka shiyasa yayi mana hani ga saɓawa iyaye ko min kankantarshi, yanzu duk wa gari ya waya..

Kuka me sauti ne ya kwace mishi a sadda ya tuna amanar Mahaifinshi da ya ci wadda shine sanadiyar barin Daadida gidanshi a baya.. Ta ina ze fara gyarawa? Yana kwance cikin tsananin jinya da ciwo? Babu abinci babu magani? In ya mutu a haka ze ga rahamar ubangiji kuwa?

***

"Hamza! Wai ka ga yadda ka koma kuwa? Hamza akan mace kake shirin kashe kanka nima ka kashe ni? Kai fa kaɗai ne abunda na mallaka don Allah ka sassautawa kanka wannan wahalan, wallahi na yarda na amince in har dae Auren hidayat ɗin nan shine ze komar da kai kaman da na amince ka aureta..."
Hajiya tayi maganan tana share hawayenta.

Da sauri ya mike zaune daga kwancen da yake yace
"Hajiya da gaske kin amince?"

Kai ta gyaɗa tana kallon tsantsar farin cikin da ya bayyana a fuskanshi, yace
"Hajiya zainab fa"

Kiranta hajiya tayi a waya sbd tana gidansu wanka, kai tsaye tace itama ta amince idan har itace zata saka walwalanshi ya dawo kaman da.

Mantawa yayi da yana fushi da Hidayat a take yayi unblocking layinta ya fara kira...

***

"Rashida kiyi hakuri ki bar fushin nan haka kiji wani labari! Tun kwana biyar baya nake son sanar dake sede bamu samu zama ba"

"me zaki gayamin bayan abun takaici da kunyar da kika aikata?"

Dariya sossai hidayat tayi don kwanakin nan walwalanta na daban ne, bata taɓa jin sanyin farin ciki me tafiya da natsuwa me kwantar da hankali ba se a tsakankanin nan, kwarai Raed daban ne cikin maza, dukda baya tare da ita yana kashe ta da soyayyar da bata tunani ko a labari akwai wadda ya kusanto irin tashi.

"Shi wadda kike taya fushin ya ma mance an yi abun yana cikin walwala da kwanciyar hankali ke kina nan kina cin magani"

Da sauri Rashida ta kalleta tace
"ban fahimce ki ba?"

Wuri guda hidayat ta kurawa idanu tace
"Rashida wallahi ban san sa'adda soyayyar Raed tayi mun mugun kamu ba, ban farga ba seda ya furta min, ban kuma tabbatar ba seda ya janye jikinshi daga gareni na kwanaki kusan takwas fasalta miki irin damuwar da na shiga a sannan ɓata lokaci ne, ban hakikance cewa idan babu shi rayuwata tana cikin hatsari ba seda ya fara dafa ni da zazzafar soyayyarsa me narkar da zuciya, Rashida ina me tabbatar miki ban taɓa son abu makamancin soyayyar da nake yiwa Raed a yanzu ba.."

Ihu Rashida ta kurma tana rungumeta cikin farin ciki tace
"kaji min matar nan! Shine kika barni ina nan ina ta fushina ku kuna nan kuna ƙonewa! Zan rama ne"

Dariya kawai hidayat tayi, Rashida zata sake magana wayan hidayat ya ɗauki ƙara, duk idanu suka mayar kai se a lokacin Hidayat ta tuna da ya hamza ma ashe fushi yake da ita tun daga ranar da Raed yayi proposing mata.

Kallon Rashida tayi da idanun ya zan yi dashi tayi, rashida tayi shrugging kafaɗa, bata dauka ba kaman yadda be hakura da jera mata kira ba.

Seda ta dawo gida ta ɗauki call nashi..
"Hidayat! Kiyi hak'uri"

Tace
"no baka min komai ba"

Yace
"idan da ban yi miki komai ba da baki ƙi ɗaga wayana a ringing na farko ba, na san kuma kina gani"

Shiru tayi mishi, yace
"Hidayat ko wanene dole ne ya shiga damuwa makamancin wadda na shiga idan yaga ana mai barazana akan soyayyarsa, baƙin cikin da nake ciki ya hana in saurare ki, da gaske Raed proposing miki rannan yayi?"

Ajiyar zuciya ta sauke tace
"Ya hamza ya zainab? Har yanzu bata sauka ba?"

Lumshe idanu yayi ya buɗe yace
"ta sauka, ta samu da namiji"

Cikin farin ciki tace
"Alhamdulillah! Allah ya raya mana ya dayyaba"

Yace
"Ameen! Hidaya Albishir"

Tace
"Goro fari Kal"

"Hajiya ta amince da aurenmu! Zainab ma ta amince da kasancewarmu family guda"
Ya faɗa cikin farin ciki.

Rassss haka gaban hidayat ya faɗi, dankari! Yanzu ya zata yi? Me zata cewa ya hamza? Ta ina zata fara? Ya Allah, ta ambata tana lumshe idanunta.

"Hidayat!"
Ya kira sunanta don tabbatar da tana kan layin sede bata iya ta amsa ba.. A sanyaye ya ɗaga wayan daga kunnenshi ya kalla yaga yana reading ya sake mayarwa ya ambaci sunanta....!

#Vote
#share
#comment

                🖤Gureenjoh🖤

Pokračovat ve čtení

Mohlo by se ti líbit

57.7K 6.4K 37
Rashi ba shi kaɗai yake samar da giɓi a rayuwa ba. Wani yana doron ƙasa amma dalilai kan sa wanzuwarsa ta kasa amfanar da makusantansa. Me zai faru d...
6.2K 234 25
labarin soyayya mai ciki da darussa iri iri mai masu tsayawa a zuci..masoyane suke nuna ma juna tsana marar adadi rana d'aya lokaci d'aya kiyaiyar ta...
38.8K 2K 19
Labarin sanyayyar tacacciyar soyayyar ruhi biyu.. Wanda akai wa auren dole da juna, Amman basu san da hakan ba. Shin ya zaman nasu zai kaya idan suka...
10.1K 686 15
Dannar kirji... Gajeren labari mai dauke da darussa kala kala na wata uwargidah da akaiwa abokiyar zama(amarya)😻💕..NA MRS JH AND MSS XOXO