MAGANA TA ƘARE

By zm-chubado

163 19 0

Ya kasance mutum kamar kowa, amma ɗabi'unsa da mu'amalarsa sunsha ban-ban dana sauran jama'a. murmushinsa rag... More

EPISODE 1
EPISODE 2
EPISODE 4
EPISODE 5
EPISODE 6
EPISODE 7
EPISODE 8
EPISODE 9
EPISODE 10

EPISODE 3

9 1 0
By zm-chubado


MAGANA TA ƘARE
true life story

Mallakar: chubaɗo✍️

Banyi editing ba 🙅‍♀️

03

___✍️Wannan shine kuskure mafi girma data aikata a rayiwarta na Taimakon Wajagal, jawota Nura yayi lokaci guda kuma ya wanka mata wani lafiyayyen mari yace "shikenan gashinan kinjanyo mana bala'i Hajjo taya kike tunanin zamu iya tserewa waƴan nan gungun ƴan daban?" Fashewa tayi da wani irin kuka sannan ta kalleshi jikinta na wani irin Rawa tace "yaya na shiga uku yanzu ya zanyi kenan ? Wllh nasan idan suka kamani kasheni kawai zasuyi!!!" Zarya Nura ya farayi zuciyarsa kamar zata faso qirjinsa sabida tsoro

Buga ƙofar gidan suka shigari inda wasunsu kuma ke karta makamansu a jikin dandamalin simintin dake ƙofar gidan, ganin da sukia wankin hula na ƙoƙarin kaisu ga dare ne yasa Suka shiga ƙoƙarin ɓalle ƙofar daga Nura har Hajjo jikinsu rawa yake sabida tsabar tsoro batama san ta saki fitsari ba, da gudu Hajjo ta shiga Ɗakinsu tareda bushe fitilar ƙwan da Innarta ta kunna sannan ta nemi lingun gadon ƙarfamsu ta shige tana maida numfashi

Hayaniya ce ta kaure kafin kace me Samba da Ɗan-calangi sun kwaso zugar su don kawoma Wajagal ɗauki, nanfa aka kacame tsakanin ƴan-Daban ƙofar wambai da kuma na Unguwar Zage ganin da sukai bazasuyi riba bane yasa suka gudu se'a lokacin suka ankara da babu Wajagal a gurin nanfa gabaɗayansu hankalinsu yay mugun tashi, Ɗan-calangi ne ya kalli sauran yace "nifa ina tunanin wancan gidan ya shiga shiyasa harsu Tagarai suke ƙoƙarin ɓalla ƙofa, kawai musa kai mu duba" Samba ne ya shiga gidan yana ƙwala masa kira amma kuma ɗib babu motsin kowa, wata cocilan ya zaro daga aljihun gajeran wandonsa me bala'in haske ya kunna

Idansa ne ya sauka akan Nura wanda ya tura kansa cikin tukwanan dake jere a kicin ɗinsu, takawa yay har inda yake sannan ya dafashi wata Uwar ƙara ya saki tareda faɗin "don Manzon Allah kuyi haƙuri wllh bani bane Hajjo ce ta ɓoyeshi!" ya faɗi hakan jikinsa na ɓari kamar mazari. Fizgoshi yayi zuwa waje tareda haske masa idanu da fitilar dake hannunsa yace "dilla wace wata Hajjo? Zaka fito da itane kosena tsarge ma ciki da wuƙa?" da sauri ya miƙe dukya gama kiɗimewa ya shiga ɗakin yana ƙwalawa Hajjo wadda ke maƙale a bayan gado kira, tana jinsa amma taƙi fitowa sanadin hargowar kiran dayake mata ne ya farkar da Inno daga nannauyan baccin daya ɗauketa, yatsina Fuska tayi tareda zaro ƙaramar cocilan ɗinta datake ɓoyewa a ƙasan filo ta kunna cikeda faɗa ta kalli Nura tace "Nura me kake har yanzu baka kwanta ba da tsohon daran nan?" kallonta kawai yake amma ya kasa magana sabida tsabar yanda yake a tsorace, ba abinda ke karyo masa illa gumi hakan yasa Inno ta tashi daga kwancen datake ta tsira masa ido tace " lafiya kuwa Nura ina hajjo take?" hajjo wadda ke maƙale a bayan gado se'a lokacin ta fito, janta Nura ya farayi tana tirjewa batareda ya bawa inno Amsa ba yay waje yana zuwa ya hankaɗo ta gaba yace "itace ta ɓoyeshi ku tambayeta tasan komai" Fashewa da kuka Hajjo tayi tareda durƙusawa a kan ƙafafuwanta jikinta se ɓari yake tace "wllh bansan komai ba nifa kawai tausayinsa naji shiyasa nayi hakan amma don Allah kuyi haƙuri wll....... "Dalla rufe mana baki muje ki nuna mana inda yake!" Samba yadaka mata wata uwar tsawa wadda tasa Inno dake ɗaki ta fito a kiɗime da ƴar cocilan ɗinta a hannu.

Tsayawa tayi a baki ƙofa tareda dafe ƙirji tace "innanillahiwa'inna'ilaihirraji'un!" da sauri ta koma ɗaki ta ɗakko zani ta nufi inda Hajjo ke tsugune tana kuka ta miƙa mata tace "haba bayin Allah meya kawoku gidan Mu da wannan daren sabida Allah? Sannan kuma me ƴata tai muku dazaku sata gaba a irin wannan halin tana Mace?" rasa wanda ze bata amsa akai a cikinsu illa kallonta kawai da sukeyi tamkar waƴanda suka warke makanta, ɗago Hajjo dake kuka tayi tace "Hajjo meya haɗaki da waƴannan bayin Allah?" tsagaita kukan datakeyi Hajjo tayi sannan ta kalli Inno tace "damafa uhmm Wajagal ne na gani ya baɗi dabda bakin bola, wasu zugar ƴan-daba sun taho daga hanyar ƙofar wambai suna nemansa zasu kasheshi shine fa na kwance zani na na rufa masa kuma na juye masa bolar gidan nan akansa, to Ashe waƴannan sun ganni shine sukazo kamani!!" Hajjo ta faɗi hakan tana rushewa da kuka.

Wata irin shewa suka fara wasu kuma daga cikinsu suka fara busa ƙahon Farauta zanin hannunta Inno ta miƙa mata ta karɓa tareda ɗaurawa a ƙugunta fita sukai gabaɗayansu su kuma su Hajjo suka koma ɗaki zuciyarsu na bugawa musamman Nura dayake mugun matsoraci kamar ba namiji ba, kamar yanda ta gaya musun kuwa hakan ne yaye zanin sukai bolar ta zube a ƙasa sannan suka kinkimeshi zuwa Kangonsu dake bayan Marinar zage, yaye wandon jikinsa sukai har zuwa cinyarsa sannan Samba ya zuba masa ruwan Giya a Ciwon nanda nan kuga kumfar azaba ta fara tashi wadda tasa Wajagal ya farka a mugun kiɗime, bayan ya gama wanke masa ne ya ɗakko wani garin magani ya zuba masa akan ciwon nan da nan gumin azaba ya fara keto masa don sosai yankan ya shiga cikin naman cinyarsa, yana gama sa mishi maganin A nan take ya ɓingire da baccin wahala a gurin se maida numfashi yakeyi

Washe garin Ranar

Kamar yanda mutanan gidan suka sabayi a kowacce rana yauma hakanne, sedai saɓanin kullum dukansu a zaune suke saman tabarma idan ka cire Umma wadda ta ɗaura da zaman ɗaki sabida Habaicin su Abuwa da Bintalo se kuma Sahura wadda ke zuba miya akan ɗimaman tuwo, dawowa tai ta zauna tareda tsoma hannu ta fara kai loma

Seda takai loma uku masu kyau sannan tace "ohni Allah wai tunda kuke da Hadiza a cikin gidannan tsahon shekaru kun taɓa ganin wani daga danginta yazo gaisheta ko kuma ita taje gunsu?"

Sheƙewa su Bintalo sukai da dariya sannan suka tafa hannu Abuwa ta kalli Sahura tace "yo kemadai kya faɗa tunda nidai na tare a gidannan muke tare dukda a nan nazo na sameta kafin mijin ta ya koma ga Allah ban taɓa ganin wani yazo daga cikin danginta ba, waya sani ma ko'a yawan duniya ya samota."ta faɗi hakan tana taɓe baki, kallon rainin hankali Bintalo ta watsa mata tace "ai wllh ko'a yawon duniya ya kwasota nasan dole tanada iyaye, nifa nafi danganta hakan da baki iyayenta sukai mata kuma suka sallamawa duniya ita, idan ba haka ba taya za'ai ta haifo wannan tsinannan ɗan daya gama zamewa kowa alaƙaƙai?" gabaɗyansu shiru sukai a lokacin da Zainab ta shigo cikin gidan sanyeda uniform ɗinta na islamiya, taɓe baki tayi lokacin dataga duk sunyi tsit sannan ta kyauda kai tace "Allah ya rabaku d cutar Munafincin datake ɗawainiya daku" babu wadda tai gangancin yi mata magana don mugun shayin yarinyar suke sabida tsiwarta, yanzun nan seta gayawa taƙadarin wanta wato Wajagal

Lomar Tuwo Sahuwa ta kuma kaiwa bakinta bayan ta haɗiye ta ta kallesu gabaɗayansu tace "Ni kunsan meyake ƙara ɗaure min kai a gameda matar nan?" girgiza mata kai sukai da sauri alamar a'a, wani dogon Fasali Sahura ta saki sannan tace "abinda yafi komai bani mamaki da ita shine kokunyar shiga cikin mutane sam batayi, wllh danice ita da tuni baƙin cikin duniya ya kaini kabari musamman ma na wanjen ɗan-hau ɗin" "ƙarfin imaninta da kuma tawakkalinta ne yafi naki shiyasa har take iya rungumar duk jarrabawar da ubangijinta yay mata!!" Atine wadda ke ɗaki tana sauraren kaf hirar da suke ta bawa Sahura amsa cikeda takaicinsu, labulan ɗakinta ta ɗaga tana kallonsu ɗaiɗai sannan taci gabada cewa "ai wllh gara Ibrahim so dubu tunda iya Daba ya tsaya baya haɗawa da satar kayan mutane, idan har zaki haɗa da ɗabi'ar ɗanki Habu wanda tun yana yaro yake fama da ɗabi'ar ɓeraye, in banda Rashin hankali da tunani irin naku ai na ruwa baya zagin kada sabida besaɓ ya zata kaya musu ba.!" tana kaiwa nan ta saki labulanta wanda hakan yay dedai da Shigowar Wajagal Gidan yana Ɗingisa Ƙafa se faman cijewa yake.

Haɗiye maganganunsu sukayi ko wacce ta miƙe ta shiga ɗakinta tana sauke ajiyar zuciya, hamdaƙa suka shiga jerawa da Wajagal beji irin tijarar da suka gama zubawa Uwarsa ba, kansa a ƙasa ya isa ƙofar ɗakinsu Sallama yayi fuskarsa a ɗan sake kaman bashi ba ya shiga ɗakin a hankali.

Umma dake kwashe farar Shinkafa kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta tareda maida hankalinta ga aikin gabanta, ɗan murmushi yayi kaɗan wanda bekai zuciya ba yace "Umma!!!" ɗagowa tai idanunta na shirin kawo ruwa yay saurin dakatar da ita ta hanyar girgiza mata kai yace "don Girman Allah Ummah karki bari waƴan nan hawayen dake kwance saman idanunki su zubo, idan kikai hakan a madadin Rayuwata ta gyaru wllh ƙara lalacewa zatayi!" sinkuyar da kanta tayi ƙasa tareda ɗaukar Robar dake gabanta ta zuba masa Abinci tace "mai zan zuba maka ko miya?" takowa yay zuwa gabanta se'a lokacin ta lura da yankan dake cinyarsa, miƙewa tayi tareda shigewa ɗaki cikin hanzari ta fito da wata baƙar jaka a hannunta wani baƙin garin magani ta ɗakko a ciki sannan ta kama hannunsa ta zaunar dashi, ɗaurin dake jikin cinyar ta kwance sannan ta fara barbaɗa masa maganin a saman ciwon.

Yatsina Fuska ya farayi sabida zafin dayakeji har tsakiyar kwanyar kansa, riƙe hannunta yay da sauri sabida zafin maganin yayi yawa ɗagowa tayi cikin yanayin rarrashi tace "nasan akwai zafi amma ka ƙara daurewa ina gama saka maka kai kanka zakaji daɗi a jikinka Ibrahim" ta ƙare maganar tana zubar da ƙwallar tausayin makomar ɗanta guda ɗaya tilo namiji wanda ya zaɓawa kansa harkar Daba.

****

Zahra ce zane saman lintsumemiyan kujerar dake folon ta harɗe ƙafa tana kurɓa sassanyan juice ɗin data zuba a cup ɗin dake hannunta, ita kaɗai se faman murmushi take tamkar wadda ta samu matsalar ƙwaƙwalwa ba komai take tunani ba illa Wajagal wanda ya gama mamaye duk wani lungu da saƙo na zuciyar ta. Wata nannauyar ajiyar zuciya ta saki lokaci guda kuma yanayin fuskarta ya sauya data tuna irin sonda takewa mutumin dama besan tanayi ba.

Wata siririyar ƙwalla ce ta samu gurbin taruwa a cikin fararen idanunta, a hankali ta sakesu zirrr suka zubo mata azalzalanta zuciyarta ta shigayi cikeda begen Ibrahim Wajagal wanda a yanzu takewa laƙabi da annurin zuciyarta, tambaya ɗayace take mata yawo a saman zuciyarta shine "ya akai ma ta kamuda son wannan bawan Allahn wanda takejin cewar a shirye take ta sadaukar masa da duk abinda ya kasamce mallakinta muddin ya amince zeyi rayuwa da ita a matsayin mata a gareshi, miƙewa tayi da sauri ta haura upstairs in Les then 5minute ta fito sanyeda haɗaɗɗiyan jallabiya baƙa siɗik da ita, a ɗaki ta sami mahaifiyanta Hajiya Shafa'atou

Faɗaɗa murmushinta tayi tace "daughter ina zaki haka da ranar nan?" ɗan murmushi tayi kaɗan wanda ke ƙara mata kyau tace "Momy zanje wajen Gidansu Amina ne kinsan munada makaranta gobe" murmushi Momyn ta mata sannan tace "to Allah ya bada sa'a ki gaida mamanta" juyawa tayi a ɗan hanzarce don idan bataga wajagal ba tabbas bazata iya bacci ba, bayan ta fito daga gida kalle-kalle ta farayi don harga Allah batasan gidansu ba tunda ba fitowa takeyi kullum ba

Tafiya taɗanyi kaɗan nesa da gidansu sannan ta Samu wata yarinyar dake suyar Awara a ƙofar gidansu tace "ke don Allah inane gidansu Wajagal?" yarinyr ta ɗago da sauri tana kallonta sabida mamaki batayi magana ba illa nuni datai mata da gidan, murmushi tai mata sannan tace "nagode sosai" cikin nutsuwa isa ƙofar gidan ba tareda tunani komai ba ta kunna kai zuwa ciki bakinta ɗauke da sallama, babu kowa a tsakar gidan se Nadiya wadda ke share gurinda tai wanke-wanke tsayawa Nadiya tayi daga barin sharar tana kallonta da fara'a tace "wa kike nema?"

Kai tsaye Zahra tace "Wajagal nake nema don Allah" nan da nan fara'ar dake kan fuskar Nadiya ta ɗauke tamkar bata taɓa dariya ba, wani ɗan iskan kallo ta shiga watsa mata wanda yasa ita kanta zahran taji tasha jinin jikinta zatai magana kenan se Gashi ya shigo Gidan idanunsa sunyi wani irin ja kamar ba nasa ba

Da alama a kusa zuciyar sa take kallon daya watsa mata ne yasa zuciyarta ta buga da mugun ƙarfi amma kuma seta dake batareda ta nuna ba.............. Kallon tsaf yake binta dashi ba tareda yayi magana ba ya raba ta gefanta ze wuce, da sauri Zahra tace "uhm dama gurinka nazo don Allah" tsayawa yay cak batareda ya juyo ba, wata irin juyowa yay tareda kafeta da shanyayyun idanunsa yace "lafiya dai ko?" ɗaga masa kai tayi alamar ae, "Muje to" Zahra ta faɗa tareda juyawa zuwa soran gidan, samun kansa yay da kasai mata musu se kawai yabi bayanta suka koma soran.

Shidai kawai kallonta yake can kuma seyay ƙasa da kansa don be saba tsayawa da mace ba, murmushi Zahra tayi sannan tace "Sunana Zahra tajuddeen mai-gwanjo" ɗagowa yay da sauri jin sunan data faɗa sekuma ya sake sunkuyar da kansa beyi magana ba, zahra ta sauke ajiyar Zuciya sannan ta kalleshi tace "Tun daran daka shigo gidan mu idanuna suka sauka a kanka, bayaɓ ka tafi a duniya naji babu wanda zuciyata keso da ƙauna sekai ban damu da irin kallon dazakai min ba amma nidai kawai ina matiƙar ƙaunarka a zujiya ta" ɗagowa yay yana binta da wani irin kallo wanda ta rasa gane ma'anarsa balle ta fahimta, nunata da yatsa yay yace "karki ƙara zuwa gidan nan, idan kuma kika sake zuwa na rantse da Allah sena kafa miki tahirin da bazaki taɓa mantawa ba" yana kawaiwa nan ya daka mata wata uwar tsawa dayasata firgice ta fita da gudu tana kuka, tsaki yay tareda komawa cikin gidan nan ma a tsugune yaga Nadiya tanata gurzar kukan besan na menene ba shigowar Mahaifinta ne yasa Wajagal yay gaba ba tareda ya tambayeta dalilin kukan nata ba

Ɗakinsu ya shiga da sallama Amma umma bata nan Se Zainab wadda kecin abinci, zama yay tareda sa hannu a kwanon datakeci ya fara ci shima se faman ɗaure fuska yakeyi

Ina gdiya sosai gareku mabiya wannan littafin, ina ganin saqwanninku tareda yawan addu'o'inku🥰

Wajagal fans ina gaisheku kyauta 😂😂😂

comment

Continue Reading

You'll Also Like

20.1K 11 7
a threesome about some teachers who just wanna have a good time 👍 none of this is real btw
38.5K 5K 50
"ඒයි ඇටිකිච්ච ඔහොම ඉන්නවා" "නේත්‍ර, නේත්‍ර... මගේ නම නේත්‍ර" "මොකද උඹේ කට ඔච්චර සද්දෙ, මට ඔය වයසට වඩා උඩ පනින්න දඟලන ඇටි කිච්චන්ව පේන්න බෑ. ඒ නිසා මට...
9.4K 31 18
This is the second instalment to my 3 Part series of Books about a Young Blonde Teen Girl who suddenly starts to loose control of her bladder and bow...
31.4K 6.6K 35
OPEN! Join a community of passionate readers, where the love of literature meets a welcoming and professional atmosphere.