A SIMPLE DARE (WASA DA SO)

By marteybee

431 7 16

More

new book
Page 2
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9
Page ten
Page 11
Page 12
Page 13
Page 14
Page 15
Page 16
Page 17
Page 18
Page 19
Page 20/21
Page22/23
Page 24/25

Page 3

20 0 0
By marteybee

✨✨
        A
SIMPLE

DARE

                              ✨✨

(WASA DA SO)

WRITTEN AND STORY
                   BY
NERNAH MARYAM
             (MEEMARH)

             Kofa a bude take ga duk me son yin joining group dina😌,Amman Hajiya don Allah in kin san ba yin comment ko karanta littafi na zai kawo ki ba I beg you in the name of Allah kiyi zaman ki ba sai kin shigo ba!!haka zalika wanann group din na mata ne zalla don Allah Maza should stay away from my group👏

       My What's app group link👇🏻
        
 
           https://chat.whatsapp.com/EUrVVaKJnIBDTlQsxurZv0

Bismillahi Rahmanin Raheem............

(    In the name of Allah the most beneficient,the most merciful)

 
  Kofa a bude ta ke ga duk wani me good quality product da ya ke son Advertising ɗin shi,as Kaya masu kyau,da inganci (TALLAH) should contact me via :
                              08100046388

              Page 3️⃣

       TALLA!!TALLA!!TALLA!!!

       https://chat.whatsapp.com/ImtxMSS1tuSKqvBpPqc03P

Assalamu'alaikum sisters🤗
KAMSHI* mace Mai kima, mace Mai daraja, mace Mai izza, mace Mai aji itace tasan darajan kamshi, if your perfume is not unique hajiyata you're just using ordinary air freshener🤣, hajiyata ko nawa Zaki kashe indai a turare ne baki Fadi ba😘 matan da suka gane suka San yanda zasu kankaro da martabar su, suke amfani da turare, a *BAKHOOR BY FAIXY* Zaki Sami Main chic, Bachelor, Husband snatcher, Her royal sexiness, Mysterious girl, Pleasure, Boovilous, White khumra, Maroon khumra, Black khumra, Hair perfume, Turaren wanka, Turaren  wuta, Turaren tsuguno, Turaren mopping,Turaren carpet Shu'umat khumra,and more, yar uwa kar kibari abaki lbr, (wholesale and retail) WhatsApp 09067621681, siyan na gari Maida kudi gida🥳

Instagram @Bakhoor_by_faixy
        

     ******************************

      Wata doguwar tsaki Sabeeha  ta ja,tare  da watsa wa Zuhran harara,sannan ta riko hannun ta gam don sarai ta san za ta iya guduwa ta bar ta,a yanda take jin zuciyar ta in ba ta ga na cikin motar nan ta fada mishi magana ba hankalin ta ba zai taba kwanciya ba.

A mugun furgice Zuhra tace "Goofy angel ki yi wa Allah ki zo mu tafi,ko kin san su waye wannan kuwa?Kin san motar wa kika bugawa wa stone?Goofy angel kin san su kuwa,yau mun shiga uku Wlhy uban mu za su ci,don sam ba su da mutunci Wallahi"a zafafe Sabeeha tace "saidai su ci uban ki Zuhra domin me cin uban na sai ya shirya don yana kasa,Wlhy Zuhra ban damu da ko dan uban Waye ba,laifi aka mun dole ne kuma a bani hakuri,domin an shiga rayuwa
ta,a bisa haka yau nayi missing ban bada assignment dina akan time ba,Zuhra and na ga motar ki ce kar na dau action?Wallahi saidai ayi duk abinda za a yi amman sai na fada ma wanda ke tuka motar nan abinda ke rai na,gaba ba zai kuma yi wa wata abinda yayi mun ba"ta kare tana hararan Zuhran.

A raunane Zuhra tace "Sabeeha Wlhy reverse suke yi nan suke dawowa,ganin ba mu isa yanda suke ba har yanzu,Wlhy Sabeeha in baki sani ba to ki sani yau kashin mu ya bushe domin kin tabo Rocket gangs,Wlhy basu da mutunci kowa ya san su don sun yi kaurin suna sosai gurin cin mutuncin bayin Allah"a daidai lokacin da motar ta tsaya dab da yanda suke,tsaki Sabeeha ta ja sanann ta yi gaba tana fadin "wannan kuma ke kika sani,in kina biyo ni mu dau fansa bismillah,in kuma baki iya wa sai ki koma hostel na gode,amman Wlhy babu uban da zai hana ni yi masa magana"ta kare tana nufan inda driver seat yake domin duk tunanin ta mutum daya ke tuka motar,and burin ta su hada ido ta ga Waye shi hakan da Zuhra ke masifan tsoron shi,don ita sam wlhy bata ma san shi ba,ganin ta nufa gurin ne ya sanya jiki a sanyaye Zuhra ta biyo bayan ta,idanu ta na cikowa da hawaye,tana me yarfe hannu domin sarai ta san su waye yan Rocket gangs,a gaban ta suka zage tare da ci  wa wata mutunci saboda dayan su yace yana son ta inda ita kuma ta ke musu forming big girl tare da jan class don yar gidan masu kudi ce yarinyar,Wlhy a tsakiyar makaranta suka sheka mata ruwan sanyi tunda daga sama har kasa,tare da yi mata zagin tsame nama,inda kuwa babu wanda yace da su pimm daga cikin malamai don zan iya cewa ma tsoron tanka su ake don kudin iyayen su,yarinyar sai da tayi kwanaki bata zo school ba don ba karamin tsinka ta suka yi ba,karshe da ke ba kunya gare ta ba ta dawo tare da amsa tayin soyayayan,shike nan kuma komai ya wuce,yanda kowa ma ya fahimta shine in kana son kan ka da lafiya to stay away from Rocket gang don yan gangs din basu da mutunci,sanann ciwa mutum mutunci abu ne da ya fi shan ruwa yi musu sauki,ba su cika shiga harkan mutane ba,gwara ma mata a hakan ma sai sun ga kin cika mace kina fama da isa da izza to a nan ne za su shigo rayuwar ki don gyara miki zama,cases akan su ya fi dubu a BUK don fittinan nu ne na kin karewa.

  Su biyar ne a cikin gang din nasu,kuma ko wanne dan ji da kan shi ne domin suna da abun jin kan,don Masha Allah duk ciki babu wanda za ka kalla baka so ka kuma kallon sa ba,don Allah ya ba su kyau saida babu kyan hali,sannan gaba dayan su iyayen su masu shegen kudi ne,don a ciki akwai yaron Deputy Gov,akwai yaran Sen sai kuma sauran yaran Attajirai ne na gaske da ke garin Kano da kewaye kowa ya san waye ubanun su,hakan ya basu daman tsula tsiyar su inda ran su ke so,don sam ba ganin kowa suke da gashin ido ba,ka sake ka shiga hannun su ne su hadu su ci ma uba.

FIK shine gang leader domin duk ciki ya fi su kyau,isa izza dagun kai,ilimi kudi tare da neman magana,saidai sam Allah ya tsare shi baya neman mata,Nabeel Attahir yaron Deputy gov ne babu hatsabibi ciki irin shi,domin kan shi ya fi na kawo gil gil,shi kam dan komai da ruwan ka ne,Jawad Harooun shima wani dan Attajirin ne shima sam bayi da mutunci ba kuma yi da hakuri,duk da zan iya cewa duk ba su da hakurin don kiris suke jira su dau mataki,Farouq Abdallah shima dan wani Minister ne yaro me ji da takama da arzikin baban shi,kunne kuwa iya na kashi don sam baya ji,sai na karshen su Akram Muhammad dan gidan Senator ne.

Gaba daya su biyar din nan bomb ne don Allah yayi su da mugun rashin ji,ko ince suka daura wa kan su,kun san ance wai sai hali ya zo daya ake abota to zan iya cewa halayen su ya zo daya,saidai inda ba a rasa ba suka banbanta, kaf  din su babu wanda za a ce yana da hakuri ko kuma ba ruwan shi,Final year suke duk su biyar din,inda suke karantar Business Administration,don masifa kaf suka hade baki kan babu wajen da za su karatu,don iyayen su ma Aminai ne so da sun so tura  su,ganin babu kasar da za su je ta  dauki iskancin su sai kasar mu ta gado ya sanya suka fada BUK,kaf cikin su Allah ya wadata su da ilimi tare da brain din daukan abu,amman sam ba karatun bane gaban su,addaba da fitina tare da sanya idanu a harkan mutane shine a gaban su,kowa da ke makarantar na tsoron su don ba karamin tantirai bane,ya sanya babu me fatan wani abu ya hada shi da su,don ci maka zarafi za suyi tare da yaga maka rigar mutunci,kuma haka suke in har ka taba daya to duk haduwa za suyi su ci maka mutunci,don wanda be san su sosai ba ma dauka za kayi yan uwan juna ne don yanda suke maida damuwar daya ta zamo na su,akwai kyakkyawar alaka tare da fahimta a tsakanin su,sannan sosai suke kauna tare da kula da junan su,hakan ya sanya suka hade guri guda tare da creating gang din su su biyar tare da sanya mata suna Rocket Gang,inda kuwa suka yi kaurin suna ba iya BUK ba,har cikin Kano an san da su.

  Kamar wani hadin baki,a tare suka bude murafen motar tare da ziro kafafuwan su waje wanda ke sanye duk cikin takalma masu masifan kyau da tsada,Masha Allah na furta a sanda duk suka fito domin kyawawane saidai FIK ya fi su kyau domin fari ne shi sol,kamar balarabe tsalle yayi tare da dalle wa ya zauna kan motar tare da folding arms din shi,inda a take su Nabeel ma suka jinginu jikin motar tare da folding arms su ma kamar yanda yayi,zan iya kiran hakan da dabi'ar su,ko tsoro babu a tattare da Sabeeha ganin maza zarata har biyar ba dayan da tayi expecting ba,ta tako cikin takun nutsuwa tare da isa gaban FIK don ta fahimci shike driving din motar,a yayin da Zuhra ta ja ta tsaya ban da fat fat babu abinda zuciyar ta ke yi.

  Idanun shi na cikin dark black shade yayin da ya dan turo cute lips din shi gaba,alamun masifa ce ke cin shi domin duk motacin shi babu wace yake so yake kuma jin dadin ta kamar wannan,shi sam Wlhy be kawo ma mace bace tayi masa wannan haukar,duk zaton shi na miji ne,saida Akram ya nuna masa ita ta mirror.

  Cikin sassanyar murya tace "Assalamu Alaika",kallo ya kare mata from head to toes ganin ta sanye da zunbuleliyar hijabi ya sanya shi kallon Nabeel yace cikin husky deep voice din shi "Gee to fa ga fa Musulimatun Abidatun yau tsaye a gaba na" duk kamar hadin baki suka kwashe da wata irin dariyar yan iska  a tare,ba karamin sosuwa ran Sabeeha yayi ba,amman sai ta daure tace "am very sure you are a Muslim ko ba komai addua nayi maka ya ci ka amsa dai"

  A zafafe Farouq yace "Ke dallah Malama kike ko Sharifiya,har wa za kiyi wa karyan addini??kalle mu da kyau ce miki aka yi mu din ba ma salla,don kin sako zumbuleliyar buhun nan shi yake nuna ke ta Allah ce?Waye be san halin ku ba,sai a sanya babbar hijabi kasa kuma Bum short ce"wata wawiyar dariyar suka kuma sakewa,kai Zuhra ta girgiza domin inda Sabeeha ta bi ta nata da Wlhy bata ma tsaida su ba,domin sam su babu abinda suke dauka serious a rayuwar su,komai da iskanci da wulakanci suke yin sa,ga dariyar wulakanci,cikin wannan dariyar sai su caka miki kalman da sai kin ji kamar ki kashe kan ki,ganin haka ya sanya ta saurin karasawa tare da kamo hannun Sabeehan kasa kasa tace "Goofy angel zo mu tafi kar mu zubar wa kan mu da mutunci,is of no use talking to them don ba ganewa za su yi ba"hannun ta ta fauce a zafafe tace "na rantse Zuhra babu inda zan je in suna jin kan su danye ne to nawa ko wuta be ma hau ba"

  "Keeeee me na ji kuna fada"Nabeel ya fada yana kare wa Zuhra kallo,da sauri tace "babu komai,kawai nace ta zo mu tafi gida ne daman yamma nayi"yanda tayi maganar duk a tsorace ya sanya su kara kwashe wa da muguwar dariya,a zafafe Sabeeha tace "Wlhy kun ji jiki,and ku gyara halin ku,yawan dariya ma ba halin musulmin kwarai bane,nau'ine na alamun mutuwar zuciya ace abu ba abu ba kun hau dariya,ko Manzon Allah SAW ya fi yawan murmushi akan dariya,and Wlhy duk sanda kuke irin wannan dariya Mala'iku za su tambayi ubangiji kan wai kyautar Aljanna aka bawa wanne yake wannan dariya haka??A yayin da Allah zai ce Aa sai su ce Allah ya tsine ma wane "ta kare tana hararan su.

  "Allahu Akbarrrrrrrrrrr,kai don Allah ku tafa mata"FIK yace yana kallon su Nabeel,a take kuwa suma suka sake kabbara tare da tafin rashin mutunci.

"Ni ban fada muku don ku min tafi ba,besides ba wannan bane a gaba na,dazu ka watsa mun ruwan laka da kuke shigowa school"da sauri yace "Nabeel what is Laaka??baki Jawad ya tabe sannan yace "Mud take nufi,kasan sai aukin zuwa school da shiga class amman brain din gashi ga shi nan ne"nan ma wani dariyar suka kuma sake wa.

"Haba guys is not fair yarinya ta gama muku wa'azi ku bi ta dariya Ai sai ku sa gobe ta ki sanya Buhun nata"Akram yace yana dariya haba nan ma suka kwashe da wata irin wawiyar dariya,kafin kuma duk suka hade rai,dan saukar da Shade din shi yayi tare da zuba mata idanu,sanann yayi mata blowing kiss 😘 "kin hadu fa yammata,I wish na gan ki dazu na ga yanda wanann Ugly face din naki zai yi looking lokacin da na watsa miki Mud,maybe sai kin fi Gorilla Muni"ya kare yana dariya nan suka kara kwashe wa da dariya sanann Nabeel yace "gashi daman kama take da Baby Gorilla,wannan ta gefen nata kuma Baby Elephant"Haba nan suka kara kwashe wa dariya.

Har wuya Sabeeha ta kai don bakin ciki da jin kalaman su,ranta in yayi dubu duk ya baci,tsaban haushi da bacin rai har idanu ta sun fara kada wa,Zuhra kam ma har ta fara hawaye wai ita ake kira da baby Elephant,ai duk laifin Sabeeha ne da ace ta zo tun wuri sun tafi da duk haka be faru ba,wai daman me take expecting ya tsunguna ya bata hakuri?Sam bata san Waye FIK ba,yau ma sun gode Allah sun yi musu da sauki,gudun kar su karasa ci musu mutunci ya sanya tayi saurin kamo hannun Sabeehan,kasa kasa tace da ita "in kina wa Allah da Manzon shi ki zo mu tafi,Wlhy wannan haukar su ya wuce duk yanda kika tsamani let's not embarrass ourselves wanda suka mana ma ya isa haka"bata iya ce da ita komai ba don in tace za ta bude baki ma zagi ne zai fito,amman ta dau alkwari ko ta tafi yau suka kuma haduwa sai ta rama wanann cin mutuncin da suka mata,haba abun yayi yawa wai ga Mari ga tsinka jaka,bin Zuhran tayi suka fara tafiya a hankali kamar wanda kwai ya fashe wa a jiki,inda saida ta galla masa harara,tafiyar da take yi a hankali be hana bum bum din ta juyawa ba,wanda sam ba wai da gangan take juya su ba,ganin suna kokarin barin su a gurin ne ya sanya FIK Sakun fi'to me masifar kara,don sam be ji a ran shi ya rama fasa mishi glass da tayi ba,tana ma hauka bayan tayi masa haka tayi tunanin walking away freely?Durkowa yayi daga saman motan tare da fara takowa ta bayan ta,a take kuwa su Nabeel suka yi shouting

  "Walking she's walking,she walk pass us"wani matsiyacin murmushi ya sake sannan yace "that's when I saw that she got fat ass"

  "Ass so fat,you stand right back"suka yi shouting back,hannu ya mike tare da nufan daidai bum bum din ta, yace "I wannan give her Papa pa"yana kokarin spanking ass din ta,tayi saurin juyowa tare da damkar hannun shi,ba tare da wata wata ba ta kwashe shi da wawan Mari har saidai glass din idanun shi fadowa kasa.

Sanann a zafafe ta  nuna masa yatsa "you are very very stupid for trying this kind of nonsense with me,you are stupid!!a fool!and wanda be san abinda yake yi ba,How dare you!!kana hauka ne?Ance maka kowa ne irin yan iskan matan da kake mu'amala da su,saboda ga ka dan iska you want to give me Papa pa,wallahi wannan kazamin hannun na ka ya taba ni sai nayi ma ka abinda har ka mutu ba za ka mance ni ba,Wawa dan iska kawai,ka watsa mun ruwa,ka sa nayi missing ban yi submitting din assignment dina ba,na zo don in sanar da kai abunda kayi mun,kai da bunch of fools din friends din ka kun hau dariya kamar wasu mahaukata sabon kamu,a karshe kuka zage mu,nayi hakuri zan tafi abuna and you did this,are you okay??ko babu mata ne a gidan ku?Kuna abu kamar wanda tarbiyya be wadace su ba,Wlhy in kuna ganin wai ana jin tsoron ku whatsoever ni bana jin tsoron ku,kuma daidai nake da ku,kar ku nutsu ku gyara rayuwar ku,ku cigaba da barin shedan na buga muku ganga ranar nadama na nan zuwa,wawaye,ta ja tsaki sanann ta juyo ta kalle shi,ka gode Marin ka kawai nayi Wlhy duk sanda ka sake kokarin mun magana ko taba ni da wanann kazamin hannun naka I will make sure to be your biggest nightmare,Allah ya shirya ku,ya sa ku gane Gaskiya ku gyara halayen ku,ko za ku ji dadin duniya da lahira,domin babu wani abun jin dadi da zama Dan iska!!"da sauri Zuhra da shock ya gama kashe ta ta janyo ta da karfin tsiya,tana kokarin faucewa haka suka wuce su bayan ta watsa musu kallon tsana,da haushi,saida ta tabbatar sun yi nisa da su sanann ta sake hannun ta,cikin mugun tsoro da firgici ta daura hannun ta a kai tare da matso kwalla "Sabeeha kin kashe mu wlhy,why will you slap him??Was that necessary??"

A zafafe tace "Dallah hold it Zuhra kar ki bata mun rai,duwawu na fa yake son dake wa Papa pa din nan a Bum bum dina yayi niyan wa da ke tarbiyya be wadace shi ba,and kina so na tsaya ya dake mun duwawu saboda ina tsoron shi?abunda yayi shi ya dace ne,Wawa sakarakaru irin su,cikin peace na je muyi magana amman ki ga cin mutucin da suka mana,ya dace abinda suka yi?"ta kare tana hararan Zuhran.

Ajiyar zuciya ta sauke "na sani ba su kyauta ba,amman Sabeeha wanann su haka suke basu da hankali sam wlhy ,why za ki biye musu,Sabeeha kin san wa kika mara kika fada mishi maganganu son ran ki kuwa??Ko kin san Waye FIK??wallahi ko cikin gang din nasu ma tsoron shi suke ji don duk ya fi su zafi da rashin mutunci"a tsawace Sabeeha tace "Ke dallah Zuhra ya ishe ni,to hell with him and the stupid gangs din nasa,hauka kike yayi mun haka na Kyalle shi,Wlhy ya gode wa Allah marin shi kawai nayi,in ke kina jin tsoron shi to Wlhy babu wanda nake tsoro banda Allah na,in ya fasa kashe ni ya raina Allah,in kin san isa ta za kiyi da wannan maganganun banzan to don Allah koma hostel ba sai kin raka ni ba,zan tafi abu na amman ba zai yu ki zo kina kuma bata mun rai ba,FIK Allah ne,ko dan shi dan masu kudi ya sanya zai yi duk iskancin da ya ga dama a Kyalle shi to Wlhy ba dai zai yi wa Sabeeha tayi shiru ba don na san ciwo da mutuncin kai na,ban raina uban kowa ba ban ga uban da zai raina ni ba"ta kare tana me jan dogon tsaki,shiru Zuhra tayi tare da bin bayan ta domin ko Karan hauka ya cije ta bata isa komawa Hostel ba what if suka tsare ta suka ci uban ta fa,saidai sam bata so  abinda Sabeehar tayi ba,yeah ta san ba su kyauta ba amman da bata mare shi ba,sannan zagin yayi yawa wanda tayi mishi,and Wlhy a yanda ta ke jin labarin su to sai sun sa zaman Kano ma ya gagare su don Wlhy babu abinda zai hana su daukan fansa,hawayen tausayin kan su ta share daidai lokacin Sabeeha ta tare me adaidai ta.

  "Ki koma hostel zan wuce gida sai kuma Monday don gobe weekend za a shiga"da sauri Zuhra ta dalo Napep din sanann tace "Mal mu je Kundila za ka kai mu"idanu Sabeehan ta zuba mata "Zuhra bina za kiyi?"

  "Tunani kike ki tafi ki bar ni,yasin yau gidan ku zan kwana"dariya sosai Sabeeha ta fashe da shi sanann ta girgiza kai,ta rasa irin wanann mugu tsoro na kawar ta,sam Zuhra bata son fada ko shiga rigima don akwai ta da tsoro,tun suna yara in ta ibo abu Sabeeha ke tsaya mata,don ita haka Allah yayi ta da karfin hali tare da strong heart kafin kace ka ga hawayen ta ma sai kayi da gaske,domin mace ce me karfin hali,ya sanya duk abinda zai yi causing mata damuwa take iya kan kokarin ta gurin ganin tayi avoiding faruwar sa,don tana da saurin hawa,da saurin fushi,har suka isa tana yi wa Zuhra masifa kan akan me za tace da bata mare shi ba,a gurin Zuhran ta karba kudin abun hawa ta biya sannan suka shigo gida,tana jin Hajiya Ladi na yaba musu habaici kan wai an gama dandin ke nan an dawo,ko kallon yanda take bata ma yi ba,banda tsaki da ta ja kasa kasa tare da jan hannun Zuhra suka shige sashin su,tana jin Hajiya na auna mata ashar tare da yi mata zagin cin mutunci amman ko juyowa bata yi ba domin bata da ma lokacin ta ,inda ranta ke saman nan in tace za ta tanka ta to Wlhy za ta iya kai su ga buguwa in hakan ta faru kuwa anyi abun kunya,saida duk suka yi wanka sannan Umma ta kawo musu abinci,ganin inda take ta kumbuare kumburan fuska ne ya sanya Umma tambayan ta kan lafiya?da sauri Zuhra ta bude baki don labarar ta wa Umma duk abunda ya faru dazu,Sabeeha tayi saurin fadin "babu komai Umma kawai Hajiya ce ta bata mun rai"kai Umma ta girgiza don ta san ba hakan bane domin inda sabo Sabeeha ta riga ta saba da halayen Hajiya Ladi tun abun nayi mata zafi har ya daina,domin Umman da kan ta ta zaunar da ita tare da yi mata nasiha game da hakuri da maida komai ba komai ba,ganin bata son sanar da ita abinda ke damun nata ne ya sanya ta fice wa daga dakin don bata son matsa mata,karshe ma maida abun tayi be  shafe ta ba don da ya shefe ta ko bata tambaya ba da kan ta za ta zo ta sanar da ita.

 
     Tun da ta bar gurin yake tsaye cak kamar an dasa shi a gurin,ko a mafarki zai iya cewa ba a taba daura hannu a jikin shi ba da sunan duka balle a zahiri,What the fuck wai shine yau wata kucakar yarinya ta mari tsadaddiyar fuskan shi,bayan fasa masa expensive glass din mota da tayi, shiru kawai yayi a gurin ya ma kasa ko motsa yatsar shi,su Nabeel ma inda ka san ruwa ya cinye su,duk mamaki da tsoro ne ya kama su,sai su ke ganin abun kamar a mafarki,don tayi taking din su duk by surprise,da kyar Nabeel ya iya daga kafafun shi tare da nufan inda yake tsaye kamar mutum mutumi.

  "Geee"ya kira sunan shi yana me dafa shoulder din shi,juyowa yayi idanun shi sun yi mugun kadawa sun koma jawur,jikin shi har bari yake tsaban bacin rai,cikin lallashi yace da shi "take it easy pls zo mu tafi",da kyar ya iya budan baki yace "Beel akwai mutane da suka ga abinda ya faru???"daman ya san abinda zai fara tambaya ke nan,thank god kuwa babu mutane a lokacin Ai da yau sun yi abun kunya.

"I don't think akwai wanda ya ga abunda ya faru let's get going pls babu amfanin tsayawar ka a nan"har ya budi baki zai yi magana sai kuma ya fasa ya juya zai nufi inda motar nasu yake,Nabeel ne ya tsunguna don dauko Shade din don ya san FIK na tsananin kaunar Shade din,da sauri yace da shi "is of no use daukan shi Beel bar shi kawai ka zo mu tafi"ganin inda ran shi yayi tsananin baci ya sanya Akram karban key din tare da cewa shi zai yi driving gudun kar su bar shi ya ja,ya je ya yarda su cikin rami,don in ran shi ya baci kamar wani me sabon hauka haka yake komawa,motar shiru don ko karan kidan ma babu,haka zalika kowa yayi shiru ana tunanin Sabeeha baiwar Allah da ta yanka wa FIK Mari,ta kuma fasa masa glass din mota,tare da yi musu zagin tsame nama,ko wanan su na saka da warwara irin matakin da ya dace a dauka a kan ta,tare da yin horo da cin mutuncin da ya dace ayi mata,da kyar ya iya budan baki yace "Akram kai ni Taheer guest palace don in na  je gida yanzu za a yi samun matsala,kun san halin Mom sarai"ba tare da musu ba kuwa ya dau hanyar Hotel din don sanin su ne sarai in dai Mom ta gan shi a halin da yake ciki to kuwa yau ba zaman lafiya,komawa yayi tare da lafe wa a jikin kujeran ya lumshe idanun shi,yana jin bakin shi har na daci zunzurutun bacin rai.

    Ko da suka isa key suka karba daman to regular customers ne,direct room 024 suka wuce duk su biyar din,inda Nabeel ne a gaba,ko da suka shiga cikin dakin kan gado FIK ya fada tare da dafe goshin shi yana jin inda zuciyar shi ke nauyi.

A zafafe Farouq yace "Guys wai har mun yi lalacewar da wata shegiya za ta daga hannu ta Mari dayan mu?Ta fasa mana glass sannan ta fadi duk abinda ta ga dama?"kamar jira yake a dauko zancen da sauri Nabeel ya cebe da cewa "Wlhy Farouq ba muyi ba Ai ko goma ta fadi Wlhy ta fi biyar"

  "Ni sam ban san garin yaya ba saukan Marin kawai muka ji,saboda ta ci liver,sa'an  ta daya sun bar gurin Wlhy da sai na sumar da yar iska,gaba ko dog din Rocket gang aka ce ta mara ba za ta yi ba dan uban ta da idanu kamar Aljanna"Akram ya kare yana jan tsaki.

Ihu FIK ya fasa tare da kai wa iska naushi,don sai yanzu abun ke kara dawo masa,da sauri Jawad da ke kusa da shi ya riko shi ganin yana kokarin mike wa,a zafafe yace "Jawad sakar ni,sakar mun hannu Jawad wai har ni ace wai ni wannan yarinyar za ta mara ta fada mun magana son ranta?Bayan fasa mun glass din mota da tayi,Jawad ni fa Mari na fa tayi right through my chic tana hauka ne??Dan uban ta!!Wlhy tallahi sai na dau fansa na rantse bata isa ba,ko Mom bata taba attempting daura hannun ta a jiki na ba balle wata jaka can daban,Wlhy tallahi billahil azim I must avenge this slap,ko da kuwa shine abu na karshe da zan yi in my life"ya kare yana nufan kofa bayan ya fauce hannun nashi daga rikon Jawad da sauri duk suka riko shi,domin ko hauka suke ba ta inda za su fara barin shi ya fita a yanda ran shi yake saman nan.

"Geee can you pls calm down let's talk this out pls?"Farouq ya fadi yana kallon shi,a zafafe yace "don't fucking tell me to calm down again Farouq!talk what out??so kake kace da ni ta ci bulus ke nan ko me?Ta Mari banza ke nan ko me?ta zagi banza ke nan kake son ce mun,in ba za ku zo mu je mu ci uwar ta ba then ku zauna I can do it alone"ya kare yana daukan car key din shi zai fita.

  "Look Farouq yana da point fa Geee fita a halin yanzu ba naka bane,ko ce ma aka yi abun mu be yi mana ciwo ba,Wlhy kai aka mara amman duk zafin a fuskan mu muka ji shi,dauka kake damuwar ka bata shafe mu ba?Kar ka manta ba fa kai kadai ta ci wa mutunci ba duk mu biyar ta ci mana,Rocket gang fa ta taba and you are expecting wai ta ci bulus?Haba kai kuwa ba a taba mu ba ma mun yi wa mutum balle an taba mu,Wlhy ko kowa zai yafe mata ka san halina sarai wlhy sai na tabbatar da na ci uban ta,sai nayi mata abinda ba za ta taba mantawa ba,amman for now try to relax abun kunya ne wlhy mu da muke firgita tare da bata wa mutane rai wai ace yau mace ne ta sanya ka irin bacin ran nan,ita din wa ita din banza Waye Uban ta waya san ta wa ta sani,da har za ta wa mutane karyan rashin kunya,kai dai kwantar da hankalin ka wlhy sai na sa ta zo ta duka a gaban kowa ta baka hakuri,take some water now ko za ka dan ji sanyi"Nabeel ya kare yana mika mishi goran ruwa,ba tare da musu ba kuwa ya karba ya fara shan ruwan don a halin da yake yanzu shima yana bukatar ya jika makoshin shi,jin maganganun Nabeel sun dan kwantar masa da hankali,don ya san halin Nabeel baya taba fada be cika ba,duk tsaye suke a kan shi har saida ya sha kusan half bottle,one thing da ke burge shi da friends din sa shine yanda suke maida damuwar dayan su na su,saida ya aje bottle din shima ya dan ji sanyi a cikin ran shi,karan sigari Nabeel ya mika mishi amman sai ya kwa da kai,ganin haka ya sanya shi maidawa aljihun shi,shiru dakin yayi kowa da tunanin shi don sun riga sun san ba zai kuma kula su ba domin akwai shi da zuciya kamar wani kuturu,kamar daga sama suka ji muryan shi yace

  "Wace ce ita??" Da sauri Nabeel yace "ita ba kowa bace kuma ban  tunanin yar wata ce duk da nima yau na fara ganin ta,amman  da ace wata shegiya ce da zan san da zaman ta a cikin BUK,ko akwai wanda ya san ta a cikin ku?"ya kare yana kallon su.

  "Sunan ta Sabeeha Uthman Dan yau,a Department din Food and Nutrition take,yar cikin Kanon nan ne amman ban san wani unguwa take ba,irin yaran nan ne da ba kowa ba kuma ba yaran kowa ba domin jeje take living life din ta,bata shiga harkan kowa kuma bata son  a shiga nata,tana saida Milk Candies(su Tuwan madara da iloka tare da gulisuwa),sanann tana yin baking kayan flour,tun randa na gan ta na so in toaster ta,sai aka ce da ni ita bata kula maza domin kaf fadin BUK babu wanda ta taba tsayawa ta saurara da sunan soyayya,and in kana son ka ga fushin ta to kace kana son ta,she hate love for God only knows why,don maza da yawa sun taya ta amman in vein don a inda na ji karatu ne a gaban ta,mutum daya take kula wa ita ce wanann kawar nata Zuhra Abdul-mudallif wanda muka gan su tare dazu,ganin haka ya sanya na watsar da kashin ta,don daman can ta burge ni ne yanda take tafiyar da rayuwar ta tare da kin shiga harkan mutane ya sa na ji sha'awar janyo ta cikin mu mu kara daga mata class don yarinyar ba karya ta hadu she get pretty face and big package,ashe ban sani ba mara mutunci ce"Akram ya kare yana zama akan kujera.

  "Sabeeha!!"duk su hudu suka maimata sunan nata,don wlhh duk ba su taba sanin ma da zaman ta ba, "kai dai Wlhy Akram yanzu in banda abun ka ina kyan da har za ka ce ka so janyo ta cikin mu?Fuska kamar na baby Gorilla,shegiya ashe ba yar gidan uban kowa bace har ta kai ta dauki filthy dirty hand din ta ta kwada masa Mari,har ta san ta zagi mutane,tana yar babu jikan ban baiwa kowa ajiya ba,sai shegen fadin rai kasan tsiyan ka da yaran talakawa ke nan,wlhy sai ta san ta taba mu"Farouq ya kare a zafafe.

"Yanzu dai me kuke ganin ya dace muyi mata,wanda za ta dade tana cikin bakin ciki kamar yanda ta bata mana rai don ina son ta ji fiye da abinda muka ji"Jawad ya tambaya, "yo kuwa me ya kamata banda ya wuce muyi wa yar iska daukan Amarya Wlhy ni da kaina zan dauko mana ita shi da ta mara ya fara barke yar iska in anyi dace ma fa Virgin ce don irin su munafukan banza ana forming na Allah na Allah a baki,amman  a boye kila buga iskancin ta take, tana nan tana cika baki kan bata son na miji bata kula maza watakil tana can tana iskancin ta ta bayan fage,don yan matan yanzu daddaya ne ake samun su cikakkun Virgin", "in kuma ba iskancin take ba ana can an baje cinya wa wata katuwa tana kwakwale ta"Akram yace, nan duk suka kwashe da dariyan iskanci sannan Nabeel ya cigaba "kun ga in ya gama hora yar iska sai mu ma mu je  mu kwashi na mu rabon"ya fada yana lashe baki don tuno inda take juyi jikin ta na girgiza.

  "Beel kai ma ka san sarai bana wanann layin ku fado wani shawarar dai domin nima ina da Yaya bana so wani yayi mata haka ba,besides bata mun ba balle har na ji sha'awar hada Jiki da kazamin jiki irin nata"ya kare yana yatsine fuska.

  "Okay why not mu hado mata abun da zaman BUK da garin Kano sai ya gagare ta ita da family din ta?Kar ka manta mune masu fada a ji a garin Kano so ta hanya mafi sauki za mu kore ta har shegiyar mayyar kawar tan nan"Jawad ya fada,mikewa zaune yayi sannan ya girgiza kai "Jawad more than this,in muka yi mata haka za su iya koma wa wani gari ta fara sabon school tare da saurin mancewa,she deserves more more than this,ina so nayi mata abunda har ta mutu ba za ta manta da ni ba,ina son barin mata tabona da har ta koma ga Allah duk sanda ta ji suna irin tawa sai ta tuno,I want to make her life a living hell and break her down"ya kare yana taunan lips.

"Yo ba shi ne nace da kai mu dauko yar iska tayi one week a dakin nan,kowa yayi abinda ya ke so da ita,don Allah wani punishment ne da ya wuce wannan guys??In har virgin ce Wlhy har ta mutu bata isa mantawa da mu ba,and haka za ta kare rayuwar ta cikin dumbin nadama da danasani,domin sanin kan ku ne ba karamin tashi hankalin mace ke yi ba yayin da wani daban ba mijin ta ba ya fara karban virginity din ta"ya kare hoping Allah ya sa duk su yarda da shawarar tashi domin daga ganin yarinyar za a fafata da ita a Oza room.

Tsaye ya mike sanann ya dan kalli Nabeel din kafin yace "Beel na fada maka sam bana wanann harkan ni fa ka ganni duk tsiya ta bana son Zina domin bashi ce ba zai yu in jawo ayi da nawa yaran ko yar uwa ta ba,and kai ma ya ci ace ka rage wannan halin son iskancin naka,in so samu ne ma yaci ace ka daina ,domin duk cikin mu kafi mu kaf son mata Wlhy,and na fada maka sam ni yarinyar bata mun ba ma balle na ji har zan iya hada Jiki da ita,na tsane ta wlhh bani da burin da ya wuce na ga wannan kwala kwalan idanun nata suna zubda hawaye,wannan shegen tsitsiyar hannun kuma da ta iya kwada mun mari tare da fasa mun mota,su zamo shi za ta daura a kai tare da goge hawayen da su,ina so na tusa mata bakin cikin da manta shi sai ya gagare ta,ina son nayi mata abinda sai ta tsani tare da nadamar zuwan ta duniya,ina son na kaskantar da ita tare da nuna mata ita ba kowa bace face yar talaka!!yar talaka wa kamar ta bata isa tayi mun abu ta zauna lafiya ba,Wlhy a yanda nake jin zuciya ta ko Raping din ta muka hadu muka yi Wlhy zuciya ta baza ta yi sanyi ba,don ana kwana biyu shike nan abun ya wuce ina son ya dau lokaci sosai kafin ta mance da wanene ni,so we have to think big amman drop yi mata daukan Amarya aside pls"ya kare yana taunan lips don har yanzu yana ganin saukan hannun ta a face din shi,jin haka ne ya sanya Nabeel dan Jan tsaki don sam ba haka ya so ba,gefe ya koma sanann yace "maybe wani cikin mu yana da better plan a mind din shi,coz nawa be yi ba"daga jin yanda yayi maganar duk sun san ran shi ne ya baci,hakan ya sanya FIK dakan shoulder din shi sanann yace "c'mon don't take what I said to heart mana,kasan ba haka nake nufi ba"harara ya dan watsa mishi sanann yace "uhmm"

Nan fa suka shiga kawo kalolin mugunta da irin abubuwan da za suyi wanda zai sanya Sabeeha kare rayuwar ta cikin kunci da danasani amman sam ya ce babu wanda yayi masa a rai,karshe ran su ne ya baci kowa ya ja baki yayi shiru don iya wa FIK sai Allahn da yayi shi,can kamar bayan mints 5 kamar wanda aka  tsinkula sai kuma ya dawo ya zauna ya kalli Akram sanann yace "Gee dazu da kake bada labarin yarinyar can kamar na ji ka ce wai ita bata Soyayya ko me ma"dan tsaki Akram ya ja sanann yace "yeah haka policy din ta yake wai ba ta soyayya,sanann bata kula ma maza,duk wani abun da ya shafi soyayya she don wash her hands and commot it from there"wata wawiyar dariya suka ga ya sake tare da tafa hannu sanann yayi shouting "Perfect!!"

Duk idanu wa suka zuba masa irin na lafiya,guri ya nema ya zauna sannan ya ce "Gee soyayyar ce bata taba ba,ko kuma daina yin shi tayi sabida Our Gender don sever her breakfast??"nan ma saida ya kara yin tsaki don maganar yarinyar ma haushi yake bashi kafin yace "ni dai a inda na ji ance bata taba soyayay ba,don duk nacin mutum saidai yayi ya hakuri don tace ita bata Soyayya"

Wata dariya ya kuma sake wa tare da kai wa kafadan Jawad duka sannan yace "Oh My God!!God you are so great,God you are so nice  to me,haba tun tuni mun tsaya wahala kan mu ga hanya nan mafi sauki mafi sauri wanda kuma zai fi cin uban ta,ta kuma dade bata man ta da mu ba cikin sauki"duk idanu suka watsa mishi don sam ba su fahimci inda ya dosa ba,sun ma yi mamakin ganin dariya kwance kan fuskan shi at this time inda ran shi yayi mugun bacin nan.

Farouq ne yace "Gee ba mu fa gane me kake nufi ba kamar Yaya ke nan?" Saida ya kuma dan dariya sanann yace "dadi na da kai Farouq gagagwa,kamar dai yanda kuka ji yeah na samo mana hanyar da za mu ci uban ta cikin ruwan sanyi,muyi mata dafi tayi lugub,kun san ta wani hanya???"ya tambaya yana smiling.

   "A ina za mu sani in baka sanar da mu ba,amman don Allah make sure da hanyar za ta wahala sosai don Wlhy abinda tayi mana ya tsaya mun a rai,babu dan iskan da ya taba fadi in fada da mu balle har ya zage mu har ta kai ga duka sai wanann me kama da yan ruwa"Jawad ya fada yana maida attention din shi kan FIK.

"Just calm down guys and listen to me,tunda na zauna nake tuannin yanda zan bi na ga mun kaskantar da yarinyar nan,Sabeeha take ko Nafisa?Sai kuma Akram ya ba mu labarin ta inda cikin sauki idea in yanda za muyi da ita ya zo mun,a duniyar da muke ciki yanzu babu abinda ya fi saurin wahala yam mata irin SOYAYYYA!!ko ina za ka ji cases din da ake ta fama da shi ke nan,wane yayi serving wance break fast,wace ta rabu da wane ta auri me kudi,ko kawar wace ta kwace wa wace saurayi,main problem din da ake fama da shi yanzu mostly akan soyayya ce,ka ga har ta kai ga wasu kwanciya gadon asibiti,and am very sure that baby Gorilla tsoron heart break take ya sanya ta kasa bude zuciyar ta ta saka wani gudun kar ya zo yayi betraying din ta at the end,kallo daya nayi mata na gane burgan ta duk
na karya ne,tana forming strong girl ne kawai but deep down she is  so soft and very Naive so kun ga destroying din ta ba zai mana wahala ba,tayi matukar kuskure da ta sanya hannu ta mare ni,da ace breaking glass din Fav car dina kawai tayi zan iya considering yafe mata,amman tunda ta mare ni harda zagi,I promise sai tayi kuka har ta gode wa Allah,dan Jim yayi sanann ya cigaba guys na yanke shawarar dating yarinyar nan,zan yi breaking record in neme ta,I will confess my feeling to her and Wlhy sai ta karbe ni ko tana so ko bata so,ba dai ta ce bata Soyayya ba to Wlhy sai ta fara a kai na,sai na sanya ta so ni fiye da yanda ta ke son rayuwar ta,zan sanya mata kauna ta da soyayya ta inda a karshe in na tashi rabuwa da ita na tashi serving din ta breakfast abun zai dame ta sosai har ciwon zuciya ya kama ta,zan koya mata yanda za ta ji dadin rayuwa da ni,zan nuna mata big big dreams,zan nuna mata abinda take missing all her life,I will shower her with unconditional love and affection a karshe kuma nayi breaking heart din ta,by doing that Wlhy na san har ta mutu ba za ta mance ni ba,domin ance ba a mance first love and lucky me Allah na so na bata taba yin soyayya ba am going to be her first so duk sanda na tashi barin ta kila sai ta kashe kan ta,ya kare yana smiling,so guys ya kuke ganin plan din nawa?"

Wata dariyar takaici Nabeel ya saka sanann yace "Wai FAIZAAN what the hell is wrong with your brain ne?For crying out loud upon all abubuwan da muka fada ka rasa wanda za ka dauka sai wanann,you dating her and making her fall for you after that ka zo kayi breaking heart din ta shine me?Duk daran dade wa za ta samu wani and dole za ta manta da kai,ni dai wanann idea din sam bata yi mun ba"

"Nabeel ke nan,kai ka san miye soyayya kuwa??ko da yake duk ba za mu sani ba tunda duk cikin mu babu wanda ke da serious girlfriend duk yan passing time ne,gwanda gwanda ma Jawad yana da one gongon girl da ya nace mata,so ask him ya zai ji in yau ta kira shi tace da shi bata taba son shi ba,kawai tayi using din shi ne  at the end tayi dumping din shi,how do you expect zai ji?a rayuwar nan ka san yanda zafin haka yake kuwa,you loving someone wholeheartedly and later on ka gano ashe be taba son ka ba after shima ya nuna maka duk duniya babu wanda ya ke so irin ka just tell me ya za ka ji?tunani ne da yawa zai zo ran ka,so for all this while daman using dina to catch cruise kawai aka yi ka gane Ai,and in her on case Wlhy da kyar in tayi saurin mance ni saboda ni ne zan zamo first lover din ta,and sai na bari ta gama shakuwa da ni zan fito na nuna mata ban taba son ta ba,wlh sai ta kusan mutuwa shike nan revenge din mu ya dauku,na yi tafiya ta tare da mancewa da ita "ya kare yana murmushi.

  "Yeah Faizaan soyayya akwai wahala oooo,and Wlhy in har yanda ka fada sai ta fara son ka za kayi breaking heart din ta to za ta dade abun nayi mata ciwo,domin har yanzu akwai natattaciyar Ex dina da har yau ta ki bari na,babu abinda ya fi ciwo kamar wasa da feelings and emotions din mutum,in aka samu weak person ma zai iya rasa rayuwar sa garin haka,amman tambaya ta shine taya ma za ta kula ka bayan ance ba ta kula samari?" "Dallah Kyalle shi Jawad shima ya san maganar banza yake yi,tana hauka ne ta kula ka bayan ta san abinda tayi maka,zuwan farko za ta fahimci ka zo ne don kayi mata wayo don ka Rama abunda tayi maka,and Wlhy daga ganin yarinyar nan kan ta babu alaman laushi za tayi wuyan shawo kan ta,and ba ma wannan ba what if along the line ka fada son ta da gaske?so tunda duk shawarar mu bata yi ma ba kawai a hakura a bar ta ta mari banza ta kuma zagi yaran banza"Nabeel ya kare yana tsaki.

"In har na cika FAIZAAN ISMA'IL KWAIRANGA to wlh sai na dau revenge akan Marin da yarinyar nan tayi mun,and Wlhy babu hanyar da za ta fi shan wahala trust me guys da ta wuce ta wannan hanyar don mata wawaye ne sam basu iya so ba,in har suna son na miji da body soul heart and komai nasu suke son su,ya sanya har yau suke wahala,don cikin sauki suke bari soyayyan mutum ya shiga fitar da shi kuma sai ka ga wasu har abada sun gagara,and abinda ke ba haushi yanda kuke behaving kamar ba ku gama sani na ba,Ni FAIZAAN ban so mata masu class da kyau tare da kudi yaran manya da suke ta bi na up and down sai in zo in so wannan kucakar yar talakawa?yar dariya yayi sannan yace never 👎 Kawai dai Wasa da Soyayar ta zan yi,in tabbatar na karya mata zuciya na sa ta a bakin ciki kamar yanda ta sanya ni,so ina so ka ma daina wanann tunanin"

  "Look Gee yarinyar nan Wlhy bata kula maza ni kai na nayi iya kokari na fada maka amman na ga ba ma zai yu ba na watsar da hidmaar ta"dan dariya yayi sanann yace "Akram ke nan kai daban FIK daban kai da ko magana baka taba mata ba maganar mutane fa ka dauka"ganin yanda ya dage kan cewa shi fa sai ya sanya ta so shi,inda su Jawad Akram da Farouq suke fadin ba za ta taba son shi ba ya sanya Nabeel a kufule cewa duk suyi masa shiru su saurare shi,nan ko suka yi shiru suka zuba masa idanu.

"Well tunda na ga Faizaan ka dage kan za ka iya sanya ta fada son ka ko?Kai ya daga alamun eh,dan numfashi Nabeel ya ja sannnan yace okay ni da su Farouq mun san sarai wahalar da kan ka kawai za ka yi don daga abinda Akram ya fada yarinyar nan yar duniya ce tana da mugun dagun kai da wani rashin kunya but since you are insisting kai hanyar da za ka bi gurin daukan revenge ke nan then fine let's do it this way, Faizaan Kwairanga we Dare you ka sanya yarinyar nan ta fada son ka"

Kallon su daya bayan daya yayi inda ya ga duk sun daga kai alamun yes sun amince da maganar Nabeel,kafin yace "Nabeel ni kuke Daring?Faizaan Isma'il Kwairanga?Sai ya dan fashe da dariya sannan yace am in"da sauri Nabeel yace "are you for real??😳"kai ya daga masa alamun eh da gaske yake yi.

Kafadu Nabeel ya daga irin I don't care sanann yace "you got only a month ka sa ta fada son ka,and month na cika dole ka sanya tayi expressing tana son ka don mu tabbatar da gaske kake,after then sai ka rabu da ita na har abada"da sauri yace "Hell nooo ba zai yu ace within four weeks na dasa mata mugun so na da kauna ta da in na zo na rabu da ita har abun ya dame ta ba,I want it to be 3 months by then mun shaku sosai inda in nace zan rabuwa da ita sai ta kusa mutuwa and I promise you guys three months din nan na cika,zan sanya tayi confessing tana so na a gaban ku a kan idanun ku za kuma ku ji da kunnuwan ku za ta ce muku ba za ta iya rayuwa babu ni ba,a nan ne za ku fito kowa ya fada mata magana son ran sa sannan na fada mata kan ban taba son ta ba,Wlhy bakin ciki sai ya kusa kashe ta in ma bata mutu ba a takai"dan shiru suka yi sai yanzu kuma suke ganin ganin maganar nashi tayi making sense fa,domin kafin ta farfado daga wanann heart break din sai an kwana biyu.

"Kun dai san ba a yin dare a banza ko so what am I getting in return in nayi WASA DA SOYAYYAR ta tare da sanya ta kuka?ya tambaya yana kanne ido daya.

"Ina Expensive Rolex watch da ka gani daure a hannun Dad kace ya maka kyau kana so?to shi zan baka muddum ka sanya yar rainin hankalin nan ta so  ka within 3 months kuma kayi breaking heart din ta a gaban mu,to zan sato maka watch din"idanu FAIZAAN ya zaro sanann yace Nabeel are you serious??"

"Am serious ma kuwa in har ka yi abinda kace consider it yours from now on,but what if you lose??"dan shiru ya dan yi kafin yace " kai ka sanin kan ka ne ban taba losing abu ba in nace zan yi must especially in har Dare ne amman duk da haka na ji,farar fav car dina da ta buga wa stone yau ya zamo naka in har na yi losing tunda daman ka sanya wa motar ido"ya kare yana dariya,shima dariya Nabeel din yayi sanann yace "I love this,ba wai ban da kudin siya ba but in har ka fadi zan ji dadin tuka motar nan na zo gidan ku,tunda siya idona daman ya ke kan ta"kafin ya  mika masa hannu  yace "Deal??"shima hannun ya mika tare da shaking hand din shi yace "Of course Deal",haba nan duk suka saka dariya sannan suka ce "Sabeeha you are doomed taki ta kare just watch and see what is coming for youuuu",dan banza sai a lokacin ya ji ran shi tayi sanyi,har ya ke jin dadi tun kafin ma ya aikata abinda yace har ya fara tausayin ta,nan fa ya sa a kawo musu abinci don sai time din ya tuno da suna jin yunwa..........

           A cigaba da Commenting ana Sharing Hilissssss🥺

  In na ga ruwan Comments za ku ga long page in sha Allah,masu thank you don Allah ana daurewa ana comment ba zallan mun gode ba.

   Ina yi wa kowa fatan Alkhairi.

Continue Reading

You'll Also Like

46K 1.3K 7
فَتاه قوية و لكِن القدر أقوى مِنها غدرت مِن اقرب الناس ، تعذبت و ضلمت مِن اشباه الرِجال كانت تحب لكن طعنت فدخل رجال آخر رغما عِنها هل ستقع في الحُب...
11.1K 1.9K 39
🐾️ Caractors වෙන වෙනම introduce කරන්නෙ නම් නෑ.. 🔞 කොටස් සහිත නිසා කැමති අය විතරක් කියවන්න හොඳේ. Daily Updates නම් දෙන්න බැරි වේවි.. පුළුවන් ඉක්මනට...
545K 22.1K 92
Join the ride full of possessiveness, love,hate,pain,happiness,joy,rudeness.
177K 8.7K 42
After going through a number of disasters I realized that actually I am reborn as the villainess character, more of a brat, Chloe Bourgeois, in a chi...