CANJIN MUHALLI

Por suwaibamuhammad36

2.2K 229 33

Ana kiranta Jidda Sufi, ƴar auta ga Governor Sufi Adam. Duk da jindadi haɗe da tsaron da suke dashi a matsayi... Más

One
Two
Three
Four
Five
Six
Eight
Nine
Ten

Seven

150 13 3
Por suwaibamuhammad36


Dukkaninsu tsaye suke a front yard gurin motoci guda uku da zasu mayar da Governor Sufi Adamu airpot shi da masu tsaronshi tare da wasu tsiraran mutane da suka mishi rakiya daga Nigeria zuwa USA don duba lafiyar ƴar autarshi da ta faɗi ta suma bayan students sun mata prank.

Sufi Adam tsayawa yayi yana kallon Jidda da ke tsaye a front porch ta saƙala hannayenta a cikin pockets ɗin loose jeans ɗinta tana kallonshi fuskarta babu yabo babu fallasa.

"Ba zaki canja ra'ayi mu koma gida ba Mamana?" Ya faɗi hakan cikin tsigar rarrashi amma sai ɗiyar tashi ta kaɗa kanta.

"Daddy mun gama maganan nan tun jiya gashi har ka fito zaka tafi kar mu koma baya please." Ta faɗi hakan tana sauƙowa kan steps ta nufi gurinshi ta tsaya a gabanshi.

Har Governor Sufi Adam ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya rufe kana ya dafa kafaɗarta yana kallon cikin idanunta cike da sonta da kuma tausayinta ya ce,

"Ki kula da kanki." Da haka ya juya ya shige motar da aka buɗe mishi sauran ma suka yi saurin shiga tasu kana motocin suka fita daga front yard ɗin har suka ɓace mata da gani.

Wata wawuyar ajiyar zuciya Jidda ta sauƙe kana ta koma cikin gidan inda ta bar Haajar a sitting room tana zaune tana jiranta.

"Ya tafi ko?" Haajar ta tambaya tana mai gyara zamanta yayin da Mrs Smith take kwashe tray na cups ɗin tea da ta kawowa baƙin nasu da suka tafi yanzu.

"Da kyar. Wallahi har na fara tunanin zai yi forcing ɗina in shiga mota mu tafi." Tayi ƴar dariya nervously.

"Allah Ya tsare wani accident ɗin don na sani sani in aka sake samun akasi Daddy ba zai barki ki ƙara kwana a ƙasar nan ba."

"Amin dai. Zan je in fara assignments ɗina." Da haka Jidda ta miƙe tsaye tana mai ɗaukar wayarta da ke kan couch ta haura stairs tana tuna draman da kuma ɓacin ran da kowa ya shiga kafin Daddy ya barta.

Yana sauƙowa daga jirgi direct ya nufi hospital ɗin da aka kwantar da ita, a can ya samu an yi discharging ɗinta bayan an duba bata da matsalar komai illa tsorita da tayi. Tun daga asibitin bai bari ta koma gidan Haajar ba ya tafi da ita gidanshi da yake sauƙa wanda ta sha zuwa hutu cikinshi, a can ya sakata a gaba da tambayoyi akan yanda ake treating ɗinta a school ɗin amma ta faɗa mishi basa zaginta kawai dai basa shiga harkarta ne, sannan ta faɗa mishi tana da friends har biyu Alice da kuma Christ wanda ta faɗi sunan shi ne don Daddy ya ga abokan nata suna da yawa ba mutum ɗaya ba ce. Tun a ranar ya yanke hukuncin cewa zamanta ya ƙare a USA sannan School ɗin sun tsananta bincike akan wanda yayi aika aikar zai fuskanci hukunci daidai laifinshi. Daddy ya san ba wani horo za'a yi na kirki ba musamman in ya kasance wanda yayi hakan Minor ne ba wanda ya ƙetare shekara sha takwas ba, hakan yasa ya dage cewa zata koma saboda idan wani ma yana da niyyar yin hakan zai yi nan gaba.

Matakin da Jidda ta ɗauka don nuna rashin yardarta da hukuncin Daddy shine ƙin cin duk abincin da aka kawo mata kama daga Dinner, breakfast da kuma lunch na washegarin ranar, a nan ne mai kula da gidan ta aikawa Daddy saƙon halin da ake ciki kan cewa Jidda was starving herself.

Rayuka sun ɓaci domin Jidda kuka kawai take yi ta ƙi sauraron Daddy da yake mata faɗa akan halin da ta saka kanta a ciki wanda zai iya jawo mata rashin lafiya, ganin ba zata ci abincin ba ya dawo rarrashi wanda a nan ma ta botsare daga ƙarshe ya haƙura amma da sharaɗi tare da rantsuwar in dai wani abu ya sake faruwa ko kashe kanta tayi zai ɗauki gawarta ya mayar gida. And she agreed! Again!

School kuma Governor Sufi Adam ya je da karan kanshi ya samu mai makarantar akan wannan cin mutunci da kuma zalunci da aka yiwa ƴar shi ba zai bari ba zai kai ƙararsu kotu saboda rashin kulansu ne ya jawo haka, wanda in hakan ya faru ba ƙaramin ɓata musu sunan makaranta zai yi ba kuma ba zasu so hakan ba. Wannan dalili ya sa mai makarantar ya mishi alƙawarin tsananta bincike don gurfanar da mai laifin tare da cewa hakan ba zai sake faruwa ba. Wannan yasa hankalin Governor Sufi Adam ya kwanta kaɗan sannan ya janye batun ƙara ya kuma gargaɗesu akan taɓa mishi lafiyar ɗiya.

Sai washegari Thursday Jidda ta koma school, tun daga bakin gate zuciyarta ta tsananta bugu amma tana isa front door na mashigar ginin ta haɗu da Alice wacce da alama zaman jiranta take yi a gurin.

"Kin faɗa mini zaki dawo amma ban yarda ba sai da na ganki yanzu." Ta faɗa tana mai isowa gareta cike da murna kana suka ɗunguma zuwa ciki.

"Gani nan." Jidda ta amsa mata tana kallon students ɗin da suke tsaye a hallway basa ko kallon inda take.

"Daga yanzu zaki ga canji a tattare da sauran students domin school assembly aka yi akan bullying wanda dama ana yi amma naki yayi tsamari har ya fita waje, principal yayi warning sannan yace duk wanda aka kamashi da laifin haka a bakin admission ɗinsa tare da rubutun bad character a cikin student data ɗinshi, and babu wanda zai so hakan saboda one bad remark a kan student zai iya sa Universities su yi rejecting mutum."

"Shi yasa yau na ga babu mai bina da kallon banza. I'm glad." Jidda ta bisu da kallo amma sai su ɗauke kai kamar ba'a yi tsironta ba wanda hakan ya so ya bata dariya amma ta riƙe dariyar tata.

Suna tsaye a bakin ajin da zasu shiga suna hira Jidda ta ji an dafa kafaɗarta kaɗan ta juya a tsorice don ta sani wani prank ɗin za'a mata amma ganin Chris ne yana murmusawa yasa ta ji hankalinta ya kwanta kaɗan amma ta bishi da ido ta kasa furta komai. Gyaran murya yayi kana ya dubeta tsam ya ce,

"I'm sorry da abun da ya faru, da fatan kina lafiya?"

"Lafiya kalau. Na ji an ce ka je dubani a hospital, thank you." Ta bashi amsa tana mamakin sauƙin kai irin nashi domin bayan Alice shi kaɗai ne yake mata magana duk faɗin school ɗin.

Kasa tafiya yayi ya tsaya suna kallon-kallon wanda lokaci lokaci Jidda na ɗauke idanunta gefe don sai take jin ba zata iya haɗa ido dashi na lokaci mai tsawo ba. Ganin abun nasu yayi yawa ya sa Alice tayi fake tari suka dawo hayyacinsu nan Jidda ta daburce ta fara gyara backpack ɗinta shi kuma Chris ya gyara gashin kanshi ya saƙala a bayan kunnenshi.

"See you around." Ya faɗa kana ya shige class ɗin ba tare da ya saurari amsarta ba.

"Wow!" Faɗin Alice tana jan hannun Jidda suka koma gefe inda babu mutane sosai.

"Me yasa kika ce 'Wow'?"

"Chris ne fa ya miki magana! Christian Cavendish!"

"Shi dai, wani abu ne?" Jidda ta tambaya don yanda Alice ta faɗi sunan nashi kamar wani babban celebrity ne a duk ƙasar America.

"Shine Captain na football team na school ɗin nan, kuma an ce familynsu masu kuɗin gaske ne wanda aka ce suna da oldest Brewery na ƙasar nan. And ba sai na faɗa miki ba shi ɗin mai kyau ne don kusan ninety nine percent na ƴan matan school ɗin nan shine crush ɗinsu, but Evelyn ta hana kowa matsowa kusa dashi don ita ce budurwarshi wacce yau suna tare gobe kuma zaki ji an ce basa tare."

"So?" Jidda ta ɗaga gira ɗaya don duk sharhin Alice bata ga dalilinta na cewa 'Wow' ɗin ba.

"Seriously?" Kafaɗun Alice suka sauƙa alamar defeat bakinta a buɗe tana kallon Jidda irin unbelievable ɗin nan.

"I'm sorry but ban gane saƙon da kike son isarwa ba." Jidda ta ƙara faɗa wacce har lokacin kanta a duhu yake.

"What I mean to say is Chris abun son kowacce yarinya ce and his family are filthy rich, and Evelyn his on and off girlfriend will set your ass on fire ko kallonshi kika yi bare kuma wai a ce ke yake yiwa magana, ya zama worse!"

"Ohh." Shine kaɗai abun da Jidda ta faɗa still bata gane ba.

"Ohh? Jedi? Shin kina jin me nake faɗa miki?" Wannan karon Alice tayi kamar ta kama kafaɗun Jidda ta jijjigata don frustration.

"I'm sorry, ko zaki mini bayanin kamar kina yiwa ɗan shekara uku?" Ta faɗa tana murmushi ƙasa ƙasa domin ta lura Alice ta fara gajiya da slow brain ɗinta.

"Chris is a bad news a gurinki! Don't get involve with him in kina son zaman lafiya da kowa a school ɗin nan da kuma crazy leech ɗinshi. In ban manta ba ke ce kika ce kina son blending da sauran students ya zama ba'a kallonki ba'a jin labarinki, honey, ba zaki iya blending ba in har kina hulɗa da Chris, zaki kasance kullum a tsakiyar spotlight. Kin gane?"

"Ohh."

"Just 'Ohh'? Alice ta tambaya cikin mamaki.

"No, I mean to say I get it. Amma ba ni nake mishi magana ba fa, shi yake zuwa inda nake yake kuma fara mini magana! Kuma I don't think ko sunana ya sani. To ma ya zan yi? Ƙin kulashi zan yi ko dai?"

"Figure that out yourself. Zan tafi class ɗina. Later." Alice tana faɗin hakan ta tafi ta bar Jidda cike da mamaki domin sai ta ga kamar ranta ya ɓaci kaɗan.

Kaɗa kafaɗarta tayi domin ta sani bata yi laifi ba balle Alice ta kamata da laifin, to ko dai itama tana crushing a kanshi ne and she is jealous yana mata magana not her? To koma menene ai ba ita take zuwa inda yake ba ko take fara mishi magana ba, and ita bata ce zata yi friendship da shi balle Evelyn budurwarshi ta sakata a gaba ba.

Da wannan tunanin Jidda ta shiga class sai dai tana neman gurin da zata zauna ta haɗa idanu da Chris wanda yake mata murmushi kana ya ɗauke kanshi da Evelyn ta kira sunanshi tana nuna mishi abu a waya, itama Jidda ɗauke nata kan tayi ba tare da ta mayar mishi da murmushin ba ta nemi guri far away from them ta zauna ba tare da wani student ya hanata ko ya mata maganar banza ba. Tana zama aka kaɗa bell students suka fara shigowa kamar ana ruwansu kana suka samu guri suka zauna don koyon lesson ɗin ranar.

A Cafeteria Jidda ta haɗu da Alice wacce a yanzu babu guntun ɓacin ran ɗazu a fuskarta suka hau layi har suka karɓi abinci suka zauna a table ɗin su wanda su kaɗai suke zama kullum. A can gefensu na hagu table ɗin su Chris yake wanda popular students ɗin school ɗinne kaɗai suke zaune a kai suna hira, ta wutsiyar ido Jidda ta kallesu ta hango Evelyn zaune a kan cinyarshi yana shafa gadon bayanta yana kuma magana da sauran mutanen gurin. 'Oh bature babu kunya' shine abun da Jidda ta faɗa a ranta tana mai mayar da hankalinta kan Alice da take bata labarin wani book da ta karanta na magic itama ta biye mata suka cigaba da hiransu.

Bayan wata ɗaya Jidda ta saba da school ɗin tare da routine ɗin rayuwar cikinta. Sosai suka shaƙu da Alice wacce duk faɗin Edwin High School bata da kamarta sai kuma Chris wanda yake binta da murmushi duk lokacin da suka haɗa ido a class, ko kuma in suka haɗu face to face ya ce mata 'Hi' itama ta mayar mishi da 'Hi' shikenan.

Yau ya kama Friday sun shiga Lab ɗin Biology Mr Doe yace zai basu assignment da mutane biyu ne zasu yi a tare don haka kowa ya zaɓi partner ɗinshi. Da yake Alice bata class ɗin sai ya kasance Jidda ta rasa da waye zai zama partner ɗinta, kuma gudun kar a disgata in ta zaɓi wani sai ta tsaya a inda take tayi kamar bata ji me ake yi ba.

A can ɗayan side ɗin class kuwa Chris ya ki amincewa da kowa a matsayin partner ɗinshi, domin kuwa kullum tare da Evelyn suke haɗewa amma wannan karon hakan bai samu ba don sun ƙara wani break up ɗin sati ɗaya da ya wuce. Hatta Evelyn ta samu partner wani abokin faɗan Chris, kuma tayi hakan ne don ta ɓata mishi rai amma sai bai nuna a fuskarshi ba sam.

"Su waye basu samu partner ba?" Mr Doe ya tambaya yana kallon dandazon students ɗin nashi.

Duk yawan mutanen cikin class ɗin Jidda da Chris ne kaɗai suka ɗaga hannu.

"Christian Cavendish zaka zama partner ɗin Jidda Sufi. Class dismissed." Da haka Mr Doe ya fara tattaren takardunshi wanda hakan kuma yayi daidai da kaɗa ƙararrawa da aka yi na tashi daga school ɗin gaba ɗaya.

Ita kuma Jidda tunda taji an ambaci sunan Chris tare da nata sai ta daskare a gurin ta ji yawun bakinta ya kafe tana buƙatar shan ruwa. A rasa da waye za'a haɗata sai Chris of all people!? Tukunna ma ina leech ɗinshi Evelyn? Ko da yake ta lura kwana biyun nan bata ganinsu tare sannan Alice ta faɗa mata cewa wai ana rumours ɗin cewa sun sake wancakalewa basa tare yanzu. In banda ƙaddara me zai haɗata da wani Chris? Me yasa ba za'a haɗata da wani ba? Sai kuma ta tuna cewa kowa ya zaɓi wanda yake so ne sai ita da shi ne kaɗai basu samu abokan haɗakan ba, don haka kuwa dole su zama partner ɗin juna. Books ɗinta ta zuba a backpack kana ta jira sauran Students suka gama fita sannan ta rataya backpack ɗin a kafaɗa ɗaya ta nufi ƙofar fita ta ji an kira sunanta ta bayanta.

"Jidda."

Juyawa tayi cikin sauri don yanda aka kira sunan babu mistake yasa ta ji tana son sanin waye ne. Chris ta gani yana takowa gurinta wannan karon gashin kanshi a hargitse kamar yayi wasa dashi amma a hakan sai ya mata kyau, kyau na sosai.

"Yes." Ta amsa tana gyara tsayuwarta bayan ya iso kusa da ita

"Mr Doe ya haɗamu, we are partners." Ya sanar da ita duk da cewa ya san ta sani.

"Eh. Zan yi mana assignments ɗin in ya so ranar Monday sai in baka ka duba." Ta amsa mishi tana kawar da kanta gefe.

"Wa ya faɗa miki ni bana son koya? Ko kuma kina tunanin ba zan iya bane?" Ya dubeta fuskarshi ɗauke da mamaki.

"Sai in baka kayi kai ɗaya." Wannan karon with a little irritation a voice ɗinta.

"Ya kamar guduna kike yi? Okay I'm sorry, zan je in mishi magana ya haɗaki da wanda kike so." Yana faɗin hakan yayi gaba kamar zai fita daga ajin amma ya ji ta kira sunanshi wanda hakan yasa yayi smirking ya juyo.

"Chris No! Zamu yi tare kar ka faɗa mishi ya haɗani da wasu please. A ina zamu haɗu?" Ta yi saurin canja ra'ayi domin ta gwammace a haɗata da shi sau goma da a haɗata da waɗanda ko magana ba sa mata.

"Your place or my place, duk wanda kika zaɓa ya mini." Ya ɗaga girarshi ɗaya sama yana jiran amsarta.

"Me zai hana mu haɗu a wani Coffee shop, zamu iya gamawa in three hours. Sai ka zaɓa mana gurin." Ta faɗi hakan don ko giyar wake ta sha ba zata taka gidansu ba haka kuma ba zata yi inviting ɗinshi zuwa gidan Yayarta ba.

"Ouch! Kina mini rowan gidanku kuma bakya son zuwa nawa, it's okay. Zan tura miki address ɗin gurin sai mu haɗu saturday evening, is that ok with you?"

"Yeah. I mean Yes, it's ok with me." Da haka ta yi gaba zata fita ta ji an taɓa kafaɗarta wanda wannan karo na biyu kenan da yake mata haka ta juyo don ta haneshi da aikata taɓata amma ya rigata magana.

"Ta ina zan tura miki text ɗin gurin?"

"Ohh" Ta ji kunya ya kamata kana ta fara kira mishi numbernta bayan ya ciro wayarshi yana sakawa a ciki.

"Done! Sai kin ji daga gareni. By the way the Hijab look good on you." Yana faɗin hakan ya fice ya barta ita kaɗai tana blushing.

Sai da ta saisaita kanta sannan itama ta fita tana jin zuciyarta na mata saƙe-saƙe na wannan haɗin da aka mata da Chris. Duk yanda ta kai da ƙi game da gudun shiga harkarshi sai gashi ƙaddara ta zo ta haɗasu wanda a yau ya karɓi numbernta har suna maganar a ina zasu haɗu! Ofcourse not as friends or anything like that but as partners na group assignment.

Mu je zuwa!!!

Mum Fateey 👌

Seguir leyendo

También te gustarán

296K 23.7K 148
Hannu da yawa...... 🤝🏻🤝🏻🤝🏻
10.4K 566 16
A wani gari, da al'ummarsa basa hada jini da mutanen wajen garin, akwai wata yarinya da alkalamin kaddara yayi mata zane a garin da bata da kowa ciki...
6.5K 145 8
During the Reiwa period of Japan, in a coal mine situated underneath a nuclear plant, a female figure was found in the midst of Rock Salt. Professor...
25.7K 1.6K 42
....what action would you take.. if you found out dat someone whom you hold so dearly.is cheater, and he secretly tried to sleep with your loved wif...