DA'IMAN ABADAN (Sanadin shi)

By JameelarhSadiq

777 38 15

Labarin soyayya mai tafiya da qaddararta da kuma qalubale iri iri More

SANADIN SHI 01-10 BEGINNING OF FATE
SANADIN SHI 21-30
SANADIN SHI 31-40
SANADIN SHI 41-50
SANADIN SHI 51-60
SANADIN SHI 61-70
SANADIN SHI 71-80
SANADIN SHI 81-90
SANADIN SHI 91-100
SANADIN SHI 101-110
SANADIN SHI 111-120
SANADIN SHI 121-130
SANADIN SHI 131-140
SANADIN SHI 141-150

SANADIN SHI 11-20

68 4 0
By JameelarhSadiq

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _SANADIN SHI_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK TWO*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba! yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*Wanna page din naku ne masoyana a duk inda kuke🫂*

*11-20*

*UKRAINE🥀*
*Wacece Hauwa'u Abdullah jibir (Beauter)*

Sunana Hauwa'u Abdullah jibir kamar yanda na gaya maku,asilina yar Nigeria ce a jahar Zamfara muna zaune a cikin birnin gusau .unguwar tunda wada unguwace wanda ta hada mutane kala kala tun daga kan tallakawa tsaka tsakiya da kuma masu arziki.

A unguwarmu  mahaifina ba'a kiranshi mai arziki kuma ba'a kiranshi tallaka tsaka tsikiya dai ,kuma yana cikin wanda suke fada aji a cikin unguwa. dan mahaifina shi mutumin ne wanda bai da wasa ko kadan a wajen bada tarbiya! ba ruwanshi da bashi bane ya haifeka ba idan har yaro ya aikata ba daidai ba har gida zaije ya hukunta yaron dai dai laifinshi.

Shiyasa kowa ke bashi girma a unguwar dan ya dauki ragamar unguwar ya daura ma kanshi,dan kuwa yaran da ya dauki nauyin karatunsu a unguwarmu yawa ne da su tun daga kan boko har isilamiya,dan ko abinci za'ayi ayi a gidanmu ba a dafashi dai dai cikin yan gida,dan gidanmu gidan mutane ne kullun cikin shigo mana ake dan baka raba gidan da mutane haka gidan yake.

Gidan mu babban gida ne kuma ginin zamani ne mai tsikiya babban parlo ne mai dauke da dakuna hudu ko wane daki yana da bathroom sai kitchen da store sai kuma toilet din tsakar gida,da kuma filin da mota daya zuwa biyu zasu samu masauki.

Mu goma ne mamarmu ta haifa maza biyar mata biyar, Muhammad ne babba sai Fatima sai Bishir sai Hauwa'u sai Sulaiman sai Aminatu sai Humaid sai Saddiqa sai Usman sai kuma Auta Rukayya...mun taso cikin gata da kuma kulawa dan babu abunda muka nema muka rasa a rayuwa duk da muna da yawa gidanmu,amman hakan bai sa muka taso cikin rashin tarbiya ba ko kuma rashin mutunta na sama da damu.

Daman na gaya maku Babanmu bai da sauki a wajen tarbiya shiyasa bamu taso mararsa ji ba a unguwa dan bai barinmu muna fita bama kamar mu matan idan har kaga mun fito waje bai wuce dayan biyu isilamiya zamu ko kuma boko!abunda ke fidda damu waje kenan,kuma bai cika barin muna hudda ko wasu kawaye ba,bama mu mata ba hatta suma mazan bai basu wannan damar ba,balle kuma mu mata da daman koda yaushe muna gida ,kuma a gidan ba zaman banza muke ba,idan bamu karatu to muna taya Mama aikin gida,idan kuma ba aikin gida muna kan keken muna koyan dinki da yake Mama taila ce ta iya dinki sosai,amman ba kowa take ma wa ba daga mu sai yaran yan uwanta mu kenan take ma wa ,da tana sana'ar dinkin sosai tunda aka taba yin dambe a gidanmu akan dinki daga ranar ya hana yace andaina yi mashi wannan sana'ar a gida sai dai a chanza wata.

Ba yanda Mama batayi dashi ba wajen bashi hakuri amman fir!yaki yarda yace ya gama magana sana'ar dinki dai ba'a gidanshi ba,dan ba zai zuba ba ido ba yana ji yana gani a maida mashi gida madaldalar fadace fadace,tun tana bashi hakuri akan ya barta har tazo da ta hakura ta koma sana'ar takalmi da jikkuna.

Gidanmu gidan boko ne haka ma isilamiyar duka anayi dan Baba yana da ra'ayin baiyi ma yaranshi aure har sai sun kammala karatu,shiyasa ma bai ba matansan unguwar fuska fara zuwa zance wajen yaranshi ba,bai kuma yarda da zance ba a kofar gida bai kuma lamince ka fara tsada yarinyarshi ba, ba tare da ka aiko manyanka sun nema maka izinin nema ba.wannan shine ra'ayin shi akan yaranshi mata.

Cikin sa'a mu ukku mata muka taso kai daya duk da ba aji daya muke a makaranta ba,amman tare muka taso kanmu daya Yaya Teemarh sai ni ana ceman Jidda ko Kulu sai kuma Meenat,haka muka taso kanmu daya dan banbanci kadan ne,Yaya Teemarh tana 400l ni kuma ina 300l sai Meenat tana 200l a nan FUG.

Ko wane da course din da yake karanta dan ba faculty dinmu daya ba, Teemarh tana humanities sai ni ina polic science sai kuma Meenat tana low shiyasa tafiyarmu take da banbanci kowa da lokacin da yake tafiya.

Tunda na taso samari sukayi man ca!kowa ka gani yazo gidanmu sai yace ni yake so da yake daman nafi duka yan gidanmu kyau bani kama da kowa sai dai kamar jini amman komai nawa daban yake akan rasa wa na biyo a cikin dangin Baba da Mama nidai gani nan kama ta daban da ta kawo..ni kuma tunda Allah yasa na taso bani kula kowa duk wanda zaice yana sona to yayi aikin banza har da wofi ma dan kayi ka gama ka kama gabanta ba lokacinka zanyi ba.

Yau tunda na tashi na fara shirin zuwa school dan muna da lecture 8,shiyasa tunda na tashi asuba ban koma bacci ba dan nasan halin Wasila da shigen nacin bala'i dan da na kuskure na ja mana makara ta dunga mita kenan har sai na bani da mitarta... shiryawa nayi cikin wata atamfa purple dinkin riga da siket ni na dinka kayana da kaina dan gidanmu ba wanda bai iya dinki ba sai dai idan baka sa kanka koya ba,size bag dina na dauka na fito parlo na tadda Mama tana hada ma Baba break zama nayi Ina cewa.."Mama Ina kwana." Kallona tayi fuskarta dauke da murmushi tace.."lafiya lau Kulu,fatan dai babu wata matsala dai ko.?"

Girgiza kai nayi na tashi na hada tea na dauki bread Ina cewa.."babu sai dai kudin hannuna sun kusa karewa fa." Murmushi tayi tana cewa."Kulu ba dai kashe kudi ba,ai Babanki bai Kai da fita ba idan ya fito sai ki gaya mashi,amman duka duka yaushe Babanku ya baki duba biyar har kin kusa ganin bayanta?kuma bayan na hanaku yawan kashe kudi kamar ba gobe."

Turo baki gaba nayi Ina cewa.."amman Mama ai nayi kokari yau fa sati da bani 5k din da kike magana,kinga dai kudin naped kanshi ya karu ga kuma handout banda abinci ai Ina ma yin maleji sosai gaskiya nidai." Har zatayi magana Baba ya fito yana cewa."sai kuta yin addua Allah ya kara budi,ya bude hanyar samu sai ai ta baku yanzun bayan kudin babu wata matsalar ko.?" Dariya nayi Ina kurbe shayi nace.."Allah ya barmana kai Babanmu,Babanmu maganin kukanmu." Dakuwa yayi man yana murmushi yace.

"Ai Allah baya barin wani dan wani yaji dadi,nidai fatana Allah yayi maku albarka ya kuma kareku da kariyarsa ya bani hanyar da zan baku halak malak."
Dan marairaice fuska nayi Ina cewa.."Allah dai ya kara maka tsawon rai Baba,banda wata matsala bayan ta kudin." Da Amin ya ansa yana cigaba da yin break dinshi na rigashi tashi,dakatar da ni yayi yana cewa.."tsaya na dauko maki kudin ko Jiddo." Murmushi nayi kawai Ina ce ma Mama."yau mai zaku girka mana da rana.?"harararta tayi tana cewa.."abunda kika nemo kika bamu mijina." Dirdira kafafu nayi Ina cewa.."wayyo Allah Mama daga tambaya." Itama yin yanda nayi maganar tayi tana cewa.."wayyo Kulu daga baki ansa." A tare mukayi dariya Ina rungumai bayanta nace.."inasonki Mama sosai,Allah yasa ki gama da duniya lafiya." Lakutar man hanci tayi tana cewa.."Nima inasonku Kullu,Allah yayi maku albarka keda yan'uwanki baki daya,ya kareku da karewarshi."

Fitowa Baba yayi yana cewa.."to masoya kun fara ko?yanzun zaku fara nunaman banbanci." Rufe baki nayi Ina cewa.."ai bamu Isa ba Baba kaima ai kasan kaine mai babbar fada a birnin Zuciyar Hauwa'u Kullu Jidda Abdullah jibir."murmushi kawai yayi yana girgiza kai ya mikoman kudi yace.."gasu nan sai a jallallauta kinji Kakata Kinga dai Baban nan naki ba kudi ne dashi ba." Ansa nayi Ina lissafawa naira dubu goma ne murmushi nayi nace.."nagode Babana Allah ya Kara bude ya Kara tsawon rai,Ina kaunarka Babana." Murmushi yayi yana cewa."ki kula kinji Kakata ,Allah yayi maku albarka." Da Amin na ansa na fito waje Ina duba time dan nasan halin Wasila ila tana kofar gida tana jira sai cika take tana batsewa.

Koda na fito cikin sa'a ban tadda Wasila ba tsaya sai na sauke ajiyar zuciya Ina mai nufar gidansu da yake unguwarmu d'aya,duk da ba jikin gidanmu gidansu yake ba amman tafiya kadan zakayi ka iso gidansu daga gidanmu.

Kafin na ida Isa gidansu Wasila ta fito tana kama baki tana cewa.."A'a yau kuwa za'ayi ruwa har da kankara Hauwa kice da kanki?." Murmushi nayi Ina cewa.."ya  son ran  yanmatan zuciyarki?ai nayi fushi nima ba zaki kara jirana ba sai dai ni na dunga jiranki daga yau dan na gaji da gorin da ake man kusan kullun." Dariya tayi tana kallona sai kuma tace..."tabbb mu gani kasa ke din? da dai baki dan banzan bacci dai,amman na baki kwana biyu kadai kafin angulu ta koma gidanta na tsamiya."daure fuska nayi Ina cewa.."wato haka ma kika ce ko.?" murmushi tayi tana yin gaba tace."eh ke din ai halinki na sani shiyasa." Bin bayanta nayi Ina cewa.."ni din dai ko.?"Daga man kai tayi tana cewa.."eh." Shikenan ni kuwa in shaa Allah sai na baki mamaki yanmata." Dariya kawai tayi muka cigaba da tafiya har muka iso bakin titi,muna isowa Yaya Auwal ya tsaya gabanmu da mota yana zuge glass din motarshi yace.."Jidda sai Ina da safenan sarauniyar mata.?" Dan karamin tsaki nayi Ina dan yin murmushi nace."Ina kwana." Da yake Ina dan jin nauyinshin abokin Yaya Muhammad ne tare sukayi karatu sai dai shi Yaya Muhammad yana ingila can yake karatun likita ya samu scholarship,amman duk tare suka taso a cikin unguwa.

Kureni da Ido yayi yana cewa.."lafiya qlau yanmata nace Ina zuwa kuma.?" Ya sake maimata tambayar dan kallon Wasila nayi da ta maida hankalinta kan wayarta,dan gyara tsiyuwa nayi Ina gyara hijab dina dan kallonshi ya fara takura ni,na tsani kallo shi kuma al'adarshi kenan kallon tsiya da kurulla,cewa nayi.."makaranta." Fitowa yayi yana cewa.."ok ku taho na saukeku mana tunda nima hanyar nayi." Girgiza kai nayi Ina cewa."mungode Allah ya bar zuminci,amman ka barshi." Ba yanda baiyi da mu ba amman muka ki shiga sai dai ya dauko dubu biyu ya bamu yace mun hau naped anjima munyi waya sannan ya wuce,yana wucewa muka tari naped muka gaya mashi inda zai kaimu.

Koda muka isa school samun waje mukayi muka zauna sannan na fiddo dubu d'aya na bata nace.,"gashi ki kara cikin kudinki." Ansa tayi tana cewa."nagode,amman Ina mamaki nikam dai."kallonta nayi ina cewa.."mamaki kuma?mamakin Mai.?" Dan murmushi tayi tana cewa."Ina mamakin yanda kike ma masoyanki abunda kika gadama Hauwa,ki gode ma Allah ke kina da samarin ma,ki godema Allah ke kina da masu sonki ma Hauwa,mu kuwa nan mun rasa masoya ba dan bamu da kyau ba kuma ba dan bamu da farinjini ba,kawai dai haka kaddararta take,amman ke kin samu kina dasu maimakon ki kama su ki rike amman sai ki kama yi masu rikon sakainai kasa,haba Hauwa wallahi banjin dadin haka."

Dan shuru tayi tana cigaba da cewa..,"kuma ni Hauwa banga aibun Auwal ba,Auwal Kinga dai yana da ilimi kuma yana da aikin yi ga kuma kasuwa har da gidan kanshi ya mallaka ke harda motar nan dai ta zamani yana da ita banga makusar Auwal ba da har zaki ringa nuna mashi baki sonshi."

Dafa ta nayi Ina cewa.."komai kika lissafo akan Auwal gaskiya ne,tabbas Auwal baida makusa kuma Auwal mutumin kirki ne sai dai kinsan shi so ba ruwanshi da mai mutum ya mallaka kuma ba ruwanshi da kyau ko na saba,nidai kawai ban sonshi nayi nayi na saka sonshi a raina na  kasa Wasi."

Dan Jim tayi sai kuma tace.."kema kinyi magana Hauwa,amman dan Allah ki daina yi mashi abunda kike mashi,ki dan dunga kulashi kina Addu'a sannu a hankali idan da rabon da shi za'ayi sai kiga kun sasanta."

Nidai ban sake ce mata komai ba,dan ni abunda na sani bani sonshi amman zan dunga kulashi ko dan na faranta ma kawata Wasi rai,dan nasan Wasi tana sona kuma tana son cigabana ,zaman tsakani ga Allah muke da ita,babu bakincikin balle maku hassada,bata boyeman komai nata kamar yanda nima bani boye mata komai nawa,Ina sonta kamar yanda take sona itama,kuma tafi karfin komai a wajena,dan furzar da iskan bakina nayi Ina cewa

"In shaa Allah zanyi yanda kika ce Wasi,Allah dai ya zaba mana abunda yafi alkhari,Allah ya bamu mazaje na gari wanda zasu somu ba dan wani abu na jikinmu ba."murmushi tayi tana cewa.."Amin ya Allah,ai ni duniyar nan tsoro take bani Hauwa,lamarin mazan ne babu tabbas dan rabin mazan yanzun ba dan Allah suke zuwa ba da wata manufa ta daban suke zuwa,abun dai sai dai addua kawai itace gaba."

"Hakane kuma Allah dai ya zab'a mana na kwarai." Da Amin ta ansa nan lecturer ya shigo  mukayi lecture sanann mukaje entery muka samu abunda muka sakama cikinmu sannan muka dawo muka sake daukar wata lecture din sanann muka nufo hanyar gida.

Koda na koma gida,taddawa nayi anyi abinci ban tsaya yin komai ba na fada wanka dan wani irin zafi ake kwalawa a gusau a ranar, gashi kuma ni ba ma'abociyar son zafi bace fada nike dashi sosai,ina fitowa wanka na samu wata halfgown na saka na saka hula na fito parlo.

Zaune suke su dukansu a parlo ana kallon fastx duk sun natsu dan tsaki na danja kadan Ina wucewa kitchen dan ni haushi suka bani yanda suka natsu suna kallon film din da babu abunda ake yi a cikinshi sai zallar karya wanda hankali baya dauka,su kuma har burgesu karyar take,abinci na zubo na dauko purewater daya na dawo parlorn samun waje nayi na zauna Ina kallonsu nace.

"Dan Allah dubi yanda kuka natsu sai kace bitar karatu ake maku,maiye dadin kallo ga karya dan Allah nidai ku chanza mana channel ku maida mana African action na tabbata suna can suna dafama recipe mai dadi ko kuma gaskiya plus." Na ida maganar Ina sunburo baki.

Dakuwa Yaya Bash yayi man yana cewa.."gidanku nace Jidda kinji,yaushe muka zama abokinki.?kwabe mashi fuska nayi Ina marairaicewa dan nasan halin yan kayana bai da sauki watarana kuma yafi ruwan sanyi , sanyi dan ba Koda yaushe ake wasa dashi ba tuni ya gama karatu shi dan ya riga Yaya Teemarh ta shiga university shi yanzun haka aiki yake a gidan nepa.

Maida kallona wajen Mama nayi Ina turo baki gaba nace.."Mamana kiyi masu magana a chanza mana wanann film din ni baiyi man kyau ba,kuma Kinga fa ina koyan girki a African action fa,kuma time din da zasu saka yayi."

Dukansu zuba ma Mama Ido sukayi suga mai zatace ,dan tama fisu son kallon fastx din tunda akace ya fito take maganarshi ayi download a kalla dan mu gidanmu fast and fesbriou baya wucesu,da an saki suke kallo har da Baba shima kallo yake dan suna son film din sosai,saboda yanda suke rairen motoci shine yake daukar hankalinsu a kallon film din.

Kallon Sule Mama tayi tana cewa.."Sule mai da mata ta kalli African action din tana gama kallon recipe's din tunda mu nan a cikin flash yake da ta gama sai mu maida mu cigaba daga inda muka tsaya."

"Daman nasan Allah cewa Mama zatayi a maida mata ,bayan kuma muma muna son kallon fastx dina fa Mama,kuma ya dauko dadin kallo dan Allah Yaya Jidda kiyi hakuri ki barmana mu kalla anjima sai ki bi maimaici haba please mana." Cewar  Humaid yana yin fuskar tausayi,harararshi nayi zanyi magana Yaya Bash ya tsadani yana cewa.

"Idan har kika kuskura na taso sai ranki yayi bala'in b'aci Jidda,ya za'ayi kin taddamu muna kallo kice ke sai an Kai maki wani waje?haka ake rayuwa nifa banson son zuciya fa."

Kasa nayi da kaina  bance mashi komai ba,sai dai har na fara tara hawaye,ni a dole sai an Kai man African action kuma nasan sun fini gaskiya kawai fastx din ne bani son kallo kuma,banji zan iya zaman daki ba saboda kallon da suke gyran murya Mama tayi tana cewa.

"Yanzun har ni zance a maida mata inda take so Ku tsaya fadin abunda ke ranku ko?kenan ban Isa da ku ba?ban Isa nace eh ba ta zauna ko?ku dukanku nagode tunda ban Isa ba bari na barku kuyi abunda kuke so,tunda yar'uwarku bata da alfarma a wajenku har da ke Teemarh da kuma Bash a matsayinku na manya a wajen nan,amman Kai Bash kama fi kowa nuna rashin amincewarka a umirnin da na bada duk nagode."

Tasowa Yaya Bash yayi ya tsuguna a gaban Mama yana kamo hannunta yana cewa.."Dan Allah Mama ki yafemana amman wallahi banyi haka dan bijirewa umirninki ba,nayi haka dan na nuna mata kuskurenta amman kiyi hakuri haka ba zata sake faruwa ba in shaa Allah Mamana,dan Allah ki daina fushin nan kin san dai inasonki kice rayuwata ban son naganki a cikin fushi Mamana."

Shafa kanshi Mama tayi tana murmushi,mu duka ta kalla a parlorn tana cewa."ku dukanku Ina sonku Ina kaunarku kuma ba wanda na fiso a cikinku dukanku so iri daya da kauna daya nike maku,Ina jinku har cikin raina yarana,Inason ku hada kanku ku mazo tsintsiya madaurinki daya,Inason ku so junanku wanda son zai kai ku sadaurkawa dan farincikin dayanku." Dan shuru tayi ta maida numfashi sannan ta cigaba da cewa.."Ina da dalili da yasa nace a maida mata ,naga mu namu kallon yana a flash.ita ko nata sai ta kunna stalitile sannan idan kuma ya wuce tayi missing dan bai zama dole tana gida ba sanda zasu maimaita kuma gashi abu mai amfani zata kalla tana karuwa sosai da kallon recipes din da suke nasan nan gaba zasuyi mata rana."

"Hakane Mama muma munsan ai kina sonmu kuma baki nuna mana banbanci daga ke har Baba,tabbas munyi dacen iyayen Allah ya Kara maku tsawon rai da lafiya mai amfani,mu da muke manya Allah ya Kara bude mana mu taimaki kannenmu da kuma iyayen da yanuwa da mabukata." Cewar Teemarh da Amin muka ansa mu dukanmu sanann kuma aka maida mana African action,cikin ikon Allah muna zuwa muka tadda ana girke girke nan muka natsu Muna kallo.

Inason kallon tashar saboda Ina karuwa da abubuwa da yawa,bama kamar wajen recipe wani abun baka taba ganinshi ba sai kaje tashar zakaga anayi,wani yayi kyaun gani wani kuma sai a slow.

Mun jima a parlo Muna kallo Muna fira sai da lokacin sallah yayi sannan muka tashi dan yin sallah,kafin na fara yin sallar sai da nayi wanka dan Ina sane da Auwal yace zai shigo kuma tunda yace zaizo na kuma nace eh to babu fashi sai ya shigo tunda wannan damar yake nema kenan a wajena dan har Baba yasan yana sona tunda kafin ya tunkareni sai da ya aiko gidanmu aka nema mashi izini a wajen Baba sannan.

Wanka na karayi na dauro alwallah atamfa na fiddo wata marron mai toching din green na saka nayi sallah ,bayan na gama sallah nazauna na fara shiryawa kwaliya nayi dai doi gwargwado poder da kwali dai man baki da na shafa ma lips dina sannan na zauna daurin dan kwali,daman duk gidanmu na fisu iya daurin dankwali har mamaki suke a Ina na koyo,watarana ni ke masu daurin dan kwalin.

Ina cikin yi ya kirani waya ga shi nan a kofar gida,bayan na ajiye wayar na fito parlo Ina cema Saddiqa. "Kije ki shigo da Yaya Auwal yana kofar gida." Tashi tayi tana murmushi tace.."laaa Yaya Jidda ashe yau Yaya Auwal zaizo,shine baki gaya man ba nace ya taho man da doki."murmushi nayi Ina cewa.."Saddiqa kenan,ke damuwarki kenan doki ko.?" D'aga man kai tayi tana cewa."eh Yaya Jidda har da Zaki ma sai mota da jirgi." Lakutar hancinta nayi Ina cewa."karki damu zan sawo maki har da jirgin ruwa ma,je ki shigo dashi." Da gudu ta fita sai tsalle take zan saya mata harda jirgin ruwa.

Koma nayi ciki na dan fasa turare na kara gyara fuskarta sannan na fito,zaune na tadda su a parlo shi da Saddiqa da Rukky sai zuba suke,sai labari Saddiqa take bashi zan sawo mata doki da zaki harda jirgin ruwa dana sama,shi kuwa sai dariya yake yana tayasu Shima zai saya masu har da Yar Baby mai magana ma,amman idan suka kawo mashi na daya a wannan term din nasu,sai murna suke suna cewa zasu kawo mashi kuwa mudun zai saya masu, chocolate ya basu suna godiya suka bar parlon murmushi nayi Ina samun waje na zauna,gaidashi nayi Ina mai mashi sannu da zuwa Meenat ta shigo da abinci da ruwa sai lemu ta ajiye mashi,ta gaidashi ta koma room dinmu,saukowa nayi na zuba mashi abinci da ruwa na koma na zauna Ina mashi bissimllah.

Kallona yayi yana cewa."Gimbiyata ganinki kawai da nayi har naji cikin nawa ya cika babu wajen da wanann abincin zai samu shiga fa."langwabar da Kai gefe nayi Ina cewa.."nidai nidai gaskiya A'a Yaya Auwal sai kaci wanann abincin idan baka san  Meenat taji ba dadi,tunda dai ita ta kawo maka bani ba." Kwafe yayi da Ido baice man komai ba,maida kaina kasa nayi Ina wasa da yatsen hannuna,dan jin idonunshi nike suna yawo a jikinta,takurewa nayi waje daya Ina dan turo baki gaba, girgiza kai yayi yana murmushi yace.

"JIDDA."

Dago kaina nayi Ina kallonshi baice komai ba,sai kuma na sauke kaina ina yar'karamar ajiyar zuciya, murmushi ya Kara yi a karo na biyu uana cewa."har ban san wani irin so nike maki ba Jidda,ban san ya zan kwatanta maki son nike maka ba,inasonki Ina kaunarki banda gurin da ya wuce na aureki kice rayuwata,karda ki juyaman baya karda kik'ini ,idan har kika zabi wani na ba bani ba ban san a wani hali zan shiga ba Jidda."

Ruwa ya dan kurbe ya ajiye ya cigaba da cewa.."zan zamai maki bango,zan zamai maki abun alfahari zan kula dake na tairairayaki kamar kwai ko kuma nace kamar tsoka daya a miya,zan baki duk wani jindadi dakike bukata a duniya zan nuna ma duniya kece sarauniyata zan nuna ma duniya cewa kece rayuwata,zan nuna ma duniya cewa kece dai Wanda ba zan iya yin komai ba idan baki a kusa dani,Ina sonki ina kaunarki Jidda."

Magangunanshi sunsa jikina yayi sanyi har ban san mai zance mashi ba,Ina mamakin wani irin so ne haka Yaya Auwal yake man?maiyasa zuciyata,ta kasa amincewa da son wanann bawan Allah?ta kasan ido na kare mashi kallo bai da makusa bai da aibu banga ta inda Allah ya rageshi ba,amman ban san hali ba maybe tana nan za'a ga nak'asun shi,amman dai yana da kyau daidai gwargwado yana da kudi yana da mota yana da kuma gida mai gate ma,ga kuma ilimin boko har da na isilamiya,amman ni ko daya ban jin sonshi a zuciyata ban jin shi ko kadan a raina,ya zanyi da wannan bawan Allah?tambayar da nayi ma kaina kenan, Ina cikin tunanin sai naji yana cewa.

"Jiddarnah."

Again dagowa nayi na kalleshi sai na sakar mashi murmushi Ina cewa."ba iya ruwa nike son ka sha ba,nidai har da abinci gaskiya nike son kaci." Lumshe idonshi yayi yana saukesu a kaina yace.."dagaske fa nike maki sonki ya cika man ciki babu waje a cikinshi." Maida kaina gefe nayi alamun nayi fushi,dan murmushi yayi mai sauti yana cewa.."Ina neman afuwa Gimbiyata zanci kadan yayi ko."? girgiza mashi Kai nayi Ina cewa.."aa baiyi ba,da yawa nike son kaci har sai ka cinye shi inba haka ba nayi maka kuka,kuma ba ruwana dakai."

Saukowa yayi yana zama kasa yace."kina son kenan yau na kwana a gadon asibiti ko.?"Dan kallonshi nayi ,sai nayi kasa da kaina ina cewa."kwana a gadon asibiti kuma Yaya Auwal.?" d'aga man kai yayi yana cewa."kwarai kuma Jidda,zan iya mutuwa ma idan har kika ce zakiyi fushi dani." Murmushi kawai nayi Ina cewa."nidai kaci kawai gaskiya Yaya Auwal." Spoon ya dauka ya fara tsokalar abincin yana ci, ya dan ci sosai sai da naga yaci yafi rabi sanann na hakura ya kyale abincin,goge bakinshi da tissue yayi yana cewa.

"Jidda cikina ya kusa fashewa fah,ga kuma abincin Masha Allah yayi dadi sosai." Murmushi nayi kawai bance mashi Komai ba,Rolex din hannun shi ya duba yana cewa. "Har Tara ta kusa Jidda ,dare nayi tafiya gida zanyi abunka da tuzuru na samu wajen da  zan yada kwafaduna,amman Jidda har zan tafi baki ceman komai ba." Cikin muryar tausayi yayi maganar, tabbas Yaya Auwal mutumin ne mai hakuri da  kawaici,wannan shine zuwanshi na uku a wajena da sunan zance,kuma duk zuwan da yake ban taba bashi ansar na yarda da soyayyar shi ba,sai dai nai ta yi mashi hanya hanya har ya tafi ,amman bai taba nunaman rashin jindadinshi ba,sai dai kullun ya dunga nunaman soyayyar da yake ma da nuna man girmanta a gareshi,ajiyar zuciya na sauke Ina cewa.

"Gaskiya kam dare yayi Yaya Auwal." Glass din idonshi ya cire yana goge zubar da ta dan kwanta mashi a gefen idon,goge glass din yayi ya maida yace. "Ai nasani dare yayi Jidda,abunda nike ce maki baki ce komai ba." Ni kunyar shi nike ji,dan har ga Allah ba zan iya ce mashi ban sonshi ba Kai tsaye,ba zan iya ba dan Yaya Auwal mutumin kirki ne ga shi kuma abokin Yaya Muhammad,da kunya na kalli tsabar idonshi na gaya mashi bani sonshi ,Ina ba zan iya ba bakina ba zai iya furta mashi wannan kalma mai nauyi haka ba,hakama bakina ba zai iya furta mashi Kalma so ba,dan nasan ko na fada karya nike mashi ba gaskiya bace kuma ni ban san yaudarar mutumin kirki kamar Yaya Auwal,gyara zamana nayi Ina cewa.

*Yanzun aka fara labarin JIDDH, Ina son kuyi man uzuri ku natsu ku karanta labarin BEAUTER ku kuma fahimce shi ku gaya man  SANADIN WAYE? Inason ta hanyar comment ku gayaman WAYE SILAR,amman sai kunyi hakuri kun bini a yanda labarin yazo ngd*

*Jama'a ku dunga sayen data fa🤓*

*AMATULLAH DATA SERVICES*

*MTN*
500MB-140
1GB-270
2GB-540
3GB-810
4GB-1080
5GB-1350
6GB-1620
7GB-1890
8GB-2160
9GB-2430
10GB-2700

*AIRTEL*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

*GLO*
500MB-180
1GB-350
2GB-700
3GB-1050
4GB-1400
5GB-1750
6GB-2100
7GB-2450
8GB-2800
9GB-3150
10GB-3500

9MOBILE
500MB-150
1GB-300
2GB-600
3GB-900
4GB-1200
5GB-1500
6GB-1800
7GB-2100
8GB-2400
9GB-2700
10GB-3000

VIA✓8160508316
Jamila Bello Abubakar
Opay bank
VIA✓0777512438
Jamila Abubakar Bello
Access bank

08160508316 for call or whatsapp

Share ✓

Continue Reading

You'll Also Like

354K 1K 10
Fun wlw sex. Different kinks and stuff, all about trying things. May even include potential plot lines and will definitely include some form after ca...
3.3M 206K 90
What will happen when an innocent girl gets trapped in the clutches of a devil mafia? This is the story of Rishabh and Anokhi. Anokhi's life is as...
3.6M 152K 61
The story of Abeer Singh Rathore and Chandni Sharma continue.............. when Destiny bond two strangers in holy bond accidentally ❣️ Cover credit...
231K 9K 35
The Sokolov brothers are everything most girls want. Intimidating, tall, broody, they are everything to lust after. Not that they... particularly car...