ALAQAR MU

By Hafsatouamjad2

70 1 0

It works on sympathetic,fiction and romantic love story More

Chapter 2
chapter 3
chapter 4
Chapter 5
chapter 6
chapter 7
chapter 8

chapter 1

34 1 0
By Hafsatouamjad2

💋_ALAQAR MU!💋_
~Our Destiny!~

©️®️~Hafsatouamjad~

Chapter 1

~DANDANO~!

✍️Tafe yake da ɗan gudun sa akan shimfiɗaɗɗiyar kwaltar da ya ƙawata street ɗin gabaɗaya, gidaje ne a jejjere wanda kusan ginin su duk iri ɗaya ne, yayin da wasu irin haɗaɗɗun flowers suka yiwa ƙofar kowane gidan ƙawanya.

Shar kwaltar take babu gilmawar motoci haka kuma ungwan yake tsit kowa na rufe cikin gidan shi kasancewar duhun asuba bai gama yayewa garin yayi haske baki ɗaya ba.

Farin saurayi ne wanda yake late 38 ɗin sa, kallo ɗaya zaka yi masa ka fahimci arziki da nasaba sun zaunar masa duba da irin yadda fatar jikin sa take sheƙi, fararen murɗaɗɗun muscles ɗin sa dake bayyane kasancewar shigar armless pajamas ɗin dake jikin sa ne zai sake tabbatar maka da shi ɗin ba irin ƙananun masu arziƙin nan bane ba, haka kuma jikin sa ke a murɗe kasancewar sa ma'abocin motsa jiki a kullum.

Ɗan dakatawa yayi da gudun da yake yana stretching hannayen sa cikin kwarewa, a takaice dai jogging ya fito kamar yadda ya saba a kullum.

Cigaba yayi da gudun nasa wanda za'a iya alaƙanta hakan da sauri, so yake ya koma gida ganin dai garin ya fara haske.

Shigowar sa street ɗin su ya nufi hanƴar gidan su zuciyar sa cike da kwaɗayin early morning coffee ɗin da mahaifiyar sa ta saba haɗa masa.

Tafiya ya soma cikin takun sa mai ɗaukar hankali hannayen sa zube cikin aljihun wandon sa yayin da yake ɗan kaɗa kansa sakamakon head-phone ɗin dake manne da kunnen sa yana sauraran ƙira'ar Sheikh Abdul Rahman Mas'ood, kansa sadde a ƙasa as usual yazo wucewa ta ƙofar gidan dake kusa da nasu, a kullum yana ƙoƙarin avoiding kallon gidan ba dan komai ba sai dan dalilin da ya bar wa zuciyar sa shi kaɗai.

Bai idda ƙarasa zuwa ƙofar gidan su ba idanun sa suka sauƙa kan wani abu da yaja hankalin sa, sam shi ba mutum ne mai shiga sabgar da ba tasa ba, but haka kurum ya tsinci kansa da dosar inda yake ganin abin wanda dai yafi kama da mutum.

Saurin ja yayi ya tsaya expression ɗin fuskar sa na canzawa zuwa mamaki, he can't believe abin da idanun sa ke gane masa.

At first yayi tunanin wucewa kawai yayi tafiyar sa sai dai kuma ba zai taɓa yin hakan ba kasancewar sa mutum mai tausayi da kuma sanin yakamata.

Jujjuyawa yayi yaga street ɗin shal babu kowa kafin yayi saurin ƙarasawa inda yarinƴar da he has no idea koh wacece ke yashe.

Durƙusawa yayi kan guiwowin sa yana ƙare mata kallo, doguwar rigar abaya ce a jikin ta wanda bai gama rufe mata fararen ƙafafuwan ta da jini ya ɓata ba, fuskar ta kuwa rufe take da doguwar gashin kanta hakan ya sanƴa bai gane koh wacece ba.

Ganin ta cikin halin nan ba ƙaramin tsorata shi yayi ba, abu ɗaya ke bashi mamaki yadda akayi aka yasar da ita anan ba tare da sanin kowa ba.

A hankali ya kai hannu ya yaye gashin da ya rufe mata fuskar yayin da idanun sa suka yi arba da kyakkyawar fuskar ta.

Wani irin mugun shock ya shiga ganin zuciyar sa na beating so very fast sakamakon wacce yake gani kwance wacce sam babu alamun numfashi tattare da ita.

Wawwaigawa yayi sai dai babu kowa anan wurin in banda kukan tsuntsaye da ya cika wurin, sake maido duban sa yayi kanta kafin ya kalli ƙofar gidan da aka jefar da ita inda nan ne gidan su yarinƴar.

Baiyi wata-wata ba ya miƙe da saurin sa ya faɗa gidan su wanda ke makwabtaka da gidan su yarinƴar, koh mai gadi dake yi masa gaisuwa bai amsa ba sai ma haɗaɗɗiyar part ɗin sa da ya nufa tare da zaro makulli ɗaya cikin keys ɗin dake jere a wurin ya fito, danna control ɗin makullin yayi take mota ɗaya ta bada ƙara haɗi da jan light inda baiyi wata-wata ba ya nufi motar ya shige, mai gadin ganin ya doso gate da gudu ya sanƴa shi saurin zuwa ya danna wani abu kamar switch take gate ɗin ta buɗe da kanta ya fice daga gidan.

Parking motar yayi tare da fitowa da sauri zuwa inda take ya cicciɓe ta ya kai mota kafin ya tada ya bar cikin unguwar.

*************

Babban private hospital ne wanda masu hannu da shuni kawai ke iya ziyarta dan kuwa rabin ma'aikatan ciki ma ba ƴan Nigeria bane, ba'a tsaya jan lokaci ba aka karɓe ta daga hannun sa inda duk rigar sa ta ɓaci da jini.

"Please come with us sir" cewar wata nurse inda yayi saurin mara mata baya zuwa wani office, file ta bashi ya cike ba tare da damuwa da wasu abubuwan da ma yake sakawa ba dan shi babban burin sa shine ta farfaɗo, ganin wannan hali da take ciki sosai ya tada masa matsananciyar soyayyar da yake yi mata wanda bai taɓa furta wani ba ya dai bar abin a zuciyar sa ne ganin tana da wanda take so har ma an sanƴa musu ranar aure nan da wata ɗaya sai kuma abin nan ya faru, he can't believe how cruel people can be, dukda bai san taƙamaiman abin da ya faru ba tukun but yana da yaƙinin fyaɗe akayi mata sannan saboda zalunci aka zo aka jefar da ita a ƙofar gidan su, sosai zuciyar sa ke mugun tafarfasa inda har jikin sa rawa yake yayin da yake cika file ɗin, ajiye pen ɗin yayi bayan ya gama cikewa sannan ya jingina da kujerar da yake kai yana mai dafa goshin sa da yake jin kamar ya faɗo dan azaba.

"Sir, zamuje kayi payment ɗin treatment ɗin ta."

Ɗan ɗagowa yayi ya kalli nurse ɗin sam ya mance bai fito da katin sa koh wayar sa ba.

Da kyar ya iya buɗar baki yace "Am sorry am not with my card, can you please start the treatment before naje na dawo, i promise to be back on time."

Shiru ta ɗan yi kafin tace "Am sorry sir, but you have to explain that to the doctor."

Ji yake kamar ya make ta dan haushi gabaɗaya ƙara masa ciwon kai take da maganar da take yi, he wonder maiyasa ma yake ɓatawa kansa lokaci bayan ya san likitoci dayawa a wannan asibitin.

Bai ce da ita komai ba ya tashi ya fice dan kuwa sam baya son rainin wayo musamman ma yadda take masa magana yana bata amsa gabaɗaya yanzu sai taga daman sa taje bayida aji dan sam mata ba'a sake musu fuska yanzu sai su bi su raina mutum, ɗan tsaki yaja ganin wani likita ya doso inda yake tsaye.

"Ohh, Mr Nurain" ya faɗa yana miƙa masa hannu suka yi musabaha.

"It's been a while how have you been?."

"Good" kawai ya amsa masa hankalin sa duk ya koma kan ɗakin da yarinƴar ke ciki inda yaga wata likita mace ta shiga yanzu hakan ya sanƴa hankalin sa ɗan kwanciya.

"Ahm, what are you doing here, wani ne babu lafiya?."

Kamar ba zai bashi amsa ba kuma ya fuske yace "Yeah, I will be going I have something to cover" yana faɗin haka yayi wucewar sa zuwa inda zashi.

Within 20mins yaje ya dawo tare da yin payment ya biya duk wasu kuɗaɗen da za'a buƙata yayi covering komai, sai dai har yanzu ba'a fito da ita daga ɗakin da aka shiga da ita ɗin ba.

Family ɗin ta ne suka faɗo masa a rai nan yayi saurin fiddo da wayar sa da ya ɗauko a gida yana shirin kiran mahaifiyar sa duba da yadda baya shiri da koh ɗaya daga cikin yayun ta masu yi masa kallon mai girman kai shi kuwa ke yi musu kallon ƴan rainin hankali hakan yasa bai mallaki numbern koh ɗaya daga cikin su, sai dai da yake mahaifiyar sa na shiri da mahaifiyar yarinƴar sosai yasa kawai yake son kiran ta ta sanar dasu.

Katse kiran yayi kawai ya maida wayar aljihun sa har sai ta farfaɗo kafin ya kira su.

Kusan mintina ashirin ya ƙara a tsaye zuwa lokacin har mahaifiyar sa ta gaji da kiran sa.

Fitowar doctor ɗin ya sanƴa shi saurin nufar ta, ba tare da ta kalle shi ba taje "Biyo ni."

Ɗan jim yayi yana kallon cikin ɗakin koh zai hango ta kafin kuma ya haƙura yabi bayan likitar da zata kai sa'ar mahaifiyar sa.

A office ɗin ta suka yaɗa zango fuskar nan tata babu walwala da alama dai ranta a ɓace yake, aikuwa kamar jira take ya zauna ta hau shi da faɗa "Wannan wani irin zalunci ne? Meke damunka kana cikin hankalinka Kayiwa Matar ka haka ?is this by force ? A wani hadisi kaji ance ka karbi hakkin ka ta karfi da yaji awurin Matar ka ,the worst thing shine desired tablet da ka bata ,Banda maganin bacci all this for what please ,gaskiya ka bani mamaki ahaka dai gakanan kamar me hankali kuma kai ba yaro bane fisabillilah kun maida Matan ku abun wulakantawa .wallahil azeem a k'aida se police sun shiga maganar nan sabida ka zalunci yarinya karama ,meyasa ma iyayenta suka aurar da ita at this early age ,, da kyar muka samu muka tsayar da bleeding ɗin da take yi, shikenan ku maza daga an aura muku mace sai ku maida ita tamkar babyn biyar buƙatar ku babu hutu, wannan abun ai yayi muni dayawa matar ka ce fah, maiyasa ba zaka bita a hankali da lallama ka samu biyan buƙatar ka ita ma ta samu gamsuwa ba, dan Allah ka gyara babu mai kwace maka ita, duk lokacin da kake son abin ka zaka iya nema amma ba ta ƙarfi da yaji ba dole sai da lallama, yanzu dai mun samu munyi mata ɗinki, sannan anyi mata ƙarin ruwa da jini, anytime sooner zata iya farfaɗowa, sai dai fah koh an sallameku ba zaka kusance ta ba har sai ta gama warkewa duka gudun kada a samu wata matsalar."

Tun da ta fara bayani kansa ke sadde a ƙasa zuciyar sa tamkar zata faso ƙirjin sa ta fito, why is she putting the blame on him, all he did was to help the poor girl ya kawo ta asibiti, koh dayake yadda ya kawo ta ɗin kowa will think ita ɗin matar sa ce, so dagaske ya tabbata fyaɗe akayi mata, sosai idanun sa suka kaɗa jijiyoyin hannayen sa dake a dunƙule duk sun tashi raɗo -raɗo, he wait to have the bastard ɗin da yayi mata hakan a hannun sa, he won't spare the devil.

A fusace ya miƙe ya fice daga office ɗin yayi ɗakin da aka kwantar da ita, jini ne ake ƙara mata inda take kwance cikin hospital gown gashin ta ya bazu akan pillow ɗin da take kwance.

Da kyar ya iya zama kan kujerar dake kusa da bed ɗin yana kallon kyakkyawar pale fuskar ta, ya ɗau minutes yana kallon ta kafin ya saki murmushi mai ciwo yana taune lower lips ɗin sa da ƙarfi, shi kaɗai ya san mai yakeji game da ita, sam bai san da cewa haka yake tsananin ƙaunar ta ba sai da ya ganta cikin wannan hali, sannan yayi alƙawarin ganin bayan duk shaiɗanin da ya aikata mata haka, koh da ba zata so shi ba shi kuma ba zai fasa ɗaukan mata fansa ba.

Wannan littafin na kudi ne it's just 500 for more enquiries contact me via 08100312134 .

Continue Reading

You'll Also Like

1.6M 140K 65
RATHOD In a broken family, every person suffers from his insecurities and guilt. Successful in every field but a big failure when it comes to emotio...
Cecilia By Anastasia

General Fiction

27.5K 639 26
Cecilia's father, a well-known and successful lawyer, was tired of her problems. Tired of the issues she had been causing for the family and it's nam...
605K 20.3K 168
The young lady from the Xue family was talented and beautiful, and married the dream husband at the age of 16. They had a loving and harmonious relat...
Alina By ihidethisapp

General Fiction

1.5M 39.3K 80
The Lombardi family is the most notorious group in the crime world. They rule both the American and Italian mafias and have many others bowing at the...