WANI GARI

By KhadeejaCandy

10.4K 566 36

A wani gari, da al'ummarsa basa hada jini da mutanen wajen garin, akwai wata yarinya da alkalamin kaddara yay... More

WG-01
WG-02
WG-03
WG-04
00
WG-05
WG_06
07
08
09
WG-10
11
12
13
15

14

465 27 1
By KhadeejaCandy

Ta juyo da sauri ta kalli Ummi hawaye na sauko mata da bibiyu.

“Ban aikata komai ba, ban yi komai ba Abiey ka yarda da ni”

Ta sake juyawa ga mahaifinta.

“Ina motarki take?”

Mahmood ya tambaya sai ta kasa furta komai, ta sani idan ta fada laifinta kara girma zai yi, kuma bata son iyayenta su sake kallon Ameer da wani laifin, bata kiyayyarsa ta girmama a zuciyarsu. Ummi ta kalli mijinta.

“Bari na yi magana da ita private”

A take Abiey ya daka mata tsawa.

“No a nan zata amsa mana, ba sai anje wani gurin ba domin police za su su tafi da ita, su ai dole ta fada musu gaskiya idan mu ta boye mana, dole ta fada mana abun da ya kai motarta Kt tare da wasu tarduna nata da suke motar da duk wasu bayananta, tun daga kt aka turowa CP na garin nan abun da ya faru, shi ya turo min komai kuma ya tabbatar min za su zo su tafi dake saboda an ga gawa a cikin motarki”

Ummi ta zaro ido tare da dukan kirji, sai a yanzu ta yarda lamarin babba ne. Gaba daya sai idon kowa ya dawo kanta, not just her body har muryarta da idonta rawa yake duk sanyin falon sai da gumi ya kwankwasa mata kofa, tashin hankali yace baki ga komai ba sai a yanzu, gaba daya sai ta manta da tsoron fadin wanda ta bawa motar, furucin mahaifinta cewa an ga gawa ya fi komai daga mata hankali.

“Ameer na bawa motar Abiey gawar wa aka gani?”

“Wane Ameer din?”

Sai a wannan karon Maleek ya saka bakinsa with confused.

“Ameer abokinka”

Ta amsa kai tsaye, a take Abiey ya sauke mata lafiyayyen mari sai da ta fadi kasa.

“Ta ina kika alakantu da shi? Miye hadinki da shi? Ina kika san shi har zaki dauki motarki ki bawa makiyin ďana? Kin kyauta gashi yanzu an yi miki sakamako kuma zaki girbi abun da kika shuka”

Ummi ta yi saurin shiga tsakiyarsu hawaye na cika idonta, kafafuwanta suka fara juyawa kamar ba za su dauke ta.

“Ga.. Ga.. Ga...ga... ”

So take ta tambaya gawar waye a motar amman ta kasa, saboda tsoro irin amsar da za a bata gashi maganar ma ta gagara fitowa. Mamaki ya hana Mahmood da Maleek cewa komai sai kallonta suke bama kamar Maleek. Abiey ya juya ya fice daga falon cikin wani irin fushi da bacin rai da ya dauki shekaru be ziyarce shi ba. Yana fita Ummi ta duka ta kama Nimra dake kuka.

“Ummi ban yi da wata manufa ba, ya fada min mahaifinshi ya koreshi kuma be san inda zai je ba, na bashi motata da kudi da ATM, amman ban san inda yaje ba, kuma ban aikata hakan da sanin cewar shi ne wanda suka yi fada da Ya Maleek ba, Allah ne shaidata ban sani ba Ummi”

Ummi ta rumgume ta tana kuka. Ummi ta amsa mata ta hayar daga mata kai alamar ta gamsu, sai dai zuciyarta ya samu rauni na rashin jin halin da Ameer yake ciki. Nimra ta dago ta kalli Maleek da ya kasa motsawa daga inda yake tsaye.

“Gawar waye a motar Ya Maleek? Kashe kansa yayi? Ko hadari yayi? Ina Ameer din yake?”

Sanin halin da Ameer yake shi yafi tsaya mata a rai sama da abun da aka zarginta da aikata, ji take idan aka samu gawar wani wanda ba shi ba abun zai zo mata da sauki, amman idan gawarsa shi ta wanne zata ji? Mutuwarsa ko zargin da ake mata?

“Gawar wata yarinya ce”

Maleek ya amsa mata, ita aka amsawa amman Ummi ce ta fi jin sanyi a ranta a take ta lumshe ido ta sauke ajiyar zuciya, kamin ta mike tsaye da sauri ta fice zuwa bangaren Abiey, ko da ta shiga ta same shi yana aikin saka sabon tufafi.

“Da gaske bari zaka yi police su tafi da ita? Abiey zaka iya kashe wutar nan daga nan gida ma ba sai an tafi da ita ba, Nimra macece be kamata a shigo har cikin gidan ubanta a kamata da laifin da bata aikata ba to miye amfanin dukiya da ikon Ubanta?”

Abiey ya juyo fuska a hade kamar garwashi ya kalli Ummi.

“To waya aikata? Miyasa kika goya mata baya ta aikata abun da ta aikata? Akan mi zaki shigar da yata a cikin lamarin rayuwar wani yaron can da bamu da alaka da shi? I warned you Zahra na fada miki ina son farinciki yayana fiye da nawa farinciki, sai dai na lura ke tashin hankali kike so, to ko hankali kowa zai tashi! Akan me zaki yarda ta bashi motarta da kudi saboda ya boya? A tunaninkin kin ni wayo?”

Na girgiza masa kai da sauri.

“Ba da sanina ta aikata ba?”

“Idan zaki hade min Qur'ane ba zan yarda dake ba, kin fi kowa kusanci da Nimra kin san duk wani abu da take in and out. Enough is enough and lemme tell you something har abada ba zan taba amsar Ameeer a matsayin ďanki ba, ba zan taba son ďan makiyina ba, ba kuma zan taba son ďan da kika kaunar ubansa har yanzu ba, idan kika aikata kuskure rayuwar Ameer zaki jefa a hadari domin zai rasa gata ta ko'ina daga nan zaki gane kuskuren neman kusancin da kike da shi...!”

Tsaye ta yi a gurin kamar an dasata, duk wasu kalamai da zasu jefata a damuwa Abiey ya furta mata su akan rashin sani, kasa motsi ta yi har ya gama canja kayan ya saka babbar rigarsa ya fice daga dakin. Sai a lokacin ta samu juyowa tana tafiya kamar bata iya daga kafar, daker ta dawo bangarenta tana tafiya kalaman mijinta na zagaye duniyar tunaninta. Ba su dauka da gaske Abiey zai bar police su shigo har cikin gidansa cikin falonsa su kama yarsa ba sai da aka taba kofar ta yi kara ta sanar musu akwai baki a waje. Kowa ya kasa bude kofar daga Mahmood har Maleek balle kuma Ummi da Nimra ta tashi ta koma kusa da ita ta rike ta tana kuka. Da ido Maleek yayi ma Mahmood alama da yaje ya bude kofar, cikin karfin hali Mahmood ya isa kofar ya bude gabansa sai faduwa yake domin abun ne da basu saba ba, shigowa gidan ma police ba su isa su yi ba sai dan izinin da mahaifinsu ya ba su. Gaba tarda kansa police din yayi a matsayin jami'in tsaro sannan ya nuna masa arrest warrant. Maleek ya nufi kofar ya tsaya yana kallon police din ya ce.

“Motar ta ce kawai, amman abun da kuke zargi ba ita ta aikata ba, ni ma kuma ba da ganganci na aikata hakan ba, daga ita har ni zamu zo station yanzu nan, amman zaku ba mu police daya da zamu tafi tareda shi a motar gida”

Su sansu sun san inda suka shigo, hakan ya saka ba su masa musun abun da ya bukata ba suka amince, sai ya juyo ya dawo cikin falon ya kalli Nimra ya ce.

“Tafi ki dauko mayafinki, kuma duk tambayar da za ayi miki ki ce ni na karbi motarki”

Ta daga masa kai sannan ta tashi da sauri ta shiga ciki, fitowarta ya zama aiki domin gani take kamar idan taje ba zata dawo ba, na tsoron yan sanda take ba domin a masu gadin gidansu ma akwai police fushin mahaifinta take tsoro kar ya sa a yanke mata hukunci mai tsauri. Maleek ne yaja motar dayan police din yana front seat Nimra kuma na baya. Aka bar Ummi daga ita sai mai aikinta da ta gagara komai sai kallon ikon Allah take, da can bata san miya faru ba amman a yanzu ta fara fahimta akwai matsala a gidan. Wani dishe-dishe Ummi ta fara gani yana jin jikinta babu karfi ko'ina ya dauki ziza kamar jijiyarta ta yi majirya ga kanta dake sarawa, dafa kan ta yi tana wani tangadi kamar wanda ta sha kayan maye, Mahmood na ganin haka yayi saurin karaso ya riketa ya zaunar da ita mai aikinta ma ta karoso kusa da ita tana mata sannu, bata iya amsawa domin bata jin wani kuzari na magana ma balle motsi, sai dai hankalinta be gushe ba, wani kalar yanayi take ji a jikinta wanda ya banbanta da wanda ta saba ji, a duk lokacin da kalar rashin lafiyar ta ziyarceta.

“Mahmood kai ni daki zan kwanta”

Ya mike tsaye da taimakon mai aikinsu suka haura da ita sama suka kwantar da ita kan gadonta, Mahmood ya lullubeta da blanket sannan ya kashe Ac dakin ya fito ransa a jagule. Lumshe ido ta yiba dan bachi ba sai dan ta samu sa'ida, tana jin yawunta ya kafe sosai har ya haddasa mata bushewar baki, 

AMEER POV.

Yana tsaka da wanke idonsa fuskar Waira ta yi masa gizo, be san lokacin da ya bude idon haka da kumfa ba, a take yaji ya shige masa a idon, a nan yaji wani sabon amai na taso masa yana ta jin kyankyami a jikinsa, tun da yake a rayuwar be taba wanka tara at the same time ba sai yau, ba wanka iya na sabulu ba har da na tsarki sai da yayi ba kuma dan yayi komai ba, sai dan ganin Waira da yayi da tabata da carpet din yake ji ba kamar ma har da wankan tsarki yana bukata saboda kazantar ta yi jawa wata kila idan be yi wankan tsarki ba zai iya jawa kansa matsala aki karbar sallah shi.
  Ya san yadda Hajiya Jamila take sakawa a tsabtace komai na dakinsa amman hakan be kwantar masa da hankali ya taba tawul din dake aje a bathroom din ba, haka ya fito ya nufi gurin da tufafinsa suke aje ya dauko sabbi fil ya saka sannan ya shafama jikinsa mai ya saka turare, talkami ya saka ya sauko fito daga dakinsa zuwa falon Hajiya Jamila tea ta fara tarbonsa da shi sannan ta zuba masa soyayyaen nama domin ya san yadda yake son naman da aka soya suya mai kyau, doya ta sarrafa masa da miyar kabeji wanda ta ji kaza, tun kan ta kawo masa abincin kamshi ya cika hancinsa.  Lafiya lafiya ya fara cin abincin kamin ya tuna da kazantar Waira sai gashi ya tashi da sauri ya nufi bathroom din Hajiya Jamila cikin tashin hankali ta bi bayansa tana tambayar ko abincin ne be masa dadi ba ko kuma wani abun ya gani a ciki. Haka ta tsaya a bayansa tana kallonsa har ya gama aman ta kunna fanfo ta tara masa ruwa ya wanke bakinsa.

“Wani abu ka gani a cikin abincin ne?”

“No inda na tafi ne na ga wata kazanta da ban taba gani a rayuwata ba”

“Ina kaje Ameer?”

“Wani daji ne, a KT”

Bedroom suka dawo, ya zauna ya labarta Hajiya Jamila duk abun da ya faru ciki har da motar da Nimra ta bashi and da reason din da yake ganin ya saka ta ba shi motar. A yanayin yadda ya bata labarin ta gama fahimtar bashi da gaskiya domin shi ya fara tsokanar abokin nasa amman tsoron bacin ransa ya saka ta kasa nuna masa sai tausarshi take kar ya aikata abun da zai zame masa matsala.

“Da ka yi hakuri ka kyaleshi Ameer idan ma ya ci amanarka zai gani a nan gaba, zalinci ba shi da kyau idan ka zalinci mutum komai ta dade sai hakkinsa ya fita, ka saka masa ido kana zaune hakkinka zai ita matukar ya zalince ka Allah ba zai bar shi ba”

“Ni ko ba a taba ni ba, kin san zan taba balle kuma an taba ni, bana bari ga Allah”

Ya amsa mata kai tsaye, numfashi ta sauke a hankali ta mike tsaye.

“A dauko maka wani abincin?”

“Na koshi, a sama min flight din da zai tafi Abuja anjima zan kwanta yanzu idan babu kuma zan je da mota”

“Ba zaka kwana a nan ba?”

“No ina son na je na duba jikin Daddy hankalina ba zai kwanta ba sai na ganshi”

Hajiya Jamila ta shafa kansa, sannan ta fice cike da damuwar da ita kadai ta santa. Kwanta yayi saman lafiyayyen gadon abun ka da wanda ya marmarin bachi nan da nan bachin yayi gaba da shi.
  Mafarkinsa gaba daya akan yarinyar da tunaninta ke saka shi tashin zuciya da mai ne, ba mafarkin abun da ya faru a dajin yake ba, mafarki yake akan wata yarinyar da aka tsabtace ta sha ido da kwalliya, kamshi ta ko'ina ta ratso taron jama'ar da ake gabatar da Event din da be san na minene ba, ta iso gare shi, sai ya risina kamar mai jiran isowarta ta saddan kansa kasa alamar girmamawa a gareta ita kuma ta cire wani zare a hannunta ta daura masa a wuya ta yi mashi murmushi, sannan ta juya ta fice daga taron a zuwa wani dakin dake da icen tuffa ga kuma wani itacen na dogon yaro (Dalbejiya or Bedi) a tsaye. Can kuma mafarkinsa ya sake daukarsa zuwa gidansu Nimra, kuka ya hango tana yi tana fadar shi yayi kisa ba ita ba, hakan ya sake haddasa fada a tsakaninsa da mahaifinsa har ya sake korarsa a karo na biyu...! Firgigit ya farko daga bachin na rana ya yarfar da hannu ya shafe wuyansa, tsabar kyamar Waira da yake ko a mafarki ya ga ta taba shi kazanta yake ji, Even though ya san mafarki ne amman hakan be hana shi sake yin wani wankan ba, har mamaki yake in wanda haukar mafarki da kwashe kwashe shi miye hadinsa da kazama da har zai kawo masa ita a bachi, ba kawo ta ne kawai matsalar ba daura masa zaren dake hannunta da tayi a wuya shi ne matsalar domin jinsa yake kamar gaske.

  Tsaki yaja yana shafa turare a wuyansa, lallai ya yarda mummunan mafarki daga shaidan yake, domin idan ba shaidan ba ta ina za a ga wannan yarinyar kazama ta yi wanka ta yi kyau tsabtsab da ita har su kamshi, a yau kam ya tabbatar da mafarkin rana shirme ne. Sai da ya saka wasu tudafin sannan ya sake komawa bathroom din yayi alwala ya fito ya karbi key din motar Hajiya Jamila ya fice daga gidan, gida biyar ya wuce sannan ya isa inda masallacin unguwar yake, yin Sallah in time kuma cikin jam'i is one of his favorites, sai dai baya jerawa da mutane sai dai ya tsaya a gafe daya, idan kuma ya samu Masallaci ya cika sai yayi sallah a waje, Saboda kar jikinsa ya taba na wani indai ba abokansa ba, sai kuma mahaifinsa da mutanen da yasan suna tsabta a yadda yake so, haka Allah yayi shi akan kyamar mutane da yake har warinsu yake ji wani lokacin.

  Bayan an sallame ya fito ya dawo gida, a nan ya samu Hajiya Jamila na hada masa cake, bayan ta gama take fada masa ba za a samu flight zuwa Abuja da yamma nan ba, amman ta masa Booking din Private jet, kuma ya jidadin haka cake din kadan ya ci daman he's not that foodie abu kadan idan ya ci ya ishe shi wani lokacin ma Lemu kawai zai wuni a cikinsa.
Karar tsayawar motar YaYan Hajiya Jamila ya tuna masa da sarewa, da sauri ya saka hannunsa aljihu yana lalabe kamar a ciki ya aje ta.

“Oh...”

Ya furta hakan yana jin wani sabon bakinciki.

“Lafiya?”

“Sarewata na bari a motar yarinyar can Wallahi”

“Mantuwa ka yi?”

“Eh ban tuna ba sai yanzu”

“Sai siyen wata kenan?”

“Ba za a samu mai kyau irinta a yanzu ba, and akwai wanda ya saka min wani abu a sarewar nan wanda idan na busa take tafiya yadda nake so”

Zanjabil da yar'uwarta Hurriyya ne suka shigo falo, suna ganinshi suka yo kansa da gudu suna murna, sai dai bacin rasa sarewarsa ya saka be wani sake musu fuska sosai ba, tunaninsa na yadda zai dawo da barsa hannunsa ne, ya san zai sha fama amman haka zai dawo da ita ko da kuwa yakin duniya na uku ne zai afku.


©Khadeeja Candy
   ©®Copyright
        2023

Continue Reading

You'll Also Like

68.6K 1.6K 38
โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€ you got me down on my knees it's getting harder to breathe out . . . โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€ ๐‘ฐ๐‘ต ๐‘พ๐‘ฏ๐‘ฐ๐‘ช๐‘ฏ . . . ๐œ๐ก๐ซ๐ข๐ฌ ๐ฌ๐ญ๐ฎ๐ซ๐ง๐ข๐จ๐ฅ๐จ ha...
625K 20.8K 169
The young lady from the Xue family was talented and beautiful, and married the dream husband at the age of 16. They had a loving and harmonious relat...
1.7M 55.9K 75
Alexander, James and Skye were triplets. They were stolen from their family at the age of 4. The family searched for them day and night never giving...
507K 11.1K 51
Two girls are exchanged at birth and are given to the wrong mothers and after 13 years the truth comes out Rosabella Rossi is different from her sist...