IMRAN

By real__ahmerd

3.8K 225 70

This story is a life hearted story about passion and compassion.... It is a story that talks about Governance... More

INTRODUCTION
0⃣0⃣1⃣
0⃣0⃣2⃣
0⃣0⃣3⃣
0⃣0⃣4⃣
0⃣0⃣5⃣
0⃣0⃣6⃣
0⃣0⃣7⃣
0⃣0⃣8⃣
0⃣0⃣9⃣

0⃣1⃣0⃣

212 18 8
By real__ahmerd

FOLLOW ME PLEASE🙏, IT WON'T TAKE YOU MORE THAN 2 SECONDS.





💐IMRAN💐
ƘIRƘIRARREN LABARI✔️

~Wannan shafin sadaukarwa ce zuwa ga Amiratuoo . Har yanzu na kasa gano kalaman da suka fi cancanta gurin nuna godiyata agareki. Ke ɗin ta musamman ce, ke ɗin tabance. Nagode sosai da irin karamcin da kikai min. Allah ya bar ƙauna!.
Itace Marubuciyar shahararren littafinnan JASMINE, idan mutum bai karanta ba yayi missing. Sannan yanzu haka ta fara updating sabon littafinta mai suna ALAƘAR MU.




SHAFI NA GOMA

Dawowar A.A Abdullahi kenan daga Masallaci yin Sallahr Magrib yayi daidai da isowar Amina bakin gate tayi horn kamar ta san da mutum a gurin, buɗe ma ta ɗan matsakaicin gate ɗin yayi ta shiga ta faka Motar ta wanda dama ba tare da wani tunani ba idan ta zo sai dai ta sauka da kanta ta buɗe gate ɗin tunda basu da mai gadi, zata iya ƙirga sau nawa ta taɓa yin horn Jummala ta zo ta buɗe ma ta, akan Abban Ubaid kam wannan shine karo na farko, tunda duk inda zata je indai ba wani sha'ani ake a dangi wanda yakamata ta kwana ba, bata wuce ƙarfe shida bata dawo gida ba, Abban Ubaid kam sai ya kai bayan Magrib ko Isha'i kafin ya dawo, idan ya dawo da wuri ne ya dawo ana gab da Sallahn Magrib.

Tana fitowa Abban Ubaid na ƙarasawa gurin ya rungumeta yana ma ta sannu da dawowa. Bayan ya raba ta da jikinshi ne ya riƙe hannunta yana faɗin...

“Sannu da ƙoƙari, ya jikin ɗan naki?. Dafatan dai ya sake samun sauƙi?...”

Ya jero mata tambayoyin ba tare da buƙatar amsar ɗaya kafin ɗayan ba. Hakan ta lura ɗabi'arshi ne tunda ta san shi. Dama ɗazun da ta kirashi da rana da buƙatar ya ɗauko Ubaid daga Makaranta ta faɗa mishi farkawan Yaro da kuma halin da yake ciki.

“Ya samu sauƙi Insha Allah tunda ya farfaɗo. Doctor dai ya mishi Allura yace yana buƙatar ya ƙara samun Hutu. Da alamun abinda ya faru da shi gagarumin abu ne da ya matuƙar taɓa mishi zuciya, faruwan abinda nake jin cewa ashekarun shi yayi ƙanƙantar da zai fara fuskantar su...”.
Ta dakata tana ƙoƙarin saisaita yanayin ta da mai da hawayen tausayin Yaron da ya cika idanunta yana yunƙurin zubowa. Duk da ƙoƙarin da tayi hakan bai hana hawayen bin gefen idanunta yana silalowa ba. Daddy ne ya sa hannu ya tallabo fuskarta yana sanya babban yatsar shi gurin goge hawayen, rungumeta ya sake yi yana tapping bayanta yana faɗin

“Allah ya bashi lapiya. Allah ya sauƙaƙa mishi ƙaddarar da zai fuskanta nan gaba a rayuwa”.

Da "Ameen!” Mummy ta amsa kafin ta raba jikinta da nashi tana zagowa gurin booth ɗin Motar ta buɗe tana fito da Basket ɗin abincin da ta tafi da shi asibitin domin Yaron, har ta bar asibitin bai farfaɗo ba yasa ta tafi da shi kawai, tunda ta kira Jummalan ta yi ma ta bayani akan kwanan da zata yi a asibitin da kuma kan abin da zata girka musu da daddaren, ta ba AlMajirai wannan ɗin kawai tunda suna zuwa watarana, ko kuma ta bawa Jummalan idan zata tafi ta biya ta gida ta baiwa Innarta. Da wannan tunanin suka shiga cikin gidan Abban Ubaid na taimakawa wurin buɗe ma ta Ƙofa suka shiga da Sallama. Ɗaki Daddy yayi yayinda Mummy kuwa ta wuce kitchen ta tura ƙofar da Sallama abakinta Jummala na amsa ma ta.
“Sannu Jummala. Sannunki da gida”.
Ta faɗi tana gani daidai lokacin ne Jummala ta gama girka abinda take girkawa tana sauke shi daga kan electric.
“Sannunki da dawowa Mummy...”. Ta faɗi tsakanin kashe Electric ɗin. Da 'Mummy' take kiranta tun lokacin da ta fara aiki a gidan lokacin Mummy nada cikin Ubaid, ita kuma a lokacin tana Junior secondary school Wanda Rasuwar Mahaifinta shine sanadiyya.
Gashi yanzu har ta gama ta zana SSCE bata da halin cigaba. Tana da burin karatu don ta zama wani abu a rayuwarta, ta tsaya da ƙafafunta kuma ta taimaki Innarta da ƴan Uwanta.

“Ya gajiyar Asibiti?. Ya mai jiki?”. ta tambayi Mommy tana fito da warmers ɗin da ta san ake zuba abincin dare acikinsu.
“Da Sauƙi Jummala. Sannunki da aiki ƴar Albarka”.  Ta faɗi tana buɗe tukunyar. Macaroni da wake tayi wanda ya ji bushasshen kifi da kayan ciki sai tashin ƙamshi yake yi. Iya girkinta na ɗaya daga cikin ababen da ya Sanya Soyayyar Jummala acikin zuciyarta, duk kuwa da cewa ita ta koya ma ta. Amma kuma bata wani sha wahala wajen koya ma tan ba kasancewar yadda yarinyar take da kaifin basira da saurin ɗaukan abu.

Duk da cewa Girki ba shi bane muhimmin abinda ya sa ta ke aiki a gidan, amma kasancewar ta iya yanzu kusan duk abincin daren gidan ita take yi yanzu. Iya girkinta a ƙananun shekaru yana ɗaya daga cikin abubuwan da Jummala zata kalli Mummy tayi Alfahari da ita. A wasu lokuta ma ta kan janyo tunanin irin soyayyar da Mummyn ke nuna ma ta kaɗan ne za'a ƙara akan wadda Inna take ma ta, sai dai kawai ta san akwai tazarar da Soyayyar da Mummyn da ta Innarta bazasu haɗu ba, Tunda ita ce Mahaifiyarta wacce ta ɗauki cikin ta har wata tara tana kwance. Yanzu ta girma ta zama budurwa sosai abun har mamaki yakan ba Amina da yadda girmanta ya faru cikin ƴan shekaru da kuma yadda ta girman. Inna tana tsokanarta akan girmanta wasu lokuta take faɗa ma ta har ta shiga watan goma kafin aka haife ta. Sai dai duk yadda ta iya girki Ubaid baya taɓa cin girkinta. Abin yana ba Mummyn mamaki ta yadda da ya sanya abincin abaki yake gane wannan ba ɗanɗanon abincin Mummyn shi bane. Kuma duk yunwar da yake ji haka yake haƙura da shi idan ba ita ta dafa ɗin ba, shiyasa take ɗiba acikin wanda tayi na rana ta saka a Fridge idan dare yayi tayi mai warming ɗin shi, baya damuwa da koma menene yake sake cin abinshi.

Mummy ce ta raba abincin a haka yau ba hirar da suka yi kowa da abin da yake saƙawa a ransa.

*******

Cikin tsananin razana, firgici, tsoro da wani irin dokawar zuciya Waleedah ke kallon system ɗin da ke gabanta, ta kasa gasgata abinda idanunta suke gane ma ta a halin yanzu. Mr. Jamaluddeen ɗinta ne ya saɓule fuskarsa izuwa wata fuska ta daban. Mr. Jamaluddeen ne da fuska biyu. Mr. Jalaluddeen ɗin da ya lalata ma ta rayuwa. Mr. Jalaluddeen ɗin da ya zame ma ta komai na ta a lokacin da bata da kowa. Mr. Jalaluddeen ɗin da ta ke da mummunan zargi akanshi. Mr. Jalaluddeen da a yanzu take bincike akanshi a matsayin Babban Mai laifin da ake zargi da ba'a da wani evidence da za'a iya kamashi da shi!!!...

Ta daɗe tana tare da Mr. Jamaluddeen tun tana 200 Level a Amoud University da ke nan Somalia. Maraicinta shine abinda ya tsayar da karatunta na wani lokaci domin dama duk hoɓɓasawar Mahaifinta AbdulMu'umin shi yake yi. Gashi lokacin da Allah yayi masa rasuwa da shi da Mahaifiyarta wacce Soyayyarta ya zame ma ta gaba a komai na rayuwarta. Ganin rashin madafar gashi ɗan abinda suke da shi da ya siyo ya ajiye na kayan abinci kafin ya rasu sai ƙarewa yake ya sa ta ɗauri aniyar fara neman aiki. Ƙaddarar haɗuwarta da Mr. Jamaluddeen shine ya sa cikin Sa'a ta samu aiki a AL-MUBARAK Hotel cikin tarin ayyukan da ta yi applying. Ƙarancin masu aiki da suke da shi a ɗan wannan lokaci ya sa aka sata room service na kaiwa waɗanda suka sauka a Hotel ɗin abinci idan sunyi Order. Da ganinta ya bayyana ma ta yadda yake ji game da ita. Tun farko ta ƙi amincewa amma saboda ita yasa ya dinga yin odar abincin da ba ci zai yi ba kawai sai don saboda ya ganta, ita kuma kafewa da tsoron saɓawa Allah ya hanata bashi haɗin kai. A ƙarshe dai haɗa kai suka yi da Chief chef na hotel ɗin aka saka ma ta ƙwayar gusar da hankali acikin ruwan shanta wanda ake bawa Ma'aikata a yayin da zataje hutawarta da daddare . Farkawa tayi kawai ta ganta akan gado, sai daga baya abubuwan suka fara dawo ma ta ɗai ɗai da ɗai ɗai ta ɓarke da kuka mai tsuma rai. Da ƙyar da lallashi ya dinga ma ta kuma ya dinga yi ma ta Alƙawurran da bata san iyakansu ba. Sai daga bisani tayi shiru tuna cewa bata da wanda zai taimaketa ko ya kula da ita sai ita da kanta. Bazata manta yanda ya ɗauketa har cikin Jakuzzi inda ya haɗa ma ta ruwan zafi yana dropping ɗinta ba. Ba zata manta irin azabar da taji da kuma yadda hawaye yake kwarara a idanunta tana yi tana tsaftace jikinta ba.

Zuwa tayi zata fice ya tsayar da ita yana mai bata wani envelope shaƙe, kamar bazata amsa ba dai ta amsa tayi gaba. Bayan ta buɗe lokacin da ta gama canza kaya zuwa Uniform zata fara aikin ranar Kuɗine shaƙe a ciki kuɗi na gugan kuɗi $150'000 Dollars!. Zuciyarta na tsananta bugu yana tsalle tamkar zai faso ƙirjinta ya fito tsabar kiɗima da mamaki, bata gama saisaita a yanayin da take ciki ba ta sake cin karo da wata wasiƙar da take cewa “Zan nuna miki Soyayyar da tafi wannan matuƙar zaki cigaba da bani haɗin kai!".

A lissafin ta zata kai a ƙalla rabin shekara tana aiki kafin ta haɗa wannan kuɗin domin Albashinta bai wuce $32'000 Dollars ba a kowani wata. Zuciyar ta ta shiga muhawara da tunaninta. Yayin da ƙwaƙwalwarta ta ɗau zafi akan wannan abu da bai taɓa giftawa ko faruwa acikin rayuwarta ba. Cikin mintina ta lissafa yadda zata kashe kuɗin da bata taɓa tunanin zata taɓa iya samun shi cikin sauƙi ba a rayuwarta, ko da yake ba cikin sauƙi bane tunda ya raba ta da abinda yafi komai ƙima da daraja cikin rayuwarta, ya raba ta da abinda da shi ne kawai zata yi Alfahari da shi a gidan mijinta. Toh amma ya zata yi da rayuwarta, wannan shine kaɗai mafita a gare ta, tunda ita dama ƙiris ya rage tayi drop out daga makaranta tunda wannan semester ɗin ya kusa zuwa ƙarshe gashi bata biya kuɗin Makaranta ba. Bata da wani mataimakin da zai taimaka ma ta, bata da abinci, suturunta ma basu wadace ta ba, mai zai sa ta damu kanta?...

Wannan ne yasa zuciyarta ta kwaɗaitu, ta ajiye aikin Hotel ɗin ta biya kuɗin Makarantar wanda na kowani shekara ya kai $100'000 Dollars, a haka ta bada kai bori ya hau. A haka ta cigaba da karatunta cikin irin kuɗaɗen da yake bata duk lokacin da suka aikata Alfahsha wanda har yanzu bata san yanda yake samo su ba. Yanzu haka tana da Business Supermarket ɗin kanta da wurin gyaran jiki. Ta kammala karatun Degree ɗinta a ɓangaren Criminology inda ta fara aiki a Department of Justice ɓangaren binciken Laifuka na ƙasa aka fara musu training, yanzu haka aikinta a kansa ya fara, akan sa yake!. Shine komai nata, shine gatanta. Shine ya tsamota daga cikin ƙangin talauci zuwa ga ni'imar arziki da dukiya. Duk da ya rabata da budurcinta da yake da matuƙar muhimmanci a gurinta, amma bai cin dalilin shi da bata cigaba da makaranta ba, da bata kai matsayin da ta kai a yanzu ba, da bata tara ɗimbin dukiyan da ta tara ba. Anya kuwa idan ta tona ashirin sa ta yi masa adalci kuwa? Ta saka Alkhairi da halaccin da yayi ma ta a rayuwarta kuwa?!. Sai dai wannan ba Mr. Jalaluddeen ɗin da take tunani bane, wani ne daban. Bata taɓa kamashi ko zargin shi da wani miyagun abu ba, sai dai kuma wannan abun da ya faru ƴan mintinan nan da ya gabata ya sa dole ta tsaurara bincike akanshi. Idan kuma aka gano yana da sa hannu a ta'addancin da yake faruwa a ƙasa dole ne a yi masa hukunci, domin ƙasar ta ce, dole ne ta sadaukar da komai domin ceton ƙasarta tunda bata da sauran komai da ya rage ma ta. Tun bayan Mai lafin da FBI ta kama yasa aka sanya ido sosai a kansa dama wasu manyan guraza da suka jiɓanci Babban Hotel ɗin.

Wayar da take kira ne aka yi picking, cikin sauri ta soma bayani “I have a suspect!...”

Cikin sauri ya katse ta “Who's he?”.

“Mr. Jama...lud...deen!” ta amsa shi muryarta na rawa.

Da sauri ya katse wayar yana mayar da hankali kan system ɗin da ke gabansa...

*******

Ni Kaina sai da na girgiza ganin DR. SHEHU UMAR GALADEEMA a gaban madubin!. Gwamnan jihar Katsinan Nigeria kuma Mr. Jamaluddeen a ƙasar Somalia. Babu wanda ya san real identity ɗinsa a ƙasar, kowa da Mr. Jamaluddeen ya sanshi, kuma sana'anshi shine export and import of farm products wanda da haka yayi ƙaurin suna kuma yake kama maƙudan kuɗaɗe a ƙasar, ga manyan ƙusoshin ƙasan wanda suke damawa da shi, yanada faɗa aji kuma babu abinda ba shi da shi na ƙasar da ya jiɓanci Passport, National identity, da ma sauransu da yake rectifying zama ɗan ƙasa. Hatta katin zaɓe yana da shi. Sai dai babu wanda ya taɓa ganinshi sai dai wasu daga cikin manyan ƙasar. Wani irin mutum ne da yake tamkar Aljani ko kuma iskokai, baya taɓa zama guri ɗaya...

Ji yayi bai yarda da rigan da ke jikinshi ba yasa ya cire ya sake da Black suit. Zai fita ya sake tsayawa ya kalli kanshi a madubi, kafin daga bisani yayi hanyar wata ƙofa dake cikin Bedroom ɗin. Ya murɗa handle ɗin kenan wayarshi da ta soma ruri ne ya dakatar da shi, ya zarota ya danna wurin amsa kira yana karawa a kunnensa.

“Mr. Jamaluddeen!” aka ce da shi daga ɗaya ɓangaren.

“I'm listening to you Inspector!”. ya faɗa da wani irin thunderous voice.

“Hukumar bincike na ƙasa ta shiga profile ɗinka yanzunnan, i don't really know what they're checking. Na sha faɗa maka cewa ka kiyaye saboda na faɗa maka cewa Kai da Team ɗin Atik kuna under investigation. Komai zai iya faruwa idan suka gano gaskiya”.

Sai yanzu yake ganin rashin dacewar taronnan da ya shirya shi a ƙasar, mafi yawan tarukan sirri irin wannan a Birnin Dubai ko Germany yafi shirya shi. Wai ganin lokaci ya ƙure ne ya kusa komawa Nigeria hakan ya sa ya shirya shi a Somalian, ko kaɗan bai yi tunanin za'a yi suspecting ɗin shi ba saboda he's been so careful kuma yanada influence.

Numfasawa yayi tukunna kafin ya ce da shi “I'll tryna be so careful inspector, Update me about every new detail happening”.

Ba'a amsa shi ba yaji wayar ta tsinke. Jawo Drawer ɗin dake gabashi yayi ya zaro bindiga ƙirar pistol, yana shafata yana kallon madubi fuskarsa a murtuke idanunsa sun sauya launi sunyi jajur, sai kuma ya ajiye yana danne danne a wayarshi kafin wayar ta fara ƙarar alamun yana kiran wani, daga ɗaya ɓangaren aka ɗauka.
“Good Morning Sir”.

“Su waye suke tracking ɗina?”.

“Yallaɓai Waleedah ce take taimakawa inspector luqman”.

Wani tiririn ɓacin rai ne ya fara taso masa yana ƙoƙarin dannewa yace
“Wani Evidence suka samu?”.

“Sun samu hoton ka da videos amma na katse network ɗin kuma na yi tracking files ɗin nayi corrupting ɗin su”.

Sai yanzu ya murmusa kafin yace
“Aikinka yayi kyau. Hundred thousand dollars tonight. Kazo ALMUBARAK Hotel 9'PM sharp!”.

Zakariyya Audu wanda aka fi sani da Zaks kenan, ƙwararren masanin Computer ne domin computer science, programming da cyber security ya karanta a ƙasar United State wanda ALHAJI UMAR GALADEEMA Mahaifin DR. shine yayi mai komai na karatunshi. Ƙwarewar shi da ƙwaƙwalwarshi itace ta sanya Hukumar bincike ta ƙasar London suka ɗauke shi aiki ɓangaren ICT aka bashi babban matsayi. Bayan murder case da aka tsinkaya na wani Minister da aka kashe a shekararun baya, cikin bincike aka fahimci cewa information ɗin Ministern ne ya fita kuma ofishin shi ake zargi, babu wani evidence da za'a iya tuhumar shi akan laifin da ake zargin shi da shi. Aikin shi is strictly confidential kuma babban laifi ne fitarwa ko siyar da information ɗin wani koma wanene a ƙasar. Babu shiri aka bashi takardar sallama wanda hakan ya sa a yanzu yazama abinda ya zama. Ya zama wani ethical hacker na gaske, ya zama Fraudster na gaske; bazaka ce damfara yake yi ta na'ura mai ƙwaƙwalwa ba, sai dai ya san yadda zai yi hacking accounts Ya kwashi miliyoyin kuɗi ba tare da buƙatar mabuɗai ko makullan sirri ba, Ya zama Mutum mai hatsarin gaske!. Contract da manya-manyan ƴan siyasan ƙetaren ƙasashe suke bashi na lalubo information akan abin farautarsu, kuɗi suke saki maƙudan kuɗaɗe amma babu wanda yafi ganin girman shi kuma yake jin zai iya sadaukar da komai domin shi irin Dr. SHEHU UMAR GALADEEMA; ko dan saboda baya tunanin akwai abinda zai iya sakawa Alhaji Umar da ya ɗauki nauyin karatunshi tunda ya rasu sai dai yayi ƙoƙarin yin duk abinda ɗan na shi yake buƙata. Hakan bashi yake hana Dr. birbiɗeshi da maƙudan kuɗaɗe aduk lokacin da yayi mai aiki ba ko da ya ƙi. Yanzu haka ma babu yadda ya iya da Dr. ɗinne, domin ya san shi wani irin mutum ne da ya tsani a mayar mai da hannun kyautarsa.

Yana gama wayar yana cusa bindigan a dai-dai ƙugunsa acikin abin ajiyar ta, sannan ya murɗa handle ɗin inda yana buɗe ƙofar sai gashi a cikin conference room ɗin. Mutanen ciki sun haɗa da Shugaban INEC ta ƙasa, shugaban INEC na Jihar Katsina, Inspector General of Police, Commissioner of Police na Jahar Katsina, Chairman ɗin Partynsu na CDP na Ƙasa, Ɗan Takarar Gwamna na Jiharsu ƙarƙashin Partynsu na CDP, da ƴan Takarar Sanata Huɗu na jihar inda suka cika su Goma cif-cif.

Ba tare da wani ɓata lokaci bayan sun gama gaggaisawa ya soma magana kamar haka “Dukkan ku kowa yasan abinda ya tara mu nan...”. Ya juya ya kalli inda INEC Chairman yake “Chairman, wannan Nasarar ba tamu bace kai kaɗai, a matsayin ka na ɗan kwangila bayan shugabancin nan da yake kanka, Gwamna mai jiran gado yana yi maka maraba da Alƙawarin sababbin kwangila masu dama, sannan ni kaina idan har muka yi nasara...”. Ya juya da kujerar da take irin office chair ɗinnan mai juyawa ya ɗauki Briefcase guda ɗaya ya ɗorata akan teburin wurin buɗewarta yana fuskantar Chairman, Ya buɗeta inda Daloli suka bayyana acikinta cike, ya ɗora da “wannan somintaɓi ne akan abinda zaka gani idan har munyi Nasara. Wannan na siyan Sabuwar Mota ne” Ya dasa aya yana tura Briefcase ɗin gaban Chairman.

Ba wannan bane karo na farko da ƴan siyasa suke buɗe shi da maƙudan kuɗaɗe, amma Dr. SHEHU yafi bashi mamaki sama da kowa. Yasan ba daga albashinshi ya samu waɗannan kuɗaɗen ba, haka kuma ba sata yake yi ba domin a halin yanzu jihar Katsina itace jiha ta biyu da take da tattalin arziki a Nijeriya. Anyway, shi wannan ba damuwar shi bane, damuwar shi shine benefits ɗin!, kuɗin!, domin baya taɓa jin akwai ranar da kuɗi zasu taɓa isar sa.
“Prof. Garba!”. ya kira sunan yana fuskantar Chairman ɗin INEC na jaha, “mun riga mun yi zancen da kai, So babu amfanin maimaitawa”. Ya jawo wani Briefcase ɗin ya tura gaban shi. Sai a lokacin ya ce “Inspector General!”

Inspector ya ɗago da kai daga sunne kai ƙasa da yayi, idanunshi sun sauya launi zuwa launin ja, yana ganin yanda jijiyon goshinshi da gefen fuskarshi suka firfito, ga wani irin zufa da ya tsatstsafo a goshinsa duk da sanyin ACn da aka ƙure aɗakin taron. DR. SHEHU ya gama karantar yanayinsa tsaf, hankalinshi yaji ya tashi ta wani ɓangaren amma shi mutum wanda baka taɓa iya karantar yanayinsa.

A second mistake!. He thought!

Da shi Yakamata ya fara tunda shi bai san dawar garin ba, watanni shida kenan da suka gabata akayi appointing ɗin shi a matsayin sabon Inspector General of Police!

ME KUKE GANIN ZAI FARU?!
SHIN KUNA TUNANIN IMRAN ZAI IYA RAYUWA KUWA?!

INA SO INJI RA'AYOYINKU. KUYI COMMENTS KUYI VOTES SANNAN KUYI FOLLOWING ƊINA DOMIN HAKAN YANA ƘARA MUN ƘWARIN GWIWA👇

SANNAN INA SO MASOYA LITTAFIN NAN SU SANI CEWA INSHA ALLAHU NA DAWO GADAN GADAN. KUYI MIN SHARING DOMIN WASU SU MA SU KARANTA SU AMFANA...

Continue Reading

You'll Also Like

OBSESSED By thisbejaja

Mystery / Thriller

95.6K 4.1K 26
obsessed
14.1K 949 33
The transfer student couldn't me anything more special.But part of me want to help her.Why? Sooha thought to herself, she decided to help the new st...
20.3K 948 24
*𝒘𝒉𝒊𝒔𝒕𝒍𝒆* "𝑾𝒐𝒓𝒍𝒅 𝒘𝒉𝒆𝒓𝒆 𝒂𝒓𝒆 𝒚𝒐𝒖 ~" "𝑫𝒐𝒏𝒕 𝒌𝒆𝒆𝒑 𝒎𝒆 𝒘𝒂𝒊𝒕𝒊𝒏𝒈. 𝒚𝒐𝒖 𝒌𝒏𝒐𝒘 𝑰 𝒅𝒐𝒏'𝒕 𝒍𝒊𝒌𝒆 𝒊𝒕 " "𝑾𝑶𝑹...
12.3K 1.9K 21
جۆنگ کوک:بە نەفرەت بیت وازم لێ بێنە چیت لە من دەوێت تایهیۆنگ:ششـ ئازیزم بۆچی هاوار دەکەی ئارام بە بۆ باروودۆخت خراپە ༄༄༄༄༄༄༄ جۆنگ کوک:تـ تۆ چیت کرد ت...