ZAMANIN MU A YAU

De NEIRNAHDISO

2.4K 100 12

wannan sanyin illa zaiyi miki acancikin ki, ai ita mace da ɗumi aka santa, ai ballagaza ita ke illata ƙanta d... Mais

ZAMANIN MU A YAU 1
ZAMANIN MU AYAU 2
ZAMANIN MU AYAU 3
ZAMANIN MU AYAU 4
ZAMANIN MU AYAU 06
ZAMANIN MU AYAU 7
08
09
10
11
12
13
14
15
16

ZAMANIN MU AYAU 5

132 4 0
De NEIRNAHDISO

*🫧 ZAMANIN MU A YAU🫧*

NA

JEEDDAH ALIYU
&
NANA DISO

*PAID BOOk*

_Team Tagwaye Biyar Novel_

005


Yau gaba ɗaya hankalinta ya ƙarkata akan abunda malamin ajin yake koyarwa ɗaliban kalmar da taji na stop shine yasata kara zura kai tana sauraronsa yana faɗin "idan akace stop Aisha ana nufi ki tsaya A'isha, kunga kenan kalmar stop tsayawa ake nufi ko? Kungane?
Gaba ɗaya ɗaliban da zasu kai adadin hamsin zuwa sittin a cikin ajin suka ce "mun gane malam. Yar uwar Rahee ce ta kallota wato Ladi harara ta shiga zabgawa Rahee tana kada kanta alamun za ki sani, Tabbas tasan sharrin ladi yau in suka koma gida tashiga uku, amma zata san duk yadda za tayi tasiyar da awarar nan tanan ne kadai tasan zata samu sassauci murmushi ta kuma yi Tunda Rahee taji kalmar take fama maimaitawa tana faɗin "top top yau na ƙoyo kalmar turaci ta faɗa tare da saurin daukar awararta ta koma bakin inda masu tallah suke tsayawa dan taga alamun ana daf da tashi. Gefen mai sayar da masara ta samu ta zauna tana mai faɗin gaskiya turanci da daɗi. Mai masara ce ta dallah mata harara tana faɗin "Wai ke Rahee ba za ki daina laiƙasu ba ko? Wata rana in suka yi miki duka ke ki kaso in banda ba ki da hankali me za kiyi da wata boko ko? Malama mu nemi ƙudi muyi auren mu ta faɗa tana kara toro da ɗan ƙwalinta waje." Takaicin mai masara ne yasa Rahee saurin faɗin "Hefe ba ki da hankali karatun ne bakyaso? Yanzu ke Kinfi son yawan tallah da jahilci? Ni gaskiya inason karatun he baba ya samu kuɗi tukunna. "Ke Rahee kyaleni da maganar karatunnan he ki damu mutum da batun karatu ina dalili? Ni maganar da zanyi miki ma kina ƙaiwa Sha'aibu kayanki kuwa? In gayamiki jiyannan he da ya bani dubu ɗaya ya siye kayana.
Rahee ce ta zaro idanuwa tare da mamakin kuɗin da abokiyar sana'ar ta ta ambata sannan ta ƙara wangale baki tana faɗin. "In ce aiki ki kayi masa ya baki kuɗi masu yawa har haka?"
Dariya mai masara tayi tace "ke wallahi na daina wahalar tallah daga makarantar nan gurinsa nake zuwa ba ki ga ina zuwa zai siyarmin da masara ta duka
"Dan ALLAH ki kaini nima ya dinga siyarmin. "Ai ba za ki yarda da abunda zai yi miki ba. "Kamar yaya?"
Rahee ta faɗa tana mai neman ƙarin bayani gami da zazzaro idanuwa. "Dallah ce he ki yi ta ƙauyanci ke Rahee, zai ɗan tattaɓaki tuƙunna wannan ɗakin nasa shi zai kai ki fa, nasan ke har dubu biyu zai baki tunda kinga ke kina da diri ga ki da nonuwa masu girma kawai dai ƙazantarki ce matsala ba kowa zai iya taɓa ƙazamin jikinki ba. Rahee ce ta ja tsaki "mtsssss! tare da faɗin "ALLAH ya shiryeki, ALLAH kuma ya tsareni da iskanci komai talaucin mu ba zan iya bari ƙato wofi ya taɓa min jiki ba, ko aka gayamiki dan banyi makaranta ba bana tsoron ALLAH?
Shi kuma ɗan Sha'aibu in shaa ALLAHU sai asirinsa ya tonu.
"Dallah yimun shiru Rahee ni za ki gayawa magana sai kace ke bakyayi ko kina so ki wanke kanki ne?."Mtsssss! Rahee ta ja guntun tsaki tare da dauƙar awarar ta ta dora akanta, ta bar wuri tafiya ce take yi tana tafe tana waƙarta duk da irin yunwar da take ji haka ta ɗaure tana zagawa dan yau kam bata tsayawa a makaranta mai masara ta ɓata mata tarbiyar ta salan Babanta ya daina kulata, samun guri tayi ta shiga ƴar carafke jikin nan nata yayi datti sosai ga uban wari dake tashi a jikinta amma saboda yanayi na sabo ba taji komai ba, bayan wasu mintuna bacci ya kwasheta, tsawan mintuna 30 tana shan baccinta, "ke Raheenatu ke Raheenatu wacce kalar kwanciya ce haka cikin ƙasa sai kace ba mace ba dubi kayan jikinki zanin ma ya yayyage, duk maganganun da wata mata take yi Rahee tayi nisa a baccinta dan bata san ma tana yi ba. Matar ce tasa ka hannuwanta ta ɗaƙawa Rahee duka cikin firgita da tsoro tayi maza ta tashi har tana rungumar bokitin awararta.
"Ke Rahee uban me ki ke yi a haka dubeki fa kamar mahaukaciya kina macce kin fara zama budurwa ki ke saka kayan nan? Dubi uban dattin da ki kayi?.
"Lahh inna A'i yaushe ki ka zo Ƙauyen?"
"Ƙaniyarki tashi mu je gidan naku kamin na ɓata miki kin zama wata ballagaza dake.
Kunkuni Rahee ta fara yi sannan tabi inna A'i abaya har suka isa cikin gidansu da mata sunfi goma tsaye kowannen su sai uban surutu sukeyi anata zabgawa inna cinikin maganin matanta, inna A'i ce ta jiyo bata ga Rahee ba hakan ya sata komawa soro nan ta ganta rakuɓe a jikin ƙyauren ƙofar tana rarraba idanuwa.
"Ke Rahee sai yaushe za kiyi hankali ne? Dan ubanki ba haka nace ki shige mu je ba zaman menene kikeyi anan?"
"Inna A'i ban fa siyarwa da inna awarar ta ba yau ko sisi banyi ba so ki keyi ta kasheni.
Baki inna A'i ta saki tana sauraron Rahee kafin tace "Dallah shige mu je in taga dama ta ɗaurawa Shatu mana tallan sai ke marainiyar ALLAH.
Cikin tsoro Rahee tace "Dan ALLAH ki barni naje nayi tallah ko rabi nasiyar mata kada ta zaneni wallahi yanzu idan aka dakeni jikina he ya yi ta ciwo yana fidda jini. Ƙokarin fizgota inna A'i take yi amma ina tuni Rahee ta falfala da mugun gudu abunka da mai ƙaramin jiki tuni tabar bakin ƙyauren tayi cikin kasuwa, cikin sa'a kuwa tayi naira ashirin a hanya, barau dan gidan mai unguwa dake sonta ne yazo bakin bishiyar da take zaune da zuwansa yace "Yan matana! ya faɗa yana mai washe haƙora.
Turo baki da duk ya bushe tayi tace "he ka dinga tsoratani ko?"
"Kiyi haƙuri me yafaru yau baki siyar da awarar ba? Ko dai munyi ƙwantai ne?"
"ALLAH ya tsareni kwantai.
"To yanzu ta nawa ce wannan?"
Murmushi tayi da ya bayyana haƙoranta jajir dasu fusƙar nan duk tayi furu-furu
"Naira ɗari biyu.
"To yau dai banida kuɗi abani ta naira 50. Murmushi tayi gami da faɗin "Nagode sosai! sannan ta zuba masa daga nan kuma ta ɗauki bokitinta tayi gaba dan harga Allah tasan barau ba ajinta bani ba ko kalaman soyayyar da yake gayamata tasan yaudararta kawai ya keyi dan gidan mai unguwa fa "tabdijan! ta faɗa.
Cikin hukunci Ubangiji kamin azahar tayi ta yi cinikin naira 180 sauranta ta naira talatin dan haka sai kawai ta yanke shawarar zuwa gurin Babanta inda yake faskare, tafiyace mai ɗan nisa tayi dan bata isa ba sai kusan bayan azahar, wani dattijo ne tunda ta hangoshi fara'ar fuskarta ta ƙara bayyana, rigar jikinsa takallah duk yadda take ganin mutuwar kayan jiķinta amma ina, yadin dake jikin mahaifin nata ya gaji da koɗewa ga shi duk ya yayyage, da ɗan saurinta ta ƙarasa tana isa kusa dashi, ALLAH sarki bacci wahala yake yi da alama faskaran itacen yake yi. Zamanta kusa dashi yasa ta sakin kuka dan tana tausayin mahaifin nata, shi kansa itacen ba jarinsa bane ba acikin na dubu ɗaya idan yayi dari biyu zuwa uku ake bashi, duk da ƙankantar shekarunta tasan mahaifinta yana cikin matsala da damuwa duk yadda zai fahimtar da inna yasan ba zata taɓa ganewa ba."Babana dan ALLAH kabar aikin itacen nan dubi hannunka yadda yayi.
ta faɗa tana mai share hawayenta.
Murmushi ya yi gami da faɗin "ƴar gidan Baba menene na kukan bana hanaki ba? Wata rana sai labari yanzu idan ban yi faskaren ba ta yaya zamu ci abinci kina ganin innarki bata ganin ƙoƙarina, so na keyi ma nasamu kudi kema nasa ki makaranta kamar yadda innarki ta saka Shatu, yau ma ba kiyi wanka ba ko Raheenatu ? Kin ji wani irin wari da ki ke yi kuwa?"
"ALLAH sarki Babana ALLAH ya ba ka kuɗin dan wallahi ina son makaranta yau ma top top aka koyawa ƴan makarantar.
Shiru ya yi zuciyarsa tana masa zafi, amma da yake dattijon kirki ne shi sai cewa ya yi in shaa ALLAHU sai kin gaji da bo koko yar gidan Babanta."
"Yanzu dai Baba kabar maganar wanka ga wannan awarar kaci nasan ba kaci abinci ba, In yaso sai nacewa inna kai ka siya za ka bata kuɗin daga baya.
Ba dan yaso ba ya ƙarbi awarar ya shiga ci, kai "Malam Audi! malam Audi! ina kuɗina ne naira ɗari da hamsin ace kusan satinka uku? Shiyasa kowa ya haƙura da ba ka rance wallahi. Babane yayi hanzarin tashi yana tarar abokin nasa dan baya son Rahee ta fahimta "Dan ALLAH ɗan birni kayi haƙuri zan ba ka dazarar na haɗa. Ƙokarin caƙumo wuyansa ɗan birni ya shiga yi yana mai faɗin "Ai wallahi-tallahi ka daina yaudarata tsohon banza.
Wani sabon hawaye ne ya zubowa Rahee kullin zaninta ta ƙwance naira ɗari da hamsin ta ɗauka sannan ta ɗaure naira talatin ɗin, cikin girmamawa tace "Baba ɗan birni gashi yanzun nan ya bani yace in kawo maka daman." Murmushi dan birni ya saki sannan yace "shine a
ka ke zolayata? Har kana so in nuna maka baƙin halina.?"
Wasu sabbin hawaye ke ƙoƙarin wankewa Baba fuska amma yayi saurin haɗiye su yana jin ƙaunar ɗiyar tashi har cikin jinin jikinsa. Gaban Rahee kawai ke duka dan tasan yau sai dai wata ba ita ba a gurin inna.

*Shaima's Mansion*

Miƙewa ya yi tare da buɗe ƙofar batoul ya gani sai gumi ta ƙeyi alamar tsoro ko kuma wani abun daban. Maryama ce ta ƙalleta tace "Ke ba ki da ɗa'a ne da zaki shigo mana babu sallama?" Abah ne ya ɗaga mata hannu sannan ya riƙe hannun batoul suka fita. Masifa Maryama ta shiga yi tana faɗin "marasa mutuncin yara su dinga yi sai kace suna son mijina nan duk makiya ne wallahi kowacce cikinku sai nayi maganinta.
Ta faɗa tana fita daga part ɗinta, Abah kuwa yana riƙe da Batoul bai tsaya ko'ina ba sai a ɗakin bakinsa, fridge ya buɗe ya tsiyaya mata ruwa ya bata sannan yace "Menene Batoul?" Cikin firgici tace Dady dan ALLAH ka dinga addu'a.
Wannan kalmar ta Dady da take gayamasa yana saka ransa ya yi sanyi sosai, cikin saurin murya alamun hankalin ta har yanzu ba a kwance yake ba tace " Na shiga part ɗin mama ɗazu banga kowannen su ba kasan ɗakin Mama na ɓangaren ƙofa duhu ne dashi sai naji ana cewa "Mun ƙarbe kamfanin yanzu kuma abunda ya rage mana yaronsa sannan sai mu wulaƙanta sa, banji me sauran suke cewa ba Abah sai dai naji anyi dariya ance har matarsa, sai kuma naji ankara da cewa aljanu ne za suyi mana.
Gaban Abah ne ya faɗi amma da yake namijin duniya ne sai cewa yayi , babu komai kinji Batoul ALLAH kaɗai ke cutarwa kinji, kuma ina addu'a nasan kinad a makaranta ko? Tashi maza kije kishirya ALLAH yayi miki albarka ya faɗa a hankali saboda yadda damuwa take ƙoƙarin fin ƙarfin kirjinsa. Har ta kusa fita yace "Batoul kiyi haƙuri da wannan uni din kinji kafin ALLAH yasa komai ya warware sai na canza miki wata.
"A'a Abah wannan ma tayi ALLAH ya saka da Alkhairi ya biya buƙatu. ta faɗa tana barin ɗakin. Wayarsa ce tayi ringing yana dubawa yaga Maleek ne ɗauka yayi yaƙ ara a kunnansa tare da sallama. " Dadyna barka da safiya I hope kuna lafiya?" Murmushi ya yi mai ɗauke da ƙaunar tilon ɗan nasa. "
Lafiya ƙalau maleek ina fata kana lafiya?"
"Dadyna mumyna ta kira tana kuka please Dadyna am sorry to say zanyi pH..."
"Dan ALLAH kadawo Maleek ina buƙatar ka kusa dani kaji abubuwa sun kacancamemin banida abokin shawara ko hira ina buƙatarka kusa dank kaji?"
"An gama Dadyna yanzu zan siya ticket.
"ALLAH ya yi maka albarka am waiting for you.
Yanayin da suka shiga shi da Maryama ne suka fara dawo masa, yasan dattijo yana can yana jiransa amma ba zai je ba sai zuwa dare dan sai ya gama thada komai na dattijon ya bashi cikin mutuwar jiki da sha'awa dake damunsa ya miƙe ya nufi ɓangaren Maryama.
Hajiya maganar me na keji haka?
"Hajara ba dole na gayamiki ba Ahmadu dai an ƙarbe company hannunsa an bawa su Isma'ila, wani daɗi Hajara taji a cikin ranta dan ita babu wanda ta tsana kamar Abah da matarsa duk da uwarsu daya ubansu daya amma yadda yake samun ci-gaba zuciyarta na mata raɗaɗi, da ta ji wannan maganar ta mahifiyarsu sai ji wani irin daɗi da farinciki aranta marar misaltuwa. "To Hajiya ai sai ayi adalcin abasu.
"Ai anyi adalcin Hajara amma halin da ɗan uwan naku zai shiga shine abun dubawa.
"ALLAH zai kawo sauƙi.
Ta faɗa cikin rashin damuwa.
Yana shiga part ɗin Maryama sama ya yi tare da ƴar sassarfa yana ambaton ALLAH tare da murɗa ƙofar ya shiga wani mugun ciwon kaine ya dirar masa ganin tana ta kuka, ƙarasawa yayi cikin sauri yana ambatar "Lafiya maryama? Wani sabon kukan ta kara fashewa dashi sannan tace "shikenan ka zama talaka ƙawayena za su yi min dariya shikenan watan kunya ta ya tsaya.
Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka, "kai wannan matar.
ya faɗa cikin ransa yana mai rungumarta, cikin yanayin buƙatuwa ya shiga zuba mata kiss ta ko'ina yana sauke ajiyar zuciya.
*SADAUKI's MANSION*
Sai daff da magariba Ummul-Salma ta sami nasarar ficewa daga gida a lokaci da taga kowa ya shige ɗaki domin gabatar da sallah, a lokaci ta sulele ta fice abinta. Sam bata tunani irin dukan da za ta sha, ta riga da ta saba da duka daga guri mommy da Abba, yayunta maza da mata har ta kai ta kawo yanzu bata tsoron duka, har cewa take yi a daki fatar jiki a bar fata ita yanzu babu dukan da zai bata tsoro.
Ta fito cikin sauri da dogon hijabi sanye da jikinta har yana ja da ƙasa, sai zuba sauri take har tana da haɗa wa da gudu-gudu. Ta nusan can ƙasar unguwar su wani gida mai farin painting ɗauke da green color gate ta shiga knocking on, tana yi tana waiga wa bayanta gudun kada wani ya biyo sahun ta.
Ta ɗauki lokaci tana knocking kafin maigadi ya zo ya buɗe mata "Ki yi haƙuri Hajiya ina sallah ne.
Bata ce dashi uffan ba ta raɓa gefenshi ta shiga cikin gidan, kaitsaye entrance ɗin gida ta nufa tana zuwa ƙofar shiga babban parlour gidan ta danna door bell after a minute ɗaya daga cikin Housemaids ta zo ta buɗe mata ƙofa "Sannu da zuwa Aunty.
Housemaid ɗin ta faɗa sa'ili da ta buɗe mata ƙofa "Yawwa sannu Yazeed fa?"
"Yana upstairs bedroom ɗinsa ki shigo daga ciki sai na kira miki shi.
"Okay ki yi sauri Dan ALLAH banaso na daɗe.
"Okay!
Housemaid ɗin ta faɗa gami da juyawa da sauri ta nufi bedroom ɗinshi, yayin da ummul-Salma ta nemi cushion ta zauna. Bata daɗe da zama ba sai ga Housemaid ta dawo da sako "Ya ce yana zuwa.
ummul-Salma ta gyaɗa kai, Housemaid ta wuce kitchen ta kawo mata ruwa da drinks.
Tako tafiya ta ji ana saukowa daga upstairs yasa tai sauri ɗago kanta Yaseera da Yusrah ne wanda suka kasance 'yan uwan Yazeed. Yaseera yayarshi ce yayin da Yusrah take ƙanwarshi su uku kacal mahaifiyarsu Hajiya Rahama ta haifa.
Da murmushi akan fuskokinsu suka ƙaraso tun kafin su zauna Ummul-Salma ta zame daga kan kujera ta gaida su da sauri Yaseera ta ɗago ta tare da rungume ta tana faɗin "Salma har sai yaushe za ki daina wannan ƙauyanci naki?" Na sha faɗa miki ki daina yi mana irin wannan gaisuwar ta tsofaffin mutane.
Ummu-Salma ta sunne kanta a ƙirjin Yaseera tana murmushi, Yusrah ta taɓe baki gami da zaunawa ta ɗora ƙafa bisa ƙafa tare da cewa "Mamaki nake yi yadda soyayyarta da Zeed tai tsawon rai alhali tana wannan ustazanci.
Dariya Yaseera tayi tare da cire Ummul-Salma daga jikinta, ta ce "Ai ita soyayya bata duba da wannan hasashen naki.
Kafin Yusrah tai magana Hajiya Rahama ta sauko cikin shirin fita kamar yadda Ummul-Salma ta gaida su Yaseera ita ma haka ta gaidata ta amsa cike da sakin fuska kana ta zarce da faɗin "Salma miyasa ba za ki haƙura da soyayyar Zeed ba tun da iyayenki basa son shi?" Ni fa banaso rayuka su ci-gaba da ɓaci kin ga haka last week mahaifinki ya tare ni a hanya kamar abin arziki sai cewa ya yi idan har Yazeed yana jin maganata na isa dashi na hana shi zuwa inda kike kin ga kuwa na isa da ɗana domin tuni ya daina zuwa gidanku sai kece ki ke bibbiyarsa. Salma ina girmama abinda 'ya'yana ke so shiyasa na bar ki ki ka ci-gaba da shigowa gidanan domin na fahimci irin muguwar soyayyar da Yazeed yake miki da ba don haka ba da ko ƙofar gidanan ba isa ki tako ba. Balle har ki shigo mana tsakiyar parlour anyway ki hau sama Yazeed yana ɗakin shi.
Daga haka Hajiya Rahama ta juya cikin tako ta na ƙasaita, da ke nuni da ƙasaitacciyar mace ce mai ji da kanta.
Yaseera ta dubi Salma da tayi zuru-zuru da ita ta ce "Don't worry Salma dama soyayya ta gaji irin waɗannan challenges ɗin.
Salma ta gyaɗa kai gami da goge hawaye da suka sauko akan kumatunta, cikin rauni da mutuwar jiki ta haura bene, dama tasan inda ɗakinsa yake tun da ba yau ne farkon zuwanta ba. Batare da tayi knocking ba ta tura ƙofa ta shiga, jin saukar ruwa a bathroom yasa ta gano yana wanka ta nemi gefen gado ta zauna jin kaɗan da zamanta sai gashi ya fito kyakkyawan matashi wanda aƙalla shekarun sa na haihuwa ba za su wuce 35-36 yana ɗauke da round face fuskarshi zagaye da ƙasumba fari ne amma ba sosai ba. Yana da manya idanuwa yayin da jikinsa yake a murɗe Yazeed Talba kenan yaro ɗan kwalisa shalelen Mommy tsoka ɗaya tal a miya. Yazeed Talba mugun manemi mata ne cikakken ɗan bariki babu club ɗin da ba za ka ganshi ba. Bai taɓa dating da budurwa suka yi wata uku a tare ba sai akan Ummul-Salma da zarar ya sami abinda yake so a wajen mace shikenan zai yi break up da ita, gashi ALLAH ya zuba mishi farin jini 'yan mata a dalili kuɗi da yake dasu gashi kuma kyakkyawa aji farko.
ALLAH ya zuba mishi masifaffiyar ƙaunar Ummul-Salma ita ce mace ta farko da ya haɗu da ita ya ji yana son ya mallake ta ta hanyar raya sunnar ma'aiki.
Ya lumshe Lulu idanuwanshi a lokaci ɗaya ya buɗe su akan fuskar Ummul-Salma ita ma ɗin shi take kallo tsawon sati guda kenan ba su haɗu da juna ba. A dalili prison ɗin da Abba yasa Ummul-Salma domin ko babban parlour bata isa ta fito ba tana ɗakinta a ƙargame jiya ne da kakarta wacce ta haifi Mommy da ta zo ta nema mata sassauci shi ne aka buɗe ta yau kuma ta sulale ta zo gun shi.
Yazeed Talba ya ware mata hannuwanshi sam bata yi la'akari da towel ne ɗaura da ƙugunshi ba ta taso da gudu ta faɗa ƙirjinshi ya yi mata kyakkyawar runguma ta hanyar zagaye hannuwanshi a ƙugunta daga bisani ya ciro ta daga ƙirjinshi ya cire mata hijabin jikinta ya yi jifa dashi kana yai connecting bakinshi da nata wani irin sha yake wa bakinta, yana murzata san ranshi ya tsotsi nan ya murza can gaba ɗaya jikin Ummul-Salma ya ɗauki rawa duk da ba wannan ne karo na farko da ya fara romancing ɗinta ba. Amma shine na farko da ya yi babu kaya a jikinsa sai faman goga mata erection ɗinshi yake yi yana sauke mugun numfashi tuni hankalinsa ya gushe, ya yi fatali da towel ɗin jikinsa cikin fitar hayyaci ya dauke ta ya kai bisa gadonsa ya yi mata rufa da faɗaɗɗe ƙirjinshi sai lokaci ta ganshi naked nan take ta tsorata ta shiga tutture shi daga sumbatar da yake kai wa gefen wuyanta zuwa ga ƙirjinta wanda tuni ya zame rigar jikinta kasancewar bata saka bra ba ya sami damar wadaƙa da albarkatun ƙirjinta.

*TEAM ƳAN TAGWAYE NOVEL*✍️

GA MASU BUKATAR ƳAN TAGWAYE DUKA
GUDA BIYAR 1500.

GUDA HUDU 1300

GUDA UKU 1000

GUDA BIYU 700

GUDA ƊAYA 400

_*RAFEEQ*_ (Hajja Ce & Asmy B Aliyu)

_*MUNƊO*_ (Ayusher Muh'd & Zee yabour)

_*FATHIYYA*_ (Billy s fari & Umm Asghar)

_*.ZAMANINMU A YAU*_ (Nana Ɗiso & Jiddah Aliyu)

_*IYALINA (A'ilaty)*_ (Zainab Bawa & Sadiya Nasir Dan)

ACCOUNT NUMBER

2083371244

Zenith Bank

Aisha m salis

KATIN WAYA

+234 706 528 3730

Continue lendo

Você também vai gostar

319K 18.4K 19
"ဘေးခြံကလာပြောတယ် ငလျှင်လှုပ်သွားလို့တဲ့.... မဟုတ်ရပါဘူးဗျာ...... ကျွန်တော် နှလုံးသားက သူ့နာမည်လေးကြွေကျတာပါ.... ကျွန်တော်ရင်ခုန်သံတွေက...
294K 34.1K 85
#Book-2 of Hidden Marriage Series. 🔥❤️ This book is the continuation/sequel of the first book "Hidden Marriage - Amazing Husband." If you guys have...
1.3M 69.9K 59
𝐒𝐜𝐞𝐧𝐭 𝐨𝐟 𝐋𝐨𝐯𝐞〢𝐁𝐲 𝐥𝐨𝐯𝐞 𝐭𝐡𝐞 𝐬𝐞𝐫𝐢𝐞𝐬 〈𝐛𝐨𝐨𝐤 1〉 𝑶𝒑𝒑𝒐𝒔𝒊𝒕𝒆𝒔 𝒂𝒓𝒆 𝒇𝒂𝒕𝒆𝒅 𝒕𝒐 𝒂𝒕𝒕𝒓𝒂𝒄𝒕 ✰|| 𝑺𝒕𝒆𝒍𝒍𝒂 𝑴�...
603K 49.7K 24
Indian Chronicles Book III My Husband, My Tyrant. When Peace Becomes Suffocation. Jahnvi Khanna has everything in her life, a supporting family, a hi...