ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

By KhamisSulaiman

180 16 1

Labarin wata yarinya ne da take bata tun bata da hankali, iyayenta basu tashi ganinta ba sai da ta zama budur... More

Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 10

Chapter 9

10 2 0
By KhamisSulaiman

        ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

*Daga Kundin ✍️📚✍️
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008
Phone no: +2348085871223

                     *page 17 & 18*

   Bayan Alhaji Ahmed da malam Buba sun kai Aisha gidan Alhaji Inuwa, suna zaune bayan sun gaisa.

      Alhaji Inuwa ya kalli Hajiya Sailuba, yace "Hajiya ki sa a kawo ruwan sha mana"

       Sai Hajiya ta tashi ta kalli Aisha, tace" Tashi kema muje ki kai kayan dakinki mana"

     Sai Aisha ta tashi su shige ciki Aisha ta haye sama ita kuma tasa mai aikinsu ta kaiwa baki ruwa sannan Itama ta haye saman wajen Aisha.

       Alhaji Ahmed yayi murmushi yace "Aisha kenan sarkin rigima!"

      Alhaji Inuwa yace "In kaji rigima ma daya kenan, ga shagwaba iri iri saboda ta samu uwa mai riritata"

       Alhaji Ahmed yace "Ai kaima kuwa ba baya ba wajen tarairayarta, ai duk ta gaya min, har cewa tayi ba don ku kuka gaya mata da kanku cewa baku kuka haifeta ba babu wanda zai gaya ta yarda ko duk jikinta kunne ne tace ko za'a shekara ana gaya mata ba zata yarda ba"

     Malam Buba yace "mu dai Alhaji babu abinda zamu ce sai dai muyi fatan Allah ya saka muku da alkhairi"

     Alhaji Inuwa ya jinjina kai yayi murmushi yace "Haba malam ai ba wani abu bane........"

      Malam ya tari numfashinsa yace "Kayya Alhaji! ai kasan hausawa sukan ce 'yaba kyauta tukuici to mu babu abinda zamuyi muku tukuici dashi daya wuce godiya da addu'a, kuma ma ai yabon gwani ya zama dole"

      Sai mai aikinsu ta musu ruwa da juice da kuma kofuna ta ajiye musu a gabansu bayan sun sha.

      Malam Buba ya kalli Alhaji Inuwa yace "Bayan haka kuma Alhaji akwai wata magana mai muhimmaci da zamuyi kafin mu tafi"

      Alhaji Inuwa yace "Ina sauraronku"

       Malam Buba yace "Kamar yadda ka sani addinin musulinci shine addini na gaskiya kuma ya umarci iyaye su dasu bawa 'ya'yansu hakkokinsu da suka rataya a wuyansu wadanda Allah (S.W.T.) ya sanar da manzonsa Annabi (S.A.W.) shi kuma ya kuma ya sanar damu, kusan duk hakkokin Aisha da suke kan iyayenta kunyi mata su face guda daya tak! shine aure. Aure dai shine mutuncin 'ya mace shine kama kamalarta, shine darajarta, mace duk iliminta duk kyawunta duk nasabarta duk dukiyarta duk gatanta, kasani mutuncinta da darajarta da kamalarta basa fitowa sai tana da aure. Don haka lokacin yayi da ya kamata a ce Aisha anyi mata aure, mun sauke sauran nauyin daya rataya a wuyanmu nata kamar yadda addinin musulinci ya shimfida mana"

      Alhaji Inuwa ya jinjina kai cikin alamun rashin jin dadi yace "Hakika na dade ina tsoron zuwan wannan rana, na dade ina tausayawa kaina idan wannan ranar ta riskeni ba don komai ba sai don irin son da nakewa Aisha. Hakika Allah ya jarabceni da son Aisha fiye da kaina da raina, shine nake ta gudun zuwan wannan rana gashi kuwa yau ta riskeni.........! "

      Alhaji Ahmed cikin yanayin tausayawa ya dafa shi yace "Kayi hakuri Alhaji Inuwa Allah da Annabi ne suka umarcemu da yin hakan......"

       Alhaji Inuwa ya dago kai ya kalleshi idonsa cike da hawaye yace "Nasan da haka Alhaji Ahmed! amma ina so kuyi min wata alfarma guda!"

     "Haba Alhaji ai kai ka wuce ka nemi wata alfarma a wajenmu mu kasa yi maka matukar bata sabawa Allah da Annabi ba"

      "Aisha tun tana karama wani  bai taba hadata da wani da namiji ba har ta kai su ga soyayya, ina son ku bani kwana biyu zanyi tunani akan wannan lamari kuma zamu yi maganar da ita abinda muka yanke zan muku waya na sanar daku"

     Alhaji Ahmed yace "Haba wannan ai ba wani abu bane kaine fa ubanta wuka da nama yana hannunka"

    Daga haka suka rufe maganar suka yi sallama da junansu.

____________

INDIA

     Da gari ya waye Salman da Suhail suka shirya suka je asibiti, suka sami Priya jikin nata da sauki kuwa don tana zaune ansa mata pillow a baya ta jingina a jiki suna hira da mamanta, a haka su Salman suka shiga suka same su, haka suma suka zauna suka wuni anan suna hira cikin farin ciki da jin dadi har bayan sallar isha'i sannan sai suka yi niyyar tafiya, amma abin mamaki sai Priya ta rike Salman tana  cewa ba zai tafi ba har da kukanta, duk sai al'ajabi da tsoro suka kamasu suna ganin kamar wani abu ne zai sameta.

      "Priya wai me yake faruwa ne? me yasa kika hanani tafiya bayan kullum haka nake yi, na iyanzu da safe kuma na dawo!" Salman ya fadi haka cikin yanayin damuwa.

      "To yau dai kada ka tafi ka taimaka ka zauna a tare dani, karka tafi ka barni!"

       "To ai in na tafi gobe ma zan dawo kema kin san haka"

        "Ni dai ka taimaka ka zauna kada ka tafi!"

        "Kinga mamanki tana nan a wajenki babu yadda za'ayi ni kuma na zauna tunda tana nan kuma dokar asibitin nan shine mai jiyya baya wuce mutum daya"

        "Ni dai kada tafi ka barni idan ka tafi na rantse shikenan"

        Hankalin Salman ya tashi sosai yace "Shikenan me?"

       "In dai ka tafi kawai nasan shikenan!"

       "Kaga kawai ka tafi ka rabu da ita, ina ga zafin ciwo ne kawai yake damunta" mamanta ce tace haka.

      Priya tayi farat ta kalli mamanta, tace "A'a mama! na rantse ba wani zafin ciwo da yake damuna, da gaske nake kada ki sashi ya tafi bana so na rabu dashi!"

     Suhail yace "Maganar mama gaskiya ce kawai mu tafi, kuma zaka gani in muka dawo gobe"

    Haka Suhail ya lallaba Salman ya janye shi suka tafi Priya tana ta kwalla masa kira tana kuka tana cewa kada ya tafi, haka Salman ya tafi da kyar ba don yaso ba. Koda suka isa can masaukinsu haka ya zauna yayi shiru yana tunanin kalaman Priya da yanayin da take furucin, Suhail yayi tayi masa hira amma baya kula shi, da ya karbo musu abinci ma Salman ko kallon abinci baiyi ba yaki ci. A haka suka kwanta Salman yana ta tunani da zullumi a fal a ransa, har Suhail yayi barci amma shi baiyi ba haka ya kwana, don da barcin ya fara daukarsa sai ya fara mafarkin gashi an zo za'a kashe Priya tana ta kiran sunan sa, haka dole zai farka cikin kidima da fargaba haka dai yayi tayi har asuba. Bayan sunyi sallar asuba shi Suhail sai ya sake komawa barci, shi kuwa Salman haka ya zauna yana ta lazimi da azkar, Allah Allah yake gari yayi haske ya fita ya tafi asibiti, ai kuwa yana ganin gari ya fara haske ya fita, ba tare dama ya tashi Suhail ya sanar dashi ba, koda ya fita sai ya rasa abin hawan da zai kaishi can asibitin don haka sai ya tafi a kasa kafin yaje kuwa har rana ta fito. Yana karasawa a kofar dakin da aka kwantar da Priya ya samu mamanta tsaye tana ta rusa, ai sai ya karasa da gudu yana tambayarta ko lafiya?

      "Mama me ya faru? Ina Priya take? Wani abun ne ya sameta?"

      Ita kuwa banda gursheken kuka babu abinda take ta ma kasa ce masa uffan! Ganin haka kawai sai Salman ya danna kai cikin dakin da sauri yana shiga sai ya tarar da ita a kwance bata motsi kuma an rufeta da mayafi har kanta, haka ya karasa kusa da ita gabansa sai faduwa yake zuciyarsa tana bugun sha tara tara, hannunsa yana karkarwa haka ya bude fuskarta, me zai gani? kawai sai ganinta yayi a mace kuma wuyanta a yanke an mata yankan rago, ai sai jin kurma ihunsa aka yi muryarsa kuwa babu inda bata je ba a cikin asibitin a floor din da suke, hakan ne yasa duk ma'aikatan da suke a wannan floor suka rankayo da gudu zuwa dakin, hakan yayi daidai da zuwan Suhail haka suka shiga wajensa yana ta kuka cin karfinsa yana surutai. Ai suna shiga sai ya tashi ya sami wani likita ya shakeshi.

     Salman yana kuka yana fadin "Me yasa kuka kashe min ita? me tayi muku?"

      Sai a lokacin wadanda basu san abinda yake faruwa ba suka duba inda Priya take kwance suka ga irin rashin imanin da aka yi mata, Suhail ma ya girgiza ganin wannan mummunan aikin da aka yiwa Priya, shi ya kwaci likitan daga hannun Salman yana rarrashin Salman yana tambayarsa ya aka yi haka ta faru, Salman yace shima bai san aka yi haka ta faru ba shima kawai ya shigo ya ganta ne a haka. Nan dai babban likita ya tambayi mamanta abinda ya faru tace ita dai lafiya suka kwanta da ita tashi kawai tayi ta ganta a wannan hali, sai likitan ya bukaci kowa ya fita su kuma suka dukufa da bincike.

     Aka kira mahaifin Priya aka sanar dashi take yace kwa gashi nan zuwa, kwana biyu da faruwar al'amarin su likitocin basu gama binciken ba balle su bada gawar a binne, to a ranar Barr. Prasad Murella mahaifin Priya ya zo kasar ya kasance shi babban lawyer ne a America, yana zuwa ya shigar da kara a court, police kuma suka kama duk wani ma'aikacin da yayi aikin kwana a ranar da masu gadin asibitin, daga nan aka jira ranar da za'a zauna a kotu.
    

_____________

NIGERIA

     Alhaji Inuwa ya fito daga gida da shirin fita office kafin ya kai ga motarsa sai ya dauko wayarsa a aljihu yayi kiran Alhaji Ahmed.

     "Assalamu Alaikum"

     "Wa alaikas salam"

     "Ya gida? ya aiki?"

     "Lafiya kalau"

     "Ya iyalai?"

      "Lafiya lau wallahi"

      "Kun tattauna akan maganar nan kenan? ai tun jiya nake jiran kiranka"

       "Eh wallahi mun dan tattauna"

       "Yauwa to ina jinka"

        "Ah maganar tana da girma ba zata yiwu a waya ba, amma Insha Allahu gobe zan zo"

        "Gobe goben nan?"

        "Eh gobe Insha Allahu"

        "To Allah ya kawo ka lafiya"

        "Amin amin"

        "Yauwa sai an jima"

   Sai ya bude motarsa yana farin ciki ya shiga ya tafi.

     
      ***           ***           ***           ***

        Da daddare suna zaune a dining cin abinci sai Alhaji Inuwa ya tsaya ya kurawa Aisha ido, can kuma sai ya dauke kai ya kalli Hajiya Sailuba, yace "In Allah ya kaimu gobe ina so zanje Kaduna gidan Alhaji Ahmed.

      "Gobe goben nan kuma?" Hajiya Sailuba ta tambaya.

      "Insha Allahu" ya bada amsa a takaice.

      "Tare da Ummi zaku kenan?"

      Yayi saurin cewa "Me kika gani?"

      "Naga kana ta kallonta kamar ka shekara baka ganta ba"

       Yayi murmushi yace "Bada ita zan tafi ba, ni kadai zani shi yasa ma zan tafi da wuri don na dawo da wuri"

      "Allah ya dawo mana da kai lafiya kuma don Allah ka gaida min da Rahima"

      "Daddy ka gaida min da Abba da Umma"

       "Zasuji Insha Allahu"

      Daga babu wanda ya sake magana har suka gama, bayan sun gama basu zauna hira kamar yadda suke yi kullum ba saboda tafiyar da Alhaji Inuwa zai yi da safe. Da sassafe kuwa haka yayi sammako ya tafi, bayan ya isa gidan Alhaji Ahmed ya huta suka yi breakfast tare, bayan sun gama sai suka zauna suna tattaunawa.

       "Shi yasa ai kaji nace ka bari nazo da kaina domin maganar tana da muhimmanci sosai tafi karfin a yita a waya. Da wannan tunanin da nayi ne zumuncinmu zai kara karfi" Alhaji Inuwa ne yayi wannan jawabi.

     "To Allah yasa haka" Alhaji Ahmed ya fada.

      Alhaji Inuwa yace "Amin, Alhaji ina so na auri Aisha!"

      Alhaji Ahmed ya kalleshi da sauri yace "Me kace Alhaji Inuwa"

      Alhaji Inuwa yace "Ina so na aureta, yin hakan shine zai kara dankon zumuncinmu kuma uwa uba ma hankalina zai kwanta daga tashin da yayi na rabuwa da ita, domin rabuwa da Aisha kamar rabuwa da raina ne"

      Alhaji Ahmed ya jinjina kai yana kallonsa yace "Duk dana san hakan ba haramun bane a addini amma hakan ba zai zama wani irin al'amari ba sabo?"

       Alhaji Inuwa ya girgiza kai da sauri yace "Haba! ai wannan ba komai bane, kaga ai bamu muka haifeta ba kuma bamu shayar da ita ba, mu marikanta ne ba mahaifanta ba, kaga kuwa wannan ai ba laifi bane"

      "To bangaren mai dakinka fa? kana ganin ba komai don bana son abinda za'a zo daga karshe ana dana sani!"

      "Don ta ita mai sauki ne saboda itama bata son rabuwa da Aisha"

      "To ita kuma Aisha fa ta amince ko bata amince ba?"

       "Itama ba matsala a gurinta"

       "To shikenan Allah yasa hakan shi yafi alkhairi"

        "Amin amin"

      Bayan Alhaji Inuwa ya dawo Kano da daddare suna daki Hajiya Sailuba tana kishingide shi kuma Alhaji Inuwa yana zaune a gefen gado. A lokacin yake gaya mata bukatarsa ta auren Aisha, ai kwa abinda zai fito daga bakinta yayi matukar bashi mamaki.

      Hajiya Sailuba ta tashi zaune tana huci tana magana cikin fada "Ba zai taba yiwuwa ba wallahi, wannan ma ai abin kunya ne, girma ya fadi rakumi ya shanye ruwan 'yan tsaki! wai kai ko kunya ma bakaji ba ko?"

         Ya kalleta cikin sauri fuskarta dauke da mamakin maganar data fada, yace "Wace irin kunya kuma? sunnar ma'aiki fa zan raya!"

        Tayi masa wani irin kallo mai dauke da Harare tace "Yarinyar nan fa mu muka reneta tun tana karama, amma yanzu kace ita zaka aura.......!"

      Ya daga mata hannu alamun tayi shiru yace "Dakata Sailuba naga hakan ai bai sabawa addini ba"

      Cikin fada take dada yin maganar "Amma ai akan bar halak don kunya!"

      Yayi saurin girgiza kai yace "Ke ba'a ko'ina ake kunya ba, idan kayi a gun da ba zaka cutu ba ba matsala, amma wajen da zaka cutu ai sai ka cireta"

       "Tunda hagu taki bari na koma dama, kai ne fa kayi min duk wuya duk rintsi ba zaka taba yin min kishiya ba ko manta shekara talatin da suka wuce kace har abada ba zaka yi min kishiya ba! ina alkawarin yake?"

                        Tabdijan!

Kada fa ku manta da:

>Like
>Share
>Follow
>Comments

      
                          📖.............. ✍️
                       *Alkhamis KSA*

Continue Reading

You'll Also Like

228K 2.5K 20
I have found an ideal life. I have a loving husband, no work and no danger. This is exactly what I wanted when I ran away and changed my identity. Bu...
120K 15.8K 34
#Book-3 Last book of Hidden Marriage Series. ๐Ÿ”ฅโค๏ธ This book is the continuation of the first and second book "Hidden Marriage - Amazing Husband." If...
792K 79.9K 55
3 lives got entangled due to the twisted Destiny...... Vidyut Rajvanshi married his college sweetheart Sanjana and was leading a happy life ......bot...
227K 17.2K 24
"ู…ุง ู‡ููŠ ุฑูŽุบุจุงุชููƒ ุงู„ู…ูุธู„ู…ุฉ ..ุฏูƒุชูˆุฑ ุฌูŠููˆู†ุŸ" "ู„ูŽุฏูŠ ุบูŽุฑุงุฆุฒ ุชุงูŠู‡ูŠููˆู†ุบ ..ู„ุง ุฑูŽุบุจุงุชุŒ ูˆูŽ ู‡ูู†ุงูƒ ููŽุฑู‚" ุขุฏุช ุฃููƒุงุฑ ุชุงูŠู‡ูŠููˆู†ุบ ูˆูŽ ูุถูˆู„ู‡ ุญูŽูˆู„ ุฑูŽุบุจุงุช ุงู„ุฃู†ุณุงู† ุงู„ู…ูุธู„ู…...