ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

By KhamisSulaiman

180 16 1

Labarin wata yarinya ne da take bata tun bata da hankali, iyayenta basu tashi ganinta ba sai da ta zama budur... More

Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 9
Chapter 10

Chapter 8

5 1 0
By KhamisSulaiman

        ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

*Daga Kundin✍️ 📚✍️
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008
Phone no: +2348085871223

                      *page 15 & 16*

    Salman da Suhail suna dauke da Priya suna gudu, bodyguards din Khodaram Moham kuma suna biye dasu suna ta gudu a cikin daji wani wajen ma har faduwa suke sannan su tashi su dauke ta su cigaba da gudu, Priya kuwa tuni ta suma, a haka dai har suka kai bakin titi cikin sa'a kuwa suna zuwa sai ga wata motar kaya ta zo wuce babu kaya a ciki irin ta kai kayan ta dawo, suka tsayar da ita cikin sa'a direban ya tsaya suka hau suka dora Priya suka sa ya figi motar suka nufi cikin gari. Sai a sannan Salman ya lura da Priya bata numfashi nan fa hankalinsa ya kara tashi ya shiga jijjigata cikin dimuwa da tsoro, a haka har suka kai asibiti aka zo da stretcher aka dorata aka turata da gudu har zuwa ICU nan likitoci suka dukufa akan don ceto ranta, a tsaye Salman da Suhail suka kwana suna jimami da farbaga har dai likita basu damar zuwa su dubata, bayan sun shiga ne sun dubata duk bata san ana yi ba, Salman har da kuka ganin duk abinda ya sameta a kansa ne sai yaji sonta ya karu a ransa, bayan sun dan dade a dakin ne suka yanke shawarar kiran mahaifiyarta su sanar da ita saboda mahaifinta baya nan yana can New York yana aiki a can, haka kuwa aka yi suka kira mahaifiyarta suka ce mata wasu 'yan ta'adda sun harbi 'yarta Priya yanzu haka suna nan a asibiti, haka uwar ta hawo jirgin zuwa Goa cikin tashin hankali da zullumi.

                       Wannan Kenan!

_______________

NIGERIA

     Alhaji Ahmed da Rahima suna zaune a falonsu suna hira yayin da Aisha take a cikin daki amma tana jin abinda suke tattaunawa akai.

        A hirar ne Rahima ta kalli Alhaji Ahmed, tace "Alhaji na manta fa ban gaya maka kayan abincinmu ya kare saura na wannan makon kawai"

       Alhaji Ahmed yayi farat ya kalleta cikin mamaki yace "Wane irin ya kare? amma tun kwanakin baya baki gaya min ba bayan kuma kina ganin ina ta wadaka da kudi baki fada ba min ba sai yanzu da kudin suka kare zaki fada min!"

       Rahima ta kalli fuskarsa jiki a sanyaye tace "Haba Alhaji amma kasan.......!"

       Bata gama maganar ba sai suji sallamar Rahina da Rahila, Rahima ta tashi da sauri ta rungumesu cikin farin ciki su karaso ciki su zazzauna su gaisa da Alhaji Ahmed.

       "Sannunku da anty" Rahima tace.

       "Yauwa sannu da gida Rahima ya aiki?"

        "Lafiya kalau ya hanya?"

        "Hanya lafiya kalau" ta kalli Rahila tace "Sannu yaya"

         "Yauwa Rahima ya gida ya aiki da fatan komai lafiya?"

        "Duk lafiya kalau wallahi" sai ta kalli kofar daki ta kwallawa Aisha kira "Aisha! Aisha!"

        "Na'am umma" ta amsa tana daga cikin daki, sai ta fito.

        "Iyayenki ne suka zo, ki zo ku gaisa"

          Sai Aisha ta karasa kusa dasu ta zauna a kasa su gaisa.

       "Ki kawo musu ruwan sha mana"

       "To umma" ta mike ta nufi inda ruwan yake.

        Rahila ta kalli Alhaji Ahmed, tace "Amma Alhaji Ahmed yanzu Aisha ta saki jikinta ko?"

        Alhaji Alhaji ya gyada kai yana murmushi yace "Sosai ma kuwa fiye ma da tunanin mai tunani, kai idan ba gaya maka aka yi ba, baza kace ba'a wajenmu ta girma ba"
      
        Rahina tace "Ah to Alhamdulillahi"

      Aisha ta dawo dauke da ruwan a hannu tazo ta ajiye musu a gabansu sannan ta koma daki.

       Rahila ta bita da kallo har ta shiga daki sannan ta juyo da kallo ga Alhaji Ahmed, tace "Alhaji Ahmed gaskiya Aisha ta isa aure don har ta kusan wuce munzalin auren, kada duniya ta zagemu, don gaza cikashe hakkinta dake kanmu wanda Allah ya umarce da muyi"

      Rahina tace "Kamar kin shiga cikin zuciyata kaga abinda ke ciki, nima naga haka, na rigaki a zuci kin rigani furtawa"

       Rahima tayi murmushi tace "Kunga nima nayi wannan tunanin amma ganin Alhaji bai yi maganar ba, sai na barta kawai a cikin zuciyata"

      Alhaji Ahmed ya jinjina kai yana rike da baki yace "Nima naga yin hakan ya kamata, to amma da nayi tunani sai naga ita Aisha ai ba anan zata zauna ba zata koma can gidan Alhaji Inuwa ne ta cigaba da rayuwa, to amma duk da haka tunda tunaninmu yazo daya, in dai Allah yasa muka koma can gidan Alhaji Inuwa zan bashi shawarar hakan, sai muyi abinda ya dace"

       Rahila ta jinjina kai tace "Ai gara ayi mata auren ta huta, don darajar mace shine gidan mijinta"

  Duk abinda suke tattaunawa Aisha tana jinsu, a ranta tace 'Tabdijan aure!' don sai a lokacin ma ta fara wani tunani ta duba taga tunda Allah ya halicceta bata taba yin saurayi ba koda kuwa irin na makarantar nan ne ko na yarinta, a ranta ta sake cewa 'in haka ne kuwa zata dade bata yi auren ba, don ita bata ma san menene so ba kuma ma baya gabanta'

       Washegari da hantsi su Aunty Rahina da yaya Rahila suka koma Kano, kamar dama Aisha su take su tafi, basu dade da tafiya ba Aisha ta fita daga gidan don Rahima ko sani batayi ba, tana fita bata zame ko ina ba sai banki ta ciri kudi sannan ta tafi supermarket tayi musu siyayyar kayan abinci irinsu shinkafa, taliya, macaroni, couscous, noodles, man ja da farin ma, da seasonings da dai sauran kayan abinci, daga nan ta wuce kasuwa ta siyo doya da potatoes da kayan miya da kaji da kifi da kwai, haka tazo ta gibgewa Rahima su a tsakar gida. Mamaki ma sai ya hana cewa komai, ta dai tambayeta daga ina? ita kuma tace ita ta siyo musu da kudin albashinta da take tarawa tunda ta fara aiki don a gidan Alhaji Inuwa babu abinda take siya, Rahima ta nuna mata kayan sunyi yawa amma sai Aisha tace ba komai ai su iyayenta ne komai tayi musu bata fadi ba. Haka da Alhaji Ahmed ya dawo haka suka yi, nan dai suka dinga sa mata alfarma.

____________

INDIA

    Maman Priya tazo yanzu ita take kula da ita ta kwana a wajenta, su kuma su Salman sai su koma hotel su kwana in dare yayi da safe kuma su dawo, anan zasu wuni suna tare dasu sai da daddare kuma su koma masuki.
Yau ma kamar kullum sun wuni a asibitin da daddare sai suka koma hotel suna zaune a dakinsu na hotel Salman yana ta research shi kuma Suhail yana chatting kawai sai yaga wata sanarwa a social media cewa Lakshmi 'yar Khodaram Moham ta janye taron zabar miji da zatayi sakamakon miji data samu, a kuma sai ga hotonta dana Salman, Suhail yana ganin haka ya nunawa Salman ransa ya baci sosai, sai Suhail ya shiga wajen comments domin yaga abinda al'ummar kasar suke cewa, Salman yace ya ringa karantawa yadda zai ji.

      Na farko sunansa Rahul yace "A India ba mazan ne da har sai tafi kasashen ketare?"

     Wannan kuma Gautam yace "Lallai wannan dan Nigeria ya shigo India da kafar dama"

     Sai Nandini tace "To wai duk ina mazan kasar India suke? ga wani yazo ya muku fintinkau"

      Abhinash kuma yace "Dama wannan ai dai dan najeriyar!"

      Kureish yace "Kwadayi dai mabudin wahala ne da wulakanci!"

      Pallabi kuma cewa tayi "Kenan duk  samarin India sun gaza sai dan wata kasar?"

      Suhail ya kalli Salman, yace "Duk kaji irin maganganun da suke wasu ma duk izgili kawai da tsokana"

      Salman yace "Ai duk don basu san gaskiyar abinda ya faru bane"

    Kawai sai wayar Salman ta fara ringing sai ya duba yaga Aman ne sai ya daga.

      "Hello Aman"

      "Salman wai me yake faruwa ne? naga wani labari wai zaka Lakshmi 'yar Khodaram Moham wadda take neman saurayi!"

       "Ba haka bane, ta dai bukaci na amince na aureta ni kuma naki amimcewa shi ta tsiro da wannan labarin kazon kuregen!

       "Haba abin ya bani mamaki! Salman din ne zai auri wannan?"

       "Wallahi ba haka bane zancen karya ne kawai"

       "Shikenan Salman, amma ka kula don ance Khodaram Moham bashi da imani kashe mutum a wajensa ba komai bane"

       Zan kula Insha Allahu karka damu, na gode sai an jima" ya katse wayar.

       Yana katsewa wani kiran ya sake shigowa ya duba yaga Raj ne, sai ya daga.

       "Hello Raj ya akai?"

       "Kai yanzu da aure zakayi amma shine ba zaka sanar damu ba sai dai muji a social media, saboda baka dauke mu da muhimmanci ba, kuma baka girmama abota"

      "Kai! Raj dahalla saurara! kada ka kara bata min rai, dama yanzu raina a bacen yake"

      "Wai me yake faruwa ne Salman?"

      "Ka bari kawai Raj! wani tsinannen mutumi ne yake son yaja min jangwam, yanzu haka ya harbi Priya a kafarta da kafadarta tana kwance a asibiti"

     "Kai! waye wannan kuwa da irin wannan danyan aiki?"

     "Waye kuwa banda Khodaram Moham mahaifin Lakshmi, kawai don 'yarsa Lakshmi ta nuna tana sona ni kuma naki amincewa shine ya farauci rayuwar mu, da hannunsa fa ya harbi Priya har sau biyu a kafa da kafada! wallahi ba zan kyale ba!"

      "A'a Salman! irin wadannan mutanen ba'a zake musu saboda ta ko'ina sun fika karfi, suna da kudi, suna kafa a gwamnati, suna daurin gindi, suna da tarin masu farauto musu duk wanda suke so kuma ko a ina suke, don haka kada ka jefa kanka a halaka!"

      "Hmn! ka bari kawai zan kira ka next time"

      "To shikenan fatan alkhairi"

    Salman yana kashe wayar sai Suhail ya miko masa wayarsa.

      Salman ya kalleshi yace "Ya akai?"

      "Sameera ce ta kirani tace na hada ku da ita ta kira ka kana waya"

      Salman ya karbi wayar ya kara a kunne "Sameera ya akai ne?"

      "Salman a babu abinda yake yawo sai hotunanku kai da Lakshmi wadda tace zata tara maza ta zabi miji a cikin su, amma wai na hau Facebook babu abinda ake sai zance wai aure zakuyi, nayi tunanin irin masu hada hotunan nan ne amma dana hau Instagram da groups Whatsapp, Twitter da Tiktok ma duk abu daya ake magana akai shi yasa nace sai na kira ka naji dahir"

       "Wallahi Sameera duk abinda kika ba haka bane kawai mutane ne suke ta shacifadi" nan ya kwashe labarin duk abinda ya faru ya gaya mata, tayi ta'ajibi sosai suna cikin wayar shima wayarsa ta fara ringing ya duba sai yaga Pooja kawai yaki dagawa ya cewa Sameera itama zai kirata, ya kalli Suhail.

     "Suhail zo kayi min video zan gayawa duniya abinda ya faru sannan karyata abinda suke ta yadawa"

     "Yauwa Salman, wannan shine mafita ta farko"

   Sai yaje ya dauko Trafford yasa wayarsa a jiki ya fara yi masa video recording shi kuma Salman ya fara jawabi.

       "Jama'ar wannan kasa da wadanda suke a wasu kasashen a fadin duniya barkanku da wannan lokaci. Sunana Salman Abdallah Ni dan Nigeria ne nazo nan kasar India ne karatu, a tsakanin jiya da yau wasu hotuna da wata mata Lakshmi suna ta yawo a kafafen sada zumunci da bayanin cewa wai ni ne wanda zai auri wannan mata, to magana ta gaskiya wannan zance karya ne! ban ayi haka dani ba bana sonta kuma ko matan duniya zasu kare ya zama ita kadai ce ta rage to wallahi dana aureta gara na mutu banyi aure!" nan ya kwashe labarin abinda ya faru ya bayyanawa al'umma bai boye komai ba har da fadar asibitin da Priya take a kwance.

     Bayan gama daukar wannan video wannan sai suka tura a duk wani shafi na social media da suke yi irin su Facebook, Whatsapp, Instagram, Twitter da Tiktok. Kan kace kuwa labarin ya kewaya ko'ina sama da mutane million sun gani ciki kuwa har da Lakshmi. Tana gani kuwa ta tashi taje wajen uban nata tana kuka ta nuna masa videon da Salman yayi.

       "Karki damu kanki akan wannan dolen sa ma ya aureki tunda kina sonsa hakan ma ya wadatar, kuma duk wannan abinda yake yi yana yi ne saboda wannan yarinyar kuma ya fadi inda take zan san matakin da zan dauka a kanta, ta haka ne kawai zai karbi bukatar mu, amma in dai yarinyar nan tana nan ba zai taba yin abinda muka ce masa ba! Don haka ki kwantar da hankalinki zamuje asibitin"

     Shi kuwa Salman ganin like da comments da share sai hankalinsa ya dan kwanta haka suka kwanta barci.

_____________

NIGERIA

       Aisha ta gama kwanakin da zata yi na hutu a gidan iyayenta, yau zata koma gidan Alhaji Inuwa ta cigaba da zama a can, kuma Alhaji Ahmed ne zai kaita, yanzu ma ya fita ya dawo yace ta shirya kafin ya dawo. Aisha tana zaune akan gado tana ta tunani tayi tagumi, sai Rahima ta shigo dakin.

      "A'a Aisha tunanin me kike yi kuma ke da nace kizo ki hada kayanki na tafiya sai kizo ki zauna tunani mara amfani"

      Aisha ta dago kai ta kalli Rahima sannan ta maida kai kasa ba tare da tayi magana ba.

      "Ki tashi ki hada kayan mana, ko sai gobe kuma mu da zamu tafi da wuri kizo kina hadawa a cikin rashin nutsuwa"

      Aisha ranta a bace ta tashi ta fara hada kayanta tana sawa a cikin trolley. Bayan Alhaji Ahmed ya dawo suka shirya suka tafi tafiyar awa uku suka yi suka isa Kano kai tsaye gidan Rahina suka wuce sai suka fara zuwa nan sannan Alhaji Ahmed ya nemi da malam Buba yayi masa rakiya don akwai maganar da zasuyi da Alhaji Inuwa idan sunje, malam Buba ya shirya suka rankaya gaba daya.

Kada ku manta da:

>Like
>Share
>Follow
>Comments

                           📖........... ✍️
                       *Alkhamis KSA*
       

Continue Reading

You'll Also Like

4.3M 287K 61
"Why the fuck you let him touch you!!!"he growled while punching the wall behind me 'I am so scared right now what if he hit me like my father did to...
5.5M 228K 68
The story of Abeer Singh Rathore and Chandni Sharma continue.............. when Destiny bond two strangers in holy bond accidentally ❣️ Cover credit...
988K 30.5K 61
Dans un monde où le chaos et la violence étaient maitre, ne laissant place à ne serrait ce qu'un soupçon d'humanité. Plume était l'exception. Elle...
225K 7.2K 55
ရိပ်ချေ ကိုကြီးကိုချစ်တယ် ။ ကိုကြီးလည်း ရိပ်ချေကိုချစ်လာရင် ဖွင့်ပြောပေးနော် ။ နွေဦးရိပ်ချေ 🍀 နေမခန်း & နွေဦးရိပ်ခ...