WANI GARI

By KhadeejaCandy

10.4K 566 36

A wani gari, da al'ummarsa basa hada jini da mutanen wajen garin, akwai wata yarinya da alkalamin kaddara yay... More

WG-01
WG-02
WG-03
WG-04
00
WG_06
07
08
09
WG-10
11
12
13
14
15

WG-05

528 34 1
By KhadeejaCandy

“Ko wace dakika da mintuna idan suka wuce basa dawowa, rashin dawowar yana nufin rasa abubuwa da dama ciki har da lokaci idan baka yi amfani da shi a lokacin da ya dace ba, kyaunku ba zai tabbatar har a bada ba, ku yi aure a lokacin da maza suke ganinku suna yaba surarku har suna sha'awar aurenku, idan lokaci ya wuce za ku neme su ku rasa a lokacin ido zai rufe wata kila ku fadawa wanda be dace da aurenku ba, ba ni da buri a yanzu kamar ganin aurenku”

Ta sauke hannunta daga fuskar Nimra tana murmushi.

“Zamu yi aure Ummi, ni kin riga da kin san inda da wanda nake so kuma da zarar ya dawo daga Umra zan masa magana ya turo, sai dai ki yi ma Namra wa'azi ta rika sauraren masu zuwa gurinta, domin ita ce mai girman kai”

Namra dake ta danne danne da complete ta dago a fusace tana kallon kanwarta, wato Husainarta.

“Okay haka kike zama gurin Ummi kina min munafurci ko? Kina ruwanki da rayuwata? Maybe I'm not ready now ko kuma dukan masu zuwan basu min ba”

Ummi ta lankwasa kai tana kallon yarta.

“Na fa san halinki Namra, taya za a ce duk samarin dake nuna suna sonki babu wanda yayi miki?”

“Ummi I'm serious gaba dayansu ni ba su min ba”

“Ba ki sake jiki da su taya za'ayi ki san wadanda suka miki? Da wandanda basa miki?”

Cewar Nimra, domin ita ce mai far'a da saurin sabo ga son mutane, yadda take friendly da kowa sai ka dauka tana kaunar duk namijin da ta yi arba da shi ne.

“Nimra this is my life, can you please mind your own business? Ni fa ba irinki ba ce kowa far'a kowa dariya har wanda be kamata ace yana sonka ba ya zo yana maka maganar soyayya”

“Ummi See? Kin ga abun da nake fada miki ko? Fadin rai ba zai bar ta ta kula samari ba”

Namra ta dauki fillon kujera ta jefawa Nimra, Hajiya Zahra ta yi saurin saka hannunta ta tare.

“Gaskiyar da ba ki so, dole mu fada miki, kuma karki yarda na sake jin bakinki ya furta cewar baya son kowa?”

Miyewa ta yi sauye bayan fadar haka ta nufi wata karamar kofa dake falon ta bude ta fita tsakar gidan da ko'ina yake tsab, matsawa ta yi kusa da flowers ta mika hannunta tana taba su a hankali, babu ranar da bata tunanin ďanta, babu ranar da zata zauna ta yi hira da yaranta akan rayuwarsu bata tuna da ďanta, damuwarshi ta haifar mata da damuwa da yawa, ta haifar masa da rashin kuzarin iya rike kanta a duk lokacin da ta tuna kamar yadda hawaye suka fara wanke fuskarta, ta kasa cire kanta a damuwa ta kasa daina tunaninsa duk da kasancewar likita ya gargadeta da ta cire damuwa a ranta saboda hawan jinin da take fama da shi. A tsorace ta juyo jin muryar Mahmood yana kiranta. Kamar hoto ya tsaya yana kallonta ganin hawaye a idonta.

“Ummi lafiya?”

Ta taba fuskarta sai ta ji hawayen sa bata san lokacin da suka sauko mata ba, murmushi ta yi ta share hawayen.

“Lafiya kalau, yanzu ka dawo?”

“Eh ni ma dauko Abiey, amman Ummi ba lafiya ba kalli fa kuka kike yi”

“Tunani kawai nake yi, makomar yayana idan bana raye that's...”

Ta karasa wasu hawayen na sauko mata.

“Haba Ummi ki daina kawo wannan abun a ranki please, ba zai taba faruwa ba tare zamu rayuwa In Shaa Allah”

Ya rumgume yana jin wani emotional, he can't imagine his life without her, ta ya za su iya rayuwa.

“Ummi ba zamu iya rayuwa ba idan babu ke, babu wanda zai rayu babu uwa a kusa da shi kuma ya more rayuwa, there's no love like a mother love for her child”

Kalaman da Mahmood yayi sai ya kara sakata cikin damuwa, ta kara tausayin ďanta, su da suka san dadinta suke fadar haka ina ga wanda be sani ba.
Lumshe ido ta yi wasu hawayen masu zafi suna sauko mata, su da suka rayu da ita kenan suka san dadinta ina ga wanda ya rayu shi kadai be san dadinta ba.

‘Ko waye mahaifiyarsa a yanzu?’

Ta tambaye kanta, kamin ta dago fuskarta ta share hawayen ta nufi kofar fita daga gurin tana sauke kanta kasa domin bata son yaranta da suke falo su lura da kukanta. dakinta ta shiga ta ci kukanta iya wanda ya isheta sannan ta wanke fuskarta ta shafa hoda da kwalli saboda ta bata da fuskar kukan amman ina ya kasa boyuwa a idon mijinta, domin a duk lokacin da ta shiga bangarensa idonta yake fara kallo ta nan yake iya karantar damuwarta.

“Zahra kukan me kika yi?”

Ya tsayar da shirya kulolin abincin da take kuma ta kasa hada ido da shi.

“Na tashi ne bana jindadin jikina”

“Amman ba zan fita ba haka na barki ba, wani abun ya faru ne? Ko yarane suka bata miki rai?”

Ta kalleshi tare da girgiza masa kai.

“No, ina tunanin ďana ne, na kasa manta ciwon har yanzu, ban san ranar da zan warke ba”

Kamar daukewar wutar nepa haka Abiey yayi shiru be sake cewa komai ba, har ta gama zuba abincin ta aje masa a maimakon ya ci sai ya mike tsaye ba tare da ya kalli abincin ba ya fice daga falon na shi ya shige dakinsa, binsa ta yi da kallo hawaye na sauko mata, haka suke yawan samun sabani a duk lokacin da zata nuna masa kauna ko tausayin ďanta da baya tare da ita, wannan dalilin ya saka ta boye abin a ranta ta daina maganarsa ko son sanin halin da yake ciki, balle har ta tambaye shi, yana raye baya raye a halin yanzu duk bata sani ba.

“Lokuta da dama bana iya tunani mai kyau, na kan aikata abun da yake zuwa ya zame min na bakinciki da nadama, ni kawai bana iya aikata komai a daidai”

Ta furta tana girgiza kai kuka take sosai irin kukan nan marar sauti.

AMEER POV.

A gurin da suka saba shakatawa suke zaune, sai dai a yau a waje suke zaune ba VIP ba kamar yadda suka saba, saboda Ameer da ya riga su zuwa ya kama guri a harabar da wasu suke zama ya zauna, a ka'ida idan ya zauna a guri, siye gurin yake irin siyewar da ko awa nawa zai yi ba za a shigo ko a zaunar da wani costumer ba, sai idan ya bar gurin ko da kuwa zuwansa ne na farko a guri, Ameer na jin wata kalar isa da kasaita kamar wani Sarki da shi kadai ya ke da ikon yin yadda yake so a ciki jama'a, sai dai a mamakinsu yau yana zaune cikin mutane and nishadin dake fuskarsa sai ka yi zaton irin samarin nan ne da ba su dauki duniya da zafi ba.

“Miyasa za mu zauna a nan wai?”

Tarig ya tambaya domin basa jin sakewa a public place like this one.

“Ban cilastawa kowa zama ba, ni kuka tarar a nan zaune kuma kuka yi deciding ku zauna, zaku iya shiga ciki idan kuna ra'ayi”

Ya fada tamkar ba shi yake maganar ba, ya tattara hankalinsa gaba daya ya maida gurin mutane dake kai da kawo a gurin.

“Ameer ya kamata ku sasanta kanku da Maleek”

“Miyasa na zauna a nan”

Ameer ya fada da sauri yana rufe idonsa domin ko maganar Maleek baya so. Tarig da yayi maganar ya kalleshi da mamakin jin furuncin da be tsammaci jinsa daga bakinsa a yanzu ba.

“Kana nufin saboda ku shirya ka zauna a nan?”

“Saboda mu kara nisantar juna dai, bana son ko gurin da na zauna Maleek ya sake zama”

“No Ameer wannan dabi'un yara ne, mu kuma ba yara ba ne, be kamata mu yi haka ba?”

“Idan ka sake min wata maganar da ta shafi Maleek Tarig sai na hada kai da shi na bindigeku, baka san yadda yaron nan ya bata min rai ba ko? Kawai yawu ya watsa min a fuska fa haba”

Ameer ya fada babu alamar wasa a fuskarsa. Tarig ya wasa masa wani kallon banza.

“Go ahead waya rike ka? Ka saka bindigar ka halbemu mana sai ka gani idan kai zama zaka yi a duniyar, kai babu wanda ya isa ya fada maka gaskiya ko ya nuna maka abun da kai ba ba daidai ba ne, wane irin girman kai ne a tare da kai?”

“Irin wanda ba a siye da kudi balle ka siye, kuma ba a saukewa balle ka raba ni da shi, ya zaka yi?”

Kallon kallo akuya kallon kura suka rika yi ma junansu.  Kamin Ameer ya mike tsaye yana ya nufi motarsa hango Maleek ya fito daga motarsa ya doso gurin. Maleek ya kalli Ameer kamar ya yi masa magana domin shi baya son gaba kuma be iya gaba ba, duk yadda zaka bata masa rai sai yayi maka magana, sai dai kuma wata zuciyar ta hana shi gudun kar Ameer ya disgashi a gaban jama'a.

“Tafiya yayi?”

Maleek ya fada a yayinda yake kokarin zama. Tarig ya sauke ajiyar zuciya ya ciro wayarsa aljihu ya soma tabawa yana fadin.

“Wani lokacin na kan rasa gane kan Ameer, yana da fushi sosai kuma yana dadewa be sauka ba, kai ma kuma abun da ka yi baka kyauta masa, na san yadda ya tsani kazanta taya zaka tofa masa yawu a fuska”

Maleek ya hade yawu na rashin jindadin abun da yayi.

“I know that's why I'm here hakuri na so na ba shi, kuma shi ma ya kamata ace yana kiyaye abun da bana so”

“idan wani ya ciza sai wani ya hura, ba wai kai ka yi fushi ba shi yayi fushi, dukamu tare muke ba zamu zabeka mu cireshi a cikinmu ba, haka kuma na za mu cireka mu zauna da shi”

A kokarin Maleek na kawar da maganar ya tambaye dayan abokin na su.

“Ina Abdull?”

“Be zo ba”

“And miyasa kuka zauna a nan?”

“Ameer na tarar a nan, baya son shiga ciki saboda kar ku zauna a guri daya”

Maleek yayi murmushi mai sauti

“Yara ne suke wannan, of course zamu yi fada mu batawa juna rai amman ban da gaba ko tsanar juna ko kyamar zama kusa da juna”

Maleek ya fadar hakan Dawood da ya karaso inda suke zaune ya daki kafadarsa yana dariya.

“That's right bro, zaman da babu fada ba taren amana ba ce, zo mu zauna shi ne zo mu saba dole ne mu rika hakuri da juna”

Maleek ya mika masa hannu suka gaisa, kana suka mike tsaye gaba dayansu suka shiga can cikin VIP din suka zauna, wani sabon shafin hira ya bude, waiter dake kawo musu lemu ya kawo tare da zubawa kowa a cups dinsa sannan ya aje ragowar, ya koma gurin aikinsa Maleek ne ya fara dauka ya sha domin coconut drink ne favorite dinsa, sannan Dawood ya sha, an jima kadan aka kawo musu abin tabawa kowaya ci ya sha, daman Ameer ne kawai baya ci ko shan wani abu a gurin saboda tsabdar da yake da ita, wai shi ba zai iya cin abincin restaurant ba domin be san iya sharing din da aka yi da spoon din ko plate ba, and be san wadanda suka girka ba, kuma ba shi da tabbacin an tsabtace girkin ko akasin haka.

After like 20 min da shan lemin Ameer ya ji kansa na masa nauyi har yana saukowa cikin idonsa, ba kuma ciwo yake jin kan na masa ba nauyi yake irin na wadanda bachi be wadace su ba, sai dai ya daure duk hirar da ake be nuna komai ba duk da kasancewar baya cewa komai sai kallonsu yake yana murmushin karfin hali.

“Hey Bachi kake ji?”

Tarig ya tambaya lura da yadda Ameer yake lumshe ido yana budewa a kokarinsa na hana kanshi bachin da be san ta ina yake fito masa ba.

“Maybe”

Ya fada cikin rashin tabbacin idan bachin ne domin ya san yayi enough bachi jiya. Ya mike tsaye ya dauki keys dinsa dake kan table din

“Bari na tafi”

Be jira cewarsu ba ya fice daga gurin yana jin idanuwansa na kara nauyi har baya son daga su sosai, kamin ya isa gurin motarsa har wani jiri jiri yake ji yana dibarsa kamar zai fadi, lalabe yayi ta yi kamin ya samu sa'ar saka key din motar a muhallinsa ya bude ya shiga sai ya dora kansa saman sitiyarin motar yana ta kokuwa da bachin mai kama da na sihiri.

“Malam lafiya?”

Ya ji wata muryar wanda ta yi masa kama da muryar da ya sani tana kokarin shigowa a cikin birnin dake kokarin gina duniyarsa a bachinsa, ba karamin shahada yayi ba sannan ya samu bude idon da suka soma sauya launi ya kalli fuskar kyakkyawan saurayin da ba zai wuce sa'ar kanensa Mahmood ba.

“Lafiya kalau Bachi nake ji”

“Subhanallah zaka iya tuka motar kuwa”

“Shi ne abun da nake tunani”

“Bari na taimaka maka, ka koma gaba zai na motar ina ne gidanku?”

Kamin ya amsawa bakon saurayin har bachin ya ci karfinsa ya tafi da idonsa har sai da saurayin ya jijjiga kafadarsa.

“Malam... Ka koma dayan side din”

Daker ya rika kofar motar ya fito yana tafiya kamar marar lafiya mutumen ya zagaya ya bude masa from seat Maleek ya shiga ya zauna, har yana masa godiya. Kamin saurayin ya zagaya ya shiga mazaunin direba har bachin Maleek ya fara nisa.
Saurayin dake sanye da kannan kaya ya tashi motar suka hau titi, minti biyu uku sai saurayin ya juya kalli Maleek dake ta bachi, unguwanin da babu mutane ya nufa da shi sai da ya lura da gurin da mutane ba za su ganshi ba sannan ya faka motar, ya ciro wayarsa ya shiga camera ya kunna, ya cire rigar jikinsa ya dago daga jikin tasa kujerar ya kwanto a ta Maleek ya fara sumbantarsa, yana shafa jikinsa.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un”

Maleek ya fada jin wani bakon yanayi da be taba jin irinsa ba, ya daga idonsa daker ya sauke su cikin na saurayin bakinsa ke hade da na shi, hancinsu yana gogar juna.

“Mi... Mi... Miye... Ha.. Ka...”

Ya furta daker sai kuma bachi ya sake yin gaba da shi, har saurayin yayi abun da zai yi ya gama ya fita motar ya zagaya side din da Maleek yake ya ciro wayar Maleek ya kashe ya maida masa aljihunsa sannan ya rufe motar yayi tafiyarsar.
Haka Maleek yayi ta kwasar bachi a motar tun karfe biyar na yamma har garin Allah ya waye. Shi ma saboda rana ta fara haska idonsa ne motsawa ya fara yi a hankali yana jin yadda jikinsa yayi tsami a ko'ina kamar ba na shi ba, wutansa sai ciwo yake har ya haifar masa da tari.

“Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un miya faru ne”

Ya tambaye kansa yana murza idonsa wannan lokacin ciwo suke masa tsakanin jiya da suke masa nauyi, gaba daya ya kasa tuna abun da ya faru, gashi ya gagara gane inda yake.

“Ya salam”

Ya fada kansa ya sake maida idon ya rufe ya dauki tsawon lokaci a haka sannan ya bude idon cikin rashin kuzari ya mika hannunsa ya bude motar ya fita ya tofar da yawun bakinsa yana karewa gurin kallo.

“Ina ne nan kuma? Miya kawo ni nan?”

Ya sake risinawa cikin motar ya dauko gorar ruwa dake cikin motar ya wanke idonsa ya kurkure bakinsa sannan ya saka hannu ya lalabo wayarsa ya kunna kamar jiran yake a kunne wayar sai ga kiran mahaifiyarsa Hajiya Zahra ya shigo a take.

“Hello”

“Maleek kana ina? Ina kake? Me ya same ka?”

Yayi shiru kamar mai tunanin abun da zai fada, ya daga gorar ruwan ya cika bakinsa ya hade.

“Miya faru?”

“Kamar ya me ya faru? Tun jiya baka dawo gida ba kuma wayoyinka a kashe ko'ina na bincika ba a ganka ba”

“Yeah...”

Ya fada yana tuna abun da ya faru, jiya yana tare da abokansa ya fara jin bachi, ya shiga motarsa har wani saurayi ya zo ya taimaka masa.... Kamar walkiya haka komai ya dawo masa a akwakwalwa lokaci daya ya tuna komai da sauri ya jefar da ruwan dake hannunsa.

“Who's that guy?”

Ya tambaya a yayinda wayar take a kunnesa.

“Waye?”

Ummi ta yi zaton sa ita yake, sai ya kashe wayar ya shiga motarsa cikin wani irin bachin rai da bakin ciki marar misaltuwa, kam yayi ma motar key kira ya sake shigowa a wayarsa, daga Abiey har na Kannensa da abokansa be daga ko daya ba, tukin kawai yake yana tuna yadda saurayin yayi kissing dinsa kamar a mafarki. Ransa be kara baci ba har sai da ya isa gidansu yana faka motarsa mahaifiyarsa da kanensa suka fito da sauri sannan mahaifinsa dake bayansu, kallo daya yayi musu ya fahimcin suna cikin tashin hankalin rashinsa musamman ma mahaifiyarsa da har lokacin kuka take, ta matsa kusa da shi sosai kamar ta rumgume shi sai dai babu dama domin danta baya son haka.

“Maleek ina ka shiga? Ka daga mana hankali miyasa ka kashe wayarka?”

Kamin ya amsa tambayar Ummi Mahmood ya jefo masa tasa tambayar.

“Ina ka shiga Maleek? Jiya babu wanda yayi bachi a gidan nan kuma an bincika ko'ina ba a ganka ba”

Ya dauke idonsa daga kallon kanensa ya kalli Abiey da shi ma tambayar yake masa.

“Ina ka shiga Maleek?”

Ya amsa kiran wayar da Abdull yake masa.

“Abdull ina gida”

Ya sauke wayar ba tare da ya jira abun da abokinsa zai tambaya ba. Sannan ya kalli mahaifiyarsa dake ta zubar da hawaye tausayinta ya kama shi.

“Ummi lafiyata kalau”

“Ina ka shiga?”

“Ban sani ba, na fito daga inda muke zama zan dawo gida na kwanta sai bachi ya dauke ni”

Cikin kallon rashin fahimta Abiey ya ce.

“Shigo ciki”

A tare suka dunguma gaba daya suka shiga cikin falon, kowa ya samu guri ya zauna sai kallon Maleek suke da idonsa suke da ja har lokacin ga wani ciwon kai da yake jin yana son saka shi gaba. Ya fara shimfida musu labari tun daga fitarsa gida har zuwa isarsa Q-town da abubuwan da suka faru be boye komai ba ciki har da kissing dinsa da Guy yayi.

“Maybe wani abu aka saka maka a drinks din”

Mahmood ya fada Maleek ya kalleshi yana daga masa kai.

“Ni ma abun da nake tunani kenan, kuma shi ma wannan saurayin turo shi aka yi”

“Wa zai maka wannan?”

“Wannan kuma sai na natsu ko kuma wani za'ayi ma aka yi kuskure”

“Ko dai abokin da kuka samu matsala da shi ne?”

Abiey ya tambayar yana kallon wayar Maleek dake ringing.

“Karka daga wayar nan, bari mu gama magana”

Maleek ya aje wayar gefe ya shafa kansa.

“Ba na jin zai yi haka”

“Wani lokacin wanda baka tunani shi zai aikata maka abu, wata kila kai baka dauki abun da zafi ba amman shi ya dauka kuma gashi har ka ce wani yayi kissing dinka wannan abun ba a saba da shi ba, kuma baka san manufarsa ta yin haka ba”

Cewar Namra cike da damuwa.

“Siyasa ai ba zamu kyale ko waye ba, musamman yadda ya tashi hankalinmu a gidan nan jiya, a inda ya kaika ya aje wani abu zai iya samunka a can din ma, kuma duk wanda zai maka wannan abun zai iya silar rasa rayuwarka, dole mu gane ko waye wannan tun daga kan drink din da ka sha”

Abiey ya fada with serious face, Maleek ya kalleshi cikin yanayin dake nuna baya son iyayens su shiga cikin lamarin domin yana jin kamar Ameer ba zai iya masa haka ba, duk kuwa da kasancewar wani bangare na zuciyarsa na raya masa shi din ne.

“Abiey wannan a tsakaninmu ne?”

Hajiya Zahra ta daka matsa tsawa.

“Wani irin a tsakaninku? A tsakaninku wani zai maka haka? Wannan shi yake nuna friends dinka ba mutanen kirki ba ne, su waye ma friends din duk ba mu sani ba, basa zuwa gidan nan sai dai ka je can kana haduwa da su wani guri”

Abiey ya saka hannunsa ya ciro wayarsa dake aljihun jallabiyarsa yayi dialing.

“Duk masu aikin gurin sai an dauresu sai sun fadi wanda ya saka su”

“Abiey kar aja abun nan da nisa kar aje inda ba a so”

Cewar Maleek domin ya fi son a bar maganar a hannunsa.

“Ba za a bari ba, Maleek kuma sai an hukunta yaron nan ko dan gidan uban waye, domin zai iya kashe ka ma”

Ummi ta fada cikin bacin rai, Nimra ta ce.

“And the most annoying part ma Yaya baya iya zama ya fadawa kowa damuwarsa sai dai ya bar abu na cinsa Allah kadai ya san abun da ya faru a tsakaninsu amman be fada ba, gashi abu har ya fara wuce gona da iri”

Kallonta kawai Maleek yayi ya mike tsaye ya nufi hanyar stairs.

“Ja ka a duba lafiyarka, whats if yayi poisoning dinka?”

Ya juyo ya kalli mahaifiyarsa dake maganar.

“Zan je, wanka zan yi na yi sallah tun jiya ban yi magariba ba”

Sannan ya juya ya hau sama yana jin yadda Abiey yake yi ma abokinsa bayanin yadda ďansa ya dawo.

“Ba zan sake bari ya rabi friends dinsa ba, ba mu san su waye yake abota da su ba, ji yadda suka saka shi ko sallah be yi ba, dole ne a hukunta ko waye....”

Wannan karon ma Hajiya Zahra ce take maganar cikin fushi tana jin kamar ace wanda ya aikatawa ďanta haka yana a gabanta.

Continue Reading

You'll Also Like

1.6M 66.4K 190
Original author: Signing At The Moon Original publisher: flying lines Original Translator: Guy Gone Bad ๐ŸšซComplete translation ๐Ÿšซ ๐Ÿšซ Offline and free...
67.3K 1.6K 38
โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€ you got me down on my knees it's getting harder to breathe out . . . โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€โ”€ ๐‘ฐ๐‘ต ๐‘พ๐‘ฏ๐‘ฐ๐‘ช๐‘ฏ . . . ๐œ๐ก๐ซ๐ข๐ฌ ๐ฌ๐ญ๐ฎ๐ซ๐ง๐ข๐จ๐ฅ๐จ ha...
38.4K 4K 13
Maybe sometimes love needs a second chance because it was not ready for the first time ๐Ÿฅ€... Ekansh Malohtra a youngest buisness tycoon (28).. A man...
623K 20.7K 169
The young lady from the Xue family was talented and beautiful, and married the dream husband at the age of 16. They had a loving and harmonious relat...