ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

By KhamisSulaiman

180 16 1

Labarin wata yarinya ne da take bata tun bata da hankali, iyayenta basu tashi ganinta ba sai da ta zama budur... More

Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10

Chapter 6

10 1 0
By KhamisSulaiman

         ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

*Daga Kundin✍️📚✍️
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008
Phone no: +2348085871223

                   *page 11 & 12*

       
    ' Kwanci tashi asarar mai rai inji bahaushe' yau kusan shekaru biyu da kama aikin Alhaji Inuwa, Ya kama daya daga cikin ma'aikatansa da al'mundahana don haka sai ya hada taro na  duk ma'aikatan, aka bawa wanda yayi ha'incin damar yayi bayani, amma duk cikin jawabin nasa zancen banza ne da surutun wofi babu wani abin kamawa, don haka sai Alhaji Inuwa ya fara yi masa masifa.

         Alhaji Inuwa cikin bacin rai yace "Zancen banza zancen wofi! wallahi in har baka fito da kudin aikin nan ba, ko kuma baka karasa aikin ba sai na daureka!"

         Ma'aikaci yace "Afuwa ranka ya dade za'a karasa cikin ikon Allah"

         Alhaji Inuwa a fusace yace "To wallahi na baka mako uku matukar baka gama ba sai na sassaba maka"

         Ma'aikaci yayi shiru ya sunkuyar da kai kasa yana nazari.

         Alhaji Inuwa ya kalli sauran ma'aikatan yace "Kuma ina so wannan ya zama izina a gareku, domin duk wanda ya ha'inci gwamnati sai gwamnati taga karshen zalincinsa" da haka ya tashi ya bar wajen taron.

         ***           ***           ***          ***

        Bayan Alhaji Inuwa ya koma gida da daddare bayan sallar isha'i suna cikin farin ciki da annushuwa tare da Hajiya Sailuba da Aisha.

          Alhaji Inuwa ya kalli Aisha, yace "Ummina kina kula kuwa a makaranta idan ana koya muku karatu?"

          Aisha tana masa dariya tace "Tambayi Aunty ka ji labari Daddy"

         Alhaji ya bata rai yace "Wane irin na tambayi auntinki sai kace tare kuke zuwa makarantar, ke dai kice ba za ki gaya min ba, to shikenan ba ruwana dake!"

          Aisha ta bata rai tace "Yi hakuri don Allah Daddy zan gaya maka kar kayi fushi dani!"

          Alhaji Inuwa yayi murmushi "To fada min ina jinki 'yar lele"

          Aisha tana murmushi tace "Daddyna ka hakura? sai ka hakura zan gaya maka!"

          Hajiya Sailuba tana tayi musu dariya.

           Alhaji Inuwa yayi dariya yace "To na hakura fada min"

           Aisha tace "Daddy ina da kokari sosai, Uncle dinmu ma yace a text din da mukayi ni kadaice naci 60 marks, haka ma Aunty dinmu ta makaranta tace mu uku ne mukaci homework da tayi mana"

           Alhaji Inuwa yana murna yace "Ummina ashe kina da kokari sosai, to ki kara kokari kinji ki dinga zuwa ta daya"

           Hajiya Sailuba tace "Ai gaskiya  Ummi tana da kokari sosai tace min likita ma take so ta zama, ko?"

           Aisha ta gyada kai tace "Kuma ance za'a gidan radio da television da mutum ashirin har dani a ciki"

           Alhaji Inuwa cikin farin ciki yace "Kaiii! naji dadi bari in an jima zamu kai ki wurin shakatawa da gidan tarihi da gidan zoo ki sha kallo kiji dadi ko?"

            Aisha ta gyada kai tana murna tace "Daddy na gode kema Aunty na gode"

        Haka kuwa aka yi washegari suka shirya suka he je gurin shakatawa mai dauke da kujeru da tebura da kayan ciye ciye da shaye shaye, sannan ga kayan wasan yara a gefe iri iri, daga nan suka wuce gidan tarihi su je dakin kayan tarihi suna ta ganin abubuwa suna dariya, sannan suje gidan zoo suna ta kallon namun daji suna nunawa Aisha, basu koma gida ba sai dare.

         Bayan kwana biyu suna zaune a dining room suna breakfast sai Alhaji Inuwa ya kalli agogo yaga karfe takwas saura minti takwas.

           Alhaji Inuwa ya zare ido cikin mamaki yace "Ummina lokacin makaranta yayi, tashi ki kira driver yazo ku tafi"

           Aisha cikin shagwaba tana sanye da uniform din makaranta tace "Gaskiya daddy yau kaine zaka kaini school"

           Alhaji Inuwa tace "Kinga fa kin kusa makara, ni kuma yau muna da meeting karfe takwas gara ki hakura drivernki ya kai ki kurum"

            Aisha cikin shagwaba tayi kamar zatayi kuka tace "Ni gaskiya kaine zaka kaini ko kuma in fasa zuwa inyi ta kuka" sai ta nannarke ta fara kuka.

            Alhaji Inuwa yace "Muje in kaiki karki soma yi mana kuka" sai su tashi su nufi kofar fita Aisha tana murna, sai da suka je daf da kofar fita ta dagowa Hajiya Sailuba hannu sannan su fice.

         Suna tafiya a mota Aisha tana tayi masa hira har suje bakin gate din makarantar sannan Aisha ta bude motar ta fita tana dagawa Alhaji Inuwa hannu har ta shige cikin makarantar da gudunta, shi kuma ya jinjina kai cikin shauki da kaunar 'yar tasa sannan yaja motar yayi gaba.

           
              WAYE ALHAJI INUWA ?

       Muhammadu Inuwa shine ainihin sunansa, dana ne a wajen Alaramma Malam Muhammadu Bello malamin soro ne mutum ne shi mai ilimin addini ne sosai, ya tsufa kuma ya tara 'ya'yaye da jikoki, matansa hudu 'ya'yansa talatin da takwas da tarin jikoki.

         Duk cikin 'ya'yansa babu wanda yayi ilimin boko mai zurfi kamar Alhaji Inuwa don har degree biyu gare shi wato masters, daga bisani kuma ya shiga harkar siyasa, Allah ya bashi sa'a yayi chairman din karamar hukumarsu ta Dala har kaso biyu tsawon shekara takwas kenan, ya rike mukamin sakataren gwamnatin jiha, kuma yayi dan majalisar jiha.

        Hajiya Sailuba matar Alhaji Inuwa 'yar uwarsa ce don da uwarta da uwarsa uwarsu daya ubansu daya a takaice dai auren zumunci suka yi tun bashi da komai har Allah ya azurtashi. Babban abinda yake ci musu tuwo a kwarya shine matsalar rashin haihuwa kuma sun ki zuwa asibiti a ga waye mai matsalar wai don kada wanda yake da matsalar yaji rashin jin dadi a ransa a haka suka zauna suka mika komai ga Allah, har a karshe Allah ya hadasu da Aisha.

CONTINUES TO STORY

        A can asibiti cikin dakin jinya Rahima tana kwance bisa gadon jinya na asibitin, Rahina da Rahila suna kusa da ita.

          Rahima ta juyo ta kalle su tace "Aunty kun ga abinda nake gaya muku ko yarinyar nan taki yarda dani a matsayin uwar data haifeta, dama kunga ai nayi tunanin haka ko su mutanen suki yarda ko ita 'yar!"

          Rahina cikin yanayin tausayawa tace "Komai nisan jifan kasa zai fado ai ba'a canjawa tuwo suna, in dai ke kika haifeta komai daren dadewa zata dawo gareki"

          Rahima ta girgiza kai tace "Kayya! abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, kin san ance juma'ar daza tai kyau tun daga laraba ake ganeta, Aisha ba zata yarda ba"

          Rahila ta girgiza kai yace "Ai naka sai naka Rahima, jini jini ne akwai wani sirri da Allah ya boye a tsakanin iyaye da 'ya'yaye"

      Kawai sai Alhaji Inuwa da Hajiya Sailuba su shigo tare da Aisha, su shiga da sallama.

         Rahima ta kalli bakin kofar inda taji sallamar, sai tagansu, Rahina da Rahila su amsa musu sallama, Aisha ta tafi da gudu ta rungume Rahima tana kuka.

         Hajiya Sailuba ta karasa kusa dasu tace "Ya mai jikin?"

         Rahina da Rahila suce "Da sauki"

         Hajiya Sailuba ta jinjina kai tana kallon Rahima dake kwance Aisha a jikinta, tace "Allah ya kara sauki"

          Rahina da Rahila suce "Amin amin" su fada suna kallon Rahima da Aisha.

          Aisha tana kuka rike da Rahima tace "Ummana ki yafe min, ni na saki a wannan halin da kike ciki, ban san kece mahaifiyata ba shi yasa har haka ta faru, ki yafe min ko na samu saukin wannan tashin hankalin da nake ciki!"

          Rahima itama tana kuka ta rike hannun Aisha, tace "Aisha na yafe miki, dama ni ban rike ki da komai ba!"

          Sai Alhaji Ahmed da Malam Buba su shigo cikin dakin da sallamarsu Alhaji Ahmed dake tsaye a bakin kofa ya amsa musu suyi musabaha.

           Alhaji Ahmed yace "Har ka dawo?"

           Alhaji Inuwa yace "Na dawo"

           Aisha ta zo gaban Alhaji Ahmed ta tsuguna tace "Abba ka yafe min abinda nayi muku!"

           Alhaji Ahmed cikin yanayin tausayawa ya girgiza kai yace "Ba kiyi mana komai ba Aisha, duk abinda kika yi baki da laifi, gaskiyarki kika fada"

           Aisha cikin yanayin kuka tace "Abba ni dai kace ka yafe min don Allah!"

           Alhaji Ahmed yace "Na yafe miki Aisha ki kwantar da hankalinki ki daina kuka"

           Da likita ya zo ya dubata yaga babu wata matsala sai ya sallame su, suka koma gidan Alhaji Inuwa gaba dayan su anan suka wuni. Da yamma Alhaji Ahmed da Alhaji Inuwa suna zaune a harabar gidan suna hira su biyu a lokacin Malam Buba ya tafi gida saboda 'yan makaranta.

       Alhaji Ahmed ya kalli Alhaji Inuwa, yace "Alhaji zamu tafi da Aisha can gidan mu na Kaduna, zatayi sati biyu sai ta dawo ta cigaba da zama anan har lokacin da za'ayi mata aure"

        Alhaji Inuwa ya jinjina kai yace "Ai ba komai zata iya fin haka ma in kuna bukata"

        Alhaji Ahmed ya girgiza kai yace "A'a, sati biyun ma ya isa don ina ganin kamar zata fi sakewa anan, don tafi sabawa da nan, kasan ance sabo tirken wawa"

          Alhaji Inuwa ya jinjina kai yace "To shikenan Allah ya kaimu"

         Alhaji Ahmed yace "Amin summa Amin"

          Alhaji Inuwa ya karkata ya kalli Alhaji Ahmed, yace "Amma Alhaji Ahmed wani hanzari ba gudu ba, batun aikin ta fa?"

          Alhaji Ahmed yace "Ehhhh! to haka ne, yanzu ya kake ganin za'ayi?"
  
          Alhaji Inuwa yace "Ina ganin da a bari a sanar a can asibitin sannan sai ku tafi, mamallakin asibitin abokina ne tare muka taso unguwar mu daya, nasan idan na sanar dashi halin da ake ciki ba zai ki yarda ba"

          Alhaji Ahmed yace "Ba matsala ai, idan aka sanar sai mu tafi"

_____________

INDIA

          A makarantar aikin likitanci ta All India Institute of Medical Science dake kasar India a garin New Delhi kuwa dalibai ne cike suna ta murnar graduation dinsu cikinsu har da Salman da Suhail wadanda su biyun sun kasance 'yan Nigeria ne.

         Bayan gama shagali suka zauna a gidan Sameera su takwas suna wani shagalin na musamman da yake group ne dasu a makarantar su takwas Salman, Suhail, Azan, Aman, Raj, Pooja, Priya da kuma Sameera. Sameera ce mai masaukin baki don haka ta musu drinks suna sha cikin nishadi suna hira cikin harshen turanci.

         "Yanzu mun gama karatu kowa zai koma garinsu wadanda ba 'yan kasar nan ba zasu koma kasarsu, to ina rokon kowannen mu da ya rike zumunci kada mu manta da juna ko don zaman amanar da mukayi a makaranta" Sameera ce tayi wannan jawabi.

         "Ai na bude wani sabon group a Whatsapp na saka kowa dake nan, ta haka zamu dinga gaisawa akan kari sannan mu san halin da kowanne dayanmu yake ciki" Aman ne yace haka.

         Priya ta kalli Salman, tace "Sweetheart yanzu fa kasar nan zaku bari ko? ka tafi ka barni!"

         Salman yace "Ni ba wai tafiyar bama, kin san kona tafi ai muna tare, zamu dinga waya calls & chats idan muna son ganin juna muyi video call ko muyi Skype"

         Priya tace "To kana da wata damuwa ne"

         Salman yace "A'a, kawai dai ina son kafin na bar kasar nan na dan yawata a kasar nan naje yawo wata jihar"

        "Wane gari kake son zuwa?" Azan ya tambayeshi.

         "Ni kaina ban san inda zanje ba, kawai na fada muku ne don ku bani shawarar naje waje kaza, ina son wajen da naje zai birgeni zai bani sha'awa, zanji dadin zuwa na kuma ababan tarihi"

           Pooja tace "Salman kaje Mumbai mana"

           Aman yace "Haba ai gara ma yaje Kurnool"

           Priya tayi farat tace "A'a Kurnool akwai rikicin fada da gaba"

           "To kawai kaje Jaipur" Pooja ta sake fada.

           Sameera tace "Ko kuma yaje Rajasthan"

           "Rajasthan akwai zafi" Raj ya fada.

            "To ai kun ki tsayar min da wajen zuwa" Salman ya fada yana dakatar dasu.

           Suyi shiru suna kallonsa, Salman yace "Ni da nafi son naje jihar da musulmai suka fi yawa"

           Azan yayi farat yace "To kaje Kashmir kawai"

           Priya ta girgiza masa kai tace "Gaskiya kada kaje Kashmir kaji sweet saboda sanyi yayi yawa snow ce fa take zuba, kaga kai kuma baka saba ba"

       "To kawai muje Goa, tunda naga suma 'yan kasar suna son zuwa hutu ko shakatawa can din" Suhail ne yace haka.

          Salman ya kalli Priya, yace "Ya kika gani baby?"

          Priya tace "Kawai muje Goa, don nima zanje ba zan bari ka tafi kai kadai ba"

          Salman yace "Dama ai bani kadai zanje ba, har da Suhail"

           Bayan shagalin ya watse kowa ya tafi zuwa nasu gidan, suma Salman da Suhail suka koma masaukinsu, suka kuma kama shirye shiryen tafiya Goa. Bayan kwana biyu kuwa suka kama hanya suka nufi Goa suka je tashar jirgin kasa suka hau suka tafi, da suka isa  basu tsaya ko'ina sai hotel suka kama daki suka zauna a ranar babu inda suka je zama sukayi suka huta, sai washegari tukunna sannan suka fita waje suka fara yawo, sune zuwa bakin Beach, sune zuwa Club, sune zuwa Garden da Park da kuma zuwa gidan zoo da gidan tarihi da yawo a tituna da unguwanni na gari kullum da inda zasu.

          Kwanan su shida a garin wata rana sun dawo daga yawon nasu daidai lokacin sallar la'asar, sun zo giftawa ta wani masallaci ana kiran sallah, sai suka tsaya suka ce da Priya ta wuce masaukinsu su zasu tsaya suyi sallah, ta wuce ta tafi da kayansu su kuma suka karasa masallacin sukayi alwala sukayi nafilla kafin a zo ayi jam'i, bayan an idar da sallar sun fito sai suka kama hanya suna tafiya sun zo daidai kan wani layi sai suka sami irin kujerun nan na bakin hanya suka zauna suna hira wadda ta shafe su. Suna nan zaune a wajen kawai sai wasu motoci guda biyu kirar Mercedes Benz sun sa luxury car a tsakiya, wani babban mutum ne ya fito daga cikin motar ta kofar dake barin da su Salman suke, ta barin dake can kuwa wata katotuwar budurwa ce mummuna ta fito daga ciki, kamar su daya da mutumin da ya fara fitowa da gani 'yarsa ce, tana zagayowa ta barin da su Salman suke kawai sai ta tsaya tana kallon Salman ta kura masa ido.

         Mutumin yana kallon budurwar cikin mamaki, da harshen turanci yace da ita "Muje mana Lakshmi, kin tsaya kina kallon wani ko kin sanshi ne?"

         Lakshmi tace "Baba wannan yayi daidai da irin namijin dana bada cigiya a social media, don haka ayi gaggawar sanarwa cewa ba sai anyi taron samari na zaba ba, na samu wani a bagas!"

           Mamaki ne ya kama Salman da Suhail suka kalli juna, sannan suka kalli wadannan indiyawan cikin rashin fahimtar inda maganarsu ta dosa.

                        Tirkashi!

Kada ku manta da:
           
>Like
>Share
>Follow
>Comments
          
   
                         📖............. ✍️
                      *Alkhamis KSA*

Continue Reading

You'll Also Like

231K 7.3K 55
ရိပ်ချေ ကိုကြီးကိုချစ်တယ် ။ ကိုကြီးလည်း ရိပ်ချေကိုချစ်လာရင် ဖွင့်ပြောပေးနော် ။ နွေဦးရိပ်ချေ 🍀 နေမခန်း & နွေဦးရိပ်ခ...
257K 7.6K 45
စဝ်ခွန်နောင်= မင်းလူသတ်ရင် ကိုယ်ကအလောင်းဖျောက်ပေးမယ့်မဲ့ကောင်ပါ baby Gumkino =ကျွန်မက ပန်းကိုင်ရတာထပ် gunကိုင်ရတာပိုသဘောကျတဲ့မိန်းကလေးတစ်ယောက်မို့ ရှ...
5.5M 229K 68
The story of Abeer Singh Rathore and Chandni Sharma continue.............. when Destiny bond two strangers in holy bond accidentally ❣️ Cover credit...
3.4M 38.8K 31
Diana is an 18 year old girl about to start her senior year until she bumps into a woman at the bookstore who has quite the personality. The woman ta...