ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

By KhamisSulaiman

160 16 1

Labarin wata yarinya ne da take bata tun bata da hankali, iyayenta basu tashi ganinta ba sai da ta zama budur... More

Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10

Chapter 4

10 1 0
By KhamisSulaiman

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

*Daga Kundin ✍️📚✍️
*Alkhamis KSA*
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008
Phone no: +2348085871223

*page 7 & 8*

Suna cikin tafiya a cikin mota Aisha tana zaune a jikin Alhaji Inuwa sun nufi gidan mai unguwar Madabo.

Alhaji ya kalli Aisha, yace "Yaya sunanki?"

Aisha tana shashshekar kuka tace "Sunana Aisha"

Alhaji Inuwa yayi murmushi yace "Ashe ma sunan mommy nane dake? kiyi hakuri ki daina kuka!"

Aisha ta gyada kanta tana share ido.

Alhaji Inuwa ya sake dubanta yace "Yaya sunan babanki?"

Aisha tace "Abba"

Alhaji Inuwa yana kallonta yace "Yaya sunan mamanki?"

Aisha tace "Umma"

Alhaji Inuwa cikin yanayin tausayawa yace "Baki san sunansu na gaskiya ba?"

Aisha idonta ya ciko da hawaye ta gyada masa kai.

Alhaji Inuwa yana kara tausayinta yace "To ina ne unguwarku, ya sunan unguwar?"

Aisha ta kalleshi tana hawaye tace "Ban sani ba nima!"

Alhaji Inuwa yana ta mamakinta yace "Baki san sunan unguwarku ba ma?"

Aisha ta sake gyada kai.

Alhaji Inuwa ya dafa kanta yace "To kiyi shiru ki daina kukan, Insha Allahu zakiga iyayenki, kinji! ki daina kukan haka"

Suna tafiya har su kai bakin layin sai suyi Parking a bakin titi sannan su sauko daga motar su shiga lungun su nufi gidan.

*** *** *** ***

A gidan Rahila kuwa ana ta hidindimun aikin abincin biki, Rahima tana zaune tana yanka alayyahu, Rahina kuma tana kusa da ita tana ferayar kabewa, suyi suna hira. Rahila kuma ita da wata mata makwabciyar ta suna ta tsintar shinkafa, can gefe kuma wata tsohuwa ce daga dangin mijin Rahila take tankaden garin tuwo, sai Salisu da Magaji su shigo daga waje suna rike da dinkin da sukaje karbowa.

Rahima ta daga kai ta kallesu tana cewa "Ku ina kuma Aishar ku ka barota, ko tana waje ne?"

Salisu yace "Bamu ganta ba, tun a hanya ta bace mana"

Rahima ta mike tsaye a razane tana cewa "A daidai ina ne ta bace muku?"

Magaji yace "Muma bamu sani ba, mu dai mun duba kawai bamu ganta ba"

Rahima ta jawo mayafinta akan igiya tayi hanyar kofar fita waje da saurinta.

Rahina itama ta mike tace mata "Tsaya Rahima mu tafi in rakaki kada ayi biyu kinga kin dade rabonki da garin nan kada ayi biyu babu"

Sai Rahina ta dauko nata mayafin su saka yaran a gaba su fita, su bar su Rahila anan suna ta salati da sallallami tare da addu'ar Allah ya bayana ta.

*** *** *** ***

Alhaji Inuwa da Aisha da jama'arsa su karasa gidan mai unguwa, su sameshi a zaune akan tabarma shi kadai, bayan sun gaisa.

Mai unguwa cikin kaguwa yace "Lafiya kuwa?"

Alhaji Inuwa yace "Dama wannan yarinyar ce ta bata, kuma anyi mata tambayoyi daidai misali amma cikin ikon Allah ba'a gano iyayenta ba ko inda take, to shine naga ya dace in kawota gareku tunda kune manya ku kuka san hanyar da zaku bi wajen gano mata iyayenta"

Mai unguwa ya jinjina kai yace "Hakan yana da kyau Honorable, Allah ya bada abinda ake nema, ai ka kyauta ba kowanne dan takara ne zaiyi irin wannan abu ba" ya kalli Aisha yayi mata tambayoyi kamar yadda Alhaji Inuwa yayi mata, kuma ta bashi amsa irin yadda ta cewa Alhaji Inuwa.

Mai unguwa ya kalli Alhaji Inuwa, yace "Honorable ina neman wata alfarma guda a gurinka"

Alhaji Inuwa yace "Ba matsala, fadi ai ba komai"

Mai unguwa yayi gyaran murya yace "Ina so ka tafi da yarinyar nan gidanka, ka kaiwa matarka ta riketa amana kafin Allah yasa a ga iyayenta sai in sa a rako su karbi abarsu, idan kuma ba'a samu iyayenta ba sai ku riketa a matsayin diyarku har lokacin da zai sa tayi aure"

Alhaji Inuwa cikin mamaki yace "Yallabai haka tana yiwuwa kuwa?"

Mai unguwa yace "Eh mana, nawa akai!"

Alhaji Inuwa yace "To in dai haka ne wannan ai ba komai babu matsala zamu riketa da amana"

Mai unguwa yace "Nima abinda yasa nayi wannan tunanin, naga yarinyar daga ganin kasan daga gidan masu hali take, kaga idan aka ce zata zauna a gida irin namu na wani lokaci zata takura tunda bata saba ba, amma kai idan gidanka ne zata sakata ta wala a cikin jin dadi da kwanciyar hankali da samun kulawa"

Alhaji Inuwa yayi murmushi yace "Ah ai shikenan ba komai mu zamu wuce" yasa hannu a aljihu ya zaro kudi ya mikawa mai unguwa, yace "Ga dan wannan a sayi ko gishiri ne ayi miya"

Mai unguwa ya karba cikin farin ciki yace "Allah ya saka da alkhairi kuma Allah ya bada abinda ake nema sannan Allah ya baka ikon yarinyar nan da gaskiya da amana"

Alhaji Inuwa shima yana farin ciki yace "Amin summa Amin"

Ya dauki Aisha su karasa gidansu su gaisa da iyayensa sannan ya basu labarin yadda aka yi ya hadu da Aisha da yadda mai unguwa yace, suyi masa fatan alkhairi tare da addu'ar Allah ya bayyana iyayenta, daga nan yaje yayi sallama dasu ya dauki Aisha a motarsa tare da jama'arsa su nufi gidansa, suna tafiya yana farin cikin samun 'ya a gefe daya kuma yana tunanin yadda Sailuba zata kalli hakan.

*** *** *** ***

Rahima da Rahina suna ta tafiya suna dube dube sun saka Magaji da Salisu a gaba su shiga lungun nan su fita su filla wancan lungun, Rahima tana ta sharbar hawaye.

Rahina tace da ita "Ki daina kuka Rahima in Allah ya yarda za'a ganta ki kwantar da hankali!"

Rahima cikin kuka tace "Wallahi har ma na rasa abinda zance, da a ce Abbanta ya sani idan yazo bala'in da zai yi sai yayi kamar ya dakeni, Allah dai yasa a ganta kafin yazo daurin aure gobe"

Rahina tace "Amin Allah ya bayyana ta, amma dai ki daina daga hankalinki"

Rahima tana kallon Rahina cikin mamaki, tace "Dole ne na daga hankalina! da a ce Aisha mutuwa tayi dole ne na hakura da ita saboda nasan ta koma ga mahaliccinta, wanda ya bani ita ya fini sonta, to amma yanzu fa bata tayi ban kuma san hannun wanda zata fada ba kuma ban san halin da take ciki ba, kinga kuwa ai dole na daga hankalina!"

Rahina cikin tausayawa tace "Kaddara ta riga fata kuma yarda da kaddara babban imani ne, shi kuma hakuri haske ne"

Rahima ta girgiza tace "Ke uwa ce kuma kin san raba da da mahaifi sai Allah, shekara nawa muna tare da 'yar amma yanzu rana daya tsaka na nemeta na rasa!"

Rahina tace "Hakurin dai shine, muje idan muka yayyawata bamu ganta ba sai muje gidan unguwarmu ko an ganta an kaita"

Suyi ta tafiya lungu da sako suna yawo kuma suna tambayar duk wanda suka gani ko ya ganta, amma basu ganta ba basu ga wanda ya ganta ba, don haka sai juya suka koma suka nufi gidan mai unguwar kofar mazugal.

*** *** *** ***

Hajiya Sailuba tana zaune a hakimce akan doguwar kujera a falo tana kallon film din wasan hausa sai Alhaji Inuwa ya shigo yana rike da hannun Aisha.

Alhaji Inuwa yayi sallama "Assalamu Alaikum"

Hajiya Sailuba ta amsa "Amin wa alaikumus salam"

Alhaji Inuwa yayi murmushi ya zauna a kusa da ita yace "Sannu dai uwar gida ran gida in ba ke ba gida"

Hajiya Sailuba tayi murmushi itama tace "Yauwa sannu da zuwa mai gidana abin alfahari na" ta maida kallo ga Aisha, tace "A ina ka samo wannan kyakkyawar yarinya haka kamar ba 'yar hausawa ba?"

Alhaji Inuwa yayi murmushi ya dafa kan Aisha yace "Tsintar ta nayi"

Hajiya Sailuba cikin yanayin dan tsoro tsoro tace "A ina kuma?"

Alhaji Inuwa yace "Kinga dauketa kuje kiyi mata wanka ki bata abinci taci, sai kizo kiji labari"

Hajiya Sailuba tace "To shikenan" sai ta kama hannun Aisha su shige ciki.

Jimawa kadan Hajiya Sailuba ta dawo ta zauna kusa da Alhaji Inuwa, ta kalleshi cikin yanayin tambaya tace "Alhaji, yarinyar nan kamar tana cikin damuwa ko?"

Alhaji Inuwa ya dan yi mata murmushi yace "Haka ne tana cikin damuwa, bata tayi kuma an rasa iyayenta, shine na kaita gidan mai unguwarmu da yayi mata 'yan tambayoyi, wanda ta sani ta bashi amsa, wanda bata sani ba tace bata sani ba, to sai yace in taho da ita nan gidan kafin Allah yasa a ga iyayenta sai ya rakosu su karbi abarsu. Idan kuma ba'a samu iyayenta ba yace sai mu riketa ta zama diyarmu har karshen rayuwarmu"

Hajiya Sailuba tana ta kallonsa cikin mamaki tunda ya fara zancen, tace "Ai shikenan Allah ya bamu 'ya, Allah ya bamu ikon riketa da gaskiya da amana"

Alhaji Inuwa yayi murmushi yace ''Dama muna tafiya ina ta tunanin Idan mun zo ko za ki amince ko baza ki amince ba''

Hajiya Sailuba tace'' Haba! kaima ai ko ban fada maka ba ai kasan dole ne na karba, saboda mai neman hatsi ne zaiyi tuwo kaga sai ya kai nika yayi tankade ya hura wuta, to sai kuma ya samu tuwon, kaga ci ne kawai ya rage masa, ya huta da duk wata wahala, kaga ai abin nema ya samu wai matar falke ta haifi jaki''

Alhaji Inuwa yayi dariya yace ''Faduwa tazo daidai da zama, sai dai muce Allah ya bamu ikon riketa''

Daga nan sai su cigaba da wata hirar ta daban, can bayan kamar minti talatin sai ga Aisha ta fito daga daki tazo kusa dasu ta zauna a kasa.

Alhaji Inuwa yayi mata murmushi yace "Ummina har kin tashi"

Aisha ta gyada kai.

Alhaji Inuwa ya kama hannunta ya jawo ta kusa dashi ya zauna da ita yace "Ki kwantar da hankalinki nasa ayi cigaba a gidan rediyo da talabijin da jarida insha Allahu za'a ga iyayenki"

Aisha ta kalleshi ta gyada kai yace "To"

Alhaji Inuwa ya dubeta cikin yanayin tambaya yace "Ummina ya aka yi kika bata, ko yawo kika fito"

Aisha ta girgiza kai.

Alhaji Inuwa cikin mamaki yace "To ya akai kika bata?"

Aisha sai ta fashe da kuka mai ban tausayi tace "Aikenmu aka yi shine wadanda aka aikemu tare suka tafi suka barni!"

Aisha ta cigaba da kuka, su kuma Alhaji Inuwa da Hajiya Sailuba suyi ta rarrashinta har tayi shiru suna sanyaya mata zuciya da dadadan kalamai.

*** *** *** ***

Mai unguwa yana tare da jama'a a kofar gidansa ana ta hira, Rahina da Rahima su karaso kofar gidan.

Rahina tace da Rahima "Kinga mai unguwar a gida amma mu shiga cikin gidan sai mu sa a kira mana shi"

Sai su shiga cikin gidan da sallama.

Rahina tayi sallama "Salamu Alaikum"

Hajiya matar mai unguwa tana zaune a tsakar gida tana sakar hannu ta ulu da kwarashi, ta amsa musu sallama "Amin wa alaikumus salam, sannunku da zuwa" ta jawo tabarma ta shimfida musu.

Rahina da Rahima su zauna akan tabarmar su gaisheta "Hajiya ina wuni"

Hajiya ta amsa cikin fara'a "Lafiya kalau"

Rahina tace "Mun zo wajen mai unguwa ne"

Hajiya tace "Ai yana waje, bari a kira muku shi, Hafizu zo ka kira musu babanku" sai ya fito daga daki yayi waje.

Hajiya tana kallonsu tace "Daga nesa kuke ne? naga kamar kun gaji ne"

Rahina tace "Daga nan bayanku muke wallahi ba wani daga nesa muke ba, wahala ce kawai saboda yawon da mukayi........"

Mai Unguwa ya shigo da sallama "Salamu Alaikum"

Dukkansu su amsa "Amin wa alaikumus salam"

Rahina tace "Ranka ya dade barka da yamma"

Mai unguwa yace "Yauwa sannunku da zuwa" ya jawo wani karamin tirmi ya zauna.

Rahina tace "Ranka ya dade daga nan baya muke gidan marigayi Dauda direba, sunana Rahina wannan kuma kanwata ce sunanta Rahima dukkanmu kannen Rahila ne matar Dauda direba nasan ka santa"

Mai unguwa yace "Farin sani ma kuwa ai Dauda mutumina ne lokacin da yake da rai in dai yana gari bashi da wajen zama sai wajena, Allah ya jikansa"

Rahina ta nuna Rahima, tace "Wannan kanwar tawa a Kaduna suke da zama, sun zo bikin gidan yayar tamu na babbar 'yarta, shine yau aka nemi diyar tata aka rasa, shine muka zo nan ko an kawota ana cigiyar iyayenta"

Mai unguwa yace "Mu dai gaskiya ba'a kawo mana dan kowa ba a yau, ban sani ba ko nan gaba"

Rahima cikin kuka mai ban tausayi tace "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"

Rahina jiki a sanyaye tace "Yanzu mai unguwa ya kake ganin za'ayi? meye shawara?"

Mai unguwa yace "Yanzu ku kwantar da hankalinku ku koma gida mu gani zuwa gobe in an kawota idan nazo daurin aure zan sanar muku"

Rahina tace "To shikenan" sai su tashi suyi sallama dasu su koma gida.

Da gari ya waye da duku duku Alhaji Ahmed ya iso ya kuma tsinci mummunan labari na batan Aisha, suna zaune a dakin Magaji, Alhaji Ahmed da Malam Buba da Rahila da Rahina da Rahima ana ta tattauna maganar jimami, Alhaji Ahmed sai masifa yake yiwa Rahima.

Malam Buba yace "Alhaji Ahmed hakuri kawai zakayi Allah ya bayyana ta"

Alhaji Ahmed cikin fada da fusata yace "Babban abin haushin shine ta san yarinyar nan babu inda ta sani a garin nan, amma ta bari tabi yara aike, kai ko a can kaduna Aisha babu inda take zuwa ballantana kuma a nan!"

Rahina tace "Wallahi Alhaji duk laifina ne! ganin an aiki yaran su karbowa yaya dinkinta shine nace su tafi tare don naga tare suke wasa"

Malam Buba yace da ita "Laifinki ne ma ashe? tunda ke kika turasu"

Rahila tace "Babu fa laifin kowa, kawai jarrabawa ce daga ubangiji, kamata yayi muyi ta addu'a mu yarda da kaddara ba wai mu dinga dorawa wani laifi ba"

Alhaji Ahmed ya rausayar da kai yace "Haka ne Allah ya bayyana cikin sauki"

Malam Buba yace "Yanzu to ya za'ayi wajen nemanta, don fa ba zama zamuyi muyi zuru ba"

Rahina tace "Ai mai unguwa yace mu bari zuwa yau mu gani ko an kawo masa ita"

Malam Buba yace "To Allah yasa ma an kawota gidan nasa"

Kada ku manta da:
>Like
>Share
>Follow
>Comments

📖........... ✍️
*Alkhamis KSA*

Continue Reading

You'll Also Like

588K 48.9K 23
Indian Chronicles Book III My Husband, My Tyrant. When Peace Becomes Suffocation. Jahnvi Khanna has everything in her life, a supporting family, a hi...
453K 26.7K 44
The story continues to unfold, with secrets unraveling and new dangers lurking in the shadows. The Chauhan family must stay united and face the chall...
424K 12.8K 37
The Sokolov brothers are everything most girls want. Intimidating, tall, broody, they are everything to lust after. Not that they... particularly car...
3.7M 291K 96
RANKED #1 CUTE #1 COMEDY-ROMANCE #2 YOUNG ADULT #2 BOLLYWOOD #2 LOVE AT FIRST SIGHT #3 PASSION #7 COMEDY-DRAMA #9 LOVE P.S - Do let me know if you...