ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

By KhamisSulaiman

180 16 1

Labarin wata yarinya ne da take bata tun bata da hankali, iyayenta basu tashi ganinta ba sai da ta zama budur... More

Chapter 1
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10

Chapter 2

23 1 0
By KhamisSulaiman

          ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE

*Daga Kundin ✍️📚✍️
*Alkhamis KSA *
Wattpad: @KhamisSulaiman
Whatsapp: +2348095933008
Phone no: +2348085871223
 

                     *page 3 & 4*

 
    Rahina tana zaune a tsakar gida tayi jigum tana tunani, sai malam Buba ya shigo.

      "Salamu Alaikum"

       Rahina ta mike tsaye tace "Amin wa alaikas salam, dama tun dazu nake jiran shigowarka!"

        Malam Buba  cikin mamaki yace "Lafiya dai ko?"

        Rahina tace "Eh lafiya dai amma ba kalau ba"

        Malam ya zauna itama Rahina ta zauna.

        Malam Buba yana kallon ta cikin yanayin kaguwa yace "Me yake faruwa ne?"

        Rahina ta fuskanceshi tace "Malam dazu da muka je barkar nan a hanyarmu ta dawowa wallahi naga wata yarinya budurwa kamar Aisha 'yar Rahima data bata!"

         Malam Buba cikin mamaki tace "Ya aka yi kika san itace har kika ganeta? yarinyar data bata shekaru goma sha biyar da suka shude!"

         Rahina ta daga murya da karfi tace "Malam wallahi zan iya rantse ma da Allah itace! naga kama da tsagun nan na fuskarmu ni da Rahima da yaya Rahila"

        Malam cikin Al'ajabi yace "To in har haka ne tana iya yuwuwa itace bari na fito daga bandaki na kira Alhaji Ahmed mu tattauna akan maganar koma kawai su zo nan sai muje ayi bincike" sai ya dauki buta ya nufi bandaki.

        Rahina itama ta mike tace "Nima bari na garzaya gidan yaya Rahila na sanar mata" sai ta zari mayafi ta fita.

       
       ***           ***           ***           ***

     Rahila tana zaune a tsakar gida tana tankaden garin tuwo, sai Rahina ta shiga cikin gidan.

      Rahina ta shiga da sallamarta "Salamu Alaikum"

       Rahila ta daga kai ta kalleta tana amsa mata sallamar "Wa Alaikumus salam"

       Rahina ta jawo wani karamin turmi ta zauna jiki a sanyaye tana kallon Rahila, tace "Yaya ina yini"

       Rahila tana mata kallon rashin fahimta, tace "Lafiya kalau! lafiya kuwa na ganki da almurun nan? ko daga unguwa kike?"

       Rahina tace "Eh, daga unguwa nake amma naje ma gida, wani abu ne yake ta min yawo a rai shi yasa nace sai nazo na sanar miki a yau!"

       Rahila cikin mamaki tace "Me yake faruwa ne?"

       Rahina tace "Akwai wata makociyarmu Saliha nasan kin santa gidanta yana kallon gidan Jazila"

       Rahila tace "Eh na ganeta babar dan Amir uban surutu"

       Rahina tace "Ita kuwa, to ita ce babbar 'yarta wadda aka yiwa aure bara ta haihu, sai mukaje barka ni da Jazila dazu dazun nan, bayan mun fito daga gidan mun zo titi, sai Jazila tace na rakata wani supermarket a kusa da  kwanar shiga layin, tace zata siyo madarar nan 'yar nijar wadda ake iloka tace ta layin namu bata da afki, munje zamu shiga supermarket din kenan sai muka hadu da wata yarinya budurwa kamar Aishar Rahima data bata, mukai mukai da yarinyar nan ta tsaya ta sauraremu amma ta ki don haka sai muka bita muka ga inda ta shiga wani gida a tudun yola"

        Rahila tace "Tirkashi! to yanzu ya, za'ayi kenan? kin sanar da Rahima?"

        Rahina tace "Malam dai yace zai yiwa Alhaji Ahmed waya"

        Rahila tace "Eh haka ne sai su zo aje a bincike a gani ko Allah zai sa itace"

        Rahina tace "Haba yaya ai itace ma! ga kamanni Rahima nan da tsagun nan na fuskarmu"

       Rahila tace "To mu dai Allah yasa muji alheri"

       Rahina tace "Amin summa Amin"

       Rahila tace "Ai sai ki tashi ki koma, ko baza kiyi girki ba?"

       Rahina tace "Tazarce nayi na rana dana dare na hade da naga zamu fita gidan barkar nan"

        Rahila tace "Kin huta kuwa"

        Rahina tace "Magaji ba'a dawo daga kasuwa ba?"

        Rahila tace "Bai dawo ba amma nasan a gaf da shigowa yake"

        ***           ***           ***           ***

  
        Alhaji Inuwa ya dawo office Aisha taje wajensa tana shagwaba tana bashi labarin abinda ya faru dazu da ita da yadda aka yi.

        Alhaji Inuwa yace "Ummina kema duk da laifinki, nayi nayi dake a koya miki mota kinki saboda tsabar tsoronki, da kinga da kanki zaki dinga tukawa kina zuwa duk inda kike so kina dawowa, amma saboda tsabar tsoro kinki, yanzu ma gashi kinga mutane kin kama tsoronsu, wannan tsoro naki yayi yawa, ke fa likita ce ana so likita ya zama mai dakakkiyar zuciya ba matsoraci ba"

        Aisha cikin shagwaba tace "Ni dai gaskiya daddy na daina fita waje kawai!"

        Alhaji Inuwa cikin mamaki da zaro ido yace "Because of  what? saboda me zaki daina fita waje? aikin naki fa?"

         Aisha ta fashe da kuka tace "Daddy barayin mutane ne fa?"

        Alhaji Inuwa cikin tattausan kalami yana rarrashinta yace "Ba wai daina fita zakiyi ba Ummina, a kasa ne wajibi ki daina fita nima bana so, tunda ga motarki nan duk inda zaki driver ya ringa kaiki yana zuwa yana dauko ki, amma wataran sai ki taho kice kina sauri bai je da wuri ba, ai dole mutane su dinga biyoki kin san ke kyakkyawa ce beautiful girl mai red skin ba'a fiya samun irinku a Nigeria ba sai a India "

         Aisha kunya ta kamata ta kyalkyale da dariya ta tashi ta haye sama da gudu. Alhaji Inuwa ya girgiza kai yana murmushi ya dauki jaridarsa yana karantawa. Da haka ya cire mata tsoron dake ranta har ta samu tayi barci a daren ranar.

        Su kuwa Alhaji Inuwa da Hajiya Sailuba da suka je kwanciya a dakina.

       Alhaji Inuwa ya kalli Hajiya Sailuba, yace "Hajiya me kika fahimta akan wannan labari da Ummi tazo mana dashi a yau?"

        Hajiya Sailuba tace "Kawai abinda na fahimta ba komai bane, ina ganin kamar ta tsorata ne da mutanen kasan Ummi da tsoron tsiya kamar farar kura"

        Alhaji Inuwa ya girgiza kai yace "Ni kuma ba wannan na fahimta ba!"

        Hajiya Sailuba tace "Me ka fahimta game da hakan?"

        Alhaji Inuwa yace "Idan kika tsaya saurari labarin nata kika yi tunani a kanta zaki iya cewa iyayenta na gaskiya ne suka bayyana"

        Hajiya Sailuba cikin sauri tace "Haba Alhaji wannan wace irin magana ce haka?"

        Alhaji Inuwa yace "Ki tsaya kiyi tunani akan abinda tazo ta fada, 'wasu mata su biyu da farko kafin suyi mata magana suna ta kallonta kallo fa na sosai, kuma daya tana da tsagu irin nata' idan har kika yi tunani irin nawa to zaki gano wani abu"

         Hajiya Sailuba cikin yanajin sanyin jiki tace "To ai ni bata ce min da wata mai irin tsagunta a cikin matan ba!"

         Alhaji Inuwa yace "To ni ta gaya min!"

         Hajiya Sailuba tace "Yanzu meye abin yi?"

          Alhaji Inuwa yace "Mu bari kawai muga abinda ya turewa buzu nadi, amma kafin nan kada kiyi zancen nan da kowa"

         Hajiya Sailuba ta gyada kai tace "To shikenan"

       
     ***             ***            ***             ***

       Washegari ya kama ranar asabar ne, Alhaji Ahmed da Rahima sukayi sammako suka zo Kano suka sauka a gidan Rahina sannan aka aika aka kira Rahila itama tazo, suka zauna su biyar Malam Buba da Alhaji Ahmed da Rahima da Rahina da Rahila suna tattaunawa akan lamarin.

       Rahila tace "To yanzu meye abin yi?"

       Malam Buba yace "Kamata yayi mu dunguma mu tafi gaba dayanmu, muje mu zauna tare da mutanen gidan muji idan itace"

        Alhaji Ahmed yace "Nima abinda nake ganin za'ayi kenan"

        Rahila tace "To shikenan ayi hakan shine masalaha"

         Rahima ta kalli Rahila, tace "Amma yaya idan muka je aka tabbatar da ita su kuma suka ki yadda su bamu ita fa, ko ita taki yarda damu a matsayin iyayenta!?"

        Rahina cikin mamaki tace "Me yasa kika ce haka?"

        Rahima cikin yanayin damuwa tace "A jikina ina jin dayan abubuwan zai faru!"

         Rahila tace "Wannan kururuwar shedan ce kawai ba komai ba, kada ma ki damu kanki akan abinda bashi tushe"

        Malam Buba yace "Yanzu mu bari da kamar karfe goma sai mu tafi"

        Nan suka zauna suna ta hira a junansu, Alhaji Ahmed da Malam Buba suka zauna a zauren gidan, su kuma matan suna tsakar gida.

        ***           ***           ***         ***

      Alhaji Inuwa yana zaune a falo yana karanta jarida, can gefe kuma Aisha ce zaune a gaban Hajiya Sailuba tana mata gyaran gashi, bayan ta gama mata sai Aisha ta dauki madubi tana gani.

       Aisha ta kalli Hajiya Sailuba, tace "Aunty wallahi dama wajen salon kika bude, saboda kinyi matukar iya gyaran kai da gashi kuma kin iya makeup"

          Hajiya Sailuba tayi dariya sosai ta juya ta kalli Alhaji Inuwa tace dashi "Kana jinmu da yarinyar nan ko?"

         Alhaji Inuwa yana murmushi yace "Me ya faru?"

          Hajiya Sailuba tana dariya tace "Wai yarinya nan don na gyara mata gashin kanta taga yayi kyau, wai dama wajen salon na bude, kaji fa tsofai tsofai dani"

          Alhaji Inuwa yace "A hakan ne kike tsofai tsofai? ke dai da son girman tsiya kike wallahi! kuma ai gaskiyarta kinga hanyoyin shigowar kudinmu sai su karu"

          Aisha tace "Ku fa ba sai kinyi da kanki ba, ke kina office yaranki ne zasu dinga yi"

         Hajiya Sailuba tana kara dariya  tace "Lallai yarinyar nan da sauranki, ita nan da gaske take" ta fada tana kallon Alhaji Inuwa.

         Alhaji Inuwa yace "Au ke da wasa kika dauki maganar, to nima da gaske nake.........."

          Sai mai gadi ya shigo cikin falon daga waje.

         Mai gadi yayi sallama "Salamu Alaikum"

         Alhaji Inuwa ya kalli inda yake ya amsa "Amin wa alaika salam"

        Mai gadi ya risina yace "Alhaji barka dai"

         Alhaji Inuwa ya gyada kai yace "Yauwa barka dai"

         Mai gadi cikin girmamawa yace "Alhaji wasu baki ne suke son ganinka a waje"

         Alhaji Inuwa cikin mamaki yace "Maza ne ko mata?"

         Mai gadi yace "Maza guda biyu mata kuma guda uku"

         Alhaji Inuwa ya jinjina kai yace "Jeka ka shigo dasu"

         Mai gadi ya tashi yace "To Alhaji" sai ya fita.

          Alhaji Inuwa ya kalli Hajiya Sailuba da Aisha, yace "To ga baki nan zasu shigo, kunji ko?"

         Hajiya Sailuba itama ta kalleshi tace "A to su shigo mana"

         Aisha tana kallon Alhaji Inuwa, tace "Daddy daga ina suke?"

         Alhaji Inuwa ya girgiza kai yace "Nima ban san daga inda suke ba an dai ce ga baki, nace a shigo dasu"

         Hajiya Sailuba tace "To Allah yasa muga alkairi"

         A daidai lokacin sai mai gadi ya shigo tare da bakin, basu kowa bane face Malam Buba da Alhaji Ahmed da Rahila Da Rahina da Rahima, su shigo da sallamarsu gaba daya, Alhaji Inuwa ya amsa musu.

        Aisha tana yin ido hudu da Rahina, sai tayi farat ta tashi tsaye ta koma bayan Hajiya Sailuba cikin yanayin firgita da tsoro tana fadin "Sune Aunty! sune! wallahi sune!"

         Alhaji Inuwa yayi magana da karfi yace "Sune su wa? me kike nufi ne? su waye su?"

          Aisha cikin kuka tana magana da karfi cikin firgici tace "Sune mana! wallahi sune! ku koresu daddy!"

      Kowannensu ya zazzare ido yana kallon dan'uwansa, duk suyi mutuwar tsaye suyi zuru zuru kamar wadanda ruwa yaci. Kawai sai Rahima ta kama hawaye.

       Alhaji Inuwa ya kalleta yace "Ya dai Rahima, lafiya kuwa?"

       Rahima itama ta kalleshi tace "Na tuna wani lokaci ne da tana karama ta  taba yin irin haka, a lokacin dasu yayarka yaya Hajara suka zo! kasanta da tsoro a lokacin da take karama, ashe har yanzu haka take, wallahi Alhaji itace!"

       Alhaji Inuwa ya kalli Hajiya Sailuba, yace "Hajiya ki kaita sama sai ki dawo"

        Hajiya Sailuba jiki a sanyaye tace "To" ta kama hannun Aisha su haye sama, ita kuma Aisha tana ta waiwayensu.

         Alhaji Inuwa ya maida kallo gare su, ya nuna musu kujeru yace "Bismillah ku zauna ga guri nan"

        Sai su zauna su dan gaggaisa sama sama.

        Alhaji Inuwa ya dube su cikin alamun tambaya yace "Ban gane ku ba kuwa, daga ina?"

        Malam Buba ya nisa yace "Daga unguwar kofar mazugal muke, kuma wata magana ce take tafe damu"

       Alhaji Inuwa cikin yanayin  mamaki da kaguwa yace "Ince dai ko lafiya?"

       Malam Buba yayi murmushi yace "Lafiya kalau wallahi, Alhaji Ahmed yi masa bayani" ya fada yana kallon Alhaji Ahmed.

        Alhaji Ahmed ya kalli Alhaji Inuwa, yace "Yarinyarmu ce ta bace kimanin shekara goma sha biyar da suka wuce, to shine muka ga tana kama da wannan yarinya ta gidan ta yanayin fatarta da yanayin halittarta da wasu tsagu na fuskarta"

        Tun daga fara jawabin Alhaji Ahmed, Alhaji Inuwa yaji gabansa yayi wani mummunan faduwa amma sai ya dake ya basar, Alhaji Inuwa yace "Yaya sunan ita yarinyar taku?"

        Alhaji Ahmed yace "Sunanta Aisha"

        Alhaji Inuwa gabansa ya kara faduwa ya danne yace "Ranar yaushe ta bata?"

        Alhaji Ahmed yace "Ranar asabar ne"

        Alhaji Inuwa yace "Da kamar yaushe ne ta bata?"

        Alhaji Ahmed ya kalli Rahima yace "Rahima da kamar wane lokaci ne ta bata?"

        Rahima da rawar jiki tace "Da kamar misalin karfe tara da minti ashirin da biyar na safe ne"

        Alhaji Inuwa ya sake tambaya yace "Meye makasudin fito da ita daga gidan har ta batan?"

        Rahima tace "Aiken su aka yi su da wasu yara shine su suka dawo ita bata dawo ba"

        Alhaji Inuwa jinjina kai yace "Ko zaki iya tuna kayan da suke a jikinta lokacin da ta fito daga gida?"

         Rahima fuskarta babu annuri tace "Riga da siket ne 'yan kanti a jikinta"

         Alhaji Inuwa tace "Wane irin kitso ne a kanta?"

         Rahima tayi shiru  kamar tana tunani kamar tana jin haushin tambayar, can kuma sai tace "Irin kitson nan ne na robali{kyauro} da dutsuwa, kuma ba kallabi a kanta"

         Alhaji Inuwa ya jinjina kai yana nazarin irin amsoshin da suke bashi, sai ya kara cewa "Shekarunta nawa a lokacin data batan?"

         Rahima tace "Shekarata bakwai da watanni uku da kwana biyar"

         Alhaji Inuwa ya kuma tambaya yace "Ajinta nawa a makaranta a lokacin?"

         Alhaji Ahmed ya kalleshi yace "Tana primary two ne"

          Sai Alhaji Inuwa ya mike tsaye ya kallesu yace "Ina zuwa don Allah!" sai ya haye sama.

Kada ku manta da:
>Like
>Share
>Follow
>Comments

                           📖..........✍️
                       Alkhamis KSA

Continue Reading

You'll Also Like

230K 7.3K 55
แ€›แ€ญแ€•แ€บแ€แ€ปแ€ฑ แ€€แ€ญแ€ฏแ€€แ€ผแ€ฎแ€ธแ€€แ€ญแ€ฏแ€แ€ปแ€…แ€บแ€แ€šแ€บ แ‹ แ€€แ€ญแ€ฏแ€€แ€ผแ€ฎแ€ธแ€œแ€Šแ€บแ€ธ แ€›แ€ญแ€•แ€บแ€แ€ปแ€ฑแ€€แ€ญแ€ฏแ€แ€ปแ€…แ€บแ€œแ€ฌแ€›แ€„แ€บ แ€–แ€ฝแ€„แ€ทแ€บแ€•แ€ผแ€ฑแ€ฌแ€•แ€ฑแ€ธแ€”แ€ฑแ€ฌแ€บ แ‹ แ€”แ€ฝแ€ฑแ€ฅแ€ฎแ€ธแ€›แ€ญแ€•แ€บแ€แ€ปแ€ฑ ๐Ÿ€ แ€”แ€ฑแ€™แ€แ€”แ€บแ€ธ & แ€”แ€ฝแ€ฑแ€ฅแ€ฎแ€ธแ€›แ€ญแ€•แ€บแ€...
5.4M 484K 98
โœซ ๐๐จ๐จ๐ค ๐Ž๐ง๐ž ๐ˆ๐ง ๐‘๐š๐ญ๐ก๐จ๐ซ๐ž ๐†๐ž๐ง'๐ฌ ๐‹๐จ๐ฏ๐ž ๐’๐š๐ ๐š ๐’๐ž๐ซ๐ข๐ž๐ฌ โŽโŽโŽโŽโŽโŽโŽโŽโŽโŽโŽ She is shy He is outspoken She is clumsy He is graceful...
120K 15.8K 34
#Book-3 Last book of Hidden Marriage Series. ๐Ÿ”ฅโค๏ธ This book is the continuation of the first and second book "Hidden Marriage - Amazing Husband." If...