IMRAN

By real__ahmerd

3.8K 225 70

This story is a life hearted story about passion and compassion.... It is a story that talks about Governance... More

INTRODUCTION
0⃣0⃣1⃣
0⃣0⃣2⃣
0⃣0⃣3⃣
0⃣0⃣4⃣
0⃣0⃣5⃣
0⃣0⃣7⃣
0⃣0⃣8⃣
0⃣0⃣9⃣
0⃣1⃣0⃣

0⃣0⃣6⃣

181 13 3
By real__ahmerd

DAN ALLAH KUYI FOLLOWING ƊINA, DAƘIƘU BIYAR KAƊAI SUN WADATAR...




💐IMRAN HAUSA NOVEL 💐

🍀An untold Love and Political Story 🍀

This chapter is dedicated to my lovely caring Mom❤️. Allah ya dawo min dake lapiya...

SHAFI NA SHIDA

Kasancewarsa Mutum ne mai dakakken zuciya, ba ƙaramin abu  ba ne yake bashi tsoro, ya sa yayi saurin daidaita natsuwarsa. Kallon shi yayi hannunshi na kan steering ya karkaɗa kansa tare da sakin wata dariya cikin dakewa yace da shi “Kai wani irin Jahili ne?. Wacce dokar ce ta bawa wani soja damar yin arrest, uhmm?. ko an gaya ma ka nima jahilin ne bansan komai ba kamar ka?. Ka gaggauta sake min hanya in wuce idan ba so kake ka rasa aikinka ba a yau yau ɗin nan!”. Ya ƙarasa faɗa yana mai tada motar. Ƙoƙarin buɗe ƙofar fannin Driver Lt. Muhammad Bello yayi wanda cikin sa'a ta buɗu, “I'm not really arresting you, akwai investigations ne da ake so ayi a kanka wanda idan hakan ya tabbata babu shakka zaka shiga hannu!”.

Wani irin duka zuciyarsa tayi, a iya tunaninsa dai ba wani abinda yayi, amma kuma lokacin da ya tuno lamarin Yaronnan da ko sunanshi bai sani ba sai hankalinsa ya tashi. Amma kuma da ya tuna cewa babu wata evidence sai ya ɗan ji hankalinsa ya kwanta. “Zan biku muje a Motata, ka sa wani ko ɗaya daga cikinku ya shigo mu tafi tare. Amma fa kasani, akwai barazanar rasa aikinka matukar a binciken aka gano babu laifina a ciki!”.
Duk da irin jarumtar Lt. Muhammad Bello da gwagwarmaya da kuma tashin hankalin da ya fuskanta a baya waɗanda suka fi wannan ma, amma kuma sai yaji na wannan abu ne na daban domin a duk mutane masu taurin kai da ya gamu da su a rayuwarsa, babu wanda ya taɓa mai barazanar rasa aikinsa!. Ya so yayi gardama akan sai dai wani ya shiga motar ya kai masa ita, amma kuma a wannan gaɓar gwara ya lallaɓa shi don ya san shi Mutum ne mai kafiya tun suna College, ba kasafai ya fiye sauka akan maganarsa ta farko ba, balle kuma yanzu da yake matakin Shugaban Ma'aikata na Jaha!

Ba tare da wani ɓata lokaci ba yayi appointing Sojoji biyu da zasu shiga motar Honourable, sannan suka sa shi a gaba suna binsa a baya kowa da saƙe saƙen da yake yi a ransa.
Babban Ofishin Security investigations suka isa inda akayi directing ɗinsa wani dark room da babu komai aciki sai kujeru biyu suna fuskantar juna sai kuma wani babban tebur a tsakaninsu, babu wani waɗataccen haske face wani ƙwan lantarki wanda yake launin ja a setin inda kujerun suke. Sojan da ya shigo da shi ne ya ja masa kujera ya zauna, yayin da ya kasa tuna dai dai da dalili guda ɗaya rak da ya kaishi ga shiga  wannan gurin. Ɗora hannayensa yayi akan teburin dake gabansa yana mai ƙurawa kujerar da ke fuskantar sa ido, har tsawon mintina Uku yana a haka yaji an buɗe ƙofar an shigo tare da sallama. Cikin natsuwar da ba ta kai har zuci ba ya amsa tare da juyowa dan ganin mai shigowar, hanjin cikin sa sai da suka kaɗa, wani irin firgici ne ya ziyarce shi lokaci guda, bugun zuciyarsa ne ya tsananta, amma kuma hakan bai bayyana ƙarara a fuskarsa ba sai mai tsananin lura da sā ido ne ko kuma wanda aikinsa ya danganci hakan ne zai iya fahimta. Ba kowa bane face Inspector General of Police Haruna Abdullahi Shinkafi shi da kansa!.

Maida kansa yayi yana kallon teburin dai dai lokacin da Inspector ya ƙaraso ya zauna a kujerar ya zama suna fuskantar juna. “Barka da wannan lokaci” inspector ya faɗa yana mai ƙare mishi kallo. Aro Jarumta Honourable yayi tare da sake gyara zaman hannunsa dake kan teburin yana cewa “Yauwa barka”.
“Sunana Inspector General Haruna Abdullahi Shinkafi. Nasan bazaka rasa jin labarina ba”. inspector ya faɗa yana mai ƙare mishi kallo. Girgiza kai yayi kawai alamun eh wanda ya sa Inspector ci gaba da magana kamar haka “Dafan kaine Honourable Zahraddeen” tsakankanin satan numfashi ya amsa da eh.

“Ban taba tunanin cewa a well behaved and discipline government official kamar kai za'a sameka kana deals irin wannan ba. Kadubi duk yadda Gwamna ke sonka, ka dubi yadda ya ke saka kana wakiltanshi a wurare wanda wannan aikin mataimakin shi ne. Ka dubi irin Alfarma da kake samu daga Federal ana baka contract. Ka dubi irin Albashi da kake ɗauka ya isa ya ishe ka rayuwa. Me yasa kake so ka ɓata Career ka ta siyasa?. Ace wai yau an samu da hannunka dumu dumu acikin ayyukan ta'addanci?. A haka Shehu Galadima yake so ka zama Gwamna nan gaba?..”.

“Mai girma inspector, ban fahimci abinda kake faɗa ba” Honourable ya katse shi a kiɗime cikin duburburcewa da rashin gano inda zancennasa ya dosa.

“Mun yi artabu da yaranka mun kashe uku daga ciki sun raunata mana Mutum ɗaya, banda fasinjoji uku da suka kashe gurin fashi da makamin da ka sanya su”
Numfasawa yayi kaɗan tare da yin wani irin murmushi mai ciwo ya cigaba da cewa
“Gaskiya yaran naka na da taurin kai, domin sunƙi fada mana wanda ya sa su duba da alburusan duka na ƴan sanda ne. Har na fara tunanin a gobe za'a kaisu kotu a yanke musu hukunci sai kuma gang leader ɗin su ya buɗi baki yace kaine....”

“Inspector ban fahimci abinda kake faɗa ba!. Bansan me kake faɗa ba inspector. wallahi bani da hannu a wani abu makamancin haka. Inspector!, nasan baka taɓa faɗa min ba, amma gwamna ya shaida min cewa kaine ka fara bashi labarina ganin irin adalcin da nake gudanarwa a matsayina na shugaban ɗalibai a makaranta da kuma irin role ɗin da nake playing. Mai yasa bazaka tsaya ka nazarci lamarin nan ba yallaɓai?”

“Karka mai dani Wawa mana wanda bai san abinda yake yi ba! Ba ƙaramin adalci nayi ma ka ba da ban sa sun tukwikwiyeka sun zo mun da kai a wulaƙance cikin sarƙa ba, sam ni banga amfanin tattaunawan da na tsaya ina yi da kai ba”. Miƙewa Inspector yayi tsaye wanda nan take wayarsa dake aljihun sa ta soma ruri, MINISTER shine sunan da ya gani yana yawo akan screen ɗin wayar.
Da sauri yayi picking, wanda acikin saurin ne ya sanya wayar a handsfree ba tare da ya sani ba.
“Ka gaggauta sakin shi idan kasan kayi arresting ɗinsa, idan kuma baka yi ba to ka gaggauta ƙyaleshi ya wuce!”. Wanda yayi kiran ya faɗa cikin yanayi na faɗa faɗa.
“Yallaɓai wa kenan kake magana?”. Inspector ya tambaya yana mai jin wani irin utter disappointment yana mamaye shi.
“Farar Aniya!”
Yana faɗin haka ya kashe wayar ba tare da ya tsaya yi mai ƙwaƙƙwaran bayani ba.

Komawa yayi ya zauna tare da hura iska mai zafi daga cikin bakinsa sannan  yace “Zaka iya tafiya!”.
Tashi Honourable yayi kawai ba tare da yace da shi komai ba yafita ya shige Mota ya ja ya fita, yana fita ya ƙara gudun motar kai ka ce zasu iya zuwa su dawo da shi.

★★★★★★★★★★★★

Mutane ne sukayi cincirindon agaban kangon, yayinda wasu dayawa ke ƙoƙarin ƙarasawa domin shaida abinda yake faruwa. Motar ƴan sanda ne masu patrol suka zo wucewa suka ci karo da faruwar lamarin. Hakan yasa DPO wanda shine ke tuƙa motar tsayawa domin neman ba'asi. Suna ƙarasawa suka kukkutsa inda suka ci karo da yaro shame shame tamkar baya numfashi yayin da wasu Mata ke kansa suna masa fifita suna zubar da hawayen tausayinsa, fuskarsa jiƙe take da ruwa alamun an zuba ma sa amma babu alamar farfaɗowarsa. Da kansa DPOn ya ɗauke shi ya aza shi a kafaɗarsa ya yayi gurin Motar su da shi yayin da sauran ƴan sanda suka mara masa baya. Gidan baya ya shiga ya bawa ɗaya daga cikin ƴan sandan makullin Motar tare da faɗa musu asibitin da zasu kaishi.

Da gudu suka isa babban asibitin Shika wanda tunkan su iso DPOn ya yi magana da a turo da gado akwai emergency. Suna gama packing aka turo gado aka sanya shi akayi emergency room dashi. Ba tare da ɓata lokaci ba likitoci suka shiga bashi taimakon gaggawa wurin ganin sun ceto rayuwarsa. Gaba ɗaya tausayin Yaron ya riga ya dabaibaye shi, sai zarya yake a long corridor ɗin da zai sadaka da emergency room ɗin da ake yiwa yaron aiki. Fatan shi ace yaron bai mutu ba, domin har suka ƙaraso babu alamun numfashi a tare da shi.

Sai da sukayi sama da awa biyu akan shi suna abu guda kafin suka samu numfashinsa ya daidaita, shima sai da suka haɗa da taimakon Oxygen, bayan binciken da sukayi kuma mai zurfi da gano irin taɓargazan da ya faru da shi, drips suka sanya mishi da wasu allurai da suke sa ran zai sa ya dawo cikin hayyacinsa, domin irin cases ɗin nan na taɓa ƙwaƙwalwa musamman yara sosai.

Fitowa suka fara yi yayin DPOn ya nufi babban likitan wanda da shi suka fi jituwa kuma shine ma matsayin Family Doctor ɗin su yana tambayarshi ko lapiya. “Ka kwantar da hankalinka, mun dai samu cikin ikon Allah numfashinshi ya dawo, amma gaskiya a irin cases ɗinnan ba'a cika samu yaran ma su rayu ba, amma Insha Allah nan da 24 hours muna sa ran farfaɗowarsa.”.
“Me ya same shi ne Doctor?”. DPOn ya tambaye shi cikin tsananin tausayawa.

“Da alamun dai haike masa aka yi wanda bama fata dai, amma hakan zai iya taɓa ƙwaƙwalwarsa”.

“Innā lillahi wa innā ilaihi raji'ūn!!!” shine abinda ya maimaita har sau uku idanunsa sun sauya kala zuwa launin ja ya dubi likita yana cewa “Wai me yasa wasu mutane suke mantawa da lahiransu ne?!, wai me yasa wasu mutane suke mantawa da cewa suma suna da ƴaƴa ne, basa tuna cewa ko basu da ƴaƴa nan gaba zasu haifa ne?!. yanzu a shekarar nan hukumar mu ta ci karo da irin cases ɗinnan sunfi goma ga kuma wannan...”
Doctor ne ya katse shi da cewa “Gaskiya na tausayawa yaron, daga gani ma bashi da gata”

“Insha Allahu zamu san yadda zamu ɓullowa al'amarin. Amma gaskiya iyaye suna sakaci ma malam. Allah ya bashi lapiya”.

Da ameen likita ya amsa kana yayi hanyar office ɗinshi....














MENENE MAKOMAR IMRAN?.
SHIN HONOURABLE ZAHRADDEEN ZAI CIMMA MURADANSHI?

Ku cigaba da kasancewa tare dani domin ganin yadda Al'amarin zata kaya..




















































#VOTE
#COMMENT
#SHARE
#FOLLOW

Comments ɗinku shine ƙwarin gwiwa na...

Continue Reading

You'll Also Like

11.1K 731 37
Jeon Jungkook, he completed his graduation in business. he is sweet but for only his family and cold for other's. he doing internship in his father'...
OBSESSED By thisbejaja

Mystery / Thriller

96.4K 4.1K 26
obsessed
46.6K 1.4K 80
"𝐻𝑎𝑛𝑠𝑒𝑜𝑘𝑎𝑎,𝑎 ℎ𝑒𝑎𝑟𝑡𝑙𝑒𝑠𝑠 𝑝𝑠𝑦𝑐ℎ𝑜𝑝𝑎𝑡ℎ 𝑙𝑖𝑘𝑒 𝑦𝑜𝑢 𝑑𝑜𝑒𝑠𝑛'𝑡 𝑑𝑒𝑠𝑒𝑟𝑣𝑒 𝑡𝑜 𝑓𝑒𝑒𝑙 𝑙𝑜𝑣𝑒 𝑤𝑖𝑡ℎ 𝑠𝑜𝑚𝑒𝑜𝑛�...
CONSUME By [ Mary ]

Mystery / Thriller

191K 5.9K 19
There's something odd about the town's most beloved police officer, he is utterly obsessed about a girl and will go to any lengths to have her.