GIYAR MULKI

By zm-chubado

102 14 3

a very heart touching story More

GIYAR MULKI

final chapter

28 6 3
By zm-chubado

GIYAR MULKI
(true life story)

             Page  02
     (The final chapter)

_______Kamar yanda ya faɗa kuwa hakance ta kasance, miƙewa yay a hanzarce dedai wannan lokacin Matarsa Hajiya Bintu ta shigo falon, cikin shiga irinta alfarma ganin shigowarta yasa Alhaji Shamsu ya dakata yana me Jifanta da wani rikitaccen kallo me tsayawa a Rai. Wani nannauyan fasali yaja don har cikin Ransa yakejin hajiya Binta na ƙara mamaye lungu da saƙon cikin zuciyarsa, komai tayi burgeshi takeyi, wasu lokutan idan tana gabansa ba ƙaramar shagalta yakeyi da shauƙinta ba.

Ba komai ne ya sama mata wannan kimar a idanunsa ba face zallar tsaftarta da son adonta, babban abinda yafi komai jan hankalinsa a tareda ita shine ni'imtaccen ƙamshin dake tashi a jikinta a ko wani lokaci, wannan yafi komai tafiya da imaninsa a tareda ita. Cikin yanayi na jan hankali ta iso gabansa se faman karairaya takeyi, cikin salo da jan hankali takai hannunta saman ƙirjinsa tana shafawa tace "Gwamnan gobe ya na ganka haka kamar akwai abinda ke neman ɓata maka rai ne?"

Murmushi ya saki cikin wani irin yanayi me cike da ɓoyayyiyar soyayya yace "Bari kawai Gimbiyar mata, nida wani amintacce na ne amma karki damu ganinki kaɗai ya share min ɓacin ran dake Zuciyata." wani ƙayataccen Murmushi ta saki sabida yanda kalamansa sukai mata daɗi , wani irin fari tayi da idanuwanta, tamkar yarinyar ƴar shekara Ashirin da biyar. Harta buɗe baki zatayi magana kira ya shigo cikin wayarsa dake ajiye cikin aljihun wandon Farar shaddar dake jikinsa.

Cikin wani kasalallen yanayi ya sanya hannunsa ya ɗakko wayar yana bin lambar dake yawo a saman fuskar wayar da kallo, tabbas ko duniya zata tashi baze taɓa manta mamallakiyar wannan number ba, da kamar baze ɗauka ba amma kuma seya ɗaga wayar tareda karata a samn kunnensa na hagu, se faman ɗaure Fuska yakeyi kmar wanda akaiwa Dole.

Cikin kamilalliyar muryrta wadda ke ɗauke Amo irin na manyantaka Talatu tace "Me sunan Yaya....."

Shiru yay mata yaƙi cewa komai hakan yasa Talatu ta saki Murmushi me sauti tace "Duk sabida ina inai maka togaciya da rudun Giyar Mulki yasa ka shafe tsahon shekaru baka zo ka ganni ba shamsu? Kada ka manta fa duk duniyar nan baka da wanda yafini, hakan yasa a matsayina na Uwa nake jiye maka tsoron Ranar da zaka tsaya a gaban Allah akan haƙƙin mutanan da kake wakilta, Shamsu har kullum ina gaya maka cewar mulki Bala'i ne, mulki Masifa ce, mulki Jidali ne, amma ko so ɗaya baka taɓa ƙyamatarsa a zuciyarka ba, sabida yanda ka tsunduma a cikin shan Giyar Mulki wadda har yanzu jirinta ya gaza sakinka. Banayi maka fatan komai sena alkhairi Me sunan Yaya, Amma ina me ƙara jaddada maka cewar duk rintsi duk wuya kada ka taɓa bari Mayan son Mulki yasa ka Rabu da Imaninka...."

Takaici ne ya cika masa zuciya, don haka yasa hannu ya janye Hajiya Binta dake jikinsa ya fara magana cikin ɓacin rai "waike Talatu don Allah meye matsalarki ne? Ubanwa ya gayamiki cewar inacin haƙƙin mutane dazaki sani a gaba kinata gaya min magana? Shikenan kuma dan kin haifeni seki samu damar dazaki dinga faɗamin duk maganar datazo bakinki? Toni gaskiya banason karan tsaye a lamari na, don haka don girman Allah kiji da kanki babu Ruwanki da rayuwata...."

Shiru Talatu Tayi kmar Ruwaya cinyeta sabida wani tuƙuƙin baƙin ciki dayazo mata wuya ya toare mata maƙoshi,wata ƙwallar ɓakin ciki da takaici ne ta fara tsatsafowa a tsakiyar kwarmin idanunta, bugun zuciyarya ne ya fara tsananta, ga wani ɗaci da yawun bakinta ke mata tamkar wadda ta tauna icen maɗaciya, bata ankara ba taji wasu zafafan Hawaye masu matiƙar Zafi suna kwaranya a saman fuskarta......

Bakin zanin Atamfar dake jikinta tasa ta goge hawayen tareda ƙoƙarin dedaita nutsuwarta, murmushin ƙarfin hali ta ƙaƙalo kamar yana gabanta tace "Kayi haƙuri ɗan nan, karan bani ne kawai irin nawa, na ɗauka cewar wannan Shamsu dana ɗauki cikinsa a jikina ne tsahon wata goma sha biyu da ƴan kwanaki ne, shiyasa nayi tunani idan nai maka nasiha zakaji ni, tunda har hakan laifine a gareka don Allah kayi haƙuri Ɗan nan, Ubangiji yay maka Albar......."

Kasa ƙarasa faɗar abinda take ƙoƙarin cewa tayi sabida tuƙuƙin cikin da zuciyarta ke mata,
Be jira cewarta ba ya katse wayar se faman huci yakeyi, kobi takan Hajiya Binta beyi ba yay gaba abinsa

Kai tsaye be dire ko ina ba se gidan Amininsa Alhaji Na'abbah, A babban falonsa ya sameshi suna hira da matarsa Hajiya Amina, da fara'a kwance saman fuskarsa Alhaji Na'abba yace "lale maraba da farin baƙo gwamnan gobe a jihar Bauchi da yardan Allah." nan take ɓacin ran zuciyarsa ya fara sauka sakamakon koɗawar da aminin nasa yay masa.

Gaisawa sukai da Hajiya Amina itama se ƙara zugashi takeyi sannan ta basu waje don su samu zarafin tattauna wa, Kallon Alhaji Shamsu yayi ganin yayi shiru yasa yace "Ranka ya daɗe lfy kuwa? "

Numfashi Alhji shamsu aja sannan ya dubi Aminin nasa yace "ina ganin yau zan shiga ƙauyen tsakuwa, don mu gana da Ɗan Saude...."

Gyara zama Alhaji N'abba yayi ta yanda zefi fahimtar maganar Alhajin Shamsun sannan yace "dawuri haka? To Allah yasa dai ba wata matsalar aka samu ba."

"ae ba wata matsala kawai dai ina buƙatar ganawa dashi ɗinne." Alhj Shamsu ya faɗi hakan yana me tsare Aminin nasa da kallo, shiru ne ya biyo baya sannan suka faɗa hira akan yanda hidimar siyasar su zata kasance. Seda suka gama tsara komai sannan yay masa sallama ya kama haryar Kano.

Gudu kawai yake tsulawa a saman kwalta tamkar ze tashi sama, don haka cikin awa ɗaya tak ya isa Ƙauyen tsakuwa, a bakin wani ƙaramin gidan ƙasa ya faka zindimemiyar Motarsa, sannan ya fito ko takalmi babu a ƙafarsa sabida haka dokar Malam Ɗan Saude take. Ba'a shigar masa gida da takalmi.

Babu kowa a gidan se wasu baƙaƙen murguza-murguzan karnuka guda Uku, idanunsu kaɗai idan ka kalla ya isa ya baka tsoro amma shi Alhaji Shamsu ko'a jikinsa haka ya raɓa ta gefansu ya wuce, A zaune ya samu Ɗan saude a saman buzunsa yana aiKn tsatsubarsa sa, amma ganinsa yasa ya dakata tareda washe baki yace "maraba lale da gwamnan gobe, yanzu haka akan aikinka nake tun jiya ko rintsawa banyi ba."

Zama yay akan wata jemammiyar fatar damusa wadda ke shimfiɗe a gaban Ɗan Saude yace "Ranka ya daɗe malam ɗan Saude, ai indai inada kai to banida sauran haufi, shiyasa yanzu ma nazo gareka akan maganar da muka fara nida kai, shin ina muka kwana? Akwai nasara a harkar nan ko babu?."

Shiru Ɗan saude yayi kamar ruwa ya cinyeshi, sannan ya dubi Alhaji Shamsu yace "Tabbas akwai Nasara ammafa kafin abin ya tabbata se'an kauce hanya, don wllh aikin me wahala ne kuma ba lallai ka iya aikatawa ba sabida nauyinsa..."

"Zan iya aikata komai indai har buƙata ta zata biya in samu kujerar nan, wllh zan iya aikata komai duk nauyinsa kawai ka sanar dani" Alhaji shamsu yay maganar cikeda zaƙuwar jin abinda Ɗan Saude ze gaya masa.

Kallom tsaf ya shiga binsa dashi sannan yay ƙasa da kansa yace "kafin ka samu wannan kujerar seka samo min maniyin da akai zina da mahaifiyarka.... To da wannan ne kaɗai zan iya sarrafa maganin dazakai amfani dashi kuma kayi nasara."

Wani irin Gumi ne ya fara karyowa daga dokin wuyan shamsu zuwa faffaɗan ƙirjinsa, kafin kace me tuni ya jiƙe sharkaf da zufa, ganin haka yasa Ɗan Saude yay murmushi yace "kaje ka yanke shawara dabara ta rage game shiga Rijiya inji masu iya magana, nidai kaga tafiyata na baka nan da kwana 2..."

Ya jima a gurin zaune sannan ya iya miƙewa kamar wanda aka zarewa laka haka ya koma mota ya tafi, babu abinda yakeyi illa juya al'amarin a ransa, har aka kwashe kwana ɗaya be tsaida matsaya ba, washe garin Rana ta biyun ya shiya cikin wata maroon ɗin gizna ya Nufi ƙauyen MAGAMAN GUMAU don ganawa da Mahaifiyarsa Talatu, wadda a yanzu ta koma gidan data gada a gurin mahaifiyarta, sabida bazata iya zama da shamsu a inuwa ɗaya ba kasancewarta me gudun duniya da abinda ke cikinta, ko'ada baya Allah shine sheda akan irin tarbiyar data bawa shamsu, haka kuma tayi gwagwarmaya me tarin yawa duk dan ta inganta Rayuwarsa, amma se gashi Ubangiji yay mata jarrabawar da ba ko wace uwa bace zata iya ɗaukar hakan ba, ita kanta tasan ba gazawarta bace tasa Ɗan data haifa yake guma mata baƙin ciki ba, face jarrabawar ubangiji, hakan yasa Talatu ta sanya hannu biyu ta karɓi abinda Ƙaddarar Haihuwar Shamsu tazo mata da ita.......

Ƙarfe ɗaya dedai a MAGAMAN GUMAU taiwa Alhaji Shamsu, kai tsaye Ƙofar Gidan Talatu mahaifiyarsa ya nufa ya parka motarsa, ya jima a cikin motar be fito ba seda aka shafe tsahon mintuna 30 sannan wasu matasan samari su Uku suka fito daga bayan motar, kai tsaye cikin gidan suka shiga

Sun jima a ciki sannan suka fito suka shiga motar shi kuma Alhaji Shamsu yaja motar suka tafi.

Seda ya koma cikin Garin Bauchi ya sauke matasan shi kuma ya kama hanyar ƙauyen tsakuwa.....

Yauma kamar kullum a zaune ya samu malam Ɗan Saude a cikin ɗakin tsatsubar sa, zama yay a gabansa yay shiru ba tareda ya iya cewa komai ba, hakan yasa Ɗan Saude ya ɗago kai ya kalleshi yace "Gwamnan gobe ina fatan an samo abinda muka ce?"

Cikin tsananin farin ciki Alhaji Shamsu ya zaro wata ƙaramar Roba a cikin aljihunsa ya miƙawa Ɗan saude yace "gashi an samo, ai dama na gaya maka zan iya aikata komai don tabbatuwar muradina, wllh duk abinda akace inyi zanyi indai har burina ze cika....."

Tsoro da fargaba ne sukaiwa Malam Ɗan Saude dirar mikiya duk a lokaci guda, cikin tsanani tashin hankali ya dubi Alhaji Shamsu yace "kana nufin wannan manin mahaifiyar ka ne ? Kaiko taya akai ka samo wannan abu?"

"fyaɗe nasa akai mata sannan na gayawa waƴanda sukai fyaɗen abinda nake so a tareda ita, shine suka samo min." Alhaji Shamsu ya gayawa ɗan Saude hakan.

Gumi ne ya fara ketowa Ɗan saude lokaci guda kuma seya fashe da kuka, al'amarin daya bawa Alhaji shamsu Mamaki kenan.

Wani irin kuka Ɗan saude yakeyi tamkar ze shide, daƙyar ya iya daidaita nutsuwarsa yana kallon Alhaji shamsu yace "wllh tunda na fara harkar bikanci ban taɓa yin arba da mara imanin ɗan siyasa kamarka ba, a lokacin da kazo min da buƙatarka na gaya maka haka nayi zaton bazaka iya aikata abinda nace maka ba, amma dayake kai ƙasurgumin mara imani ne se gashi ka aikata fiyeda abinda nai tsammani, billahillazi'la'ilaha'ilahuwa Shamsu bazaka gama da duniya lafiya ba.........."

"Asragfirullah Allah na tuba Ubangiji ka gafarta min laifukan dana daɗe ina aikata maka, haƙiƙa na yarda da abinda bahaushe ke cewa inda Ranka kasha Kallo a duniya, yau gashi na haɗu da ɗan ta'addan daya fini Rashin Imani, wllh yau itace Rana mafi haske da farin ciki a Rayuwata sabida a sanadin ka nabar duhu na dawo haske.

"Ada nayi zaton alaƙar dake tsakanin ɗada Mahaifiya tafi dangantakar dake tsakanin ƙashi da tsoka ƙarfin, amma yau danai Arba dakai na ƙaryata hakan. Ya ubangiji ka raba mu da haihuwar ƴaƴa irin ka Shamsu........" da gudu ɗan Saude ya fice daga ɗakin sabida tsabar tso da firgicin dayake ciki, don gani yakeyi kamar ubangiji ya tashi sakkowa da Shamsu bala'i to harshi za'a haɗa...

Wannan ta'addanci da Alhaji Shamsu ya aikata shine ya zama silar Shiryuwar Ɗan saude har yay murabus daga kujerarsa ta bokanci..

Ya jima a ɗakin yana zaune banda gumi babu abinda yake keto mata, daƙyar ya iya miƙewa da sauran ƙarfin daya rage masa, a haka ya koma mota jikinsa duk babu ƙwari a hkaa ya tuƙa motar ya koma Bauchi, babu abinda ƙirjinsa keyi se bugawa tamkar zuciyarsa zata tarwatse, haka ya sake ƙoƙartawa yaja motar ya Nufi MAGAMAN GUMAU, Haka kawai seya samu kansa dason ganin Talatunsa, ummansa wadda itace komai nasa, gatansa kuma tsaninsa, duk matakan nasarar daya taka a Rayuwa itace Sila. Wannan Talatun dai Me surfan hatsi da dawa ita dai yake nufi, wadda ke kwana da yunwa shi yaci abinci, wadda yake hanawa bacci da kuka.

Wadda keyin wankau ɗin mutane da duk wani aikin ƙarfin duk don ta inganta Rayuwarsa, amma wai itace yasa aka keta alfarmarsa duk a sanadin GIYAR MULKI....

"INNANILLAHIWA'INNA'ILAIHIRRAJI'UN..... wannan wace irin masifa ce haka ?"

Kafin ya ƙaraso gidan haka Tuni Talatu ta jima da amsa kiran Ubangiji, a dedai lokacin daya gama faka motarsa a dedai lokacin aka futo da gawarta, ganin haka yasa ya fito daga motar a haukace kamar sabon Mahaukaci, bekai ga ƙarasawa gurin da mutanen suke ba ya faɗi ƙasa timmm kamar kayan wanki, kaɗan daga cikin mutanen ne suka isa gareshi sauran kuma suka nufi filin daza'ai sallar gawar, shamsu be tashi farfaɗowa ba se bayan ankai Talatu makwancinta na Gaskiya.....

Shamsu yasha kuka kamar baze bari ba, wannan shi ake kira da IHU BAYAN HARI, ko in kira hakan da AIKIN BANZA HARARA A DUHU... Ina amfanin kukan Shamsu ga Talatu bayan shine Ummul'aba'isin komai?

Bayan kwana uku ta Mutuwar Talatu

Shamsu ne zaune cikin mota se gursheƙen kuka yakeyi, haka ya kamo hanyar Baushi yana tafiya yana kuka, kmaar a mafarki yaga abu ya gifta masa ta gaban idanunsa, nan take motar ta ƙwace daga hannunsa ya tabka mummunan haɗari, a take ƙafarsa ta dama ta fice fit hakama hannunsa na hagu, a wani ƙaramin ƙauye da akewa laƙabi da MIYA BARKATAI, da taimakon mutanen dake gurin aka iya zaroshi daga motar, sun zaroshi kenan ba jimawa motar ta kama da wuta, da ƴan karume -karume aka kaishi Asibiti cikin yanayin fitar haiyaci. Yanaji yana gani komai nasa ya ƙare yayi babun baɗilahu babu mulkin kuma babu lafiya, bugu da ƙari kuma babu Inuwar Rayuwarsa wato Mahaifiyarsa Talatu.....

Se'a yanzu yake ganin abinda take gaya masa a baya amma yaƙi saurararta, yanzu ME GARI YA WAYA?

INA AMFANIN BAƊI BA RAI?

Ya ubangiji ka bamu zuriya ɗaiyiba, ya Allah kada kai mana mummunar jarrabawa, idan zaka jarabce mu kai mana jarrabawar dazamu iya ɗauka ya Arhamurrahimin.....

Ya Allah ka sakawa iyayen mu mata da alkhairi, ubangiji ka basu aljanna firdausi maɗaukakiya.

Allah kasakawa iyayen mu maza da alkairi, Ubangiji ka basu aljanna, ya Allah ka shirya mana zuriya kai musu albarka

Allah ka mana tsari da mummunar ƙaddara

Tammat bi hamdillah a nan na kawo ƙarshen wannan gajeran labari, darasin dake ciki kuma ubangiji ya bamu ikon ɗauka, kuskuren dake ciki kuma ubangiji ka gafarta min, ya Allah kajiƙan Talatu kai mata Rahama, kasa Aljanna ta zama makoma a gareta

Wannan labarin true life story ne don haka mata muyi hattara, mu dage da roƙon Allah ya shirya mana zuri'a, duniya ta daɗe da canzawa idan har ɗa ze iyaywa uwar data haifeshi haka to waye baze iyaywa haka ba??????


ZAINAB MUHMD CHUBAƊO

08102777485

Mamana help me to share it pls

Continue Reading

You'll Also Like

11.3K 1.3K 34
"කොල්ලො දෙන්නෙක්ට ලව් කරලා සෙක්ස් කරන්නත් පුළුවන්ද බන්.." ?
40.7K 933 6
Hiroki has recently discovered that the four women he once knew and loved, his girlfriend (Nao), sister (Kanoko), best friend (Ayumu), and mom (Kaede...
19.1K 501 7
Yasmin Monroe signs up for Love Island 2024 looking to find her perfect match.
15.8K 2.5K 19
ආදරේ කියන්නෙ හුත්තක්. එච්චරයි __සිතුම් ආකාෂ් ෆ්‍රනෑන්ඩෝ