ZAFI BIYU

By Qurratou

490 9 4

Labari ne dake dauke da sark'ak'iya da kuma dana sani a lokacin da wuri ya k'ure. More

ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFIE BIYU
ZAFIE BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
MAKANTAR ZUCI!
MAKANTAR ZUCI!

MAKANTAR ZUCI!

20 1 0
By Qurratou

MAKANTAR ZUCI!

DAGA ALK'ALAMIN
                                MARYAM ANKUDIE {QURRAH}

🌟✨🌟✨🌟✨🌟
*_TAURARI BIYAR!!! 2022_*
🌟✨🌟✨🌟✨🌟

✍ *✍ G̾O̾L̾D̾E̾N̾ P̾E̾N̾ W̾R̾I̾T̾E̾R̾S̾ A̾S̾S̾O̾C̾I̾A̾T̾I̾O̾N̾* ✍✍

https://www.facebook.com/Golden-Pen-Writers-Association-102095951667849/
____________________

_EPISODE 1_

Zufar dake bin fuskata ne na goge da Hijab dina kasan cewar yau antashi da rana mai zafi kallon karamin kanena nayi dake gefe rike da jikar ruwa biyu a hannu (Pure water) yana dagawa.

Kallona yayi yace;"Gaskiya nide nagaji Ummu tun dazun muke yawo da ruwan nan akai amman babu mai saye saboda ba sanyi kuma kin san idan ana zafi mutane sunfi son ruwan sanyi nide gida zani yunwa nakeji tun kokon safe fa"

Murmushi nayi cikin Lallashi nace;"Audu kayi hakuri mugani zuwa anjima kadan mana kaga naka saura hudu zamu saida kuma kasan halin...."

Bata idaba suka hango wata Bakar mota ta shigo gidan Man da suke tsugunne a gefe.

A guje su duka suka mike hadda wasu yara su biyu maza dake gefen su suka nufi motar.

"Hajiya ga ruwa Alhaji ga ruwa"

Motar kasan cewar a kulle har yanzu hakan yasa suke lekata duk da duhun glas ya hana suga wanda ke a cikin ta.

Wani ma'aikacin gidan Man ne yazo inda muke yace;"Yaran nan bakujin magana bana hana ku tallah a gidan Man nan ba? Saboda rashin hankali irin naku mi wadan nan mutanan zasuyi da Pure water ku wuce daga nan ko saina kore ku baki daya"

Tsayawa nayi ina kallon motar da idanuna da yunwa tasa sun kara fitowa.

Ji kawai nayi anture ni da hannu nayi k'asa baki daya.

"Ke kowa yabar wajen saike mai shegen taurin kan tsiya"

Bata faduwar da nayi nake ba, Ba kuma ta magan ganun Ma'aikacin nan nake ba ta Pure water na biyu daya fadi nake cikin sauri na dauke shi ina gogewa da daudardar Hijab dina kana na tashi ganin wasu masu mashin sun shigo.

Cikin azama na mike  na nufi inda suke, Cikin sa'a ko suka amsa saide ganin K'asa jiki yasa suka maido.

Jikina har kyarma yake nace;"Dan Allah kuyi hakuri Kanena zai kawo maku wani ga robar mu chan kunji"

Duk maganar nan da mukeyi suna tafiya da mashin ni kuma ina bin su, Cikin daga murya nace;"Audu kawo ruwa biyu"

Audu najin ciniki yasa shima ya dauko ruwa a guje yayo inda muke yabar robobin ruwan a chan.

Lokacin sun isa wajen da ake zuba Man dai-dai lokacin kuma angama zubama motar da ake korar mu kada mu tab'ata.

Audu ya iso ya miko man ruwan yana haki.

Yar dariya nayi ina kallon yadda yake zufa kana na amsa na mika masu.

Suna amsa suka taba suka juya dayan wanda ke baya yace;"Wannan ai ba sanyi anshi bamu saye, Mai sanyi muke so.

Kai yaron nan kawo naga naka nada sanyi"

Miko man yayi kasa amsa nayi Audu ne ya amsa tare da jan dogon tsoki.

"Kai mu kake ma tsoki kasan komu suwaye ne ko kasan...."

Wata kara da mukaji yasa mu duka muka juya.

Robobin tallar mune wannan Black din motar ta taka tawa data Audu.

Sakin duka Pure water dake hannun mu mukayi muka nufi wajen a guje.

Ganin motar bata tsaya ba yasa na dauki wani katon dutsi na jefa ma Motar.

Kusan rabin Glas din motar na baya ya zube.

Duk wanda ke cikin gidan Man nan saida ya kasa motsi.

Kuka na aza mai sauti kana na duka ina hada banlin roba ta ina Kuka batare dana kula da motar dana fashe ma glass ba.

Ina duke naji an fizgo hannu na tamkar za'a rabani biyu.

Tangal-tangal nayi zan fadi kana na samu kafafu na suka tsaya ina kallon wanda ya fizgoni.

Wata matashiyar mace ce nagani tsaye a gabana tana huci.

"Ke gidan ku basu koya maki tarbiya bane? Ke diyar gidan Uban wanene? Saboda baki san darajar mota ba shine zaki fasa mana glas?"

Juyawa tayi ga Diver din ta tace;"Kai kuma na dawo kan ka kasan mota babu Mai ka dauketa yanzu gashi nan wajen shan Man kalli abinda ya faru inaga nafi shekara fiye da goma ban shiga gidan Mai ba to a bakin aikin ka sannan ka kira wani driver yazo ya kaimu gida ke kuma kowaye Uban ki yau saikin kwana a Sell"

Ta fada tare da maido kallon ta waje na da nike tsaye ina haki.

"Mallama ke kisan wani Sell nide ku biya ni Robata da ruwana"

Kallo na take kallon mamaki ganin yadda nake ya mutsa mata baki.

Ga mamaki na sai naga tayi murmushi ta juya.

Driver ya matso kusa damu yace;"Yan sanda zata kira su kama ku su daure"

Murmushi nayi nace;"To ai mu mun saba da yan sanda saboda Babban yayan mu kullun yana wajen su muma dan an kaimu ai za'a amso kamar yadda ake amso shi nide ta biyani robana da ruwa na"

Jin magan ganuna yasa ta dan leko tana kare mani kallo.

Wata mota ce ta iso wadda tafi wacen kyau.

Matar ta fito daga waccan itada wani matashi dako kallon inda nake bai yiba ganin haka nayi tunanin shine Ogan su hakan yasa na nufi inda yake.

Shi kuma motar ya nufa cikin wani tako kamar basarake.

Cikin azama ganin yaku isa wurin motar yasa nayi wani tsalle saide naga na tsabki farar rigar shi da hannu da da jar k'asa ta bata shi.

Wani kallo ne yayi mani batare da yayi magana, Hmmm kallon kade da yayi man ya isheni hakan yasa na saki rigar shi ina kallon shatin ya tsuna a jikin rigar shi.

Jikina a mace na koma wajen da Audu yake tsaye nima na tsaya.

Ina kallon shi ya shiga motar dayar Matar ma ta shiga saiga driver ya fito Yana zuwa ya mika mana yan dubu-dubu.

Wani ihu nayi nida Audu tare da rungume juna muna murna rawa muke sosai kana nabi motar da kallo driver din harya shiga a guje na isa wajen motar yanzu ma duhu ne ga Glass din motar ba'a ganin wanda ke ciki ganin haka yasa na fara rawa ina lika kudin a jiki na daman godiya nazo yi masu ganin ba'a gani na hutar da kaina ina nan ina tsalle na suka wuce.

Masu machine din da sukayi mana wulakaci suka ki sayen namu wajen su na nufa suna gyaran mashin din gefen hanya.

Muna isa nida Audu muka fara masu dariya Audu yace;"Allah ya k'ara"

Nace;"Kunki sayen ruwan mu  gashi nan mashin dinku ya lalace mu kuma kunga kudin mu lol😂😂"

Daya daga ciki ne ya biyo mu muka  ruga muna dariya.

Kudin sabbi ne hakan yasa naki karya su na rike su a fili duk inda muka nufa kallon mu ake hakan yasa saikara fiddo su nike.

Wajen wata majalissa ta Samari muka isa ganin Samari yasa naja Audu mukayi baya.

Maganar K'awata Salame ta dawo man dana tambaye ta miyasa ni banda Samari tace;"Saboda bamu da kudi kuma ban gayu"

Murmushi nayi kana nace;"Audu tsaya kagani yanzu nima zanyi saurayi"

Na fadi maganar ina kyalkya cewa da dariya.

Zanena na kwance na gyara kana na gyara Hijabi na sannan na gyara rikon kudina da hannaye na biyu na fiddo su sosai yadda ko daga nesa ka hangoni zakaga kudi ne hannu na.

Kallon kafafu na nayi naga duk kura dan tsoki nayi kana na kama gefen zanene nayi na goge kafuna dan tsoki na kara ganin lasassun Silifas dina nace a fili;"Bakomi gobe na siya wasu"

Audu yace;"Nide kiyi sauri fa yunwa nake ji kamar na fadi"

Hararar shi nayi kana muka kama hanya nan fa ganin mun iso wajen samarin na fara tafiya kamar na fadi ni a dole yanga nake naga maza ganin ko sun kuraman ido su duka yasa na kara rage tafiya ta ina wata tafiya kamar zan fadi.

Audu ko sai kallo na yake chan yace;"Waike mi kika taka kike tafiya a gefe daya kamar zaki fadi"

Wani kallo nayi mashi kamar zanyi kuka ganin zai dizgani kana nace a k'asa-k'asa;"Yanga ce nikeyi kayi shuru kaji"

Wata dariya Audu ya fashe da ita dai-dai lokacin da mukabar wajen, Nima dariya nike tace;"Audu kaga yadda suke kallo na kuwa?"

Audu baiyi magana sai dariya da yake man.

Ganin Samari biyu daga cikin wadan chan sun nufo yasa na tabo Audu nace;"Audu yi shiru gasu nan sunzo suce suna so na idan sukaga muna dariya zasu raina mu kaga kuma idan nayi saurayi mun huta dan zai dunga zuwa fira yaban kudi kamar yadda ake ma Samira"

"Kai haka ne kamar Samira kenan nagane nabar dariya"

Nace;"Yawwa d'an Kanena shiyasa nike son ka kana da ganewa yanzun mu shiga cikin lungun nan kaga zaifi dadin fira saboda nan kaga mutane na giftawa zasu saka mana ido"

"Hakane muje"

Cikin wani dan lugu muka shiga sai kara gyarawa nake ina kashe ido waini budurwa hmmm.

Ina tsaye ko suka iso shi kuma Audu yana bakin lungun bai ganin mu.
"Yan mata sannu de"

"Yawwa"
Nace cikin wata murya da ban san inada itaba.

Dayan wanda yayi man magana yace;"Amman ba'a nan unguwar kike ba ko?"

"Eh mana muna gaba sosai daku chan gidan nan nazo talla..."

Rufe baki nayi tare da tunanin maganar Samira ba'a surutu sosai a gaban Saurayi gashi ni har na manta na dauko wani zancen, Mtsww surutu bai yiba gaskiya shiru nayi ban karasa ba.

"Kai wannan kudin fa aiken ki akayi?"

Murmushi nayi kana nace;"A'a kawai de Baban mu ne ya bamu mu sayi Alawa"

"Tofa wannan duk na Alawa ne?"

"Eh Baban mu Maikudi ne a bisa kudi ma muke kwana"

Kallo na su duka sukayi daga sama har k'asa kana dayan yace;"Kawo na kirga naga Nawa ne?"

Wanda ke maganar yace haka shi kuma dayan sai waige-waige yake.

Banyi wani dogon tunani ba na mika masu ina ya tsina fuska ni diyar Maikudi.

Wanda ke waige waigen naga ya duka kamar zai gyara takalmi aiko yana dagowa ya watsaman k'asa a ido.

Wani ihu na kurma saboda ban gani ina kiran sunan Audu.

Audu na zuwa yace;"Ummu lafiyar ki de mi sukayi maki"

"Audu! Audu! Kudi! Kudi! Kudi! Na shiga ukku na bani na lala ce yau sai Inna ta kashe ni wayyo Allah kudi na"

Nan fa na fara ihu ina buga kafa babu kowa saboda lungu ne bare wani yaban hakuri haka na mike muka fara tafiya nida Audu shi kuka ni Kuka.

A bakin kofar gidan mu muka iske Innar mu wani kallo da tayi mana saida muka sha jinin jikin mu.

"Munafukai ku tsaya nan"

Nan muka tsaya mu duka jikin mu kyarma yake.

Zuwa tayi a gabana ta miko man hannu ina kudi tallar kuma ina robobina dana ara maku?

Audu yace;"Wallahi Inna itace taja aka amshe kudin"

Nan Audu ya fadama Innah yadda akayi.

Aiko nan ta makaroni ta shigo dani gida nan na iske yan Uwana na kusan goma sha hudu wanda kusan kowa ne da Maman shi kuma kowa ne shike cida kan shi.

Nan ina ta fara dukana sai data ga ban numfashi kana ta kyaleni.

Bude ido nayi naga Audu kusa dani yana bacci ya aza kanshi a bisa jikina, Mikewa nayi zaune lokacin dare ya raba tsakiya tada shi nayi muka koma daki na dauko mana tabar man mu muka kwanta kamar yadda sauran yan Uwana keyi kowa da dan Uwan shi wanda suka hada Uwa yake rayuwa mune Kananu nida Audu amman babu mai taimaka mana.

Tunda Safe muka tashi nayi Sallah na dawo na zauna Audu kuma ko Sallah baiyi ba Wai idan ya tashi juwwa yake gani saboda yunwa muna nan zaune Inna ta dama Kunu Audu yaje wajen ta yace;"Inna dan Allah ki dan mani Kunun nan yunwa nake ji kamar zan mutu"

"Ka mutu Uwar ka kayi ma asara su Samira ma dakaga na basu Uwar su tazo ta basu dari biyu shine muka hada muka sayi gero toku Uwar taka tunda ta tsallake ta barku har yau bata waiwayo kuba yanzu shekara Goma kenan haka kuma danginta ko kare babu wanda ya taba zuwa dan haka idan ka mutu ita data haife ka kayi ma asara koda yake bata da asara tunda ba son ku take ba dan idan tana son ku tazo tagan ku ko dangin ta, Idan ka matsaman nan zan bige ka"

Shiru nayi ina kallon sauran yan Uwana wasu kusan duk wata sai sunga Mahaifiyar su wasu kuma har hutu suke zuwa idan zasu dawo hadda sabon din ki.

Shiru nayi ina tunanin mu miyasa Mahaifiyar mu bata taba zuwa ba haka dangin ta? Kenan maganar Inna gaskiya ne bata son mu? Lallai bata son mu.

Lokaci daya nima naji bana son koda ganin ta ne ada kullun cikin saran ganin mahifiyar mu nake amman a yau na fidda rai kuma na fidda ta daga rayuwata nida Audu zamu fara rayuwa da sunan marayu daga yau bamu da Uwa a duniya.

Mikewa nayi dai-dai lokacin da akayi Sallama yaron yace;"Ana kiran Kamilu inji Kanin Maman shi"

Kallon Audu nayi da bakin shi ya bushe na kama shi nace;"Muje"

Wani kallon banza Inna tabini da shi.

Koda muka fito muka iske Yaya Kamilu shida Kanin Maman shi suna wasa suna dariya da d'an Kanin Maman shi(Abokin wasa)

"Ummu ina zaku tunda safe?"

"Zamuje nan baya zamu dawo"

"To sai kun dawo"

Bance komi ba muka wuce muka kama titi muna tafiya duk da Audu da kyat yake tafiyar wasu lokuttan saina kama shi.

Audu zama yayi kana yace man"Nifa Ummu Sata gaskiya zan fara"

Zaro ido nayi nace;"Babu kyau kada ka kara fadar hakan kaji ko"

"To nide yunwa nakeji kuma babu mai bamu, Yaya Sabi'u da yake Sata kullun ba gashi nan da kudin shi ba"

Zama yayi a bakin hanya yana kakarin Amai nanko ya fara Aman jini.

Kuka na aza mai sauti ina kiran sunan Audu shi kuma yana cewa;"Ummu abinci! Ummu abinci"

Kuka na aza ina bin mutanen dake wuce ina cewa;"Dan Allah ku taimaka ku bamu abinci kada Kanena ya mutu"

Babu wanda ya kulani wasu ma ture suke kada na taba su.

"Audu muje ga Chemist chan su baka magani"

Kama shi nayi jikina sai kyarma yake na dauke shi muka nufi wajen muna zuwa na aje shi daga gefe na shiga wajen kayatuwar wajen yasa ni rude da kyat na iya magana nace;"Dan Allah kuba Kanena magani Aman jini yake"

Babu wanda ya kulani sai wani da yazo wuce kana yace;"Yarinya mi kikeyi nan tafi gida ko na maki allura"

Ya fada yana murmushi nan na fada mashi abinda ke faruwa biyoni yayi muka fito yana duba Audu yace;"Yunwa ce tafi ki samo mashi abinci idan yaci saina baku magani kinji"

To! To! Audu jirani kaji zan dawo da abinci"

Audu bai ko iya magana saboda jikin shi ya saki, Mikewa nayi cikin sauri nabar wajen.

Tafiya na danyi kadan kana na hango Maishayi wajen naje ina kallon yadda matasa ke kalaci wasu Tea da bread wasu Indomie da kwai naje nace;"Dan Allah ku taimaka ma Kanena abinci zai mutu idan bai ci ba, Bamu da Uwa mu marayu ne"

Nan suka fara korata na tsaya daga gefe ina kallon ko akwai wanda zai rage ganin kowa na cinyewa ya tashi yasa jikina ya mutu na fara hawaye.

Chan wani yazo aka dafa mashi Indomie da Kwai ya amso ya aje bisa tebir yaje wanke hannu ganin ba kowa ko nayi sadab -sadab na dauke plate din na zura da gudu.

Koda ya waigo ba Indomie chan ya hangoni ina gudu da abinci.

Aiko ya biyo ni yana cewa;"Barauniyar Abinci jama'a ku kama mani"

Haba kara gudu nayi wajen Audu kawai nake son in isa.

Murmushi nayi ganin na isa wajen runtse ido nayi hawaye dadi.

Karab! naji na hade nida wani cikin sauri na bude idona.

"Wayyo Allah abinci na"

Nan na fara kwashe na saman na dauke kwan saboda bisa takalmin mutaunan ya fadi takalman kuma sabbi ne sai daukar ido suke hakan yasa na kwashe.

Sunan Audu kawai nake kira ina dagowa mukayi ido hudu da mutunan dana fasa ma Glass din mota shine na juyema Indomie yanzu a kaya.

"Barauniyar abinci Allah ya kama ki"

Dai-dai lokacin da wanda na daukar ma abinci shi kuma ya iso ina waigawa naga Maimashin din jiya ne da muke ma dariya wanda ya biyo mu.

Shima kallon mamaki yake man ya bude baki zaiyi magana.........

MARYAM ANKUDIE {Qurrah}

Continue Reading

You'll Also Like

82.3K 193 29
မူရင့းနှင့်သက်ဆိုင်သူများ credit
174K 2.2K 30
mikha and aiah found out na mag tita sila!!
307K 4.9K 61
𝐈𝐍 𝐖𝐇𝐈𝐂𝐇 𝖬𝖺𝗂𝗌𝗂𝖾 𝖦𝗋𝖾𝖾𝗇, 𝖺 𝗐𝖾𝗅𝗅-𝗄𝗇𝗈𝗐𝗇 𝖼𝗈𝗇𝗍𝖾𝗇𝗍 𝖼𝗋𝖾𝖺𝗍𝗈𝗋 𝗂𝗌 𝖽𝖾𝗆𝖺𝗇𝖽𝖾𝖿 𝗍𝗈 𝗉𝖺𝗋𝗍𝗇𝖾𝗋 𝗐𝗂𝗍𝗁 𝖬...
33.6K 2.9K 26
ඒ ආත්මෙ වගේ රූපෙ නොතිබුනත් අපි අපේමයි ඒ කෝපි ඇස් ඒක සනාත කරනවා.