ASMA...

By Zaynab_yusuf

181 13 3

Alokuta mabanbanta idan na duba rayuwata,ina farawa ne daga lokacin da iyayena suka rasu,daga lokacin da na r... More

Episode One-The beginning and end of me.
Episode three-First Encounter
Episode Four: Obsession
Episode Five:Dilemma
Episode Six:Heekmah

Episode Two: Affairs of the Heart.

22 2 0
By Zaynab_yusuf




Episode Two: Affairs of the Heart.

   Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke alokacin da idanunshi suka sarƙe acikin na Kiki,tafiya take cikeda yauƙi jikinta sanye da white top da dogon crazy pencil jeans black color,hannunta na dama riƙe da files, yayinda na hagun ke riƙe da wayarta ƙirar Iphone 13pro Max,Tsayuwar shi ya daidaita yana ƙara kallon fuskar ta,wacce take fitar da yalwataccen Murmushi,saida ta ajiye files ɗin sannan tayi taku biyu backward tabashi wata kyakkyawar hugg,ajiyar zuciyar dabai shirya ba ya sauke even though ko riƙe ta baiyi ba,hasalima hannayen shi na rungume asaman ƙirjinshi,bakin ta mai girma wanda yasha nude lipstick ta ɗora asaman kunnen shi tace"good morning starshine,the Earth says hello"tareda manna mishi light kiss akan ears ɗin.

Yace"morning"tareda ɗaukar file ɗinda ta ajiye,saurin riƙe hannun shi tayi,tace"baby you look pale,meyake damunka? bakada lafiya ne?".samun kanshi yayi da cewa"I'm just overthinking akan mafarkin danakeyi these days". Yafaɗa with his well arranged extra white teeths,ƙamshin breath taking mouth wash ɗinshi mai ƙamshin gaske yasa ta lumshe idanu sannan tace"karka damu,komai zai wuce,we should be more prayerful"cikin aminta da maganar ta yace"thank you".tareda komawa mazauninsa ya zauna,a kujerar dake opposite dashi ta zauna tana duba himilin files din dake jiran shi,and from all indications mafarkin na damun shi,miƙewa tayi tsam ta zagaya inda yake, tare da zama akan laps ɗin shi,hannayen ta dogaye wanda suka sha zirconia ring tayi cupping fuskar shi,tana kallon shi cikeda tsantsar tausayi,ƙauna, girmamawa da kuma mutuntawa,tace"bari na tayaka Aikin".bai ce komai ba illa kallon ta daya cigaba dayi kamar wani gaula, hannunshi na dama ta riƙo Wanda yake fari tasss,mai tsananin taushi da santsi,pen tasa mishi ahannun Sannan takama hannun nashi (kamar yadda ake koyama yara rubutu)haka tariƙa buɗe files suna signing papers ɗin da Yakamata,wanda bai kamata ba kuma su ajiye a gefe,duk da ita ke jan ragamar aikin amma He's very focused akan papers din,sunyi masu yawa kafin daga bisani ta ajiye pen din ta waiwaya tana kallon fuskar shi wacce take ahaɗe kamar hadarin gabas,cikin rashin son halin dayake ciki tace"baby Please,ka cire abunnan aranka, Focus on me and your work,munfi muhimmanci agareka koba haka ba?".

Gyaɗa kai yayi asannu yace"kiki koda nayi ignoring ɗin shi,yana matuƙar damuna, saboda jikina yana bani babban al'amari ne". tace"bazan yafe ma wannan mafarkin ba tunda yana sa ka cikin damuwa,i want you to worry about nothing and be happy forever".

Yace"You too". yafaɗa Da cute pink lips ɗinshi ƴan madaidaita masu shegen kyau,da kallo tabi lips ɗin tana haɗiye wani miyau mai ƙarfi,wanda da daƙyar ya iya wuce mata,tana bala'in son James,so na bugawa a jarida,irin son daya ke mamaye zuciya,domin bata ganin komai da kuma kowa sai shi, tana son tayi tasting bakin shi,tana son sun kasance tare da juna,amma takasa gane kanshi, domin ko sau ɗaya bai taɓa bari hakan ta faru ba,kamar ba namiji ba,duk wata seductive kwalliya babu wacce batayi but to no avail, ahankali take kokarin manne lips ɗinsu, bayan ta yi dabarar riƙe hannayen shi,tana sakar mishi wasu looks wanda suka daskarar dashi awurin,lips ɗinta na ƙasa ne ya haɗu da nashi na sama,atake sukaji wani electrification,ya runtse idanu tare da fizge hannun shi ɗaya ya yi shunning kiss din as usual,sosai hakan ya ɓata mata rai,duk ba ba yau bane karo na farko dayake mata hakan,amma na yau ɗin yafi tsaya mata arai sannan yafi mata takaici,saide yadda take bala'in son shi baze bari ta iya faɗa mishi magana ba,haka nan sonshi baze bari ta ɓata mishi rai ba.

Dan haka saita miƙe tana gyara zaman jeans ɗinta,wanda ya fito da Asalin figure 8 dinta,wanda suke madaidaita,bai kalli gefen datake ba domin ya tabbatar da biyu takeyi.batareda tace komai ba ta fita daga office din,lumshe idanu yayi yana jin wani abu na tsarga mishi tun daga maɗigar kanshi har tafin ƙafafuwan shi, cappuccino coffee as usual ya haɗa yana kurɓa da zafin sa, domin shine ke ɗebe mishi kewa akodayaushe.

Afusace ta koma office ɗinta,wanda yake akusa dana James,takalli Daniel cikeda ɓacin rai bayyananne sannan tace"lafiya?meya kawoka office ɗina?". ƙaramin Murmushi yayi sannan yace"nazo ne na duba ki, fatan kina lafiya".

Cikeda takaicin kalaman shi tace"nida nake tare da Chairman (James )ai dole na kasance cikin ƙoshin Lafiya".ta watsa mishi magana kai tsaye,saide ko kaɗan baiji haushi ba,yace"kiki kenan".tareda miƙewa ya fice daga office din,a Bakin ƙofa suka ci karo da Fancy,wacce shigowar ta kenan,ko kallo bai isheta ba tamishi banza ko amsa gaisuwar shi batayi ba ta shige ciki,a fusace kiki ta ɗago saide ganin Fancy ce yasa tasaki Murmushin jin dadi tareda saurin miƙewa suka rungume juna,Fancy da Kiki are best of friends tun ƙuruciya, hasalima Fancy ce tasa James ya ɗauki Kiki aiki sannan take iyakar kokarin hada su,Saboda yadda kiki ke masifar son James.

ASMA

  Fahimtar cewa kuka bazai min maganin Matsala ta ba yasa na goge hawaye na,amma ko ba komai kukan ya yaye min kaso mai yawa na cikin damuwa ta,saide ya barmin ciwon kai da zazzabi wanda nake fatan idan na watsa ruwa zan dawo normal,cire gown din atampar dake jikina nayi,na daura customised towel ɗina na Versace,wanda iyayena suka siya min tun suna raye,wanka nayi mai rai da lafiya da shower gel dina mai ƙamshin gaske na Makari,ina fitowa na tsaya gaban closet ina tunanin kayan dazan saka,even though yanzu ban fiye banbance colors ba saboda yadda zuciyata take baƙiƙiƙirin,banda preferences banda zaɓi,ina aiwatar da lamurana kai tsaye,wata nude gown na ɗauko wacce ta sha stones madaidaita,babana ne ya siyo min sanda yaje Uk,daga sama tana da kauri zuwa waist,daga waist kuma zuwa kasa transparent ce,saida nasa dogon skin tight nude color wanda shima kyauta ce daga wurin babana, lokacin dazai siya rigar ya siya dashi, ina jin kaina cikin nustuwa aduk sanda zan saka kayan da iyayena suka siya min, musamman da hannun su,sune Abinda Ya rage min aduniya wanda zan iya sadaukar da rayuwata Saboda su,Yes i can trade my Life for them.

Kasancewar cikin yanayin sanyi ake yasa na shafa cream dina na Makari as well, kafin daga bisani na feshe jikina da Versace perfume wanda shima baba ne yafara siya min shi lokacin ina SS1,And I fell in love with it, shiyasa har yau banda turaren daya fishi,Turban nude color nasa as well sannan na sanya black colour Hermes flat shoe wanda shima kyautar baba ce daya je Paris ya siyo min,haka kawai nakeson fita,ina buƙatar fresh air, cikin takuna mai ɗaukar hankalin mai kallo na fita,a falo na tarar da Salman da Mommy suna zaune, tattaunawa sukeyi gameda finlak industries mallakin mahaifina(wanda yake a matsayin gado na)ganina ne yasa mommy canza akalar maganar,ta saki Murmushin yaƙe tare da faɗin"Asma kin fito?dama yanzu nake son kiranki nasan boredom ya isheki".Duk Da ba tsakani da ALLAH tayi maganar ba,nace"haka ne,fita ma nake son Yi anjima".

Tace"yawwa,let me know when you're leaving".bance mata komai ba illa Kai dana gyaɗa mata,Salman yace"Asma how far?ya kike?"cikin son basar dashi nace"fine"kallona yakeyi har na ƙurema ganinsa, Kitchen nashiga domin yin Lunch kamar yadda Daddy ya maida ragamar girkin akaina,Saliha ɗaya daga cikin masu aikin gidan ce ta shigo, lokacin ina ɗauraye tukunya,tace"mommy tace kibar girkin "cikeda mamaki na kalli salihan sannan nafita batareda nace komai ba, mommy ce ta tabbatar min da ingancin maganar sai na jinjina kai ahankali na koma ɗaki,domin alokutan mabanbanta ina mamakin halayyar mutanen gidan, musamman Daddy Da son zuciya ya rufe mishi idanu,baya ganin gaban shi bare bayan shi, tamkar mai tafiya ne acikin duhu baisan inda yake saka ƙafafun shi ba,na sauke ajiyar zuciya domin mommy badaga baya ba itama,sun samu saɓani mai girma da mama lokacin tana raye,kuma mama mace ce mai tsayawa akan gaskiyar ta kai da fata,dakuma son Da Kakarmu hajjo ke ma mama fiyeda yadda take ma mommy, da arzikin da ALLAH yaba babana mara misaltuwa,wannan dalilin yasa mommy ta tsani mamana domin tana ganin tayi mata zarra ta kowacce fuska.

Idan na kalli Salman,yana tafiya ne abisa turbar Da Mommy ta ɗora shi akai, halayen ta gabaɗaya babu wanda Salman ya bari,saide ba lallai ka fahimci hakan ba, Saboda iya taku dakuma ilimi mai zurfi da yayi,bakamar mommy ba wacce ba ko yaushe take zurfafa tunani ba.

Yusrah ƙawata ce, Aminiya tace,kuma shaƙiƙiya tace,ita kaɗaice ta damu da damuwata,take son wanzuwar farin ciki acikin rayuwata,Wayata ƙirar Iphone 11 pro max wacce babana ya siya min yana gab da rasuwa na ɗauka dake gefena,tun jiya ban taɓa wayar ba sai yanzu, saboda banga amfanin ta ba adaidai wannan lokacin,numbar Yusrah nayi dialling ina gyara kwanciyata, lokacin tana zaune a office tana tunanin Halin da Asma ke ciki,cikeda farin cikin ganin kirana,tayi saurin ɗauka,"Hello ƙawata,fatan kina lafiya?".

Ajiyar zuciya na sauke sannan nace"kina office ne?"tace"ehh my dear, I'll be expecting you pls".nace"yh zanzo anjima Insha Allah".ina gama faɗin haka na kashe wayar tare da lumshe idanu.

Misalin ƙarfe huɗu na yamma ina kan sallaya na idar Da Sallah,hannu na biyu asama,hawaye Masu ɗumi na zubo min,ina nema ma iyayena gafarar Ubangiji,na daɗe sosai kafin daga bisani na miƙe ina goge hawayen dake zubo min, kasancewar nayi wanka yasa na shirya cikin black and golden gown ta Versace,wacce ta dace da medium figure 8 feature ɗina,black veil ɗan madaidaici na yafa sannan na saka Black color flat shoe fendi Da Fendi slingbag as well, Mukullin mota ta ƙirar Land cruiser na ɗauka,saida nayiwa mommy sallama sannan nafita tunani cike da zuciyata, driving nakeyi cikeda sanyi har na ƙarasa MVO communication company Dake Lekki phase 2 inda Yusrah ke aiki,ma'aikata ce mai kyan gaske wacce zata burgeka akullum,Kuma mai kampanin ke gabatar da komai cikeda tsari yadda Yakamata,shiyasa kampanin yayi fice saboda reliable network,ga data package's dinsu masu sauki da durability, kasancewar parking lot ya cika da motoci yasa nayi parking Mota ta awani keɓantaccen wuri wanda akai parking G-box,motar danake matukar ƙauna aduniya,saide ayanzu ko kallo bata ishe ni ba domin komai yafita akaina,shiga ciki nayi na hau elevator, Mutum ɗaya ne aciki ya juya baya, jikin shi sanye da dark blue ɗin suit,gashin kanshi akwance sai kyalli yake da sheƙi,atake naji gabana yayi mummunan faɗuwa,saina jingina tareda lumshe idanu na saboda yadda ƙamshin turaren shi ya danne nawa, ahankali kuma cikeda sanyi ya juyo,idanun mu suka sarƙe dana juna, kallon cikin ido na yakeyi kamar yau yafara ganin halittar ɗan adam,sai nayi saurin  kawar da kaina daga kallonshi,hakan ya bashi damar kallona tun daga tsakiyar kaina har zuwa ƙafata......,








ZAYNAB MOHD YUSUF✍🏼✍🏼✍🏼

Continue Reading

You'll Also Like

487K 17.2K 195
(Fan TL) Won Yoo-ha, a trainee unfairly deprived of the opportunity to appear on a survival program scheduled to hit the jackpot, became a failure of...
140K 6.8K 28
Hooked onto drugs, no family, no guidance or sanity until she met HIM. Cover Creds: @Triceynexttdoor ❤️ -BLICKY.
58.7K 1.4K 40
standalone ~ mafia siblings series "You can't make me stay here! I will get an emancipation." I yell. Flashbacks of the gun in my hand, the almost-de...
591K 16K 80
A butler was the job description. Do what he wants. Get what he desires. That's all I have to do, but suddenly, I am thrown into a completely differe...