ZAFI BIYU

By Qurratou

478 9 4

Labari ne dake dauke da sark'ak'iya da kuma dana sani a lokacin da wuri ya k'ure. More

ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFIE BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
MAKANTAR ZUCI!
MAKANTAR ZUCI!
MAKANTAR ZUCI!

ZAFIE BIYU

39 1 0
By Qurratou

Z_B

Written by_Qurrah
Wattpad_Qurratou

Page_5

GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION ✍️

Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Gefen wata katuwar bola muke zaune cikin wani Kango, Tagumi nayi ina tunanin yadda zamuyi da sauro zuwa anjima, Gashi  ba'a son mai ciki sauro ya cije ta toni gani a gidan shi.

Ina zaune har dare ya fara nan naga sauran yan Uwana masu bara sun tashi kowa yayi hanyar samun abincin.
Mikewa nayi da katon ciki ina kallon Babah Indo dake kirga kudin ta gasu nan tuli guda a gaban ta mafi yawa duk chanjine.
Mamaki nake yadda ta samu kudin Kuma duk a cikin Bara kasa daurewa nayi nace;"Babah Indo ko kina wata sana'a ne naga kin tara kudi da yawa haka"

Murmushi tayi kana ta fara maida kudin cikin wani ma'ajiyar kudi dake a jikin ta saboda mutane sun fara dawowa kana tace;"Yarinya kenan Bara da kika ganta kudi take kawowa harmade tsallaken Nigeria ada ban yadda ba lokacin da k'awata ta fadaman saida na fara kana"

Shiru nayi ina tunanin nima yanzu haka zanyi kenan?

"To Babah Indo taya nima zan samu kudi?"

"Kada ki damu ki bari gobe mu isa Legos zan nuna maki yadda ake samun kudi da Bara yanzude ga Naira d'ari ki sawo dankali kici gashi chan bakin titi su Hanne sun sawo"

"To nagode Babah Indo"

"Basai kinyi godiya ba duk abinda na kashe maki idan muka isa Legas zaki nema ki biyoni"

"To shikenan duk da haka nagode"

Tashi nayi nabi Hanne muka nufi wajen wani mutum wanda ke soya Dankali da doya da kwai.

Muna isa suka gaisa da Hanne na mike kudi ya zuba mata Dankali sannan ya saka mata doya da kwai a cikin.
Murmushi tayi kana tace;"Nagode "
Tana maganar tana kashe ido kamar tana magana da Mijin ta.

Mika mashi kudina nayi naira d'ari tare da nuna mashi Dankali.
Zubaman yayi kana nima ya saka man Doya da Kwai amman kadan ba kamar na Hanne ba, Godiya nayi kana na mika hannu zan amsa.
Abin mamaki kawai sai mai Dankali ya rike hannu na tare da kashe mani Ido.
Zame hannu na nayi Danklin ya fadi k'asa da Doyar k'asa cikin bacin rai nace;"Minene haka nazo siyayya zaka rike mani hannu na?"

Hanne ta rike man hannu duk da bata jin mina ce saboda bata jin French gaisuwa kawai ta iya amman tasan fada nake.

"Malama dakata Kada ki tara man mutane anshi kudin ki bana saidawa kuma Kada ki k'ara dawowa"

Amsar kudina nayi ina tsoki kana na juyo na taho nabar Hanne tana bashi hakuri.

Ina dawowa na zauna cikin fushi ina tsoki Babah Indo na tambayata Lapia ai ban bata amsa ba saboda yadda raina ya baci Hanne ce ta shigo nan ta fadi abinda ya faru.
Kawai sai naga matan nan na dariya wasu kuma na tsoki irin na basu haushin nan.

Kama hannu na Babah Indo tayi tace;"Beedah Mai doya bashi da laifi kece mai laifi, waya  gaya maki a banza ake samun kudin bari nayi maki misali da Hanne, Hanne da kika gani yarinya ce Haihuwar ta biyu suka rabu da Mijin shine Maman ta ta kawo ta wajen Talatu  kinganta chan itace k'awata wannan shine zuwan ta na farko amman saikinga dukiyar da zata koma ma mahaifiyar ta da ita sannan da kayan amfani kuma ba'a Bara kade ta sami wadan nan  abubuwan ba , d'an haka idan zaki dage ki dage kibar wannan sakarcin cikin jikin ki bazai hana maki komi ba d'an haka ki shirya idan mukaje Legas yanzu na maki Uzuri saboda baki san kan harkar ba"

Hanne ce tazo inda nake ta miko man Dankali biyu da doya guda na amsa nayi godiya.

Bayan na gama ci na kalli Babah Indo nace;"Babah amman miyasa bazaki ba Hanne shawara ba akan ta zauna gida tayi sana'a zaifi naga da karfin ta"

"Hmmm yarinya kenan baki san Nigeria shiyasa kika ce haka, Hanne taban labari bayan mutuwar auren ta yaran ta a hannun suke Maman ta bata da kafafu ta tsufa sosai yan uwanta kuma basu da karfin cidasu nan ta fara sana'ar Awara a Nigeria mai karamar sana'a da wahala ta daure saboda yau idan kaje sayen waken gobe idan ka koma ya kara kudi haka Man suyar to daman Jarin nata na kayan dakin tane data saida daga karshe de ya mutu shine dalilin da yasa ta biyo mu"

Shiru nayi lallai Hanne taban tausayi amman wannan ai bai zama dalilin da zaisa da kuruciyar ta ta fito Bara ba.

Nan naga sun fara daura Net ina nan zaune saiga Hanne tazo ta kama hannu na wajen Net din ta ta ajeni tare da yiman nuni dana kwanta kwanciya nayi itama ta kwanta saida kowa yayi bacci naga ta mike ta nufi fita cikin kangon da muke zaune ruwa naga ta samu ta wanke jikin ta kana ta fita binta nayi a baya sai sauri take chan naga ta kwankwasa wani shago banga wanda ya bude mata ba saide naga ta shiga dawowa nayi nashiga Net din na zauna amman nakasa bacci saboda ina tunanin taya zanyi wannan rayuwar a Legos??

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

"Malama nace maki ki fita ko, ko bakijin abinda nake cewa"

Juyawa tayi  ta fita tana mamakin miyasa Hanah kuka hadda sauti da Dad din Hanah sukayi kicibus nan yace yana son zasuyi magana fada mata abinda zatayi mashi yayi.
"Bakomi zanyi insha Allah"
Tana fadar haka tabar wajen shima part din shi ya koma.

Da kayan jikin ta tayi bacci saida safe tayi wanka ta nufi part din Dad din ta tana zuwa ta iske yana waya Zama tayi kusa dashi har ya gama.

"Dad ina kwana"

"Lapia kalau Princess ya jikin ki?"

"Naji sauki sosai Dad, Magana nazo muyi"

"To yanzu de time din breakfast ne kibari mugama sai kuyi maganar ku taso"

"Amman Mom ina son muyi maganar yanzu tun jiya da ita nayi bacci"

"Ban yadda ba muje chan kunyi maganar"

Badan taso ba ta tashi suka nufi dinning area suna zuwa taja Sit ta zauna Dad din da kanshi ya zuba mata breakfast ya tura mata batayi gardama ba ta fara ci.

Saida suka gama kana tace;"Dad akan maganar karatu ne ina son zanbar k'asar ne"

"Miyasa zaki bar k'asar bayan ba'a gama maki shirye shirye ba sannan ko zabar School din da zakiyi bakiyi ba, Taya zan barki kibar kasar"

"Dad idan kana son farin cikina kabarni na tafi please"

Tana fadar haka ta mike dai-dai lokacin da Nanny tazo hada kayan da sukaci abinci.

"To shikenan zanbarki amman kamin ki tafi saura two days Birthday din ki kibari ayi Kinga Mom din ki tayi hidima"

"Bazan iya zama ba inason nabar k'asar yau ko gobe"

"To amman Hanah taya zakibar k'asa babu shirya-Shirye taya ma zaki bar kasar a yau ko gobe?,"

"Amman Mom Dad ai wannan ba komi bane wajen shi yanada hanyar da zan fita k'asar"

"Zan duba amman bani two days"

"Okay thank you Dad"

Tsayawa tayi bakin kofar dan tasan Nanny din ta sai tasa baki ganin batace komi ba ta kwashe kaya tabar wajen yasa itama tabar wajen.

Tana koma ta fara hada kayan ta dan tasan wannan matar dake bata matsala yau bata bata bata ba.
Wayarta a kashe take tun jiya ko Friends din ta a yanzu bata bukata tafi son zama ita kade a cikin daki.

✨✨

Hakeem da Imran suka fito yaje da traveling bag wajen Annie suka zo suka gaisa.

"Dan Allah ku dawo akan lokaci saboda ku hallaci meeting din da za'ayi ranar Friday"

"Okay to shikenan Annie sai mun dawo"

Addu'a tayi masu tare da fatan alheri har bakin get din part din su ta rako su inda mota take jiran.

"Hajiya Babba burina biyu a rayuwa idan kika cika man shi to kin gama man komi, Ina son auren Hanah ina son Sarautar gidan nan a lokaci daya, Inason na zama mai fada aji na zama abokin sarakuna da manyan kasar nan ya kasance sunajin magana ta"

"Wannan baki daya zaka same su a cikin sauki Auta na ka kwantar da hankalin ka su duka kamar anyi angama ne"

"Yawwa Hajiya wai yaushe Uncle zaidawo ne ina son ayi komi a gaban sa hakan zaisa komi ya tafi dai-dai"

"Munyi waya dashi wai kuma yanzu ya koma Turkish ban son mi yaje yi chan ba amman idan yasan ka samu mata da gudu zai dawo"

"Yawwa bari na kira shi a WhatsApp zaifi na bashi labari komi"

"Wannan tsakanin ku idan ma ya dawo nasan a Zariya zai sabka saboda Maimartaba baijin dadi amman nasan idan yaji labari zaizo nan "

"Ai bari kawai naje na bashi labari"

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Safiya nayi muka fara hada kayan mu duk dani bana kaya na Babah Indo ne nake taya ta wani kosai ne Babah Indo ta miko man guda ukku tace;"Naira Hamsin yake saiki saka shi a cikin lissafi"

Amsa nayi tare da godiya Lallai kam Allah ya kawo ni Anya matar nan tanada Imani kuwa kosen Hamshin ace hadda shi zan biyata lallai kam koda da halin sa amman son kudin ai yayi yawa.

Bance komi ba muka tashi wasu duk sukayi wanka a cikin wannan kangon nima nayi maida kayana, Hanne ce tazo ta miko man kayana tayi man nuni dana cire wadan nan.
Godiya nayi na amsa na cire kayan tane taban wankakki riga da Zane ita ta daura man zanin haka nake tafiya dashi ba sauri kamar zan fadi ganin haka yasa na linkashi biyu na daura kafafu na duk a waje.

Daukar kayan Babah Indo nayi mukaje wajen motar wata katuwar mota ce mu duka muka shiga Babah Indo ta biyaman kudin mota.

Hmmm ashe banga wahala sai a hanyar LEGOs to Cotonou hanyar bata kyau ga mototi akan ta sunyi yawa idan muka fada rami sainaji cikina ya juya haka mukai ta wahala ko ruwa bamu samu muka shaba.

Gashi tafiya kadan sai mun hadu da jami'an tsaro wasu sai bin cika kayan mu wasu kuma mu wuce mune bamu iso Legos ba sai yamma.

Mota muka dauka haya ban san inda zamu ba saide duk wahalar da nake ciki bai hanani kallon mutanen Legos ba ina raba Ido ko zanga Baban Baby naba .

Wani waje aka ajemu naga sun hadu da yan Uwan su sai gaisawa suke suma Hausawa ne nan suka amshi kayan su muka nufi inda zamu sabka.

A karkashin wata Gada muka sauka inda sauran dayar tawar suke.

Gabana ne ya fadi nace;"Hausawa kenan su duka Mabarata ne yanzu kenan Family din Baban Baby na suma suna bara? Kilama akwai su nan ci"

Baki daya jikina yayi sanyi kallon inda muke nayi buhu ne aka shimfida mana wajen wari sai toshe hanci na nakeyi.

Ciki na nayi yana juyawa addu'a na fara ina rokon kada na haihu anan.

"Beedah zama bai ganki ba tashi muje na nuna maki inda zaki samu kudi saboda kwana biyu zamuyi ranar Jummu'a za mubar nan"

"Haba Indo baki ganin halin da take ciki"

"Dakata Talatu wannan yarinyar da kika gani saida mukayi ajanda da ita kana na yadda ta biyoni haka kawai ban san yarinya ba ta zame mani wahala sisina bata magani banyin asara d'an haka tashi maza"

Duk wanda ke wajen ya tausayamani Saboda halin da nake ciki.

"Babah Indo bari na baki kudin motar ki saboda Beedah na bukatar hutu ta wahala a hanyar nan da kyat take nishi kinya ya kamata ta huta"

Hanne ta fada tana dafani.
"Bani kudin dana kashe mata idan kina son ta huta"

Hanne ta kwance bakin zanen ta taba Banah Indo Rabin kudin da take bina

Nan Babah Indo tayi man bayani yadda sukayi da Hanne kana tace gobe sainaje na nemo na motar zuwa Kano da sauran.

Nayima Hanne godiya sosai har na rasa taya zan gode mata ma naso ace Hanne najin yarena da nayi mata bayanin komi.

Anan kasan gadar mukayi bacci yau ma a Net din Hanne na kwana tunda safe karar mota da mashin ta tadamu mukayi mike muka kwashe shimfida a karkashin gadar naga masu abinci sun fara kasawa nan naga masu Mashina sun fara zuwa siye duk mai mashin din da yazo sai ya gaisa dasu Babah Indo a cikin harshen Hausa abin Hausawa naban mamaki kenan har mazan su nan suke zuwa neman kudi toko Baban Baby na nan yake zuwa Shima?

Hanne ta dan man abincin da ta siya nashi kana Babah Indo tazo tace;"Beedah tashi kije zuwa neman kudin motar ki da sauran kudina"

Tashi nayi da kyat kana muka fara tafiya a cikin burnin Legos kyaun burnin yasa ni sakin baki sai Babah Indo ta rikoni dan har titi nake hawa ban sani ba.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Kyataccen Hotel su Imran suka sabka Safiya nayi Imran ya nufi office din shi domin aje aiki sannan ya dauki sauran kayan shi.

AbdulHakeem Friend din shi ya kira Muhsin tare sukayi karatu a BUK kamin yaje Saudia shi kuma iyayen shi dama Legos suke zaune amman asalin yan Jigawa ne yana zuwa suka fito domin ganin gari.

Tsoki yaja ganin yadda Hauswan mu ke yawo a kan titin Legos suna Bara.

Muhsin yace;"Malam lapia de naji kana tsoki?"

"Mtsww Muhsin bakomi"

"Fadaman de yanayin garin ne bai maka ba yau akwai rana inaga muje muci abinci kawai zuwa anjima sai mu fita zai fi dadi"

"Okay"

✨✨✨✨✨

Abinda keban mamaki duk inda mukaje hantarar mu ake Ba'a son mu bare a bamu sadakar.

Nide tun ina tafiya da karfi a jikina har ya zama babu wani karfi a jikina da kyat nake tafiya ga cikina ina jina alamun yana juyawa.

Runtse ido nayi Saboda azaba na durkushe wajen nace;"Babah Indo ki taimaka man yunwa nake ji bana iya tafiya"

"Kutumar Uba ke jini da yarinya saida nace ban zuwa dake dan kada ki zaman man kaya kikace kina iyawa dan haka wallahi maza ki tashi muje"

Hanne dake tsaye tace;"Babah Indo ciki ne fa jikiin Yarinyar nan kuma mu duka mun dauke shi mun san yadda yake dan Allah kibar ta hada hakanan nifa na fara tsoron kada yarinyar ta haihu a hanya saboda jiya a hanyar nan tasha wahala sosai kawai dan tanada karfin hali ne"

"Idan ma zatayi kokari  ta tashi ki tashi dan idan kika haihu anan to a titi zaki haihu"

Mikewa nayi ina cije baki saboda yadda nakejin azaba.

A bakin wani wajen cin abinci muka isa muna zuwa Security din dake wajen ya fara korar mu amman duk da haka mun ki tafiya saima wani wuri da muka zauna wanda duk wanda zai wuce saiya ganmu.

"Wasu matasan samari ne guda biyu suka zo shiga daga ganin su kaga Hausawa cikin sauri Babah Indo ta tashi tace;"Ke dallah tashi ga muje"

Yadda ta hizgeni ya sakani k'ara hakan ya jawo hankalin su wajena.

"Subhanallah "

Muhsin ya fada yana kallon su yasan Hausawa ne dan suke Bara a Legos.

"Alhaji a taimaka domin Allah, Sadaka guziri ce"

Babah Indo ta fada tana mika masu hannu tare da ingizani inyi magana.

"Al...ha..ji"

Nace da kyat saboda ban san ta yadda zan fadi kalmar hausa ba.

"Sannu" Muhsin ya fada.

Hannu yasa a Aljihu ya dauko kudi yan dubu-dubu ya bamu guda ukku.

Karab Babah Indo ta amshe kudin nan, Nan ta fara godiya ta kirari sude suka shiga ciki.

"Babah Indo zanci abinci yunwa nakeji"

"Dami zakici abincin ne? Wannan kudin ai nawa ne saboda ni nayi Bara aka ban ke ba kasa magana kikayi ba waike Kinga Maza, yanzu muje gaba kiyi kokari ki samu kona abinci ne"

Raina baci yayi zanyi magana Hanne tace;"Amman Babah Indo mutanan fa saboda Beedah suka bada kudin fa dan su duka  kallon tausayi suke mata saboda abinda ke jikin ta"

"Malama dakata dakata daman kilbibi da sa ido yasa kika biyo mu saboda ai badake muke Bara ba"

Zanyi magana Hanne ta rikeni ta girgiza man kai nayi shiru.

Mikewa nayi rai bace na nufi titi saboda in samo abinda zan saka

Juwa naji na dibana ban ji karar mashin ba a baya na saide na ganni k'asa ya tureni.

Cikin sauri nayi saurin tashi amman kafata ta rike bawani ciwo naji ba dan mashin din kadan ya tabani kurjewa ce kawai nayi.

Cikin sauri maimashin din ya sabko suka kamani shida Hanne suka kaini bakin hanya suka zaunar Cikin sauri ya nemo ruwa ya kawo man yanata man sannu nida ban iya amsa saboda yunwa ta galabaitar dani.

Nan suka kamani muka koma wajen shimfidar mu duk wajen akwai mutane hakanan muka zauna abinci mai mashin din ya siyo mani hadda lemo abincin ma da nama nan da nan nacinye na kwanta nan nabarsu da Hanne suna fira sai yamma na tashi gab da magrib Sallah nayi kana na zauna.

Bayan isha'i saiga Maimashin din nan da abinci ya kawo man godiya nayi sosai saboda na samu sauki saima naji dadin da aka ban kadeni.

Babah Indo koya jiki bata hadamu ba nima ban mata magana ba.

Maimashin din nan ban jin mi yake cewa amman saide suyi fira da Hanne saide idan muka hada ido ya sakar man murmushi nima na maida mashi sai da daddare sosai wajen goma kana ya tafi yana daga man hannu nima na daga mashi hannu.

Tsoki Babah Indo tayi tare da tabe baki kana tace;"Bari kiji jibi zamu bar nan mun samu wata mota data kawo Shanu ita zamubi mu koma dan haka gobe kiyi sabbko ki samo kudin biyana sai wani langwabe wa kike bayan babu ciwon da kikaji gurjewa ce "

"Babah Indo Daman ba ciwon akeji ba cikin jikin ta yasa ake tausaya mata"

"Hanne na lura shishigin ki yayi yawa ki shiga taitayin"

Hanne batace komi ba daga nan haka wadan ke wajen basuyi magana ba saboda kowa tsoran masifar Babah Indo yake kuma itace shugaba.

✨✨✨✨✨✨

Dare nayi Imran da Hakeem suka je wajen cin abinci Hakeem sai juya abici yake ya kasa ci.

"Hakeem lapia de mike faruwa naga ka kasa cin abinci?"

"Mtsww Uncle dazun muka fita da Muhsin wajen cin abinci amman narasa miyasa baki daya titin nan garin nan Hausawa ne ke yawon Bara miyasa mutanen mu suke Bara??"

"Ohhh Daman shiya hana maka cin abinci kaman ta da wannan kaci abinci saboda lamarin ba naka bane"

Girgiza kai yayi ya cigaba da cin abinci amman akai-akai yana tsoki.

✨✨✨✨✨

Tunda safe na shirya ko takan Babah Indo ban biba muka fita Bara ni kade saboda zan iya dawowa kuma ba nisa zanyi ba.

Ba laifi na dan samu kudi kodan yana safe ba kamar jiya ba.

Ina nan tsaye bakin titi zan sayi doya da kwai na hango su Babah Indo sun nufo wajen mu su duka yadda Babah Indo ke tafiya yadda kasan zakanya.

"Mike faruwa ne nagan su haka kamar zasu yaki? Gashi naga Babah Indo cikin tashin hankali?"""

MARYAM ANKDUIE {Qurrah}

Continue Reading

You'll Also Like

135K 3.7K 25
Warning: 18+ ABO worldကို အခြေခံရေးသားထားပါသည်။ စိတ်ကူးယဉ် ficလေးမို့ အပြင်လောကနှင့် များစွာ ကွာခြားနိုင်ပါသည်။
84.7K 2.2K 82
an eighteen-year-old boy, trying his best to save his ass from being whipped by his soon-to-be husband, and at the same time, he wants to get away wi...
75.7K 8.4K 14
Dragonwall's queen no longer remembers who she is. Her magic is locked away at the hands of an evil sorcerer. Kane hoped to deal the drengr monarchy...
33.9K 1.4K 11
Oc female Jackson x Hermes x Apollo x Ares