ZAFI BIYU

By Qurratou

478 9 4

Labari ne dake dauke da sark'ak'iya da kuma dana sani a lokacin da wuri ya k'ure. More

ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFIE BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
ZAFI BIYU
MAKANTAR ZUCI!
MAKANTAR ZUCI!
MAKANTAR ZUCI!

ZAFIE BIYU

23 0 0
By Qurratou

Z_B

Written by_Qurrah
Wattpad_Qurratou

Page_4

Masu Complain akan rashin post kullun kuyi hakuri yanzu ai aka fara zaku same shi a kullun insha Allah, Maganar kuma kada na wahalar da Beedah sosai kodan cikin jikin ta ba dagani bane daga Labarin ne Nagode🙏

GOLDEN PEN WRITER'S ASSOCIATION✍️

Bissimillahir Rahmanir Rahim.

Dafe kaina nayi da duka hannaye na saboda yadda yake man ciwo baki daya na kure tunanina amman na kasa tuna ina ne yake a cikin State din nan, Runtse idona nayi ko zan tuna wani abu amman nakasa, Duka hannaye na nasa ina  bugun kai na dan ya tuna wani abu amman saima tunanin ya tsaya waje daya kwalwata tabar aiki.

"Malama lapiar kide?"

Bude idona nayi a hankali kana nace;"Ka taimaka man bazan iya tuna komi ba game da wannan garuruwan daka ambata man"

"Tab lallai kam kinada aiki Babba zakije k'asar da baki taba zuwa ba sannan ace ko sunan Jahar da zaki baki sani ba to taya zaki ga wanda kike nema?"

A jiyar zuciya na sabke ina kara runtse ido na koda zan tuna wani abu, Saurin bude idona nayi tare da cewa;"Yawwa na tuna Mom din shi ta kira shi da Prince kenan kaga shi prince ne"

Hawaye ne suka zuboman na dadi saboda na tuna abinda zai taimake ni wajen ganin Baban Baby na.

Dariya Maimashin din nan ya fashe da ita yana kallo na.
Kallon shi nake cikin mamaki ina tunanin miyake ma dariya kuma.

"Prince a Arewa cin Nigeria ai ba daya bane kuma kowa ai ana iya kiran shi da Prince Uwa zata iya kiran d'an ta da Prince"

Bata fuska nayi ganin ya maidani kamar wata marar kai kana nace;"Amman shi ai Prince ne sunada Kingdom ai ya fadaman"

"Idan suna da Kingdom duk garuruwan nan dana lissafa maki sunada Kingdom's bayan su kuma akwai wasu jahohin da yawa a Arewa da suma sunada Kingdom's"

Shiru nayi ina taba cikin jikina baki daya tausayin abinda ke ciki na ya kamani amman de zanyi kokarin nema mashi Baban shi koda zan rasa raina.

Ganin yana niyyar tada mashin din shi yasa nayi saurin rike mashin din nace;"Ka taimaka man ka kaini Nigeria"

"Yarinya nan ma ai kin shigo Nigeria kusa kike da Legos"

"Ina nufin wajen Hausa"

Shiru yayi yana nazari sai chan yace;"Ohhh na tuna akwai wasu kungiyar yan Bara Hausawa ne sun dawo   Bara daga Ghana yanzu gida zasu zan kaiki cikin su saiki bisu Hausawa ne amman cikin su akwai masu jin French kadan saboda suna zama Cotonou ki shiga cikin su zan kaiki ga shugabar su"

Murmushi nayi nace;"Nagode"

Godiya nayi ma Allah saboda wahala ta ta kare Daga yau.

Dauka ta yayi da mashin din shi mukayi tayi mai d'an tsayi kana muka iske wasu mutane duk mata ne kuma mafi yawa tsaffi ne sunkai su ashirin.

"Sannun ku ina wunin ku"

Maimashin dina ya fada yana gyara parking din shi.

"Lapia kalau Tukur  kanada sako ne"

"A'a Babah Indo, Ga bakuwa na kawo maku gida zata itama saide bata jin Hausa saide French"

Kallo na Babah Indo tayi da alama itace Shugabar su tace;"Kai tana iya zuwa Kano a haka kalli fa abinda ke jikin ta kuma mu ai tafiyar mu munayi muna tsayawa a hanya mu kwana biyu saboda wasu wuraren muna tsayawa mu k'ara nema kada ta zamo man kaya fa kuma kaga nima ta kaina nake yi"

Nan ya fadaman abinda Babah Indo ta fada cikin sauri nace;"A'a zan iya kuma bazan zame maki kaya ba zan iya"

"To nawa ne gareki?"

Shiru nayi tare da dukar dakaina ina tunanin mizan fada.

"Banda kudi"

"Baki da kudi kuma?"

Daga kai nayi tare da addu'a a cikin zuciya ta Allah yasa ta taimake ni.

"Nima Naima na fito kuma ban naima ba d'an naba wani ba dan haka ki zauna ki nemi kudi anan kana ki shirya tafiya"

"Dan Allah ki taimaka man"

"Babah Indo ki taimaka mata mana"

Maimashin dina ya fada.
"Zan taimaka mata zan biya mata kudin mota zuwa Legas (Legos) Idan mun isa kwana biyun da zamuyi kamin mu samu motar zuwa gida to ta tabbata ta nemi kudin biyana sannan kuma ta nemi na zuwa Kano idan ba haka ba a Legas zan barta inyi tafiya ta idan ta yadda to ga wuri nan ta zauna"

Nan yayi man bayani abinda tace cikin sauri na d'aga kai alamar Eh.

"Babah Indo ta yadda"

"To shikenan Tukur ba matsala sai mun dawo"

"To muna gaida yan gidan nagode"

Kallon su nayi ko wace da kunshin kaya tambayar kaina nayi shin basu da 'ya 'ya suka barsu suka fito Bara ne?

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
"Kamal idan ka gama kallon ta saika zauna muyi magana"

Sosa kai yayi yana zama bisa kujera kusa da Hajiya Babba.

"Wannan yarinyar ita ya dace ka nema yar dangi ce sannan babu wanda bazaiyi kwadayin ya hada zuri'a dasu ba kuma ita kade ubanta ya mallaka kaga gatan ya mata yawa"

"Hajiya ban damu da wannan ba koma de minene yarinyar tayi man"

Murmushi Hajiya Babba tayi tace;"Yanzu sai kaje wajen Iman ta baka number din ta idan kuka dai-dai ta komi tsakanin ku kaga saimu shiga maganar"
"Hajiya kada ki damu  wannan yarinyar ta zama tawa kawai"

Rahama dake gefe tana latsar waya tace;"Uncle Kamal amman fa yarinyar kamar tanada girman kai fa"

"Rahama duk wanda yafi to daga Family din nan dan yayi girman kai ai bawani abu bane"

Hajiya Babba ta fada tana murmushi dan kara karfafama Kamal.
"Hajiya gyale ta ni mace duk girman kanta ai saita saduda idan tazo hannu wallahi"

"To Allah ya taimaka kayi kokari ayi abun cikin kankanin lokaci dan idan ka samu yarinyar nan nima zanyi farin ciki sosai da hakan"

"Kima fara kirga kwana kin auren mu"

Annie zaune Hakeem na kusa da ita ta kalle shi tace;"Abdulhakeem"

"Na'am Annie"

"Kana da ilimi basai na tsaya tuna tar da kaiba kai ya kamata ka tunatar da al'umma nasan kasan minene aure kuma kasan matsayin shi a musulunci to miyasa ba zakayi shiba a kananun shekarun ka, Shekarar ka ashirin da tara d'an Allah kamin ka shiga talatin ina son kayi aure babu bukatar in maka jawabin ladar dake cikin auren da karfin shi"

Shiru yayi yana tunanin ta ina zai fara? Miyasa Annie kesan yayi aure? Imran ya girme shi haka Kamal kusan duk sun girme shi kuma babu mai batun aure sai shi?

"Annie"

"Na'am"

"Ban san mizan ce ba kawai kiyi man komi"

"Kamar ya?"

"Annie ban san taya zan tsaya da mace ba kawai ki sama man mata sai ayi komi"

Murmushi tayi tace;"Tofa kana namiji ace baka iya magana da mace ba taya zan san abinda kake so ni?"

"Annie duk wanda kika zab'a man zan sota ai"

"Kayi alk'awarin duk wadda na baka bazakayi gardama ba"

"Eh Annie"

"To shikenan Allah yayi maka Albarka yanzu ka maido komi hannu kenan zanyi nazari akai"

Imran ne ya shigo da wata dattijuwa a tare da shi.

"Annie albishirin ki"

"Goro"

"Fari ko Ja?"

"Kajini da yaro ya maidani karamar yarinya"

"Nide fadaman idan kina so na baki albishir"

"Fari"

"Ga Baba Laure na maido maki"

Yayi maganar yana kaucewa Baba laure ta fito tana dariya.

"Ahh Laure sannu da zuwa ashe zaki dawo nata aike akan ki dawo"

"Wallahi jika nane dake Kabu-Kabu a Legas shine ya fadi da mashin nayi zaman jinyar shi amman yanzu yaji sauki har ya koma ma"

"Ayyah Allah Sarki Allah ya k'ara tsarewa"

"To Ameen ya Allah"

"Annie bari naje na gyara dakin nawa"

"To shikenan"

"To Annie yanzu za'a barni na koma wajen aiki ko?"

"A'a duk da haka ban yadda da zuwa Legos din nan ba ina son  ka dawo nan"

"Ohhh Annie mizan maki ki yadda da wannan aikin nawa?"

"Babu"

Ta fada tana mikewa tayi hanyar bedroom.

"To Annie na yadda zan aje zan dawo nan shikenan ko kibar fushi"

Juyowa tayi da murmushi tace;"Ko kaifa bana son kuyi nesa dani"

Dawowa tayi ta zauna ta kama hannun shi shida Hakeem tace;"Bana son abinda zai nesan ta ku dani ne ina son mu samu lokaci a tare mu duka saboda ni nasan ba wani dadewa zanyi ba a duniyar shiyasa kukaga na matsa maku akan aure wannan dalilin yasa bana son ku nesan ta dani nasan kana son aikin ka amman kayi hakuri"

"Annie kibar fadar haka mana ban son naga wannan hawayen na zuba kuma basai kin bani hakuri ba na fahimce ki"

Murmushi tayi tana shafa kansu kana tace;"Allah yayi maku albarka"

"Ameen "

Suka amsa su duka.

"Annie zamuje nida Hakeem muyi kwana biyu a chan saboda na kwashe kayana dake a chan"

"Okay ba matsala amman kwana biyun nan kawai na baku"

"To shikenan Annie har yanzu de baki yadda dani ba? Saboda ki yadda dani yasa zan tafi da Hakeem"

"Nima hankali na zai kwanta idan kuka tafi taren, Amman idan ka tafi kai kade sai naga kamar zaman ka zakayi"

"To yanzu de shikenan zuwa anjima zan mana booking din flight"

"To shikenan Allah yayi maku albarka"
"Ameen"

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Cikin sauri Mom din Hanah ta kamata tace;"Maimuna lapiar ki kuwa?"

Da kyat ta iya bude idanun ta tace;"Hajiya kaina ne kenan ciwo bari naje daki jiri nake gani"

Tana juyawa sukaji ana buga gida da karfi su duka suka nufi bakin get din.

Suna isa bai gadi ya leka ta karamar kofa kana ya bude yana budewa Hanah ta fado kamar mahaukaciya babu kallabi a kanta daga ita sai riga babu wando a tare da ita.

"Mom!!"
Ta fada tana fadawa jikin Mom din ta tana kuka.

Nanny din ta ce tazo ta cire Hijab ta saka mata ita kuma ta juya ta nufi part din su.

"Hanah! Hanah, Kalli Hanah bata motsi innalillahi"

Mom din ta ta fada cikin tashin hankali.

"Kira driver muje hospital"

Dad din hana ya fada yazo inda take kwance yace;"Yi sauri tado driver muje hospital"

Bude ido tayi a hankali taga Dad din ta da Mom din tsaye bisa kanta.

"Mom!..."

Da kyat ta samu Mom din ta fito a fili.
"Alhamdulillah Hanah kin farka nagode ma Allah"

"Hanah"
Dad din ta ya fada yana rike hannun ta.

"Yes Dad inane nan?"
"Kina hospital jiya da daddare muka kawo ki nan"

A jiyar zuciya ta sabke tare da tuna abinda ya faru da ita a daren jiya, Hawaye suke zuba a gefen fuskarta.

"Hanah! Miyasa kike hawaye ne? Fadaman Hanah miyafaru dake?"

Runtse ido tayi hawaye na zuba daga idanun batace komi ba.

"Hanah! Fada mana muna son mu dauki mataki akai fadama miya same ki"

Bude ido tayi tana kallon Dad din ta dake rike da hannun ta kana tace;"Babu komi Dad wasu ne suka amshe man mota"

"Ansar maki mota bazai sakaki kuka ba bazai sakaki ki razana ba Ki fadaman gaskiya jiya kin dawo babu kallabi a kanki riga kade ce jikin ki fadaman miya faru?"

Shiru tayi tare da juya baya kana tace;"Dad lokacin da suka tsaidani naki tsayawa sai suka gifta man dole na tsaya da sukace na basu Key nakiya sai suka maren har hular dake a kaina ta cire"

"To shifa wandon kayan ki?"

"Haba Alhaji Questions din sun isa haka ka duba halin da take ciki mana"

Shiru yayi ba tare daya yadda da abinda Hanah ta fadaba lallai akwai wani abu a k'asa amman zai lallabata ta fada mashi gaskiya.

Commissioner din yan sanda ya kira ya fada mashi abinda ya faru.

Doctor na shigowa aka dubata yace ba wata matsala zasu iya tafiya.

Part din Mom din ta suka sabka itake mata komi saboda har yanzu taki sakin jikin ta shiya Mom din ta ta kawo ta part din ta.

Tun safe Hanah bata ci komi ba da kyat Mom din ta tasa taci abinci shima kadan.

Da yamma Dad din ta ya shigo yace ta fito parlo.

Katon Hijab din Mom din ta da take Sallah tasa ta fito parlo bakon dake zaune a saman kujerar parlo din ta gaida tare da zama.

"Hanah, nine Commissioner na yan sandar jahar Kano ina son ki fadaman abinda ya faru dake saboda ba b'arayin mota bane kika hadu dasu dan mun samu motar ki tare da key a jiki komi ba'a taba ba kenan ba b'arayin mota bane kika hadu dasu ki fadaman gaskiyar abinda ya faru dake sannan kuma kina iya gane wadan da suka tsaida ki ina nufin kina iya tuna fuskar su?"

Dagowa tayi ta kalle shi tace;"Bana iya tuna komi kuma na riga dana fadama Dad abinda ya faru dani dan haka bana bukatar ku sannan kuma tunda har anga motar tawa kenan komi ya wuce ina son ka rufe Case din nan a yanzu "

Daga haka ta juya tabar dakin part din ta ta koma saboda bata son yawan tambaya.

"Yarinyar nan kamar ta boye wani abu fa?"

"Hakan yasa na kira ka saboda ban yadda da abinda ta fada ba, Dan an amshi motar ta bazai saka ta razana ba harta suma saboda ai ba mota daya bace gareta sannan tasan zan siya mata duk wadda take so hakan bazai razanar da itaba"

"To yanzu Alhaji ya kake ganin zamuyi mata?"

"Zan saka Nanny din ta ta saka mata ido itace suke waje daya"

"Yawwa to shikenan kace mata idan friends din ta sunzo ta dan labe taji ko zata fada masu wani abu"

"Okay to shikenan nagode saika jini"

Tana shiga ta fada bisa gado ta saki kuka mai sauti.

Jin kukan yasa Nanny din ta ta shigo dakin Cikin sauri.

"Kina lapia? Mike faruwa fadaman mikike so ko a kira Doctor?"

Tashi tayi daga kwance da take ta kalli Nanny din dake tsaye hankali tashe tana jero mata tambayoyi.

"Malama babu ruwan ki da matsala ta dan Allah ki fita Kada ki karaman ciwon kai"

Nanny dake tsaye tamkar andasata ta kasa fita saida Hanah ta daka mata tsawa.

"Ki fita nace!"

MARYAM ANKUDII {Qurrah}

Continue Reading

You'll Also Like

70.3K 7.8K 13
Dragonwall's queen no longer remembers who she is. Her magic is locked away at the hands of an evil sorcerer. Kane hoped to deal the drengr monarchy...
62K 1.6K 63
"mom, dad, Im married!" lahat ng relatives namin ay nagulat sa announcment ko. Sino ba naman kasi ang mag aakala na ang unica ija ng pamilyang Letpr...
124K 3.5K 25
Warning: 18+ ABO worldကို အခြေခံရေးသားထားပါသည်။ စိတ်ကူးယဉ် ficလေးမို့ အပြင်လောကနှင့် များစွာ ကွာခြားနိုင်ပါသည်။
69.8K 3.6K 37
• Ranbir a cold hearted person , have a anger issue • Prachi a kind hearted person , the most stubborn girl both are different in their ways what w...