ANYA BAIWA CE?

By AmeeraAdam60

9.6K 193 29

Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa, " Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Ba... More

PAGE 1
PAGE 2
PAGE 3
FREE PAGE 4
FREE PAGE 5
FREE PAGE 6
FREE PAGE 7
FREE PAGE 8
FREE PAGE 9
LAST FREE PAGES

BONUS PAGE

1.2K 26 14
By AmeeraAdam60

*ANYA BAIWA CE?*
     
    PAGE 19

                   BONUS✋🏻😂🤚🏻

    Kamar yadda Sarki Aminullah ya zubawa sabon Bawan nan ido haka shima ya zuba masa idanu yana yi yana zagaye kaskon wutar kamar yadda abokin takararsa yake yi, Zagaya wutar suka fara yi suna yi suna ɗiban yashin gurin suna murzawa a hannunsu da jikinsu, idanun jama'ar gurin gabaɗaya ya koma kansu dan ganin wanda zai fara tsokano wutar tunda ita kanta wutar ita kaɗai ma neman abokin lasarta take yi, Haro ne ya gyara tsayuwarsa ya damƙi ƙasa ya watsawa wutar aikuwa kamar wanda ya watsa mata Fetir haka ta kuma tashi sama tana cin bal bal bal kamar zata fara lasarsu tun basu basu taɓa ta ba.

  Daga Haro har Sabon Bawan ja sukayi da baya kowa na ayyana ta yadda zai fara ɓullowa lamarin wutar, saboda sihirinta ya wuce tunanin me tunani. Daga cen gefe Mai Martaba Aminullah ne ya yi murmushi yana kallan Aminansa biyu, Sarkin Adamawa Dr Musa Ɗan bahaushe ya kalli Amininsa yace. "Wa kake ganin zai iya cin wannan nasarar?" Sarki Aminullah ya yi murmushi yace. "Alamar ƙarfi tana ga mai ƙiba. Dan nasan waye Haro ka ga kuwa ruwa ba sa'an kwando bane." Sarki Musa yace. "Amma ba'a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare" Sarki Aminullah ya yi wani irin murmushi sannan yace. "Duk faɗin gurin nan kana gani babu wanda ya yarda ya shiga gasa da Haro, saboda wanda ya taka wuta, idan ya ga toka sai ya yi nesa da ita. Su kansu sun waye Haro wancen yaron ma da alama baƙo ne dan na lura da yanayinsa." Sarkin Nupe Sarki Abdullahi murmushi shima ya yi yace. "Yanzu fa duk harsashe ne kawai muke yi amma tuni Ubangiji ya zaɓi me yin nasara." Gabaɗaya suka amsa masa sannan suka mayar da kallansu wajen su Haro.

    Kallan kallo aka shiga yi da tsakanin Haro da Sabon Bawan sannan Haro ya yi kukan kura ta nufi wutar gadan-gadan, shima daga ɓangarensa Sabon Bawan cikin ƙwarin gwiwa ya nufi gurin nan take suka fara artabu da wannan wutar dake cikin kasko, duk lokacin da jikin Haro dana Sabon bawan ya haɗu sai kaji ya bada wani irin sauti kamar haɗuwar takubban da ake tsaka da azababben yaƙi. Sannu a hankali rigunan jikinsu suka fara ƙonewa suna bajewa cikin toka ya zamana daga su sai wandunan ƙarfe. Al'amarin da ya ƙara jan hankulan al'ummar da ke gurin, kowa ya yi shiru banda sautin kokawarsu babu abinda yake tashi agurin. Wasan ne ya fara ɗaukan zafi saboda yadda wandunan jikinsu tuni suka amsa tayin turirin zafin da wutar take yi musu, ganin wankin hula na hiyyar kaisu dare yasa Haro ya ƙara bada azama wajen ganin ya juya akalar wutar zuwa ga wannan Sabon Bawa, kamar wacce ya sanar da ita  wutar haka ta juyar akalarta zuwa gareshi har ta fara ƙoƙarin kaishi ga halaka, ganin haka ba ƙaramin faranta ran mutanen da ke gurin ya yi ba saboda kowa fatansa bai wuce ace Haro ya yi nasara ba.

    Sabon Bawan na ganin haka ya miƙe a zabure yana motsa bakinsa nan take wutar ta juya ga Haro har ta kwantar shi ƙasa, miƙewa ya yi tsaye yana murmushin nasara sai dai babu walawala  a fuskokin mutanen da ke gurin, ganin wutar ta tasamma halaka Haro yasa ya ƙarasa gurin ya kashe ta a lokacin tuni Haro ya fita hayyacinsa.Daga cen gefe Sarkin ƙira ne ya fito yana tafi haɗe da girgiza gwangwani mai ɗaure da wuri a hannunsa, yana zuwa ya kama hannun Sabon Bawan ya ɗaga sama tare da ɗaura masa wata ƙatuwar laya a damtsen hannunsa. Amma wani abin mamaki yana ɗaura layar sai ta suɓuce ta faɗo ƙasa ya gwada haka ya fi a irga, gabaɗaya mutanen gurin ido suka zubo musu suna kallon abin da yake faruwa. Da sauri wasu manyan Bayi suka ɗauke Haro da yake cikin wani irin yanayi. Sarkin Maƙera ya kalli Sabon bawa da mamaki shima shi yake kallo yana yi masa shu'umin murmushi. Sabon Bawan ƙasa ya yi da murya yace. "Ni da kake gani nafi ƙarfin siddabarunku ya kama ni" yana gama faɗa zubawa layar ido nan take ta hau ƙuncewa da kanta sai ga wasu irin ƙananun allurai da karyayyun reza haɗe da wani irin rubutu a ciki. Mutanen da ke zagaye basu san me yake faruwa ba a tsammaninsu Sarkin Ƙira wani abu na girmamawa yake masa dan haka aka ga sun haɗa kai guri ɗaya. Sabon bawan ya kalli Sarkin Ƙira yace. "Idan zaka gina ramin mugunta gina shi gajere dan bakasan wanda zai faɗa ciki ba, daga yanzu idan zaka shuka mugunta kasan wanda zaka aikatawa." Kunya ce ta kama Sarƙin ƙira yana shirin tsugunnawa ya roƙeshi ya ruƙo hannunsa ɗaya yace. "Idan kayi haka sauran jama'a zasu fahimci halin da ake ciki gwara ma mu bar lamarin a tsakaninmu, amma da sharaɗi guda ɗaya" bakin Sarkin ƙira har rawa yake yace. "Me nene sharaɗin a yanzu na aikata maka" Murmushi Sabon Bawan ya yi ya huro iska akan tafin hannunsa nan take sai ga Sarƙin ƙira tsaye tare da Haro yana yi masa bayani kafin shigar su Haro da Sabon Bawan filin gasa.

   Haro yace. "Sarkin ƙira kamar yadda aka saba duk shekara wannan shekararma haka zamu yi da kai ga layar nan a duk lokacin da muka shiga fafatawa idan kaga za'ayi nasara a kaina ka dinga murzata, idan kuma har anyi nasara akaina lokacin da zaka bawa abokin hammaya kambun girmamawa ka naɗa masa a hannunsa kafin a tashi daga taron wasan al'ada zai kwanta ciwo kamar yadda muka taɓa yi da Marigari Iliya Mudubi, dan wallahi da girmana ya faɗi gwara uban kowa ya rasa." Sarkin ƙira yace. "Maganar gaskiya Haro tsoro nake ji karfa asirinmu ya tonu dukda dai ba'a taɓa samun matsala ba,  amma ina gudun ɓacin rana" Haro yace. "Haba kamar ba wayayye ba ina baka kana ƙin karɓa, kasan dai bana maka ƙaramin alheri duk shekara kawai ka share haka za'a yi" Sarƙin ƙira ya amsa tare da cewa. "Amma farashin wannan shekarar ya ƙaru sai ka ninnikamin kyauta ta" Haro yace. "Wannan mai sauƙi ne"

    Sarkin ƙira tun bai gama gani ba jikinsa ya hau tsuma a tsorace yace. "Tuba nake dan Allah ka rufa mini asiri" Sabon Bawan yace. "Idan ka bi abin da zan saka ka ba.  Kaga dai ba a gaba kuka yi ba ko?" Da sauri Sarkin ƙira ya gyaɗa kai.

   Sabon Bawan yace. "To yadda na ganku ba tare da kun sani ba haka yanzu zan ganka a lokacin da na baka wannan aikin" yana gama faɗa ya huro iska daga bakinsa nan take sai ga wata farar leda me ɗaure da wani irin gwamamman rubutu a jikinta, cikin ta wani farin yashi nemai ƙamshi haɗe da sanyi, miƙawa Sarkin ƙira ya yi haɗe da cewa. "Wannan yashin nake son ka haƙa rami me zurfi a cikin gidan Sarki ka binneshi a haka, abin da nake so da kai kenan amma muddin ka saɓawa haka wallahi sai na kasheka da kisa me tsanani." Sarƙin ƙira na jin haka ya ɗago a firgice yana kallansa bayan ya karɓa yace. "Indai wannan ne ai ƙaramin aiki ne" Sabon Bawan yace."Ka adana shi sannan ka cigaba da shagali kamar komai bai faru ba." Sarkin ƙira karɓa ya yi ya sa a aljihu sannan ya ci gaba da wasa Sabon Bawa haɗe da rawa yana waƙa kamar yadda yake bisa ga al'ada ga duk wanda ya ci.

     Sarki Aminullah jin jikinsa yake wani irin sam bai so ace ba Haro ne yaci ba amma babu yadda ya iya, bayan fitar Sarkin ƙira da Sabon Bawa sai masinta suka fito suma suka shiga nuna tasu bajintar dan ganin sun faranta ran Mai Martaba.

     Kifaye masu rai suka fito da su suka zuba a ƙasa nan take Kifayen suka fara iyo a ƙasa kamar waɗanda suke cikin ruwan bayan kamar wasu mintuna sai suka ciro fatsarsu ta kamun kifi, saida suka ɗaga ta sama suna nunawa kowa babu komai a ciki sai suka sauke suka fara bazasu duk bazawa ɗaya idan mutum ɗaya daga cikin su ya yi sai ya ɗago fatsarsa cike da kifi fiye da goma a ciki kafin wani lokaci tuni sun cika fatsar su da kifaye manya da ƙanana. Sarkin masintan ya umarci a da ayi gaggawar haɗa wuta, ba'a ɗauki lokaci ba aka haɗa wuta tare da ɗora wani babban kasko aka shiga hidimar soya kifayen manyan daga ciki kuma aka dinga gasawa, wasan ba ƙaramin ƙayatarwa yake ba dan haka mutanen garin idan bikin ya ƙarato kowa da irin shirin da yake yi.

      Basu jima ba aka kamalla wasan masinta tare da gama suyar kifi suma suka tattara kayansu suka bar wajen, fitar su babu jimawa Wanzamai suma suka shigo suka fara nuna tasu bajimtar. Ɗan sarkin wanzamai me kimanin shekara goma ya fito rataye da jakar wanzamai, yana zuwa ya dire ta a tsakiyar wajen ya juya ya gaida Sarki cikin girmamawa, daga cen ɓangaren Bafaden Sarki Aminullah ya amsa da. "Sarki ya amsa an gaishe ka Ɗan sarkin wazamai" Yaron juyawa ya yi yace. "A cikin ku akwai wanda yake buƙatar aski daga nan gurin da yake?" Kallon kallo suka fea yiwa juma aka rasa wanda zai amsa har sai da ya kuma maimatawa a karo na biyu sannan wani Matashin saurayi ya ɗaga hannunsa tare da cewa. "Ga ni" Yana rufe baki Yaron ya kalli Jakarsa ya yiwa aska magana kaman wanda yake wa mutum magana, yana gama mata magana Jakar ta buɗe da kanta aska ta fita bata tsya ko'ina ba sai wajen saurayin da ya yi magana. Kafin wani lokaci tuni ta aske kan matashin, wannan abin da yaron ya yi ba ƙaramin ƙayatar da Sarki da Aminansa ya yi ba harma da mutanen wajen.

    Sarkin Aska da kansa ne ya fito ya juya ya fara kallan mutanen gurin ɗaya bayan ɗaya sannan ya bada umarnin a kawo masa babban mazubi, da sauri wani bafade ya ɗauko masa babban bokiti yana kawo masa ya zauna a gaban bokitin ya fara kwara aman jini a ciki ya jima yana abu ɗaya sannan ya cika bokitin fal da jini, gabaɗaya mutanen guri zaro ido sukayi suna kallan abinda yake faruwa, miƙewa ya yi yace a ɗauke bokitin aje a zubar dashi a wani gurin. Yana tashi ya ɗauki jakar wanzanci ya ɗagata sama sannan ya fara wulwulawa yana ajiyeta da ya buɗe sai ga Jaririya ya yafito da ita tana ta mutsuniya a cikin tsumma a wannan lokacin gurin hautsinewa ya yi da hayaniyar jama'a, a hankali Sarkin Wazaman ya taka ya miƙawa wani Dogarin Sarki yace a kaiwa Sarki Aminullah Jaririyar.

     Duk wannan shagali da yake faruwa Fulani Zaliha da Salf na gida a zaune dan yadda ta ɗau zafi taci alwashin komai na masarautar ta daina shiga, shima Saif saboda rashin jansa a jiki da Sarki Aminulllah yake yi yasa ko kaɗan bai ma yi gigin fita gurin wasan al'adar ba. Haka daga ɓangaren su Inna Habi gabaɗaya bayin gidan suka yi zuga suka tafi filin wasan al'ada, babu kowa daga ita sai Abu banda kuka babu abin da Inna Habi take yi musamman idan ta tuna halin da Maryo take ciki, dan ma Abu na ɗan kwantar mata da hankali tana ɗan rage damuwar.

    A lokacin da ake tsaka da shagalin wasa Sarkin ƙira ne ya saci jiki ya wuce cen gidan Sarki, yana shiga yaci sa'a babu mutane sosai yawanci sai masu tsaron ƙofofi. Ganin suna ɗan kallansa yasa ya wuce ya shiga dube-duben gurin da zai samu faragabar binnewa ba tare da wani ya gansa ba. Sai da ya yi tafiya me ɗan nisa sannan ya samu wani guri fara haƙa sai da ya yi haƙa me zurfi sannan ya binne yashin. Yana gama binnewa ya fito da sauri ko waiwaye baya yi, Sarkin ƙira na gabda ƙarasowa gurin da ake gudanar da wasan Al'ada yaji wuyansa ya yi ɗaure kamar wanda aka rataye, hannu biyu yasa yana riƙe wuyansa saboda azaba ya durƙushe a gurin kafin wani lokaci rai ya yi halinsa.

    Saif na zaune da mahaifiyarsa suna hira yaji kansa ya sara masa da sauri ya dafe kan nasa yana rumtse ido, rufe idonsa keda wuya ya hange shi a wani makeken fili da alama nemen wani abu yake daga cen nesa ya hango wata mace riƙe a hannun wani namiji yana gudu da ita tana fisgewa, yana shirin bin su yaji ƙasar gurin ta fara zabtarewa nan take ya faɗa ciki ƙasar ta rufe da shi, cikin wata irin murya yake faɗin, "Rayzutaaaa, Zulik karka tafi da ita" Fulani Zaliha a tsorace take bin Saif da kallo ganin irin surutan da yake yi yasa ta fara karanta masa addu'a tana tofa masa, buɗe idanunsa sukayi da suka rine jawur Fulani Zaliha har sai da ta tsorata da ganin idanunsa, kallanta ya farayi muryarsa a dace yace. "Ammi wani mafarki nayi yanzu" ƙara zaro ido tayi jin abin da ya faɗa ita dai tasan da faruwar yanayin da ya shiga ko minti biyi baiyi ba, ace mutum ba bacci yayi ba ya yi mafarki. Amma sai ta basar ta ce. "Meye a mafarkin?" lumshe ido ya yi ya buɗe yace. "Wani ne ya tafi da wata amma sai nake ganin kamar tana da muhimmanci a gurina."

    Maryo da ke kwance a asibiti firgigit ta miƙe zaune kamar wacce aka jonawa wutar lantarki haka jikinta ya ɗauki wani irin shock, da sauri ta fisge robar ƙarin ruwan da ke hannunta ta diro daga kan gado ta nufi hanyar bakin ƙofa a guje. Da sauri wannan Dogari ya bi bayanta tare da sauran Dogarawan da ke zaune a gurin, Maryo wani irin gudu take kamar wacce zata tashi sama, basu suka samu nasarar kamata ba sai da suka jima suna tseren gudu a tsakaninsu, suna riƙeta ta fara fisge-fisge tana cewa. "Ku barni na tafi zai cutar da shi dan Allah ku ƙyaleni, Furzaaan wayyooo zai cutar mini da shi" sai da sukayi da gaske sannan suka samu suka iya kama Maryo suka wuce da ita ɗakinta, wanda har lokacin bata daina ƙoƙarin ƙwacewa ba.

    Suna shiga suka rufe ƙofar da key suna mayar da numfashi, wani irin hawaye ne yake zuba daga idanun Maryo tsugunnawa tayi kan gwiwowinta ta haɗa hannuwanta biyu murya a raunace ta ce. "Dan Allah kar kuyi mini haka wannan ita ce dama kusan ta ƙarshe karku bari na ƙara rasashi wannan karan bazan jure rashinsa ba, kuyi haƙuri ku dubi halin da zuciyata take ciki idan ban isa gareshi ba komai zai iya faruwa, banasan na cutar da ku domin kunyi mini hallaci ku buɗe min na fita." Ganin basu da alamun buɗewa yasa Maryo ta durƙushe a gurin ta rusa wani irin kuka me tsuma zuciya, dukda Dogarawan nan basu san dalilin kukanta ba amma kukan nata ya taɓa zuciyoyinsu. Suna nan tsaye suka ji likitan ya ƙaraso suna buɗe ƙofar ta zabura zata fita lokacin tuni hancinta ya fara zubda jini, da sauri suka kamata suka mayar da ita kan gado cikin shammata likitan ya sakar mata alluran bacci, babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita suna ganin haka suka kwantar da ita amma wani abun mamakin har tayi bacci hawayen idanunta basu daina tsiyaya ba, haka jinin da ke fita ta hancinta shima yana ci gaba da fita lokaci-lokaci tana sauke ajiyar zuciya.

   Likitan ne ya kalle ya kallesu cikin damuwa yace. "Yarinyar nan har yanzu tana cikin zafin ciwo gashi har tana surutai so gaskiya sai an sa ido sosai a kanta, zan turo nurses su gyarata." Dogarawan cikin ƙosawa suka gyaɗa masa kai, dan su har sun fara gajiya da ciwonta cikin kwana ɗaya yarinya ta hanasu sukuni gashi suna burin ganin bikin al'ada amma bisa umarnin Sarki akanta yasa suka kwana suka wuni a asibiti.

     Wasu matasan ƴan mata da ke zagaye da gadon Maryo wanda likitan da Dogarawan basa ganinsu suka ja gefe cikin yanayin damuwa, idanunsu ɗauke da hawaye suka russuna gaban Gadon Maryo cikin haɗin baki suna faɗin. "Fartu kibarsi wargakina umkasu jilbas, wargisu fisadu kijalbi mirzatu Zulik gurwatu bisanit kaljuwas fargista kalminfat wargas girbat?"

    (Tuba muke ya shugaba amma bamu so kika ƙi bamu dama ba, yanzu haka zamu sa ido akan Zulik wannan karanma ya yi nasara akanmu?) miƙewa sukayi suna hawaye suka fara binta kusurwar bango suna wucewa.

   TO FA MEYE HARSASHENKU NE KUNA KAN BAKARKU NA MARYO BAIWA CE? KU DUBA DAI DA KYAU ANYA BAIWA CE? 🤣🤣🤣🤣

YANZU FA SAI KUCE INA NEXT PAGE 🙄

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

Continue Reading

You'll Also Like

35.6K 1.7K 74
true love never exists right?? or If it does than only give pain. "It's amazing how someone can break your heart, and you can still love them with al...
39.6K 5.8K 58
စာရေးသူ - ယွီရှောက်လန်ရှန်း ဇာတ်ဆောင် - ရှန်ချန်းလင် x ချင်ရှောက်ယွီ - ယဲ့ကျင် x ရှန်ချန်းဖုန်း
20.3K 213 133
The ancient saying goes: Most generals come from Guan Xi, while ministers come from Guan Dong. He Lisa was born to be a Star General. She was merely...
388K 15.7K 137
Fern is the younger sister of a famous author known for 'The Promise Under The Moon.' At just fourteen, she was the first to read her sister's debut...