ANYA BAIWA CE?

Door AmeeraAdam60

9.7K 194 29

Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa, " Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Ba... Meer

PAGE 1
PAGE 2
PAGE 3
FREE PAGE 4
FREE PAGE 5
FREE PAGE 6
FREE PAGE 8
FREE PAGE 9
LAST FREE PAGES
BONUS PAGE

FREE PAGE 7

655 12 4
Door AmeeraAdam60

*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️

*ANYA BAIWA CE?*

             Na

*AMEERA ADAM*
          

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

   FREE PAGE 7

      Wani abu ne ya tsargawa Fulani Maryama tun daga tafin ƙafarta har tsakiyar kanta nan take jikinta yayi sanyi, a sanyaye ta kalli Jakadiya murya a raunace ta ce. "Jakadiya ina jin tsoron wanda Boka Marduska zai ɗauka, tsoro nake kar wani mummunan abu ya faru da Yarima Salman" Jakadiya cikin zuciyarta ta ce. "Ya rabbi samawati kasa jinin Salman ne tukuwicin da Boka zai ɗauka, yooo dama duk wanda ya sayi rariya ai yasan zata zubda ruwa" jin Jakadiya tayi shiru yasa Fulani Maryama ta ce.

   "Jakadiya magana nake fa kina ji na" Jakadiya ta sauya fasalin fuskarta zuwa yanayin damuwa ta ce. "Allah ya taimakeki ba dan kar kalamaina za suyi kaushi ba da nace ki gaggauta yin istigifari saboda Salman Kainuwa ne dashen Allah, domin Jelar raƙumi tayi nesa da ƙasa babu wanda ya isa ya cutar da Salman da yardar Allah shine Sarki me jiran gado." Fulani Maryama ajiyar zuciya ta ce. "Jakadiya shiyasa duk cikin masarauta babu wacce nake ƙauna kamar ke saboda ke kike kwantar mun da hankali a duk lokacin dana tsinci kaina a wani hali" tana gama faɗar haka ta fara karanta kalaman data saba sannan suka koma masarautarsu.

    Washegari da asubar fari saƙo ya iso musu daga Masarautar Gombe na  rasuwar Mahaifin Fulani Maryama wanda shi kaɗai ya rage mata a duniya, Dattijon arziƙi ne shekarunsa Tamanin da bakwai. Jam'ar ƙasar Gombe ba ƙaramin jimami sukayi ba na rashin adalin Sarkinsu marigayi Sarki Abdullahi bn Abdurrahman, lokacin da Mai martaba Sarki Aminullah ya samu wannan saƙon ba ƙaramin jimami yayi ba, tunaninsa ɗaya yadda zai sanarwa da Fulani Maryama rashin mahaifinta musamman da ya tuna yadda take matuƙar ƙaunarsa.
     Fulani Maryama tun da gari ya waye ta ga Salma cikin ƙoshin lafiya damuwarta ta lafa amma a daren ranar ko baccin kirki batayi ba, saboda fargabar abinda zai faru batasan waye Boka zai ɗauka daga cikin ahalinta ba. Tana zaune Yarima Salman na ta ƴan wasanninsa Jakadiya ta shigo da sallama, ga wanda zai ƙarewa Jakadiya kallon tsaf zai fahimci tana cikin farinciki tana shiga ta sauya fasalin fuskarta cikin damuwa ta durƙusa ta ce. "Barka da kyakkyawar safiya uwar gijiyata Mai martaba ya umarceni da sanar dake yana jiranki a turakarsa." Buɗe ido Fulani Maryama tayi da mamakin kiran da Sarki yake mata ta ce. "Jakadiya kinji sabon labari ne?" Jakadiya a zuciyarta ta ce. "Mugun labari ma kuwa amma idan kinje kyaji da kanki" a fili Jakadiya ta ce. "Ranki shi daɗe babu wani sabon labari da ya iso fada a wayewar garin nan"

   Fulani Maryama miƙewa tayi gabanta na faɗuwa ta wuce har taje bakin ƙofa ta juyo ta ce. "Ki kira Binto ta kula mun da Yarima ina dawowa" Fulani Maryama bata jira cewar Jakadiya ba ta fice. Jakadiya ta bi bayanta da wulaƙantaccen kallo a hankali ta ce. "Fulani Maryam kenan ai duk wanda ya sayi tsintsiya yasan zatayi shara da sannu zaki fara girbar abinda kika shuka" ta ƙarasa gaban Yarima Salman ta waiga hagu da dama sannan ta dungure masa kai ta ce. "Kai kuma Falalu sai zare idanu kake kana fala-fala da kunnuwa, ko waɗannan fatalin kunnuwan naka ya isa a gane basu da alaƙa da Mai martaba." tana jin ya fara kuka ta ɗauke shi tana cewa. "Yarima babban gwarzo badai ƙyuya kake ba ke Bintoto zo maza Fulani Maryama ta tafi gurin takawa" bata rufe baki ba sai ga Baiwar ta shigo da sauri, Jakadiya cikin masifa ta ce. "Ke dalla ki dinga nutsuwa yarinya sai rawar kai kamar taci sadakar miji." Jakadiya dangwara mata Yarima tayi ta miƙe ta ce. "To gashinan ki kula da shi dama aikinki ne ni kinga wucewa ta"

     Fulani Maryama zaune ta samu Sarki bayan ta gaisheshi ya amsa sannan yace. "Maryama kinsan dukkan mu daga gurin Ubangiji muke kuma gurinsa zamu koma, yarda da ƙaddara me kyau da marar kyau wajibi ne ga duk musulmin ƙwarai kuma duk wanda kikaji anwayi gari da mutuwarsa to Ubangiji ya fi mu ƙaunarsa shiyasa ya ɗauke bawansa." Fulani Maryama ta gyaɗa kai  jiki a sanyaye Sarki Aminullah ya cigaba da cewa."A ɗazu aka aiko ɗan aike daga ƙasar Gombe cewa Allah ya yiwa Mai martaba rasuwa, Allah ya jiƙansa ya gafarta masa Ubangiji ya kyauta namu zuwan" Tun Sarki Aminullah bai rufe baki ba Fulani Maryama ta rushe da matsanancin kuka, ana cikin haka sauran Matan sarki suka ƙaraso ganin yanayin da Fulani Maryama take ciki ya sanyaya jikinsu. Zama sukayi cikin ladabi suka gaida shi sannan ya ci gaba da cewa.

   "Dukkan Mai rai mammaci a yanzu ba kuka ya kamata kiyi masa ba yafi buƙatar Addu'arki, Mai martaba mutum ne mai karamci da dattako dan haka Addu'a ya kamata muyi masa Allah ya jiƙansa ya gafarta masa dan haka ku shirya zamu kai gaisuwar rashin mahaifin Maryama Ƙasar Gombe nan ba da jimawa ba." Jiki a sanyaye Su Fulani Zaliha suka yiwa Mai martaba da Fulani Maryama ta'aziyya sannan suka miƙe kowacce ta shige sashenta. Fulani Maryama tana kuka tana haɗa hanya ta tashi ta nufi ɓangarenta zuciyarta fal damuwa da jimamin rashin Mahaifinta.

   Fulani Maryama bayan ta gama shiryawa ita kaɗai a ɗaki ta fara magana. "Wannan masifa da me tayi kama saboda Allah a ce wai tsiyar Boka Masduka akan Mahaifina zata ƙare alhalin ni babu wata tsiya da naga ta sauya, aikuwa  wallahi ba zanyi rashin mahaifi a banza ba kowa yaci tuwo dani miya yasha." tana rufe baki ɗau jakarta ta rungumi Yarima ta fito, lokacin da suka fito ita da baiwarta a lokacin tuni Sauran Matan Sarki sun fito tsayuwarta babu jimawa sai ga Fulani Zaliha ta fito rungume da Saif a hannunta. Mai martaba na fito daga turakarsa ya ƙare musu kallo Fuska a ɗaure ya kalli Fulani Zaliha ya ce. "Ina zaki da yaron hannunki?" Fulani Zaliha bata kawo komai a ranta ba ta ce. "Allah ya taimake ka gurin rasuwar da ka bada umarnin zuwa"

   Sarki Aminullah yace. "Ki mayar da shi ciki" a firgice ta ɗago da kai ta ce. "Bangane ba ranka shi daɗe" Sarki Aminullah yace. "Abinda na faɗa da farko, ya za'ayi mu tafi da nakasasshen yaro cikin jama'a" idanun Fulani Zaliha ne suka ciko da ƙwallah nan take ta fara hawaye, Mai martaba bai jira cewarta ba ya wuce ya barta a gurin. Babu wacce ta tanka mata haka suka wuce suka barta a gurin, Fulani Maryama dukda tana cikin halin jimami hakan bai hanata jin zuciyarta fes ba saboda ko ba komai tasan batayi asarar mahaifi a banza ba. Kafin ta ƙarasa tuni Mai martaba ya shiga cikin motarsa itama ta wuce motar da su Fulani ta suka shiga, suka ɗauki hanyar tafiya. Motar da suke ciki mota ce irin ta wancen lokacin me shige da fasalin Ladi ba ɗuwawu, tafiya sukayi me nisa har suka ƙarasa ƙasar Gombe.

     Kwanan su ɗaya a masarautar Gombe suka juyo gida duk wanda yaga irin kukan da Fulani Maryama take yi sai ya matuƙar tausaya mata, Fulani Zaliha kuwa duk a ɗaɗɗare take kasancewar ta lura da Mai martaba kamar fushi yake da ita, ko gaishe shi tayi ciki-ciki yake amsawa a haka har suka dawo gida zuciyarta a dagule musamman idan ta tuna da abinda Mai martaba ya gaya mata. Tun daga ranar kuwa Sarki Aminullah ya daina shiga sabgarta da ta Saif, shi da ita sai dai kadaran kadahan babu wata kyakkyawar alaƙa a tsakaninsu, ko turakarsa ta zo da Saif zai ce mata ta mayar da shi. Haka Fulani Zaliha ta ci gaba da ƙunsar baƙin ciki idan abun ya yi mata ciwo sai dai ta shiga ɗaki tayi kuka me isarta, cikin dare kuma bata fasa kaiwa Allah kukanta ba haka ta duƙufa ba dare ba rana ta fauwalawa Allah lamuranta. A haka rayuwa ta cigaba da gangarawa har aka shefe shekara biyar sai a wannan lokacin cikin ƙudura ta ubangiji ta fahimci Saif ya fara koyon zama dukda har ya kai waɗannan shekarun bata fasa koya masa zama ba, kuma bata fasa kaiwa Allah kukanta ba. Babu wanda ta gayawa kuma a ranar da ta ga haka ba ƙaramin murna tayi ba, a cikin ƙasa da wata huɗu zaman Saif yayi ƙwari dan a yanzu tana iya zaunar da shi ta tafi aikin gabanta, har sai da zamansa yayi ƙwari sannan wata rana suna zaune da Mai martaba ta sanar masa. Ga mamakinta sai ta ga bai yi wani murna ba dama kuma batayi tsammanin zai nuna jin daɗin nasa ba, tun da yadda ta lura ba wani ji yake da shi ba ko dan shi nakasasshe ne oho, saɓanin Salman da yanzu duk inda Mai martaba yake yana gefensa. Shikuwa Saif sai ya shafe sama da sati biyu basu haɗu da Mahaifinsa ba, saboda ko kaɗan Baya ƙaunar Fulani Zaliha ta raɓo shi da shi. Sarki Aminullah shi kansa abinda yake yiwa yaron yake damunsa sam baya jin daɗi a ransa wani lokacin  abun har damunsa yake yi, sai yayi kamar yace a kawo masa Saif sai kuma yaji sam baya ƙaunar ya raɓe  shi, a wannan lokacin Saif na da shekara shida yayinda Salma yake da shekara bakwai a duniya, Fulani Maryama babu wani abu da yake damunta a yanzu saboda bata da wani abu da zai ɗaga mata hankali, tun da ba ita kaɗai ba hatta sauran mutanen da ke cikin masarautar sun san fifikon da Sarki Aminullah yake yi tsakanin Saif da Salman.

     Lokacin da Saif ya kai shekara goma lokacin ya ƙara girma sosai kammaninsa dana Sarki Aminullah ba ƙaramin ƙara fitowa sukeyi ba, a wannan lokacin cikin ikon Allah ya fara jan ciki a haka yake zuwa duk inda yake san zuwa a sashen mahaifiyarsa, dan ma ta hanashi fita saboda bakin mutane da ƴan tsegumi yana fita ake dandazon zuwa kallansa, da ƙyar Fulani Zaliha ta shawo kan Mai martaba aka samo me koya masa karatu, da farko Sarki Aminullah faɗa ya rufe ta da shi lokacin da ta sameshi da magananar. Sai da ya gama sauraronta yace.
   "Haba Zaliha ke meyasa kin fiye fitina yaron da yake a nakashe ta yaya zai iya koyan karatu?" Fulani Zaliha ta ce. "Allah ya taimakeka hakan ba yana nufin zamu barshi haka babu ilimi ba tunda yaron nan ba ciwon hauka yake yi ba kuma babu abinda ya samu ƙwaƙwalwarsa, Allah ne ya hallitoshi haka ba dan baya ƙaunarsa ba, yaron nan ba kurma bane duk abinda nake faɗa yana jina kuma wata baiwa da yake da ita duk inda na aikeshi a ɗakina kome nace ya ɗauko min zaije ya ɗauko min, kana ganin idan muka barshi babu ilimi Allah bazai tuhumemu ba Mai martaba? Dan Allah idan ma bazaka ja shi a jikinka ba saboda nakasarshi ka taimaka masa ya samu ilimin bautawa Ubangijinsa, Amma ina tuba gurinka bansani ba ko kalamaina sunyi ƙushi" ta ƙarasa maganar tana zubda ruwan hawaye. Mai martaba shiru yayi yana jin tausayinta cikin zuciyarsa yake ayyana  tabbas yasan abinda ta faɗa gaskiya ne sai yaji gabaɗaya bai kyautawa kansa ba, janyota yayi jikinsa ya rungume ya fara lallashinta ya ce. "Ina ji a jikina sam ina aiwatar da rashin adalci amma ni kaina bansan me yake damuna ba, na rasa sanda na zama haka dan Allah ki dinga taimaka mun da addu'a kinsan mijinki da ba haka yake ba, Dan Allah idan ina cutar da ku ki yafe karki bari Ubangiji ya kamani da laifin da bansan ina aiwatar da shi ba." Ɗagowa tayi ta kalli ƙwayar idanunsa tabbas tasan da ba haka yake musu ba ita da ɗanta, idan batasa son zuciya ba zata iya cewa duk cikin matasan yafi ƙaunarta, idanunta ne suka cigaba da kawo ƙwalla murya a sanyaye ta ce. "Ina yi maka addu'a a duk lokacin da na sanya goshina a ƙasa nayi imani da Allah addu'a ta bazata taɓa faɗuwa  a banza ba, Allah zai kawo mana mafita kuma nida ɗana bamu taɓa ƙullatakar a zuciyarmu ba" Lumshe idanunsa yayi cikin jindaɗin kalamanta yace. "Insha Allah zan sa a kawo Malami ya dinga koya masa karatu shikenan" murmushi tayi tana gyaɗa masa kai sannan suka cigaba da hira.

   Tun daga ranar aka samowa Saif Malamin da yake zuwa yana koya masa karatun addini dana boko, kuma sosai yake ganewa dan dai bashi da baki da yake mayar da karatun da aka biyasa ne, Saif Allah ya bashi basira ita kanta Mahaifiyarsa har mamaki takeyi idan yaji muryarka sau ɗaya ya gane ka, kuma yana daga kwancen nan yake taya mahaifiyarsa wasu ayyukan, ya lura Mahaifinsa bayasan ya dinga ganinsa a fada hakan ne yasa ya ganje jikinsa sai ya shafe wata guda bai halarci fada ba idan yaje ma Salman ya dinga hantararsa kenan yana ƙyararsa daga ƙarshe ma har suna ya sa masa kwantaccen. A haka rayuwa ta cigaba da gangarawa da daɗi babu daɗi har aka shafe wasu shekaru masu yawa.

   BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYU

      Wata rana Sarki Aminullah ya tafi ɗaurin aure ƙasar Adamawa a hanyarsa ta dawowa  suna tafe a mota shida dogarawa uku tayar motarsau ɗaya ta fita, duk yadda direban motar yaso dakatar da motar hakan bai yuwu ba saboda kan motar ya kwace masa, da sauri motar bayansu tayi parking wacce sauran dogarawansa ne a ciki, Motar su Mai martaba cikin daji ta shiga bisa tsautsayi ta dinga bi ta kan wasu masu Fulani  sai da ta kai ga wata bishiya sannan motar ta mutu, wani ikon Allah Sarki buguwa kawai yayi a kafaɗa sai gocewar ƙashi da yayi a ƙafarsa, Direban motarsa ne suka  ya samu karaya sauran mutanen motar kuma duk buguwa ce. A hankali ya buɗe motar ya fito kasancewar jin koke-koken yaran da motarsu ta bige.

    Kafin ya ƙarasa tuni Dogarawan ɗayar motar sun nufo gurin da suke da sauri suka kama Sarki Aminullah suna masa sannu, cikin galabaita yace. "Ku ƙyaleni kuje ku duba bayin Allahn cen" da sauri suka ƙarasa gurin suka samu mata Huɗu a akwance sai ƴaƴayensu uku da suke kuka Cen gefe suka hango wani bafulani da alama iyalansa ne jini na zuba ta kansa, Sarki Aminullah ne ya kira jami'an tsaro na garin Kano ya sanar dasu halin da ake ciki, ba'a ɗauki Jami'an tsaro na garin da suke suka ƙaraso tare da motar asibit suka kwashe su gabaɗaya zuwa asibiti.

     A cikin mutanen da motar Mai Martaba ta bige mace ɗaya ce ta rayu, sai ƴaƴansu biyu suma kuma basu ji wani ciwo sosai ba, Mai martaba ya bada umarnin a wuce dasu gida a haɗasu da uwar bayi. Su kuma sauran gawarwakin tare aka yi musu suturu Mai martaba da kansa ya sallace su aka kai su makwancinsu.

     Daga cikin Waɗanda aka wuce da su gida Akwai Inna Habi sai Maryu da Abu, tunda aka doshi shiga gidan sarautar Maryu ta fara ganin wata irin walƙiya na hasawa tana giftawa har tana neman kashe idonta, kanta ne yayi mata wani dummmm ga jiri da yake neman ɗaukanta, suna shiga cikin gidan kanta ya hau sarawa nan take zazzaɓi ya rufeta, sama-sama take jin kamar hayaniya akanta amma tana waigawa babu waɗanda suka hayaniyar babu alamarsu.

😄😄TO FA YANZU WANSAN ZAI FARA ƊAUKAN ZAFI😄😄

_UMMOU ASLAM BINT ADAM_😉

Ga verder met lezen

Dit interesseert je vast

Beyond Times Door Woody

Historische fictie

101K 6.2K 57
-"And where do I reside?" -"You reside in my heart, Priye!" Two broken souls, who endured pain and loneliness all their life. Destiny united them and...
94.2K 5.7K 65
"I spent half of my life away from you and in every step, in every moment I thought about you and moved forward, knowing you would be proud" ...
15.8K 1.3K 35
Disclaimer: this is a work of fiction. Every characters (beside my OCs) belongs to Maharishi Ved Vyas. "RAGHUKUL REET SADA CHALI AAYI, PRAN JAYE PAR...
Erica Door Sam

Historische fictie

2.9M 159K 88
They say her voice was once bewitching to all who heard it. She was like a siren luring sailors to their deaths on quiet nights... Those are just rum...